Littafan Hausa Novels

Mai Ciki Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Mai Ciki Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

MAI CIKI

 

 

 

“`Story and writing

By

 

*Aisha mika’il*

*_(Ayousherh)_*

 

_ALLAH SHINE GATAN MU_*

 

 

*Dasunan Allah me Rahma me jin KAI*

 

 

“`Sadaukarwa ne ga duk iyaye maza da mata musamman mata masu ciki ALLAH ya raba lfy ALLAH ya saka muku da gidan aljanna firdausi Allah ya bamu ikon yi muku biyayya tareda kyautatawa gareku ina yiwa daukacin musulmi iyaye maza da mata barka da sallah

 

*This story is Just for fun gajeren labari ne kuma*

 

 

*1*.

 

*Gidan jafar*

 

____________Kuka takeyi sosai kamar karamar yarinya tanayi tana bub-buga k’afa, sosai mijinta ke rarrashin ta amma taki yin shiru, idan da sabo ya riga ya saba se karfe goman dare take tashi tace ita awara takeso ko kosai ko alala, duk ranar daya sayo seta cemai ita ta koshi,haka yake gajiya ya shareta tayi tayi har bacci ya dauketa,

Matar Oga Na Hausa Novel Complete

*Gidan sa’idu*

 

“Kai sa’idu! Sa’idu!! Sa’idu!!! Wata mata ce mai katon ciki take tashin mijinta tsakiyar dare,shikuwa yaje gona yagaji yana so yahuta amma ina, kuma yana jinta ya share dan yasan jarabar tane ya tashi.

” ke kinga ki kyale ni wani mahaukaci ne zai tashi da tsakiyar daren nan yaje daji domin ciro miki mangoro, idan na kawo miki kina shane ba saidai nagan shi kin zubar ba to babu inda zani cikin daren nan ga mayu ga aljanu kila ma idan sun jiki suzo su kawo miki”.

Yakare maganar yana bata baya, aikuwa kaman yadda yayi zato hakane da sauri ta kwanta tareda kudundune shi tana 6oyewa jikinsa, dariya ce ta zomai gimtsewa yayi beyiba don kada ta gano shi, yasanta da bala’in tsoron mayu da aljanu da tafara haka yake mata se su rabu lafiya.

 

*Gidan badamasi*

 

“Yanzu Halima saboda ALLAH da annabi wannan abinci keda waye anya lafiyar ki klau, kwana biyu wani bala’in ci gareki harda na ALLAH ya isa, toh wlh dole muje asibiti aduba wannan lamari anya ba tsutsar ciki ne yasameki ba?.

Itakuwa Halima ko ajikin ta taliya kawai take zubawa cikinta don yanzu plate na uku kenan da ta karo tana ci,

 

*Gidan Farouq*

 

“Haba Jamila wannan ai mugunta ne kince kaza zaki ci shikenan kudin dake hannuna domin na faranta miki haka na sayo miki kazar nan yanzu kice wai wari yakeyi baza kici ba wannan wani irin rayuwa ce”? yana magana kamar zeyi kuka.

” dan ALLAH yaya Farouq kayi hakuri wlh dazu naji kaman zan mutu idan ban ciba yanzu kuma wari yake min “.

 

Bece da ita komai ba yakama hanya yafici abinsa.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment