Littafan Hausa Novels

Lallen Gargajiya Kunshin Gam Kunshin Salatif

Written by Hausa_Novels

Lallen Gargajiya Kunshin Gam Kunshin Salatif

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Lallen Gargajiya Kunshin Gam Kunshin Salatif

Ga kadan daga cikin amfanin lalle da muka zakulo muku:

CIWON KAFA: Yin lalle na rage ciwon kafa. A kwaba lalle da ruwa ya yi kauri, a shafa wa kafar na tsayon lokacin da ake bukata sannan a wanke. Yin haka na rage radadi da zugin da ke damun mutun a kafarsa.

 

Lallen Gargajiya Kunshin Gam Kunshin Salatif

DATTIN CIKI: Shan ruwan lalle na wanke dattin dake ciki. Idan aka jiga lalle da ruwa aka tace, sai a sha ruwan daidai gwargwado. Yin hakan na wanke dattin ciki.

GYARAN FATA: Ana amfani da lalle wajen gyara fatar jiki da kawar da datti da kuma sanya fata haske mai kyau. Domin haka, sai a zuba lalle da ruwa a rika wanka da ruwa lallen akalla so daya a rana.

Kunshin mata

FATAR FUSKA: Lalle na sa fuska ta yi laushi da haske. Bayan an kwaba lallen da kauri a rika goga fuskar ta ita. Bayan minti 20 zuwa 30 sai a wanke fuskar da ruwa. Za a iya yi sau daya zuwa uku a rana.

Sirrin Doguwar Mace abinda ya kamata ka sani game da sirrin gajera da doguwar mace

KURAJEN FUSKA: Ga masu

 

fama da kurajen ‘pimples’ sai su kwaba lalle da ruwan lemon tsami ya yi kauri suka rika shafa kwabin a fuskar. Zuwa wani lokaci pimples din za su bace.

AMOSANIN KAI: Ana a wanke gashin kai da ruwan lalle domin maganin amosarin gashi. Ana yin hakan ne ta hanyar kwaba lalle a ruwa ya yi dan ruwa-ruwa sannan a jika gashin a cikin ruwan. Bayan minti 20 sai a wanke kan. Yawan yin hakan na kashe amosarin kai.

GYAMBON YATSA: Masu gyambon yatsa (dankankare) na amfani da lalle wajen neman sauki. Akan kwaba shi a sanya a wurin da ke da gyambon a yatsar don neman waraka ko busar da shi.

KWALLIYAR GASHI: Maza da mata na amfanin da shi domin kwaliya a gashin kansu da kuma gemu. Domin yin hakan, sai da a kwaba lalle da ruwa a shafa a waurin da ake bukata na ‘yan mintoci sannan a wanke.

ZAYYANA FATA: Ana kuma amfani da lalle wajen yin ado ta hanyar zayyana a fatar ji. Akan kwaba lalle ta yi kauri, sannna a lika leda mai dauke da nau’in zayyanar da za a yi a fatar, sannan a shafa lallen a sama. Daga nan sai a bar shi ya yi awanni kafin a wanke. Ana kuma iya yin zayyarar kai tsaye da kwababben lallen ba tare da sanya ledar ado ba.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment