Kishiya a Yau Hausa Novel Complete
🌈(KISHIYA A
YAU)🌈
*PART *
1
(TURE LIFE STORY)
Na
LUBABATU MAI CHANJI
hajiya Haneefah ce zaune adakinta dake saman bene tana karatun alkur’ani bayan ta idar da sallar walha kamar jiya yauma hayaniya takeji yau harda kuka daga makwaftanta ne take jiyowa kasancewar tagar bedroom dinta dake saman bene tana sauraren hayaniyar duk dake tashi agidan makwaftan nata saidai Bata fahimtar meke faruwa,Dan haka saitacigaba da karatunta,zuwa can Kuma sai ta runka jiyo sautin Yana kara karfi dole taruke alkur’ani bayan tayi sheda tamike da sauri tanufi kofa,hartagama saukowa daga matattakalar Bata lura da mutum a palour ba, saidai taji magana ummy lafiya? da sauri tawaiga saifudeen ne,zaune saman darning Yana break,tace masa inazuwa, malam iro ta kwalawa maigadinta kira, alokacin Yana bakin get Yana sauraren redio,dasauri ya iso yafara gaisheta tace mlm iro lafiya yau makwaftan mu? Yace eh to wallahi hajiya nima dai bangane Mike faruwa ba Amma dai komeye dai bamai dadibane domin kuwa tundaga jiya bayan magaruba nafara jin hayaniyar,yau Kuma akawayi gari da ita,ko adubo ne haj,,,,,,,,,,,,,,
Nata Matar Aljan Hausa Novel Complete
maganars tamakale sakamakon bugun kofar da akayi da sauri ya waiwaya, sai yaga yarinya dagudu ta nufosu tana fadin ku taimaka mani,da sauri hajiyar tatarbota ganin tana layi kamar wadda Tasha kayan maye hijabinta jirkice fuska tayimata suntum kafar ta ba ko takalma,tana zuwa kusa da ita sai tayi kasa asome,cikin karaji hajiya ke ambaton sunan Allah,San nan tshiga Kiran Deeny,da sauri yanufo wajanta yqnafadin ummy lafiya meke faruwa?tace koma ciki kadauko kayan aikinka kafara Bata taimakon gaggawa dagudu shima yajuya ganin abinda ke faruwa,Koda yazo hajiya tadan gyara mata hijabinta San nan yashiga auna numfashin ta yace ummy Danshafa mata ruwa afuskarta ahankali ko taja ajiyar zuciya tafara motsa idanunta harta budesu ahankali duk da snyi mitsi mitsi alamar tadade tana kukan,hjy tace alhamdulillah tashi kinji mushiga cikin gida,tadan girgixa Kai ahankali murya Bata kofita sosai tace yace kada na kuskura nazauna ako ina naje nashiga duniya hajiya kibarni natafi kawai su Abba sundaina sona,,,,,
takara fashewa dawani sabon kukan hjy tace to shiya koreki nikuma nace kitaho gidana, gidana kuwa aiba gidan sabane, tashi muje kinji, ahankali takamata ta mikar da ita mlm iro da Deeny sai duban tausayi suke mata, Dan sunsan ba karamin abubane yafaru,da itaba Dan kuwa yaran gidansu suna da tarbiya sosai,ganin sunnufi cikin gida malam iro yakoma bakin aikinsa yanafadin Allah yakyauta, Deeny ma abinda yafada kenan Yana jinjina abin aransa,Koda suka shiga ciki dakin hjy dake sama cantawuce da ita takaita harbaki toilet tashiga da ita harciki domin kuwa taji jikinta haryanzu baidaina rawaba tashiga tahadamata ruwan gumi masu Dan zafi tace kishiga kigargasa jikin ki kinji tadan gyada kanta, tafuto tajamata kofar palour tanufo tashiga buda kayan break din dake zube darning tahada mata tea maikauri da kwai da dankali sai soyayyar agada,taloda atire ta nufi sama dashi,data shiga saita samu wani Dan table tadora tiren sama tabude wadurop dinta tazakulo wata doguwar riga marar nauhi mai yankakken hannu hade da dankwalinta ta aje ta bakin gado,San nan tadan zauna nadan mintoci,
hardai tamike tasake komawa tadan kwankwasa toilet din tace mekike ne?San nan taji alamun motsin ruwan San nan tadawo ta dauki wan nan rigar dakoma tadan kwankwasa tace anshi ga riganan kicanza ta jikinki ki Kuma dauro alwallah kafin kufito,tabude kyauren toilet din Tamika hannu ta anshi rigar harda godiya, tafuto bayan tagama, hajiya ta nuna mata waje tace zauna anan domin kuwa alamu sunnuna bayan damuwa harda yunwa kedawainiya dake,sallah kuwa natsuwa takeso Dan haka yi sauri kicinye plet din nan tas,tadago Kai tadubi hjyr tace eh hakanake nufi, ahankali ta dauki cup din tea din tafara kurba guminsa yafara ratsamata uwar hanji tadan dakata,San nan tacigaba da kurba hajiya tasake tura mata plet din dankalin tace hada da wan nan cikin yafiyi maki nauhi, ahankali tasa supoon tana Dan tsakura ahankali,hajiya tayi shiru tana kallan ta tana aiyyana abubuwa da yawa acikin zuciyarta,ganin tana ture plet yasa ta kalleta tace harkinyi mene? ahankali tace hjy nakoshi nagode Allah yasaka da alkhairi,daga nan hajiyar Bata tursasataba Dan tasan damuwa Bata barinma kaji yunwar hakanma tayi kokari,tace to RAHAMA tashi kigabatar da sallah ko raka’a biyu ce daniyar Allah yayi maki maganin damuwar da yajarabceki da ita domin kuwa ita kanta damuwar ibadace jarabawa ce Allah keyiwa bayinsa domin yagwada karfin imanin mummini,
ahankali ta Mike domin zuwa inda taga dardumar sallah alamun nanne wajan bautar hajiyar,daga nan hajiya tahada kayan tayo kasa dasu zuwa palour ba kowa sai tv daketa aiki ita kadai tasan tunda bataga Deeny ba yaje yayi sallar walha, Dan haka saita hada sauran kayan break din dama bawani dayawa takeyiba dai dai su take masu saiko maigadinta datake Mika mawa Koda yarage dai baida ywa batada son almubazaranci, palour tas yake sai kawai tadan kunna masa bouner kasancewar ta mace mai son kamshi,tajuya zuwa sama,Koda tashiga tatarar da ita hannu sama tana kaiwa Allah kukanta, hjy ta jinjina Kai,abin zuciyarta yafuto fili Bata saniba fadi take yah Allah kadauki Raina inhut,,,,,,,,,,,,
wata tsawa hajiyar tayi mata saida tarazanata Dan bataji shigo wartaba,tace inadalili idan yadauki rannaki mikika tanazar wacan din daharkike tunanin damuwar duniya tafi ta kiyama sauki ,ina iliminki yake na islama,ya ubangijin mu yace Mana (INNA MAAL USURIN YUSURAH)bayan tsanani akwai sauki aduniya ne kike fita da kunci alokacin da Allah yaye maki aduniyar nan Babu abinda ke tabbata walau dadi walau wuya,ashe kuwa idan Allah yajarabci bawansa yadace yadaina saurin yanke kauna domin kuwa sauki na nan tafe,alahira canne matabbata take,Dan haka maza kitubarwa Allah,kicigaba da neman daukinsa yanajinki Yana ganinki ki rufe dakaranta suratul yasin tana yaye damuwa, bayan kin idar Kuma inason ganin ki kisameni palour,tajuya zuwa kasa tana ta Al ajabin wan nan Lamari to mi yayi zafih?Kai Allah yakayauta ta fadi tana sauka zuwa palour saida ta canza tashar TV din San nan ta zauna tana jancarbin hannunta………
Daga taskar Yar gidan Mai chanji
🌈 KISHIYA A YAU 🌈
PART
2
Na
LUBABATU MAI CHANJI
Tukwici ne ga Mai gida Ran gida Alh Aminu jabulus Allah ya Kara taimakon ka a ko yaushe Kuma ko Ina
ADDU A ne ga mahaifi na Alh Ali Mai canji mannar gangare Ubangiji ya yi maka Rahama da gafara da dukkan Al Ummar musulmi da suka Rigaye mu Gidan gaskiya
🌈
………..Koda RAHAMA tagama ibadarta saitajita sakau kamar an yaye mata duk wani dabaibayin da yayiwa zuciyarta da sassan jikinta, ahankali ta shafa fatiha adukkan jikinta taiwa Allah godiya San nan tamike tsaye tashiga tattara ma hajiyar dakin duk da hajiyar macece maitsafta komi nata tsaf Amma saida tadan yi mata gyara Sannan taja mata kofar dakin tabiyo matattakalar benen ahankali tana saukowa motsinta yasa hajiyar tadago Kai tana kallan ta harta iso inda take zaune hajiya tafadada murmushinta tanayiwa Allah tasbihi tace sannu da hutawa hajiya, cikin murmushi tace Masha Allah rahama ke keda sannu,
rahama Tamika mata hannu tace zauna anan, ahankali rahama ta isa kusa da ita kanta akasa tana Dan murmushi sai tazauna dai dai kafafuwanta maimakon inda tanuna mata saboda girmamawa, hajiyar tadafa kanta tace Allah yayi maki albarka rahama idan Babu damuwa inaso inji meye damuwar ki,Kuma Dan Allah adaure arunka sama zuciya salama ayau rayuwa saboda karancin lafiya da sukuni ba komi yadace kabari Yana wahalar da rayuwar muba komi yai tsanani kabarwa Allah nasan ita damuwa ita keyin kanta to Amma abinda yadace idan tazo maka yi kokari kayaketa da karfin ikon Allah domin kuwa shiyasaki ciki Kuma yanajinki yanaganin ki Kuma Yana daga cikin soyayyar mahaliccinki gwada imanin mutum idan kina ikirarin kina da imani to akullum ko kina cikin jarabawar ubngj harta kaiga ta zame maki jiki, ahankali nasihar hjiya nashigarta natsuwa nakara shigarta domin kuwa tunda tashiga wan nan hali Babu Wanda yataba zama yayi mata nasiha kwatan kwacin haka,tasa hannu tashare hawayen dasuke gangaro mata asaman fuska, taja hancinta tace hajiya Babu abinda zamfara cewa face godiya ga Allah dayajeho ni gareki nayi imani da cewa Allah yanatare Dani tunda yau kusan wata daya kenan dafara shigata wannan hali tun inajuriya inarokon Allah hartakai nafara sarewa hajiya nafara gayama ummana Amma Babu wani abu datace Dani face intai inyi hakuri inzan iya hartakai zuciya ta tafara yi mun huduba da kururuwa akan inbi hanyar da Bata bullewa wato inje inkai Lamarin ga malamai,Amma ayau nakara godewa Allah Kuma insha Allah hajiya yanzu zangaya maki damuwata nayi Kuma imani ga Allah zansamu mafutar Dana ke tanema,,,,,,,,
Wacece Rahama?
hajiya sunana rahamatu kamaryanda kika sani iyayena da kowa nawa kinsani hajiya agabanku akahaifeni kedin uwace agareni ,hajiya tagyda kai,tace hajiya ayau shekarata shidda da aure mijina muhamud munyi auren soyayya Kuma muna zaman jindadi da kwanciyar hankali aynzu muna da yaranmu biyu Al’meen da meenat mungina raywarmu mai kyau gidanmu cike yake da so da kauna aduk inda mijina yake tunanin mu nida yarana shine atare dashi hakan yake garemu nida yarana, inada kawaye saidai nidin bancika kwashe kwashen kawayeba saboda yanda zamanin mu yakoma,Amma duk da hakan hajiya yau nawayi gari mijina Babu kowa agabansa face kawata tsakanina da shi sai kyara sai hantara,,,,,anan kuka yaci karfinta yanda taji wani katon gululun bakincikin datafara binnewa ayau yamotsa hajiya Bata tsidataba domin kuwa itama wan nan labarin yatabo mata wani gyambo datayi fama dashi ashekarun baya Wanda itama tsananin rokon Allah da Kuma sauran Shan ruwanta agaba kila da yanzu babi ita, da yanzu yaranta sunzama marayu, ahankali tashiga ambaton Allah domin kuwa ta tsani duk wani abinda zaisanya ta tunano kuncin da tashiga ashekarun baya, ahankali abin yalafa mata taja doguwar ajiyar zuciya,itama rahama haryanzu kukan take nazucci hajiya tadafa kanta tanadan girgixa wa alamar tayi shiru,
Sannan tadan gyra miryarta tace rahama to keda baki da kawaye a’ina ne mijinki yaga kwartaki?rahama tace ummy Dan Allah kifahimceni narasa yanda zanyi mutane su fahimci ba kishine ke damuna ba ayau bakincikina wadda zai aura ban isa inhansa aureba Amma ummy nace yayi hakuri yacanza wata,ummy tace Babu Wanda zai fahimceki ko idanba Wanda yataba dandana irin gubarba,harshi uban gyaiyar wato mijinki, abinda maza suka kasa fahimta irin wan nan auren wallahi Babu abinda yake jawowa sai tashin hankali daga farkonsa harkarshensa domin kuwa naji ire iren auren nan dayawa Amma wallahi kadan ne naji ansamu kwanciyar hankali acikinsa su aganinsu auren wadda kika sani ko yimaki kishiya da kwarki zai kawo masu kwanciyar hankali harkiji suna ikirarin kinsan halinta tasan naki, uhum wan nan bahaka bane,domin kuwa wadda duk ta amsa sunan kawarki ce to yadace tatayaki jinciwon abinda ke maki ciwo,Amma inayiwa daywa mazan dasuka samu kansu da irin wan nan auren uzuri ,saboda dayawa matan yanzu babu Allah acikin Lamarin su sai anzauna tare dake ansan komi nagidan aurenki kafin asan ta inda zaa cafko wuyan mijinki,kiyi tunani mai zurfi kigani ayau in mijinki baida shi ba kowace kawa ma tadamu dakeba Amma idan yanadashi akagani ajikinki da jikin yqranki to kowama sonki yake inkinje gidan biki wata baki santaba dataga suturar jikinki to tafara rawar kafa wajan son yin kawance dake,kisani ayau matan aurema suna bin mijin kawa indai yanadashi abinne saidai muce (innalilahi wainna ilaihirrajiun) rahama tayi tagumi tana kallan hajiya tana mamakin yanda tafahimci Lamarin mazan yau, tace cigaba rahama,taja ajiyar zuciya tacigaba ummy akwai kawayan mu namakaranta duk idan wata ta haihu daga cikin mu ana haduwa aita zumunci har anahada ma wadda ta haihu 1k amatsayin taimakon juna,
inbiki zakiyi Kuma 2k akwai uwar kungiya maana wadda akanada akan tarunka hada kudaden inhaihuwace to da kinhaihu insha Allah kafin suna anhada haka inbikine,mufida Usman itace mai hadawa ni Kuma muna kawance da ita sosai asanda muna school saidai ita haryanzu batayi aureba har biki ansanya mata dai Allah baiyiba,ayau duk yanda kake da mutum baka shaidarsa Dan haka bazan iyacewa ga yanda mufida takeba haduwar makaranta ce ko amakaranta ita tanuna tanayi Dani nima nake kulata Kuma dayake mahaifinmu bamai San yawace yawace bane bamu zuwa yawan bingidajan kwaye yanzu nema nake muamula da kawayenmu tunda duk yawancin mu muna dakunan mazajanmu,ayanzu kuwa yawan haduwar da akeyi wajan hidimar yan’met yasanya mufida tadawo mun tun inadari dari da ita hartakai nasaki muna chat da ita akai akai bandai taba zuwa gidan iyayen taba,itama batacika zowa gidanaba intazo to sai dai ko in wata hidaimar tatashi intaimun waya tagaya mun inda kudi alokacin zance tabiyo ta anshi nawa in Kuma bakudi ahannuna zance nataho dasu ranar sunan, batasan mijinaba kasancewar sa dankasuwa ba mazaunin gida bane indai bayayi tafiya ba,suna zuwa garuruwa irinsu Legos da Abba wajan sawo yadin da ake hijab dasu inyafita da safe to sai yamma ko abincinsa akasuwa yake turo yaransa yakarbar masa,watarana maimunatu Umar tahaihu itama kawarmuce aranar munyi da abban meenat zaibiyo yadaukeni kasancewar dama duk inda zanje shi zaidaukoni,idan yadawo kasuwa sai yabiyo muwuce, to aranar munatsakiyar fira da kawaye kamar kada arabu ,sai naji karar ringing din wayana ko kafin infiddota ajikka Kiran yayanke,bandamuba dannasan ogane alamar yataho inzauna cikin shiri,Dan haka natashi daga inda nake nafiddo hijabina ajikka ina warwareta akabini da kallo ramlat bala tace to matar Dan kasuwa halan abban meenat ya iso shi sai anacikin fira maidadi sai kawai yadauke Mana ke,
fadar hakan datayi akayo mun cah ina dariya nace to yasanranku daga yabaku ni aro Kuma kummanta inyatafi tunsafe bamu Kara ganin junanmu sai kamar wan nan lokacin haba kawaye na kuyi Mana adalci Mana munyi missing din juna wlh,gaba daya aka dauki sowa irinta kawaye ,ramlat tace haka nakeso kawata wlh Kara himma mazan yau saida kula idan ba hakaba kuwa matan yau sunzama kamar kuraye wajan farautar mazan mutane akakara fashewa dadariya,nima nakarayi masu bankwana nabi kowaccensu mukayi musabiha tare dafatan alkhairi,nayo gaba duk abin nan da ake mufida nagefe tanata chat awayarta saidai tayi dariya intaji andara,har na aza kafata wajen get din naji anakirana nadan waiwaya nibankoba Kuma nibanfita wajeba gashi Kuma nahango motar abban meenat acan nesa kadan daga gidan sunan,mufida usman ce dagudu tace ga kayanki ashe banbakiba,nayi dariya nace ni wallahi nama manta kayan sunan ne lemune da ruwa da yajin jego da sitikar baby acikin Yar jakkka mai kyau nace to nagode Allah yaraya Muhammad,
Koda tabani saida tabiyo ni mukajero muna tafiya nadan kalleta nace wai kema harkigama sunan?tadan girgixa Kai tace nadai gaji ne dayawa shiyasa nace bari indantaka maki nace to,aeko inagodiya,muna isowa kusa da motar abban meenat nace to inagodiya my sister,nakama hannun motar zanbude saicewa tayi rowar ogan akemun ne ?
azuciyata naji wani abu kadan Amma dai nayi saurin kawar da shi,ina yar dariya nace ameye narowa saikace nama,tayi dariya tace aega alama wan nan ogannaki yafi nama,nayi dariya nace wan nan hakane my sister
,nadan leka kansa yanakallon wayarsa nace abban meenat ga kawata zaku gaisa,yayi Dan Jim yace kawarki Kuma,nadga masa gira,saiyayi murmushi yace okay muje my real,yadanfuto daga motar Amma baibar kusa da motarba ko marfin motarma bai sakiba daga nan yadaga mata hannu yace barka da yamma kawar real ykk,naji dadin hakan dayayi sainakai dubana gareta harda lanagabe Kai tace barka kadai mijin kawata yakake ya kasuwar? Yajuyo Yana kallona yace komi alhamdulillah,yace muna godiya sosai,ko kafin tace wani abu yakoma ciki nima nadaga mata hannu nace my sis munwuce itama tadaga mun hannu tanafadin bye kawata sai kinjini insha Allah nace okay Allah yakaimu muna fara tafiya nadan waiwayo wajansa nace my real one ya kasuwa,yadan ruke mun hannu yace my real kasuwa alhamdulillah na Dan matsa hannunsa nace Masha Allah ya kallan yadan yi murmushi tare da kashemun ido nima namayar masa da murtani
YAR GIDAN MAI CHANJI
[…] Kishiya a Yau Hausa Novel Complete […]
[…] Kishiya a Yau Hausa Novel Complete […]