Littafan Hausa Novels

Man of the world Hausa Novel Complete

Auren Yarinta
Written by Hausa_Novels

Man of the world Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

Man of the world Hausa Novel Complete

Book 2

 

 

3️⃣5️⃣➡️3️⃣6️⃣

 

 

Yana ɗaura haɗaɗen rolex a hannunsa kamar kullum ba wanda ya tarar a falo se Meemah datasha uwar kwalliya kamar wadda zata gasar kyau abinka da miskilin mutum ya fiske kamar besan da zaman wata halittaba yayi hanyar waje cikin ƙissa ta miƙe haɗe da cewa”Ya Abdallah kaifa nake jira mutafi su Mum duk sun tafi airport ɗin”.

ba tare dayabi takanta ba ya cigaba da tafiyarsa abunsa ganin be kulata ba yasata ta fita cikin sauri tabi bayansa lokacin data fita har security ɗinsa sun buɗemasa sabuwar G-box ɗinsa yana niyyar shiga cikin sauri ta ƙarasa gurinsa tana niyyar shiga kallo daya jefeta dashi ne yasa ta fasa shiga ya shige abunsa har Sani driver ya tada motar yaji Man of the world cikin husky voice ɗinsa yace”tashiga motar security mutafi”.

“okay Sir”.

nanya fita bejimaba ya dawo ya tada mota suka fara tafiya .

 

Romantic Hausa Novels Complete

 

Jingina yayi da jikin kujera ya rasa meke damunsa akanta daya rife idanunsa ita yake gani wani sashi na zuciyarsa se tsunkuninsa yake kan yaje gurin aiki koze ganta wani murmushi ne ya suɓucemasa ya rasa na menene a fili yace “wai meke damuna ne narasa dalilin dayasa dana rife ido ba wadda nike gani se wannan yarinyar anyako ba mayya bace”.

tsaki yayi sakamakon duk yanda yaso kauda tinaninta zuciyarsa ta hansa har suka isa airport yanata tsaki bemasan sun iso ba sakamakon duniyar tinani daya lula suna isa cikin nutsuwa Sani driver yace”Sir mun iso”.

firgigit ya dawo daga duniyar tinanin daya shiga yace”ok “.

yafita yazagaya ya buɗemasa a hankali ya zuro haɗaɗɗen takalminsa waje gabaki ɗaya idanun mutanen gurin na kansa kowa so yake yaga wanene ze fito daga motar sake zuro ɗaya ƙafar yayi ya fita baƙaramun ɗaukar hankalin matan dake gurin yayiba yafara cikin takun zaratan maza ko takan Meemah bebiba yana shiga cikin gurin ya tadda Rahma rungume jikin Granny tana ganinshi ta saki Granny ta ruga da gudu tayi kansa shima a nashi ɓangaren buɗemasa hannuwa yayi alamar ta taho garesa hakance takasance kuwa tana zuwa ta rungumesa cikin murna ƙara rungumeta yayi tsam a ƙirjinsa yanajin wata irin ƙaunar ƙanwartasa na ƙara shigarsa sun daɗe a haka kafin su saki juna yakama hannunta murmushi Ammi tayi tare da cewa”ja’irar yarinyar badai ni kikaiwa haka ba kan wannan sangamin zakizo ki sameni ina zaune a shararren gurina nima bazan kulaki ba kuma kya koma gurin sangamin kifara kwana badai ɓangarena ba kije can duk abinda ze cinyeki ya cinyeki banda asara tunda dai ba ɗana ya cinye ba”.

dariya gabaki ɗaya gurin sukayi hadda Mommy dake ta faman yaƙe Abbih yace” yau kuma keda ƙawar taki ake jin kanku kuma”.

“eyi aiwai ita me ɗan uwa tana ganinshi ta sakeni tayi gurinsa”.

dariya Rahma tayi tace”tuba nike ƙawata nike Ammina”.

taƙarasa faɗa tana me kama kunnenta alamun bada haƙuri nan suka ɗunguma suka shiga motocinsu seda zasu shiga mota Rahama ta lura da Meemah nan taita farinciki suka shiga mota ɗaya suka nufi gida.

 

 

 

Tsaye suke a bakin titi suna jiran me napep Inteesar tace”Aunty sekuma yaushe zaki dawo”.

ɗaga kai sama Badi’ah tayi alamun tinani sannan tace”jibi zan taho sekuma Allah yakaimu biki ya tashi”.

“kai Aunty dan Allah kizo da wuri”.

“ki kwantar da hankalinki insha Allahu da wuri zanzo”.

“yauwa Auntyna”.

tunda suka fara magana Jameelah ke sakin wani shu’umin murmushi wanda ita kaɗai tasan ma’anarsa karaf sukayi iso huɗu da Khadijah dake ƙoƙarin tsaida me napep harara suka sakarma juna kwafa Khadijah tayi nan suka yi sallama da Aunty Badi’ah tashiga napep sukuma suka juya saurin yin gaba Khadijah tayi tabarsu binta sukayi da kallo gabaki ɗayansu suka cigaba da tafiyarsu har suka isa gida.

 

 

 

Suna shiga gida Jameelah taƙara narkewa tayi kalar tausayi alamu batason binsu saboda aga laifin Khadija sosai ran Inteesar yakai ƙololuwar ɓaci ganin yadda Khadijah keta ware Jameelah tana ɗari-ɗari cikin muryar kalar tausayi tace”Aunty Inteesar se anjuma”.

“kitaho mutafi man”.

“a’ah Aunty banason ina hana ƴar uwata sakewa naga Khadijah kamar batajin daɗi”.

“rabu da ita sakarai ce batasan nata ba zanji da ita”.

“dan Allah Aunty karkiyimata komai domin banason ranta yana ɓaci ata dalilina”.

taƙarasa faɗa tana mai shigewa ɗakinsu sosai tabasu tausayi tana shiga ɗaki taɗan leƙo taga yadda duk ransu yaɓaci dariya tayi tare da cewa”gaskiya Ummah naga plan ɗinnan naki yana tafiya yadda yakamata”.

“nidai abinda nike so dake kiƙara shigewa jikinsu harki samo lambarsa daga nan aiki yaƙare”.

“ai anjumannan zanje insaci numbersa a wayarta zasu gane kurensu dangin matsiyata kawai”.

“yauwa tawan”.

nan sukaita hirarsu ta tsara plan ɗin da zasu mallakeshi.

 

 

 

“Kewai Khadijah wacce irin mahaukaciya ce ya yarinyar nan tana binmu sauda ƙafa amma ke kina nunamata rashin ƙauna ƙiri-ƙiri Ummih wallahi bakiga yadda yarinyar tabamu tausayi ba saboda yarinyar ta natsu taita nunawa Khadija soyayya amma tayita wulaƙantata”.

“wallah Ummih ba tuban Allah da Annabi tayi ba ɗazu ina kallonta tana harar Aunty yazanyi in nike inso wanda kullum ƙoƙarinsa yaga bayana nikuma ina ƙara shigemasa kamar wadda batasan ciwon kanta ba “.

yin kanta Inteesar tayi a harzuƙe zata doketa saurin ɓoyewa bayan Ummih tayi tana huci tace”ni kike faɗama bansan ciwon kaina ba Khadijah saboda kin rainani to wallahi senayi maganinki matsawar baki fita daka harkata ba mara mutunci kawai”.

“wallahi bazan fita daga harkarki ba Aunty ina na fita daga harkarki wazan kula”.

dakatar dasu Ummih tayi ta hanyar ɗaga musu hannu tace”ke Khadijah banason rashin kunya meye dan ƴar uwarku tabiku ai duk arziƙine wallahi idan baki dena wannan halin naki ba watarana sena karyaki sakarai kawai kuma naƙara ganinkinmata wani abu zakiga yadda zanmiki wallahi”.

nan Ummih tayita yimusu faɗa ana cikin haka wayar Inteesar tayi ƙara dubawa tayi taga sunan Pure one na yawo akan screen ɗin wayar murmushi tayi tare da ɗagawa tayi tare da cewa” salamu Alaikum ina yini”.

daga ɗaya ɓangaren ko amsa gaisuwarta beyiba kamar wani mejin haushinta yace”!!!!!!!!!!!!!

 

 

 

 

 

*MAN OF THE WORLD*

Sighn and update by Real eeshow

 

 

 

_Dan Allah sisters mukasance masu riƙe amanar juna dan Allah idan kinsan baki biyaba karki karantamun idan kuma kinbiya dan Allah karki fitarmun._

 

 

 

 

 

_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_# Real eeshow

 

 

 

_*Paidbook ,Amount Nml grp 300,Vip 800, pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga ƴan Niger kuma zaku turo da katin Airtel na daidai kuɗin da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki ta wannan number 08108362334.*_

 

 

Book 2

 

 

3️⃣7️⃣➡️3️⃣8️⃣

 

 

“ki fito muna jiranki a ƙofar gidanku”.

ya gimtse wayarsa ba tare dayaji tabakinta beyiba shiru tayi tashi ga duniyar tinanj taji muryar Ummih tace”lafiya kike tinani mamana”.

ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da ƙaƙalo murmushin yaƙe tace”bakomai Ummih ba tinani nake ba”.

“kidena saka abubuwa a ranki dukkan tsanani yana tare da sauƙi kuma haƙuri baya taɓa faɗuwa ƙasa banza komai kikaga yafaru da bawa to da sanin Allah kimiƙawa me duka komai dake damunki insha Allah bazaku tama wofanta ba kedai a kullum ina muku nasiha daku riƙe gaskiyarku da amsar ƙaddararku hannu bibiyu”.

“insha Allah Ummih na”.

Ummih zatayi magana kenan Khadijah tace”Ummih wai Abbah har yanzu beyimiki zancen kayan ɗakin Aunty bane naga har yau ba’ah saimata ko tsinke ba gaskiya Abbah baya kyautawa da bikin Jameelah akeyi da yanzu yashiga ya fita yayimata”.

“kewai wacce irin me kunnen ƙashi ce ne da bakyajin magana ne iyi meye naki akan kayan ɗakin ko dole se anyi kayan ɗaki ake aure”.

ɗage labulen ɗakin Abbah yayi har yana huci yace”yayi munafuka to yaudai Allah yakamaki wato idan nafita tara ƴaƴanki kike kina ƙona namana to banyafe ba suɗin da kike kaiwa ƙarata me suka isa suyimun bakuma zanyi ko zare ba inkinyi zuciya kiyimata naga abinda yazama dole”.

 

 

 

 

Miƙewa Imteesar tayi tana gyara zaman hijab ɗinta dakamata tsawa Abbah yayi haɗe da cewa”kee kuma ina zaki”.

jiki na rawa tace”shine yazo yana waje”.

washe baki Abbah yayi yace”toh toh shine kuma kika tsaya san iyawa kika shanyashi”.

“ba shanyashi nayi ba Abbah yanzu ya kirani”.

“toh sarkin tsari kota ina aka ɓullomiki sekinsan yadda zaki kare kanki”.

muryar Uwar Gwarama sukaji tace”kaima dai Malam aikasan an tsotsa a mama yaza’ayi barewa tayi gudu ɗiyarta tayi rarrafe ai halin uwarta halinta har son nuna ita ta Allah ce fir’auna a zuciya duk ita ta biyo”

“saura kuma inya baki kuɗi ki ɓoye kiga yadda zanyi dake”.

“gwara dai ka gayamata domin tana iya maƙalewa ta kawowa uwarta”.

jiki a sanyaye ta fice sukaci ka haɗu da Jameelah na fitowa daka ɗakinsu tana ganin Inteesar ta wani wage baki tace”Aunty dama yanzu nake shirin zuwa gurinki”.

“Allah ko “.

“eyi wallahi inason intura whatsapp ne nawa yayi expired”.

“aiko fita zanyi Sis sede nabaki wayar idan kingama turawa ki ajemun”.

wani farin cikine ya mamaye zuciyar Jameelah a zuciyarta tace”yau zan samu cikar burina daka yau keda Zaid har abada shegiya tsinanniya sarkin rashin wayo”.

a fili kuma murmushi tayi tace”Yah Zaid ɗinne yazo ne Aunty naga irin wannan wankan haka ai wannan sekisa ya kifa Aunty”.

miƙamata wayar tayi haɗe da yin murmushi tace”kudai bakwa rabo da shiririta ingoni sena dawo”.

taƙarasa zancenta tana ciremata password ta miƙamata ansa tayi tare da sakin wani shu’umin murmushi tace”adawo lafiya Auntyna maganin kukana”.

murmushi kawai tayi ta wuce abinta tanajin wata irin ƙaunar ƙanwarta na shigarta.

 

 

 

Tana fita ta hangeshi tsaye shida babban amininsa Muhseen sun haɗe cikin ƙananun kaya sunyi matuƙar amsar jikinsu sunyi sharr dasu cikin nutsuwa take tafiya kamar wadda take tausayin ƙasa tsaki Zaid yayi ya shige cikin motarsa cikin masifa yace”baza ka taho mutafi koko haifarmu tayi da seta gama isarta zata fito kamar wata uwarmu nina ƙiji jinin baƙin wulaƙanci ko wani abun mukazo nema gurinta da zata rainamana hankali sannan tabamu”.

“anya ko Zaid hankalinka ɗaya Inteenka cefa”.

a zafafe yace” koma wacece da Allah Malam ka taho mutafi inbazaka shigoba ni zan wuce”.

“to Invitation ɗinda zamu batafa”.

“nafasa ko dolene satayi gayyar kashigo mutafi”.

ganin Muhseen bashi da niyyar shiga ne yasa yiwa motar key ya tafi a guje tare da bulamusu uwar ƙura mamakine yakama Muhseen a zuciyarsa yace “anya ba wani abun Inteesar tayiwa Zaid ba kuwa domin naga kwana biyunnan koson inyimasa maganarta bayayi wanda da har so yake ayimasa zancenta gaskiya da abinda yake faruwa bara inji tabakinta koma meke akwai zanji”.

jiki a sanyaye taƙaraso gurin nunawa tayi kamar bataji duk abinda ke faruwa ba a tsakaninsu ba cikin girmamawa tace”ina yini Yah Muhseen”.

sakarmata murmushi yayi haɗe da cewa”amarya bakya laifi kokin kashe ɗan masu gida lafiya ƙlau”.

murmushin yaƙe kawai tayimasa haɗe da cewa”hmm haka dai kace Yah Muhseen amma ni ai bankai ba”.

“harma kin wuce domin ninasan halin kayana mekika yiwa abokinane naga yaƙi tsayawa”.

“hmm wallahi ba abinda nayimasa “.

“tino dai domin hakanan baze riƙa jin haushinki ba daliliba”.

shiru tayi secan tace”wallahi nidai a iya sanina ba abinda nayimasa”.

“ok zan tambayeshi inji dama zuwa mukayi mu tambayeki events nawa zaki sekuma iv ɗin ɗaurin aure da zamu baki yaƙi tsayawa “.

baƙaramun sanyi jikinta yayiba sakamakon jin abubuwan dataji Zaid na faɗa akanta ta girgiza kai haɗe da cewa”ba abinda zanyi Yah Muhseen “.

waro ido Muhseen yayi hakan dayayi seda yabawa Inteesar dariya yakama baki yace”haba ƙanwata baki isa ba kinko san yadda muka daɗe muna jiran wannan ranar ta bikin Zaid kuwa da zakice haka “.

“a’ah wannan dole mutumina yariƙa jin haushinki walkahi ace biki kamar na Zaid ba’ayi komai ba sekace bikin bazawara to bazeyiwu ba dole ki faɗi abunda za’ayi inke bazakiyi ba mu zamu haɗa dakanmu”.

“toh nidai Yah Muhseen walimah kawai zanyi sauran kuma nabarmaka komai a hannunka duk abinda kace haka za’ai”.

“ok yanzu kika yi magana zan tsara komai insha Allahu”.

“tom “.

“yauwa gobe zan dawo tunda kinga jibi za’ah fara biki gobe zamuzo mu kawomuku kuɗin ƙunshi koma dai meke akwai zamuyi waya ina Tweeny ɗin taki”.

murmushi tayi tace”tana gida inkirata ne”.

“a’ah kibarta nakirata a waya muji schedule ɗin ita data tsara”.

“toh “.

nan yayimata sallama yana mamakin canzawar aminin nasa lokaci ɗaya shiga gida tayi shikuma ya wuce.

 

 

 

 

Zaune yake akan haɗaɗiyar kujera system nakan cinyarsa yana operating ɗinta tashigo ɗakin ko ba’ah faɗaba yasan ba wanda ze shigo masa kai tsaye se Sweetheart ɗinsa da gudu taƙaraso inda yike tare da yin hugging ɗinsa ta baya tace”I miss you Ya Abdallah”.

sauke system ɗin dake kan cinyarsa yayi tare da cewa”miss you too dear ina zaki kika sha wannan wankan haka kamar wadda zata gasar kyau”.

yaƙarasa faɗa yana jan kumatunta kyalkyalewa tayi da dariya tare da cewa”shan ice cream zaka kaimu sannam inaso inyo shopping ɗin wasu abubuwa”.

murmushin daya ƙara yimasa kyau yayi hakan yasa Meemah dake tsaye tana kallonsu ƙara narkewa a duniyar ƙaunarshi yace”menene wasu abubuwa kiyi list kibada su Abubakar su siyomiki man Sweetheart kinga kingaji da yawa ki huta”.

cikin shagwaɓa tace”Allah Allah ni bangaji ba ka shirya ka kaimu yaushe rabona da ƙasar please Bro”.

jamata kumatu yayi tare da cewa”toh shagwaɓatuna bara na shirya muje kizauna a falo kijirani”.

yaƙarasa zancensa tare da kallon bakin ƙofa Meemah yagani tsaye ta shagala da kallonsa ɗaure fuska yayi kamar be taɓa dariya ba tsallen murna Rahma tayi tare da cewa”seka fito Bro dan Allah fito da wuri domin so nike mu zagaye garin Abuja”.

“toh “.

nanta miƙe cikin farinciki suna haɗa ido da Meemah yajefeta da wani kallo tafice ba tare data shiryaba.

 

 

 

 

Cikin wata dakakkiyar gizna yafito brown se ɗaukar ido take baƙaramun amsar jikinsa shadda tayi ba abinka da cikakken namiji me jini a jika daɗan sassarfa yake sakkowa daga stair zaune yasamu su Mummy suna hira Rahma naganin sakkowarsa ta miƙe zumbur tare da cewa”tashi mutafi Sis ga Yayah nan”.

mumrmushi Mummy tayi tare da cewa”toh ƴar gidan Yayah se tafiya ko to adawo lfy”.

“Allah yasa Mum”.

cewar Meemah murmushin gefan baki yayi tare da cewa”Mum semun dawo”.

“toh adawo lfy kardai ayi dare”.

“insha Allah “.

yafaɗa yana tafiya nansuka tafi.

 

 

 

Tsaye suke a gurin jeweleries suna dudubawa juyamusu baya yayi yana waya yana katse wayar ya juya yana bin jeweleries ɗin gurin da ido sexy eyes ɗinsa ne ya sauka kan!!!!!!!

 

 

 

 

*Wannan littafin na kuɗine inbaki biyaba dan Allah karki karantamun inkuma kinbiya dan Allah karki fitarmun mu riƙe amanar juna Sighn and udate by Real eeshow MAN OF THE WORLD*

 

 

 

Votes and comments

 

 

 

_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_# Real eeshow

 

 

 

_*Paidbook ,Amount Nml grp 300,Vip 800, pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga ƴan Niger kuma zaku turo da katin Airtel na daidai kuɗin da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki ta wannan number 08108362334.*_

 

 

Book 2

 

 

3️⃣9️⃣➡️4️⃣0️⃣

 

 

 

Wasu diamond necklace se ɗaukar ido suke guda biyu iri ɗaya baƙarmun kyau suka yimasa ba hakan yasashi kai hannu ya ɗakkosu jin muryar Rahmah yayi tace”wow Yayah ya akai idanunka ya hangomaka wannan haɗaɗen necklace ɗin ba tare damu mungashi ba”.

“baku da ido “.

“hhh kaji Yayah bani dan Allah”.

satar kallon Meemah yayi ta gefan ido yaga yadda ta tsaresu da ido tanata zabga smiling murmushin gefan baki yayi tare da cewa”gashi”.

ansa tayi tare da cewa”wannan ta hannunka fa “.

yana lumshe sexy eyes ɗinsa kyakyawar fuskarta yagani lokacin daya kamata tana ma hotonsa kiss sake tinowa yayi da lallausan lips ɗinta daya yiwa kiss batare daya sani ba murmushi ya suɓucemasa bazato yana duniyar tinani yaji karaɗin muryar Rahama tace”gaskiyane Yayah niko zanso inga Auntyntinnan tawa me sa’ah haka datayi wuff da zuciyar ɗan uwana lokaci ɗaya haka naga ka mutu akanta haka amma ko wacece me sa’ah ce zanso ganinta dan nasan ɗan uwana bazeyi zaɓen tumun dare ba nifa harna ƙagu danaga photonta dannasan ba baya bace Yayah meye sunanta “.

murmushin dabe shirya yinsa bane ya suɓucemasa ya shafa yalwataccen sajensa tare da satar kallon Meemah daketa faman doka murmushi a tinaninta ita yake nufi murmushin gefan baki yayi haɗe da cewa”ina ruwanki zata bayyana nanda lokaci ƙalilan kedai kullum ki wanke ido domin nasan kema zaki yaba da ita 100%”.

 

 

 

 

 

Wani farin cikine ya lulluɓe zuciyar Meemah a zuciyarta tace”ashe dama shima yana sona yaketa jamun aji yana nunamun kamar bayasona nifa dama nasan yana sona domin duk wani namiji me lafiya ya ga irin shigar da nikeyi dole hankalinsa ya tashi aiko yanzu zan fara nunamaka zallar ƙauna ashe dama bason wannan kucakar yarinyar yakeba kenan dole inzo inzage gurin nunamaka zallar ƙaunar da nike maka”.

jitayi Rahama ta taɓata tare da cewa”yadai Sis tunɗazu naketa magana kinyi shiru koke bakyason kiga matar da Yah Abdallah ya mutu akanta ne”.

“inaso inganta man Sis”.

riƙe ɗaya sarƙar yayi a hannunsa ba tara daya saka cikin kayan siyayyarba suka nufi gurin biyan kuɗi suka biya suka nufi hanyar oasis.

 

 

 

Ɗaure yafito da towel a ƙugunsa hannunsa kuma ƙaramin towel yana sharce gashin kansa ta mirrior ya ga abokinnasa kama haɓa yayi alamun mamaki yace”mutumin shine zaka ƙaraso koka taɓani”.

harara Muhseen ya maka masa tare da cewa”yanzu ai seka koma tunda nima bakason ganina”.

“nina isa ince banason ganinka”.

“harma kayi yawa tunda ka iya tozartani a idon duniya muje gurin yarinyar nan domin bata invitation shine sekace wanda ze bar gari kashiga zazzaga ruwan masifa ta inda kake shiga batanan kake fita ba kafin ta ƙaraso kabar gurin aini a tinani ko wani abun tayimaka bekamata koni na sani ba seka hukuntata iya kaida ita shine so na haƙiƙa bakazo kana tozartata a gaban kowa ba idan ni kayi a gabana ai wani be kamata kayi a gabansa ba domin su magauta haka suke so yarinyar nan ko mara haƙuri ce bekamata kayimata haka ballema ita bameson fitina bace dan Allah abokina abinda nakeso dakai koda wani abun tayimaka kariƙa bari daga kai se ita seka nunamata abinda tayi ba daidai bane seta gyara ba tare da wanima yaji abinda kuke cikiba”.

zama Zaid yayi kan kujerar gaban dressing mirrior tare da cewa”zancen gaskiya ba abinda yarinyar nan tayimun abokina kawai lokaci ɗaya naji na tsaneta koson ganinta banayi kai datake matsowa bakaji wani shegen wari na fita daka jikinta ba kamar jaɓa zahirin gaskiya kuma banajin zan iya rayuwa da ita domin se yanzu nagane ba ajina bace Jameelah ce daidai da class ɗina”.

 

 

 

 

A gigice Muhseen ya ɗago jin furucin abokinsa murya na rawa yace”anyako Zaid kana cikin hankalinka kuwa Jameelah fa ƙanwar Inteesar wanne irin mummunan abu kake ƙoƙarin aikatawa haka”.

duƙawa Zaid yayi a gaban Muhseen kamar wanda zeyi kuka yace”niko nasan menake cewa Muhseen zancen gaskiya bazan kwari zuciyata ba na tilastata kan abunda bataso ba dan Allah ina roƙonka daka tayani neman mafita domin idan na rasa Jameelah wallahi zan iya samun babbar matsala Inteesar kuma dan Allah kazo muje nabata haƙuri domin gaskiya yanzu bana ra’ayinta……”.

cikin tsananin ɓacin rai Muhseen ya bugamasa tsawa tare da dakatar dashi da hannu yace”nagaji da jin wa’innan miyagun kalaman naka marasa daɗi kuma bari kaji infaɗamaka karka indai seda sa hannuna zaka samu Jameelah wallahi bazaka taɓa samunta kuma daka ranar daka aikata wannan mummunan aikin da kake ƙoƙarinyi karka ƙara nuna kasanni domin ni bazan iya rayuwa da mutum butulu irinka ba mayaudari wanda besan abinda kemasa ciwoba mezaki da ragowar maza yarinyar daba abinda tasani sebin maza”.

a zafafe Zaid yaci kwalar Muhseen yana huci idanunsa sun rine se uban huci yake yace”kai waye da zaka riƙa faɗan munanan kalamai akan farincikina to bari kaji infaɗamaka abinda bakasani ba kan Jameelah a shirye nake dana ɓata da uban kowa dan haka iname gargaɗinka da indai kanaso mushirya dakai kaso abinda nake so “.

fizge jikinsa yayi daga riƙon da Zaid yayimasa cikin ɓacin rai Muhseen yace”ni ba kowa bane face abokinka meson ganin cigabanka amma tunda kace zaka iya ɓatawa da uban kowa kasani daka yau bani bakai kowa ya kama gabansa ko a hanya kaganni karka ƙara nuna kasanni ka manta dani a babin tarihin rayuwarka banza butulu kawai”.

a harzuƙe Zaid yace”seme ninamafi son haka sarkin takura kawai kai kaje ka aureta man shine zan tabbatar dakai ba butulu bane ɗan sa ido kawai rayuwarka ko tawa”.

nan Muhseen yafice rai ɓace tsaki Zaid yayi yacigaba da shafarshi yana gama saka kaya wayarsa dake kan gado tashiga ringing zama yayi a gefan kan gadon tare da jawo wayar hakan yayi daidai da katsewar kiran buɗe wayar yayi yashiga cal log dan duba waye mekiran wani kiran yaƙara shigowa baƙuwar number ya gani har ze jefar da wayar yafasa ya ɗaga tare da karata a kunnensa daga ɗaya ɓangaren Jameelah naji anɗaga tasaki doguwar ajiyar zuciya tare da cewa”Yah Zaid ina yini”.

jin muryarta ne yasashi lumshe idonsa haɗe da buɗe lokaci ɗaya yace”lafiya ƙlau dawa nake magana”.

yaƙarasa faɗi tare dason ƙara tabbatarwa dakansa ba gizon data saba yimasa bane murmushi Jameelah tayi me sauti wanda yaƙara narkar dashi a duniyar ƙaunarta taƙara narkar da murya tace”au Yayana baka ganeni bane ƙanwarka ce Jameelah”.

“a’aahhh kice Malama ce”.

“eh Yayah nice ya gida dasu Ummah”.

“lafiya ƙlau ƙanwata ya dalibanki”.

“Alhamdulillah ai se anjuma zasu zo Yayah”.

“ok masha Allah Malama Jameelah yaushe nima za’ah fara koyamun karatun nima”.

dammm ƙirjinta ya buga sakamakon jin ze ƙureta dakyar ta aro jarumta tace”haba Yayah aiku manyanmu ne kune masu koyamana mukuma mu koyawa na ƙasa damu”.

“a’aaah ƙanwata kice dai bazaki koyamunba dai”.

“zan koyamaka man amma ba yanzu ba dama kira nayi naji ya lafiyar Yayana”.

“aiko naji daɗi ƙanwata idan da kina free baki da wa’inda zaki koyawa karatu anjuma danazo kin rakani unguwa”.

“kaji Yayah meze hanani rakaka aiko sunzo nabasu haƙuri na tafi raka babban Yayana inmun dawo na koyamusu kazo kawai na rakaka baka da wata matsala”.

“nagode ƙanwata da kulawarki gareni idan kin shirya kiyimun flashing senazo na ɗaukeki mutafi”.

“bakomai Yayah ka taho yanzu mutafi a shirye nike nanda 8pm ma dawo”.

“toh gani nan zuwa”.

“yauwa”.

nanya kashe tare da ɗaura wayar a ƙirjinsa ya rungume yanajin ƙaunarta naƙara nunkuwa miƙawa yayi yaje bakin mirrior yaƙara turare a jikinsa tare da saka hula matching ɗin kayansa ta ɗauki wayarsa da car key ɗinsa ya nufi down stairs.

 

 

 

 

A falo yasamu Mum ɗinsa da Yasmeen zaune suna hira cikin girmamawa yaƙarasa inda suke ya langwaɓar da kansa tare da cew”Mum sannu da hutawa”.

“yauwa Son ina zuwa haka naga kasha uwar kwalliya kamar wanda zashi gasar kyau kodai gurin ɗiyae tawa zaka”.

sosa ƙeya yayi alamun kunya tare da cewa “eh Mum can zani”.

“ok idan kaje kace ina gaisheta”.

“zataji”.

Yasmeen da kanta ke cinyar Mum ce tace”Yayah wai wanne event Aunty zatayine naga guri na ƙurewa har yau bamu sani ba”.

dammm ƙirjinsa ya buga yawun bakinsa ya ƙafe lokaci ɗaya a zuciyarsa yace”bazan sanar daku gaskiyar al’amari ba domin nasan halin Mum zata iya yimun wani abun”.

yana cikin zancen zuci yaji muryar Mum tace”kayi shiru saboda tanaso tashiga cikinsu ne ayo komai da ita”.

wata dabara ce tafaɗomasa yasaki murmushi yace”Mum nima na tambayeta mezatayi tace wai ita batason ayi bidi’ah a bikinta batason komai wai idan akayi bidi’ah a biki befiye albarka ba na rasa yadda zanyi da ita dana dameta da maganarma harda yimun kuka nikuma banason abinda zeriƙa ɓatamata rai shiyasa na haƙura nima”.

 

 

 

 

 

Murmushi Mum tayi a zuciyarta tana ƙara godewa Allah daya bata kamilar suruka a fili kuma tace”aiko daughter bata isaba dole ayi ko kamune duk salahancinta kuwa ina za’ayi biki sulungudi kamar na mutuwa”.

“wlh kuwa Mum kinji Auntynnan tawani kwafsa mana data bari ansha shagali aida ba haka ba nifa harta ɓatamun rai “.

murmushi Mum tayi tace”da gaskiyarta gaskiya yarinyar nan tanada hankali shiyasa nake ƙara godewa Allah dayayimun kyautarta a matsayin suruka samun irinta a wannan zamanin se an tons kariƙa dakyau Zaid domin yarinyar bata da laifi insha Allahu zan kula da ita tamkar Yasmeen ka gaisheta kace nace dole ayi kamu”.

“zataji Mum sena dawo”.

“toh seka dawo Allah ya tsare”.

“Ameen “.

nanya fita yabar Mum da Yasmeen sunata yabon Inteesar.

 

 

 

 

Direct unguwar su Inteesar ya nufa ya tsaya daka ɗan nesa da gidansu yayi parking yayi hakan yayi daidai da fitowar Hauwah zata shiga gidansu Inteesar daga nesa ta hangi kamar motar Zaid mamakine yakamata ganin ya tsaya nesa da gida shiga gida tayi cikin sauri Jameelah dake raɓe a zaure tana ganin wucewar Hauwah cikin sauru ta fice ta nufi inda yayi parking tashiga yaja suka ɗauki hanyar oasis.

 

 

 

 

Samun Inteesar tayi ta fito daga wanka se ƙamshi ketashi sakamakon anfara yimata gyara cikin girmamawa tace”Ummih sannu da hutawa”.

“yauwa Hauwah”.

“Inteesar kunyi waya da Uncle Zaid ne naga motarsa a ɗan nesa da gidannan”.

“a’ah mekika gani “.

“motarsa nagani aɗan nesa da gidannan “.

“ko ɗaya wataƙila gurin Abbah yazo zasuyi wata maganar”.

“ƙila kuwa”.

nan suka cigaba da hirarsu batare da zargin komai ba.

 

 

 

 

Suna isa Oasis yana gama parking cikin shaukin so yace”ƙanwata bara na buɗemiki saboda banaso kina aikin wahala”.

“kaji Yayah daka barshi ma na buɗe aiki ni nake aikin abincin gidanmu gabaki ɗaya”.

“eh dai kidaibari na buɗemiki”.

“toh”.

nan ya fita ya zaga ya buɗemata suka fito suka nufi cikin gurin ɓangaren Namijin duniya ma baƙaramin siyayya yayiwa su Rahama ba shikuma yasamu seat ya zauna yasa sukayi oder duk abinda sukeso aka kawomusu bayan sun gama cine yabawa Rahama atm card ɗinsa aka ciri kuɗin abubuwan da suka siya yayi gaba suna binsa a baya necklace ɗin dake hannunsa ce ta faɗi ya duƙa da niyyar ɗakkowa kafin yakai ƙasa Zaid ya rigasa!!!!!!!!!

 

 

 

 

 

*Kuyi haƙuri Sisters bani da lafiya se yau na samu sauƙi dan Allah ku sakani a addu’o’inku .*

 

 

 

 

Votes and Comments

 

 

 

 

 

_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_# Real eeshow

 

 

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment