Littafan Hausa Novels

Lokacin da Nake Raye Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Lokacin da Nake Raye Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

LOKACIN DA NAKE RAYE

 

NA

 

JAMILA UMAR TANKO

(JUT)

 

Ko baa fada min ba na san na bar duniyar da take cike da zage-zage, cuta, mugunta, gulma, sharri, kage, yarfe da kazafi.

Na shigo duniyar da babu abinda kunnuwana su ke jiyo min sai kalamai masu kwantar da hankali kuma masu dadi.

Ba na ganin kowa, amma da alama,su suna ganina har ma sun san sunana.Ko baa fada min ba da alama na yi dace bayan mutuwata. Domin ina jin kamshi mai dadi, hade da sanyin iska mai ratsa jijiyoyi. Duk da ba na iya motsa ko dan yatsana amma ina jin radadi da zugi daga wasu sassan jikina. Ina kyautata zaton an yi min azaba ne akan laifukan da na aikata a duniya kafin nan daga baya aka dawo da ni cikin ni’ima.

 

Fitar Rabo Hausa Novel Complete

Tabbas ni mai laifi ce “a lokacin da nake raye,” manyan laifinka ma kuwa, dan haka ina ganin an yi min hukunci mai sauki ma hakan. Domin Allah mai afuwa ne kuma mai gafara ne.

Ina ihu ina kuka, sannan ina ta tuba gami da neman ceto daga wanda aka ce zai cecemu wato Manzon tsira S.A. W, da alama babu mai ji na.

Wannan ita ce ranar da ake fada mana zata zo, wasunmu mu na ganin qarya ne ba zata zo ba. Ba zan iya tuna komai ba, na manta duk abinda na sani a duniya da sanadin da ya faru da ni, har ya kawo ni nan.

Ina cikin tsoro mai yawa da fargabar abinda zai faru da ni a cikin wannan rayuwar da nake ciki, wato rayuwa bayan mutuwa.

Ina da dukiyata mai yawa a duniya. Yanzu ina duniyar take? Ina dangina suke? Ina samarina suke? Amma babu kowa, daga ni sai halina.

 

” Innalilahi wa inna ilaihi rajuun.” Na ke ta fada a zuciyata ina ta maimaitawa.

 

To be continue ….

 

Madallah da ALQALAMIN JUT…

[10/03, 8:20 pm] +234 706 331 4484: LOKACIN DA NA KE RAYE 2

 

Na

 

JAMILA UMAR TANKO.

 

Sai kawai na ga ana tafiya da ni ba tare da an dauke ni ba, ko an taba jikina ba, wannan karon ina ta kokarin bude idanuwana in ga abinda yake faruwa da ni amma na kasa, haske kawai nake hangowa kadan-kadan.

Su ka kai ni zuwa wani waje mai tsananin duhu, na tabbatar an bar gidan rahma an shiga gidan azaba. Nan da nan zuciyata ta hasko min manyan zunuban da na aikata a LOKACIN DA NAKE RAYE.

Ban sha giya ba amma na siyar da giya, ban taba barin musulumci ba amma na auri ahlul kitabi, duk da ban yarda da abin da ya ke bautawa ba sai dai na sha shiga wajen bautarsu.

Suturar da nake sakawa ba ta yi daidai da koyarwar YARENA ADDININA ba, ina kwaikwayon tufafin nasara. Na ziyarci gidajen holewa babu adadi. Na guji iyayena ban kula da hakkunansu da su ka wajaba akaina ba, na sami dukiya mai yawa amma ban taimake su ba. Sai dai qawaye ne suka mori dukiyar.

Abu daya na sani na rike salloli biyar kuma na kan yi su akan lokacinsu, ina yin azumin farilla a watan Ramadan kawai.

Ina da halin da zan sauke farali amma ban taba zuwa aikin hajji ba ina jira sai na tsufa zan je. Na fi mayar da hankalina wajen ziyara kasashen holewa akai-akai kuma duk tsadarsa.

Dukka zunubaina tsakanina da mahaliccina ne, ban taba cutar kowa ba sai dai ni da aka cutar da ni. Babu wanda yake bi na bashi kuma, sai dai ni ce nake bi kuma an hana ni. Dan haka nake saka ran Allah Zai yi min afuwa Ya sassauta min.Yau ce ranar nadama sai dai nadamar ba za ta yi min amfanin komai ba.

Ba na ganin komai amma na ji ana tattaba ni ana jujjuya ni kamar waina, yayin da ko ina na jikina ya dauki wani radadin zafi marar musaltuwa, tabbas mai rai ya shiga uku.

Tun daga nan hankalina ya dauke ban sake sanin abinda yake faruwa ba kuma.

 

*** *** ***

Na ji wata murya mai sanyi ta yi min rada daidai kunnena. Aka ambaci sunana kamar dai ana tashina daga dogon baccin da nake yi, ko kuma doguwar suma ko kuma in ce daga mutuwar da na sake yi. Muryar Namiji ce, amma ba da yarena yake magana ba, sai dai ina jin yaren da yake yi min magana, a lokacin da nake raye.

Ya ce ” Hino samba, ni na san ki a LOKACIN DA MU KE RAYE, amma ke ba ki sanni ba, ina rokonki da ki zauna da ni a sabuwar duniyar da mu ka zo, ina fatan mu bude sabuwar rayuwa a wannan duniyar. Na kasance mai matukar qaunarki wacce ban taba yiwa wata ‘ya mace ba. Ina ki ka buya duk tsawon rayuwarmu ba mu taba haduwa ba sai bayan da mu ka shude? Ba mu hadu ba sai a lokacin da ba ma raye.

Hino samba! Yau za ki shiga wani siradi mai hatsarin gaske ko ki dawo ko kuma kin tafi kenan. Idan kin tafi ba ki dawo ba ki saka a ranki ba zan taba mantawa da ke ba kuma kullum zan rinka tunawa da ke. Kuma ina rokonki da ki yi min masauki a kusa da ke, dan ina nan biye da ke ba da dadewa ba.

Na so ace a rana daya za mu yi wannan tafiyar, amma Allah Bai kadarta mana haka ba. Idan kuma kin dawo kin same ni ki yi min fatan idan za mu tafi mu tafi tare, idan kuma kafin ki dawo na yi gaba to ina can ina jiranki. Soyayyarmu ba za ta rabe ba har abada”

 

“Shin Ina za a kai ni ne? Daman akwai wata mutuwar bayan mutuwa?” Na tambayi zuciyata.

 

Ruwan hawayensa ne na ji ya disa a kan fuskata, nan da nan hankalina ya tashi. Tunda aka fara yi min kuka na tabbatar zan shiga wata sabuwar masifar da har ake tausaya min. Dan haka na yi iyakacin kokarina wajen bude idanuwana don in ga abinda yake faruwa a cikin wannan rayuwa, ta bayan mutuwa.

Giftawarsa na gani wato gefen fuskarsa sai kuma qeyarsa ya juya yana tafiya yana sharce hawaye. Ba irin halittarmu daya ba. Farar fata ne ba bakar fata ba, mai tsananin hasken fata da bakin gashi mai tsawo har kafadarsa.

Kamar wancan lokacin tafiya ake yi da ni ba tare da an taba jikina ko an ciccibe ni ba, haka ba tare da ana ja na a kasa ba. Ni baa sama ba, kuma baa kasa ba.

Wasu mutane na gani a kawaye da ni masu yawan faraa, fuskar kowannensu a cike da murmushi, su na yi min kalamai masu kwantar da hankali kuma su na ambaton sunana, sai na ji hankalina ya dan kwanta.

Kowannensu yana kiran sunana kuma yana yi min murna da na dawo duniyar da suke sannan su na masu yi min addua da fatan cewa wannan karon ma zaa yi nasara zan sake dawowa.

“Ina nake tafiya kuma nake dawowa? Wanne siradi zan shiga da har ake yi min fargabar ko in dawo ko ba zan dawo ba na tafi kenan?

 

Madalla da ALQALAMIN JUT

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment