Littafan Hausa Novels

Kishiyar Kabila Hausa Novel Complete

Sirrin mata
Written by Hausa_Novels

Kishiyar Kabila Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

KISHIYAR ƘABILAH

 

 

 

_BY SURAYYAHMS._

Wattpad@Surayyahms.

 

 

_®Any resembelence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence._

 

 

Bi-ismillah..

 

Episode 1️⃣

 

 

A hankali yake kai desert din dake gabansa ixuwa bakinsa kansa a sunkuye yana dan murmushin nan nasa mai kyau da ya kai ga har ana iya ganin lotsawar dimples dinsa.

 

Acikin sigar nitsuwa da kamala sosai yake xaune jikinshi sanye da wata petite cambridge grey colour zegner french suit dinsa datamai kyau ajikin shi bana wasa ba.

Sweet 22 Hausa Novel Complete

Sassanyar muryan mahaifyarsa ne yake ratsa shi,ahnkli ya dan girgixa kai snn ya dago lumsashun idanunwansa yana kallon dattijiyar matar dake Zaune akan kujerar dake kallon nasa fuskarta a daure takafa masa ido tana kallonsa, “murmushi yakuma yi mai sauti xai yi magana ta rigasayi a fusace tace “ohhhh,ni ce ma na xama abun dariyarka yau ko Ahmad? Maganan yarinyar nan kafayat fa nake maka but ure busy smilling at me kamar wani abun arxiki nace ka aikata mata..arent u ashame? Yadda ta karashe a fusace yasa shi kara sakin murmushi wanda ya dada tunxirata,

muryanta cike da fusata tace “ohhhhhh wato ga mahaukaciya nan na maka ihu ko,Ahmed are u out of ur mind?..

 

Babu shiri ya dan marairaice fuska snn ya ajiye fork din hannun sa da murynsa mai taushi da dadi kasa kasa yace pls calm down, i am really sorry maa, wallh ba haka bane Mamee,ni nama isa in maidaki mahaukaciya ne? ai naji me kikace akanta, toh ni wallh bansan ranta ya baci ba ma saida kika fada ynx,toh wai meye nata na yin fushi ne dan ban tsaya a wajen birthday partyn ta ba sai kace wani ni saurayinta ne? Wani ruwan Takaici ne taji ya shake mata makwogoro daya furta hakan.

 

tsimewa tay bata ko kulashi ba dan tasan ranta ne kawai xai kara baci inta tsaya yin masa wani bayani, baki bude take kallonsa acikin yanayin mmkin halin basarwa irin nasa yo ace duk wani walakanci da cin fuskan dayay ma yarinyar nan agidan nan shibaima san yana yi ba..

 

Kyabe bakinta tayi tanamai karkada kafafunta aranta tana jin tsananin takaicinshi ayayinda take tuno da irin baqar wahalar da kafayat din tasha agidan nasu kwana biun nan, wani irin sihirtaccyar ajiyar xuciya mai nauyi ta sauƙe cos Kafayat whud have been the perfect doter inlaw and a responsible wife for her son Ahmad domin yarinyar nan itace ta san shi tun suna yan kanana tun basu san kansu ba suke abota.

 

Gashi tun xuwanta Nysc take xama dasu agidan dan sabida tana kulawa da su na musmn sabida son Ahmed din datakeyi aranta duba da shine first love dinta, hatta mahaifin sa ya bala’in amincewa da kwaxo da kuma halayyar kirki irin na kafaya,gata nan masha Allah black beauty omo yoruba, gaba da baya full option,gata da tsafta, ga son shara, ga iya wanki da guga, ga iya wanke wanke,uwa uba ga iya girki,ga kuma ladabi da biyayya,duk tayi musu luguden hidima agidan sabida shi amma waishi baima gani ba.

 

Acikin sassauto da muryansa kasa kasa sigar lallami yana kallon yanayinta yace iyami”,my mamee, harararsa tayi tun bai fara mata dadin bakin ba, yace “toh kiyi hakuri mana mama naa inadai kafayat buraimo ne?i promise i will apologise for ur sake! kikace wai dan naki attending birthday din da kuka hada ne yasa tayi fushi ta bar gidan nan ko? Lumshe ido tay dan harynxu mamki yake bata ganin cewa baima san lefin daya aikata ba, Girarsa ya dage sama ahankli, da har dai xaice “She is soo silly” sai kuma ya kumshe sauran maganan abakinsa yy shiru,dauke kan datayi yasa ya dan shafa kansa da yanayin damuwa a muryansa yace “mamee pls now, kidena fushin nan mana nide nasan damuwarki bai wuce kice xancen relashp dina da kafayat ba,i told u i need time..kuma aikinsan komai fa lkci ne, AUREN nan xanyishi in lkci na yayi,kawai su Dad sun kasa gane hkn ne kema kika bi bayan su,sun ki fahimtar abinda nake nufi batun auren nan,i swear im still searching for a good nd decent wife just for u,kuma nasan idan lkci na yy na aure xan kawo muku matar Aurena ko ba kafayat ba,am just bored of all dis match making da kuke min. Kubari mana uhmm iyami?..

 

Ta cigaba da kallonsa rai bace batace mai uffan ba,shafa kansa ya kuma yi har lkcn fuskar sa na dauke da damuwar yanayinta dan sosai ya tsani yanaganin bacin ranta,saidai shikansa baisan mesa suka saka kafayat aransu hr haka ba, sallamar da aka yi ne yasa duka suka maida hankalin su ixuwa ga bakin kofar tare da amsa sallamar baki daya.

 

Mikewa tayi ganin yan uwan mijinta ne suka shigo su subiyu, Anty temi (ramotou) da anty (moslimat) Mojushola,da wata kyakyayar budurwa mai suna maryam wacce kallo daya kamata ya ishi kasan bahaushiya ce,da fara’arta ta tarbesu tana masu sannu da zuwa basu wani tanka ta sosai ba suka karaso cikin falon aka shiga gaggaisawa sama sama dan duk hnklinsu da nitsuwarsu nakan dan saurayin ne.

 

A cikin nitsuwa ya rusuna ya gaishe su snn ya mike tsaye yanamai kallon mahaifyar tasa, adan gaggauce yace “mamee ni xan wuce sai na dawo ko xuwa gobe”..kafin ta amsashi har Anty Temin tay sauri ta amshe xancen cikin sautin babban muryanta na giant woman, fuskan ta babu alaman fara’a tace “oshey Damilare, wat do u mean by dat statement? _Ahhh dami, iwọ ko si oju iberu ti o ni ibanujẹ?_ (ahhh dami,u no dey fear face?)..Daga xuwan mu ne sai kace gobene xaka dawo? but Dats not fair oo,ta kalle babban dadan su da batace uffan ba cikin bambami ta karashe xancen fuskarta a daure “Ahhh see Shildren of now adays,kadai dawo xuwa anjima kar kakai daddare dan bamu gama magana dakei ba, tana maganan tana kallon cikin kwayar idanunsa suna hade ido sai ta kalle budurwan data sunkuyar dakai kasa da alaman ta fahimtar dashi abunda suke nufi, ahnkli yyi murmushi yace its okay “toh in’ sha Allah xan dawo anty rahama.

 

Shiru tayi batace mai uffan ba sabida she love them to be adressing each oda da sunayen yaren su amma sam shi bayaji, shiyasa ma ita sam bata kiransa da Ahmad aganinta sunan hausawa ne irin na maman sa, sudei a fannin uba saidai sucemai “DAMILARE ” ko “DAMI” KO “LANRE” sabida sunan nasa inkiyar sunan baban mamansu ne so they respect dat name alot.

 

duk maganan nan da ake Anty mojushola batace musu uffan ba banda cika iska da hura hanci da yatsine datake bin su dashi, dan itadin ta manyanta sosai dan itace first female child da mahaifinsa yake bi,sai uncle dinsa bakare,anty temi (ramotou) kuma itace autarsu.

 

Bayan sunyi hakan sai yyi musu sallama ya fice daga falon yana kallon agogon hannunsa daga nan yanajin anties dinsan sunakan watsa habaici wa mahaifiyarsa na cewa tunda yaki auren mace daga kabilarsu aiga nan bahaushiya sun kawo masa daga nata irin kabilar, sam dangin mahaifinsa basa da sauki,they just love to be in control of evrthing. A farko ma sunedai suka soma cusawa kafayat ra’ayin xama agidan iyayensa dan tana musu bauta,so during her nysc session sai ta xo just to get his attention ayi aure, dukkan dangin ubanshi suna matukar son ace kafayat ce ta auri Ahmed just for the simple fact that itama kabilar su ce na yoruba.

 

gun motarsa ya nufa da sauri yana tafe yanamai kallon agogon hannunsa acikin gaggawa ya buɗe ya shiga ciki ya kunnata da sauri yabar harabar gidan nasu.

 

Ahankli yake tukin aransa yanata tunanin yadda xai kawo karshen wann matsalar data kunno masa kai acikin familyn sa musammn na yadda kowa yake son yaga lallai ya aurar dashi acikin gaggawa..

 

 

After some few hrs…

 

 

_National communicable disease control Theathre hall maitama Abuja._

_5.56PM_

 

 

Manyan likitoci da public health professors ma’abota ilimi da wayewa da kuma kwarewa a bangaren yaƙi da yaɗuwar cututtuka ke shige da fice a babban hall din NCDC dake garin Abuja kowa da alaman fara’a akan fuskan sa.

 

Lectures din da suka yi yau was very interesting Dan Sai yanzu duka suka fahimci abinda minister of health na kasa yake nufi a lokacin da yake

ce musu the youngest professor dinsu AHMED BELLO JIMADA is the best and leading young epidemiologist da sukay employing acikin CCD project dinsu na wnn shekarar sabida yanada gwaxo sosai,snn yana bin komin sa ne a dalla-dalla cikin nuna ilimi da kamiya. And He makes sure He carries everybody along acikin kwarewarsa. Snn Yana making good references da abubuwan da yaje ya koyosu a kasashen waje yanamai kara budasu tareda yin gamsashen bayani akansu using simple terms wanda ko the most dummiest and stupidest person zai fahimce shi.

 

Yau yay musu electronic lectures ne akan manyan pandemic and prevalant diseases dake addaban iyakar boundaries na tsakanin kasa da kasa kamar su COVID19,i:e corona virus, Acquired immuno-deficiency syndrome(AIDS) da severe acute respiratory syndrome (SARS)da wasu ire iren viral flus.

 

Anan kowa ya kara fahimtar cewa shi mutum ne mai tsantsar nutsuwa da ilimi, komai nasa a hankali yake yinsa. He is very gentle bashi da hayaniya sam saidai daga ganinsa za ka iyasanin cewa yana mugun ji dakansa sabida wani irin tsantsar self assurance da kuma zazzafan self confidence dayake nunawa ayanayin sa musammn in yana fidda bayanansa acikin kwarewa da ilimi daya gama ratsashi.

 

 

Wajajen karfe biyar ya wuce suka kammala lectures din ya fito cikin takun nitsuwa jikinshi sanye da hadadden petite cambridge grey suit dinsa dayake wani irin fallasa tsantsar burgewan dake tafe da karancin shekarunsa dan matsakaicin 32-33yrs da haihuwa as one of the current youngest leading professors and doctor of epidermiological science a Abuja.

 

Prof.Dr Ahmed bello jimada kyakkwa fari ne amma ba fari can ba dan za’a iya kasa shi acikin light skin yoruba demons mai yanayin tsiririn hanci da fuskar uwarsa ta asalin fulanin garin illori..

 

Saidai kuma da akwai wnn kamannin da kuma zubi na Jinin mahaifinsa na cikakken bayarben oyo state msmn ayanayin ginanne kuma tsayayyen siffar jikinsa da kuma yanayinsa mai tsananin burgewa,yana da cikakken saje da dan matsakaicin gashin gemu da kuma fasalin kamala ta kyawawan mazajen arewa daya debo acikin jinin xuriar mahaifyarsa.

 

A matsayinsa na matashi mai ji da ilimin zamani da kuma wayewa da daukaka yasaka yake da karancin lokacin yin sabbin abokai bare kuma ajega yan mata,daga scndry schl har izuwa jami’an dayay baida sabbin abokai duk abokansa na yanzu tun na childhood dinsa ne.

 

iyakan aikinsa da karatunsa sune kawai agabansa cos he alwys believe serious girl friends and new friends to be a distraction to his career and success, shiyasa ko wani soyayyar arziki bai taɓa tsayawa wajen yi arayuwarsa ba saidai yayi soyyaya ta sharholiya na lkci kalilan.

 

In his life dan yay keeping companyn mace na kwana biyu ko yay tarayyar sati daya ba wani abu bane sanin cewa lokcin aikin sa nayi to shikenan soyayyar ya kare,shiyasa shi bai taɓa cewa yana son kowacce mace dagaske ba,saidai duk wacce taƙuso masa kai ta kawo kanta wajen shi zai iya bata lkcin shi na kwana biyu ko sati guda da ita daga nan in aikinsa ya tashi bazata kara ganin idonsa ba.

 

Mata dayawa har sunyi sun gaji sun hkura sun dena sakashi aran su sanin cewa inya gama da mace xai iyayin ma kamar bai taɓa ganinta arayuwrsa ba, halin sa yasaka mata dayawa ke muradinsa a matsayin miji cos he is really hard to get type,yana da high taste wajen xabar macen da xaiyi tarayya da ita,shi irin kalar maza ne da mata ke mutuwar son kasancewa da su sabida yana da sakkaken hannu kudinshi bai dame sa ba, saidai shi namijine da bai da saukin kai,ba asaka shi ba kuma hana shi,he alwys need to be pleased gashi da tsinannen shiga rai da iya nuna ko in kula da komi musmmn ma in amfaninsa ya kare agaresa.

 

mata dayawa daga nigeria har waje sunsha sako burin su akansa kodama zai tsaya ayi wata magana ta soyayya da aure amma haryau baida wann ranar bare kuma lokci,wasu sunyi sunyi tun yana 20s har sun gaji till he is 33yrs old now kuma babu abunda yanema ya rasa arayuwar sa, ilimi, kudi, kyau, gata, snn shine namiji daya talli kwal awajen mahaifyar sa mai suna hajiya khadijatu muhammad gidado wanda takasance cikakakkiyr bafulatana ce a garin kwara,jihar illori.

 

Ahmed yay karantunsa ne adan kankanin shakeru sabida irin kyakkyawan kulawar dayasamu arayuwarsa yayunsa uku da suke uba daya uwa daban daban duk sun girme shi nesa ba kusa ba kuma kowannen su yana kulawa dashi sosai.

 

mahaifinsa Alhaji Bello Ayodeji jimada,bayarbe ne daga garin oyo,jihar ibadan, shi kabilar yoruba ne da sukayi xaman cirani da lumana tare da fulanin garin illorin,a sanadiyar rasuwar matarsa na fari wato alhaja simiat laide ne ya auro matarsa na biyun bafulatana wato hajiya khadijatu muhammad gidado wanda itace ta rike masa sauran yayansa.

 

Babban dansa shine Kazeem wanda ake cewa Aremu (Qasimou) sai mabiyinsa hamzat Dimeji (hamusé) da kuma ta mace wato Zainab moturayo (senap) kafin nan Ahmed(Damilare)

 

Ahmed shine dan Autan gidan nasu,ya kammala first degree dinsa ne a can obafemi awolowo university ta ibadan oyo state garin mahaifinsa while he is 21yrs,yay masters dinsa a kasar waje acan United kingdom for 12month afannin CCD(control of communicable disease)

Sauran kuma ya karasa a university of manchester wanda sabida gwaxonsa ne yasa he became the youngest professor of comuncble disease at age of 31, bayan ya kammala karatunsa 2yrs ago ne yafarajin kamar is high time yafara enjoying life dinsa.

 

saidai wani hanxari ba gudu ba, his family only desperately wanted him to get married akan lokci sabida Xpectations dinsu kenan akan duk wanda ya kammala karatun sa ya kuma samu dukan wani achievement dinsa na rayuwa sabida su kare mutuncin yayansu dana xuriarsu daga haifo yayan shegu awaje.

 

saidai shi har yanzu shi bai da wata tsayayyar budurwa bare ajega matar aure dan baisan yama za’ayi ya fara soyayya ba bare aure snn har acikin xuciyrsa in akwai abunda ya rantse baxai amince ya yarje akansa ba shine auren hadi..

 

SHIN KO YA XA’AYI AHMED YA KAWO MUSU MATAR AURE?

 

#SURAYYAHMS grp

08060712446 chat only no calls.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment