Littafan Hausa Novels

Kyawuna Hausa Novels Complete

Babbar Yarinya By Oum Aphnan
Written by Hausa_Novels

Kyawuna Hausa Novels Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

𝐊𝐘𝐀𝐖𝐔𝐍𝐀

( 𝑻𝒓𝒖𝒆 𝒍𝒊𝒇𝒆 𝒔𝒕𝒐𝒓𝒚)

 

𝕊𝕋𝕆ℝ𝕐 𝕬𝕹𝕯 𝕎ℝ𝕀𝕋𝕋𝔼ℕ

𝓑𝓨

𝑳𝑰𝑬𝒀𝑺𝑯𝑬𝑹𝑻

 

 

𝐃𝐀 𝐒𝐔𝐍𝐀𝐍 𝐀𝐋𝐋𝐀𝐇 𝐌𝐀𝐈 𝐑𝐀𝐇𝐌𝐀 𝐌𝐀𝐈 𝐉𝐈𝐍𝐊𝐀𝐈!!

 

 

 

🆂🅷🅸🅼🅵🅸🅳🅰

 

____________

A rayuwa kowa ne ɗan Adam yana da irin jarabawar sa, Babu wanda ya isa ya canza Abinda Allah ya kaddara masa. Haka rayuwar AISHATU ta taso Allah yayi mata wani irin Kyau, wanda mutane ke kiranta da 𝐀𝐋𝐈𝐒𝐇𝐁𝐀 . Fara ce sosai irin white milk ɗin nan, haskenta me tsananin kyau ne da ɗaukar ido, doguwa ce daidai misali sannan tana doguwar fuska me ɗauke da dara-daran idanuwa ƙwayar idon ta wata kala like cat eyes, tana da dogon hanci wanda ya dace da fuskarta sannan tana cute lips kalar pink masu kyau da ɗaukar hankali. Tana da diri sosai me ďaukar hankali wanda ake kira da coca cola shape, komai nata me KYAU ne, Allah yayi mata baiwar murya me daďin gaske idan tana magana kamar ana busa sarewa haka mutum zaiji saboda zaƙinta. Tana da natsuwa da hankali sosai komai tana yinsa ne cikin sanyi da hakuri da kuma tsari. KYAWUNTA ya jawo mata damuwa da tashin hankali, yan uwan mahaifinta sun kyamace ta sosai saboda KYAWUNTA, sun ƙwace dukiyarta wadda ta gada wajen mahaifiyar ta. Sun kore ta bayan sun san bata da kowa sai su, barin ta gida ya kara jefa rayuwarta cikin garari, KYAWUNTA ya kasance wani Haske ga wanda suka ďauke shi a matsayin hakan . KYAWUNTA ya bar mata wani tabo wanda bazata iya mantawa dashi ba.

Mijin Mu Daya Hausa Novel Complete

Shin ita kaɗaice me KYAU a duniya daya zamar mata bala’i da ƙuncin rayuwa ? Babu wanda yake raɓar ta saboda Allah sai don KYAWUNTA, Ta yaya ne zata fuskanci rayuwa ta gane masoyanta na gaskiya? Wace duniya dangin mahaifiyar ta suke? Kuma a ina ne zata gano waďannan dangin mahaifiyar tata….

 

******

Malam Mannir Muhammad mazaunin garin Katsina ne yana da yara goma sha ďaya da mata ukku gidan Malam Mannir gidane da duk wanda yake cikin ansan sa saboda tambarin da suke dashi a unguwar. Rayuwar wannan ahali akwai darasi da yawa a cikinta . Gaba ďaya gidan babu me girmama na gaba dashi, kowa harkar gabansa yake a cikin wannan gida babu me damuwa da damuwar wani, Amma duk da haka suna kaunar junan su basu yadda a taba su ba. Cakwakiya da sharholiyar dake ake zubawa gidan Malam Mannir tana da ban dariya da nishad’i…

 

******

AHMAD ɗa daya tilo ga Alhaji Abdullahi Ibrahim me Dollar , AHMAD ɗan gayu ne na bugawa a jarida yana ji da tsanin kyawu da kuɗi ya kasance irin mazan da suka amsa sunan su a ko ina, hakan yasa bai ɗauki uban kowa da daraja ba. Yana da mugun son wasan kwallo baida lokacin kowa a rayuwarsa daga na mahaifansa sai kwallo, yana da ilmin boko sosai don yayi masters har biyu a kasar London Fannin engineering. Yana da son gayu da kwalisa bai, rayuwarsa ta daban ce ba kamar sauran mutane ba. Ya tsani talaka a rayuwarsa bai ɗauki rayuwar takala abakin komai ba, bai shiga harkar kowa haka koma ba kowa yaba damar shiga harkarsa ba .

ƴan mata na haukan son sa sai dai kash basu gaban sa a cewar sa baiga ajin auren sa ba a ƙasar nigeria.

Mace kyakkyawa yake da burin aure, yafi son yadda yake da mugun kyau to matarsa ma ta kasance lamba ďaya a kyau.Yana son matarsa ta kasance wadda suke da kuďi na tashin hankali don babu abinda ya tsana a rayuwarsa sama da talaka, bai kaunar yaga talaka ya rabe shi a cewar sa basu da aiki in ba roko ba, bai san ko fita saboda kar ya haďu da talaka a hanya. Sai dai wata kaddara ta ratso rayuwarsa lokacinda bai shirya ba…..

 

****

 

NASEEM ɗan gayu me ji da kuɗi da kwalisa , ɗa daya tilo ga Alhaji Muhammad Mukhtar Naira , Naseem ya taso cikin so da kauna a wajen iyayen sa, basa ƙwabarsa ko kaɗan sai daya shekara Ashirin a duniya sannan akayi masa kanwa Najma. Yana da son girma da jin kai, bai yadda a raina shi ba koda da wasa ne yasha shiga gasa ta miliyoyin kuďin akan abin banza saboda kar a raina sa , sai dai yana da tausayi sosai abu kaɗan yake karya zuciyar sa, yayi karatun sa a kasar America, inda ya karanci computer science, ya iya sarrafa computer sosai Allah ya bashi wannan baiwar maye ne sosai babu ta yadda bazai sarrafa computer ba. Yana da ƴan mata sosai, sannan yana masifar son mace mekyau hakan yasa yake da ƴan mata sosai don in har kina da kyau to ke tashi ce. Yana da son ace yar wane me kyau budurwar sa ce , yana harkar mata sosai dan babu me cin kuďinsa inba Mace ba sai dai duk harkar shi baya taba Aikata Haram….

 

***

ALINA yarinya me tashe ƙyaƙƙyawa ajin farko tana kyau sosai , Ƴa ɗaya tilo ga Alhaji Umar Farouk Umar ta taso cikin gata da soyayya, bata da mutunci ko kaɗan sannan bata da ragowa balle tausayi, fitsararra ce sosai bata ganin uban kowa da gashin Arziƙi. Tayi karatu a kasar Egypt inda ta karanta medicine cikakkiyar likita ce me zaman kanta.jin kanta da isar ta yana da yawa bata harka da kanan mutane komai kuďin ka baka wuce wulakanci a wajen ALINA ba . A rayuwar ta bata kaunar ace ga wata tafita, tana da tsananin kishi akan hakan ta fiso ace komai a wajenta aka fara gani ko a wajenta aka samo . Tana harkar social media sosai kuma tayi suna a Fannin babu wanda baisan ALINA ba.

itace me zamani a wannan zamanin sarauniyar kyau me tashe, motarta babu mace me ji dakanta da take hawanta. kawayen ta da 𝑺𝑼𝑷𝑬𝑹 𝑺𝑻𝑨𝑹 suke kiranta saboda ajinta yakai….

 

 

KYAWUNA! KYAWUNA!

kai daga jin sunan kasan salon na daban ne. da zafinshi yake tafe kudai ku biyo ni don jin wannan kayataccen labari. basai na koda maku shi ba idan kun biyo zakuji komai.

 

Ubangiji Allah ka sadamu da Alkhairin dake ciki ya kiyaye mu daga sharrin dake ciki.

 

𝑰𝒏𝒂 𝒌𝒂𝒖𝒏𝒂𝒓𝒌𝒖 𝒎𝒂𝒔𝒐𝒚𝒂𝒏𝒂. 𝒔𝒐𝒏 𝒔𝒐 𝒅𝒐𝒎𝒊𝒏 𝑨𝒍𝒍𝒂𝒉!

 

𝕠𝕦𝕞 ℕ𝕚𝕙𝕒𝕝

08060377780

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment