Littafan Hausa Novels

Karuwar Gida Hausa Novel Complete

Siffofin Mace Mai Ruwa
Written by Hausa_Novels

Karuwar Gida Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

KARUWA GIDA

“`LOVE and

ROMANTIC STORY“`

 

 

 

*PAGE 1-2*

 

Ɗan ƙaramin towel na jawo nayi ɗaurin ƙirji wanda ya tsaya min iya ƙugu bai sauka kan gwiwai ba,ƙarami na ɗauka na naɗe kaina da shi ta yadda zai tsane.A hankali na fito kamar mai tsoron taka ƙasa ban zame ko ina ba sai bisa ɗan maidaidaicin bed ɗina, Teddy ɗina na jawo wanda ya ke ƙatoto na rungume tare da lumshe idona ina tunanin abinda ya zame min ibada wato tunanin wanda zai aurena,ina mashi wani irin so wanda ba zan iya ƙiyasta shi ba dan tuni soyayyar shi ta game gangar jikina da ruhina.

Amman tambayar da ni ke yawan yiwa kaina wanene shi?a ina ya ke?dan ni kaina ba zan iya cewa ga shi ko ga kamar shi,abinda na sani kaɗai shi ɗin dogo ne,wankan tarwaɗa,mai saje da yalwatacen gargasar ƙirji.”Hummm!”na sauke wani gwabron numfashi saboda ganin suffar shi da nayi a idona ta na min gizo amman banda ainahin fuskar shi saboda in banda dogon gemun shi da ƙayatacen sajen shi babu abinda ni ke iya ƙiyastawa.

 

 

“Mimi lafiyar ki kuwa?”cewar Mami wacce ta shigo ban ma san ta shigo ba, murmurshi nayi nace “Mami yaushe kika shigo?”ba ta ban amsa ba sai tea ta miƙo min ta na cewa “ungo karɓa ki sha wannan in ya so kya sauko ƙasa ki ci abinci yanzu Daddyn ku ya yi min waya ya na kan hanyar dawowa ma”karɓar tean nayi na fara kurɓa dan dama ta wannan fannin na ƙware dan ba ka sau ni ke cin abinci ba sai in su Mami sun matsa min ita da Daddy.

 

Sai da na shanye tas sannan na miƙa mata cup ɗin ,fita tayi ni kuma na nufi wajen coiffeuse ɗita na jawo lotion na shafe farar fatata da shi sannan na shafa kwalli hakan ya fiddo kyawun fararen idona man leɓe na shafawa baƙaƙen laɓana uwanda a ko da yaushe ni ke muradin sun canza launi zuwa jajaye.

 

 

Wata baƙar riga tee-shirt mai shatin love na saka tare da sket ɗin ta wanda ya kasance na jeans ne,tsaf na fito abuna gwanin kyawu dukan shap ɗina ya fito irin coca-cola.

 

Fita nayi zuwa falo Teddy na riƙe da hannuna,tun kafin na ƙarasa ni ke jin hayaniyar yara sama-sama kuma ina jin murya Daddy alamun abun da suka saba ne rigima shi kuma ya na yi masu shari’a.

 

Imane ce ta rugo da gudu ta nufo ni ta na mai cewa “anty Mimi rufe idon ki zan gwada maki wani abu”tayi maganar ta na mai kamo hannuna,ina shirin rufe idona Ihsane tayi caraf ta na cewa “anty Mimi sabon Teddyn da Daddy ya sawo maki ta ke son nuna maki dubo shi nan”tayi maganai ta na mai ɗago min wani ƙaton Teddy rose dan har ya fi na hannuna girma.

 

Ihu Imane tayi tare da saka kuka ta na birgima da ƙasa,duƙawa nayi na tallabota ina rarrashinta tare da kamo hannunta mu ka ƙarasa cikin falon.Sai da na zauna sannan na dubi Daddy nace “ina wuni Daddyna?”da murmurshi ya amsa”lafiya lau Mimi ya jikin naki?”nace “ai na ma ji sauƙi”Teddyn ya miƙo min nayi mashi godiya ina mai ɗaukar shi hoto da wayana sannan na ɗora a statut/status a ƙasa na rubuta “`thank You my dear Daddy“`🥰 ina gama ɗorawa na kashe data saboda Mami da ta kawo mana abinci.

 

Bakar Ayah Hausa Novel Complete

Cikin tray guda duk mu ka kewaya mu na ci har da Daddy dan haka al’adar gidan mu ta ke saboda ƙarin zumunci,kamar wacce aka jefo haka Ameera ta shigo ɗakin babu ko sallama idonta bai zame ko ina ba sai kan Teddy na.

 

 

“Kam bala’i wai ba dai wani sabon Teddy aka kawo maki ba? Daddy ni shine ba ka sawo min ba?”Ameera ta faɗa cikin jin haushi tare da nuna tsantsar hassadar ta gare ni.

Wata uwar harara Mami ta watsa mata tace “sannu Hajiya Babba (cewa da mahaifiyar Daddy)da fatan kun shigo lafiya?to barka”sosa ƙeya tayi tace “laaa ashe ban gaishe ku ba? please na tuba dan Allah Mami kiyi haƙuri, Daddy ina wuni Barka da dawowa”ta faɗa ta na wanke hannunta ta saka cikin trayn abinci.

 

Cike da sakin fuska Daddy ya amsa tare da ɗorawa da “Ameera uwayen kishi,to ke ma yau na kawo maki abinda kike bala’in so shikenan sai kowa ya huta da mitar ki”cike da zumuɗi ta cire hannun ta daga abincin tace “Daddy dan Allah bani tun yanzu”tsawa Mami ta daka mata hakan yasa ta miƙe ta na gunguni,har ta fara tafiya Daddy yace “kin ga fah Ameera dawo ki karɓa ta shi nan cikin leda”da murna ta zo ta ɗauki ledar ta na mai fiddo galleliyar wayarta TecnoPop2 ihu tayi ta na murnar yau ita ma ta zama kamar kowa an barta za ta riƙe wayar hannu,dukan su dariyarta suka shiga yi dan kusan kowa ya san yadda ta ke son kullum Daddy ya barta ta fara aiki da waya yau kuma sai gashi ya sawo ya bata da kan shi.

 

 

Ko da mu ka gama cin abinci na tattare wanda mu ka zubda na gyaran wurin,kishingiɗawa nayi ina shart ina duba saƙonni abokaina uwanda suka min comment na Teddyn da na ɗora.Murmushi nayi na ɗora Teddyn a ƙirjina nayi selfie na sake ɗorawa nan kuwa wata ƙawata Nabee ta min reply da “`wlh mijin ki na da aiki,saboda wannan iskancin naki ya fara yin yawa kin ɗauki Teddy kin ɗora a ƙirji sai kace wani mijin ki.Ni kuwa ko dai aljannun ki ke son Teddy ?“` da ɗan mamaki na maida mata “aljannu kuma?”ta maido min da “`eh mana tunda sun hanaki ki yi saurayi kin ce duk Mazan duniya ba su burge ki sai mutumen da ke kan ki ba ki san waye ba,to a nan minene in ba alkannu ba?“` shiru nayi ina tunanin furucinta sai na ga kuma kamar ta na da gaskiya,fuska na ɗan ɓata tare da tashi zaune ina mai maganar zuci “to wai ma ya aka yi na son shi alhalin babu wata alama da ke nuni ya san da zamana?na fara jin tsoro gaskiya”ban san duk abinda ni ke Daddy na ankare da ni ba sai da naji yace “Mimi ya dai?”a daburce na kalle shi ganin ya kafe ni da ido nace “kaina ke min ciwo” “ok tashi ki je ki kwanta ƙila ƙarar tv ce ga kuma ta uwannan (cewa da twins da suke zaune kusa da shi)”jiki a mace na ɗauki Teddyna duka biyun na nufi ɗaki.

 

 

Daram ƙirjina ya buga saboda abinda kunnuwana suka jiyo min,na zaro ido waje ina kallon Ameera wacce daga bata waya yau har ta fara aikata masha’a da ita.Ba komi naji ba sai sautin blue Film da ta ke kallo,komawa nayi da baya dan alamu sun nuna ba ta san ma na shigo ba tsabar yadda ta ƙure volume.

A falona na kwanta kan bisa doguwar kujera na rungume Teddyna gam kamar za’a ƙwace min shi, ba komi yasa ni yin haka ba sai tsoro da ni ke ji “ta yaya Ameera da ba za ta wuce 13years ba har ta san kallon blue Film?wane irin ƙawaye Ameera ke mu’amula da su a makaranta?shin dama can ta na kallo koko yanzu ne da Daddy ya bata waya aka turo mata?”wannan sune tambayoyin da ni ke yiwa kaina.

Jin motsin zubar ruwa alamun ta shiga wanka yasa ni saurin shiga ɗakin,wayar na ɗauka wacce ta aje kan bed da sauri na dawo falo “tashin hankali na furta a fili”ganin videos sun fi kala goma cikin wayar alamu sun nuna ta WhatsApp aka turo mata su.

Ɗaya na kunna na tsaya ina kallon ikon Allah yadda turawan ke iskancin su babu ko kunya,har tsawon 5mns vidéo ta ida saurin maida mata wayarta nayi ina mai tambayar kaina “to miye amfanin kallon?”dan kuwa ni dai Allah na gani ban ji wani abu wai shi désir ba,amman dan son sani yasa na turawa Nabee text kamar haka “`dan Allah wai minene amfanin kallon blue Film?sannan mi ya ke ƙarawa“` ba’a ɗau lokaci ba ta maido min da amsa “`domin nishaɗi da rage damuwa sannan za ki ɗan rage zafi da dattin mara“`🤪 tsayawa nayi ina ta juya kalaman ta a ma’auni amman sam na kasa fahimtar su wanda kuma lalle ina buƙatar ƙarin bayani.

 

 

Ina nan zaune Ameera ta fito cikin shirin doguwar riga ta atamfa ta cire uniforme ɗin makaranta,saurin kawar da idona nayi daga kallonta saboda wata irin kunyarta ma na ji……

 

 

 

Comment and share Please

 

 

Jikar Rabo ce

KARUWAR GIDA

“`LOVE and

ROMANTIC STORY“`

 

“`MRS SADAUKI

 

 

*PAGE 3-4*

 

Teddyna na kwasa na wuce bedroom,kan bed na zube na rungume sabon da Daddy ya sawo min ɗayan kuma sa ka shi tsakiyar ƙafafuna ban jima ba barci ya ɗauke ni.

 

 

A hankali ya fara kusanto da fuskar shi ga tawa wanda hakan ya sa bayi saurin lumshe idona,danshin yawun shi naji tare da saukar lips ɗin shi kan nawa.Ya ranƙwafo yayi min rumfa sai kuma yayi ƙoƙarin miƙewa da sauri na jawo shi hakan yayi sanadiyar ɓallewa batoran rigar shi wacce ta ɓoye sirrin cikar haibar shi, murmurshi na saki ina mai buɗe idona na zuba su ga fafaɗen ƙirjin shi wanda ya ke cike da gargasa.Hannu na kai na ɗora saitin heart ɗin shi wacce ina jiyo sautinta a duk lokacin da mu kayi kusa da juna,ina shirin ɗagowa na kalli fuskar shi kawai yayi saurin miƙewa tare da juya min ya fara takawa ya nufi ƙofar fita.

“Kar ka tafi ka bar ni please mafarkina ka tsaya na kalle ka”jin wani abu mai shegen nauyi ya sa ni firgigit na farka daga ɗan barcin da ya ɗauke ni,ture Ameera nayi wacce ta faɗo jikina ta na dariyar da ban san ta mice ce ba.

Kallona tayi ta na nuna ni tare da cigaba da yi min dariya,shiru nayi ina tunani nan take mafarkin da nayi ya faɗo min a rai wanda kuma babu shakka yau ma ɗin a bayyane nayi ta kiran masoyin mafarkina.

 

 

Ban tankata ba na jimƙe Teddyna ina mai jin wata irin kewa wacce ban san ta mice ce ba,kawai dai ina jin nayi missing wani abu mai muhimmanci da rayuwata ta ke buƙata.

Ina nan kwance har aka fara kiran sallah Asar na miƙe na ɗauro alwala na gabatar da sallah,haka ma Ameera ta zo tayi sallah dan gaskiya a gidan mu kowa na yin Sallah kan lokaci hatta da twins da ba za su wuce 8 years ba.

 

 

Da dare bayan duk mun gama dîner na wuce ɗakina,sai da nayi wanka sannan na saka spleeping dress uwanda suke dogaye ne masu rufe jiki saboda ɗan sanyin da aka fara.

Har na jawo Teddy zan kwanta na ga saƙon Daddy ya na kira na a ɗakin shi,miƙewa nayi wayata a hannu na nufi part ɗin shi.

 

Sallama nayi bayan an bani izini na shiga,a zaune ya ke kan sallaya alamun idar da sallar shi kenan ya na jan tazbaha.

Har ƙasa na durƙusa cikin sanyin muryata nace “Daddy ga ni”ɗagowa yayi ya ƙare min kallo tun daga yalwatacen gashin kaina wanda ya zubo kan kafaɗata har zuwa farcen ƙafata,wata leda ya miƙo min na karɓa ina jiran yayi bayani sai naji ya ƙyale hakan ya sa na ɗago dan ganin ko lafiya da sauri na mayar ganin ashe ni ɗin ya ke kallo.

 

Sai da yayi gyaran murya sannan yace “Mimi ga kaya nan na sawo maki,ki bar zama haka nan kin ji ko?”kai na jinjina ba tare da na buɗe ledar ba na gani “tashi kije ki tabbtar kin sha maganin ki”miƙewa nayi nace “toh Daddy mu kwana lafiya”.

 

Ina zuwa ɗaki na zazzage kayan, breziya ce wajen kala biyar sai wasu ƴan riguna ƙanana masu kamar bra ɗin sai dai su ba suda soso hasalima kamar dai riga suke.Cike da murna na ɗauki ɗaya na saka sai na ga tayi min tsaf kwanciyata ,ina jin Ameera na yaba bra ɗin kasancewar lokacin da na shigo ta na toilet.

 

 

 

Washegari tun da safe na shirya cikin uniforme ɗin makaranta dan yau mu na da lectur da na fi so wato English,a falo na fito inda na tarar tuni kowa ya na cikin shirin sa na tafiya school.

Gaishe da Daddy da Mami nayi na ja kujera na zauna,tea ɗin da Mami ta haɗa min tun tuni na ɗauka na fara sha,”Mimi in kin tafi school please ki kula da kan ki banda shiga wajen mai ƙura sannan ki guji duk abinda zai saka ki yawan dariya”cewar Daddy ya na mai aje spon ya na kallona, jinjina kai nayi nace “to Daddy in shaa Allah can ma kuskure ne”na faɗa ina ɗan ɓata fuska saboda ni kaɗai na san irin uwar wuyar da na sha da ciwona na asama ta tashi sanadin dariyar da su Nabee suka sa nayi,a ƙarshe sai kawo ni suka yi gida cikin mawuyacin hali.

 

 

Daddy na gamawa ya miƙe yace “in kun gama ku same ni a mota”da “toh”duk mu ka amsa yayinda Mami ta miƙe dan yiwa mijinta rakiya wanda ku san kullum sai ta kai shi har mota ta na yi mashi addu’a wanda hakan ba ƙaramar ɗaga tutar ta yayi kama daga mu ƴaƴanta har izuwa Daddy.

 

Abincin su Twins na ɗauka ko wace na saka mata a bag ɗin ta sannan na goya masu,kallon Ameera nayi wacce ke ta cin abinci kamar wata shanuwa nace “Malama ke mu ke jira”ta turo baki tace “ba ki ga abinci ni ke ci ba? “gaba nayi Twins na bi na a baya amman sai nayi saurin juyowa ina kallon su zuciyata na bugawa da ƙarfi,sam na tsani halin Mami na rashin kunya ba ta san inda za tayi abu ba ita babu ruwanta yanzu a tsakar gida ta wani shishigewa Daddy ta na sumbata da shafar shi ba ta tunanin akwai ƴan aiki in tace mu ƴaƴanta ne mai gadi fah da mai baiwa fulawa ruwa?ko da wasu su kan ce ki zama *KARUWAR GIDA* a gaban mijin ki ai ana sirrintawa.

 

 

Muryar Daddy naji ya na cewa “ina ita Ameerai?”ban juyo ba sai na ida gyarawa su Twins hijab ɗin su sannan na juyo na kalle su yanzu Daddy ƙoƙarin shiga mota ya ke yayinda Mami ta koma gefe ta ƙura mashi ido,ƙarasawa mu ka yi har yanzu zuciyata na bugawa.

 

Gidan baya na buɗe mu ka shiga kamar kullum,zuwa can Ameera ta fito ta shige gaba seat ɗin mai zaman banza.

Mami ta ɗaga mana hannu alamun bye bye dan ita ba ta zuwa ko ina,kullum ta na gida duk wata Daddy na yi mata salery.

 

 

Ni aka fara ajewa a ISB sannan aka wuce da su,Twins évangélique su ke yayinda Ameera ke Ɗan Koulodo kowa Sarki.

Da gudu Nabee ta tare ni ta na cewa “oyoyo my cakuleti”ture ta nayi ina hararenta nace “ba wani nan tun shekaran jiya da kika kai ni gida ba ki sake waiwayata ba sai yanzu za ki min murnar kare”dariya Nabee ta tuntsure da ita tace “ke rufa min asiri ba ki ga irin masifar da Mami ta dinga yi min ba wai duk laifina ne tunda na san yanayin ciwon ki,shi kuwa dear ɗina ina ji lokacin da ya ke cewa wace ƴar iskar ce Nabeela da har ta tayar mata da ciwon?”buge bakinta nayi nace “Nabee wlh ki fita idona in rufe kar ki sake yi min wannan wasar Daddyna ba tsarar ki ba ne da har za ki rinƙa kiran shi da chéri ki wannan ai cin kashi ne”gira ta ɗaga min tace “to sai mi dan ka cewa wanda kake so chéri ?wlh ni kuwa da zai aure ni da…”ban tsaya saurarenta ba na wuce classe dan kusan kullum sai tayi min hirar ta na son Daddy duka-duka sau biyu ne kawai ta taɓa ganin shi shikenan ta haukace da son shi da roƙona in bata number shi,ta yaya ma mai hali irin na Nabee zan barta ta raɓi wani nawa?macen da ta mayar da kanta *KARUWAR GIDA* kullum ta na cikin yawon bin hotel-hotel da gidajen rawa?.

 

Rungumo ni tayi ta baya tace “haba Fadimatuna miye na yin fushi da ni kuma a nan?” “Ba fah fushi nayi ba kawai na ga ba ki gajiya da faɗar abinda ko a mafarki ba zai taɓa yiyuwa ba”na faɗa ƙoƙarin ɓanɓare hannuwayenta da ta riƙe ni da su,tambayata tayi da “dan miyasa kika ce haka?”ba tare da shakka ko fargaba ba nace “saboda inganci da rashin sa ba za su taɓa haɗuwa ba”sake ni tayi ta dawo a gabana ta na kallona cikin ido tace “Ni kam sai na gwada maki ta yadda za su haɗu har su garwaya”ta na gama faɗar haka ta samu waje can ƙarshen classe ta zauna ta bar ni da faɗuwar gaba,tabbas na fi kowa sanin wacece Nabee duk namijin da ya burgeta to tabbas sai ta san yadda ta yi ta same shi.

 

 

Nabee kuwa shiru tayi ta na ta tunani ashe maganata ta daketa sosai taji haushinta,ni kuwa a gaba na zauna na fiddo book ɗina na fara dubawa kafin malami ya shigo.

 

 

Students sai zuwa suke a sannu yayinda kowa ke harakar gaban shi wasu kuma na hira,Nabee na tunani yayinda ni kuma ni ke révision.Babu jimawa duk students suka shigo aji saboda ganin teacher ya nufo ajin mu,”good morning class”cewar teacher lokacin da ya shigo duk amsawa mu ka yi.

Cours ɗin shi ya fara na koyar da mu halshen English saboda ko da wani patient ya zo mai jin language ɗin amman a zahiri babu ma anglais cikin programme ɗin karatun likita.

Question ya fara kamar kullum ni ce ke yawan amsawa ya na gamawa mushen science ya shigo,haka dai mu ka ta yin cours har lokacin récréation yayi.

 

 

Fuuu Nabee ta bi ta gabana ta wuce ba tare da tace min komi ba saɓanin yadda mu ke tafiya kullum,har ƙasan raina naji babu daɗi sai na kwashe Books ɗina na bi bayanta ina kiran sunanta amman ta share ni sai da nayi ta bata haƙuri sannan ta haƙura saboda muna matuƙar son junan mu.

 

 

***

 

“Anna wai Abba cewa Nasir yayi sai na gama jami’a sannan za’a yi maganar auren mu”cewar Fadila ta na mai kallon mahaifiyarta ta wacce ke tatar ƙulun koko,kallonta Anna tayi tace “eh jiya ma mun yi maganar da shi sai na ga hakan ne ya dace kin ga ki na gamawa sai ayi bikin daga nan shi Nasir ɗin ba sai ya nemo maki aiki ba tunda baban shine shugaban ɗalibai?”cike da takaici Fadila ta dubi Anna tace “yanzu ke ma kin yarda Anna?in yi ta zama a har sai nan da wata shekara biyar alhalin ina cikin shekara ta Ashirin da bakwai a duniya?”tatar kokon Anna ta aje tace “Fadila kin san ciwon kan ki kuwa?ana son yi maki gata ke kuma ba ki gani?duk faɗin gidan nan wa kika ga yayi dogon karatu in ba ke ba?ina ce saboda kiyi karatu mu ka sayar da komi na mu dan inganta rayuwar ki,kishiyoyina najin haushin ba ƴaƴan su ba ne ke kuwa ki na baƙin cikin ɗan farin cikin da ni ke burin samu”da sauri Fadila tace “subahanallah haba Anna ta yaya Ƴa za ta yi baƙin cikin mahaifiyarta?”

“Eh ga shi kuwa ke ki na yi min,yanzu in Allah ya sa kun kammala karatun ki kin samu aiki mai ƙwari ai shikenan sai ki saya mana sabon gida mu samu mu fita daga cikin na laka”sororo Fadila tayi ta na kallon Anna kafin ta miƙe ta shige ɗan ɗakin su na laka wanda tsabar tsufan shi har ya fara tsatsagewa.

 

Nasir ta kira ta shaida mashi yadda suka yi da Anna “Fadila gaskiya ba zan iya zaunawa har 5years ba tare da aure ba,kin fi kowa sanin yadda ni ke son ki”cikin kuka Fadila tace “dan Allah Nasir kar kace haka wlh mutuwa zan yi in ka rabu da ni”cikin ɗan ƙasa da murya yace “naji zan jira ki amman da da sharaɗi”da sauri tace “na yarda minene sharaɗin?”Nasir yace “ki bari har mu haɗu school zan faɗa maki”….

 

 

Comment and share Please

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment