Littafan Hausa Novels

Kufan Wuta Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Kufan Wuta Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

KUFAN WUTA

 

 

Free page 01

 

*TAFIYA DA GWANI ME DADI*

 

*ZAFAFANKU BIYAR sune suka sake dawo muku da wasu sababbin tsararru kuma zafafan labaransu guda biyar kamar yadda aka saba*

 

RAYUWAR MACE

rano

 

NOOR ALB

Mamuhghee

 

MASARAUTA

miss xoxo

 

BAK’AR INUWA

Billyn Abdul

 

KUFAN WUTA

Huguma

 

Zaku samu gaba daya labaran akan naira

 

1k kacal

2_400

3_500

4_700

 

*Zaku saka kudin ta wannan account din*

 

1487616276

BILKISU IBRAHIM MUSA

ACCESS BANK

 

*SAI KU TURAWA WANNAN NUMBER SHAIDAR BIYANKU*

 

09032345899

 

*KATIN MTN KUMA*

 

09166221261

 

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*

_MUJE ZUWA_

 

 

 

 

 

 

Dogon layi ne sosai kamar irin na kowacce unguwa ta masu matsakaicin qarfi,hagu da dama na layin gida jene a jere na masu matsakaiciyar rayuwa,wadanda basu cika mugun kyau ba,kamar yadda kuma basuyi lalacewa da rashin kyan gani ba,duk da cewa wani gidan yafi wani kyau,kamar yadda kowa da irin yadda ubangiji S W T ya tsara masa matakin rayuwar da zai wanzu a kai.

 

Yawancin gidajen plate ne masu soraye,masu ginin benen daga cikinsu ‘yan qalilan ne,haka nan gaban gidajen akwai kwata wadda tabi ta kowanne qofar gida,saidai kuma a rufe take da slap,duk da cewa zakaga daya biyu na wani gurbi da babu slap din,gurbin dake nuni da cewa cirewa yayi ko karyewa,ko kuma an tsigeshi ne bisa qarfi da da yaji,da kuma qiriniya irin ta yara,wanda bisa dukkan alamu ma slap din an hada taro da sisi ne daga mazauna layin an ginashi.

 

Daga can tsakiyar qarshen layin,wanda zaka iya karya kwana ta shiga dakai wani layin daban,dandazon yarane a tsaye carko carko sunata hargowa,idan daga nesa ka taho,zaka iya hangen yadda qura take tashi a wajen,alamu dake nuna cewa fada ake sosai a wajen.

 

Idan ka duba tsakiyar wajen sosai,yara ne guda biyu,wadanda gaba dayansu ba zasu zarta shekara goma ba gaba dayansu,’yar baqar dirarriyar yarinyar nata qoqarin kada abokiyar fadan nata,wadda idan kayi mata kallon farko ba zaka zaci zata iya dambe haka da abokiyar fadan nata ba,kasancewar bata kai wancar garin jiki ba,fara ce ba sol ba,kana iya hangen doguwar sumar kanta me santsi yadda ta debi qasa da yashi na wajen,sakamakon cirewar danwakalin kanta,baya ga hijabinta data ci damar dashi tun daga sanda za’a fara fadan.

Rayuwata Hausa Novels Complete

“Iman…..iman…..ga malam nan” wata yarinya ta qaraso wajen bayan taja birki tana haki,da alama daga wani sashen ta kwaso gudunta ta kuma tuqe a nan.

 

Sarai iman din ta jita,saita qara himma da hanzarin ganin ta yar da rahama kafin malam din ya qaraso,ta tabbatar matuqar bata gama ba ya qaraso fadan yazo qarshe,hakanan kuma babu makawa itace me laifi a wajen malam din,koda kuwa ta fisu gaskiya.

 

Saidai bata kai ga cimma burin nata ba taji tsawar malam din a kanta

 

Dattijon mutum,wanda a qalla shekarunsa sun tasamma hamsin,sanye da fararen kaya qal,riga ‘yar ciki da wando,sai babbar riga malum malum,kansa sanye da farin rawani,hannunsa dauke da buzu daya nade wani abu a ciki,daya hannun nasa kuma yana riqene da baqar leda

“Ke hajaru,kinci gidanku!,saketa nace” Ya fada cikin kaushin murya idanunsa duka bisa yarinyar.

 

Tunkude rahama hajar iman tayi,ta duqa tana kwasar takalmanta da dankwalinta da suka turbude cikin qasa,ranta a bace na rashin samun damar tumurmusa rahama da batayi ba,dai dai lokacin malam ya waiwaya ga yaran yana musu fada,tare da kora kowa zuwa gida,bayan ya bude ledar hannunsa ya fidda alewa ya rarraba musu.

 

“Muje gida ke kuma,’yar qaniya” ya fada yana tasa qeyar iman zuwa gida,suna tafe yana mata sababi har suka isa qofar daya daga cikin gidajen dake jere a layin.

 

Tun daga qofar gidan zaka karanci cewa gida ne na makaranta,ma’ana gidan da ake karantar da almajirai,saboda babbar rumfar kwanon da tabarmi dake malale saman simintin dake qasan rumfar kwanon,tun daga malalen simintin,tabarmin dake shimfide din zuwa qasar dake gaban gidan a share wajen yake fesss,kai kace lomar tuwo zata fadi ka duqa ka dauka abarka kaci saboda tsabar tsabta.

 

Da hanzari almajiran dake zaune a wajen,wadanda basufi biyar ba suka miqe

“Sannu da zuwa malam” duka suka furta,daya daga cikinsu ya matso yana niyyar karbar ledar hannun malam din,sai ya dakatar dashi

 

“Yi zamanka habu….inasu haladu?” Ya jefa tambayar ga daya daga cikin mazauna wajen,wanda ya fisu girma da wayo

 

“Basu dawo ba tukunna,amma nasan suna hanya” kai malam din ya jinjina

 

“Shikenan,ku fara shirin sallar magariba,duk wanda ya dawo kada ya fita,inason ganinku gaba dayanku”

 

“To malam” suka amsa masa cikin girmamawa,saiya juya ya saka kai zuwa soron gidan.

 

 

Faffadan tsakar gida ne mayalwaci sosai,wanda ke dauke da bishiyar mangwaro da babu kamarta a unguwar,wata iriyar bishiya da Allah ya sanyawa albarka,me yawan fidda ‘ya’ya masu dadin gaske da kusan kowa yake amfana da ita.

 

Dakuna biyu ne daga hannun damanka wanda suke falle daya da kuma rumfa da uwar daki,sai wasu da suke kalloka kana shigowa gidan,suma rumfa da uwar daka ne gaba dayansu,baya ga wani babban dakin falle daya dake a soron gidan.

 

Gab da soron gidan anan rijiyar gidan take,ma’abociyar ruwa me kyau da sanyi,wanda koda da rani ne nata qafewa,anan kusan duka ‘yan unguwar ke diban ruwa idan aka shiga yanayi na rani wanda ake yawan samun qafewar rijiyoyi da kuma janyewar ruwan famfo,bandakinsu na daga can wani dan sakaye sai kitchen dake taqi kadan daga dakunansu.

 

Yadda qofar gidan da sorayenshi suke qal haka cikin gidan yake,komai a killace cikin tsafta a kuma muhallinsa.

 

Daga qofar kitchen din wata farar macace zaune saman kujera ‘yar tsugono,sanye da wata jar atamfa data qara ma haskenta kyau,duka duka matar shekarunta na haihuwa zasuyi arba’in,saidai da alama ita din ma’abociyar tsafta ce da ado.

 

Kwando ne a gabanta wanda ke cike da alayyahu tana tsinkewa,baya ga albasa data gama yankanta tuntuni,cikin sauri sauri take aikin,da alama bata saba kaiwa dare kamar haka bata gama abincin dare ba.

 

Sau daya tak ta daga kai ta kalli iman wadda fa shigo tana gursheqen kuka,tabi takalmanta da ta riqo a hannu saboda tsinkewar da yayi,saita maida kanta taci gaba da aikinta,kamar ma batasan da wanzuwarta ba,abinda ya sake tunzura iman din,tayi zaman ‘yan bori a waje tana aje takalman nata a gefe,tare da sake bude muryarta tana sakin kukanta.

 

Ko dagawa ta sake kallon iman batayi ba,saboda irin wannan koke koken da rigimar ta banza da wofi ba yau ne farau ba a wajenta,kusan kowa na gidan yasan da zaman wannan,har zuwa sanda malam yayi sallama ya shigo,sai tayi qoqarin rage sautin kukan nata,ta hau zazzare idanu.

 

Da malam din ya kalleta dariya ta bashi,amma saiya danne,ya maida kansa ga matarsa safiya da ake kira da inna,wanna tuni ta miqe tana masa sannu da zuwa,bayan ta ajjiye aikin da takeyi ta qaraso ta rusuna ta karbi ledar hannunsa.

 

“Yanzu ke hajaru…..bakya jin fada kenan ko?” Malam din ya fada yana kama kunnensa da hannu daya

 

“Sau nawa zan hanaki fada da yara?,…..ina cewa ko sati ba’ayi ba kukayi fada da asama’u….naja miki kunne,shine har kin manta?” Tsuru tsuru tayi tana raba idanu,tsoron yadda malam keta fiddo mata manyan idanunsa irin nata ya shigeta,takan jima har ma ta manta kafin malam yasa hannunsa ya daketa,duk ranar da ya daketa din kuwa lallai ba shakka ta qureshi ne…..kuma fa zata ji a jikinta

 

“Daga yau bazan sake miki magana ba,amma zan saki a mari idan baki wasa ba” ya qarashe maganar yana sakin kunnen nasa.

 

Inna da tuni ta koma bisa aikinta tana saurarensu,haushi sosai yake cikata kan yadda malam din bai iya zagewa ya daki iman sosai kamar yadda takeso,saida yakan gaya mata cewa,duka baya tarbiyya,kuma bashi ke gyara yaro ba,saidai ya batashi,nasiha da kuma nusarwa sune suka kamata.

 

Sannu da gida yayi mata kamar yadda ya saba,yana tambayarta kowa lafiya,ta amsa masa da lpy qalau,wannan kusan dabi’arsa ce,mutum ne shi managarci,wanda yake matuqar kula da iyalinsa dama buqatunsu,bakin gwagwadon ikonsa,abinci abinsha da suttura duka bai yarda sunfi qarfin iyalinsa ba,komai qanqantar abu ya daukewa gidansa,saidai duk da haka bai hana inna sana’a ba,saboda sanin muhimmancinta ga diya mace.

 

Gangarawa malam yayi ya daura alwala,ya maida rawaninsa yana shaidawa innar zai sake fita,bazai shigo ba sai an idar da sallar isha’i

 

“A dawo lafiya,Allah ya tsare” tasan ya fadi hakanne don kada ta damu da rashin gamaabincinta akan kari,shi yasa ya fita ya bata sarari don ta samu ta kammala a nutse.

 

Fitar malam din kamar dama jira hajar take ta sake bude baki da sabon babin kuka,abunda ya qule inna sosai,tayita qoqarin danne zuciyarta don kada ta kaiwa hajar din hannu,amma ko alamun sassauta kukan hajar batayi ba,abinda ya dinga tunzura inna kenan,taji babu makawa saita jibgi hajar din sannan zataji sassauci,don haka ta saki dambun data gama hadawa tana maidashi madambaci hawa na biyu,ta miqe a fusace.

 

Malam na gyara hannunsa daga qofar fita daga gidan,yana magana da wani babban dalibinsa sahabi,ya daga kansa a hankali sanda ya fara jiyo muryoyinsu,duk kuwa da cewa basu kai ga qarasowa inda yake ba,amma kuma har zuciyarsa ta tafi inda suke.

 

Su dinne kuwa,matasan yara su biyu ne tafe,suna jere da juna,dukkaninsu shekarunsu basu wuce sha bakwai ba,yanayin fuska da kuma yadda suke tafe cikin raha zai iya sawa mutum yace ‘yan biyu ne,saidai kuma kamanni da sukayi matuqar shan bambam a tsakaninsu zaisa ka gane ba twins din bane.

 

Matashin farko ya dara dan uwansa fari da haske da kuma tsaho kadan,wanda idan baka da lura ma babu lallai ka gane hakan,yana da zagayayyar fuska da madaidaicin hanci mai tudu,siraran labba masu kyau da kwantaccen gashin gira,duk da cewa akwai sauran shekaru masu tarin yawa a gabansa…..amma kuma sai gashi saje ya fara fito masa sosai,alamun dake nuni da cewa mutum ne me yawan gargasa,don sumar kansa ma kawai ta nuna alamun hakan.

 

Wani irin idanu gareshi kamar na mai jin bacci,saidai idan kuma ya budesu sosai xaka fahimci manya ne suna da girmansu,duk da bai gama girmansa ba,amma kuma zaka fahimci shi din dogo ne,ya fito daga jinsin yaren da sukafi alaqa da fulani,yana sanye da riga t,shirt me kwala mai gajeran hannu,sai wani wandon jeans wanda ya danyi fari kadan,qila saboda yawan morarsa da yakeyi ne,saidai kana kallon jikinsa kasan gwani ne wajen tsafta,domin kuwa…..duk da wuni da yayi wajen aikinsa,hakan baisa koda karin gugarsa ya bace ba bare akai ga yin dauda,muhammad al’ameen kenan.

 

Saurayi na biyu shima farine,don har yafi dan uwansa fari,hakanan shima ba baya bane wajen kyau duk da cewa shima shekarun nasa basu gama bayyana komai ba,abu gudan da ya sake bambanta su….yafi dan uwan nasa garin jiki,shi kuma shadda ce a jikinsa,duk da cewa ba wata ta azo a gani bace ba,amma shima fes yake,saidai hannunsa da yayi baqi,sabida aikin gyaran mota da yake koya a wani garage,umarul farouq kenan wanda ake kira da faruku.

 

A ladabce dukkaninsu suka qarasa daura da malam,suna masa barka da yamma,fuskarsa fadade da fara’a,zuciyarsa kuma cike da alfahari dasu yake amsa musu da

 

“Yawwa…..ya wajen aikin?”

“Alhmdlh” suka amsa masa a kusan tare

 

“To ma sha Allah” sai suka miqe suka nufi cikin gidan,wanda al’adarsu ce kowacce rana,idan suka dawo gida lokaci irin wannan,basa shiga dakinsu dake soron,wanda shi suke fara tararwa,har sai sun shiga sun yiwa innar sannu da gida sun shaida mata dawowarsu.

 

A fusace inna ta ciri wayar radio dinta dake a gefanta,wadda ko awa biyu ba’ayi da kawota daga gyara ba,aikin da ya kacame mata yasa bata samu tashi ba bare ta miqa ta daki,sai tayi kan iman cikin fushi tana fadin

 

“Bari na dakeki da kyau…..sai kiyi kukan me dalili”

 

“don Allah innarmu” kalmar data ratsa kunnensa kenan,abinda ya sanyata tsaiwa cak daka dukan iman da tayi niyyar yi,ko da bata juya ba tasan waye,ba yau ta fara jin hakan daga bakinsa ba,matuqar yana gidan,matuqar kuma yana kusa baya yarda da adaketan,ya gwammace ya horata ta sassauqar hanya,amma baya qaunar a daga hannu a daketa.

 

Kafin innar ta gama miqewa tsaye daga durquson dukan da tayi shirin mata….tuni har ita iman din ta miqe da hanzari,ta kuma falla da gudu tayi inda alameen din yake tsaye.

 

Kafin ta iso ya duqa,ya kuma yiwa jikinsa garkuwa da hannyensa,saboda yasan tana zuwa din jikinsa zafa fada da shagwabar nan tata,abinda ya jima da yi mata shamaki da aikatashi,saboda yadda a kullum take qara girma,shekarunta suna daduwa.

 

Ilai kuwa tana zuwa abinda ta shirya yi kenan,saidai ya sanya hannayensa ya riqe nata hannuwan,ta sakar masa kuka,cikin sigar lallashi ya fara magana

 

“Ya isa haka…..ya isa,karki bari aga hawayenki mana” yana maganar ne tare da sanya gefan dankwalinta yana goge mata fuskarta,sannan ya miqe daha durquson da yayi ya kama hannunta suna takawa zuwa tsakar gidan.

 

Tsaki yaji daga bayansa,ya kuma san ba kowa bane illa sadiqu,wanda ya tabbatar da cewa zuciyarsa yayi matuqar kaiwa nesa,da kuma kara da yayi masa yau,banda haka tabbas ya sani….da tuni ya jima da kai hannu jikin iman din,kamar yadda ya saba duk sanda wani abu irin haka ta faru.

 

Yana riqe da hannunta har suka qarasa inda inna ke tsaye daura da qofar kitchen,ya russuna yana fadin

 

“Barka da gida inna” yana kuma ajjiye mata daya daga cikin baqaqen ledoji guda biyun da ya shigo dasu

 

“Barka kadai aminu,ya wajen aikin?”

 

“Alhmdlh inna”

 

“Ma sha Allah,Allah ya qara albarka” ta fada tana ajjiye kallonta kan Ledar da ya ajjiye ya tura gaban innar

“Alhamdulillah inna” ya amsa mata,saidai hankalinsa yana kan iman,wadda har yanzu take kumburi

 

“Me iman tayi inna?” Lamin ya maida dubansa ga innar bayan ya dauke idanunsa daga kan iman

 

Sai da innan ta tabe bakinta sannan ta ja ledar ta fara budawa kafin ta bashi amsa,amsar da tasan koda ta bashin babu abinda zai sauya zani

 

“Fada dai fada dai ita da yara,fadan da kuma kai da kanka sai da ka rabashi amma malam ya ganta da yaran bata haqura ba,ita ba za’a gaya mata ba taji kenan?”.

 

Kansa ya juyar ga iman,wadda ta sake tale baki tana shirin fara wani sabon kukan

 

“Me yasa iman?,ina cewa ni da malam duka mun raba wannan fadan ko?” Cikin muryar dake nuni da cewa tana gab da sake sakin wani sabon kukan tace

“To ba sune ba…..da na fito sai su fara tsokanata….bayan kuma ni ban kula su ba…..wai idona irin na mage” qaramin murmushin da ya sake qawata fuskarshi ya sake,yana kuma duban qwayar idanun da take magana a kai,tabbas qwayar idanun nata dama eye lashes dinta ba irin na kowa bane,wannan yasa yara da yawa suke tsokanarta,abinda ita kuma ta tsana kenan,yake kuma yawan hadata fada da yaran,tasha sanya kuka kan a cire mata idanun a sauya mata wasu,duk saboda yadda yaran suke tsokanarta,ko kallonta inna batayi,alameen dinne yake tsayawa ya lalace bata haquri da lallaminta,tare da qoqarin yi mata bayanin cewa ba ciwo bane.

 

 

Cikin nutsuwa ya tattara hankalinsa a kanta

 

“Sau nawa zaance ki daina damuwa uhmm?,dukanmu muna son ganinki haka,kuma ke me kyau ce,bakiga duka kin fisu kyau bane?ke ta dabance kinji?,ki daina damuwa da abinda zasu fada” murmushi ta saka kamar kowanne lokaci idan ya yarrasheta irin haka,sai ta gyada kai tana murmushi,abinda ya sanya dimple dinta na hagu da dama lobawa,sai shima ya biye mata wajen sakin murmushin

 

“aminu…..an kira salla,ka tashi kayi buda baki ka rabu da wanann sakaryar” cewar inna,tana turo jug na ruwan sanyi data jefawa qanqara gabansa,waiwayowa yayi ya dauki ruwan kana ya miqe yana duban iman

 

“Zanje sallah na dawo….”

“Ina tsarabata?” Ta fada a shagwabe tana langwabe wuya tun kafin ya qarasa maganar da yakeyi,murmushi ya sakamar mata,shi kansa yana yaba rigima irin na iman,shi yasa babu wanda suke shiri dashi kaf gidan saishi kadai,sai kuma malam wani zubin

 

“Zan taho miki da ita” ya amsa mata yana shirin daga qafarsa

 

“Qaniyarki….ke me yasa kullum bakya hankali?”

 

“Idan na iso wajen saina balla mata dan yatsa,laifinsa da yake biye mata” saddiqu daya gama daura alwalarsa a bakin famfo ya fada bayan ya zubda ruwan kuskure bakin da ya guntsa,yana warware dogon hannun rigarsa tare da jefawa iman din harara kamar idanunsa zasu zazzago qasa

 

“Amma dai ina cewa ba da kai take ba ko?,to ba ruwanka” alamin ya fada yana watsawa saddiqun nashi idanuwan,sanda yazo gab da shi zai fice daga gidan,xuwa qofar gidan don miqawa malam kofin ruwan sanyi suyi buda bakin tare,kamar yadda suka saba,kusan dukansu suna azumin litinin da alhamis,hatta da iman qaramarsu ta fara,yau dinne kawai ya zamana shi da malam ne kawai suka samu damar yi,saddiqu yayi zazzabi na kwana biyu,bai jima da warwarewa ba,abinda ya hanashi yi kenan,ita kuma inna uzuri irin namu na mata,sai kuma iman wadda tun safe al’amin ya daure mata qarqashi kan cewa yau akwai rana,tasha ruwa abinta,ta bari sai ranar alhamis tayi,inna tayita mita har ta haqura ta sanya musu idanu,idan da sabo ta saba da wannan dabi’ar ta al’amin da iman,bama ita ba,duk wanda ya rayu dasu koda na ‘yan kwanaki ne sai ya fuskanci haka.

 

_ina matan dake fama da qaranci ko daukewar sha’awa saboda gajiya qarancin sinadarai ko kuma gajiya a jikinsu?,kina fama da maigida wajen rashin samun gamsuwa fannin auratayya?,dukka matsalarku ta yanke da HILTI UNISEX CHOCOLATE,maza garza kizo ki nema taki_

 

_CHOCOLATE CE da zaki shata kamar sauran chocolate,saidai kuma aiki a jiki,ba ruwanki da neman tarkacen magunguna mata marasa inganci,AKWAI TA UWAR GIDA AKWAI TA MAIGIDA_

 

_GAME BUQATA KO KUMA SON QARIN BAYANI,SAIYA TUNTUBI WANNAN NUMBER_

 

+234 818 401 7452

 

*Tasted and trusted*

[7/19, 10:01 PM] Mummyn Yara:

 

 

*FREE PAGE 02*

 

 

_ina matan dake fama da qaranci ko daukewar sha’awa saboda gajiya qarancin sinadarai ko kuma gajiya a jikinsu?,kina fama da maigida wajen rashin samun gamsuwa fannin auratayya?,dukka matsalarku ta yanke da HILTI UNISEX CHOCOLATE,maza garza kizo ki nema taki_

 

_CHOCOLATE CE da zaki shata kamar sauran chocolate,saidai kuma aiki a jiki,ba ruwanki da neman tarkacen magunguna mata marasa inganci,AKWAI TA UWAR GIDA AKWAI TA MAIGIDA_

 

_GAME BUQATA KO KUMA SON QARIN BAYANI,SAIYA TUNTUBI WANNAN NUMBER_

 

+234 818 401 7452

 

*Tasted and trusted*

 

 

Basu shigo gidan ba su duka sai bayan sallar isha’i,saboda suna tsayawa daukan karatu wajen malam cikin almajiransa,hannunsa riqe da baqar leda wadda taketa maiqo dauke da awara me zafi da tasha cabbage da yaji mai uban yawa.

 

Dai dai lokacin da iman din ke zaune gefan tabarma tare da innarmu wadda ke lazumi bayan ta gama tata sallar,abincinta na gefe bata tabashi ba,innar tana ankare da ita amma bata kulata ba,iman din irin yaran nan ne da ko kadan basa qaunar abinci,wani lokaci har sai innar ta ajjiye madoki kusa da ita sannan zata ci abincin,wannan dalilin yasa bata da kumari ko kadan,kusan duka sa’anninta sun fita girman jiki.

 

Tana jin sallamar alamin ta miqe daga shirin kwanciyar da takeyi,ya qaraso gefanta ya zauna yana ajjiye mata ledar awarar,fuskarta a wadace da murmushi ta janyo ledar ta fara budawa tana cewa

 

“Na gode yaya alamin” shima murmushi kawai yayi ba tare daya amsa ba,suka bita da kallo sanda ta miqe zuwa kitchen,da alama plate din da zata juye awarar take nema.

 

 

Kusan lokaci daya suka dauke idanunsu shi da inna,sai innar ta ajjiyr carbin hannunta gefan daddumarta tana cewa

 

“Zauna aminu” sabule slippers din qafarsa yayi,ya zauna daga gefa,cikin yanayi na nutsuwa

 

“Me yasà koda yaushe saidai ka yita biyewa shirmenta?,ta yaya ku da kuke nema ya kasance koda yaushe baka da aiki sai batar mata daa kudi?,yanzu meye laaifin daambu da bazata ci ba,saidai awara?” Murmushi ya saki kawai,sannan a nutse yace

 

“Inna mu din mune dolen imaan,mu ya kamata ace munyi mata daman,idan bamuyi mata ba waye zaiyi mata,kuma bata roqan kowa a waje saimu da muke yayyenta,kuma ma amfanin neman kenan inna,iman ba wani abu take tambaya ba da ya wuce dan abun marmari” kai kawai innar ta raausayar,dama tasan zaa rina indai lamin ne,wannaan ba shine karo na farko da magana irin wannan ta ratsa tsakaninsu ba,ta rasa wacce irin qauna da kulawa ce wannan da yakewa imaan din,duk da cewa sun kyautata masa matuqa da gaske,kyautatawar da duniya ma ta shaida da hakan,amma kulawar da iman ke samu daga gareshi ta musamman ce.

 

Koda ta matsa wajen ganin cewa ta hanashi,ko kuma ya rage tasan bata bakinta ne kawai,lamin din bazai sauya ba,a nata hasashen da ganin kamar ya kamata ya rage din,tunda ko babu komai akwai yayarsa dake aure a qauyensu,wadda wasu nauye nauye nata dana yaranta duka ya daukesu bisa wuyansa,kasancewarsa yaro jan gwarxo,mai himma qoqari da kuma neman na kansa,komai dadi komai wuya,kuma komai rintsi,kwata kwata baisan wata kalma ta lalaci,son jiki ko kuma qyuya da ganda ba,dukkan wani aiki da zai samar masa da kudi na halak yana tallafarsa,ya kuma karbeshi hannu bibbiyu yayi,babu girman kai babu ha’inci ko son jiki.

 

“Shikenan,Allah yayi muku jagora,yasa albarka a nemanku”

 

“Ameen inna…ameen” ya fada yana jin dadin addu’arta,uwa ce me yawan addu’a ga ‘ya’yanta,kome qanqatar alkhairi idan sukayi,bakinta baya gajiyawa da yi musu addu’a dare da rana.

 

Duk sanda tayi masa addu’ar sai yaji dadi qwarai da gaske qasan ransa,ya rasa mahaifiyarsa tun hankali bai fara riskarsa ba,sai gashi Allah ya musanya masa da wata makwafinta a sanda baiyi zato ko tsammani ba,a lokacin da ya dauke haso ya kuma debe tsammani daga samun dukkan wani tattali kulawa ko kuma jin dadi,cikin tausayi da kuma jin qai na ubangiji ya hadashi da wasu kwafin na iyayensa.

 

Daga inda take zaune take binsu da kallo,sanda ya karbi awarar da kansa ya juye cikin farantin robar da iman din ta dauko,sannan ya zauna yana gutsutsura mata da daya da daya yana miqa mata tana ci suna hira,kallo daya xakayi musu ka tabbatar da cewa lallai akwai shaquwa me girma a tsakaninsu.

 

Lumshe idanunta inna tayi,bahaushe yayi gaskiya da yake cewa

“Da da da dukiya babu wanda yasan me morarsu sai Allah” ta Sauke idanunta tana tuna ranar farko da suka fara sanin lamin,ya kuma shigo rayuwarsu ya zama daya daga cikin iyalan gidan.

 

 

Malam ibrahim khalili shine cikakken sunansa,haifaffen garin maiduguri,cikakken babarbare wanda ya fito daga gida na ilimi da karatu,asalin gidansu malam khalili gida ne na malamai,da suka gaji karatu tun daga kakanninsu,malam khalili yana daya daga cikin yara uku da suka gaji mahaifinsu,duk kuwa da cewa su biyu rak mahaifiyarsu ta haifa Allah yayi mata rasuwa.

 

Khalili ya tashi da son karatu da kuma nema tuquru,wannan yana daya daga cikin dalilan da suka sanya yabar maiduguri,ya shiga duniya neman karatun qur’ani dama na addini haiqan,daga gari zuwa gari,har ma wasu qasashen da muke maqwabtaka dasu.

 

Sosai karatu ya daukewa khalili hankali,bai samu yin aure da wuri ba,har zuwa sanda ubangiji ya nufeshi da zuwa qasar niger.

 

A canne ya hadu da fatima buzuwa,tana zuwa daukan karatu makarantar wani abokinsa,yarinya ce a sannan me qwazo da kuma hazaqa,don lokacin ma ta kusa kammala haddar qur’ani,tana izifi na hamsin da biyar,tun daga baqara take rubutawa a allo ta haddace sannan ta wanke a sake yi mata qari,ta samu tarbiyya me kyau da kuma kulawa,duk da cewa mahaifinta ya rasu,amma mahaifiyarta batayi sakaci da tarbiyyarta ba,saboda ita daya Allah ya basu.

 

Lokaci daya soyayya da shaquwa ta shiga tsakaninsu,suka fahimci juna da kyau,manya suka shiga maganar aka tsaida maganar aure,ba dadewa suka angwance,ya kuma daukota ya taho da ita garin kano,inda anan ya bude tsangayarsa shima,yana karbar almajirai daga kowanne gari ko qasa.

 

Almajirancin makarantar malam khalili ba kamar sauran almjirci bane da muke gani ayanzu,wada aka watsar da duk wani mutunci da kuma kimarta a yanzu,yara suke wahala da sunan neman ilimin alqur’ani me girma,wanda sam hakan bashi da tushe bare asali sam cikin addininmu.

 

Dukka yaron da zai karba sai ya kasance makusancinsa ne ya kawoshi,zaa rubuta adreshinka da lambar wayar wanda ya kawoka,sunan gari dana qauyenka da kuma inda za’a iya samunka,sanna bai yarda a kawo masa yaro babu haka ziqau ba babu abinda zaici,abun kwanciya da kuma kayan baqatun yau da kullum,saboda shi din bai yarda da fita bara a makarantarsa ba,karatu aka kawo yaran shi sukeyi,yakan baka zabi idan ka soma hankali,kana da sha’awar karatun boko?,idan kana dashi zai shaidawa iyayenka ya sanyaka a makaranta,idan baka buqata kuma zaka kama sana’a ne,don bai yarda da zama babu sana’ar yi ba,saidai kowacce sana’a kake kana yinta ne bisa sanya idanunsa da kulawarsa,da kuma tabbatar da cewa sana’ar da kakeyi din bata sabawa addini da kuma al’ada ba.

 

Wannan dalilin ya sanya makarantarsa ta kasance mai tsari,mutane da dama sukeso kawo yaransu karatu nan wajensa,saidai duk shekara akwai adadin da yake dauka,idan suka cika kuma baya sake dauka sai wata shekarar.

 

Zamansa da fatima wani irin zama ne me matuqar dadi da kuma ban sha’awa,khalili wani irin mutum ne managarci,mai halaye da kuma dabi’u masu kyau,tsayyen akan harkar gidansa da kuma sauke nauyin iyalinsa,idan kaga fatima zakayi tsammanin tana auren wani me halin ne,saidai ko daya,tsabar kula da take samu ne da kuma tsaiwar mijinta wajen sauke nauyinta,babu abinda ta nema ta rasa,tana matuqar jin dadin xama dashi,kamar yadda shima yake yaba mata,yake kuma matuqar jin dadin xama daa ita,saaboda ita din macace ta gari,mai tarin biyayyawa mijinta,wadda tasan dai dai ta kuma san akasin hakan,bai taba cewa tayi ta musa ba,kamar yadda bai taba cewa ta bari taqi ji ba,Shi yasa shima yake qaunarta,da kuma qoqarin ganin ya hidimta mata iyakar iyawarsa,bata nema komai ta rasa ba cikin gidanta,cikin wannan yanayin,shekara biyu da aurensa Allah ya albarkaceta da samun haihuwar santalelen da namiji,aka sanya masa abubakar saddiq.

 

Daga kan saddiq tayita haife haife suna mutuwa wato WABI,makusanta da wasu cikin dangi sukayita so malam khalili ya qara aure,amma yace sam baiga dalili ba,yanajin dadin zama da matarsa,bai nema komai ya rasa ba,idanma ta hahuwa ce,kana iya haifar yaro guda daya amma ya zame maka me albarka fiye da masu tarin yaran,indai yana da rabo a haihuwa zata qara,ita kanta a sannan ta bashi dama amma yace bazaiyi ba,Cikin ikon Allah kuma sai Allah ya basu haihuwar hajar iman,haihuwar da duka fidda rai da ita,zuwan iman a daidai wannan lokacin ya janyo mata soyayya mai tarin yawa,saboda tazo a sanda basu zata ba,ta kuma zo a dai dai lokacin da suke marmari da buqatar qaramin yaron cikin gidan.

 

Shekarar iman daya a duniya da watanni biyar lamin ya shigo rayuwar cikin gidan a lokacin.

 

Yadda jama’a keta yabawa malam khalili kan yadda makaranta da kuma dalibansa suke a tsare ya sanya malaman wasu tsangayun dake unguwarsu da kuma wasu unguwannin suka shiga adawa da kuma takun saqa dashi,suke kuma matuqar jin haushinsa,ganin cewa ya fita daban da sauran malaman tsangayu,babu bautarwa ko azabatarwa ga dalibansa,kamar yadda bai yadda ya zama cima zaune me matacciyar zuciya ba,sai abinda iyayen yara suka dauko suka bashi,aah,shima kamar kowa,duk sanda ya tashi dalibansa shima yana tafiya neman kudinsa,ya dawo kuma lokacin da aka kusa sake zama ci gaba da karatu,komai nasu na tafiya a tsare ne,kana ganin dalibansa da yadda yake tafi da komai dole ya baka sha’awa.

 

Daren wata jumma’a ne,tana zaune tsakar gidanta daya kasance sai ita daya,sai hajar dake kwance a gefe saman wani abun shinfidarta me hade da katifa maras tudu,duk kuwa da cewa akwai motsin almajirai da hayaniyarsu daga qofar gida amma cikin gidan ba kowa,saboda babu wanda ke shigarwa malam gidansa gaba gadi don suna almajiransa,idan kaga yaro cikin gidan,to qaramine wanda shekarunsa basu wuce wanda shari’a ta wanzar da hani na shigarsa gidajen matan aure ba,tana da mai mata aike da maiyi mata wanki ana biyansa duk a cikinsu,bai yarda suyi mata aiki ba tare daya biyasu ba,saboda yace su din mutane ne suma kamar kowa.

 

A hankali hayaniyar tasu ta fara raguwa,da alama an gama rabon abincin dare ne,wanda ake auna cikin abincin kowa a hada,manya a cikinsu su dafa a rabawa kowa,a wani gida da suke zaune wanda yake daura da gidan malam din,gida ne da wani bawan Allah ya bayar kyauta su dinga kwana,hankalinta bai wajen sosai,yana can ga tunanin abinda ya tsaida malam da din bai dawo yadda ya saba ba,shi da saddiqu da yayi masa rakiya.

 

 

“Taho a hankali….riqeshi sadiqu” ta jiyo maganar malam din tun daga soro,abinda yasa ta ajjiye allon da take rubuta fasayakfika humullah ta maida hankalinta ga qofar shigowa gidan.

 

Malam dinne da sadiqu da wani dan farin yaro da bata sanshi ba,ta miqe tana masa sannu da xuwa,ya amsa hankalinsa yana kan yaron

 

“Maza dora ruwan zafi innar saddiqu” malam din ya fada yana tsugunnawa a gaban yaron,yana yage ragowar rigar jikinsa,da hanzarinta ta koma madafa,ta hada ragowar itacen data gama girki ta kunna ta dora masa ruwan,sannan ta dawo tsakar gidan,inda malam ke tsugunne gaban yaron yana masa sannu,sadiq na tsaye a saman kanshi yana kallonsu.

 

Kujera ‘yar tsuguno ta jawo ta zauna,idanunta akan yaron da yake cikin hali na galabaita ta yiwa malam sannu da zuwa

 

“Yauwa binta” ya amsa da alamun rashi na a bace ne

 

“Ki duba maganin zafi don Allah idan akwai,idan ruwan yayi zafi ki juye sadiqu ya tayashi gasa jikinsa,bari naje na dawo” daga haka malam din ya miqe ya fita.

 

Duk yadda malam din yace tayi haka tayin,ya gasa jikinsa da kyau,sauran ta sakashi ya shiga bayi yayi wanka dashi,cikin kayan sadiqun ta zabo wasu ta bashi ya sanya,don xasuyi kai daya dashi,yana gamawa ta zuba masa abinci,ta koma ta dauki iman data tashi ta fara rigima ta fara bata nono,daga inda take din tana kallon yadda sadiqu ya sanyashi a gaba yana kallo,tun dazun shima zuciyarsa a karye take fuskarshi ta nuna hakan.

 

Malam ne yayi sallama,ya qarasa gaban yaron yana duban yaron daya ambata da lamin,ya bashi paracetamol din daya shigo dashi da kuma ruwan tea me zafi a leda,yace idan ya gama yasha yasha maganin,sai saddiqu ya kaishi daki ya kwanta.

 

https://arewabooks.com/book?id=628235bbb77ff582983d6c6b

 

 

Da ɗumi-ɗuminsa

 

Please

*_Follow me_*

*_Share_*

*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

 

 

*_KUFAN WUTA_

_Safiyya Huguma_

 

*1*~ *_BAQAR INUWA_

_Billyn Abdul_

 

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅

_Hafsat Rano_

 

*1*~ *_MASARAUTA_*💪

 

 

 

*KATIN MTN*

 

09166221261

 

 

*_TEAM ZAFAFABIYAR

 

 

*KUFAN WUTA*

 

 

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar_

 

 

*YADDA AKE BUDE ACCOUNT A AREWABOOKS*

 

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form din kamar haka: –

 

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

 

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

 

*Enter an username* (Sunanki)

 

*Enter your password:* ( misali 12341234)

 

*Confirm password:* (misali 12341234)

 

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks

 

*Continue with Google* – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

 

*Register* – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

 

 

*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

 

 

 

 

Masu iPhone

 

Zaku iya bibiyar shafinmu

https://arewabooks.com

 

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*

 

 

*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

 

+234 903 177 4742

 

 

_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan_.

 

 

 

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

[7/19, 10:01 PM] Mummyn Yara: 03

 

 

 

 

 

 

 

*ZAFAFA BIYARRRRR*

 

 

*_INGANCIN LABARAI_*

 

*_FASAHA NUTSUWA DA IYA SARRAFA ALQALAMI_*

 

*_TSARI DA TSANTSAGWARON HIKIMA_*

 

*_SOYAYYA MAI RATSA ZUKATA DA NARKAR DA ZUCIYA_*

 

*_JIGON LABARAI DA YASHA BAMBAM DA NA SAURA MAI SANYA ZUCIYA MAMAKI DA TUNANI_*

 

*_YIN LINQAYA CIKIN DUNIYAR LABARI KAJI KAMAR DAKAI AKEYI DA GASKE NE_*

 

*DUKA SAI CIKIN GAMAYYAR LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

 

*_ADADE ANAYI SAI GASKIYA_*

 

*_HIKIMA KASHIN KWANCE_*

 

*ABOKAN HIRA NE GA WANDA KE CIKIN KADAICI!*

 

*ABOKAN TAFIYA GA WANDA KE CIKIN NISHADI*

 

*WARWARAR MATSALA GAME NEMAN MAFITA*

 

 

*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥

_Safiyya Huguma_

 

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥

_Billyn Abdul_

 

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅

_Hafsat Rano_

 

*1*~ *_MASARAUTA_*💪

_Miss Xoxo_

 

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥

_Mamuhgee_

 

 

 

Guda 1👉300

Guda 2👉400

Guda 3👉500

Guda 4👉700

Guda 5👉1k

 

 

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

 

Bilkisu Ibrahim Musa

1487616276

Access bank

 

Number shaidar biya👇🏼

 

*_09032345899_*

 

 

*KATIN MTN*👇👇

 

09166221261

 

 

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*

______________________________

 

 

Ajjiye iman inna tayi sannan ta nufi daki,ta dauko babbar tabarmar malam din da yakan zauna a kai ta shimfida masa,sannan ta gabatar masa da abinci da ruwan wanke hannu,ta zauna nesa kadan dashi tana ci gaba da shayar da iman wadda ke rigima saboda bata qoshi ba,ta sakeyi masa sannu da xuwa

 

“Yauwa sannu binta,ya hidima ya gida”

 

“Alhmdlhi” ta fada tana dan murmushi,duk data saba da irin wannan kulawar tashi,amma duk sanda ya tambaya din hakan yana mata dadi,saboda tasan cewa mata da yawa ne suke neman hakan basu samu ba

 

“Wannan yaron da kike gani sunansa lamin,na tsinceshi ne a can unguwar da naje nida saddiqu dubiyar abokina,abinda ya bani mamaki yaro qarami yashe gaban famfon tuqa tuqa,jikinsa duka tabo na duka,yasha ruwa yanata amansa,wadda ina tsammanin babu komai ne a cikinsa,yayimin kama da almajiri don haka na matsa kusa dashi,sai daya dan rage aman na tambayeshi sunansa da kuma inda yake,yamin bayani,ashe almajirin makarantar malam dan lami ne,sai na tuna kwanaki uku da suka wuce tabbas naji ana neman wasu cikin daliban,na tambayeshi me yakeyi to a nan,kansa tsaye ya shaida min guduwa yayi,na masa fada na kuma nemi dalilin da yasa yabar makarantarsu,shi baya jin tsoron wani abun kada ya sameshi,a yadda na fahimta tsoron malamin da makarantar yafi tsoro akan duk abinda zai sameshi,abun takaicin kudi malamin yake sanya musu duk ran laraba,kowa sai ya kawo wadan nan kudaden,idan kuma ba haka ba,zai ma yaro duka mai tsananin da zai gwammace koma ta yayane ya samo ya kawo masa,to shi kusan duk sati sai an dakeshi,saboda baya iya kawo komai,don yace bazai iya yadda sauran sukeyi ba,don cikinsu harda masu sata don kawai su kawo,lamarin ya dagamin hankali,na daukeshi na maidashi gaban malamin,duk da inajin tausayinsa,amma babu gatan da xanyi masa da ya wuce hakan,saidai abun mamaki abun takaici kuma abun haushi,sanda naje ga malamin,tunda ya tambayi waye ni ya fara yimin wani kallo,nasa ma’anar kallon,tunda sarai nasan waye malam dan lami,yana daga cikin masu adawa da tsarina,amma ni hakan bai dameni ba,burina da fatana shine kowa ya gyara,tun kafin nakai ga cewa komai ya soma dakawa lamin tsawa,tare da jifansa da miyagun sunaye da kuma kalamai,ya kuma fara hanqoran neman manya cikin dalibansa su dauke lamin su saka masa shi a mari,abinda bai jima da fita daga ciki ba,a nan na nuna masa nima ainihin xafina,na hana kowa yaxo wajen ya taba yaron,a nan malam dan lami ya tada husumar cewa dalibinsa ne,kuma babu wanda ya isa ya hanashi yi masa duk hukuncin da yaga dama,tunda a hannunsa aka danqashi,indai kuwa bazai hukunta laminu ba,saidai yabar masa makarantarsa,ya koreshi,ya kori yaron ba tare daya tsaya yaji meye zance ba,bai tsaya yaji me yaron shima zaice ba,bai kuma sanar da magabatansa ba bare susan ina yaronsu ya koma”

 

“Na fuskanci tijara yake ji,don haka bance komai ba na tattaro al’aminu,na wuce dashi chemist saboda yanayin ciwuka da raunin dake jikinsa na tabon bulalai da duka da kuma mari daya dade a qafarsa ya zame masa ciwo. A hanya nake tambayarsa wayeshi da kuma qauyensu,ya shaidamin shi din dan birnin kudu ne,mahaifiyarsa ta jima da rasuwa tun yana qarami,yayarsa da ita ta riqeshi har zuwa sanda ya tasa,mijin yayar yace bazai iya daukar nauyinsa ba saboda shima bashi da komai,yayarsa bata da yadda zata riqeshi saboda shi da itan duka marayu ne,hakan ya sanya mijin yayar ya kawoshi bara,ya damqa shi a hannun malam dan lami,tunda kuma ya tafi bai waiwayoshi ba,duk da cewa bai wani jima a makarantar ba,azaba ba wacce bai gani a waie malamin ba,don kusan karatun ma dana tuntuba ba wani mai yawa bane,azabar da suke sha tafi karatun yawa,wanna dalilin ya sanya na yanke shawarar kawoshi makarantata yayi karatu,zuwa sanda zai warware kuma mu nemi ita ‘yar uwar tasa ko mijinta mu gaya masa inda yake a yanzu”.

 

Kai inna ta gyada idanunta na kan lamin,zuciyarta cike da tausayinsa,tunda malam yake kawo almajirai bata taba ganin yaron da taji ya kwanta mata ba kamar lamin din,a dan awannin da yayi dasu wanda bai wuce awa daya da rabi ba,ta fuskanci nutsuwar dake tattare da yaron,komai nashi a hankali yakeyi cikin nutsuwa

 

“Allah ya rufa asiri,ya gyara mana xukatanmu” shine abinda inna ta fada,suka kuma fara rayuwa da lamin din,wanda cikin kwanaki biyu ya sake da sadiqu,wani irin sabo sukayi sosai dashi,saika zaci sun dade tare.

 

Tun farko dama aminu din bai soma kwana cikin almajirai ba,cikin dakin saddiqu suke kwana,hakanan hatta da suttura ta saddiqun yake sanyawa,kafin daga bisani malam ya bayar da kudi inna ta samo musu gwanjo masu kyau shida saddiq din,sosai sadiq ke murnar samun dan uwa,lokaci kadan lamin ya shiga jiki da zukatan su inna,saboda yarone haziqi,duk wani aiki da saddiq keyiwa inna da malam alamin din ya daukeshi,sai malam da inna na hanashi suna raba musu kowa ya dauki nasa.

 

Kusan tare sukayi rainon iman da inna,idan inna tana aiki tofa iman tana hannunsa,yayita tiri tiri da ita kenan,tun tana masa qyuya har ya zamana duk cikin gidan babu wanda take yarda dashi Kamar yadda take yarda da alamin,wani lokaci idan aiki ya kacamema innan idan ya dauki iman sai tayi da gaske ta korashi makaranta sannan zai tafi,sannu a hankali sai sabo da shaquwa suka shiga tsakaninsu,baya son kukanta,baya son abinda zai taba iman din,da a daki iman din gwara a dakeshi,koda malam ya sanyasu makaranta sai ya zamana sai ya fara kai iman sannan shi zai wuce,koda kuwa shi xaya makara,kudin break dinsa kuwa badai yaci a cikinsa ba,komai ya gani shi zai kwasowa iman din ya kawo mata,idan kaga yadda yake matan sai ka rantse da Allah ciki daya suka fito.

 

Kamanni ne kawai zasu tona asiri,saboda kowa a cikinsu kamanninsa daban,hasken fata ne kawai ya hadasu,tun iman na qarama ta fita daban,tana da kyan fuska qwarai da kuma yalwar suma,wadda ta gajeta daga wajen inna.

 

‘yar lele iman take a wajen alamin tun tana da qananun shekaru,zai iya hana cikinsa ya bata,duk abinda tace tana so to matuqar yana dashi sai ya bata,idan babu kuwa zai nema mata,abinda yasa ya tashi kenan da zuciyar nema,zama da madaukin kanwa inji hausawa sukace shike kawo farin kai,tun saddiqu bashi da ra’ayi har zama da lamin ya sanya ya zama mai neman na kanshi kamar alamin din.

 

Kusan duk kudin daya samu wajen nemansa fiye da rabinsa siyawa iman wannan ne siya mata wancan,tun bata isa ado ba yake mata siyayyar kayan kwalliya da qyale qyale,tun malam da inna na fada,har suka fahimci a jininsa yake kulawa da iman,bazai iya dainawa ba,dole suka haqura suka sanya masa idanu,saidai innan tayi masa fada da kuma dabarar ya dinga aje wani abu saboda yayarsa,wadda a yanzu shekaru ke sake jaa nauyi na dada hawa kanta,tana kuma da buqatar taimako ko yaya ne.

 

Alamin shine kewa iman komai,itama duk abinda take da buqata alamin din take durafafa kanta tsaye,bata ko kallon sadiqu dan uwanta,saboda yana da zafi shi din,hakanan yanzu yanzu ba wani abu bane yakai mata bugu idan tayi ba dai dai ba,sabanin alamin…..wanda bashi da daukan zafi a kanta,hasalima yana tare duk wani abu da yasan xai bata ranta ko ya cutar da ita,idan tayi ba dai dai ba cikin ruwan sanyi zai nusasheta ya kuma gyara mata,tana kuma daukan maganarsa fiye data kowa cikin gidan.

 

 

Dinki dashi lamin yafi qwarewa,ya iya dinkin mata kamar masifa,har zuwa yanzu da yake kan shekara ta kusan goma sha shida,wannan yasa iman dake da shekaru goma sha daya cikin rayuwarta tun a sannan ta zama abun kallo,indai tayi kwalliya kowa sai ya yaba,tana da kyau sannan kuma alamin din yana fitar da ita da dinkuna sai kace wata qatuwar budurwa,don idan kaga dinkunan da take sanyawa saika tambaya waye yayi mata,sau tari idan yayi dinkuna ya samu kudi sosai,yakan je kasuwa ba tare daya gayawa kowa ba,ya samo mata atamfa falle bibbiyu masu sauqin kudi ya mata skert da riguna tsala tsala,saboda bata iya daura zani ba har yanzu,abinda yake hadata da inna kenan,kullum fama take amma har yanzu iman din bata iya ba,koda yaushe saidai ayi mata riga da skert ko kuma doguwar riga.

 

Idan kaga iman din saika dauka diyar wani ce,saboda bata rasa komai ba,kullum tsaf zaka ganta cikin suturu masu kyau.

 

 

Amin Abubakar haifaffen garin birnin kudu ne dake jahar jigawa,bafulatani ne uwa da uba,abinda yasa ya gaji kyau kenan shima tun quruciyarsa,tun shekarunsa basu fara nuna ba,yaro ne da tun a halittarsa Alla ya masa baiwa masu tarin yawa,yana da nutsuwa qwarai da gaske wadda ta hade masa da miskilanci,miskilancin da tun zamanin quruciya ya sanya ba kasafai zaka ganshi cikin wasanni irin na yara ba,yafi ganewa yana zaune daga gefe yana kallonsu,idan abu ya burgeshi ya saki murmushi kawai.

 

Kafin rasuwar mahaifiyarsa ya samu tarbiyya qwarai daga wajenta,wannan tasa ya zama wani na daban,idan yana wasu abubuwan saika dauka wani babba ne me shekaru.

 

Yadda malam da kuma inna suka riqeshi abune da bazai manta dashi kafatanin rayuwarsa ba,sun masa wani gini sun kuma zame masa garkuwa kuma ginshiqi cikin rayuwarsu,ya fahimci daga inna sadiq da kuma malam dukkaninsu suna qaunar iman,suna dannewa ne saboda yanayi irin na tarbiyya,shi kuma baiga abinda zaiyi ya faranta musu ba fiye da kula da abinda sukeso,hakan yasa ya sanyawa kansa bawa iman din dukkan kulawa,sannu sannu kuma sabo da shaquwa suka shiga tsakaninsu.

 

Wani lokaci har mantawa yakeyi,yakan kallo iman din a matsayin ‘yar uwarsa ta jini,har sai idan wani abun ya gitta da zai sanya ya tuna cewa ba jininsa bace.

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment