Littafan Hausa Novels

Ma’aikaciyar Gomnati Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Ma’aikaciyar Gomnati Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

MA’AIKACIYAR

GOMNATI

 

 

1

 

 

By

Asmabaffa

 

 

Masoyana naga sakonku sosai na yabo da jinjina kan novel dina na maraicin rahma,ban San Kalmar da zanyi amfani da ita ba wajen gode muku,na gode kwarai Allah ya bar kauna,Allah ya biya muku dukkanin bukatunku na alkhairi.

 

Anyi Walkiya Hausa Novel Complete

 

 

LONDON na nufa a 80 jirgi ya saukeni da kyar na hada kudin zuwa ma sabo da jin dadinku readers bazan bari ya wuce Ku ba,wani gida Wanda ya amsa sunansa gida ko a kasar ba duk gida ba,ko ina ya tsaru wani handsome na hango narke a 3seater yana latsa wata dankareriyar iPad ga wata computer new design itama iPad a gefe yana ta aiki ciki hade da danna waya,tun daga yatsunsa nasan kudi da Hutu hade da jin dadi sun ratsashi,don guy karshene wajen haduwa da kyau OMAR MOHD OMAR kenan dan kimanin 35yrs sunan kakansa yaci.Baban sa mohd Omar Ibrahim shahararren dan boko ne kuma dan kasuwa kuma dan siyasa,shi kadai tilo iyayensa suka Haifa kafin rasuwarsu,yan asalin jahar gombe ne,fulanin gombe,babansa ya tsaya masa yayi karatu kafin rasuwarsa,yanzu kam mohd Omar sai yan uwa da suke gombe kawai suka rage masa,yana musu alheri da ziyartarsu, dattijon kirki yayi aikin gomnati kala kala,ya rike mukamai da dama ta fannin siyasa,yayi mulkin siyasa state rep sau daya,house of rep a abuja har sau uku,senator sau daya,ya rike minister sau 2,yanzu haka ambassador ne na Nigeria a Russia.ga kamfanoni da yawa,harkar business iri iri,ya Tara dukiya kadarori barkatai,a takaice dai hamshakin me kudine na gasken gaske dake zaune a abuja birnin tarayya.yana da mata biyu hajia amina itace uwar gida tana da yara uku dan Allah bai bata haihuwa da yawa ba,Omar shine na farko,sai abdullah dan 18yrs sai autarta suleim yar9yrs.matarsa ta biyu hajia rahina yaranta duk matane guda 5 sadiya 27yrs,Aisha 25yrs,zainab 23yrs,naja 21yrs sajida 15yrs autarta.hajiya amina yar kauyen gombe ce,dan haka batayi karatu ba iyakacinta secondary shima bayan mohd Omar ibrahim ya aureta ya sata tayi.ita bata aiki bata zuwa ko ina ta rike yaranta ta basu tarbiya tare da mijinta,

 

Rahina kuwa da yaranta uku manya duk suna aikin gomnati sunyi degree,kullum sai iyayi a hau mota fuuuuuuu ko wacce ta tafi aiki,in salary yazo ai ta gasa da juna. Baffa yayi yayi su fito da miji tunda sunyi degree amma sunki,shi yasa gidan ya Tara mata rida rida.gashi na bangaren amina sune sukafi kowa kyau,musamman Omar,shi yasa suka kara tsanarshi.

 

Basa zaman lfy ko kadan, dan hajiya rahina bata kaunar hajia amina da yaranta,dan amina tana da maza ita bata dasu,ganinta zata fita cin gado,gashi alhaji mohd yafi son amina da yaranta musamman Omar,da wannan yasa rahina dagewa lallai yaranta mata baza suyi aure ba sai ko wacce tayi degree tana aikin gomnati,suma yaran nata a akidar haka suks taso kuma halinta kaf suka dauko,ga karya,rashin mutunci da nuna su wasu ne,a junansu ma basa zama lfy,daga munafunci sai fada a titi,sai gasa da junansu ko wacce naso taga tafi kowa,gasu da bin malamai uwarsu ta dorasu,ita kuwa Allah sarki haj amina mutuniyar kirki ce mace ta gari,abin duniya bai dameta ba,ga hakuri da addini.addua kawai take zabgawa kanta da yaranta musamman Omar dan sunfi kishinsa,shi kam Sam baya shiga harkar kowannensu sai iya nasu dan yaga kannen nasa ba tarbiya.

 

Kyakyawa ne na karshe ko shi yayi Kansa iya yanda zaiyi kenan,omar fari ne amma ba kal ba,dan baza ace masa chocolate ba dan ya wuce yakai fari za a kirashi,dogone amma ba zankaleleba dai dai,ba ramamme ba kuma ba me kiba ba,a tsakiya yake da kirjinsa me fadi normal,hancinsa me kyau da tsari kuma baiyi tsini can da yawa ba,gashin kansa Wanda ya tarashi luf dashi baki ga santsi da laushi kamar na India,girarsa me yawa ga kyau,idanu dara dara farare kal,habarsa me dan tsayi,bakinsa das dan daidai lips dinsa su ba pink ba amma kamar light pink.baza Ku sha mamaki ba readers sai danaga yayi daria kusan sumewa zakuyi yanda hakoransa suke yar yar farare kal kal,ga wani dimple nasa,skin dinsa sumul luwai sai taushi laushi da sheki,tana sulbi,kafarsa da yatsu hannayensa duk abin kallo ne da birgewa,cinyarsa da kaurinsa gashi kwance masu kyau,kirjinsa kuwa da sauran jikinsa das suke ba komai luwai luwai.duk inda kuke kallon da tunanin kyau na Omar ya wuce nan.kowa sai ya kalleshi,hattana fararen fata dake London yaba masa sukeyi wajen tsaruwa da kyau,

 

Ta bangaren halaye kuwa Omar kusan 95% yake,baya shan komai,baya ko saurarar mata duk yanda suke rubibinshi, yama tsani yan mata shi,basa gabansa,baya shiga harkar kowa,bai damu da matsalar wani ba,sai in ka nemi taimako wajensa zai baka,matsalarsa akwai zucia da saurin fushi,ga girman kai,da rashin fara’a dan baya daria ba komai ke sashi murmushi ba.yana da tausayi in yaganka cikin masifa amma shi baya shiga rayuwar wani bare ya kai masa agaji sai ka nema zai maka,baya son surutu da hayaniya.yayi karatunsa na degree a London ya karanta economics,yanzu yayi masters tuni.bangaren addini kuwa ba a cewa komai yana da haddar ya kai izu 40,banda sauran wasu littafai na addini daya haddace,kuma ba laifi yana aiki da ilminsa,yana kuma addini sosai,baffa ne ya matsa masa kan lallai sai yayi aure,yana 30yrs ya nemo masa auren yar gidan wani governor wato sahar,yar boko ce itama dan medicine ta karanta tana aiki a wani babban hospital dake abj,tana da private nata guda biyu..

 

Sahar kyakyawace ba laifi chocolate ce amma tsabar body cream ta dawo fara tas,ga daukan wanka ammafa in zataje aiki.bata ganin kowa da mutunci ganin tana juya naira,motocinta 4 laba laba,duk ma’aikantan gidansu tsoronta sukeyi,sabo da cin mutunci,bata da tarbiya,ba kamun kai,dan a wurin aiki har tafawa take da maza,give me five saleem bam kaji sun kashe.

 

Haka maza suyi ta yaban kyanta da turarenta gaskia kin hadu,mijinki ya more,tayi ta zancen batsa da mazan aiki.wasu kamilallun matan ma’aikata sunsha bata shawara amma taci musu mutunci,

 

Tsiyar sahar bata tsaya nan ba har kan mijinta Omar bata ganinsa da gashi ko kadan,bai San mene aure ba,bai San dadinsa ba,bai San love ba bai tabayi ba,dama baffa ne ya lika masa dole,

 

Sahar addini bai dameta ba,ita kawai kudi da aikin gomnati,ga kawaye marasa tarbiyya,a rana sai ta fita sau biyar kullum bata gida,da anyi magana tace aikinta.

 

Taki yarda ta haihu Sam tace ina bata shirya ba,bataso ta lalace,Omar ma sabo da kudinsu ta yarda ta aureshi,dan ita burinta kudi.Omar gajiya yayi da bakin cikin halinta ya tafi London ya huta,ita kuwa ko a jikinta,ya mata fada da nasiha taki ji,bata bari ya kusanceta sai in bukatarta ce,ko tana son karbar kudi wajensa,shi kuwa baya sonta bashi da feeling a kanta yanayi ne don sauke hakkin dake kansa,shi yasa ma yake tunanin anya yana da lafiya kuwa danshi bai taba jin sha’awar matarsa ba Sam,mata kuma ko inda suke baya kalla bare ya gano matsalarsa.

 

 

Amma babban abokinsa sultan yace dan baya son matarsa ne shi yasa,duk ranar daya hadu da real love dinsa zatayi busting dinsa sanannan zai tabbatar lfy yake.Omar kuwa gani yakeyi karyane kawai.yaki yarda kwata kwata,yaje hospital da dama a turai sunce lfy lau yake. Wannan kenan kadan daga the most handsome and sexy OMAR.

 

 

Ku biyoni readers yanzu akafara Taku har kullum

 

Asmahbaffa.

 

MA’AIKACIYAR

GOMNATI

 

 

2

 

By

Asmabaffa

 

 

Nigeria na dawo abuja garin da ake ji da naira.wajen gari na fita gidajen masu rangwamen gata,wanda suke kaiwa da kyar suna yar sana’a,da suke haya a wajen abuja Kafin a karasa cikin garin abuja,dai dai gefen titi na hango wata yarinya tana saida apple da dafaffen kwai,a titi take bi tana mikawa ta window na mota,apple and egg tana bi mota mota a round tana dagawa masu mota domin su siya,

 

Kallonta nayi sosai yarinya ce yar kimanin 15yrs ta hada gumi sakamakon ranar da ake zabgawa,sanye take da wata yar doguwar Riga ja da kadan ta wuce gwiwarta,rigar taji jiki ta kode ta jeme,ta fita daga hayyacinta da dankwalinta baki,amma kana kallon yarinyar fes da ita rigar kar kar ba dirty,da gani gidansu da tsabta,

 

Yarinyar na kurawa ido na kasa dauke idona sabo da tsananin kyau da tsarin sura na wannan yarinya,kerarriyar yarinyace me cikar zati,dan kana kallonta Kazan ta hada jinsi da larabawa basai an fada ma ba,da gani nan gaba za ayi mashahuriyar budurwa,duk motar data wuce sai ta kalleta wasu har tsayawa sukeyi suce suna sonta,

 

Santala santalan kafafunta na kalla na jinjina kai,sama nayo naci karo da makeken hips dinta da tudun mazaune wasu das dasu,nan nace to fa yarinya karama kenan nan gaba fa za asha kallo,ina yin gaba naga idon garin wato boobs dinta suma dai basu girma ba kananu yanzu suke tasowa nan gaba suma uhmmm…wuyanta na kalla naga wasu yan digo digo baki sun kai biyar Wanda ake Kira tawadan Allah, wuyanta mul dashi kadan ake ganin kashi,

 

Fuskarta na tafi sawa ido,bakin nan na hango light pink dan cut,lips masu matukar kyau,hakora kanana tas farare,hancinta na kalla me kyau da tsayi gami da tsini amma ba mai yawa ba,da digon baki dis a kan hancin Wanda ya kara kawata fuskarta,idanu dai dai ba manya ba ba kanana ba farare tas kamar madara,

 

Gashin kanta Wanda yayi luf har gaban goshinta ga saje kadan yala yala baki sidik,bata da girman goshi lol,gashinta ta tubke jelarsa har ya wuce tsakiyar bayanta,

 

Sa idona bai tsaya nan ba readers sai Dana kai kallona wajen kunnenta kanana masu kyau,fara ce kar,rana da wahala ma yasa ta danyi duhu a hakan.tallanta kawai takeyi a titi bata sauraran kowa,wasu dan kyanta suke siya,wasu dan ta kulasu su sami damar lalata mata rayuwa,shi yasa bata kulasu sam,dan haka tana zuwa talla take siyarwa,

 

Wata yar yarinya na gani baza ta wuce 9yrs ba me kama da me tallan apple da egg ita amma sai dai a kirata da light chocolate dan ba fara kar bace,hannun me saida apple ta kamo tana anty IKLAS kizo inji ummi tallan ya isa,wai yunwa mukeji ki dafa mana abinci,

 

Hannun yarinyar iklas ta rike tana murmushi ok suhaila dama yanzu zan dawo gida,ya schl?normal anty,ance ban biya kudin books din da akace mu siya ba,ranar Friday za a rufe.

 

Sorry baby akwai kudin zan baki gobe never mind,botikinta ta dauka dan tuni egg ya kare apple saura Leda biyu,gida suka wuce ita da kanwarta,nima na rufa musu baya,tafiya sukayi ba wani nisa da titi wani gida suka shiga Wanda zai iya zuwa na 3 a lalacewa kaf gidajen dake unguwar suna cikin mafi rangwamen gata.

 

Gidane na bilon siminti amma kamar kango tsabar lalacewa,daki biyu ne,sai toilet Wanda rabin katangar toilet din na karfen langa langa ne,sai kitchen dinsu suma na langa langa ne,gidan ko ina da simintinsa a dabe yake,dakinsu kuwa duka ledar tsakar dakice kusan sabuwace ma,abin mamaki wani bed na gani na gaske kalar na kasar waje yasha katuwar katifa,ga wata spare katifa jingine a bango,gefe guda wasu kayan kitchen ne dana cin abinci na gaske masu tsada a katon kwali har biyu,gefe can wata sip ce itama kalar bed din da gani ansha wuya wajen shigarta dakin,rabin sip din kayan sawarsu rabi kuma suke boye kayan abincincinsu da sauran tarkace,Duk a daki daya,daya dakin kuwa Leda ce da center carpet me kyau kuma da gani me tsadar gaske ne,nayi mamaki,wasu kujeru na gani na alfarma 3 seater 2 seated da 1seater,da badan ginin marar kyau ba da palon yafi haka kyau,wata TV na gani katuwa me kyau kamar plasma tsarinta girke a kan wani glass TV stand,

 

Gidan ko ina kal kal yake sai kamshin turaren wuta ke tashi,wata dattijuwa na hango a zaune tsakiyar tabarma tana fere doya,na kare mata kallo wannan sai dai a kirata kakarsu amma ba ummi ba da naji sun fada,jikinta suka zube wash ummi tsohuwa me ran karfe,mun gaji,ko wacce tana ta dakuna tsohuwa tace dalla Ku dagani zaku karasani,sai warin rana kuke,ke faratu tashi ki mana girki,kiyi wanka ki huta,gashi na rage miki hanya.na fere doya,na miki jajjage,to ummi na gode,bari nayi sallah tukun.

 

Sallah tayi ta shiga kitchen.faten doya ta yi musu sannan sukaci,wanka tayi ta shirya kanwarta suhaila ta rike hannunta sukawa ummi sallama ummi mun tafi islamiyya daga can zamuje kasuwa domin saro apple zamuje ma gidan gona siyo kwai sabo da siyarwa gobe,addua ta musu suka wuce.

 

Wai wace IKLAS NE

 

Babansu abdurrahman saddiq dan asalin kasar libiya ne,balaraben libiya a can wani kauye a yankinsu,ruwan sama aka musu mai matukar yawa Wanda ya haddasa ambaliyar ruwa a yankin,da kyar aka samu aka ceci mutane ba Sufi 10 ba,wasu kuma mutum biyar suka taimakawa Kansu da rakuminsu suka yo hanyar Nigeria,su kwana su tashi a sahara har Allah ya kawosu Nigeria,har suka sauka a jigawa state da rakumansu,maza ne su biyar,haka suke fadi tashi a kauyukan jigawa,ciki harda abdurrahman saddiq babansu iklas kenan,ana haka har mutum biyu suka rasu suka rage saura 3,sauran biyu suka koma libiyansu suka bar abdurrahman a Nigeria,yasha wuya yasha talauci a kauyuka,har ya fara Aron gona yana noma,da haka yaci gaba har ya fara samun kudi,ya mallaki gonaki, a wani kauye dake cikin roni nan ya hadu da abu bafulatana wato Babar su iklas,kishiyar babar abu ce ke gallaza mata kasancewar kafin Baban abu ya rasu sun rabu da babarta,shi yasa ya kwace yarsa abu ya bawa matarsa riko,

 

Nan abdurrahman ya fada sonta ya tausaya mata,da haka ya dage saida aka aura masa abu,bayan aurensu arzikin abdurrahma ya shahara ga kauyen ana masa sharri dan mafiya,haka abu ta haifi iklas wacce sak babanta ta kwaso,daga nan ya kwashesu suka koma abuja da zama tare da Babar abu wato hajia asmau,wacce yanzu suke hannunta kenan,suke kiranta da ummi tun tasowarsu sukaji mamansu da abbansu suna kiranta ummi shi yasa suka saba suma.har yau suke ce mata ummi,

 

Abdurrahman sai da ya mallaki gida a abuja ga har noma ta haka ya biya musu aikin hajji sannan ya ziyarci kasarsa ya nunawa matarsa yan uwansa maza guda biyu da suka rage a duniya,haka gaj asmai ummi kenan,duk ya hada musu hanyar da ko sabo da halin rayuwa zasu iya Neman yan uwansa,

 

Bayan suhaila Nada shekara 7 da haihuwa abu maman su iklas da mijinta abdurrahman Baban su iklas suna hanyar dawowarsu daga jigawa zuwa abuja suka tafka hatsari inda Allah yayi musu rasuwa,dukansu,anyi jaje da jimami,yayinda kakarsu ummi ta kira yan uwansa ta sanar musu,har Nigeria sunzo,kuma sun bawa su iklas nasu gudunmuwar,dan suma ba yan uwansa na jini bane,dangi ne kawai sama sama shi yasa basu dauki su iklas ba suka koma kasarsu,

 

Ummi kakarsu iklas ce taci gaba da kula dasu,tana sana’ar saida kayan miya,irin su citta,maggi,manja,wake,barkono etc,har abincinsu ya kare,kudin hannunsu ya kare,komai nasu ya kare kat hattana kudin makarantar su babu,lokacin iklas tana ss1,suhaila na primary 2,da haka suka yanke shawarar saida gidan da suke ciki,haka suka siyar da gidan Ganin matane yasa aka cucesu sosai aka siyi gidan arahar banza,

 

Da haka suka tashi suka koma wajen abuja gidajen dake kusa da garin abuja kafin a karasa cikin city,anan suka sayi wannan gidan da suke ciki,an musu tsada sosai anan kudin ya kusa karewa,shi yasa suka ebo wasu kayan na gidansu da suka siyar Wanda zasu iya amfani dasu suka zuba a gidan da suka siya,

 

Sun biyawa suhaila kudin makaranta tun daga primary 2 zuwa jss3 gudun kar a sami matsala,abinci suka jibge komai da suke bukata sai da sukayi dai dai kudinsu,har da jarin kwai da apple,ita kuma ummi takeyin sana’ar siyar da kayan miyarta a gida,

 

Islamiyya ma sun biya kudinta na shekaru,iklas ma an canja schl me saukin kudi,ta biya daga jss2 har zuwa ss3.ga saida apple da egg,tana dawowa daga schl zata wuce tallanta, zuwa 4 su tafi islamiyya,haka suke rayuwa har yanzu sun kwashe 2yrs.

 

Yanzu komai ya dagule musu,da tallan da iklas ke zuwa da sana’ar kakarsu ummi suke ci suna sha,da sauran abubuwan rayuwa Wanda ya zama dole.

 

Iklas bata da burin da ya wuce tayi karatu me zurfi tayi aikin gomnati dan ta tallafawa kanwarta da ummi,bata da burin da ya wuce tayi aikin goMnati,gashi aikin gomnati na burgeta, ita ko me aikin gomnati ta gani a titi to birgeta takeyi,ko ji tayi ma’aikata na labarin wajen aikinsu to sai ta tsaya ta saurara.

 

In tana tuno aikin gomnati ita kadai zaka ga tana daria,idan kana so kaga dariarta ko jin dadinta to ka mata adduar Allah sa ki zama ma’aikaciyar gomnati ko ta company,dan haka duk layinsu in ta wuce ko abokanan tallanta zakaji ana gomnati gomnati wasu suce ma’aikaciya,arnan ko gwarawa da marasa jin Hausa da suka Santa sai kaji suna kiranta the manager.murmushi take musu sosai,

 

Indai kana so a nuna ma gidan su iklas to kace gidan su gomnati ko ma’aikaciya,ko gidansu manager.

 

Ya halayen iklas sukene

 

 

Asmabaffa

[27/03, 17:48] Hassan Atk: ⓂⓂⓂ

MA’AIKACIYAR

GOMNATI

ⓂⓂⓂ

 

3

 

By

Asmabaffa

 

 

 

Readers kar Ku gaji da hakuri da typing error sometimes ba time na editing.tnx

 

 

 

IKLAS nutsatsiyar yarinya ce kamila,ga addini hankali da sanin ya kamata,ga kamun kai,tsabta da son kwalliya,bata so ace taci baya sai gashi talauci yasa ta zama sai a hankali,gata da kokari ita da suhaila,gaskia iyayensu sun iya tarbiya kuma Allah ya amsa adduarsu ya basu yara nutsatsu,ga yarda da kaddara,Sam basu dau duniya da zafi ba.

 

Iklas bata da tsoro,tana da hakuri amma indai ka tsokaneta ko ka rainata to fa ba mutunci,bata kyalewa,gata tana da surutu amma ba me yawa ba,itama akwai zucia,gata da fara’a da mutunci da karrama dan Adam shi yasa kaf yankin da suke kowa ya Santa kuma ana sonta maza da mata,komai nata a nutse,ita sam bata son raini,Suhaila ita bata fiye son surutu da hayaniya ba. In dai kaje unguwar su iklas baka isa ka nunata da yatsa ba yanzu matasa yan unguwar zasu hada ma jini da majina,shi yasa suke zaune gidansu lfy.

 

Ummi ma tana fitowa za kaga ana kwasar gaisuwa sabo da iklas ta siyo musu mutunci.wannan ne asalin da tarihin iklas .

 

 

Ci gaban labari

 

Baffan su Omar ne ya kirashi a waya,Omar na daga wayar baffa ya fara fada haba Omar kasan ina Russia na bar ma komai na business dina a hannunka ga iyalinka can na jiranka amma ka tare a London kaki dawowa,bayan Kaine babba wa zai kula da harkata in ba kai ba,kasan kannenka basu da hankalin da zan dorasu kan harkata,pls ka koma gida nan da 3days.cike da ladabi yace alright baffa insha’allah zan koma yanda kace,dadi baffa yaji that’s my son,yana son Omar sosai.

 

Omar kuwa nazari ya shiga yana tunanin yanda zai je ya hadu da mahaukaciyar matarsa wacce take bata masa kullum wato sahar.amma ba yanda zaiyi dole yabi umarnin baffansa ya koma Nigeria,

 

Yana cikin wannan tunani sahar ta mako masa kira,tsaki yayi hade da daga wayar dan yasan kudi zata roka ko wani shirmen,ba ko gaisuwa kawai ya London tace sannan tace baby wlh kudin da ka bani sun kare kuma gashi za muyi bikin wata yar wajen aikin mu,

 

A hankali yace yace OK zan miki transfer,yanzu ke sahar baza kiyi hankali ba,yanzu haka ake kula da miji.ganinki kinyi dai dai,tunda na bar gida ko kirana bakiyi ba,kiji tsoron Allah sahar,kiyi amfani da damarki kafin ta wuceki,kunkuni ta fara yanzu ya kake so na maka,kullum bani da time fa busy nake,kasan aikin mu ba daga kafa,ke kullum Aiki aiki baki da wani abu sai aikin gomnati.

 

To ni kaga karka dameni dan ka samu na kiraka,da bukatarki ta taso ba,ae hakkinkane ai taja tsaki hade da kashe wayar.omar sarkin zucia har zucia ta kawoshi wuya,take idonsa ya canja,sai bacin rai da huci yakeyi.

 

Mama ya kira a waya suka sha hira ta hadashi da kannensa suleim da abdullah sun sha labari.yau ne ranar da omar zai dira a Nigeria,karfe 4:30pm mama,suleim da abdullah suka dauko handsome daga airport,sai murna sukeyi cike da kasaita ya bisu suka wuce gidansu na alfarma.tunda yaran hajia rahina wato umma sukaji labarin saukar Omar suka fara gulmace gulmace,hassada da bakin ciki,ko wacce part dinta daban amma su umma wato rahina sun dami rayuwarsu sabo da mugun halinsu.

 

Sadiya ce ta parker motarta kuuuuuuuu ta fito dawowarta daga wajen aiki kenan,direct part dinsu ta wuce,duka yan matan kannen nata da umma suna zaune suna gulma da zage zage,sadiya ma zama tayi dabar kasancewar ita ce ba,umma kice tsinanne ya dawo kasar,Aisha tace na tsani yaya omar wlh waishi dole me kyau,me kudi,umma tace duk Ku saurara shi din banza wlh sai nayi maganinsu gaba daya har uwar tasu,

 

Zainab tace wlh umma karki daga musu kafa,naja tace har mu zai nunawa kudi aikin banza wai wannan sahar din matarsa har ta isa ta ganni tamin kallon banza,yanda take ji ita me kudi ce muma haka,domin aikin gomnati ne muma shi mukeyi,

 

Sadiya tace hmmm umma zatayi maganin ogan nasu ai,haka suka kai har dare suna zage zage,a karshe suka yanke zasu je masa sannu da zuwa don sugano kwakwaf,

 

Ita kuwa baiwar Allah mama tasa danta gaba yaci ya koshi dan tasan matarsa ba matar kirki bace,addua take Allah masa canjin alkhairi,amma ita kam wulakancin sahar ya isheta,nasiha ta masa sosai tare da Jan kunne wajen dagewa da addini,sannan ta turashi kan dole yaje ya gaida hajiya rahina umma,

 

Badan yaso ba bayan sallar isha ya isa part din,da zuwansa ya gansu a Palo rida rida a kwance ko wacce na latsa waya,umma na gefe,suna ganinsa dukkansu gabansu sai daya fadi dan mugun tsoronsa sukeyi,ga kwar jini da yake musu, Sam baya musu ko murmushi,dama duk zaginsu a bayan ido sukeyi,risunawa yayi ya gaida umma,da kyar ta amsa tana masa kallon harara,su kuwa yan matan kowacce yaya sannu da zuwa ka dawo lfy,lfy kawai yace ya ficewarsa cike da kasaita

Yana fita suka dasa gulmarsu kunga maye yanda ya kara kyau ga iya daukan wanka,ko wanne kaya yasa kyau suke masa.wurin mama ya wuce ya roketa kan ta barshi ya kwana gobe sai ya tafi gidansa,kyaleshi tayi dan tasan matarsa ba kula take dashi ba,

 

Suleim tana manne a jikinsa sai bacci takeyi,washe gari da safe uban yan daukan wanka omar sakkowa yayi daga sama yana zuba kamshi,sanye yake da wani yadi fari Sol ya matukar masa kyau,hattana takalminsa fari ne,ba hula a kansa sai gashi kwance luf.sallama yawa mum bayan ya cika tumbinsa ya basu tsaraba,wucewa yayi gidansa dake zone 11princess suit,gidan ya tsaru,

 

Driver ne ke tukashi har gidansa,tun daga compound yake jiyo hayaniya sama sama,a nutse ya shiga palon da sallama,frnds din sahar ya hango arna da musulmai maza da mata suna jin kida hade da hira,ga kayan ciye ciye nan,

 

Ran omar ne yayi mugun baci suna masa magana amma ko kallon su baiyi ba ya wuce room dinsa,ita kuwa sahar baki ta tabe hade da Jan tsaki,

 

Saida wata kawarta zuby tace sahar kije wajen mijinki kinga kamar ransa ya baci,tsaki sahar ta ja to sai me yanzu akansa zaku tafi haba mana frnds,next time zamu dawo yanzu kije wajen mijinki cewar wani saleem abokin aikinsu,bata so ba suka tafi ,yar aikinta ta bugawa tsawa kan tazo ta gyara wajen,direct dakin Omar ta nufa tana cika tana batsewa,sanye sahar take da T-shirt baka da skert din atamfa sun kamata kam,kanta ko dan kwali babu,

 

Tana shiga ta ganshi kwance kan gado yana latsa waya,baki ta turo ta kare masa kallo gaskia mijinta me kyau ne,ga iya wanka,a nan take sha’awar Omar ta motsa mata ba abinda takeso sama da ya biyaa mata bukatarta,gashi tasan fushi yake yi yanzu bare ya mata abinda take so,

 

A gefen gadon ta zauna sannu da zuwa baby ya hanya?tunda yaji haka yasan tabbas sahar wani abun take so ya mata,dan bata aikin banza sai da dalili,ko kallonta baiyi ba,sha’awace ta kuma lullubeta tace baby kayi hakuri nasan na ma laifi,kallonta Omar yayi tabbas yasan da dalili,sahar baza ta taba bashi hakuri ba tare da kudirin wani abu ba,a hankali yace ya wuce,in mutum yayi da kyau shima ya sani in ya bata ma ya sani,kisani ke baki isa ki sani bacin rai ba,Wanda ka damu dashi shi ne in ya bata ma rai kake damua,sahar taji haushin kalamansa amma sabo da tana neman wani abu tayi shuru ta kara cewa am sorry hade da hayewa kan bed din,yana kallonta ya gano me take nema,sha’awa ya hango zalla a idonta,kwancia tayi a kirjinsa,dan sahar ita bata da kunya ko kadan.

 

Shafashi ta fara tana wani shagwaba,babyna I missed u alot,tabe baki yayi yana kallonta ta fara cire masa Riga,baya son ya wulakantata,kuma yasan hakkinta a kansa musamman da ya tafi London ya Dade bai dawo ba,sabo da wannan dalilin ya biye mata yayi manage ya biyamata bukatarta,sahar tana jinta zam zam dan Omar gwarzon maza ne ya tsaya ya biya mata bukatarta sosai taji dadi har jinjina iya sex na Omar takeyi,guy ya hadu ta fannin romance da sex,ni kuwa nace danma ba zabinsa bace ke,bashi da feeling akanki.

 

Sahar tana jin zam zam ta mike tayi ficewarta,shi kuwa Omar baiji wani dadinta da yawa ba dan sahar ko dan gyaran da mata keyi na shan tsumi bata yi Sam,ita fa indai ba aikin gomnati ba to bata ganewa komai.washe gari Omar ya shirya tsab cikin suit baka yayi kyau yana baza kamshi ya sakko cike da takama da kasaita,dakin sahar ya shiga tunda ya tashi bai ganta a bed dinsa ba,room dinta ma wayam bata nan,Palo ya zo ba kowa sai hindatu me aikinta,ina sahar take cewar Omar,har kasa hindatu ta duka ta gaisheshi da sakin fuska ya amsa,yanlabai ta tafi wajen aiki tun 6am wai tana da tiyata,

 

Tsaki yaja ya fice gaba daya daga gidan ko dining bai kalla ba,yana mamakin yanda sahar ta rainashi ace matarka ta fita ko fada ma baza tayi ba,tsaki yaja hade da ci gaba da karanta jaridarsa yayinda ya kame a bayan wata luntsumemiyar motarsa Wanda takai milyan 40,driver ke gaba yana tukashi,shi Omar Sam bai damu da driving ba yafi so a tukashi kaji manya fa readers.

 

Hadadden gidansu yace a kaishi direct wajen mama ya nufa,a Palo ya sameta tana turaren wuta rungumeta yayi hade da gaisar da ita,mama kintashi lfy?lfy babanmu ya gida,great mama,to alhmdllh.mama breakfast fa?juyowa tayi da alamar tambaya gidanka ba a baka ba,wlh mama kin San dai komai,yan aiki keyi ni kuma kin San bana son kazanta,kuma yau mama inaso naje na duba gidan gonarki da kike kiwon kaji,kinga an Dade ba a duba ma’aikatanba da sauran abubuwa,murmushi tayi yawwa babana Allah maka albarka,da har na yanke shawarar zuwa da kaina,haba mama da raina da lafiyata na barki ki wahala.to Allah maka albarka.su abdallah suna schl ae ai ka sani.OK.

 

Haj amina tana da shahararren gidan kiwon kaji dake wajen garin abuja,baffan su Omar ne ya gina mata ya bata kyauta ganin haj rahina na aikin gomnati shi yasa ya bata wannan kyauta.

Haj rahina umma ta tafka bala’i akan wannan kyautar ta baffa,haka ta hakura.

 

abinci yaci ya koshi yawa mama sallama ya wuce office,karfe 2pm ya bar office ya wuce gidan kajin mama.

 

Asmabaffa

 

MA’AIKACIYAR

GOMNATI

 

4

 

By

Asmabaffa

 

 

1:30pm iklas ta shigo gida ta dawo daga tallanta,domin schl din da ta koma 8to12 ce ta irin manyan mutane ce Wanda basuyi karatu da wuri ba,irinta ta koma sabo da tallan da take zuwa domin da shi suka dogara,dan haka 12 tana dawowa zata tafi talla kan titin kwalta,1-1:30pm ta dawo,tana cin abinci zata shirya ta tafi saro apple da egg,tana dawowa sannan suhaila ta dawo sai su shirya su tafi islamiyya,Saturday Sunday kuwa da safe take zuwa talla zuwa 3 to 4pm ta dawo,haka take rayuwa kullum ba Hutu,gashi watarana har girkin gida ummi take sata dan bata so iklas tayi aure bata iya girki da sauran ayyuka ba,dan haka take sata dole,shi yasa ta iya komai dama gata jaruma,

 

Wanka tayi ta shirya cikin wata yar rigarta doguwa itama wata Igbo ce ta bata ita,light blue ce me ratsin ja ja da digo digon baki,daga sama ta dan matseta kasa ta bude amma itama da kadan ta wuce gwiwarta,basu da kayan kirki,dan ma waiyayenamure na taimakawa su basu kayan da suka musu kadan,wasu kuma har sabo suke basu,ita ma suhaila tana samun na yaransu,wasu kuma iklas na kokarin sai musu gwanjo,shi yasa kusan kayansu gaba daya English wears ne,tsangalallu ne badan suna sa dankwali ba sai ka dauka arnane suma saboda rashin wadata.to daya suke samun na ci ma.

 

Bakin gyale siriri ta yana kanta,batayi kwalliya ba powder ta shafa kawai sai Vaseline da ta shafa a lips dinta,tayi kyau dama me kyau ko ba kwalliya me kyau ne,wani takalmin roba me igiya baki ta saka,shima wani ne da yake siyarwa ya bata kyautarsa yaga tana da hankali,ga babu ta zauna musu.tayi kyau sosai a nutse ta dauki botikin saro kwai da ledar siyo apple ta yiwa ummi sallama ta wuce,a kofar gida suka hadu da suhaila ta dawo daga schl,anty har kin shirya?yeah iklas ki jirani muje tare mana,no je kici abinci ki huta ki shirya zuwa islamiyya kafin na dawo OK.OK anty sai kin dawo,Allah tsare shafa kanta tayi ameen suhaila,tana matukar kaunar kanwarta.

 

Tafiya tayi da dan nisa ta isa gidan kaji domin siyo kwai da apple,mutane da motoci birjik sunzo sarin kwai da apple suma,gaskia kowa ya kalli gidan gonar yasan an kashe dukiya,part part ne wurin kaji da kwai daban,part din fruits daban,kifi daban,ga sauran tsuntsaye da abubuwa kala kala.

 

Da araha suke bada sarin shi yasa ake cika gidan gonar,shi yasa iklas ke saro nata can dan ba karamin riba take ci ba,ratsa ciki tayi ta shige,ma’aikatan ciki sai fara’a suke mata suna gaisawa,dan sun saba da ita,gashi sun karanci nutsatsiya ce me mutunci da kamin kai,suna tausaya mata mace kamar ta tana sa’a irin wannan,da gani suna cikin talauci,shi yasa suke Mata arha fiye da kowa.

 

Tana tsaye tana jiran a sallami Wanda suka rigata, wata arniyar mota ta shigo cikin wurin,kowa bin motar yake da kallo,babu Wanda ya taba ganin kalar motar,har jira ake aga waye me motar,

 

Ita kanta iklas duk tsaiwarta a titi bata taba ganin mota irin wannan ba,su kuwa ma’aikatan gidan sun San bazai wuce Omar ko mama ba.sun San irin wannan babbar harka sai iyayen gidansu Wanda suke jin dadin aiki karkashinsu,shi kuwa Omar tun shigowarsu kansa na kasa yana duba jarida,driver ne ya fito da sauri ya bude masa kofa,subhanallah shine abinda iklas ta furta a ranta ganin takalmi da kafafuwan Wanda ke fitowa,

 

Basu gama sumewa ba sai da Omar ya fito gaba dayansa daga mota,wani daddadan kamshi ne ya mamayesu gaba daya,iklas tana kallonsa gabanta ya fadi ji kake daram dam,sunga zallar baiwar kyau da kwarjini da cikar zati,iklas tace tab yau ga Wanda ya takeni a kyau,ido ta lumshe hade da bude kafafen hanci tana shakar ni’imantaccen kamshin Omar, shi kuwa Omar iklas ya fara hangowa da tsangalalliyar rigarta,kasancewar fara ce kar sai ta haske gidan. Gonar gaba daya,kallo daya ya watsa mata shima gabansa yayi mugun bugawa,bai taba ganin dan Adam me kyanta ba,duk kyansa sai yaga ga wata yarinya ta fishi,shi bai taba jin faduwar gaba ba sai akan wannan tatsitsiyar yarinya,

 

Fuska ya yatsina kamar yaga kashi yayi mata kallon kaskanci ya wuce ta gabanta,da mutanen wajen maza ya gaisa ya mika musu hannu,sannan suka dan kebe da babban me kula da wajen suna magana.

 

Iklas kuwa ta cika fam sabo da irin kallon banzan da ya mata,bata son raini,dan suna talakawa shine zai yatsina mata fuska,hmm duniyace a ranta take wannan magana,ana haka har akazo wajenta aka cika mata botikinta ta mika kudi,lokacin Omar ya gama da wajen kwai ya wuce wajen fruits,da kyar take daga bokitin ta karasa wajen fruits itama ta mika kudi aka cika mata katuwar ledarta da apple,ta juya zata wuce sukayi karo da da botikin kwanta tayi karo da mutum gwaraf,amma batafi saman cikinsa ba,botikin kwai ya tuntsire wajen guda ashirin sun fashe,shi kuwa take yaji wani mugun shock a jikinsa zirrrrrrrrrrr wanda bai taba ji ba,sakamakon haduwar jikinsu,daurewa yayi ya dawo hankalinsa,tsaki yaja ya furta psycho kawai,haushi ta karaji ya mata abu maimakon hakuri sai zagi,ledar hannunta ta apple ta ajiye gefe,gabansa ta sha ta rike kugu hade da harara,malam kamin laifi da barna ka kasa bani hakuri sannan ka zageni,da nayi niyyar yafe ma amma wlh tunda ka zageni ka kasa bani hakuri to ba kira ba abinda zaici gawayi,sai ka biyani each and every egg da ya fashe,dan akanka bazan dauki asaraba,

 

Daria yace ta kamashi ya danneta,bai taba haduwa da funny girl haka ba sai yau,yar yarinya da Karin magana haka,ga masifa har wani jijjiga takeyi gaban katon namiji kamarsa.

 

Allah ya taimakesu ba wasu mutane wurin sai masu shirya fruits,tasowa sukayi daya daga ciki yace haba gomnati basai kinyi fada ba za a biyaki,shine me wajen,a fusace tace dama haushinsa nakeji ni time din daya shigo yamin kallon Tara saura kwata,dan haka wlh sai ya biyani,tofa wannan yarinya da kuruciya sosai kanta ga tsiwa cewar Omar aransa. Wasu ma’aikatanne suka zo wajen suna haba gomnati ikon allah bamu sanki da haka ba,wani ciki yace the manager wannan oganmune fa,murmushi ta saki jin an kirata da sunan da tafi so wato gomnati, Wanda ya tafi da imanin Omar, tace to na yafe masa sabo da Ku

 

Gefe ta matsa tana gyara bokitin kwanta hade da kunkuni kawai an cuci mutum,wannan days fashe ni haushina ma daya asararsa da akayi,yanzu wannan ya ishemu mu soya muci da su ummi har na 5days,ko mu soya doya da kwai ta kwana biyu,ai kuwa da munci dadinmu.duk surutun nan da takeyi Omar na jinta,sai daria yakeyi a zuciyarsa,yarinyar so funny,ya dade rabon da yayi nishadi irin na yau,kwai aka kawo mata guda 100 a Leda,kallon mutumin tayi laaaa ai nace na yafe masa wlh,ai oga ne yace a baki gashi guda 100 ma aka baki kinci riba…no na yafe ai,fafur iklas taki karban kwan nan,,sunyi sunyi taki karba,Omar ne ya karba hade da daka mata tsawa karba ban son shirme,tsoro ne ya kamata,taf aka cika botikinta da kwai,aka kara mata apples da yawa sannan aka mika mata kudinta,mamaki tayi sosai ta kalli Omar a tsorace na gode oga Allah kara arziki,sosai yaji dadin adduar ta matarsa bata taba masa ba,sai wata a titi,it’s OK zaki iya tafiya, uhm….uhm…..dama oga dazu kaga fadan Dana ma,nayi ta masifa rainane ya baci kanwata na aika taki zuwa,shine raina ya baci,amma maganar gaskia bada kai nake ba,da kanwata nake.

 

Murmushi Omar yayi Wanda yasa iklas sandarewa ganin kyau da dimple na Omar,shi kuwa a ransa yace yarinyar nan da wayo take.a fili hade rai yayi ya tabe mata baki ya shige mota driver ya ja suka wuce.itakam taji haushin tabe mata baki da yayi,ya rainata.anyway sun sami kudin abinci lallai yau tazo a SA’A.

 

Yau taga lailatulqadari sunan da ta lakabawa Omar kenan kayanta ta dauka da kyar ta nemi taxi,kayan sun mata nauyi,ga murna an vata komai kyauta,shi yasa yau ta shiga taxi,ta matsu ta koma gida ta bawa kaka ummi labari.

 

 

Asmabaffa

 

MA’AIKACIYAR

GOMNATI

 

 

5

 

By

Asmabaffa

 

 

 

Har kofar gida me taxi ya sauketa da kayanta,da sauri ta shiga da kayan ta fara kwalawa ummi kira tsohuwa kaka ummi…ummi…tsohuwa wai kina ina haka,ke lfy kike rafka min kira haka kamar kina bina bashi cewar kaka ummi,iklas ce ta rungume ummi tana ummi lailatul kadari na gani yau,kinga yau komai kyauta aka bani kwai da apples ummi sai nayi 1wk banje sari ba,duk na kyauta zan siyar,kinga kudin yanzu zamu tafi kasuwa dama abincin mu saura na kwana daya,

 

Kaka ummi ce ta kalleta da murmushi tana mai cike da farin cikin kalaman iklas,to iklas wai waye lailatul kadari naga ta kaina yar nan karfa kiyi mana sabo,ummi oga ne me gidan kajin ya bani komai kyauta,nan ta kwashe labari ta fadawa ummi,ummi taji matukar farin ciki,dama basu da abinci ba kudi,

 

To alhmdllh iklas kece wacce ta iya tsari da lissafi sai muyi shawara,ai ummi yau baza mu islamiyya ba,dan kasuwa zamuje da suhaila,Biro da jotter ta dauko suka zauna a tabarma nan iklas ta fara planning,dama iklas akwai iya planning din rayuwa,nan ta rubuta abubuwan da suke bukata ta tsara komai,ta bawa ummi na cefane taja hannun suhaila suka wuce kasuwa.

 

Omar direct gidansu ya wuce wajen mama,cike yake da tunanin yarinyar da yaji ana kira da gomnati ko manager sunan ne ya bashi daria,ya kara nanatawa a ransa bai San sanda ya saki murmushi ba,nan take ya shiga tunanin yanda take masa tsiwa a gidan gona,a haka ya karasa palon mama

 

Zaune ya sameta suleim na gefenta suna game ita da abdallah,sallama ya musu ya kwanta Shana Shana cinyar mama yana shagwaba sai shafa masa gashi mama keyi tana wani lallabashi,dining ta jashi ta zaunar dashi,da kanta take bashi a baki har ya koshi,

 

Mama sosai take tausayin dan nata sabo da yanda tasan halin matarsa bata da hali.adduarta kullum Allah masa chanjin alkhairi.Omar yayi aure amma kullum a gidansu yake rayuwarsa,kullum babu Wanda zaice ya taba aure,Rabin kayan sawarsa gaba daya yana room dinsa a part dinsa bangaren mama.bashi da banbanci da gwauro.mama kuwa bata hanashi.

 

Direct room dinsa ya wuce,wanka yayi hade da sallah ya kwanta sai bacci.iklas kuwa Niki Niki suka shigo gida dauke da kayan abinci dai dai kudinsu.ummi ta kawo musu farar shinkafa da miya hade da salat harda kifi,dan iklas duk talaucinsu bata yarda aci fara da yaji ba sai in suna sha’awa ko da dalili,dan gaskia tana da son cin dadi,ita ta yarda su rasa komai suci abinci me kyau,tunda suna Sana’a kuma suna samu ba laifi shi yasa take musu cefane me kyau na talaka.Rabin rayuwar gidan kaf a hannun iklas take

 

Wanka sukayi suka zauna hira kafin magrib ta karasa,bayan sunyi sallar isha iklas ta shiga kitchen ta dafa musu indomie da dankalin turawa harda kifi,a baki ta bawa suhaila taci ta koshi,sannan suka ebo littatafansu sukayi karatu,nafila sukayi sannan suka haye gadonsu suka kwanta,kaka ummi kuwa dama a katifa take kwana,wai gadon ji takeyi tayi sama dogogo.suhaila da iklas a katon gadonsu,

 

Haj rahina tana ta kulle kullen mugunta kawarta na hango suna zuba hirar mugunta a zaune a palon umma,ita da babbar kawarta hajiya binta suna shirya tuggun da zasu kullawa Omar da mama,rahina tace binta ko wajen bokaye zan je ne?daria binta tayi tace share bokaye watarana aikin baya ci,kin San munafukar akwai addua,mufa mata ne ba irin tuggun da baza mu iya kulla musu ba Wanda zai jefa su cikin wani hali,ke in ta kama har gidan nan sai sun bari,tsabar iya tuggu da sharrinmu,haba rahina kin manta mu ne, tun muna yara kin San tsiyarmu.daria da shewa sukayi hade da tafawa, su sadiya yaran rahina sunaji sai murna suma sukeyi suna tafawa,dasu ake shirya komai.sai kara zugasu sukeyi,

 

Iyaye da dama na kuskure manya manya duk wani gulma,munafunci hassada sai a dingayi gaban yara,ana daria kaga wasu har tafawa sukeyi da yaransu mata ana cin naman wasu,duk iyaye masu haka su sani suna gurbata tarbiyyar yaransu,da haka zasu taso suma sunayi,kuma uwa ko yaushe batawa yaranta fada,tana wasa da daria ko yaushe da yara baza su taba jin maganarta ba,rainata zasuyi,ba a hana hira wasa da Jan yara a jiki ba amma a dinga sanin kalar Wanda za ayi,kuma wasa ba ko yaushe ba,shi yasa za kaga yara na dakawa uwarsu tsawa,ta sasu abu sukiyi, suma fada mata direct baza suyi ba,sai kaga idan ubane an masa da wuri a na rawar jiki,da yace a bari an bari,ba raini,amma mu iyaye mata mu ke zubar da kimarmu gaban yaranmu,matsala iri iri,Allah sa mu gyara.

 

Omar na hango yana tafiyarsa ta takama sanye da wani blue jean pencil da red din Riga me dogon hannu,wandon irin an dan farfasashi daga gwiwa zuwa cinya,amma ba me yaga ba dan ba a ganin jikinsa,driver ne da sauri ya bude masa wata sabuwar arniyar farar mota,yana yin ribas motar sahar ta cinno kai gidan,tsadajjen gogon hannunsa ya kalla yaga almost 5pm,kawayenta ya hango biyu a cikin motar.horn ta masa hade da daga masa hannu,haushi ne ya kamashi, wurin 2days baya ganin sahar sai yau,ko yaushe tace duty dare ne da ita,kwana takeyi a hospital,yanzu kuma da rana yawo da kawaye da shirme a gari aikinta kenan.sai shewa sukeyi da frnds,wurin babban abokinsa sultan ya wuce,sultan doctor ne babba shekarunsu daya tare sukayi schl a london,har secondary,sultan babansa ya rasu daga shi sai mamansa,sun gaji dukiya ta gaske shi da mamansa,sultan baiyi aure ba amma an kai kudin aurensa gidan wata yar beauty dinsa yasmin,a asibitinsa ya sameshi zaune a office,hannu ya mika suka tafa sultan yace shegen kaya ya kk,ka dawo amma sau daya ka nemeni,omar yace bari Frnd kasan office ba Hutu,baffa ya hadani da aiki,oh na zata amarya sahar ce ta boye min kai,kana can kana Jan kaya,tsaki omar yaja kaifa dan iskane sultan,kasan komai tsakanina da ita kana min tsiya,Allah kyauta cewar sultan,kaga malam gobe around 1pm zaka rakani wani company na baffa zan duba aikin da akeyi,kasan da nisa fa sai an bar garin abuja.

 

Allah kaimu cewar sultan.wai Frnd har yau baka samu wacce kake so bane,tsaki omar yaja karka dameni malam.daria sultan yayi yana ci gaba da tsokanarsa.

 

Washe gari kamar kullum 1pm tana titin kwalta sai bin motoci takeyi a round tana daga apple da kwanta a ledoji ,ga yayyafi anayi ruwa ya jiketa da dangalalliyar rigarta wacce taje gidan kaji da ita,duk ruwan sama ya jikata kayan sun kara dameta a jikinta,sai boobs dinta kana kana duk sunyi caro caro,hips ya fido,gashinta ya kara kwantowa a goshinta sai digar ruwa sukeyi,

 

Omar da sultan suna bayan mota a lafke driver na jansu,suka kawo dai dai danjar da iklas take,suna tsayawa ta karaso wurin motar tasu ga iska ta taso haka take daga musu,ido hudu sukayi da Omar wata uwar zabura yayi hade da nunata da yatsa yace you? Bata jin me yace saboda glass din motar a zuge yake,amma ta karanta lips dinsa ta gane me yace,murmushi tayi me kayatarwa ta daga masa hannu,itama tace oga da karfi,yaji abinda tace ai bai San sanda ya saki murmushi ba,yawa driver umarnin zuge glass kasa,kallonta yayi yanda iska ke daukanta,gashi ta falle mata gyalen da ke kanta gashi yaraf har kusan duwawunta,iska na kadashi sai ta kara kyau,driver yawa umarnin karbar apple da egg din hannunta,dubu biyar yawa driver umarnin mika mata,yana bata ta karba ta duba,hangame baki tayi ta dauki dubu daya,dama shine kudin apple dinta da egg da suka karba,ta mikawa driver sauran,da sauri omar ya kalleta yace karba nakine na baki,daria tayi ta glass ta girgiza kai tace tnx oga amma bazan karba ba.lips dinta ya karanta ya gane me take nufi,hannu ta daga masa ta juya cikin nutsuwa ta dauko dan gyalenta ta wuce,omar kasa dauke idonsa yayi daga kanta,sultan kuwa tuni yayi suman zaune yana kallo da mamakin abokinsa tare da jinjina kyau irin na iklas.

 

Danja taba da hannu amma omar sai waiwaye da kallon iklas yake,yanda take kai kawo a tsakiyar titi,yarinya irin wannan amma tana wannan sa’ar.take yaji ransa ya baci tausayinta ya mamaye zuciarsa, yar waye wannan aka barta tana garari a titi,tana da kuruciya haka,musulma.

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment