Hausa Novels Littafan Hausa Novels

Mai So Na Hausa Novel Complete

Hausa Novels
Written by Hausa_Novels

Mai So Na Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

MAI SONA* πŸ’žπŸ’ž

*1*

BY *Reefat Yahya*

 

Bismillahi rahmanirraheem….

*note* ~is just a short n imaginary Lov story~ *hapy reading*

 

 

Zaune take tana kallon farin watan da ya haskaka ko ina…yanayin sararin samaniya take kallo yana matukar debe mata kewa ga wani iskan dake kadawa a hnkli ta lumshe ido tana jin wani nishadi amma kash!! Rashin masoyin nata kusa da ita shine babban matsalarta a wannan lokacin a hnkli ta furta “Allah sarki *mai sona* yana raye ne oho? Idan yana raye kuma nasan dole yayi auri yana can tare da matarsa ya manta dani a rayuwarsa” wani sirirn hawayene ya fito a idanunta dai dai lokacin aka dafa kafadarta ckn firgita ta juya a hnkli tsohuwar ta xauna a gefe fuskarta dauke da murmushi “jikata kiyi hakuri ki cigaba da adua wata ran Allah xai bayyana masoyin naki idan da rabon xaku sake haduwa”ta kwantar da kanta ajikin tsohuwar tana hawaye dakyar ta rarrasheta ta daina kukan da take tana bata tarihin xamaninsu haka nan ta mance da duk wani damuwar da take cki…

Da safe ta tashi ta share gidan nasu fes tayi wanke2* bayan ta gama ta fada wanka tana fitowa a falon tsohuwar ta hadu da mahaifinta har kasa ta xauna Suka gaisa ya amsa ckn faraa da sakin fuska “er Abba yaushe zaki koma makarantar taku? “Abba IT xamuyi ba skul xamu koma bah” “toh yayi kyau Allah ya taimaka ya bada saa” “ameen nagode” daga nan tayi shigewarta daki ta shirya ckn atamfa mai kyau ta fesa turare a nan na tsaya na kare mata kallo…doguwace ba har can bah, tsayinta dai2* da jikn da take dashi wankan tarwadace tana da shape iya gwargwado ga dogon hanci se dan karamin baki , gashin idonta xara2* se kuma dimple da take dashi ga kuma wushirya masha Allah kyakkyawace ba karya ta hadu sosai.hijabi ta dora sannan ta fito har ynxu mahaifin nata yana nan hira suke da tsohuwar ta wucesu wani bangare ta shiga wata mata kyakkyawa tana rike da tea flask ta fito daga kitchen.”ina kwana umma ” “lfy ya kuka tashi ya kakan naki” “lfy alhmdllh” daga nan matar tayi shigewarta falo nan tabi bayanta tace “umma akwai aikin da xan tayaki dashi ne” “babu na rigada na gama” tayi shiru wata budurwace ta fito daga ckn dakin bacci hannunta dauke da cup da ruwa a cki se kuma brush da toothpaste “ina kwana anti maryam” ko uffan bata ce mata bah tayi ficewarta waje tayi brush se da ta gama ta dawo falon ta galla mata harara tace “nikam bansan ke wace irin halitta bace..a ckn gidan ma yawo xaki dinga mana da hijab, wllhi umma da islamiya kawai kuka turata Abba ya daina bata kudinsa a banxa don wannan batayi kama da en boko bah” “uhmm Abban naku shiyake biye mata ai nikam na rasa gane kan ruhaimat wllhi..kin fita daban ckn ya’yana ” wacce aka kira Ruhaimat ta sunkuyar da kanta kasa tana sauraronsu idan da sabone ta saba muryar maryam naji tana cewa “in banda kauyanci ya xakima mutum magana ko brush beyi bah”πŸ˜³πŸ™Š hmmm….muryar Abba Suka ji yana cewa “sannu Ya’r birni ..wllhi maryama ki kiyayeni fah,kullum ina gaya muku Ku daina sangwamarta amma Baku jin magana , kuji tsoron Allah Ku canza hali ” ya juya gun umma yace “me kuma Allah yaganar dake ..ban taba ganin wacce take sangwamar Ya’r cknta ba sai ke ,ki dai bi a hnkli ita wacce kike rainawa…

“Dakata Alhaji..nifa ba tsanarta nayi bah, ina Neman wayar da kantane sabida naga tana ckn duhu.da kke xancen na tsaneta kuma wannan kai ka janyo saboda anki a rada sunan mahaifiyata don son kai ka sanyawa taka mahaifiyar ” murmushi yayi tare da cewa “Allah ya ganar dake Halima, er Abba taho muje mu ci abinci koh” sumui2* ta tashi tabi bayan mahaifin nata umma da maryam sukabi bayanta da harara.

Mai so na

😘😘 *Reefat CE*

[1:52PM, 11/12/2016] β€ͺ+234 703 007 7024‬: πŸ’žπŸ’ž *MAI SONA*πŸ’žπŸ’ž

*2*

BY *Reefat Yahya*

 

*Asalin labarin*

Alhaji Abubakar Hammawa shine asalin sunansa..su 3 iyayensu Suka haifa , Alhaji Ahamdu shine babba yana aikin gwamnati a garin kano yana da mata 2 da yara 8. Sai Hajiya maryam wacce take aure a yola ma’aikaciyar asibiti senior nurse ce *FMC*yola yaranta 4, se Alhaji Abubakar shine auta.asalinsu mutanen garin jada ne na jahar Adamawa a can aka haifesu har suka girma.mahaifinsu Allah yayi masa rasuwa se mahaifiyarsu Hajia Aishatu wacce suke kira da Hajja Dada , Alhaji Abubakar yayi karatun primary da secondary daga nan ya fada kasuwanci har Allah ya buda masa yayi aure ya auri Halimatu er garinsu.ya’ya 6 Allah ya basu Mohammed ( Hamma).. Ahmadu..Zainab..Yusuf..maryam..Aisha ( Ruhaimat) daga nan haihuwan ya tsaya musu cak..halima taso a sanyawa Ruhaimat sunan mahaifiyarta Amma Alh Abkr ya sakawa tasa mahaifiyar sunan yarinyar daga wannan lokacin umma take jin haushin surukar tata harda ita jaririyar. Mohammed wato Hamma yayi karatunsa yana aikin banki a can kano ya auri Ya’r baffansa Ahmadu, Ahmad Wanda ake kiran tijjani yayi karatunsa shima da ya kammala degree ya fada kasuwanci yana aiki tare da mahifin nasu duk fadin garin jada ansan shagunansu ya auri wata Ya’r jada suna xaune yaransu 2,se zainab wacce take yola da aure bata aikin kome mijinta barrister ne suna da yara 2,se Yusuf ya kammala karatunsa yana bautar kasa a nan garin jada Maryam wacce take aji 4 a jamiar modibbo Adama uni of tech yola.sannan auta Ruhaimat wacce take Adamawa state uni tana aji 3 a bangaren biochemistry ynxu xasu fita IT wannan kenan.

*Cigabn labari*

Bayan sun kammala kari ita da mahaifin nata ta gyara masa falon daga nan ta wuce bangaren Hajja Dada.. tana xaune a falonta “jikalle kin dawone” “nadawo takwarata” “kin ci abinci kuwa..gashi na ajiye miki , wannan Mara kunyar yayar taki ta kawo ina tambayanta kina ina bata amsa min bah” “hmm anti maryam se a hnkli” “ko ina xata samu mijin aure da wannan rashin kunyar tata oho” dariya sosai Ruhaimat take tana ckn haka wayRta ya hau ruri “masoyiyata” sunan da tagani kenan ta daga tana murmushi “Allah sarki tawan nayi missing naki” “haba ruhi Nah shine kwana 2 ko flashing babu” “yi hakuri kinsan idan ina kusa da Hajja Dada baa cewa komai” “uhmm..wato xaki manta da kowa kenan harda *mai sona*” ckn sauri tace “a’a rufamin asiri, idan na manta da *mai sona*ai ban numfashi a duniya kenan” “uhmm..ruhi kenan har ynxu de kina nan kina fama da son mutumin da baki San ko ya mutu ko yana Raye bah” “insha Allah yana nan da ransa don ina jin ajikina na kusan haduwa dashi” “toh malama Juliet Allah ya bayyana shi” “ameen nagode” haka Suka cigaba da waya daga bisani sukayi sallama.

Karanta Masarautar Jordan Hausa Novel Complete

😘😘 *Reefat ce*

[1:53PM, 11/12/2016] β€ͺ+234 703 007 7024‬: πŸ’žπŸ’ž *MAI SONA*πŸ’žπŸ’ž

*3*

BY *Reefat Yahya*

 

Da misalin 4:30pm wani yaro yashigo yace ana sallama da Ruhaimat maryam tayi dariya tace “jeka abunka tana nan fitowa” daga nan ta tashi ta nufi bangaren Hajja Dada Ruhaimat na kwance rike da littafin *bulagul husum* tana karantawa ” malama Ruhaimat wani yana sallama dake yana jiranki” ta xare ido tace “wayene anty maryam” ta tabe baki tace “nasan miki..ko ustazunki ne yazo who knows ” “nidai banyi da wani akan xaixo wajena bah” “ya rage naki yarinya..in banda wahalalle ma waxai xo wajenki xance mtsww” daga nan ta juya ta tafi Hajja Dada ta juya tana kallon Ruhaimat tace “kije mana takwara..jeki duba wanene” “gskiya babu inda xani” “bana son gardama tashi kije” ta mike se faman kumbure2* take dole ta xare hijabinta ta xumbulashi sannan tayi hanyar fita , maryama na xaune tana danna wayarta da alama chat takeyi tana ganin Ruhaimat ta xare ido tare da cewa “na shiga 3 ni Ya’r gidan siddiki hammawa..ahakN xaki fita? Kim xumbula dogon hijabi har kasa tamkar matan limanπŸ˜‚πŸ˜‚ ahakan xai soki?” Ruhaimat ta daure fuska tace “idan bai masa bah yayi gaba dama bani na kirashi bah” daga nan tasa kai tayi ficewarta.

Yana tsaye a kusa da Babur dinsa yasha gayu yyi kyau sosai wani fyn boy ne se qamshin turare ke tashi ta karasa tare da sallama ya amsa ckn jin dadi “ya kike malama ” “lfy alhmdllh” “ya gida ya karatu” “lfy kalau..pls kayi sauri bana son mahaifina ya dawo ya tarar dani xaimin fada”

“Eyya sorry ..dama ba komai bane Ruhaimat na dade ina dawainiya da sonki a ckn xuciyata ..sunana Aliyu ” “Aliyu nagode but kayi hakuri ina da miji” “miji kuma? ..amma seda na bincika aka tabbatarmin da cewa baki da wani tsayayye kafin naxo gidanku” “hakane Amma akwai Wanda mukayi alkawarin aure dashi kayi hakuri” “ba komai nagode Ruhaimat” nan ya cire wata katuwar Leda a bayan Babur dinsa ya mika mata taki karba nan ta masa sallama ta koma ckn gida. Yusuf yana cin abinci taxo wucewa yace “ke ..xonan” a kusa dashi ta xauna “naam yaya” “matar liman yaushe kika fara soyayya..wato an fidda tsammanin ganin *mai sona* koh” “a’a yaya..har gobe ina nan ina jiransa nasan xai zo” dariya suke harda kyakyatawa maryam tace “toh ya kukayi da wannan Wanda yazo”

“Na gaya masa ina da Wanda zan aurah” yusuf yyi murmushi yace “hmmm..inaga baki da lafiya, toh idan bahaka bah ya xaki ce kina jiran gaibu?

“Yaya ba gaibu bane *mai sona* yana…”dakata dallah, yusuf ya katseta a yayinda ya cigaba da cewa “wannan fa gaibune my dear.. For hw long zaki jira mutumin nan umm? Hw many years sukabar garinnan? Kuma idan xakiyi tunani a wancan lokacin da kuka so juna Ku yarane bakusan komai bah, ynxu ba mmki shiya manta dake Amma ke kinbi kin damu kanki kina korin maneman ki y?..gskiya ki sake tunani sis” wani yaro ya shigo rike da bakar Leda a hannunsa yace an aikesa gun Ruhaimat, maryam ta tashi ta karba tana xuba godiya ta mikawa yaron #10 sannan ya tafi ckn rawar jiki ta bude ledar turaruka masu kyau guda 3 se kuma man shafawa da chocolates a cki.”wow gayen ya iya shopping wllhi daga xuwa se kaya haka..wllhi kin kofsa da mun chabe da shopping wllhi , Amma naji haushi” yusuf yana dariya yace “shegiya lashe money” “ba zancen lashe money bah yaya..u knw irin gayu haka nake so wllhi idan xaka koma skul a maka shopping lafiyayye” Ruhaimat duk haushin yayar tata take ji daga nan ta tashi ta koma bangaren Hajja Dada.

Da dare tana kwance a bisa tabarma a waje idanunta na kallon sama ..fuskar masoyin nata kawai take tunawa ko ina yake oho! Duk inda yake ta tabbata cewa yana ckn yanayin da take a halin ynxu..tasan ya kara girma yayi kyau ga kasaita ..ta lumshe ido tare da furta “Allah sarki *mai sona* ”

“aikin kenan..kowane dare a zauna ana ambaton *mai sona*..anya lfyanki kuwa?..ni narasa gane kan wannan lamarin abin naki se gaba yake Allah de ya kyauta”

Murmushi Ruhaimat tayi tare da cewa “Hajja am ki tayani da adua Allah ya cikamin burina” “uhmm..Allah de ya yaye miki”

Murmushi tayi ba tareda tyi magana bah.

 

😘😘 *Reefat CE*

[1:54PM, 11/12/2016] β€ͺ+234 703 007 7024‬: πŸ’žπŸ’ž *MAI SONA*πŸ’žπŸ’ž

*4*

BY *Reefat Yahya*

 

 

Bacci yake ckn kwanciyar hnkli bisa wani lafiyayyen gado mai kyawun gaske a hnkli take masa tafiyar tsusa agadon baya ba shiri ya bude idanunsa ahnkli yasake lumshesu ruwan sanyi ta xuba masa dan kadan a saitin fuskarsa firgigit ya tashi xaune daga shi se vest da 3qtr wando nan yabiyo ta da gudu tabar dakin Suka fara tsere ..wani tangamemen falo da xaa iya kiransa da aljannar duniya can Suka nufa wata kyakkyawar mata farasol mai masakaicin jiki tana xaune tasa TV agaba tana kallon Xee cinema award batayi aune bah taji mutum ya fada a kanta “ke lfy..”. “Wayyo mami ki taimakeni bro xaimin duka” “me kike masa” dai2* nan ya karaso yana ganin mami ya shagwabe fuska yace “mami kin ganta koh…ina ckn baccina mai dadi har na fara mafarkin *mai ni* fah taxo ta xubamin chilled water” ya karasa maganar tmkar xeyi kuka.ta juya gun yarinya ta xuba mata harara tare da cewa “tashi kiban waje Mara kunya kawai..Allah yasa ya dokemin ke tunda baki jin magana” ta tashi tsaye tana xumbura baki tace “toh mami bashi bane jiya yacemin yau xamuje national stadium kallon match din club namu..nasan baxai tashi da wuri bah shiyasa naje tashinsa” “mtsww…aikin banxa, da ruwan sanyi ake tada mutum daga bacci neh..Allah meenah ki shiga hnklinki” ta fara bubbuga kafa tace “toh ni mami me nayi” mami ta tabe baki tare da cewa “kuje can Ku gama haukar taku kunga nabiye muku har an wuceni a bada award din ma..mtsww” daga nan ta mayar da hnklinta gun kallo meenah ta juya tana kallonsa ya harde hannu a kirji yana kallonta shima ” yaya am sorry” “wllhi karyanki ba u r sorry bah se na babballaki agidan nan yau” “a’a yi hakuri big bruh kar a ballamin only Dota” muryar mahaifinsu Suka jiyo yana shigowa fuskarsa dauke da murmushi meenah tana ganin haka ta ruga aguje xata fada Jikinsa ya daga hannuβœ‹πŸΌ”dakata madam..my wife first” nan ya sumbaci mami a goshi yace “matata hasken idaniyata far in ckn rayuwata dafatan kin tashi lfy” murmushi tasakar masa ta amsa da cewa “alhmdllh mijina uban ya’yana dafatan kaima haka” “alhmdllh shine baki tasheni bah kinsan yau ranar Ku ne bani da lokacin kowa se na iyalaina abun alfaharina” “haba baban meenah kasan bazan tasheka bah saboda nasan ka gaji sosai yaune ranar hutunka ” murmushi sukewa juna meenah tace “oh mami n Baba ikon Allah..soyayyarku bata tsufa” “my bby gal ai shi so baya tsufa saidai su masoyan su tsufa” “toh..nima Allah yabani masoyi Wanda zai soni har abada”

“Ameen dear..idan kinyi dace da masoyin kwarai kin more Rayuwa” mami CE ta fada ayinda take kallon mijin nata “morning baba” “morning son ya kake” “lfy alhmdllh” “ya naganka da vest at dis hour” “ga yarinyar nan Mara kunya ita ta katsemin bacci mai dadi wllhi” “sorry son..baby gal meyasa kikayi haka ba kyau avoid it pls” ta bata fuska tace ” tashinsa kawai nayi fan..kuma yacemin da safe xamuje kallon fbal match ” “duk da haka de da zaki jira ya tashi da kansa koh, is ok kuje Ku shirya kuyi wanka kuxo muyi brkfast ni yunwa nake ji” daga nan kowannensu ya wuce bangarensa don shiryawa.

Ambassador mukhtar Aliyu kenan tare da iyalansa hajiya zainab macece mai kirki da sanin darajar Dan Adam hafaffiyar garin yolace na jahar Adamawa sunyi sosai matuka tare da mijin nata tun haduwarsu a jamian mautech…tana karatu shi kuma aiki yake a makarantar a haka Suka fara soyayya har ha kaisu ga yin aure.

 

😘😘 *Reefat CE*

[1:55PM, 11/12/2016] β€ͺ+234 703 007 7024‬: πŸ’žπŸ’ž *MAI SONA*πŸ’žπŸ’ž

*5*

BY *Reefat Yahya*

 

~short n imaginary lov story~

 

Sadik da meenah sune yaran da Allah ya basa yadau son duniya ya dora akansu yana matukar ji dasu.sadik ya kammala karatunsa na degree a Cyprus da masters a UK dawowarsa kenan daga UK bai wuce 1 week bah a gidansu dake can birnin tarayya, meenah ko tana aji 3 a jamiar base dake garin Abuja.Ambassador mukhtar Aliyu shine ambassadan Nigeria na Amurka ya tara dukiya mai dumbin yawa saboda ya rike mukamai daban2* har xuwa lokacin da aka basa ambassador yana da kamfanin motoci a Lagos da kuma kamfanin sarrafa shinkafa a can kano sannan ya bude wani sabon kamfanin sarrafa drinks da ruwan sha ingantacce Wanda duk duniya ansan da xaman kamfanin maisuna *AMZ* a can garin yola..akwai amz water , amz orange drink, amz mango drink, pineapple drink, apple drink n guava drink.katafaren kanfani ne yayi fice sosai a kasashen duniya duk inda kaje xaka ga amz drink wannan kenan.

Suna zaune a babban teburin cin abincin se karan cokula kawai kake ji kas..kas sunyi shiru suna cin abinci dama al’adarsu kenan idan suna cin abinci babu mai magana a cknsu har sai sun gama.bayan wani kankanin lokaci sun kammala cin abincin ambassador mukhtar ne ya fara magana ” dana kayi karatu ka gama Allah ya albarkaci abunda ka karanta” gaba daya Suka amsa da ameen” ya cigaba da cewa “naso a ce kayi aure kafin ka fara aiki Amma tunda Allah baiyi bah..ka cigaba da adua Allah ya fito maka da mace ta gari , ynxu ka fara shirye2* next week xaka koma can yola ka kula da amz company” ya daga kai ckn tsananin jin dadin an ambaci sunan yola yayi saurin cewa “ba komai baba insha Allah I will make u proud” “haka nake son ji..ka tsaya ka kula da aikinka kuma kada kayi wasa da ibadanka” “insha Allah zan kiyaye” “Allah ya bada saa” “ameen” ya juya gun matarsa yana murmushi yace “kinyi shiru..baki ji dadin hukuncina ba koh, kinfi son danki ya xauna kusa dake ki shagwaba shi” “ba xancen shagwaba ba Alhaji..idan yaje yola wa xai kula dashi” “don’t wory shi ba karamin yaro bane xai kula da kansa kedai ki tayashi da adua ok” a hnkli ta furta “ok Allah yasa hakan shine mafi alheri” “ameen” meenah dai ko uffan bata CE bah ta cigaba da kurba tea tana binsu da idanu bayan ta gama ta ajiye cup da karfi Suka juya suna kallonta tace “kuna zancen wazai kula dashi bayN kunsan cewa *mai ni* tana can yola tana jiran xuwansa, Baku lura da yanayin da yake cki bah..se murmushn jin dadi yake tundazu ina observing” “ke ..bana son iskanci fah, da nasan gidansu *mai ni* zan tsaya bata lokaci a nan garin ne? But anyway Allah ya cikamin burina ya bani ikon ganinta ckn sauki” baba ya juya yana kallonsu yace “kun tsakamu a duhu..wacece kuma *mai ni*??” “A’a sundai saka ka a duhu..inda sabo ai na saba da jin wannan sunan , waka ce kawai ya rage ” “bangane me kke nufi bah” “uhmm..gasu nan ai ka tambayesu” ya juya gun sadik yace ” wacece mai ni????

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment