Littafan Hausa Novels

Kanwar Matata Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Kanwar Matata Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

K’ANWAR MATATA

 

_Matar Sayyadee_

_Wattpad @Matar_Sayyadee_

 

 

_K’anwar Matata ba kirkirarren labari bane! Sai da na samu yarda da aminta sannan na soma rubuta shi. Dan haka idan yayi shige da naki irin labarin, arashi aka samu. Sannan ina gargad’i da babbar murya, ban yarda a juya min labari ta ko wani siga ba, ba tare da izini na ba ko kuma a d’aura min a YouTube!_

 

_Complete ne ga masu buĆ™ata. It’s only 1k via 0592412800 Zulfau Saeed GTbank sai ki tura shaidar biyanki zuwa 08128755583_

 

 

Page 1

 

Kuka take yi sosai a gaban doctor d’in tana fad’in, “Na rantse da girman Allah doctor ban tab’a yin sex ba a rayuwa ta! Ban san ta yanda aka yi wannan ciki ya shiga ba. Sai dai idan ture aka yi min.” Shuru doctor Kamal yayi yana kallonta irin kallon ta raina masa hankalin nan. Daga shigar jikinta gaba d’aya ya fahimci ita d’in ba mai kamun kai bace. Wando ne pencil a jikinta sai monkey jacket d’in da ta daura a kai. Kanta kuwa wani uban kitson attachment ne wanda aka yi mata shuku _Ghana weaving_ dashi kalar maroon da bak’i. Gaba d’ayanta bata yi kalar mutunci ba. Hatta k’umbar hannunta artificial ne irin zaro-zaro d’in nan. Gashin idanunta ma artificial d’in ne suma zaro-zaro dasu. Kallon results d’in dake hannunsa yayi wanda ya nuna masa 2weeks pregnancy a jiki sannan ya kuma d’agowa ya kalleta tare da mik’a mata yana fad’in, “Scanning machine ba zai tab’a maki k’arya ba! Sau uku kenan ina tura ki kina yin scanning, na k’arshen nan ma da kai na naje nay maki saboda confirmation. Amma still the results is same. Dan haka, ya rage a gare ki da ki koma kiyi tunani da kyau a inda kika samo cikin jikin ki. Lot’s of patient are waiting outside. I’m done with you!” Fad’in doctor Kamal yana nuna mata hanyar waje. Don tuntuni yake ta danne fushinsa.

Muna Daki Hausa Novel Complete

 

Ya tsani yaga mace mara kamun kai a rayuwarsa. Wani irin kuka ta kuma fashewa dashi tare da fad’in, “Please doct….” Bata kai ga k’arisa maganar ba ya nuna mata k’ofa a fusace tare da fad’i, “Out of my sight right now before I call security to throw you out. Y’an iska yara k’anana daku sai biye-biyen maza saboda abun duniya. Sai bayan sun d’ura maku ciki sai kuzo kuna mana kuka wai baku san ta yanda akai kuka yi cikin ba saboda kun raina mana hankali. Idan kuma aka sakar maku fuska sai ku fara rok’o akan a zubar maku da cikin. Dama Allah ya rik’a d’aukar rayuwar ku lokacin da ake k’ok’arin cire maku cikin. Y’an iska kawai!” Doctor Kamal ya fad’i. Ita kuwa tun lokacin da ya buga tsawa na farko tayi saurin d’aukar handbag d’inta da paper d’in da ya turo mata ta fita da sauri gabanta na fad’uwa don ta tsorata sosai da yanayin doctorn. Fita tayi daga asibitin gaba d’aya. Sai da tayi nisa da asibiti sannan ta nai mi wani waje gindin bishiya ta zauna tana kuka sosai.

 

Wata mota ce tazo ta wuce ta gabatar da gudu, can kuma motar ta dawo da baya da baya har inda take. Sauke glass mai motar yayi tare da fad’in, “Sssss, hi babe! Wani irin d’agowa tayi tare da watsa masa harara sannan ta mai da kanta tsakankani cinyoyinta tana kuka. Mai motar kuwa yaja motarsa ya bar wajen ya bar mata k’ura. Tashi tayi ta soma tafiya a hankali dai-dai lokacin da aka yi wani irin tsawa alamar hadari ya had’u sosai. Da sauri ta kalli sama taga gab ake da a tsuge da ruwan sama. Bata damu ba ta cigaba da tafiya. Ko taku biyar bata yi ba aka tsuge da tuwan kamar da bakin kwarya. Bata fake ba ta cigaba da tafiya a k’afa, don ji take dukan ruwan kamar shi zai yaye mata halin da take ciki. Sai da taga bata iya ganin gabanta da kyau sannan ta samu wani d’an rumfa da few mutane ke tsaye a wajen wanda kusan gaba d’ayan su y’an achab’a ne da passengers.

 

Ruwan nan ya kai tsayin awa guda kamun ya sassauta saboda lokacin gab da magriba ne. Yayyafi ake yi irin wanda zai iya jik’e jikin mutum jagab. A hakan ta kuma shiga ruwan ta dunga tattakawa. Duk da irin nisan da gidansu ke dashi haka ta tako a k’afa tun daga wani k’aramin private hospital dake fire brigade dake tudun nupawa har Jos road by Abeokuta Street. A wannan lokacin har d’iga take yi tun daga tsakiyar kanta har cikin pant d’inta. Ko da ta tura k’ofar gidan su ta shigo, babu kowa a tsakar gidan as she expected, sai tayi saurin shiga d’akinsu. Kwance ta taras da Na’ima a kan gado tayi d’ai-d’ai tana waya sai mulmula take yi from edge to edge d’in gado.

Kallo d’aya tayi mata ta d’auke kai tare ajiye handbag d’inta a kan side drawer sannan ta soma cire boyfriend jacket d’in jikinta ta ajiye a gefe ta zame dogon jeans d’in jikinta ta kasance daga ita sai pant sannan ta nufi wajen wardrobe ta d’auki zani ta d’aura a k’ugu sannan ta zame pant d’in jikinta ta cire tare da unbuttoning shirt d’in jikinta ta cire har da bra sai ta ja janin sama. Zare ribbon d’in kanta tayi ta had’a da jik’ak’k’un kayan da ta cire ta saka a wani bokiti yellow mai tambarin Maggi Star da ba ruwa a ciki sannan ta dauki towel wanda ke hannun wardrobe ta rufe kanta tare da d’aukar butanta da babu mai tab’awa a cikin gidan ta fita ta nufi bayin su dake tsakar gida tayi fitsari ta kama ruwa ta fito daga bayin ta d’aura alwala sannan ta koma d’akin. Wardrobe d’in ta bud’e ta d’auki doguwar riga jallabiya ta saka.

 

Towel d’in da ta fita dashi kuma, ta yi amfani dashi ta goge jik’ak’k’an attachment d’in kanta sannan ta dauki hijjab ta saka tare da shimfid’a darduma ta tada sallar magriba. Har ta idar da sallah Na’ima bata gama waya ba, kuma babu abunda take fad’i sai dirty talks ita da wanda take wayar dashi. Juyawa tayi ta kalleta for 3seconds sannan ta cire idanunta ta mayar kan kwan fitilar da ya kawo haske a d’akin alamar an kawo wutan lantarki.

 

Mik’ewa tayi ta nannad’e dardumar ta mayar inda yake sannan ta cire hijjab d’in jikinta ta ninke ta ajiye sannan ta dauki kettle ta cika ruwa a ciki ta jona. Tana jonawa ana d’auke wuta kamun kuma tayi wani yunk’uri suka sake dawo da nepar. Hamdala tayi a cikin zuciyarta sannan ta bar wajen ta dawo kan kujera one sitter dake d’akin guda d’aya tal ta zauna tare da had’a kai da guiwa tana tunanin ta ina ciki ya shiga jikinta ba tare da d’a namiji yayi penetrating a jikinta ba. Wasu hawaye masu zafi suka shiga gudu a kuncinta.

 

“What I’m doing to tell him now? Our marriage is in 4weeks now. Kuma nayi masa rantsuwar ban tab’a sanin wani d’a namiji ba a rayuwata. Sai kuma ga ciki yanzu! Ta ina zan fara yi masa wannan bayanin ya yarda dani. I’m dead! Shikenan wannan ma zai gudu kamar sauran. Nima bazan tab’a aure ba kamar sauran y’an uwa na. Na shiga uku na!!” Ta fad’i a cikin zuciyarta tana hawaye daidai lokacin da ta soma jin wani shuuuuu alamar ruwan da ta saka a kettle ya soma tafasa.

 

Cikin sauri ta isa wajen ta kashe socket d’in sannan ta zare igiyar kettle d’in tare da d’aukar kettle d’in ta juye ruwan zafin a cikin wani bokiti ta fita ta nufi wajen pampo ta kunna ruwa. Kasancewar ruwan na zuba da uban gudu, sai take yi tana saka hannunta domin jin yanayin zafin ruwan. Kashe pampo d’in tayi bayan yanayin zafin ruwan yayi mata ta d’auki bokitin ta kai ruwan bayi sannan ta dawo d’akin ta d’auki soso da sabulun wankanta ta fita, kuma har lokacin yayarta Na’ima bata gama wayar da take yi da saurayinta ba.

 

Bayan kamar 15mins ta fito daga bayin dai-dai lokacin da mahaifiyar su Lami ta fito daga nata d’akin tana fad’in, “Sarah, ashe kin dawo cikin gidan nan shine baza ki iya zuwa d’aki ki fad’a mi kin dawo ba saboda bak’ar mugunta irin naki! Duk saboda kar ki sammun abunda kika samo ko? Dad’in abun ba ke kad’ai na haifa ba” Turo baki Sarah tayi tare da fad’in, “Ni fa Lami asibiti naje ba wani waje ba.

 

Allah ya kiyaye inyi yawon banza.” Rik’e baki Lamin tayi tare da fad’in, “Iyeeh! Za kici ubanki ne shegiya asararriyar yarinya. Da kyawun ki zaki je ki lalata kanki. Uban wa kika ga yayi aure a cikin yayyinki su hud’u gasu nan kina gani? Kuma a cikinsu babu wacce bata kawo abun arziki cikin gidan nan. Ku shidda mata Allah ya kashe ya bani domin ya wanke min bak’in cikin da mahaifin ku ya saka min a zuciya shekara da shekaru. Amma babu wulak’antacciya mara mutunci da rashin son cigabar uwarta sai ke Saratu! Kai Allah yayi wadaran naka ya lalace. Kin nane a jikin namiji guda d’aya, d’an iska yaron da ba wani abun arziki gare shi ba. Kin kafa k’ahon zuk’a shi kike so sai kin aure shi, to don ubanki shine ajalinki da y’an k’ananun shekarunki. Yaro d’an iska sai fankama shi ba uban kowa ba. Zan ga yanda za’ayi auren nan wallahi.

 

Zaki ci uban ki! Dani kike zancen.” Da kallo Sarah ta bita har ta shige d’akin da shine mallakin mahaifin su a gidan. Ta jima tsaye da bokiti a hannu sanyi na busata kamun ta ja k’afafunta da suka yi mata sanyi ta shige d’akin su.

Turus ta tsaya lokacin da ta d’aga labule tana kallon Na’ima wacce ke rik’e da takardar result d’in dake nuna Sarah wanda ke nuni da tana d’auke da juna biyu. Cikin sauri Sarah ta fad’a d’akin tare da warce takardar a hannunta tana mai hararar Na’ima. Na’imar ma hararan take maka mata tare da fad’in, “Munafuka annamimiya! To yau asirin ki ya tonu. Ashe kema shek’e ayar ki kike yi a wajen, amma idan kin shigo gida sai ki rik’a nuna kamar ke ta Allah ce. To yau dai asirin ki ya tonu. Kuma wallahi sai na fad’awa Lami.” Tana fad’in haka tayi saurin sauka daga kan gadon ta bangaje Sarah ta fice daga d’akin tana kwala kiran sunan Lamin. Da sauri Lami ta fito daga d’akin mijin nata tare da fad’in, “Lafiya haka Na’ima kike kwala min kira? Ko wani abun alkhairin ne ya same mu” fad’in Lamin dai-dai lokacin da Nuratu, Hassana da Marfu’a suka fito suma suna tamabayar lafiya.

 

Na’ima kuwa wani shewa tayi tare da nuna k’ofar d’akin su inda Sarah ke ciki tana mai fad’in, “Yau dai anyi walk’iya a cikin gidan nan. Mai mana gori da mun aje y’ay’an shegu ita ma tana gab da ajiye maki shegen jika.” Ta k’arisa maganar tana mai kallon Lami da ta saki baki tana kallonta. “Ke ban fahimta ba, fitar damu cikin duhu dan Allah Na’ima.” Fad’in Nuratu.

 

Sai da Na’imar tayi wani shegen gud’a sannan tayi nuni ta baya izuwa ga d’akin su tace, “Ustaziyar gidan nan dai ciki ne da ita. Dama kwana biyun nan kullum sai inga tana ta kuka, idan ta tambayeta mai ke damunta, sai tace min babu komai. To yau dai bayan ta fita zuwa bayi domin wanka, sai na bud’e jakarta don in d’auki turarenta in fesa saboda Ajeeb ya kira ni yana k’ofar gida, kawai sai ganin takarda nayi a ciki, shine na fiddo na bud’e, nan kuwa nayi arba da ciki har na sati biyu a jikin takardan.

 

“Gaba d’aya wani irin shewa suka d’auka dashi har da tafawa. Nuratu tace, “Zancen gori ya k’are a cikin gidan na. Wallahi Lami yarinyar ta k’ara min rashin kunya ko kuma ta dukan mu y’ay’ana a cikin gidan nan sai naci uwarta yasin.

 

Shegiya y’ar iskan yarinyar mai mugun hali. Dama fa ni Lami tuntuni na gane Sarah tana biye-biyen maza a waje. Abunda ya saka take nuna mana kamar bata yi, duk dan saboda kar ta kawo wani abu cikin gidan nan ne a amfana da ita saboda bak’ar rowarta da mugun hali. To yanzu dai anyi walk’iya. Wallahi duk abunda kike fita kina samowa sai kin fito dashi kowa yaci a gidan na. Tun da muma duk abunda muka samo dake ake cinsa. Ehe! “Sai a lokacin Lami tayi magana, “Lallai yau naga abunda ya girmi kakana! Dama haka halinki yake Sarah? Lallai! Dama ance makashin ka na tare da kai.

 

Wai ni yau y’ar da na haifa da ciki na ce take kyamatar bani abunda take fita tana samowa. To Wallahi fitowa za kiyi fi fad’a min uban da yayi maki ciki, don billahil lazi bazan kyale sa ba, list zan yi masa na abubuwan da zai kawo cikin gidan nan. Don ba zai yuwu in ciyar da ku y’ay’ana ba, kuma sannan in ciyar da y’ay’an ku ba.

Ko su y’an uwanki da kika ga ina d’awainiya da y’ay’ansu, biyana suke yi su da samarin nasu. Ki fito don ubanki Nuhu kamun nazo d’akin nan na idda ke!”

 

 

 

_Ya kuka ji labarin?_

 

 

08128755583 WhatsApp only!

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment