Littafan Hausa Novels

Kunan Zuciyata Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Kunan Zuciyata Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

KUNAN ZUCIYATA

LABARI MAI TABA ZUCIYA,

 

_Labarin masoyan da hali da d’abiunsu ya sha banban, sun banbanta ta ko Ina, haka iyayensu, ma kuma suka banbata, shin yaya kuke Ganin Soyayyan nasu zai kasance?_

 

_By Ummu Fatima marubuciyan DIJAH KAYA_

 

ABINCIN ZUCIYA TA

 

*Na fara da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai, tsira da Aminci su tabbata ga Annabin Rahama*

 

Kofata abude take ga dukkan Wanda yaga gyara ya gyaramin, dan Allah kada a boyemin,

 

_Littafinnan na kudine, da free naso yi wlh to anma Mabiyana sunce Ina jirga littafin kyauta, nafi yin na kudi akan Kari, Dan haka suka hanani yin free, so insha Allah wanna littafin ba zai dau lokaciba, sannan bazan yi delay ba zan keyi Akai akai,_

 

Kudin sayan littafin 300 kacal, ta asusun bank

4626334012

Fcmb

Asma’u Muhammad

 

*Nagode Nagode masoyinka shike sayan kayanka,*

 

Page 1

 

Katafaren gida ne da In ka kalla sai ka Kuma kallonsa, a bakin hanya yake, a cikin wata unguwan na hamshakai, duk da baka rasa tsirarun yaku bayi a gefe gefe, Gidan yana dauke da manya manyan Gate har Hudu, Gidane na Bene, wato gidan sama, tsananin girman gidan da kyan gidan shi zai tabbatar maka da mamallakin gidan ba karamin Attajiri bane, acikin attajiranma,

 

Sanadin Hijira Hausa Novel Complete

Wannan Gidan mallakin major General Abdallah sanusi kenan, sannane Kuma fitaccen shugaban Sojojin Nigeria, Haifaffen cikin Garin Zaria mazaunin Cikin kwaryan Kaduna,

 

Wato idan ka shiga cikin gidan zakama rasa ta Ina zaka fara mema zaka fara kallo, Kai da za’a barka zaka iya rantsuwan cewa ba kasannan namu na Nigeria kakeba,

 

D’aya daga cikin paert din gidan,

 

Kwance yake a katafaren Gadonsa, Mai shape din zuciya, gadon lullube yake da zanin gado Pink, da yagaji da kyau da tsaruwa, yana tsakiyan pillows ne masu shape kala kala, dasuka kewaye shi, yana lullube da tattausan Bargo, Shima pink, ya Lula sosai cikin bacci Mai tsananin Dadi, Sam baimasan gari ya wayeba,

 

 

Mahaifiyarsa Hajiya Salma, ta turo kofan a hankali sanye take da doguwar Riga baka’ da ta sha aiki da duwatsu Ruwan kasa, Kalan rigan ba karamin Kara fitowa da tsananin farin fatanta da kibanta yayiba, kyakkyawar mace Mai cikan haiba,

 

Murmishi tayi lokacin da taga Dan nata Rungume da uban Pillows ajikinsa ta gayra mayafin rigan nata, lokacin da ta iso jikin gadon, ta d’an rankwafa gami da yaye Bargon da yake lullube dashi, Sannan ta fara rage pillows din da ya manne jikinsa da su, yayi juyi gami da Kara rarumosu ya rungumesu gam akirjinsa kaman zai maidasu cikin jikinsa,

 

Cikin sanyin Murya tace “Ajmal tashi mana, garifa yagama wayewa bakayi Sallah ba, ya Dan ja gajeren tsaki yana yatsina Fuska, kaman zai yi Kuka yace “Pls Mom ki barni inna tashi anjima zanyi,

 

Mom ta Dan hade Fuska ta sa duka hannayenta ta dagoshi gami da zaunar dashi acikin Pillows din nashi, tana kallon Fuskansa tace “Me ke damunka Ajmal, ban gayamaka irin ukuban da mutum yake shiga ba idan yana wasa da sallah, kafa Balaga shekarunka 15, ba Abun da ba’a Rubuta maka Mai kyau da mara kyau, inkuma wuta kake son shiga to shikenan, ta karashe tana kwab’e Fuska.

 

ya ware manyan idonsa yana kallonta, yace “Mum Dad fa yace sai na zamo Babba nayi su gemu, shine na Balaga, yace har yanzu ni yarone.

 

 

Mum ta tab’e Baki cikin takaici, tace “Balaga tana farawa namiji da mace ashekaru 15 ne Ajmal ko kayi gemu ko bakayiba, muddin kacika 15 years ka balaga, Sannan Kuma kana iya balaganma ta alamomin da zasu bayyana ajikinka, Koda kuwa baka cika 15 years dinba,

 

Ka tashi kaje kayi Sallah na gayamaka, zai Kuma magana ta dalla masa Harara, ya Mike da kyar yana kunkuni, “Mum fa jiya banyi Bacci da wuriba, Na Kai wajen karfe 1 Ina game, Da ido kawai tabishi har ya Ida shiga cikin bayi, ta sauke ajiyan zuciya, gami da fad’in Allah ya shiryar da Kai Ajmal, Sanna ta tashi ta gyaramasa saman Bed din ta shirya Uban pillows din da yake kwana a cikinsu, sannan ta karasa jikin mirrow ta d’auki room freshener ta fesa sannan ta wuce sashinta, Har ya Ida Alolan ya fito yana kunkuni yazo ya haye Sallaya yayi Sallah, sannan ya tashi, yana Shirin komawa gado yaye labulen Windownsa, can k’asan layinsu ya dinga dubawa, kaman Mai Niman Ganin Wani abu,

 

Ai kuwa can ya hango wata Yar matashiyar mace da wata yarinya da baxata wuce shekara biyarba, sanye da Uniform din islamiyya tana ta tirjewa, akan bazata Makarantanba, da sauri ya sake Labulen ya juya da Dan sauri Mai hade da gudu ya nufi kasa, yana gama sauka,

 

 

 

A katafaren Palourn su na kasa ya tarar da Dad nashi da Wani managern Bank suna lissafin kudin da zaije ya ajiyemasa, kallo daya ya musu yasa Kai zai fita, Dad yace “Son where are u going?

 

“I’m coming, kawai ya fada ya cigaba da tafiya, har ya fito fallelen farfajiyan gidansu yana sauri, security suna Ganinsa suka tashi a gaggauce suka Bude masa gate ya fita, ta baya yayi Wani Kwana da saurinsa ya fito Wani lungu can ya hango mata da y’ar nata suna tafiya har yanzu Kuka takeyi ya karasa da sauri yana fad’in Aunty Aunty,

 

Matar da yakira da Aunty ta juyo dai dai lokacin yarinyan ma ta juyo, da sauri ta k’wace hanunta cikin na Auntyn Tayo gunsa aguje, tana share hawaye, ya durkusa gami da ware hannayensa ta fad’o jikinsa, ya dauketa gami da mik’ewa da ita, ya manneta a kirjinsa yana Dariya, yana fad’in Mai kukan zuwa school kawai,

 

Ya karasa ga Mahaifiyar nata yana Kara gyaramata zama a kirjinsa, yana murmishi, yace “Aunty Ina kwana, Auntyn ta kallesu tana sauke ajiyan Zuciya tace “lfy Boy, yau har ka tashi daga Baccinka, duk du mun fito da wuri kada ka hangomu, ya gyada Kai sannan yace “ki koma barin kaita,

 

Juyawa matar Tayi tana k’unk’unin y’ar nata k’asa k’asa, ta d’an harareta, ta juya can ta hango Nasiba tana daf da shiga cikin school din kasancewan dama ba Wani nisa suke da makarantan ba,

 

 

Dagata yayi cak ya Dora akan bayan wuyansa kaman yanda ya sabarmata, Ta Dora hanu akansa cikin Dariya tace “My Aj na zaci yau bazaka zoba, ya murmusa yace “shiyasa kikayi ta ihu ma Aunty ko, dai dai lokacin suka Isa bakin makarantansun, ya saukota da ita ya rike hanunta suka karasa shagon gefen makarantan yace “shiga ki dauko duk abunda kike so My luve, murmushi tayi cikin Jin Dadin wannan suna da yake gayamata ta shiga ta nuna Cizey da cingum, sai minti Mai tsinke, da chocolate Mai shagon ya mikomata yana fad’in sannu Yar Daru, Ya Kalli Ajmal yace Mai gida har yanzufa akwai Sanjinku Mai yawa, Ajmal ya yatsina fuska gami da riko hanunta, yace “Kana fa damuna, dariya kawai Mai shagon yayi Dan ya Riga da ya saba da halin Ajmal, d’an rakota da yakeyi jifa jifa, dan mafi yawanci yana Baccinsa Mahaifiyar ta take kawota,

 

Yana rike da hanunta har aji, yarinya daya suka samu a ajin, ya dagata ya dorata akan Benci da take zama, ya zaro hanki a aljihunsa ya goge mata Fuska, gami da sumbatan lips dinta, yace promise to me zakiyi karatu my luve, ta sa hanu ta shafi Fuskansa kamar yanda ya koyar da ita, tace “promise u, my Husband zanyi,

 

“Gud ya fada gami da Kara sumbatanta ya Mike suna daga ma juna hanu ya fita,

 

 

Kai tsaye gida ya koma, Dad yana tsaye a farfajiyan gidan yana ta masifa ma security da sukace sun fita ba suga Ajmal ba, suna hada ido Dad din ya karasa gurinsa da sauri, ya damko hanunsa cikin damuwa yace “Son Ina kaje anduba duk tsukinnan baka nan, gayamin Ina kake zuwane a weekend? Na lura mafi yawancin weekend sai kafita da safe, dafatan ba gurin Yaran Gators kake zuwaba,

 

 

Ajmal ya Dan yatsina fuska yace “kawai nakan Dan leka wajene Dad, daga haka ya k’wace jikinsa yayi ciki da sauri, Mum tana zaune a Dining ta k’irashi Murya adan zafafe, “Zonan Ajmal! Ina ka fita da sassafennan, malamin Islamiyyanka yana ta Jira, meyasa ne baka son Mai da hankalinka a kan karatun addini shinefa Rayuwanka, kasani duk zurfin Bokonka na banzane matukar ba Addini aciki,

 

A fusace Dad da ya shigo yace “Stop it Salma, bana Jin dadin irin lafuzan da kikeyi akan yaronnan, yazakice karatunsa na banza,

 

Ajmal ya kankatar da ido yace “Dad ni banama son malamin acanjaxamin shi, da sauri Mum ta Mike tace “Baka isaba Ajmal, Malamin da ko sati baiyiba, kace baka sonsa, malamai nawa aka canzamaka a watannan? wai me kake nufi?

 

Cikin tsananin Fushi Dad ya kamo Hanun Ajmal yana kallonta, yace “Daga yau kada ki sake kawomin Wani kato gida wai da sunan malamin Son, tunda yace baya so, ya Isa haka, daga haka yanufi kasa, Kai tsaye waje ya nufa da hanu ya kira ustazun da yake tsaye agefe da aswakin sa da littafan Addini, yana Jiran dalibin nashi, da d’an saurinsa ya iso, yana Shirin dukawa ya gaidashi ya dakatar dashi gami da dibo kudi Mai yawa daga Aljihunsa ya damka ma malamin Fuska a murtuke yace “Daga yau kar inkara ganinka a gidannan, Get about! cikin Dan tsoro Usazu ya juya ba tare da yace Uffanba, ya fita, har hulansa na Shirin faduwa ya karasa bakin Gate ya fice, Dad ya juyo yana rike da Hanun Ajmal, Suka dawo, ya zaunar dashi a kan kujeran Dining sanan ya zuba masa Abinci shi da kansa ya bashi yaci, Bai Wani ci da yawaba, ya Mike yace “Dad barinje inkwanta, Dad ya gyada Kai Yana murmushi yace ok my heart kayi barci da yawa, yana tafiya yana gauraye hanya, shi adole yana Jin Bacci dai dai zai shiga kwanan pert dinsa, yaji sheshshekan Kukan Mum dinsa, cikin tsananin damuwa ya juya tana tsaye a balcony ta kifa kanta akan karfe, ya karasa gami da tabata, “Mum me yafaru? Wanine ya mutu? Ko Baki da Lafiya ne?

 

Mum ta zamo a hankali ta durkusa akan gwiwowinta, a dame Ajmal ya tsuguna yana kokarin sharemata hawaye, Dan duk abunsa idan yaga Mahaifiyar tashi tana Kuka gaba daya yakan shiga damuwa,

 

“Ajmal! Mum din ta rigashi magana, “Ajmal kalan Rayuwan da mahifinka yayi, zaka yi? Ajmal So ka keyi kayi tashin yaran masu kudi marasa tarbiya, ba ilimin Addini sai na boko? Ajmal Duniya kawai kake bukata? Dan Allah Ajmal kada ka biye ma mahaifinka, kada ka dauki Rayuwan da yake Doraka Akai, ni Yar talakawane Dana San Darajan dan’uwana talaka, ni Yar Malamin Addinine, nasan mahimmancin karatun Addini, Dan Allah Yarona kada ka bari Kayi mummunan rayuwa, duk malamin da yazo dan koyar da Kai Addini sai kuncimasa mutunci Kun koreshi, why? Why Ajmal? Ta k’arashe kaman zatayi Yaya da ranta.

 

Ajmal yasa Hanu ya Kuma sharemata hawaye, yace “Mum akan haka kike Kuka? Dan Allah kiyi shiru, ki Daina bata hawayenki, nace miki zanyi karatu, ni wannan malaminne bana so Bai iya gayuba, kayansa duk squeezing mum baya son sa kaya Mai kyau.

 

Mum ta girgiza Kai cikin takaici,

 

Ya Kuma dafa kafad’anta “Allah Mum zanyi karatu in kika samo min Wani anma Mai tsafta, kinji!

 

“Banga alamaba Ajmal, malamai nawa Kuka kora Kai da Dad din naka a gidannan, meyasa ba kwa Koran malaman Boko? Ina ruwanka da gayun malami? Gaye yazo koyar da Kai ko karatu? Ilimin Addini shine garkuwanka, Kada ka bari Kayi asaran lokacinka, idan bakayi yanzuba, yaushe zakayi?

 

 

Yadan yatsina fuska “Dan Allah Mum kiyi shiru wlh zanyi, tashi mu tafi ya fada gami da mik’ewa yana kokarin dagota, ta tashi tana gyara mayafin riganta suka nufi sashinta, zuciyanta fal da tausayin tilon Dan nata da take Gani ubansa yana Shirin jefa rayuwansa cikin Wani hali,

 

 

_____________________________

 

Tabbas ta San waye Major, Tasan irin badakalansa, Shima ance mahaifinsane ya sangartashi kasancewan sa shine na miji guda a cikin yaransa, na biyu Kuma Mahaifiyar sa ta rasu, Dan haka ya sangartashi ya lalace iya abunda yake so kawai yakeyi, ba Wanda ya Isa lankwasshi,

 

Bayi Ganin kowa da gashi, a haka ya girma rabin rayuwansa a kasan turawa, ba irin d’abiubsu da bai aikatawa, shine shaye shaye, Niman mata da sauransu, a haka kwatsam bayan ya dawo Nigeria idonsa ya fada kan Ummu salma, yarinya nitsatsiya Mai tarbiya, ga kyau ga kyan jiki, fara tas da ita kaman Yar larabawa, duk da tsananin kyaman talakawa da yake dashi, haka ya likemata, ba karamin gumurzu akayiba, Dan Salma nunawa tayi duk Duniya bata da makiyi kamanshi, Hankali ya tashi matuka, Dan ya kwanta a asibiti yafi abunda ya Fi asanadin Salma, haka yake sa mahaifinshi agaba yayi ta Kuka kaman jariri, Yana fad’in inbai auri Salma ba mutuwa zaiyi, yayinda ita Kuma Salam take fad’in masa cewa in aka auramata shi, mutuwa zatayi,

 

 

Manyan Malamai abokan mahaifin Salma Mahaifinsa ya dinga diba suna zuwa suna tayashi rokon ya taimaka ya basu Salma, ahaka dai ta Allah ta kasance, aka aura masa Salma yarinyan da kwata kwata basu daceba, haka ya karbeta tana kukan bakin ciki yana kukan Dadi, ahaka Salma ta daure tayi ma Mahaifinta Biyayya tacikamasa alkawarin da ta d’auka na zata zauta tayi Biyayyan aure, sosai major yake bata kulawa, da rarrashinta tunda yasan yana tsananin sonta, ita Kuma tana tsananin k’insa, Bai rageta da komiba, daga ita har iyayenta, tun tana kyamatansa har dai ta sauko, yasha wahala sosai kafin ya sameta, a shimfidansa, sun zaga kasashe da dama a lokacin yana ganiyan aikinsa.

 

 

Shekaransu Goma cif da aure kafin Allah ya basu Ajmal, tofa major kusan zautacce ya dawo akan Ajmal tsananin son d’an da yasa aransa, abun dai ba’a cewa komi, Ahaka yake ta tasowa duk abunda yace yana so duk muninsa baya Hana shi, haka baya bari Mahaifiyar tashi ta masa fada, ko ta hukuntashi, saidaifa idan bayanan, hankalin Hajiaya Salma ba karamin tashi yayi ba, sai dai kullum cikin Addu’a take kaman yanda ta dage akan Majorn har Allah ya rabashi da kaso Sabai’n na Muna Nan Halayensa, haka take ta fama akan d’annata, tana Addu’a Allah yasa kada yayi irin Rayuwan mahaifin nasa.

 

_________________________________________

 

 

Sallama Ajmal yake ta rafkawa kaman dai yanda matar gidan ta koyar dashi, tana can ciki tana faman tuka tuwo a kitchen ta jiyoshi, ta d’an d’aga Murya ta amsa, sannan tace shigo Boy, ya tura kofan ya shigo, yana sanye da wando tree quarter fare tas da top da yad’ameshi Shima fari tas, gashin kansa a kwance sai shek’i yake, ga Wani daddad’an k’amshi Dake fita ajikinsa, kallo d’aya zaka masa ka Gano d’an attajirine ba ma k’aramiba, fatansa har Wani glowing yake, kaman jikin mace, gashi d’an gaye, yana da tsaban son gayu da tsafta, sai da ya ciro hanki ya shimfi’a asaman turmin da yake kife a k’ofan kitchen din kafin ya zauna, Fuskansa d’auke da d’an murmushinsa da yake karamasa kyau, yace “Aunty Sannu da aiki, itama cikin Fara’a tace “Sannu Boy, kwana biyu kuwa kana Nan, yad’an shafi kansa wlh Ina Nan, Rana ne yake hanani fitowa, yau ai na hango ku da My luve Kina kaita school ba gardama, Aunty ta d’an murmusa tace “Ummi Duniya kwana biyu da bata ganinka ai ta daddara, dai dai lokacin, Yaran ta guda biyun, ya da k’anwa suka yi sallama, sannan suka shigo, Babbance a baya, karaman a gaba, suna had’a ido, Ajmal ya bud’e hanunsa gami da fad’in “wawww my khairi, da gudu cikin tsananin Doki Tayo kansa da niyan fadawa kirjinsa, tana daf da fadawan, ya mik’e gami da zillemata, ta Kuma bin yanda yayi, yasake Zillemata ta tsaya tana kallonsa kaman zatayi Kuka sai ya durkusa yana Dariya “zo zo my Luve, kada kiyi fushi ta saki dariya sannan ta Isa aguje, tana daf da fadawa jikinsa ya mik’e ya gudu, Nan ta tsuguna ta saki Kuka, da sauri ya iso gareta, yana Shirin d’agota ta mik’e itama ta gudu, ya dinga binta tana zillemasa da k’yar sai da yagama gajiya kafin ya samu ya kamata ya d’agata ya manneta da k’irjinsa, sannan ya rik’e kunnenta da hakorinsa, yana hukuntata, Aunty da tagama kwasan tuwonta, ta zuba musu Miya duk ta fito dasu ta ajiye akan tabarman da yake shimfide a gun, ta juyo tana kallon Abunda sukeyi, Sam ita irin wannan wasa da Ajmal yakeyima yarinyantan bayi mata Dadi, “Boy sauketa taje ta cire uniform tazo taci Abinci, kaima ga naka nasamaka, yau nayi miyanka dakakeso, duk da sai ka ga dama kake cin ciman talakawa, ta k’arashe cikin d’an murmushi, Shima murmushin yayi, ta juya ga Babban ‘yar nata tace “Nasiba je ki cire uniform ki wanko hanu, daga haka ta nimi guri ta zauna,

 

Ajmal ya sauko da Ummi da tayi fushi, tana Kuma kukan cizonta da yayi a kunne, ya tsuguna gami da d’orata akan gwiwansa, ya zare Hijab din jikinta, yasa harshe yana lasan hawayen Fuskanta, Aunty ta mik’e ta k’arasa gunsu da sauri ta rik’o Ummi da take ta lafewa ajikinsa, tace “Kai Boy na gayamaka Dan Allah ka Daina mata haka, k’ara rungomuta yayi ya tashi da ita a hanunsa yana Dariya yace “pls Aunty ki Daina samana ido Dani da wife Dina, na gayamiki I really luve her, Aunty tace “Ina! na lura dai so kake ka dasamin cuta a zuciyan ‘ya, ka barmu da damuwa, Sam Ummi ba sa’an aurenka bace, kaima Kuma kasani, inba dai kuma so kake Mahaifinka ya harbe duk zuri’anmu ba, Cikin Dariya da ko inkula Ajmal yace “na gayamiki bani da Mata sai Khairi,

 

Khairina waye mijinki? Khairi ta d’ago tana murmishi tace “Kaine Mijina Ya AJ, Aunty ta girgiza Kai, “Wlh duk ka koyamata rashin Kunya, kala kala, Boy Dan Allah ka Daina kagafa ita mace ce, daga haka ta juya har ranta bata Jin Dadin abunda Ajmal din yake koyama ‘yannata, sannan ta lura Wani tsananin shak’uwane yanzu atsakaninsu, ita dai Allah ya gani abun na bata tsoro, musamman idan ta tuno halin Mahaifinsa na tsananin kyaman talakawa, Tasan duk randa ya San yana shigowa gidansuma da kyar inbai sa an koresu a Unguwan ba.

 

 

Buta ya d’auka ya wanke mata hanu sannan ya ciremata Uniform daga ita sai pant da Best ya ninke uniform din ya mikamata yace ta Kai d’aki, ta juya ta Kai ta fito yana tsaye yana kallon Nasiba da take cin tuwo yace “Kai Addanmu dagani kinfi mu Loma, murmushi kawai Nasiban tayi tana ci gaba da cin tuwon tsari miyan busashshen kubiyanta,

 

 

Ummi ta iso ta d’auko kujera ta ajiye masa sannan ta d’auko hankinsa da yake kan turmi ta shimfida masa akan kujeran kaman yanda taga yanayi kafin ya zauna, ya k’araso ya zauna, Sannan ta mik’omasa tuwonsa da Aunty ta samasa spoon Akai, ya zaunar da ita a bakin tabarma yace suci tare, tasa hanunta ta yanki Loma tasa abakinta, sai da tagama cinye na bakinta, ta Kuma yanko Wani Ajmal ya mik’o bakinsa yace “Samin my love, tasaka masa sannan ta yanko Wani, haka tana ci tana bashi yana ci, idan tasaka masa a abaki haka zai rike yatsun nata a Baki yayi ta tsotsa har yana Wani lumshe ido, sai su saki dariya kafin ya sake mata ta ci ta Kuma bashi, haka sukayi tayi har sukaci Mai yawa, can Kuma ya zabura, gami da kallon agogon Hanunsa, ya Kalli Aunty da ta rafka tagumi tana kallonsa ya tashi da sauri ya d’auki buta ya kurkure bakinsa, ya Kalli Aunty,

 

 

“mhmm Dad fa yana d’aki yana jirana cewa yayi inje in d’aukomasa passport d’ina jibi zamu England dubo Results d’ina, shine danaga ba kowa ak’asa na fito, Aunty ta jinjina Kai tace “Allah ya shiryar da kai Boy, ka shanya Bawan Allah yana can yana jiranka,

 

Ya matso ya sumbaci Khairi a chick sannan ya juyamata nashi Chick din itama ta sumbaceshi, tace “Ya AJ zaka dawo, yad’an hargitsa Fuska, “bana hanaki gayamin wanna sunanba? Me nace kidinga gayamin, ta d’an saci kallon Aunty Murya k’asa k’asa, tace My Husband, ko my Aj, ko my Heart, ya Kuma sumbatanta yana murmushi yace “Gud Girl daga haka ya mik’e, yana musu Sai anjima, Aunty dai rakiyan ido ta masa tana mamakin k’aramin yaro da irin wa’innan abubuwa, ko Dan acikin turawa ya tashine? Ta tambayi kanta, tana jinjina Kai, ta watsa ma Ummi da take ta murmishi Wani kallo,

 

 

 

Ummu Fatima ce

 

Asusun bank

4626334012

Fcmb

Asma’u Muhammad

Sai kimin magana in adding naki a paid

 

*KUNAN ZUCIYA TA*

_(KE ZAKISATA TAYO SANYI)_

 

*BY ASMA’U GALADIMA*

 

 

 

*Ummu Fatima marubuciyar*

*DIJAH QAYAH*

 

*Nafara da Sunan ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K’AI*

 

Littafina na kud’ine, 300 kacal,

 

Page 2

 

 

“Major Dan Allah ka fahimceni, ba wai Ina k’in Ajmal bane, Duk Duniya ba Wanda zai kaini son ganin ya zama Wani,

 

 

“Ya Isa Salma ya katseta da d’an zafi, sai Kuma ya sassauta murya, “Bakin San yawan takuri ma yaro da dak’ile buk’atansa yana sa shi ya shiga Wani haliba, ai irin takurin da kike nunamasa shine yake sa yaro ya lalace, Dan Allah ki dinga sassautawa, meye aciki Dan yaje Birthday, Birthdaynma na Yar Amini na, da suka taso kusan tare,

 

 

Mum ta sauk’e Wani irin dunk’ulallen ajiyan zuciya, ta d’an jingina bayanta tana d’an tsotsan lips d’inta a hankali, ita kad’ai Tasan abunda take ji aranta.

 

Dai dai lokacin Ajmal ya fito, cikin Riga da wandon jeans Mai mugun kyau da tsada, red and white, in and Out, Wani tafkeken Agogone manne a hanunsa irin na manyan yarannan dai masu ji da kansu, shima red, Hannayensa biyu rik’e da wayoyinsa, Dad ya k’yasta hanu cikin Jin dad’i yace “waw my Son kayi kyau, murmushi yayi yace Dad kud’in account dina ya kare, “ok barin sa maka Wani Dad din ya fad’a da sauri, Nan take kuma ya aikamasa dasu, ya d’an zauna a gefe cikin son shawo kan Dad din, yace “Dad motanka sabuwan Nan, sai Kuma yad’an Sosa keya, Dad yace “A’a Son d’azufa naga anwake taka tas, kaje Driver yakai ka aciki ya fad’a cikin Dariya,

 

Ajmal ya d’an b’ata Fuska kaman zaiyi Kuka, yace “Pls Dad nine fa Babban Bak’o a taronnan,

 

Dad ya gyada Kai gami da nuni da hanunsa, tace olright, ga key dinta can, ka d’auka, make sure driver ne zai kaika, and body Guard naka su take muku baya,

 

Cikin Wani irin farin ciki ya jinjina ma Dad din yace “Yes I luv u Dad, dadine sosai ya kama Dad Ganin D’an nashi cikin farin ciki haka,

 

 

Bayan ya d’auki key d’inne ya juyo ga mum da tayi k’uri da idanu tana kallonsu, “Sai na dawo Mum abinda ya fad’a kenan a d’okance, Bai Jira cewanta ba ya fice.

 

Steps bibbiyu ya dinga hadawa da tafiya Mai kama da gudu har ya sauk’a Sannan ya fita, Kai tsaye gunda sabuwar motan take ya nufa, ya bud’e rigan da aka lullube ta dashi, sannan ya Bude ya shiga, yayima motan Key, cikin sauri Drivernsa ya isoshi, tun kan yayi magana cikin tsawa yace “Dalla Malam Dad ne yace inyi Driving da kaina, sannan kada Wani ya bini, inba kayarda inje inkirashi yazo Yama bayani da kansa,

 

Driver yayi saurin Jan baya, Yana fad’in Allah ya tsare, na yarda.

 

Sojojin da suke bakin Gate dinne sukayi saurin wangame masa Gate ya fice cikin Wani irin Gudu, yana jinsa a kan titi, ya saki murmushin nasara, ya Kalli kansa ya Kalli mota Mai biliyoyin kud’i, ba abunda yafi burgeshi, irin kalan shigansa, kalan motan, nan ya d’aga waya ya k’ira freind dinsa Dini, ya gayamasa inda zai tsaya yazo ya d’aukeshi,

 

Misalin k’arfe Goma cif suka Isa katafaren Hotel din da Ake Birthdayn Zarah ‘yar abokin Dad, nanfa guri ya d’au tafi ana ga Aj ga Aj, cikin Wani irin taku Mai ji da Isa gami da yaranta ya Isa gun, Zarah ta fito cikin sassarfa ta rungumeshi, nan aka saki kid’a Rawa suka dinga tik’a cikin gwanancewa, jama’a suka fito suna d’auka a wayoyinsu ciki har da Mahaifiyar Zarah, da manyan Aminanta, sukan sunga abun burgewa awajen, kusan 3o minutes DJ ya dakatar dasu, gami da jinjina musu, da yabama wannan irin Rawa nasu da suka nishad’antar da Mutane, sannan yace anjima za’a Kuma nimoshi, kasancewansa Babban Bak’o agun Zarah da kanta ta kama hanunsa ta kaishi kan Wani kujera na musamman da aka tanadar agun kusa da nata, Nan aka gayyota k’ana nan yara suka fito Suma suka fara cashewa, daga nan DJ yace Mai gayyar ta fito ta taya Yaran cashewa, nan ta fito, tana Kuma tik’an rawa, Ajmal ya tashi ya fita ya fara mata b’arin kud’i, nan aka d’auki Sowa da tafi raf raf raf, ya b’arar da kud’i Mai yawa, kafin ya koma ya zauna, haka aka dinga k’iran masu Ruwa da tsaki a abun suna fitowa suna cashewa, a haka har aka kuma k’iran AJ dashi da abokin rakiayansa wato Dini,

 

 

Ba b’ata lokaci suka fito suka dinga Tik’a Rawa, wannan karon rawan AJn da banne da wanda yayi dazu, Jama’a da dama sun fita sun masa manni, har da Mahaifiyar Zarah da itama ta tayashi, rawan, Zaranma ta fito nan guri ya kacame, har sai da Ajmal din ya dakata da kansa ya koma kujera kafin gun ya sarara,

 

 

Ajmal ya ciro wayansa da yake ta ruri a aljihu, yana dubawa da Sam baijiba sai yanzu da ya fito, Ganin yawan Missed call d’in da Dad yamasa ne yasashi saurin mik’ewa, yasan komi akayi yanzu Kam Dad ya Ankara cewa shi kadai ya fita a mota, Bunch din kudi da Bai San yawansu bane ya ciro ya ajiye agaban Zarah matsayin Gift Bai Jira Jin abunda take fad’a ba, ya fice da sauri yana yafato Dini da yake kallonsa acikin mutane, ya fito kimanin mintuna biyu Dinin Bai Ida fitowa ba, ya shiga motan ya figeta a guje yana Ganin yanda Zarah ta fito a guje tana masa Hanu ya shareta ya wuce, Dan abunda Bai so shine Body guard dinsa su biyoshi, Dan yasan lallai Dad zai nimi venuen ya turosu, gudu yake tayi abunsa ba tare da tunanin komiba, Yana shawo kwana yaji Jiniyan tawagan Dad Dan haka yayi saurin sauk’a akan titin yana son b’uya can gefen Wani yaro Mai faci ya nufa, Wani Dattijo yana Shirin hawa abun hawansa, ya dinga jeramasa Horn kaman zai d’agashi sama, a fusace Dattijon yace “Haba bawan Allah, ya kakeson inyi kayi hak’uri mana ai dai zan baka wuri, a fusace Ajmal ya fito yana fad’in dallah can malam tsoho ka bama mutane wuri wlh ko intureka, Yaron da yake faci a wajen ya d’ago cikin Fushi ya kalleshi, “Kai d’an Uban waye Dan kazo da mota zaka ci zarafin Dattijo kaman wannan? Ajmal baiyi wata wataba, ya karasa yayi tsalle ya d’aura ma matashin Mari,

 

 

Cikin tsananin mamaki da Wani irin haushi Matashin ya damk’o wuyan rigan Ajmal yana fad’in lallai yau sai naga ubanka a garinnan ba mota ka d’auko ba wlh ko jirgin samane, yad’aga Hanu yana Shirin kaimasa duka, yaji Ruwan Belt da kulake ajikinsa, kafin ya Ankara yaganshi a Hanun sojoji tuni yagama jikata, Dittijon Nan ba irin magiyan da baiyiba ma Sojojin Nan anma Ina ko kulashi ba suyiba, Ganin haka ya k’arasa gun Dad da ya rik’e Ajmal cikin tsananin damuwa yana shafa wuyansa da Matashin ya shak’e, yana fad’in are ok my son?! durk’usawa Baban yayi gami da had’a Hannayensa yana magiyan su barshi, a fusace Dad ya Rik’e Ajmal Suka shiga mota, ba tare da ya Kuma kallon tsohon ba, ya lek’o yace ma Sojojin su tafi da shi suje su kulleshi, har sai ya nimeshi, nan suka sashi acikin mota, yana Kuka kaman zaiyi Yaya yana rok’on suyi hak’uri,

 

_________________________________________

 

 

 

“Ya AJ!

“Shiiitttt!!! Ajmal ya fad’a gami da d’ora yatsansa akan lips din khairi da take zaune bisa cinyansa, “Bana hanaki cemin Yaya ba? Ke nifa da Ina da k’annema duk yarinyan da tacemin Yaya b’allata zanyi, ni ko ‘ya’yana ba zasuce min Wani Dady ko Baba, Aj na zallah zasu fad’a,

“To ai Aunty ce tace Indinga cemaka Yaya, indaina cemaka My Husband, ko my AJ, ko my Heart, Ummi ta fad’a tana kallon Fuskansa, d’an murmushi Yayi ya shafi Fuskanta, yace “Khairi kina sona ko Baki sona? Khairi ta juyo da sauri ta Kalli k’ofan d’akin Aunty Sannan ta Kalli Nasiba da take zaune da Qur’ani tana karatu,

 

“Don’t worry Dear gayamin, ya fad’a yana Jan kumatunta,

Bakinta ta sako cikin kunnensa cikin rad’a tace “Ina sonka soasai sosai, ya saki murmushi gami da gyaramata zama acinyansa yace “Gud my luv ki dinga kirana da Husband ai fata kike mana, ni Dake mata da Miji ne, kinga ni Babban Soja zan zamo, zanyi kud’i da yawa, ba Wanda zai hanani aurenki sabida Ina da kud’i, Kuma zan Gina miki k’aton gida kinji, ta d’anyi Jim! Tace

 

“My Husband yanzu baka da kud’ine?

Ina kud’in da ka sayamin Chocolate jiya,

 

Dariya yayi har sai da kyawawan fararen hak’oransa suka bayyana, yace “Ba irin wannan kud’inba Khairi,

 

Zamewa tayi daga jikinsa tace “barin kawo maka kudin da Yayan Aunty ya bamu ranan da muka je yawon Juma’a, ya damk’o hanunta yana girgiza Kai yace “ki ajiyemin zan karb’a anma ba yauba, tace “to dai dai lokacin Aunty ta fito daga d’aki ta zauna kusa da Nasiba tana amsa gaisuwan da Ajmal yake mata, ta jingina bayanta tana fad’in shekaranjiya na bi gefen gidanku naganka da Mahaifinka da masu tsaronku, fusakan ka a murtuke, Lafiya kuwa?

 

 

Nan da Nan ya had’e rai, yace “Birthday naje aunty, na wata friend Dina, a hanyan dawowa Wani d’an rainin hankali ya kawo min raini, nan ya kwashe yanda akayi ya gayamta, ya d’ora da fad’in anjima zamu je da Dad inda aka rufeshi, wlh sai na masa Mari Biyar masu kyau, kafin a rufe, banza d’an talakawa, mara tarbiyya,

 

Aunty da ta tallafi hab’anta tana aikin kallonsa, ta numfasa tana d’an gyad’a Kai, ta Kuma kallonsa tana tuno randa ta fara ganinsa, wata ranan Asabar,

 

ta tashi da nak’udan cikin Ummul Khairinta, ta fita Dan ta motsa jiki kafin na asalin yazo, tayi yawo sosai ta gaji ta b’ullo ta bayan gidansu kenan Wani irin azababben ciwon mara ya kamata, Nan ta rarrafa, ta zauna a inuwan Flowers d’in gidansu tana hutawa, kusan mintunan ta uku agun tana Jin sanyin flowers din yana ratsata, ga Wani k’amshi da yake tashi, har ranta taji dad’in zaman gurin duk da ciwon da yake mutstsininta, Wani Soja ya fito daga gidan yana tambayanta “Malama bara kika zo ne? Ta juyo ta kalleshi a sanyaye tace “a’a ba bara nakeyi ba, Ina d’an hutawane, cikin Wani irin tsawa yace “Dallacan tashi kibama mutane wuri, sai kuzo ku zauna ajikin gidan mutane da Kun samu dama kuyi wuf ku shige ku musu sata, Ba k’aramin takaici maganan yabataba, to anma kowa a gidansa ai sarkine, da k’yar ta yunk’ura ta mik’e, zata d’aga k’afa gwiwanta ya rik’e ta fad’i akan gwiwan dai dai lokacin Ajmal ya dawo daga masallaci yana Shirin shiga gidan, da mum ta korashi yaje, da sauri ya k’arasa inda take ya duk’a, yana k’ok’arin d’agota, kallon k’aton cikin nata yake cikin tausyi ya dinga jera “Sorry Aunty, Sorry! da iya k’arfinsa ya dage yana d’agata, da k’yar ta mik’e, ta kalleshi tana yatsina fuska tace nagode k’anina, ya juya ya gallama sojan da yayi tsaye yana kallon su Harara, yace “me tamaka ka tureta?

 

 

“No no sir bani na turetaba, sojan ya yafaad’a yana kallonta,

Ajmal ya Kuma kallonsa cikin Fushi sosai yace

“Maza kaje ka had’a kayan ka ka bar gidannan, tun ban had’aka da Dad ba, mara tausayi kawai,

 

Aunty ta d’anyi murmushi cikin ciza lips, tace “bashi ya tureni ba Boy, kafana ne ya hard’e, na kuskuri faduwa,

 

Ya rik’o hanunta yace “Sannu muje in rakaki Asibiti Aunty, ta kalleshi tana hango tsananin tausayin nata acikin indanunsa, shi Kuma duk maganan da yakeyi Idonsa na kan cikinta,

 

Ta dai daita tsayuwanta, tace “kada ka damu gida zan koma banji ciwoba, ta fad’a gami da shafa kansa, sannan ta fara d’ingisawa tana tafiya, yayi sakare yana kallonta sannan yabi bayanta,

 

Da sauri Sojannan yabi Ajmal yana fad’in “kaga kazo ka shiga gida kada Dad d’inka yazo yayi fad’a,

 

Da har zai masa tsiwa sai Kuma ya sassauta Murya, “Barin Rakata, yanzu zan dawo, kar ka fad’a ma Dad, kaji.

 

 

Ba yanda Aunty batayi ya koma ba, Anma ya coge sai da yabita,

 

Har cikin gida ya Rakata ya dinga jera mata sannu yana karema gidan kallo, godiya ta masa, sannan tace masa yaje gida, kar amasa fad’a,

 

Bayan kwana biyu Ajmal yazo duba Aunty, nan yasamu ta Haifi ‘yarta da taci Suna Ummul Khairi, Tunda ya karb’i ‘yar yake ta Dariya, Uwa Mahaifiyar Mai gidan tace “yadai d’an sauryi ko kana sonta ne? Da sauri ya gyad’a Kai Alaman Eh, duk d’akin sukasa dariya, Uwa tace nabaka ita, yana murmushi ya mika’ata ya fita, Dan daga Masallaci yake, ya faki idon security ya taho,

 

 

Aunty ta sauk’e ajiyan zuciya, ta Kuma kallon Ajmal, cikin sanyi tace “anma Boy ban sanka da irin wannan halinba, wannan dawowankan naga duk ka canza hali, ko haka dama zaman England yake?

 

Dan Allah don girman Allah Boy, kayi hak’uri kacema Dad d’inka ya sake yaronnan, Dan Allah Boy na rok’eka,

 

Ajmal yad’an hargitsa Fuska aransa yana Jin ba’abinda zai Hana Matashin baiyi Prison ba, yace “Aunty kwala nafa yasha, har da cewa zaiga waye Ubana, wlh sai na koya masa hankali,

 

Ummul Khairi da ta dafa kafad’ansa tana kallon Fuskansa, tace “Dan Allah my Aj kayi hakuri ka barshi kaman yanda Aunty tace, ya d’ago Yana kallonta ta d’ora goshinta saman k’irjinsa, cikin sanyi tace “Dan Allah kayi hak’uri kaji,

 

Ajmal ya d’agota yana kallon manyan idanunta da suke kullum kaman sun Tara Ruwa, yace shikenan Khairi na, Sunci Albarkacinki daga shi har babanshi, Anma sai kincemin I luve u, cikin Dariya tace “I luve U my Luv, rungumeta yayi yana kallon Aunty da take kallosu, ya mik’e gami da ciro chocolate a Aljihunsa ya b’are yasamata a Baki, sannan ya juya yana fad’in Bye, Aunty ta tace “Boy zaku sakeshi? yace “yaci Albarkacin Wife d’ina Aunty yanzu zan je ince ma Dad na yafe masa asakeshi, gyad’a kanta kawai tayi tana binsa da kallo, yayima Khairi signa da ido, tana Shirin bin bayanshi, Aunty ta rik’o hanunta, “dawo ba inda zakije ai kunyi sallama, ya kwab’e Fuska, “Kai Aunty Wani magana fa zan gayamta,

 

“Kafa fita a idona Boy, Aunty ta fad’a tana nunashi da yatsa, ya saki Dariya Mai sauti ya juya yana fad’in kada ki damu Khairi zan dawo da daddare, daga haka ya fice,

 

 

“Ni Kam Ajmal Ina kake zuwa ne Wani lokacin idan kaje Sallahn Azahar ko la’asar?

 

Ajmal ya d’an shafi kansa yace “Mum Ina da freind fa, Mum ta zaro ido waje tace “lallai Ajmal baka jin magana idan ka sake Dad Dinka ya samu Wannan labari ka tabbata zaka koma Abuja, tun lokacin tafiyan school baiyiba, wato had’a Baki kayi da security ko? Dan nasan yanda yaja kunnensu akanka da baza su barka ba,

 

Dan murmushi yayi da ya tuno irin kud’in da yake basu kafin su barshi su dawo, Dan masallacin ma Dad sasu yayi su rika kaishi, in an idar su dawo dashi,

 

“Idan kasake na sake Ganin an idar da Sallah baka dawoba, sai nagayama Major, ya d’an marairaice Fuska zaiyi magana tace “yimin shiru kaje d’auko Qur’ani ka ban karatun da nabaka, ya tashi kaman yanda ta umurceshi,

 

_________________________________________

 

Bayan shekaru biyu, Tawagan motocine luntsuma luntsuma duka bak’ak’e a Jere suka shigo cikin Unguwan, direct daga Abujah suke, so yake yayi shigan sirri ma gidan nasa shiyasa Bai bari sun Saka jiniya ba, Sannan Bai sanar dasu zai dawo yau ba, dai dai Wani d’an siririn lungu ya hango d’an nasa, da sauri yacema Drivern yajuya, Nan suka juyo suka nufi lungun a bakin lungun yace ma Sojoji biyu, “naga kaman Ajmal a layinnan Maza ku dubomin shi, ya fad’a yana yarfe Hanu, yana ji aransa idan Ajmal d’inne, lallai yau zaiyi ma duka ‘yan gidan Tijara, ya Kuma kallon lungun aransa yace “Yaran talakawa! Da Yaran talakawa my Son yake relation? Cab! Yafad’a cikin zafi aransa,

 

 

Ajmal da ya mak’ale a jikin gidan Aunty da baikai ga k’ofan shiganba, ya d’auke numfashinsa gami da zaro ido yana hango k’afafun Sojojin da suke tink’aroshi, yana tunanin ba abun da Dad d’in ba zai iya yi ba idan yasan gidan da yake zuwan.

 

 

Taku Ummu Fatima

Kudin littafi 300

Asusun bank

4626334012

Sai kimin magana a layina

08065091824

Kofa a bude yake ga Mai bukatan saya tayi magana asata a paid group thanks

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment