Littafan Hausa Novels

Maciji ne shi Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Maciji ne shi Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

MACIJINE SHI

 

 

 

Na mammy kabeer

(Anty mammy)

 

 

Elegant online writer

 

Free book

 

Page 1

 

 

Bismillahir rahmanir rahim,Ina godiya ga Allah daya bani damar fara wannan littafi ,bayan kammala littafin soyayyata.Allah kasa yadda na fara lafiya naga bayansa lafiya ameen.

Yaron Gidana Hausa Novel Complete

 

Gargadi banyarda wani ko wata ya juyamin wannnan littafi ta kowace sigar ba.

 

 

 

 

 

_______________Wata kyakkyawar yarinya na hango sanye da kaya irin na Fulani ,wato rigar saki dakuma zaninta,duka duka rigar da kadan ta wuce cibiyar ta,saidai kuma ta daura zanin ya rufe mata cikinta ta yadda ba wanda zai ga jikinta awaje.

 

Farace irin mai sirkin yallow -yellow din nan,tana da doguwar fuska mai kyan tsari dauke da dogon siririn hanci har baka,bakinta dan karami kamar gidan tsutsa,tana da irin manyan idanunnan masu kamar tana jin barci,ga gashin ido zara -zara.

Girarta kuwa ,kamar wacce aka dora Mata ita dan saiti,gaban goshinta wasu yan kananan gashine kwance lub lub kamar na jarirai.

Masha Allah yarinyar ta lafiya

ta hadu ,dan doguwace marar jiki saidai fa Allah ya hore mata hips Kai kace wata babbar macece Sannan akwai alamun girma akirjinta , ma’ana dai akwai dukiyar Fulani dasuka fara tasawa akirjin nata.

 

Duka duka wannan yarinyar bata wuce shekara 15/16 ba ,amma kallo daya zaka yi mata kasan Allah yayi halitta agurin.

 

Sandace irin ta Fulani ahannunta tana dagawa sama ,da alama tana son hada kan wasu tarin sha’nun dake kiwone wani kayataccen jeji ,dan kuwa ciyawace agurin Kore sharr da ita ,sha’nun suna ta cin abarsu .

 

Tafiya ta farayi gurin shanun dake dan nesa da ita ,dan ita tana daga jikin wata bishiya ne tana kallon yadda suke kiwo abinsu.

 

Kanta ta daga ta kalli yadda garin ke hada wani irin hadari baki kirin dashi ,kuma da alama koda yaushe ruwa na iya saukowa.

“Kuzo mu tai gida abokaina kada ruwan nan ya sauko ya taba mu banin son nai mura aradu”

Cikin Yaren fulatanci take musu magana ,tana daga sandarta .aikuwa kamar wanda suke jin me take fadi suka fara yin hanyar gida .

Murmushi tayi tana mai binsu tana kara daga sandarta .

 

 

Tafiya suke cikin jajen ita kadai daga ita sai wadannan garken shanun ,sam ba alamun tsoro tattare da ita,yar wakar tama take tana daga sandar sama.

 

Kusan tafiyar minti biyar sukayi ,sannan na fara hango bukkokinsu dake can gaba kadan .

AHankali naga duk wani annurin dake kan fuskar yarinyar ya dauke ,nan da nan damuwa ta maye gurbin nishadi da take ,sosai naga jikinta yayi sanyi har suka karasa wata bukka dake farkon rigar da alama nan ne gidansu.

 

Garken shanun ta fara zuwa ta daure su tsaf sannan ta nufi cikin gidan,bakinta dauke da sallama.

Lokacin har anfara yayyafi .

 

Ba kowa a tsakar gidan nasu ,hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da nufar wata bukka cikin sauri.

Saidai kafin ta karasa kofar bukkar aka daka mata wata uwar tsakar da saida sandar hannunta ta fadi kasa.

 

Afirgice ta juyi jikinta na rawa sosai kamar dan mazari.da sauri ta karaso gurin matar data daka mata tsawar,

“Gani gwagwgo”ta fada cikin rawar murya. Kallon matar nayi sai na tarar da

matar farace saidai kuma kazanta da rashin kulawa yasa tayi wani irin baki baki fari fari,sannan tana da jiki sosai sam fuskar ta ba alamun rahama a cikinta.

Tana tsaye a kofar bukkar ta tana hararar yarinyar dake durkushe gabanta.

Cikin masifa da bala’i matar ta fara magana da hausarta marar kyau.

 

“Da kake kokarin shigewa dakin,ubankane zai debi ruwan?

Ko kin ajiye bawanki ne a gidan?matar ta fada cikin zaro ido.

Kan yarinyar akasa jikinta na rawa ta fara magana

“Allah hukkumu hakuri gwagwgo naga ruwa na don sauka ne shiyasa ban deboba”ta fada cikin rawar murya da tsoro.

 

Wani wawan mari matar ta kai mata cikin rashin imani da tausayi cewar yanzu ta dawo daga kiwo kuma ko abinci bata ci amma take kokarin sake turata rafi.

 

“Shegen yaro mai bakin hali wllh yanzu koke kidobo min ruwan nan dan ubanki karuwa kawai”matar ta fada tana mai hankade yarinyar .

 

Faduwa tayi sosai hannunta ya bugu da wani dutse dake ajiye tsakar gidan da alama na zama ne.

 

Kara ta saka cikin azaba tana mai dafe hannunta dake mata wata irin azabtar zafi.

“Wayyo handi ɗin boni lalashewa gwagwgo hannu na ta ɓalle” ya rinyar ta faɗa cikin azaba.

 

“Shege wllh dama zai karye danafi kowa jin dadi yarinya kamar aljana,ace kinfi kowa kyau arugarnan? Na tsaneka fatto saina bata wannan shegen fuskan baki.maza ki tashi kona shakeki agurin ki mutu kowa ya huta” cewar matar cikin bala’i da tsantsar nuna tsana ga dattin.

 

Cikin hanzarin ta mike ta zari wani boket din roba ta fice tana kuka sosai.

 

Tafiya mai nisa tayi kafin tazo rafin, har zuwa lokacin kuka take hannunta sai zogi yake mata, ruwan ta debo cike da sauri dan kuwa ruwan da ake ya fara karfi.

 

Saidai me ?tana juyawa tayi arba da wani murtukeken maciji katon gaske ya fasa kai yana huci.

 

Wani irin mugun tsorone ya kamata nan da nan jikinta ya kama rawa har batasan lokacin da boket ɗin ya fadi kasa ya fashe ba.

 

 

Tashin hankali kenan wanda ba’a sa masa rana ,iyakar rushewa da tashin hankali yarinyar nan ta shiga.

Hannu ta ɗora aka tana mai kara ƙarfin kukanta.

 

“Wayyo ni fattu bukar na mutu na lalashe ya zanyi da rayuwata nashi zai karni wayyo baffana wayyo Allah ,taimaka min”

Ta faɗa tana kallon boket ɗin dake tarwatsa,dama kuma rana ta gama cin ubansa.

Shi kuwa macijin nan ganin yadda ta tsaya tana kallon sa kuma tana kallon fasashshen boket ɗin ta ,sai taga kamar neman makami take ,dan haka afusace yayi kanta

 

 

Ihu ta kwalla mai karfin gaske tare da zubewa agurin sumammiya dan ganin yadda macijin nan yayi kanta baki bude.

 

Masu karatu ya kukaji?

Meye ra’ayinku akan wannan Nobel ɗin?

Ina bukatar comment dinku idan buk din nan yayi muku dadi muci gaba.

 

Takuce har kullum anty mammy

 

Msr babi

 

MACIJINE SHI🪱🪱🪱

 

 

Na mammy kabeer

(Anty mammy)

 

 

 

Elegant online writers

 

Free book

 

Page 2

 

 

 

_______________Ihu ta kwalla mai ƙarfin gaske ,tare da zubewa agurin sumammiya,dan ganin yadda macijin nan yayo kanta baki buɗe .

 

Hakan ba ƙaramin tsorata ta yayi ba .

Dai dai lokacin ne kuma wani katon macijin ya nufo wannan macijin da gudun gaske ,yana zuwa ya sarkeshi suka fara kaiwa juna sara .hakan shi ya hana wannan katon macijin ya sami damar karasawa inda fattun ke kwance asume.

 

Sosai macizan nan ke kaiwa junansu sara suna murdewa cikin jikin juna.ko wanne na ƙoƙarin illata dan uwansa.

 

Ahankali fattu ta fara bude idanunta da sukayi mata mugun nauyi tana kuma lumshesu,hannunta ta daga da nufin dafe kan nata,saidai wani azababben zafi da radadin ga wani irin zugi dataji hannun yana mata ,shine ya sanyata sanya kara tare da fashewa da kuka.”washhhh hannuna wayyo kaina”ta fada cikin kukan tana mai dafe kan da dayan hannun marar ciwon.

Sai kuma ta zabura cikin azama ta zauna tana mai zare idanu da rarraba su,sakamakon tunowa da katon macijin da yayo kanta dazu.saidai kuma can ta hangi macizan biyu suna ta artabu,gaba daya sun jima kansu ciwo jini yana ta zuba akikkunansu,amma sunki daina fadan.

 

Tsoro ,fargaba ,tashin hankali da rudewa suka saka fattu kurma wani uban ihu tare da yunkurawa ta felle da mugun gudu tana ihu cikin rudewa dan ganin macizan sun zama biyu wato har fada suke akan waye zai cinyeta.

 

Duk da irin ruwan da ake zugawa mai ƙarfi ga iska ,haka tayi ta cin uban gudu ko gabanta bata gani.ikon Allah ne kawai ya kawota gidansu lafiya.

Kai tsaye ta danna cikin gidan da gudu ta shige dan dakin dayake amatsayin nata,cikin rawar jiki ta janyo wasu karare dogaye guda hudu ta kara a kofar,dan sune

Matsayin murfin kofar tata.

 

Dakin ba komai sai wata yar yaloluwar taburma ,wacce kallo daya zaka mata kasan cewa taga duniya,dan gaba daya ta ciccinye kuma tayi lakwam da ita.sai wani zani dake gefe daure ,da alama kayanta ne acikin.

Tana tsaye atsakar dakin ,har lokacin jikin ta rawa yake ,ga ruwa sai zuba yake ajikinta yararara!!!

Kallo daya zaka mata kasancewa afirgice take sai kif-kifta ido take tana kallon kofa,gani take kamar macizan nan zasu biyota.tayi kusan minti biyar acikin wannan halin ,kafin ta fara cire kayan jiki ta dake yararin ruwa.”masha Allah nace,sakamakon ganin wani uban dogon bakin gashi mai santsi akanta,lokacin da take zame dan kwalin dake kanta .an raba kan biyu an daure ko wanne bangare sai kuma aka nannade ko wanne abarinsa kamar gammo.hakan da akayi shine ya hana mu ganin gashin nata tun farko.

 

Daurarren zanin nan ta kwance ta dauko wani zanin irin wanda ta cire da rigarsa ,saidai kayan fa sun sha jiki sosai ,sun kode sun jeme sunyi wani fari,sai wata hula baka irin ta sanyin nan ta dauko ta ajiye kusa da kayan ,sannan ta mike tsaye ta cire rigarta ta ajiye ta gefen ta barmar ahankali ta warware tsangalallen zanin shima ta ajiye gefe,ya zama daga ita sai wani kodadden pant Wanda kana gani kasan shima yaga rayuwa.kallonta nayi tun daga sama har kasa kawai nace Masha Allah.dan sura kam Allah ya halicce ta agurin fattu jikintahar wani sheki yake kamar yar masu kudi wacce ke rayuwa cikin jin dadi.

 

Haka ta dauki kayan ta saka ajikinta tanayi tana kuka abin kwanon ban tausayi.

Bayan ta kammala sanya kayan ne kuma saita dauki wanda ta cire ta matse sannan ta makalasu ajikin karan dake jingine akofar dakinta.

 

Zama tayi akan yar tabarmarta ta dukunkune jikinta tana kuka.abubuwa dayawa ke dakinta ahalin yanzu,na farko tsantsar tsoron macizan data gani dan bata taba ganin irin wadannan macizan ba,dan dayan kam jikinsa mai matukar shekine da kyau,sai kuma hannunta dake mata azabar ciwo uwa uba kuma yunwa,rabonta da abinci tun safe data sha nono har kawo yanzu da magrib ta sanyin kai ba abinda taci.

Sosai take tausayi rayuwarta, tabbas rashin uwa babbar gibine arayuwa,yanzu da innarta na kusa da ita data rungumeta ta fada mata damuwarta,amma rashin dace ta daya shine sam batasan koda fuskar innarta ba ,bata sani Bama kotana raye koya mutu Allah shine masani.

Tana cikin wannan halin taji an ture kararan data rufe dakinta dashi.

Azabure ta mike tsaye tana shirin sanya ihu.

 

“Ke fattu nutsu mana nine fa ,nine baffanki”wani dattijo ne fari mai dan tsayi yake maganar,yana sanye da riga da wando na wani yadi mai arha sai takalmin sau ciki na roba,da hula irin mai malafar nan.ya shigo cikin dakin da wani kwano hannunsa.

 

Ajiyar zuciya ta sauke sakamakon ganin baffan nata ,da sauri ta karasa kusa dashi tace “baffan usee wollahi na tsorata ne”ta fada idonta akan kwanon dake hannunsa.

 

Murmushi yayi yace “hoo fattu akwai tsoro,sannu maza karbi wannan tuwon ka shinye nasan kanajin yunwa,kayi sauri kar hansai ta gani”yana fadin haka ya mika mata kwanon yayi saurin fita,dan kar matar tasa ta fito ta ganshi ya shiga uku.

 

Cikin sauri _sauri fattu ke cin tuwon nan kamar zata kware, tas kuwa ta cinye ta side kwanan, da sanda tafice tsakar gidan ta wanke kwanon ta ajiye akicin sannan ta sha ruwa tayi alwala ta koma daki.

Sallar la’asar tayi da magrib dan tuni an kira.

Har zuwa lokacin ruwa ake saidai bai kai ƙarfin na farko ba.tana zaune cikin zullumin matakin da gwogwgo zata dauka akanta ,na fasa mata boket har akayi ishsha tayi salla sannan ta kwanta tana mai karanta addu’a ,nan da nan barci yayi gaba da ita,har baffanta ya shigo ya duba ta yaga tayi barci addu’a yayi mata cikin tausaya wa halin kuncin da take ciki kafin yayi saurin fita.

 

Gwagwgo kuwa tana daki ita da yaranta suna ta hira suna cin gyada ,ba ruwansu da wane halin fattu ke ciki,shin ta dawo gidanma ko yaya taci abinci ko bata ciba?sam ba wanda ya damu ,kuma ba wanda yayi Sallah a cikinsu.

 

Can cikin dare fattu na barcinta damuwa da tsoro dan kuwa mafarkin macijin nan take ,saidai kuma ba na farkon bane yazo mata yanzu wannan mai kyakyakywan jikin ne,saidai gaba daya jikinsa jini yake zubarwa,ga wani irin hayaki da tururi dake fita ajikinsa, sai burkima yake yana wani irin kuka da wata murya mai amon sauti,kuma yana nufota da ƙoƙarin hawa jikinta .

 

Wani razanannen ihu ta kwalla tare da mikewa zaune afirgice ,tana mai waige waige,ba abinda take iya gani saboda duhun dakin ,hakan yasa tayi saurin komawa ta kwanta tare da karanta addu’a kala_kala,hannu ta mika dan janyo zaninta ta rufe jikinta dashi ,saidai kuma hannun nata taji ya sauka akan wani abu mai dan karen sanyi da santsi.

Cikin tsoro take shafa abun dan jin ko menene,tabbas MACIJINE dan kuwa ta tabo har kansa ….

 

 

Masu karatu badai macijin ne ya biyo fattu da gaske ba?

 

Wane hali fattu zata shiga ?

 

Muje zuwa yaki ce dai anty mammy

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment