Littafan Hausa Novels

Littafin Daren Farko Hausa Novel Complete

Hotunan Yadda Ake Kwanciya Da Mace
Written by Hausa_Novels

Littafin Daren Farko Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

A DAREN FARKO
Marubuciya: RABI’ATU NASIDI ABUBAKAR.
Kotun tayi tsit, kowa yayi jugum ana sauraron abinda zai fito daga bakin alqalin Wanda ya sukuyar da kansa yana rubuce-rubuce.

Lauyoyi da sauran ma’aikata wadanda suke da alhakin xama a kotun saboda sauraron shari’ah, kowanne yana zaune a mazauninsa daya dace dashi, haka ‘yan kallo da iyayen yarinyar da ake gudanar da shari’ar a kanta, al’amarin ya ba kowa tausayi shiyasa indai mutun ya kalli fuskokin kaso tara cikin mahalarta kotun sai kaga kowa cikin matsananciyar damuwa musamman wadanda abin ya shafa, iyayenta da ‘yan uwanta kenan.

Mai sharia Usman Muhammad ya daga kansa a hankali ya dubi wacce ake qara tana tsaye inda ake tsaida wadanda ake tuhuma hannayenta biyu sanye da ankwa. Baqar Riga ce da baqin hijabi sanye a jikinta kanta ba dankwali, idanuwanta sunyi wani irin ja saboda tsabar kuka, bata son dago kai ta dubi kowa saboda tsanar kanta da tayi, don haka ma da alqali ya kira sunanta bata dago kanta ba ta dai amsa cikin dusasshiyar murya wadda daqyar ake iya jin abinda take fada. Alqalin ya kuma cewa “Fatima Musa” ta amsa “na’am” “ke kika kashe Abubakar Siddiq Wanda akafi sani da doctor Khalifa”??? Fatima tayi shiru alqali ya maimaita tambayar har sau uku bata yi magana ba, yadda kasan kotun ba kowa saboda tsabar shiru. Kowa Fatima da mai sharia yake kallo ana sauraron abinda Fatin xata ce amma taja bakinta tayi shiru kamar dama can yadda Allah ya halicceta bata da bakin magana.
Mai sharia Muhammad Bamaina yana magana cikin yanayi na tausasa harshe yace “Fatima kotu tana tuhumarki da laifin kashe mijinki Dr. Khalifa kamar yadda aka kama ki da gawarsa shiyasa muke son ki bayyanawa kotu gaskiyar al’amari da bakinki tunda ke ba bebiya bace kuma ba kurma bace kina jin abinda muke fada kuma kina iya magana, idan ke kika kashe shi ki fadawa kotun , sannan ki fadi dalilin dayasa kika kashe shi, idan ba ke bace ki danyi magana kiyi bayani.
Fatima ta dago kanta a karo na farko ta dubi jama’ar kotun suka had a Ido da mahaifiyarta wadda ta zuba tagumi duk da nisan dake tsakaninsu da Fatima, Fati tasan kuka take wiwi tana girgiza kai, Fati ta dubi mai sharia said kawai taji kanta yana juyawa qafafunta suka shiga rawa, hakan yasa suka gaza ci gaba da daukarta gangar jikinta ta zube a gun, nan take mai sharia Usman M. Bamaina ya daga sharia zuwa uku ga watan gone un Allah ya kaimu.

Daren farko
Kotu ta rude da hayaniya, koke-koken iyayen Fati da ‘yan uwanta ya cika kotun, ga ‘yar uwarsu a matsanancin hali amma ba yadda xa ayi su taimaketa, suna ji suna gani wash ‘yan sanda mata suka daga Fati aka five da ita gaggawa saboda numfashinta me yake sama-sama kamar xai dauke.

Yammaci me aqalla zamu iya kiran lokacin qarfe biyar na gamma da wasu mintuna, Ummi na xaune gefen tabarma ta hada kai da gwuiwa tana kuka kamar ranta zai fita, Goggo Abu ce gefenta itama tana goge hawaye cikin yanayi na tsananin damuwa ko barka sansu ba kaga halin da suke ciki said ka taya su wannan kuka da suke, ko ba a maka bayani ba kasan damuwar dazata sa ayi irin wannan kuka ya is a a tayashi kuka. Malam Musa ya shigo da carbi a hannunsa yayi sallama ya tsaya daga can bakin qofa yana kallonsu tsawon mintuna biyar sannan ya qaraso inda suke, Allah sarki bawan Allah mai sauqin kai wanda bai dauki duniya baking komai ba, fuskarsa cike da tausayi da karaya yake kallonsu ya kasa magana, xuwa can Goggo Abu ta goge hawayenta cikin qarfn halo race Malam ka dawo? Sannu da zuwa. Ya daga mata hannu yace gaisuwar taki tunda idanuwanku baxasu daina xubda hawaye ba akan damuwar da muka samu kanmu ciki. Goggo Abu tace “Malam to yaya xanyi tunda abinnan ya faru Ummi bata daina kuka ba, nayi lallashin duniyar nan yarinyar nan taqi ta daina kuka had na rasa wacce kalma zan gaya mata wadda zatasa tayi haquri.

 

Malam have “Ummi kiyi haquri komu da muka haifi Fatima babu abinda zamu iya akan wannan lamarin sai addu’a. Cikin matsananciyar damuwa Ummi tace “Shin Baba shikenan saga haquri babu abinda zaku iya gaya min wanda xan samu sassauci a zuciyata game da halin da Fatima take ciki?? Wayyo Allah kaicon rayuwata ni Ummi in har xan xauna ina rayuwa a cikin tunanin Fatima na kulle a kurkuku ana tuhumarta da laifin da ni daku da duk duniya sun san baxata taba iya aikatashi ba. Yaya xa’ayi ace Fatima xata kashe rai? Kisan ma ace tarasa Wanda data kashe sai mijinta? Ka dubi wannan al’amari ayi wani abu akai har yaushe muna xaune Fatima na cikin mummunan xargi irin wannan.

Malam Musa yai zaman dirshan a wurin yace “Ummi to yaya xamuyu”? Saboda girman Allah me kike ganin xamu iyayi kinsan indai ace munada bakin yi din da yanxu va wannan xancen akeyi ba. Kinsan mudai ba kudi garemu ba, kuma ko idan mutum nada kudi in akace case din me xafi ne da tsanani iron wannan baka da ta cewa, kudinka baxa suyi amfani ba don baxa su sayi ran da aka kashe ba balletana ka sya domain ko diyya da ake biya idan wani ya kashe wani ba a irin wannan yanayin ake biyan diyya ba, kinsan ita sharia sabanin hankali CE duk yadda kake tunaninta ta wuce nan. Kuma idan ma muna da abin yin yanxu baxamu iya ba idan Fatima ba ita ta kashe Dr. Khalifa ba tai magana mana a kotu, kinaji kina gani daxu a kotu tayi shiru, ta bude bakinta tace ba ita ta kashe shi ba ta fadi yadda abu ya faru aqalla idan ma akwai abinda xa ayi ayi tunda tayi shiru me xa’ace?? Ya girgixa kai cikin dan xuciya yace “Allah kadai yasan yadda wannan abu ya kasance sai kuma Fatima.
Ummi ta ciji yatsa har yanxu kuka take mai ciwo a rai tace ” Shikenan Goggo tunda kuma kun yarda Fatee ita ta kashe Doctor sai kusa I do itama a kasheta ba tare da haqqinta ba, amma dai inaso Ku Sani ko ku kuka haifi mutum baku kuka halicceshi ba yadda kake da haqqin yayi ma biyayya haka shima yanada haqqinsa a kanka idan ka danne Allahu Subhanahu wa ta’ala xai tuhumeka Baba. Nikam ba zan bar maganar Fatee ta wuce haka ba, ba xan bari a cigaba da xalintarta akan abinda bata aikata ba, xan shiga in fita ko xan rasa xanin daurawa sai na taimaki Fatee In Shaa Allahu.

Boddiya Hausa Novel Complete

Malam yace Ummi bana shakku akan abinda kika fada mun tabbatar zaki aikata fiye da abinda kika fada akan Fatima qaunar dake tsakaninku ta wuce a fadeta da baki, Allah kadai yasan iyakacinta, sai dai inaso kisani ba wai mun yarda cewa Fatee itace ta aikata kisan ba, ki fahimci wani abu daya Ummi bamu da kudin da xamu iya daukar lawyer da xai kare Fatee, baki da buqatar mu gaya miki halin da muke ciki na qa-qani kayin rayuwa a gidannan kinsan kome da ina mukaga halin daukar lawyer sannan idan ma mun dauka da wacce hujja xamu fidda Fatee daga wannan zargi tunda taqi magana? Wannan shine dalilin dayasa muka miqawa Allah lamuranmu , idan Fatee ba ita ta kashe Doctor ba In Shaa Allah Allah xai bayyanar da gaskiyar al’amari Allah xai kawo mana mafita.

Ummi duk wanda nasa ya shiga matsanancin hali irin wannan ya gama kwanciyar hankali kada ki dauka bamu damu da ita ba illa iyaka shi lamari irin wannan idan kaga kanka a cikinsa baka tsananta damuwa wadda ita dama rayuwa jarbawa ce a cikinta, idan Allah ya jarrrabeka da wani lamari ka gode masa kawai ka roqeshi ya baka juriyar cin wannan jarbawa da yayi maka domin ba wanda ya isa ya kaucewa jarbawar Ubangiji. Kiyi haquri Ummi.

Ta jinjina kai face ” Na haqura Baba, na da kuka da hawaye tunda baka son ganin hawayen said dai ba xan iya haquri da Fatee ba koda nima xan shiga halin da take ciki, ko nima zan rasa raina, idan ba halin daukar lawyer ai Muna da halin daukar akwai guraren da ake taimako a samu agaji su taimako ne a gabansu kawai gabansu ba kudi ba, su ake kira gatan mara gata. Goggo tace Allah shine gatan mara tata shi xai xama gatanmu, Ummi kiyi haquri. Tayi murmushin qarfin hali tace Goggo na kanyi mamakin masu cewa inyi haquri akan maganar Fatee, waya ce banyi haquri ba? Tabbas nayi haquri domin na haqura da duk wani farin ciki In Shaa Allahu akan nemawa Fatee haqqinta sai inda qarfina ya qare koda hakan shi xai kasance abinda zan aikata na qarshe a rayuwa ta.

Suna a wani dab daki Mara girma Ummi da Barrister Nuruddeen, aka bude wata qofar dakin, wani kakkauran Dan sanda ne a gaba fuskarsa ba fara’a, Fatee na bite dashi a baya kamar ko yaushe baqar rigar nan itace a jikinta da baqin hijabi kai ba dankwali ta rame sosai tayi duhu idanuwannan kamar gauta saboda jan da sukayi, hannayenta biyu cikin ankwa, wani dan sanda a bayanta saidai shi fuskarsa akwai sassaucin ra’ayi.
Fatee ta dubi Ummi tayi murmushi cikin dusasshiyar muryarta tace “Ummi kune”? Dan sandan yace Ku gaggauta yin abinda ya kawoku Dan kar kuyi asarar lokacinku. Ummi ta girgixa kai hawaye wasu na bin wash ta taso ta dafa kafadar Fatima tace sannu Fati da izinin Allah zai kawo mana Marita a cikin al’amarinnan, min Shiga tashin hankali da damuwa akan halin da kike ciki Fati inajin ciwon damuwarki kamar zuciyata xata buga saboda tashin hankali. Wannan shine Barrister Nuruddeen Mustapha, na daukeshi ne don ya xamo lauyan da xai kareki a kotu. Fati inaso ki bamu hadin kai duk tambayoyin da xai miki ki bashi amsa sannan idan anje kotu a xama na gaba ki bude baki kiyi magana.
Fatima tayi murmushi hade da hawaye tace “Ummi bansan da wani kalamai amfani gun gode miki ba, komi na fada ba xai wadatar da xuciyata ba har inji cewa na nuna miki godiya ta kan soyayyar da kikemin da kuma qoqarin da kike don ganin kin ceci rayuwata daga wahala. Saidai inaso ki fahimci wani abu duk yadda kaso yankewa mutum wahala idan Allah bai qaddara lokacin yankewar wannan wahala tasa tayi ba baza ka iya yanke masa ba. Na godewa Allah daya qaddara min shiga wannan hali ina fatan wannan jarrabawar da Allah yayimin ta zamo kaffara a gareni, Ummi inaso ki sani ban tsananta baqin ciki akan halin da nake ciki ba ni a karan kaina wannan kukan dako yaushe xa aga idanuwana nayi ina yinsu ne saboda tausayin iyayena daku yan’uwana bisa halin da xaku Shiga da baqin cikin halin dana tsinci kaina a cikinsa, da kuma uwa uba rashin mijina Wanda zuciyata bata da juriya akan wadannan abubuwa biyu, wannan damuwar ba xanyi kuka ba in har akan halin danake ciki ne.
Zaman danake Ummi ina jiran ranar da za ayanke min hukuncin kisa ne inbi mijina. Idan har akwai taimakon da nake buqata daga gareku ayanxu shine ku taimaka a yanke min hukunci in huta wannan damuwar kuma ku huta domin idan an kasheni kun daina ganina dole wata rana Ku haquri, idan ko ina Raye haka xakuyi ta zama cikin damuwa.
Wannan shine dalilin dayasa naki magana a kotu kuma ina nan akan bakana na ba xance komai a kotu ba don bani da abin cewa duk abinda xan furta bai wuce ince bani na kashe Doctor ba, idan nace ba ni na kashe shi ba ina neman kariya kenan wadda ke nufin in ci gaba da rayuwata a duniya ba.
Ummi kiyi haquri kiba iyayena da duk yan’uwana haquri ki roqar min su gafara kowa yayi haquri ya manta dani bana buqatar taimakon kowa a gareku sai addu’a, na gode qwarai da gaske kada ki sake wahalar da kanki gun dauko min lauya……. Ummi ta katseta cikin huci tace “Fatima kin amince ki dauki laifin da ba naki ba, kin amince ki kashe kanki? Wayake kin taimako kin amince ki jawa dukkan zuriarku abin fadi?
Kina xaton wannan ba xai xama mugun aibi ga xuri’arki ba? Wanda xai ja a dinga aibata muku zuria mata su rasa maxajen aure?
Kina xaton idan an kashe ki wani xai sake zama lafiya cikin iyayenki da yan’uwanki?
To ki sauya tunani lauya tunda kince baki so na janye shi, amma ko shakka babu kuskurene babba wanda xaki tafka idan har kikayi iqirarin kece kika kashe Dr. Khalifa alhalin ba ke kika kashe shi ba.
Fatima tace to idan ni na kashe shi fa Ummi?
Ummi tayi murmushin takaici tace bakece kika kashe Doctor ba, don kuwa baki da dalilin kashe shi, kina fadin hakanne kawai Dan kin gaji da da duniya bakya son rayuwa a halin da kina son ki gaggauta barinta, shiyasa kike furta abinda xai raba ranki da hangar jikinki…. Dan sanda yace “lokaci yayi” Ummi ta ce kayi haquri ina fada mata abinda xai amfaneta ne. Yace bashi da amfani gareta da sai ta karba kidaina wahalar da kanki.
Ya tisa qeyar Fatee, kallon data waiwayo tayiwa Ummin ta wuce shiyasa tsigar jikin Ummi ta shiga tashi ta zube qasa ta riqe kanta da hannu bibbiyu. Shi kansa Barrister Nura jikinsa yayi sanyi, ya jima xaune a gun yana kallon Ummi, daga can yadan ja numfashi yace “tashi mu tafi Ummi fun anan na tabbatar yarinyar nan Fatee ba ita ta kashe Doctor ba duk da cewa taqi amincewa da duk wani taimako daxa a bata ta rufe duk wata qofa ta kariya daxa a bata, ba wani abune kuma yasa tayi hakan ba tayine kawai saboda baqin cikin dake damun xuciyarta Wanda yake tafarfasa xuciyarta yasa rayuwa ta fita a xuciyarta.
Hakan yasa taqi magana a kotu wannan taqi yarda da taimakon da za a bata, ba komi Allah yana tare da masu gaskiya, sannan baya goyon bayan xalinci, indai bata da haqqi da sannu xakiga hukuncin da Allah xaiyi.
Ummi bata kuma cewa komi ba har suka fice daga gun.
*********×××************
Da sauri ya goge hawayen dake xuba a idonsa jin sallamar matarsa, Goggo Abu ta xauna sharaf a gabansa jikinta na rawa ta ajiye flask din abincin da tazo kawo masa, yadda jikinta ke rawa haka muryarta take rawa, tace Innalillahi wa inna ilaihirraji’un Malam kuka kake? Yayi dan murmushi yace “haba dai kuka ba kuka nake ba Zainabu” race “don Allah kar kace haka Malam bayan ba gani da idona kana kukan kuma naji shasshekar kuka, Malam idan kayi kuka akan wannan al’amari mu kuma yaya xamuyi da ranmu? Kai kake nuna mana muyi haquri bisa fushi da yin Allah me xai sa kai kayi? Malam Musa yace ” Zainabu al’amarinnan yana matuqar bani mamaki da daure min kai, yaya xa ayi Fatima ta iya kashe mutum? Idan mince ba ita ta kashe shi ba wane ya kashe shi? Alhalin daga ita sai shi a gidan dakin a rufe da sakata ta ciki. Me yasa Fatima ta kashe Doctor Khalifa me yayi mata? Meye iyayen Khalifa basu yi mana ba? Shi kansa Khalifa n meye bai yi mama ba? Ace Fatima ta rasa tukuicin da xata sakawa wadannan bayin Allah sai da wannan mummunan aikin? Goggo Abu tace “Malam ka yarda Fati ta kashe Doctor Khalifa? Yace “to Zainabu idan ba ita bace waye? Daga ita sai shi a daki ya shiga ya rufe qofa shi xai kashe kansa ne Zainabu?” Tayi shiru na lokaci mai tsawo, daga bisani ta jinjina kai tace ” ko shakka babu a cikin wannan al’amari akwai rikitar da qwaqwalwa sannan duk Wanda yayi wannan aikin Wanda yasan sirrin gidanne , tabbas Fati ba ita ta kashe Doctor ba don bata da dalilin kashe shi ko tanada dalilin kashe shi bata da qarfin halin da data aikata wannan mumnunan aikin, saboda xuciyarta ta tana da sauqi akan al’amura, Allah kadai yasan yadda al’amarin ya kasance.
Cikin sanyin murya Malam yace “Zainabu nima abinda yake damuna kenan kowa ma haka yake fada su Kansu iyayen Khalifa haka suke cewa basu yarda Fati ta kashe shi ba, to amma me yasa baxa tayi magana a kotu ba idan aka cigaba da tafiya a wannan hali xa a samu mafita? Tunda ba it a bace tayi magana mana ” wannan shine abinda ya damu kowa ma ba kai kadai ba Malam.
***********×××**********××********
Kasancewar mahaifin marigayi Dr. Khalifa babban mutum, daya daga cikin masu fada aji a cikin gwamnatin garin ya basu damar ganin Fatima cikin isasshen lokaci ba tare da tsayawar yan sanda ba, ko kuma ankwa. Alhaji Muhammad Nazif mahaifin marigayi Dr. Khalifa da Hajiya Maijidda mahaifiyarsa suna zaune a wani babban daki da aka qawata da kujeru, Malam Musa da Goggo suna zaune gefensu sai babban wan su Fatima da kuma Ummi da Barrister Nuraddeen , Fatima na tsakiyarsu kanta a qasa ba kuka take ba su dinne baki dayansu ke sharar qwalla sakamakon matsanancin tausayi da bayanin da take furtawa ya basu, Alhaji Muhammad yace “Fatima abinda nakeso ki gane shine dukkanmu nan munsan ba me kika kashe Dr. Khalifa ba saboda kamar wanda xaiyi kisan kai ya fita daban, koda auren dole akai maki dashi ba xa ki iya kashe shi ba balletana anyi aurannan ne da amincewarki, ke yarinya ce mai biyayya ga iyayenki, wadda kike xaune da kowa lafiya kowa na yabon kyawawan halayenki tayaya xa ayi mu yarda kin kashe Dr. Khalifa.
Ki bude bakinki Fatima nan ba kotu bane mu ba lauyoyi bane mu iyayenki ne duk duniya ba wanda kike dasu wadanda suka fimu idan rufin asiri ne ba rufin asirin dayafi na Allah, ba wanda xai rufa miki asiri bayan my, ki gaya mana sauran lamari waya kashe Dr. Khalifa?
Falon yayi tsit kamar ba kowa sai qarar AC ko motsi Fati bayayi ba balletana tabasu amsa, Malam Musa yace Fatima dake muke magana ki gaya mana yadda akayi idan ma ke kika kashe Dr Khalifa yaya xanuyi dake? Khalifa dai ya mutu kuma baxai dawo ba, fada mana gaskiya shi yafi dacewa, kullum hankalinmu a tashe yake Fati bamu da sukuni idan mun kwanta don muyi barci barci baya yiwuwa, abinci baya ciwuwa, muna cikin matsananciyar damuwa bansan da wani ido xan kalli iyayen Khalifa ba, bansan da wanne ido xan cigaba da kallon yan’uwansa ba da mutanen unguwa, ba wani abu ne ma ba Fatima shirun da kikayi har yau baki fadi wata magana wadda za a kama ba akan maganar nan kin mana adalci, dukkan yan’uwansa da masoyanki kowa yana cikin damuwa. “Ni na kashe shi baba”
Akayi tsit kowa ya zuba mata ido, Maijidda kallonta kawai take tayi tagumi dansu da suke mutuwar so Khalifa ta sake rushewa da kuka. Goggo Abu tace “shikenan tunda kin ce ke kika kashe shi to lallai ne ki daina wahalar da mutane idan anje kotu ki fadi dalilin dayasa kika kashe shi, kinsan ba wai kice me kika kashe shi kiyi shiru ba dole ne ki fadi abinda yasa kika kashe shi.
Ummi ta riqe hannun Goggo ta xaunar da ita tace “Goggo meye amfanin yin hushi da Fati alhalin kowa anan yasan takura matan da akayi da maganar nan yasa tace ita ta kashe shi to haka idan ma akaje kotun aka takura mata abinda zatace kenan qarshe idan tace ita ta kashe shin dole tayi shiru tunda bata da dalilin da xata fada wanda yasa ta kashe shi.
Goggo tace shikenan Ummi haka za muyi ta xama cikin damuwa tunda ba ita ta kashe shi ba idan anje kotu ta fadi iya abinda ta sani mana.
Fatima tana kuka tace “kiyi haquri goggo baqin cikin damuwar da nasa ku yafi damuna fiye da kowa saidai ba yadda xanyi, Goggo baxan iya cewa bani ba kashe Dr. Khalifa ba saboda gaba daya bayan sun tabbatar da cewa ni na kashe shi. Kuyi haquri shirun da nayi a kotu wannan shine yafi damuna, idan nace xanyi maganar bansan avinda zan fada ba qarshe dai nasan duk abinda shirun nawa xai haifar bai wuce a yanke min hukuncin wanda yayi kisan kai bane a kashe ni.
To dama abinda nake jira kenan, ni kam rayuwa ta qare a guna sai dai jiran lokaci ko ba’a kashe ni ba baqin cikin halin da iyayena kuka shiga a sanadiyya ta da baqin cikin rashin mijina shi xai sa xuciyata ta buga in mutu baxan iya cigaba da rayuwa ba shiyasa bana buqatar taimako ta kowani fuskar lauya don kubutarwa idan akwai abinda nafi buqata bai wuce addu’a ba, wannan ba sai na roqeku ba nasan kuna yimin. Don Allah ku yafe min babu abinda xan iya cewa a kotu.
Aliyu yayan Fati yayi magana a karon farko tun xamansu a dakin yace “Fatima bamu amince kici gaba da yin shiru a kotu ba dole kiyi magana”.
Tace shikenan yaya xanyi maganar.
Alhaji Muhammad da kowa yafi sani da Abba yace “kar kice ke kika kashe shi Fati”.
Tace “Abba idan nace bani na kashe shi ba waye? Idan akayi bincke aka gane ni din ce abinda ake guru shi xai faru, kuna fadin haka ne don fa Ku Samar min mafita wadda xata bani damar ci gaba da rayuwa a duniya, yayin da ni kuma bana son rayuwar ta fita daga raina so nake na bar duniyar yadda mijina ya barta.
Aliyu yace ” Anya Fati baki samu tabin hankali ba?
Tace “lafiya qalau nake yaya” kowa ya rasa abin fadi akayi shiru.
************×××*************
Da sassafiyar ranar da xa a koma kotu Hajiya Maijidda da aka fi Sani da Mama tana kwance kan faffadan gadonta na na alfarma tunani da baqin cikin duniya ya isheta ta rasa abin da ke mata dadi, tana mutuwar son danta an kashe mata shi, wata qanwarta dake tayata zama wato Aunty Sadiya ta shigo dauke da abincin karin kumallo ta xauna kusa da ita suka gaisa tace “kidaure ki sha koda ruwan sanyi ne xama da yunwa yafi komi illa duk abinda ya faru rubutaccen al’amari ne babu Wanda ya isa ya goge shi”.
Ta miqe zaune ta xubawa Aunty Sadiya ido tace “Aunty Sadiya kina ganin haka ya dace mu xubawa lamarinnan ido kullun Alhaji yana cewa Fatima baxata kashe Khalifa ba, toh ni so nake a gaya min wa ya min dana?
Aunty Sadiya ta ce “tabbas kam Fatima baxata iya aikata wannan mugun aiki ba, abinda yake sarqaqiya shine daga shi sai ita a dakin to waye ya shiga ya kashe shi?
Mama tace “ke Sadiya idan ma ba ita ta kashe shi da hannunta ba to da hadin bakinta aka kashe shi saboda ana ganin ubansa yana da dukiya dansa dayane ko don a mallake dukiyar ubansa xata iya yi masa haka.
Aunty Sadiya ta ce “ki gafarceni amma tari numfashinki ba to amma idan haka ne da hadin baking Fatima yaya xa ayi ita data kashe shi ko ta hada baki aka kashe shi bats gudu ba har akazo aka kamata? Allah (SWT) dasu kuma mahukuntan tunda Allah ya basu basiran gano gaskiyar wannan al’amari cikin hikima da ixinin Allah zasu gano mana wanda ya kashe mana da jininsa tafi a banxa ba.
A bisa hanyarsu ta xuwa kotun ne cikin mota mitar da Mama ke tayi wa Abba kenan yayi tsit yana jinta ko tari baiyi ba yayi tagumi yana jan carbi.
Suna shiga su Malam da Goggo suka shigo suka gaisa, Abba yace “Malam bana jin dadi yadda kake kaucewa haduwa dani tunda wannan abu ya faru”. Malam ya rufe fuskarsa yace “haba Alhaji me xan ce dakai? Me nake dashi wanda xan gaya maka da har xaisa in tsaya in kalleka, kaico. Ina baqin cikin faruwar wannan al’amari har ina cewa ina ma ace banxo duniya ba dadai ace ‘yar cikina ta kashe Dan mutumin kirki kamar kai dinnan Alhaji Muhammad.
Abba yaja hannunsa suka wuce cikin kotu ba tare da yace komai ba, wuri daya suka zauna mutane suna mamaki sosai yadda suke ganin iyayan wanda aka kashe da iyayan wacce ake xargin tayi kisan. Wannan abu yana matuqar baiwa mutane mamaki haka xakaga jama’a na kallonsu, yau dinne ma dai Hajiya Maijidda ta sauya fuska sama-sama suka gaisa ba wani magana da sukayi fuska tamau, koda aka shigo da Fatima ma ko kallon inda take batayi ba.
Ummi kamar tafi su kansu Fati shiga tashin hankali ta rame ta lalace.
Fati na shigowa kotu da Ummi suka fara ido sannan ta dubi iyayenta da sauri ta dauke idonta zuwa qasa tashin hankalin da take ganin iyayanta a ciki ko wannan ma ya ishi mutum tashin hankali da baqin ciki ina amfanin rayuwarta.
Yau kam duk abinda xai faru saidai ya faru saita kawo qarshen wannan xaman kotu.
Bayan da akayi abubuwan daya dace ayi aka xauna mai karantawa ya karanto, tuhumar da akeyi wa Fati na ta kashe mijinta a ranar da aka daura musu aure a daren farko.
Mai sharia Usman Muhammad Bamaina yace ” Fatima kinji tuhumar da ake miki a karo na biyu?
Ta gyada kai tace naji ya mai sharia, yau kowa najin muryarta sosai, kuma kowa yaji dadin yadda tayi magana har alamun nutsuwa a fuskar iyayanta da yan’uwanta musamman Ummi wadda jikinta har tsima yake a ranta tana fadin yawwa Gwara kiyi wa kanki adalci da iyayanki damu masoyanki. Mai sharia yace “Fatima Musa me xaki iya fadawa kotu akan haka? Ma’ana kin amince ke kika kashe mijinki Dr. Khalifa?
Kai tsaye ta ware muryarta tace “Eh ni na kashe shi ya mai shari’a.
Gaba daya kotu ta rude da salallami kowa ba fadin albarkacin bakinsa, iyayan Fati dasu kansu surukan suka rude, Ummi kuwa hannu ta dora aka tana fadin “wayyo Allah na wayyo Fati me yasa kikace ke kika kashe Dr. Khalifa bayan ba ke kika kashe shi ba.
Mai sharia yayi tsawa akayi tsit sai dai kukan ‘yan’uwan Fati da baya qarewa, ita kuwa Fatin yau tana tsaye qyam ko gezau ga dukkan alamu xuciyarta ta fara soyewa, idanuwan amma ba kuka take ba xafin zuciya ne, bata son ta kalli iyayanta taga mummunan tashin hankalin da suke ciki, dama can ita mutum ce mai tsananin tausayin mutane balletana iyayenta.
Mai sharia yace “Fatima kotu tanason kiyi mata bayanin dalilin da yasa kika kashe mijinki a daren tarewarku.
Fati tace “bansan dalilin da yasa na kashe shi ba, ba abinda xan iya furtawa akan haka ya mai sharia ina roqon wannan kotu mai alfarma da ta taimaka min ta yanke min hukuncin kisa a yau inbar duniyar in huta, bana son bugawar da xuciyata keyi ya xamo sanadin mutuwa ta nafi son a yanke min hukunci daidai da laifina.
Ta numfasa tana kallon alqalin daga bisani ta dauke idanunta daga kansa xuwa kan jama’ar dake kotun, gaba dayansu suma ita suke kallo kowanne da abinda xuciyarsa ke saqa masa game da ita.
Tayi shesshekar ajiyar xuciya tace iyayena da ‘yan’uwana da dukkan masoyana ina roqonku don girman Allah wannan yanayi da nasa ku na damuwa sannan kuyi min addu’a ,rayuwata ta fita daga raina minti daya bana son in qara a duniya nafi son inbi mijina.
Tayi shiru kamar yadda kotun ma tayi tsit kai kace ba kowa a kotun, alqali yana ‘yan rubuce-rubucensa, haka a bangaren lauyoyi wasu suna rubutu wasu shiru kawai sukayi suna kallon Fatima.
Ta cigaba da fadin ya mai sharia a karo na biyu ina roqon a taimaka a yanke min hukunci daidai da laifina nice na kashe mijina.
Wani daga cikin lauyoyi ya miqe ya nemi ixinin magana daga gun mai sharia yace kanada daman magana.
Yayi godiya ya ce sunana Barrister Abbas Mukhtar ina son kare wadda ake qara saboda na fahimci ba ita tai kisan nan ba ina nufin Fatima Musa ba ita ta kashe mijinta Dr. Khalifa ba ina roqon wannan kotu mai adalci data bani damar yin cikakken bincike akan wannan al’amari, kuma inason a bani damar da xan yiwa Fatima tambayoyi akan abinda ake tuhumarta dashi.
Mai sharia yace “kana da damar yin haka. Yayi dariya yana dan murmushi ya qara maida fuskarsa ga Fatima wadda itama shi take kallo fuskarta a tsuke, yace Malama Fatima Musa qarfe nawa aka kaiki gidan mijin kuma a wacce ranace? Fatima tayi shiru kamar ba da ita ake magana ba, Barrister Abbas ya qara maimaita tambayar tare da roqon kotu data tursasa Fati tayi maganar.
Mai sharia yayi hakan amma Fatima cewa tayi “nagode da kake burin taimakona a bisa halin da nake ciki, saidai inason kayi haquri gaskiyar magana baxan iya baka amsa ko daya ba abisa tambayar da kake min saboda ba so nake in kubuta daga halin da nake ciki ba, wanda yake buqatar lauya shi yake son tsira, na gaya muku bana buqatar rayuwa don Allah ku yafe ni.
Mai sharia Usman Muhammad Bamaina ya dubi wani dogon dan sanda dake tsaye a gefe yace “xa a gwada qwaqwalwar Fatima don mu tabbatar da mai hankli muke sharia, idan munyi xama na gaba xamuji sakamakon sannan mu dora inda muka tsaya. Daga nan aka daga qarar xuwa mako biyu idan Allah ya nuna mana, amma kotun ta bawa bangaran lauyoyi guda biyu damar suyi duk bincikensu akan yadda al’amarin ya kasance don bada kariya ga wadda ake xargi.
Yau ma kamar wancan karon kotun ta tashi da hayaniya kowa na fadin albarkacin bakinsa akan kafiyar da Fati tayi a shariar mamakin datake bawa yawancin mutane shine tayaya xa ayi mutum yace shi ya fidda rai kwata-kwata da rayuwa mutuwa yake muradi, wasu suna ganin wannan ya isa kowa ma ya amince ba ita tayi kisan ba, yayin da wasu ke ganin dan ace ba ita bace shiyasa ta sallama ta miqa wuya, idan ba ita bace waye? Gida su biyu kacal ba kowa daki a kulle su biyu inhar ance ba Fati ta kashe Dr. Khalifa ba to saidai ace shi ya kashe kansa, hatta Hajiya Maijidda mahaifiyar marigayin da yawwa daga ‘yan’uwansu abinda suke gani kenan wannan kukan da take abinda suka dauka shine na munafunci ne kawai.
A harabar kotun kafin su tafi gida Malam Musa ya tsaida Barrister Abbas yana masa godiya a bisa qoqarinsa na kare ‘yarsa, Barrister yayi murmushi yace “ba komai kada ka damu Baba nayi wannan ne domin Allah da tsananin tausayin da Fatima ke bani tun randa aka fara tsaida ta a gaban sharia na tabbatar ba ita tayi wannan kisan ba, duk wanda ya kashe Dr. Khalifa na gida ne wanda yasan sirrin gidan In Shaa Allahu da ixinin Allah xamu gano ko ways, saidai inason ka taimaka min Fatima ta dinga bada ansa a kotu sannan xanje in ganta ku taimaka min tayi cikakken bayanin duka tambayoyin daxan mata dan insan yadda xan bullowa al’amarin. Malam yace “to ni na rasa me yasa Fati ta ke tsuke bakinta komi sai tace ba xata iya fada ba saboda rayuwar ta fita daga ranta. Barrister yayi murmushi yace “ba komi tsananin damuwane yasa take fadin haka, matsayinku na iyayenta ku ya dace ku lallabata ta fadi yadda akayi.
Malam yayi masa godiya mai yawa, bayan tafiyarsu Malam din Barrister na xaune a motarsa shi kadai yana naxarin al’amuran Fatima tausayinta har yayi mass yawa a xuciya, daurewa kawai yau yayi yazo kotun run a wancan xaman da akayi hankalinsa ya tashi sosai game da al’amari n yarinyar, run lokacin abinda yake daga masa hankali matsalar daya kowama itace shirun da Fati ta yi tana neman mutuwa ido rufe taqi bada hadin kai ballantana a samu mafita.
*****************××××***************
A hankali Ummi ta fito daga motar tabi mama cikin gida, ko wanne xuciya ba dadi, a falo suka zauna gaba daya yayin da ita ta dawo da baya xuwa ainihin dakin Dr. Khalifa na gidan har yanxu makullan dakin yana hannunta ita kadai take budewa ta shiga tun daga lokacin da ya mutu xuwa yanxu, komi na nan yadda yake wani irin qanshi mai dadin gaske yana tashi a dakin, gaba daya kayansa na sawa suna jere a cikin wardrobe gwanin ban sha’awa manyan hotunansa da akayi enlargement dinsu guda biyu na gefe da gefe na gadon yayi kyau bana wasa ba.
Ta xauna a gefen gadon tasa hannu ta dauki hoton ta rungume kam-kam idanunta a rufe hawaye wasu na bin wasu xuwa can ta ajiye ta shiga bude durowowin jikin madubin hotunan bikinsa birjik musamman ma gun launching da dinner da yawa ya rungume Fatin ne kam-kam a qirjinsa wasu kuma tare da abokansa maza da mata.
Kan cinyar Ummi ya jiqe da hawaye kamar ruwa aka xuba mata a cinya tun ranar da aka kashe Dr. Khalifa take kuka amma bata taba kuka irin na wannan ranar ba, har saida taji numfashinta kamar xai dauke.
Ba xata taba mantawa da abinda ya gaya mata ba a yamnacin lahadin da xa’a kai Fatima gidansa wanda kuma a wannan ranace aka kashe shi bai sake kwana a gidan duniya ba.
Yana tsaye a harabar gidansu tare da many an abokansa biyu wadanda baida aminai kamar su, manyan likitoci Dr. Hafiz Bala Muhammad da Dr. Mustapha Abubakar Kura, yana tsakiyarsu suna hira, sai ita Ummi ta fito daga cikin gida tana ganinsu tahau yi musu photo a wayarta, Dr. Khalifa ya harareta yace “wai me yasa kike da raina mutane ne Ummi ni kikewa hoto? Sai Dr. Mustapha yace “kaima kana da saurin fushi Khalifa ko wacce rana idan an maka abu xaka bata rai banda wannan rana wadda ta zamo ta auranka da matar da ta zamo allurar cikin ruwa kaine ka xamo mai rabon daka xuqota” Dr. Khalifa ya rausayar da kai yana murmushi tare da lumshe ido yace “ka fadi gaskiya Dr. Mustapha tabbas nine na cafko wannan allurar data xamo ta mai raboce, a daidai lokacin da ba fidda rai da ita sai na jita kawai a hannuna, tabbas wannan rana ta dace ta xamo ta farin cikina, ranar da xan sadaukar da komi nawa saboda Fatima”.
Ummi tayi murmushi tace “shiyasa nima nake maka hoto domin kayi min kyawun da ban taba ganin kayi shi ba a duniya dukda cewa kai din me kyau ne kullum kyau kake da ado”
Dr. Hafiz Bala yace “har bayan hoto yanada kyau yayi miki kyauta ta mussamman Ummi”
Dr. Khalifa yayi murmushi yace “ko shakka babu a wannan rana ina cikin farin cikin da ban taba samun kaina acikinshi ba, saidai kasan tun safe gabana ke faduwa bansan dalili ba wannan yayi sanadin dayasa tun ruwan shayi da nasha rabin cup dazun bayan daurin aure ban iya cin komi a bakina ba.
Ummi tayi wal da ido tace “faduwar gaba kuma Dr a irin wannan rana? Nidai nasan ko kusa bakayi kama da wanda mace xata bawa tsoro ba ballantana ince firgita kayi saboda Fatima. Dr. Mustapha ya bugi kafadarsa yace “wa wannan? Ni tunda nake ma ban taba ganin namijin da yayiwa mata farin sani irinsa ba, farin cikine yayi masa yawa saboda soyayayyarsa yasa ma gabansa yake faduwa……
Tunanin Ummi ya katse anan lokacin da Mama ta turo qofar dakin ta tsaya tana kallon Ummi kukan da take ya bata tsoro ta qaraso da sauri takamata ta kwashe hotunan da suka jiqe da hawaye ta mayar, ta kamo hannunta ta fito da ita ta rufo dakin ta karbe makullin tace “daga yau ko qofar dakinnan banaso ki sake xuwa,haka kada ki qara xuwa kotu baxa muyi biyu babu ba, mun rasa Dr. Khalifa muna cikin baqin ciki mai tsanani kema damuwa na neman xama ajalinki to bazai yiwu ba.
Cikin kuka Ummi tace “Don Allah Mama kada ki haramta mini shiga dakin likita, yin hakan ne kadai xaisa xuciyata ta sassauta daga damuwar da nake ciki, na rasa dan uwana ga aminiyata na cikin matsanancin xargi nabi duk hanyoyin daya kamata inbi don ganin Fatima taba lauyoyi hadin kai taqi burinta a kashe ta, me yasa baxanyi kuka ba Mama? Mama tayi tsaki tace “ina mamakin yadda ke da Alhaji kuka dauki damuwar duniya kuka dorawa kanku akan Fatima shin da kuke cewa batace komi ba me xata ce? Fatima bata da abin cewa shiyasa tai shiru, ko a hankalce kun san qaryane ace akwai mutumin da ake tuhuma irin haka yaqi amsar taimako daga lauyoyi don kawai yana burin mutuwa.
Kin taba ganin wanda ya xauna yana jiran mutuwarsa kuma yana maraba da ita, saidai fa in taxo a karbeta don ba yadda xa’ayi da ita.
Ummi ta saki hannun Mama ta xuba mata ido muryarta a dishe tace “Mama shin kina nufin kin amince Fati xata iya kashe likita?
Mama tayi murmushi tace “Ummi kiji tsoron duk wanda kika taimaka wa. Akoda yaushe idan xaki taimaka wa mutum ki taimaka keshi kai tsaye don Allah bawai don xai saka miki da alkhairi n da kikayi masa ba, shi dama mutum babu abinda yake cika cikinsa sai qasa shi mai butulcewa mahaliccinsa ne ma ballantana ace wani gama garin mutumin don haka ba abin mamaki bane ga mutumin da ka dauko shi daga rana ka dawo dashi inuwa shi kuma ya tura ka ranar, a cikin mutane mutumin da yake salihi ko mai shiru-shiru irin Fatima mutane basa xarginsa da mugun abu saboda yanayinsa amma Allah (SWT) daya halicci xuciya shi yasan abinda ke cikinsa.
Ummi ta yi shiru na lokaci mai tsawo daga bisani tace “Mama kina nufin kin amince a kashe Fatima akan kisan likita?
Tace “Ummi bani da masaniyar abinda shariar xata haifar, saboda ita sharia macece da ciki ba wanda yasan abinda xata haifa sai Allah mudai mun miqa kukanmu ga Allah ya bayyanar da gaskiya”.
Tayi gaba tabar Ummi tana binta da ido jikinta yayi sanyi qalau daqyar ta daga qafa ta bita cikin gida.
Maganganu sunyi yawa akan abubuwan da suke faruwa a kotu, wasu sun fara yarda tunda tace ita ta kashe Dr. Khalifa yayin da wasu har yanxu suna ganin baqin cikine ya hanata magana dukda cewa su dinma suna ganin Fatima batada hujjar da xata sa bakinta tayi shiru taqi cewa komi.
Kwana biyu da xaman kotu Malam Musa da mahaifiyar su Fatima da Ummi da Barrister Abbas suka isketa a inda take tsare a bisa alfarmar mahaifin marigayi, Alhaji Muhammad amma fa akwai sa idon yan sanda guda biyu.
Fatima ta rusuna ta gaida mahaifinta ciwon rai ya qara damunta sakamakon ramewar dataga ya Dada yi ya fita hayyacinsa kaida ka gani kasan yana cikin matsananciyar damuwa da takaici, sannan ta gaisa da su Ummi da Barrister.
Malam yace “Fatima”.
Ta amsa “Na’am Baba”.
Yace “Fatima wannan shine xuwa na qarshe da xanyi gunki akan in roqi kiyi bayani a kotu idan kinga dama kiyi maganar Fati idan bakiga dama ba kici gaba dayin shiru tunda kinfi buqatar muci gaba da xama cikin tashin hankali da rashin sanin abinyi.
A yau naxone ba dan in roqeki kiba lauyoyi da alqali amsar duk tambayar da suka buqata a gunki ba xuwa nayi in baki umurni a matsayina na mahaifinki idan ya cancanta kiyi min biyayya kiyi Fatima idan kuma ban isa ba kici gaba da yin shiru kamar yadda kika saba.
Fatima tace “Baba idan nayi bayanin xai sauya qaddara ne? Ko kuwa bayanin nawa xai dawo da Dr. Khalifa xuwa gidan duniya, Baba idan nice na kashe Dr. Khalifa idan ma ba ni bace Allah SWT ya san haka tunda shi yake ganinmu a lokacin da muke kulle mu biyu acikin dakin ni da Dr. Khalifa, nidai abinda nakeso ayi amfani dashi shine tunda naji na gani na amince nice na kashe shi nayi iqirari da bakina ayi min hukunci daidai da laifina shikenan sharia sai a gaban Allah SWT wannan itace rana da xa a tsage gaskiya ranar da kowa zaiyi bayanin abinda ya aikata da gabobinsa bama da baki ba kuma itace dawwamammiyar rayuwa wadda baxata qare ba har abada.
Don Allah Baba kayi haquri kada kayi fushi dani akan haka babu abinda bakina xai iya furtawa a lamarin kisannan.
Ummi tace “Fati mahaifanki sun kasance suna masu alfahari dake a bisa biyayya da kike musu, baki tabs yin musu dasu ba, ba a taba samun wata rana da suka baki umurni kika saba ba, me yasa a wannan karon xaki saba musu? Baki da hujjar daxa kice rayuwarki taxo qarshe Fati, ko kuma don kina jiran mutuwa shiyasa kike ganin biyayya ga iyayanki bata da amfani?
To bari in tunatar dake wani abu guda daya Ance akwai mutumin da xaita aikin alkhairi wanda yake share masa hanyar tafiya aljanna sai qarshen rayuwarsa taxo sai kawai ya aikata wani abu wanda xai kaishi wuta sai ya shiga wuta. Yayin da wani xaita aikata aikin da xai kaishi wuta gab da mutuwarsa sai ya aikata abinda xai kaishi aljannah sai ya shiga aljannah.
Fatima ina roqon kiyi abinda iyayanki suka buqata baki da hujjar da xaki saba wa umurninsu, baki da tabbacin kwananki ya qare mutuwa xakiyi Fatima.
Barrister kallon Fatima kawai yake ya yadda xai yi da tausayinta a xuciyarsa, ya matso daf da ita muryarsa qasa-qasa yace “Fatima qarfe nawa aka kaiki gidan Dr. Khalifa?
Ta amsa “qarfe biyar da rabi xuwa shida a wannan tsakanin bai wuce haka ba.
Gaba daya saida fuskokinsu suka nuna jin dadin hadin kan da ta fara badawa. Barrister yace “a wacce rana kensn Fatima? Ta amsa ” A ranar lahadi biyar ga watan uku”
Ya gyada kai yana murmushi yace “Fatima suwa da waye suke cikin motar da aka kaiki? Tayi dan jim daga bisani tayi murmushi tana kallonsu tace “Ummi xata fini sanin su waye a motar da aka kaini saboda ni fuskata a rufe take ba wanda xan iya shaidawa a lokacin saidai tabbas na san ina tare da manyan aminai na guda biyu kamar ita Ummin da dayar aminiyar tawa Jiddah.
Barrister yace “yawwa ko xaki iya tuna qarfe nawa kowa ya watse a cikin gidan aka barki ke daya lokacin da kike jiran ango kamar yadda al’adar amare take a ranar da aka kaisu dakunan mijinsu?
Tace “lallai kam baxan manta ba bayan anyi sallar Isha’i wuraren qarfe takwas na dare su Ummi da Jiddah da wasu qannan mahaifiyata biyu kadai suka rage a gidan inda mukayi sallar Isha’i tare dasu sannan sukayi shirin tafiya gida suka tafi gaba dayansu. Barrister yace “bayan haka waye ya shigo gidan kafin xuwan Dr. Khalifa?
Ta jima tsit tana nazari tace “gaskiya ba wanda ya shigo kuma banji motsin kowa ba ni kadai na xauna.
Barrister yace “xaman minti nawa kikayi qiyasi kafin sai xuwan ango?
Tace “ba ayi minti sha biyar ba naji tsayawar motarsu shi da manyan abokansa guda biyu wadanda sukayi masa rakiya.
Barrister yace “kafin dai zuwan ango ba wanda ya kira ki koda a waya ne?
Ta girgixa kai ba wanda ya kirani in banda shi angon Dr. Khalifa.
Me yace miki?
“Cewa yayi inyi haquri suna hanya”
Ke kuma me kika ce masa?
Cewa nayi to Allah ya kawosu lafiya.
Yace dukda haka bakiji koda alamar motsi a gidan ba har lokacin da Dr. Khalifa da abokansa suka I so?
Ta girgixa kai gaskiya babu wani alamun motsin danaji sai fa lokacin da suka shigo”. Su nawa suka shigo?
Barrister yaci gaba da tambayar har yanxu idanuwansa na kanta.
Tace su uku wato shi da abokannasa guda biyu.

Yace “yaya sunayensu? Ta amsa “daya sunansa Dr. Mustapha Kura daya kuma Dr. Hafiz B. Muhammad”.
Yace kafin auranku yaya alaqarku dasu abokannasa? Ina nufin sun amsheki a matsayin matar abokinsu ko kuwa basa yi da ke?
Fatima tace “Ni kam Alhamdulillah Dr. Khalifa da iyayansa da abokansa da ‘yan uwansa ko sau daya babu wanda ya taba nuna min qyama ko wani abu wanda xai sa ince lallai wane baya qaunata, daidai gwargwado ina samun had in kai daga garesu to sai shi kuma abinda yake na nasani mutum yake da masaniya akai abinda ya xamo na badini Allah kadai keda masaniya akansa saidai mu barwa Allah ikonsa”.
Barrister yace “to Fatima xaki iya gaya mana maganar da sukayi lokacin da xasuyi sallama daku a wannan dare?
Tace “Eh gaba daya tunda suka xo nasihohin xaman lafiya suke mana bayan haka sun mana addu’o’i na neman xaman lafiya bayan haka sukayi mana sallama suna mana barkwanci irin na abokan ango ranar siyan baki irin wannan.
To daga nan sai me ya faru?
Tace “sai ya rakasu”
Ke kuma kina ina?
Ina xaune akan gado ko motsi banyi ba kamar yadda suka sameni, bayan ya rakasu sai ya dawo ya xauna kusa dani yana dan xolayata.

Barrister yace “dukda haka a lokacin ba wani motsi a gidan sannan shi dinma bai nuna miki yaji motsin wani abu ba ko kuma ke kin fahimci wata raxana a fuskarsa?
Tace ” gaskiya banga komi ba yana cikin nishadi sosai yadda ya kamata ango ya kasance a irin wannan dare”.
Daga nan fa?
Sai yace dani kinga hayaniya tayi yawa a kaina ko sallar Isha’i banyi ba nayi qoqarin inyi kafin mu taho su Mustapha suka daman akan inyi sauri su garin xasu bari a daran.
“Garin xasu bari? Inji Barrister ya fada yanayinsa ya sauya.
Tace “haka dai yace daga nan kuma bai qara fadar wata magana wadda ta shafi wadannan abokai nasa ba ya tashi ya fita bansan ina yaje ba sai ya dawo.
Yayi kamar minti nawa da fita kan ya dawo?
Tace “xayyi kamar minti goma sai ya dawo ya core babbar rigar jikinsa ya ajiye kan gado yace ya kamata inyi sallar nan gashi kuma ina jin yunwa fun daxu Aunty take cemin ga abinci na kasa xama inci saboda jama’a gaba daya naji abincin ya fita daga raina bana sha’awarsa sai yanxu nakejin yunwa, amma bari in yiwa Mama waya tasa a kawo mana abincin hatta kaxar amarcinki ma tana gun Mama ita tace xata gasa da kanta akwai tanadin da tayi miki a ciki.
Duk yayi wadannan maganganun ne a tsaye yana murmushi tare da daddanna wayarsa ta hannu ya kira Maman bayan sun gama wayar sai ya ajiye wayar akan madubi da nufin ya shiga toilet sai aka kirashi yayi magana mai tsawo da wanda ya kirashi din sannan ya kashe ya dubeni yace “idan mutum yana harka da jama’a sai haquri, tashi kema kiyi alwala idan nayi sallar Isha’i sai muyi nafila ko, bari inyi tawa a dakina sai in taho da littafina , daga nan sai ya fice waje ni kuma na shiga toilet na idar da alwala na fito ne na iske gawarsa akan gado.
Barrister ya girgixa kai cike da tausayi yace “Fatima”
Yanayin fuskarta ba dadin gani saboda tamkar lamarin da take bayarwa yana fama mata wani gyambo na xuciyarta wanda yake mata tsananin xugi a xuci yake rabata da duk wani xaman lafiya da walwala a zuciyarta, hatta kallon data yiwa shi Barrister n lokacin da ya kira sunanta ya firgitashi xuciyarshi ta buga yayi mata tsai da ido don yana son taci gaba da bashi amsar tambayoyin da yake mata.
Yace “Fatima kin kai minti nawa a toilet din lokacin da kika shiga da nufin yin alwala.
Tace “minti kamar goma don na danyi wasu abubuwan kafin in gabatar da alwala.
To sai kika fito inda kika ga gawar mijinki Dr. Khalifa shimfide akan gado, hakane? Tace “eh ina daga ban daki naji motsin bude qofa sau biyu da kuma motsin bude kwaba kome xan kawo a raina don naji wannan motsin, dauka xanyi shine tunda ba kowa a gidan a sanina daga ni sai shi.
Yace “kuma ba motsin gudu?
Tace “gaskiya banji wani motsi wanda yake tabbatar da rashin gaskiya ba ko kuwa.
Yace “to bakiji qarar mijinnaki ba ko wani abu da yayi kama da haka a lokacin da xa a kashe shi?
Tace “nidai banji komi ba yadda na gaya maka naga gawarsa haka na ganshi ba wani abu da na sani bayan wannan.
Yace “dame aka kashe shi?
Ta amsa “wuqa ce qarama.
Kin taba wuqar?
Tace” eh lokacin da na fito daga ban dakin hankalina ya tashi na tafi da gudu na daga wuqar daga cikinsa domin wuqar tana kan cikinsa ne bsyan an luma masa sai aka xareta aka dora akan cikinnasa ni kuma da naxo saina daga wuqar shine dai lokacin da qaninsa Isma’il ya qwanqwasa qofa jin ina ihu Innalillahi wa inna ilaihirraji’un saiya danno qofar ya shigo da food flask din abinci a hannunsa wanda Mama ta bashi ya kawo mana.
Barrister yace “Fatima lokacin da kika iso kan mijinki Dr. Khalifa yana da sauran rai ko ya mutu?
Tace “da sauran ransa don kuwa har yana dan juya kansa yana cewa ta kashe ni ta kashe ni har lokacin da shima Isma’il ya shigo dakin yana magana ganin yanayin daya iskemu a ciki yasa Isma’il din ya watsar da abincin hannunsa ya isa kan dan uwansa a gefe yana fadin “Yaya waya kashe ka” ya kasa kunnuwansa daidai bakin Dr. Khalifa n yana cewa don Allah gaya min wadda ta kashe ka nima yanxu in kashe ta.

Bansan ya akayi ba ko shi Dr. Khalifan a lokacin bansan waye a kansa ba yake masa magana bane bansani ba naji da kunnena dai lokacin da Dr. Khalifa ke cewa Fatima ta kasheni, Fatima ta kashe ni.

Fatima tayi shiru xuciyarta na bugawa kamar lokacin abin ya faru, daga Barrister har Malam da Ummi dashi kansa Dan sandan dake tsaye akansu sun jiqe sharkaf da gumi saboda tsananin tausayi da tashin hankali.
Idanuwan Fatima sun qafe ba xancan hawaye sai tsananin xugi da radadi da suke mata qirjinta kuwa kamar xai balle dan axabar xafin da yake mata numfashi na fita daqyar.

Tunda al’amarin ya faru yau ne ta iya bude baki ta bada labarin yadda abubuwan suka wakana.

Sun jima xaune shiru tuni lokacin da ya dace su fita ya wuce shi kansa Dan sandan ya kasa cewa su fita hankalinsa shima a tashe yake.
Barrister Abbas tagumi kawai yayi da tambayoyi a bakinsa, bakin yayi masa nauyi labbansa sun bushe daqyar yake iya numfashi tare da cewa shi cikakken lauya ne kuma qwararre mai cin gashin kansa don tuni ya jima da qasaita akan aikinsa saboda matakin daya taka na karatu, irin wadannan abubuwan ba baqin al amura bane gareshi, aikinsu nako yaushe jin abubuwan tashin hankali amma bai taba fuskantar al’amarin dayake tsananin daga hankalinsa da bashi tausayi irin wannan ba, ya damu da maganar qwarai da gaske.

Kafin ma yayi mata tambaya taci gaba da fadin “Abinda bakinsa ke furtawa kenan har yabar duniya, wato “Ta kashe ni Fatima, ta kashe ni Fatima”
Isma’il yana ihu akansa yana cewa “Yaya Fatima ce ta kashe ka? Fatima ce ta kashe ka? Bai qara motsi ba yaci gaba da jijjigashi ko shurawa baiyi ba, tuni jini yayi faca-faca akan gadon.

Wuqar tana hannuna ina tsaye har ixuwa lokacin da Isma’il ya sake shi ya fita baice min komi ba, ban ajiye wuqar ba sai lokacin da yan sanda suka shigo dakin wani a cikinsu ya lullube hannunsa da safa ya karba wuqar daga hannuna.

Tayi ajiyar xuciya tace “ba wani abu dana sani bayan wannan, babu kowa a gidammu lokacin da aka Dr. Khalifa saimu biyu a gidan ni dashi ni kaina na shaida banji motsin kowa ba, idan ba ni na kashe shi ba wa xance ya kashe shi?
Idan nace ba ni na kashe shi ba dole inyi bsyanin wanda ya kashe shi, to waye? Sannan ni aka xo aka iske wuqa a hannu na hakanan bakinsa yana furta ta kashe ni, idan akace wa sai yace Fatima…..

Fati ta rushe da kuka mai tayar da hankalin mai imani tace “kaicon rayuwata nayi nadamar xuwa wannan duniya ace an wayi gari a rasa wanda xai kashe Dr. Khalifa sai ni Fatima me xanyi da rayuwa…….

Me xan tsinta a cikinta , wane farin ciki xanyi a gaba?

Don Allah ku daina yunqurin kareni Ku yarda ni na kashe Dr. Khalifa a kashe ni in huta da wannan baqin cikin rayuwata bata da amfani. Wannan bayanin da nayi iyakarsa xan iya fada baxan taba budar bakina a kotu ince wani abu ba game da ranar da Dr. Khalifa yabar duniya, hukunci kawai nake jira kuyi haquri Ku yafe min.
Barrister Abbas yace “to shikenan munji ke kika kashe Dr. Khalifa gaya mana me yasa kika kashe shi?
Ta amsa “nima bansan dalilin dayasa ba kashe shi ba.

Ba wani laifi da yayi mini?
Bai min komi ba sai alkhairi, ba komi tsakanina dashi sai alkhairi, ban sani ba ko alkhairinne yawa nayi masa sakayya da kisan kai”

Tsakiyar dare ne xamu iya kiran lokacin qarfe biyu da rabi na dare, Fatima na xaune kan dandayyar siminti ana muku-mukun sanyi ne a lokacin amma ita ta jiqe sharkab da gumi sakamakon matsanancin halin tashin hankalin da gararin da rayuwarta ke fuskanta. Ita kanta yadda al’amuran suka faru suna matuqar bata mamaki, ko yaushe tambayar da take wa kanta itace waye ya kashe Dr. Khalifa? Me yayiwa wanda ya kashe shi? Me yawa ba’a kashe shi ba sai a darensu na farko? A DARAN FARKO na amarcinsu aka biyo shi har cikin gida akan gadonsu aka kashe shi, tabbas duk wanda ya kashe Dr. Khalifa ya isa axxalumi, ita da Dr. Khalifan ne baya so shiyasa aka kashe shi a sigar da duk wanda ya gani xaice itace ta kashe shi.

Ita da Dr. Khalifa me suka yiwa wani daya daidaici irin wannan dare a gunsu ya kashe mata miji?
Wannan itace tambayar da take wa kanta tun lokacin da aka kulleta a wannan guru, itace tambayar da ciwon da yake mata a xuci ke baraxanar sa xuciyarta ta buga ta tadda nata ajalin saboda tsananin damuwa, Allahu Akbar ashe ko kwana daya baxatayi a gidan miji ba, bala’i xai fada musu A DARANSU NA FARKO.

Sai kace ana tariyo mata rayuwarta da abinda ya gudana a tarhin rayuwarta gaba daya haka ya rinqa wanxuwa a xuciyarta da qwaqwalwarta kamar shirin film.
**************××××***************

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment