Littafan Hausa Novels

Laifi Tudu Page 20 Hausa Novel

Toilet infection
Written by Hausa_Novels

Laifi Tudu Page 20 Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

*Laifi Tudu*

(Ka Take Naka Ka Hango Nawani)💘💘

 

Writing by Ummalkairi Lawan Abdullahi

 

 

*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟*

{R.S.W.A}

 

 

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

 

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

 

*Page 22*

 

 

……..Zaune take cikin kwanciyar hankali da jin dad’i,

 

Ta mi’ke ta shige cikin d’aki, tabar mutanan dake parlour suna jimamin abinda ya faru,

Rashin Mahaifiya Page 46 Hausa Novel

Wayar ta ta ciro ta k’ira malamin ta cikin farin ciki ta soma magana, “ya aiki ya jama a?”

daga can ‘bangaran aka bushe da dariya “Hhhhhhh hajiya Maryam nasan kin k’ira ni ne dan kimin godiya aikinki yayi kyau ko Hhhhhh ai na gaya miki zan yi aikin a sanda ya dace”.

 

“Eh wallahi aiki yayi malam nan da d’an anjima zakaji ragowar kud’in ka, nagode”.

 

Tana kashe wayar ta ‘kira Fauzy,

 

Tana zaune tayi tagumi ta rasa mai ke mata dad’i,

 

K’iran wayar da ya shigo ne ya katse mata tunani,

 

Da sauri ta d’auka ganin cewa Mama ce take kira “Hello Mama ina kwana?”

 

Fauzy ta fad’i cikin zumud’in san jin abinda Maman zata fad’a.

 

“Lafiya lau Fauzy yau dai burinmu ya cika, Anne mi Yarinyar can an rasa, aikin malam yayi kyau wallahi”.

 

Da sauri Fauzy ta kwalla wata ‘kara cikin murna da jin dad’i,

 

Har ta jawu hankalin sauran mutanan dake d’akin suka fara tambayar ta me ya faru, “bakomai kawai tace ta tashi ta shige band’aki.

 

Su Abbu sun je wajan y’an sanda sun bada rahoto, sun kuma bada sanar wa agidajan redio ko Allah zaisa a dace,

 

Daga nan gida suka yo inda suka tarar da mutane sun ciki harabar gidan har da masallacin dake jikin gidan,

 

Cikin mutanan harda waliyyan Fauzy wayan da suka zo domin d’aurin auran,.

 

Hak’uri suka bawa mutane sannnan suka fad’a musu abinda yake faruwa, uziri suka nema ad’an basu lokaci, suka shiga cikin gida.

 

Abba ne ya fara magana da cewa “ni inaga nin kawai tinda mun tara mutane kuma ga abinda yazo ya faru, gara a d’aura auran yaran nan gaba d’aya tinda itama Safiyya muna fatan za a ganta in sha Allah”.

 

Abbu ne ya tare shi da cewa “gaskiya ne nima abinda nake tunani kenan, gara a d’aura idan anganta aganta amatsayin matarshi”.

 

Baffa dai bai iya cewa komai ba, “duk abinda kuka yanke yayi”, abinda ya iya fad’a kenan.

 

Abba ne ya dafa kafad’ar Baffa ya ce “kayi hak’uri muma duk muna jin abinda kake ji kuma in sha Allah za’a ganta”.

 

A tare suka amsa da Amin,

 

Fitowar su Shahid kenan daga makarantar su Sofy bayan sun saka hotonan ta a social media,

 

K’iran Abbu ne ya shigo wayar shi da sauri ya d’aga “kuna inan?” Abbu ya tambayesu.

 

“Gamunan” Shahid ya fad’a,”to kuyi maza ku zo gida”.

 

Bayan isowarsu gida suka tarar da cincirundan mutane, har da yan jaridu,

 

Bayan fitowar shi daga mota jama’a sukayo kanshi anata yi mai jaje da addu’ar Allah yasa aganta, y’an jaridu kuma na ‘kokarin tambayar shi abinda ya faru, shidai bai yacewa komai ba kawai ya wuce cikin gida.

 

‘bangaran Abba ya nufa inda suke, da sallama ya shiga cikin d’akin inda ya tarar dasu kowa acikin damuwa, musamman Baffa fad’ar damuwar da yake ciki ma bazai yiwuba.

 

Asanyaye ya nemi waje ya zauna zuciyar shi tana mai wani irin ciwu,

 

Abbu ne ya katse masa tunani da cewa “Shahid duk kanninmu nan muna cikin damuwa da abinda yake faruwa, Kamar yadda kaima yanayinka ya nuna, ba abinda Sofy take bu’kata yanzu sai addu a kuma muna fatan cewa in sha Allahu za aganta”, yaci gaba da cewa “mun tattauna akan maganar auranka kuma mun yanke shawara cewa za a d’aura maka aure da duka matan ka da zarar an ganta to tana matsayin matarka”.

 

Hakan yayiwa Shahid dad’i dan dama babbar fargabar da ya shiga a yanzu ita ce kada afasa d’aura mai aure da Sofy, haka ya tashi ya fita.

 

Sashinshi ya nufa inda tarin Abokanan sa suka bishi suma jiki asanyaye,

 

Momy tana zaune a parlour banda kuka da addu’ar Allah ya bayyana Sofy ba abinda take, mami ce da sauran y’an uwan Momy da suka zo daga Lagos suke ta aikin rarrashinta, gefe kuwa su Aisha ne da Farida suma ido yayi jajir alamar sunsha kuka,

 

Ahaka Baffa ya shigo yake sanar musu da shawarar da suka yanke ta d’aurin auran,

 

Momy Bata so haka ba dan tana ji a zuciyar ta cewa akwai sa hannun su Mama akan ‘batan da Sofy tayi, Amman sai tabar abin azucuyar ta dan duk abinda yake faruwa tin bayan dawowar su gidan bata ta’ba gayawa kowa nata ba dan haka danginta basu san me yake faruwa ba.

 

Ummi ce tayi tsalle ta dire ita wallahi ba za’a d’aura aure da yarinyar da ba asan inda take ba “waya sani ma ko yawanta ta tafi daza a…..”fau taji saukar mari wanda yasa sauran maganar ma’kalewa.

 

“Yar d’an uwan nawa kike jifa da irin wannan maganar to wallahi bazan laminta ba kisani ina sane da duk abinda kike kullawa akan yarinyar nan nayi miki shiru amma ba zan d’auki wannan ba.

 

Abba yayi ficewarshi ya barta nan ri’ke da kunci,

 

Fuuu ta d’akko mayafi tayi b’angaren Mama,

 

Samun ta tayi itama tana sallallami akan hakan.

 

Kiyi hak’uri Ummi in sha Allah ma ba zata ta’ba dawowa ba ballantana ma ta zama matar tashi, kirabu dasu suje su d’aura auran mugani zai zauna da babune kikwantar da hankalinki kawai,

 

Kowa ya shaida wanzuwar aure tsakanin Shahid da matansa biyu Sofy da Fauzy……..✍️

 

Writing by Ummulkairi Lawan Abdullahi

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment