Littafan Hausa Novels

Kibiyar Ajali Hausa Novel Complete

Zuciyar mutum
Written by Hausa_Novels

Kibiyar Ajali Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

Kibiyar Ajali Hausa Novel Complete

KIBIYAR AJALI…..!!!!*

_(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_

🏹👑👩‍❤️‍👨💝

 

 

*MALLAKAR:- NANA HAFSAT 🧕🏼*

*(MISS XOXO)*

 

 

*©️®️ZAFAFA 5: 2021*

 

 

BABI NA: 1

 

 

[1:1] بسم الله الرحمن الرحيم

 

In the name of Allah, the Gracious, the Merciful.

 

 

_*KAUYEN DURB’UN*_

 

 

“Mudi!Mudi! Mudikalle na dan albarka! Dan Allah duba waje ko zaka gano min keyar yarinyar nan tunda tafita siyo koko tun duhun safiya bata dawo ba har yanzu.. Oh ni salamatu wannan yarinya ko yar bankadaddiya. Fita ka nemo min ita na casata a gidan nan.”

 

Mudi dake goge hakoran sa da gawayi yaja dogon tsaki yana mai kuskure korayen hakoran sa da sukai tamkar gansa kuka, Kafin ya mike cikin mita ya dubi mahaifiyar tasa yana sakato kwanannan daskararren tasonan hancin sa,

 

“Gaskia gajiyalle nagaji. Ke kullum aike aike, Ni Ina zansan inda shedaniyar nan take..?”

 

“Haba Mudi na! Yi hak’uri kaji temaka ka nemota saboda kai ma na aiketa tasiyo.”

 

Mudi yana cuno baki gaba haka yafice bayan ya jefi mahaifiyar tasa gajiyalle da harara. Can kasan bishiyar dirimin layin su ya hangota da cincirindon yara akanta, Kowa ya tsaya yana kallon su. Ga ledar kokonta a gefe ta fashe kokan ya tsiyaye, Ta cakumo wuyan yaron wanda da alama shine ya zubar da kokon. Rantsuwa ta shiga kwarara wa tana kifa masa mari. Jikin yaron gaba d’aya rawa yake yi kuma da alama a girme ya girme mata.

 

“Kutumelesin kan babban bala’in dirimin durbun, Walle ko dan haladu (Baban sa)ne zai zo wajen nan sai na lallasa ka. Kokon har na wazobiya ace ka barar min? Bazan yadda ba ko wajen mai gari za’aje.”

 

Na sake duban kokon daya malalar ina tuno yadda gajiyalle zata caskalani, Zuciyata ta kara zafi na daga hannu na sake dirka masa rankwashi a kwanyar kansa ji kake,

‘Qwas..’

 

“Ke! Ke! Ke! Toh kizo inji gajiyalle banza bankadaddiya.”

 

Daga jin yadda aka kirawoni bankadaddiya nasan Mudi ne, ‘Dan gajiyalle matar babana. Na dubi Mudansiru dake hawaye sha’be shabe yana shafa kuncin sa dana lallafta masa mari. Ai kuwa na kame awajen naki zuwa wajen Mudi, Cikin haka sai ga dan haladu mai rake mahaifin mudansiru, Yana tafe yana kankare raken sa, Mudansiru na ganin sa ya sake barkewa da kuka yana nuno ni, Ni kuwa na shiga harara ina watsa hannu sama domin ba yadda zan yi ba.

 

“Kai Meya faru? Waya dake ka?”

 

Dan haladu ya tambaya yana mai janyo mudansiru jikin sa, Na tabe baki ina mika hannu na saitin sa tamkar ance na mika,

 

“Koko na na wazobiya ya barar min nace ya biya ni yaki biya.”

 

Na karasa fada ina gatsine. Dan haladu yaja dogon tsaki yana mai dankarawa mudansiru Harara,

 

“Shine ka bari mace ta maka duka? Allah ya sawwake. Ke kuma Ungo talatin domin bakici hamsin ba tunda kin lafce shi.”

 

“Meyaci murtalar (nera ashirin) din?”

 

“Laftar sa da ki kai. Rike kafin na maida kudi na.”

 

Na karbi kudin ina karewa murtalar din kallo na girgiza kai,

 

“Kai bazata karbu ba yasin ta yage da yawa.”

 

Wafcewa dan haladu yai ya cillo min wata na karb’e ina cuno baki gaba. Dan haladu ya tisa k’eyar mudansiru gaba yana sake jibgar sa akan bari da yai na tule shi batare daya rama ba, Sauran yara dake wajen suka sa shewa suna tafa hannaye, Suka shiga yi min kirari na wanda kaf kauyen durbun kowa yasan da shi,

 

“Woo Dijangala oganniya , Qadangaren bakin tulu, Ta gajiyalle mai yar hakiya.”

 

Tabbas ni oga ce shysa sauran yara ke kira na oganniya. Domin duk wani fada lungu da sako nike cinye shi sannan wani lokacin har siyan fada nake na tarewa marasa k’arfi. Mudi ya cakumo hannu na ya kwace talatin din sannan ya tisa keya ta har gida. Tun a farkon layin mu na yai nasa wuri ni kuma na kama hanyar shiga gida, Ina kambama mamakin Mudi da halin satar sa, Kusan kullum hakan yakeyi Idan gajiyalle ta aike ni. Ina zuwa gajiyalle tundaga soro tana tsaye da muciya a hannun ta tana gani na ta janyo ni ta hau bugu tamkar tasamu jaka. Tana yi ina kirga duwarwatsun hannu na, Domin Inde duka ne na saba ya zama jiki sam banajin zafin sa ko kadan.

 

“Shegiya almura da idanu zuru-zuru, Yar iskar yarinya, Mumugunciya yau kuma wani fadan kika rakito. Ina kudin dan uban ki?

 

“Mudi ya…”

 

Ruwan ciki na ta haye ta hau duka na tana yakushi na kamar mage.

 

“Guzumar uba! Narantse da uban da ya haifeni zan cire miki hakora, Yau ma Sharrin zaki masa? Kinje kin kashe kudin Shine zaki sake karairakin da kike? Ban haifi barowa ba, Kece barauniya da kika tsotsa a mama. Matsa kafin na shureki ki mutu. Bankadaddiyar banza bankadaddiyar wofi.”

 

Matsawa nai gefe ina goge hawayen bakin cikin da Mudi da gajiyalle ke kunsa min kullum, Ina ji ina gani ta fita ta sayo kosai da zafin sa sai kamshi yake yi ga kunun gidan yar asabe daya sha kayan kamshi, Mudi ya dawo suka shiga ci suna korawa da kunun hankalin su kwance. Ni kuwa cikina sai kukan yunwa yake yi. Baya na juya musu Ina tunanin yadda zanyi na samu abunda zan sanya a baki na, Domin nasan yau gaba d’aya gajiyalle bazata bani abinci ba.

 

Tulin wanke wanken dake jira na na kalla, Mi’kewa nai dakyar Ina bubbuga konkosona na karasa wajen na duka na fara dauraye su ina tara kanzo a gefe. Cikin haka Laraba mai kaya ta shigo gidan tana doka sallama, Gaisawa sukai dasu nima na gaishe ta ta amsa tana bantarar goro,

Inayah Hausa Novel Complete

“Gajiyalle! Gajiyalle ta ubale, daga ke ba kari sai dabbobin ki da kajin ki da Mudin ki..”

 

Gajiyalle ta dashare hakora tana mutstsuka kananun kwayar idanun ta mai dauke da hakiya. Jinta take a sama a duk lokacin da aka yi mata wannan kirarin.

 

Ruwan dauraya ya kare sai na ebo acan gangaren bakin gari. Mikewa nai na dauki bokiti ina sosa kai na dake min kaikayi rabona da wankeshi tun sallar bara sai tsami yake yi yana tashin doyi. To yaxanyi? Babu sabulun dazan wanke dashi, Wanka ma haka nake yi ba sabulu, Shiyasa na kan dau tsawon lokaci shima kafin nayi. Ficewa nai kogin na gangare ebo ruwa, Kafata ko takauni babu domin babu halin samu…

 

Kafin dai naje rafi na dawo nayi fa’da da yara ba adadi, Wani daga rabiya abu ya dawo kai na, Wani kuma ni na sai fadan. A haka dai na ebo ruwan ina ‘digirgire gab da gangaren unguwar kuka na sake hango cincirundan yara ana dambatuwa. A sukwane na ajiye bokitin kai na, Na dira a tsakiyar filin, Ganin yadda ake tular Nafisa yar Badamasi kansilar garin mu, Kuma ba kowa bane ke dukan ta fyace kabiru dan gidan Nanun me kyamis. Wai Kabiru Nafisa ke bari yana jibgarta. Kabiru fa? Kabiru dai abu kamar ka hure shi ya fad’i saboda rashin auki. Kankace kanzil na janyo shi na lallafta masa mari a duka kuncinan sa, Ba tare da neman ba’asin asalin fad’an ba.

 

Yara dake gefe suka hau tafin,

 

“Woo ke Dijangala oganniya, Ta mai gari..”

 

Na sheke da dariya ina bin Kabiru dake hawaye da kallo, Nafisa ta matso kusa dani tana min godiya, Na sosa duddugaggen gashi kai na daya lalace saboda rashin gyara. Kafin nace,

 

“Sai ni Dije-Dijangala-Ta mai gari.. Oganniya yar baffan ta..”

 

Sauran yara suka hau shewa suna tafa min. Kabiru ya kwashi takalman sa ya zura a guje. Nafisa ta rik’o hannu na tana dashare hak’ora. Na cuno mitsitsin baki na gaba ina gatsina shi, Kafin na daga hannun dama na sama, Na kwararo rantsuwa na buga a zani na,

 

“Dame zaki biya rabiyar fadan ki? Kinga dai siya nayi, Idan baki yadda ba na kira Kabiru ku karasa daga inda kuka tsaya,”

 

Na karasa fada ina bubbuga kafa ta hade da jijjiga kwankwaso na. Nafisa tayi rau-rau da idanu tana murza hannun ta alamun dai batada abunda zata bani, Naja shewa ina shata layi a tsakanin mu da ita,

 

“Kan babban balai, Alo tsiya alo danja, Shege ka fasa dan halak sai yanka… Kina nufin ba zaki biya ba?”

 

“Kiyi hak’uri Dijangala, Yanzun bani da abunda zan baki…”

 

Kukan kura nai na cakumo wuyan rigar ta ta yan gayu, Dai dai lokacin da Mudikallen Gajiyalle ya karaso wajen yana mai dakamin tsawa,

 

“Ke dalla can zo ki wuce mu tafi gida uwar ƴan masifa kawai.”

 

Yayi magana yana banbare hannun da na ri’ke kwalar Nafisa.

 

“Idan na bar wajan nan ayi gunduwa-gunduwa dani, yo yama za’a yi na siyi fadanta, Tak’i biya ace na hak’ura? Hum uhm!”

 

“Marar kunya kawai, ni kike gayawa wannan maganar? Zaki tafi gida ko sai na koya miki hankali yanzu a wajan nan.”

 

Na shiga huci kamar wacce zaki ya biyo daga jeji na sakarwa Nafisa wuya, Ina faman murgud’a baki nace.

 

“Wallahi bashi ne ki kaci sai kin biya ni.”

 

Na figi bokiti na nufi gida ina masifa kai kace wani gagarumin abu aka yi min . Da zakara na fara cin karo a zaure yana kwance, Zuciyata sai zugi take, Nasa kafa na shure shi, ya tashi firrrr yana kuka ya shige cikin gidan. naja tsaki Ina galla masa harara tamkar da mutum nake,

 

“Da karka tashi, wallahi da sai na karya maka kafa d’aya. Gaji..! Gaji..!! Gaji wai kina ina!!!?”

 

Gajiyalle ta fito daga cikin daki hannunta ri’ke da mafici wanda alamu suka nuna fifita take yi saboda zafi.

 

“Ya aka yi kike ta faman rafka min kira tamkar wata tsohuwar makauniya?”

 

Na sanya bayan hannun na dinga murza ido kamar wacce na yiwa sarki karya. Na sake zukar iska cikin hanci na tare da murguda baki ina kifta ido nace.

 

“Gajiyalle rabiyar fada nayi tsakanin Nafisan kansila da Kabiru Dan gidan mai kyamis. Nace Nafisan ta kawo ladan tariyan fadan taki. Kuma wallahi yunwa nake ji, ciki na zafi kawai yake yi kamar ana hura garwashi.”

 

Gajiyalle ta kalli Dije sama da kasa cikin takaici, zuciyarta na tafasa kamar taje ta shake ta haka taji. Juyawa tayi ta koma cikin dakin tana mai jan tagwayen tsaki,

 

“Dan guzumar uban ki mezan miki? Kafaffiyar yarinya bakida aiki sai fada a gari, kin gunduri kowa. Zaki cigaba da wanke wanken ko sai na lallasa ki.?”

 

Idanuwa na suka kawo ruwa, Cikina sai neman agaji yake. Na dinga rarraba ido cike da tashin hankali, yunwa nake ji sosai tamkar naci kasa haka nake ji, saboda jiya ma haka na kwana ban samu abin da zan kai ciki na ba. Wajan bishiyar darbejiyar dake tsakiyar gidan mu na nufa tare da sanya hannaye na na rungume ina sakin wani marayan kuka. Da haka mahaifi na ya shigo daga zaure shi yana gyara hular kanshi wacce ko lankwasuwa ba tayi tsabar rashin gyara da ba’a mata. Kafadar sa ta dama saqale take da fatanya da alama daga gona yake. Shi dinma sai jera hamma yake. A hankali ya shigo bakin sa dauke da sallama. A jeme yake tafiya saboda wahala sautin jan kafarsa ce tasa na juya na dube shi ina mai shanye hawayen daya tahomin,

 

“Baffa! Sannu da zuwa.”

 

“Sannun ki d’iyar albarka.”

 

Dake haka yake kira na kasancewa ta yar fari. Karasawa nai kusa dashi na karbi fatanyar na ajiye ina jera masa sannu. Kallo d’aya yai min ya zura hannu a hujajjen aljihun sa. Murtala/Nera ashirin ya d’akko da alamun ita kadai ce dama aciki. A kudindine tasha facin salatif,

 

“Ungo diyar albarka. Jeki sayo ko awara ce a bakin yar kasuwa kici kinji.?”

 

“Baf…”

 

Ban karasa ba sakamakon iskar danaji tashige da gefen kunne na, Ashe Gajiyalle ce ta cika tayi fam zata fashe,

 

“Guzumar uba! Bashari nagaji da wariyar launin fatar da kakeyi a gidan nan, Kullum dan munafurci da bakar mugunta, Ba zaka bada ishasshen kudi ayi cefanen abinci ba sai dai kaba shedaniyar yarinyar nan tasai kayan kwadayi, Idan anyi magana ka fara sakin karairakin ka na yau da gobe. Gotai gotai dakai kana tafiya a jeme, Wai ungo diyar albarka. Toh wa aka samu bata hanyar halas ba?..”

 

Ta karasa fada tana gwada yadda Baffan mu ke tafiya. Baffan mu yai murmushi kawai yana mai saqale hular kansa akan gajeriyar katangar gidan mu data rabamu da gidan su Mari mai kitso. Tab’e baki nayi na fara kokarin wucewa don siyo abin da zan sanya aciki na kenan Gajiyalle ta danko wuya na,

 

“Ai babu inda zaki shafaffiya da mai, Har sai kin kammala wanke wanken can da kika bari.”

 

“Kyaleta taje zan karasa yi.”

 

Cewar Baffan mu, Ya fada yana mai nunamin hanya dana tafi. Arcewa nai a guje ban tsaya ko ina ba sai yar kasuwa wajen masu saida kayan dadi. Rasa abunda zan siya nayi na nera ashirin. Cikin haka sai ga Nafisan kansila tana tafe tana afawa bakinta awara. Gabanta na sha na Kece da dariya ina buga zani,

 

“Dan-dan-dan wa na kama?”

 

Nafisa tayi rau-rau da idanu, Tana bin ko’ina da kallo ko zata samu mai tare mata. Na sake shekewa da dariya ina bubbuga k’afa ta,

 

“Yanzun sai na caskala ki, Na casa ki. Nayi futu-futu dake kamar yadda ake casa maiwa. Dan bakin munafurci na sayi fadan kice ba zaki biya ba. Tabdijan.”

 

Na karasa fada ina mai nannade hannun doguwar rigar atamfa ta datai du’ku-duku saboda rashin tsafta. Nafisa ta rarumo hannu na cike da tsoro, Ta samin cakulet a hannun tana murmushi,

 

“Ungo chakulat kisha, Zan kuma sai maki kankarar madara mai sanyi ta murtala (Nera ashirin).”

 

___

 

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE:::

 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

 

Guda hudu 4 Kuma 500,

 

Guda uku 3 Kuma 450,

 

Guda biyu 2 Kuma 400,

 

Guda daya akan 300.

 

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

 

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

 

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

 

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

 

*+234 903 234 5899*

 

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

 

*09033181070*

 

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA

SABON SALO

 

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

 

 

 

 

 

*MISS XOXO*👩🏽‍🦯

[3/2, 9:29 PM] +234 903 234 5899: *KIBIYAR AJALI…..!!!!*

_(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_

🏹👑👩‍❤️‍👨💝

 

 

*MALLAKAR:- NANA HAFSAT*🧕🏼

*(MISS XOXO)*

 

 

*©️®️ZAFAFA 5 2021*

(PAID NOVELS)

 

 

*BABI NA 2*

 

 

Na karbe da sauri tare da gyara tsayuwa saboda naji banza ta fadi, dan dama Nafisa ba wani cikakken wayo ne da ita ba. Turo kallabi na nayi gaban goshi tare da kama kugu ina girgiza jiki nace mata.

 

“Idan karya kike min wallahi duk randa na ganki sai na fasa miki hanci, kinsan ni fa bana san alkawarin yan nefa.”

 

Cikin raunin murya Nafisa ta kwaso rantsuwa ta dire min tare da kallon cikin ido na tana cewa zata bani da gaske, sannan ne na matsa mata ta wuce nima na tafi ina dukan cinya tare da cewa.

 

“Hahahaha hooo ni Dije…, Dijan gala ta mai gari bazan auri talaka ba… Kodan bakin cikin Gajiyalle matar uba.”

 

Nayi dariya kamar ina kusa da wani sai dai babu kowa hasalima kowa harkar gabansa yake yi ba ruwan wani da kowa. Gaskiya chakulat akwai dadi, tunda nasa ta a baki na naji ina neman rasa harshe na, duk a zato na ma harshe na ya tsinko daga cikin baki na saboda zaki, tabbas ina son dadi gashi Allah be yo ni a gidan da ake cin mai d’an maiko-maiko ba.

 

Kai tsaye wajan mai siyar da kan kifi naje na siyo na naira biyar, na tsaya a gurin na dangwali yaji na cinye. Daga nan naje na siyi yajin masau shima na naira biyar ya rage sauran goma, na hango rumfar mai gasa zabi, wayyo Allah garin daɗi yana nesa, miyau na ya tsinke sai kawai na girgiza kai tare da tsayawa gurin mai rogo na siyo na goma. Gefe guda na samu na zauna na cinye tas sannan na samu randar da ake zuba ruwa, duk mai bukatar amfani da ruwa indai bashi da kudin siyan wanda ake kulawa a farar leda to wannan ruwan shi zaka sha, almajirai, yan garuwa, masu walda da dai sauransu duk da shi suke amfani, haka nima naje na dauki abin diba nasha, aikuwa na saki wata katuwar gyatsa kamar naci duniya da abinda ke cikin ta.

 

Kwanaki biyu da yin alkawarin mu nida Nafisa naji shiru bata kawo min ba, bayan na gama share tsakar gidan mu da Gajiyalle ta sanya ni nayi, na dauko mayafi na naci d’amara kamar yadda na saba yi. Da gudu na fita dan karma ta kuma sa ni wani abun daman ga wanke-wanke nan ba’a yi ba kuma idan har ta ganni sai ta ce ni zanyi, dan haka kai tsaye gidan su Nafisa naje, tana zaune a tsakar gida ita da kawayenta suna wasa, gani na da tayi yasa ta saurin mikewa ta shiga dakin Umman su. Ko tsoro banji ba haka na tsaya ina faman girgiza kugu alamun akwai tsantsar rigima a tare da ni, can sai gata ta fito rike da kankarar madara tana zuwa ta miko min jikinta yana rawa tace dani.

 

“Dan Allah Dije kiyi hakuri, tun jiya na siyo zan kawo miki gida aka hanani fita. Gashi nan Umma ce tasa miki a cikin kankarar zobo shi yasa ma bata narke ba har yanzu.”

 

Nan da nan na saki jiki tare da karɓa ina yake baki, har cikin rai na naji dadi dan tun kwakin da Gajiyalle ta damka min a hannu ban sake saka komai a cikin baki na ba. Na zauna wajan su muka ci gaba da wasa, amman fa nice na zama shugaba a cikin su, domin sai naga dama ma zan bari a taba kayan wasan kuma babu mai ce min dan me? Tun daga lokacin kuma muka zama kawaye sosai da Nafisa, kullum ina gidan su muna wasa har ranar da Baban su ya siyo musu talabijin ina gidan akai ta murna kansila ya siyo talabijin da janarato.

 

***A duk lokacin da naji mahaifina yana sauraron radio ko kuma idan muka je gidan su Nafisa wato ƴar kansilan mu muna kallo a talabijin, na kan yi mafarki da kuma hasashen nima ina ciki ana damawa dani. Babban abin da yake daure min kai shine ta ina mutanan radio suke shiga suyi magana har a jisu radau kamar yadda muke ji? Abin sake daurewar kan kuma shine, wadanda nake gani a talabijin, kuma kullum cikin shiga ta alfarma, na kan ce ko a ina suke samun kaya tsala-tsala haka? dan naga basa maimaita su idan suka sanya.

 

Kasan cewar baki na baya iya yin shiru akan duk abin da nake son sani, Hakan yasa na ke yawan tambayar Bello yayan Nafisa cewar.

 

“Wai dan Allah Bello ya za’a yi nima idan na girma zan iya irin wannan aiki?”

 

Sai ya galla min harara irin ta wulakancin nan yace min.

 

“Ke dalla gafara yiwa mutane shiru, uban waye ya gaya miki jahili ko jahila suna iya yin aikin jarida? Tafi ki bawa mutane guri keda ko fensir baki iya rikewa ba bare shiga aji d’aukar darasi.”

 

Ya kamata inji haushi idan ya furta min haka, amman ina wata irin k’ek’eshasshiyar zuciya Allah ya bani da ba komai ke bata min rai ba, musamman irin wannan da nice na tambaya. Sai na yatsina fuska na taɓe baki ina jujjuya idanuwa, a rai na na kan ji tabbas zan iya aikin jarida koda kuwa zan riƙewa ma’aikatan abin da suke magana dashi. Idan na koma gida na kan tambayi Baba na.

 

“Shin Baffa ya zanyi na zama ƴar jarida?”

 

Ya kalle ni yana dariya irin tasu ta masu hangen nesa, ya gyara zama yace dani.

 

“Ummi na zaki iya amman sai kin yi ilimi na zamani da na addini.” Lokacin ina cikin duhun kai, sai na ce dashi.

 

“Toh Baffa a ina suke ilimin zamanin dana addinin yanzu naje na debo san rai na?”

 

Baffa ya yi dariya cike da ganin wauta irin tawa.

 

“Ummi na kenan, su ai ba shukawa ake yi ba, kuma ba a kasuwa ake sai dawa ba bare kije ki siyo. Karatu ne na boko dana islamiya, su zaki yi sai ki zama ƴar jarida ko likita ko lauya da sauran su.”

 

Ina jin haka a lokacin nace da Baffa.

 

“Kai! Aradun Allah bani ba yin karatu, kullum kana zaune cikin wani ɗaki, na taɓa ganin yadda ake zama a wani fim da muka kalla gidan kansila, wallahi Baffa bani ba zama guri gudu kamar akuya a daure.”

 

Sai na tashi nayi tafiya ta na barshi a gurin, nasan yana tausaya min kawai babu yadda zai yi min ne, na tafi nayo faɗa ko na siya sai na samu abin da zan sawa ciki na.

 

<<<<>>>>> <<<<<<>>>>

 

Ranar wata laraba da safe misalin karfe takwas Kauyan mu ya samu halartar wasu mutane daga can birni, su kusan goma sha huɗu suka zo a mota, yan garin mu suka cika kofar gidan mai gari kasan cewar anan bakin suka sauka. Mune yan sahun farko a wajan kallo, mun kasa mun kuma tsare kamar wadanda aka tilastawa zama. Suka zauna akan tabarma suka korawa mai gari jawabin da yake tafe dasu akan cewa za’a zo a buɗe makarantar boko a kauyan saboda yara su samu ilimi. Tunda jama’ar kauyen mu suka ji wannan al’amarin suka fara bijirewa suna tsinewa wanda ya bada shawara da umarnin cewa azo a gina makarantar bokon.

 

”Gaskiya bama so, mu ba arnaye bane.” Na faɗa da karfi yadda kowa sai da ya juyo yana kallo na.

 

”Ke! You’re very very stupid, kinga sa’anninki a cikin maganar da ake yi?”

 

Cewar wani mutumi da yake sanye cikin kotu (suit) sanye da gilashi fari a idanunsa. Yadda naga yana hararata ya tabbatar min da cewar ransa a ɓace yake da furuci na, dan haka na yi fari da ido na tare da turo baki na gaba ina kun-kuni. Kalmar sa ta very stupid ta tsaya min a zuciya tana sani jin wani nishad’i, duk a zato na kalmomin farin ciki ne. Mai gari ya gyara zama ya kalli manyan dake zaune dashi wato mai unguwa, liman da dai sauransu yace.

 

”Ku duba wannan zancen nasu, ya kuke ganin za’a yi. Shin mu yadda da umarnin gwamnati ko kuwa dai a barshi ba sai an yi ba tunda ba wai sabawa mukai da irin karatun ba?”

 

”Beri sutufid….!”

 

Na faɗa bayan mai gari ya kai maganar sa karshe.

 

Duk suka buɗe baki suna kallo na da tsantsar mamaki a fuskokin su. Ni kuwa ban gane ba na ci gaba da ƙirgar duwatsu ina sawa a cikin ramin da na yi ina kirgawa. Wani saurayi da yafi kowa kankanta a cikin bakin ya taso yazo gurina tare da kafe ni da ido yana yatsina fuska tamkar yaga kashi yace.

 

”Ashe baki da mutunci?”

 

”Aramma da na yi maka me?”

 

”Ohhh! Bama kisan abin da kikai cewa mai gari ba ko? Saboda baki da mutunci kinga saanininki a can gurin?”

 

Ya faɗa yana nuna da’irar da suke zaune, na gyada kai alamun a’a ban ga sa’ana ba.

 

”Toh ki sake magana a gurin nan ki gani, sai na turmushe wannan dogon hancin naki mai kama da yatsun kaza.”

 

Yana gama faɗa ya koma gurinsa, ya yin da yaran gurin suka saka dariya saboda tanka min hanci da ya yi, ni kuma na dinga shafa hancin nawa dan gano ko da gaske yake yi irin yatsun kaza ne. Haushi ya kamani da na gano cewa rashin mutunci kawai ya yi min. Daga cewa very stupid kawai zai tanka min halittar da Allah ya yi min. Na sake dubansa tsab daga sama har ƙasa naga shi sam bama shi da hancin har yake tanka nawa, haushi ta ishe ni na yi kwafa dan bani da abin cewa kuma. Can kuma ana ta kai ruwa rana tsakanin jami’an birni da namu na gargajiya sun kafe kan cewa ba za’a kawo musu wata makaranta ba indai ba ta addini ba, a ganin su zuwan boko zai sanya al’adun mu da tarbiyar mu zasu lalace. Da kyar da sidin goshi Allah yasa suka yarda suka amince.

 

Bayan bakin sun tafi mai gari yasa aka kirawo mutanan gari ya shaida musu duk abinda suka tattauna tare da sharaɗin cewa indai aka kammala gina makarantar, dole kowa zai kai ɗan sa ko ƴar sa dan a koyar da su karatu. Hmmm Ina daya daga cikin yaran da basu son makaranta, Baffa na ya kira ni ya yi ta lallashi amman fur na ce ba zan yi boko ba dan bazan je nasha wahala ba.

 

Ci kawai nake ina shaƙewa saboda rashin ruwan da zan kora dashi, gashi sai loma nake dan kara Gajiyalle ta shigo ta kwace. Sai da naci kusan rabi na ajiye ragowar ba dan na koshi ba, a’a tausayin Baffa naji dan nasan shi zai zo yaci shima ya kwanta. Na sake lallaɓawa na leko tsakar gidan naga babu kowa sannan ta yi wuf na shige inda nake kwana tare da jigawa jikina kayan wankin Gajiyalle ta yadda ba zata gane ina ciki ba. Kamar dama ɗan lokaci Allah ya aramin sai kuwa naji muryar ta a tsakar gida tana masifa ita kadai.

 

”Wato wannan shegiyar yarinyar ba zata dawo gidan nan ba ko? Daman ta saba zama a titi dan haka yau idan ta kwana a can ba wani abin tashin hankali bane, ja’ira kawai da fuskarta kamar kwallon kwakwa.”

 

Ni dai tun daga nan ban sake jin muryarta ba kasan cewar bacci mai nauyi da ya ɗauke ni. Kiran sallar farko naji an kwaro min ruwa mai wari da doyi a jikina, gashi sanyi karara dashi, na tashi a firgice ina neman hanyar fita.

 

”Ina zaki munafuka? Yau mai rabani dake a gidan nan sai Allah dan kuwa sai na yi miki jina-jina da fatar jikin ki.”

 

”Dan girman Allah Gajiyalle kiyi min rai, dan Allah karki doke ni wallahi na dena bazan sake yi miki gardama ba, kiyi hakuri.”

 

Wata irin bulalace da ko kaɗan bata karyewa da ita Gajiyalle take doka na duk sanda taso. Da yake ba mutunci da tausayi gare ta ba, haka ta zage ta dinga labtar min jiki kamar ta samu jaka. Baffa ya fito daga cikin ɗakin sa yana son ya kwace ni amman Gajiyalle ta haɗa dashi wajan dukan tamkar wasu ya’yanta. Sai da ta gaji dan kanta sannan ta rabu da mu. Baffa ya rungume ni a jikinsa yana shafar baya na, duk da bai yi magana ba a zahiri, baɗininsa a bace yake, gashi ba zai iya yi mata hukunci ba, shi kanshi wani lokacin shakkarta yake yi.

 

”Gobe ma na kuma saki aiki kiyi min rashin kunya, wallahi sai na dinga lallasaki a gidan nan marar kunya kawai. Kuma ki tashi kije ki debo ruwa dan ko na wanke fuska ba zaki samu ba a cikin gidan nan. Tashi nace ko nazo na sake zaneki a nan gurin.”

 

Baffa ya sake ni da sauri, ganin haka da nayi ne yasa ni kuma fashewa da kuka ina tuna mahaifiya ta. Nasan da tana raye ba zata bari ayi min wannan wulakancin ba, duk yadda za tayi sai ta sanya ni farin ciki, ba zata zuba min ruwan dauda mai wari ba bare har ta sanya bulala a jikina, uwa akwai daɗi duk lalacewar ta tasan muhimmancin abin da ta haifa. Na sosa cikin idona zuciya ta na sake tsagargarewa na kalli Baffa sannan na dakko mayafi na wani baki da kullum shine a jiki na tamkar na gado, na yi damara tare da nufar kofar gida. Sai da nayi kamar zan ɗauki abin dibar ruwa sai kawai na ruga da gudu na bar musu gidan.

 

”Bazan debo ruwan ba wallahi sai dai ayi kuli-kulin tara sisi dani, an mai dani jakar gidan ko? Toh sai dai a yanka ni aradu dan na dena wahala a gidan uba na, kiji ni da kyau Gajiyalle.”

 

Ina gama faɗa na tsaya a kofar gida, Baffa sai kira na yake amman nayi shiru dan idan na amsa mai dani zai yi ta doke ni ba iya cewa komai zai yi ba. Duk da cewa duhu ne garin masallacin kofar gidan liman ana ta assalatu da yake akwai farin wata sai ban wani ji tsoro ba, haka na fara tafiya ga sanyi saboda a jike nake iska na sake hurani naje na zauna a kofar gidan Aramma Auwalu, da yake akwai buhun-hunan taki a wajan. Zuciya ta ce take ta hasashen yadda zan yi na samu kuɗi yadda zan wulakanta Gajiyalle domin rashin su ne yasa ta mai dani tamkar wata bola abar zuba datti. Ina nan zaune har Aramma Auwalu ya fito ya wuce masallaci ba tare da na bari ya ganni ba, a gurin bacci ya kuma ɗauke ni duk da irin iskar da take shiga jiki na.

 

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment