Littafan Hausa Novels

Laifin Waye Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Laifin Waye Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

LAIFIN WAYE ?

 

 

 

Na

Rabi’atu Muhammad

(Maman Khaleel)

 

Short Story

 

Marubuciyar:

 

Habiba

Nike da gaskiya

Yan uba ne

Kishiyar zamani

Muda shuwagabannin mu

Namijin kishi

Badawiyya

 

Dasunan Allah Mai rahma Mai jinkai.

 

Sauri yake tayi Yana tunani azuciyar sa ,yai nisa wajen tunani ,ga shi yamma tayi ga shi babu abun hawa, kowa yanata sauri ya samu abin hawa yaje gida cikin iya linsa ,ya tare Keke napep takai 5 kowacce a cike take zuwa, gashi Dan abinda yasamo ba yawa,can wata zuciyarsa ta bashi shawarar ka tsallaka can shagon ka Auna Koda garin tuwo ne in kaje gida aji da na ce fane,ya haura yaji ancema na kusa da shi in har ka tabbata ba Sabon kudi gareka ba to katafi wani shagon Dan mukam ba mu amsa ,Dan in har muka amsa mune zamuyi asara in har ya Kai gobe ,turus yaja ya tsaya Yana share wani gumi Mai zafi ganin shi yau gaba daya kudinda yayi ciniki Bai haura dubu biyu da Dari bakwai ba gaba daya ,Kuma da kyar ma yayi Dan babu ciniki yau Dan kowa sai kaji yace yau ba takaya mukeba yau ta abinci muke Dan bamusan yadda canjin kudin zai Kaya ba ,shi Bai da muba Yana nan zaune har Allah ya kawo Masa wadda tazo tayi Masa wannan cinikin ,Ashe zai hadu da kalubalen da yafi nakasuwa Muni ,yayi dogon ajiyan Zuciya yace Allah ka kawo Mana mafita ,yajuya ya dawo bakin Hanya yaciga ba da jiran abin hawa har Allah ya kawo wani Wanda yake Neman cikaton mutum daya yace Unguwar Sunusi,bayan ya shiga ya zauna suna cikin tafiya wani yayi tsaki yace “Kai wannan rayuwa sai hakuri shi dai talaka komi shi ake kwara akowani mataki na kasar nan…..!

Harijin Namiji Hausa Novel Complete

Maman Khaleel din kuce…..

 

LAIFIN WAYE ?

 

 

Na

Rabi’atu Muhammed

(Maman Khalil)

 

Short Story

 

page 2

 

Marubuciyar :

HABIBA

NIKE DA GASKIYA

YAN UBA NE

KISHIYAR ZAMANI

MUDA SHUWAGABANNI MU

NAMIJIN KISHI

BADAWEEYYA

 

and now

LAIFIN WAYE?

 

“Kai wannan rayuwa sai hakuri shi dai talaka komi shi a ke kwara a kowani Mataki na kasar nan,gashi mun Zama kaji da an yafa Mana tsaba sai kaga an dage muna son kashe junan mu ,Kai Allah ka kawo Mana mafita.”

 

Gaba daya na cikin Nafef din Nan suka amsa “Ameen ,Amin ya Allah “.

 

A na zuwa Bustop ya sauka ya Ciro kudi Zai bayar na kusa da shi yace “basshi kawai Baba jeka zan bashi”

 

Malam Ali yayi ta godiya ya nufi gida zuciyar sa Babu wannan kuncin da ya baro a kasuwa akalla ya samu saukin kaso 80 cikin 100 ,tun daga soro yake jin hayaniyar yaransa suna Wasa yayi Sallama ,gaba daya suka amsa tare da fadin “sannu da zuwa Baba ,kadawo lafiya ?”

 

Yayi Murmishi yace “lafiya Lau na dawo.

 

“Maimuna ba ta Nan ne?” ,inji Malam Ali yake tambayar yaransa Mamansu.

 

Kafin su bashi amsa sai yaji muryar Maimuna a bayansa ta fito daga make wayi , hannun ta dauke da buta ,tana fadin gani Nan Baban Bilki ,sannu da dawowa,ta shiga dakinta ta dauko Masa tabarma ta shinfida Masa ya zauna ta shiga daki ta de bo Masa ruwa a Kofi ta kawo Masa tace”Baban Bilki wannan hamma haka kamar zaka hadiye mu ,dariyar yak’e yayi yace “ke dai bari kawai Maimuna, ya kurbi ruwan da takawo Masa cikin sa yayi wata Kara k’uuuuh! Kai yau an wahala ba ciniki ,ga yunwa Ina ji ,yau wata dabara kikai Mana a gidan?’

 

Maimuna tace “yo Baban Bilki yau duk Wanda ka ba kudi Bai karba ,ka ganta Nan Dazu na aiki Bilkisu ta siyo garin kwaki ,Anki karba sai kanzo maman Khalid ta ban …..!

 

Maman Khalil dinku ce….!

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment