Littafan Hausa Novels

Kaddarata Ce Haka Hausa Novel Complete

Auren Yarinta
Written by Hausa_Novels

Kaddarata Ce Haka Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

ƘADDARATA CE A HAKA

©Maryam Abdul’aziz.

MAI_ƘOSAI.

 

P__1

 

Bisimillahir Rahmanir Raheem.

 

 

Zaune take gefen kan lafiyayyan gadonta. Hannuwanta duka biyu shimfide bisa kan kyakkywan kuncinta. Kallonta a haka kaɗai ya isa ya gamsar da kai cewar lallai tana cikin matsananciyar damuwa. Hawaye ne suke gangarowa daga cikin kurmin idanuwanta zuwa kan dandamalin fuskarta.

 

Mutunta Kai Hausa Novel Complete

” Me ya sa gwaggwo da Baffa za su yi mini haka?? Me ya sa suke son saka ni cikin Wani hali? Me ya sa ba za su bar ni na aure Wanda zuciyata ke da muradi ba? Su ne maganganun da ke reto a cikin zuciyarta. Kuma tabbas tasan lallai babu mai amsa mata waɗannan tambayoyin sai su. Hakan ya sakata miƙewa daga zaunen da take zuwa tsaye tare da saka kai ta fice daga d’akin.

Gwaggwo na zaune kan kujerar tsugunno a tsakar gida,tana yankan farce, ta kalle ta tare da furta,

” Gwaggwo don Allah ki daɗa yiwa Baffa bayani akan lamarin nan  nasan idan yaga kin daɗa dagewa akan batun zai duba lamarin nan nawa don Allah. Ni Wllh ban san me ya sa bakwa son aurena da yaya Nasir ba? Wai Gwaggo wani laifi ya aikata muku haka da ba za ku iya amsar shi ba? Me ya yi muku da ba zaku ƙauna ce shi ba?”

Gwaggo ta dubeta a karka ce kafin takai ga cewa,

” Ai hakan da kika yi yana da kyau kizo ki tutsiye mahaifiyarki akan wani ƙaton gardi ko? Kema ai za ki iya zuwa ki sami shi gyatumin naki ki yi masa magana ,sai ya fi jin maganarki ma akan ni, sai dai ina so ki sani tunda muke bamu ta’ba ƙin wani d’an Adam ba, amma ki sani munsan mahimmancin *alƙawari*”

Tana kaiwa nan ta mayar da magananta kan yankan farcen da take yi ba tare da ta ƙara ce mata komai ba.

Ita kam ganin yadda Gwaggon ta harzuƙa ya saka ta miƙewa ta koma d’akinta , tabbas tasan da man Gwaggon na ta ba za ta ta’ba goya mata baya ba, amma ta bawa zuciyarta amanna da abin da take son aikata wa yanzu.

Cikin sauri ta miƙe tare da faɗawa bayi shaf-shaf ta watsa ruwa ta fito, ko mai ba ta tsaya shafawa ba da yake garin ana zafi, kayanta ta sanya tare da zarar mayafinta ta fice.

Har lokacin Gwaggo na zaune inda ta barta, kallonta ta yi kana ta ce ” Gwaggo ni zanje wajen Inna , ba dad’ewa zan yi ba”

” Ki yi sauri dai ki dawo, in kika jima har Baffanki ya rigaki dawowa to tabbas zance ban ma san kin fita ba. Kin ji ko?”

Zun’buro baki ta yi kana ta ce ,  ” Kai Gwaggo! To ayi mini sassauci kada a ce haka”

” Oho miki ki tsaya kar ki tafi” Gwaggo ta fad’a.

” In banda ma kisa baiwar Allah surutu ni banga uwar abin da za ki je yi a can ba”

” Ni dai na tafi, sai na dawo ”

Ta fad’a tana mai ficewa daga gidan.

” ki gaisheta ” gwaggon ta fad’a tana d’an daga sauti yadda za ta jiyota.

 

**********

Tafiya take yi sannu a hankali duk da wani sashe na zuciyarta a cunkushe yake da abin da iyayen nata suke son yi mata amma hakan bai sakata kasa tunawa da mafi soyuwar abincin ruhinta ba.

” My one”

Kamar daga sama haka ta jiyo sautin zazzaƙar muryarsa wacca ba za ta ta’ba manta mai ita ba balle ita kanta muryar. Caak ta tsaya tare da juyowa ta fuskance shi cike da murna da annushuwar ganinsa da ta yi ,dan sosai ta yi matuƙar kewarsa.

Ya d’an matso kaɗan kusa da ita har suna masu shaƙar numfashin junansu kafin ya kai ga cewa, ” Hankalina ya gaza kwanciya musamman yanzu da naga duk kinyi wani iri My, naga fuskarki kamar kinyi kuka me aka yi miki? Me yake faruwa dake?”

Kallon shi ta yi tare da son daidaita nutsuwarta, kana ta ce da shi,

“Kai yaya Nasir waya ce ma na yi kuka? Ni ba abin da ke damuna babu komai”

Ƙara kallonta ya yi na wasu ‘yan sakanni kana ya ce,

” Gaskiya ban yarda ba, tabbas akwai abin da gimbiyar tawa ke son boye mini ko ma take kan ganiyar ɓoye min , ma za fad’a mini ko sai na yi miki kuka?”

Ya karashe yana mai langwabar da kai.

Sanin halinsa wanda indai ba fad’a masa ta yi ba bazai ta’ba barinta ta wuce ba ya sanyata rausayar da kai kana ta ce,

” Ya zan yi yaya Nasir? Tabbas ina cikin damuwa ba kaɗan ba , sanin kan kane idan na rasaka bazan iya rayuwa ni kad’ai ba. Ina sonka yaya Nasir son da bana yiwa kaina shi, sai dai har yanzu Baffa da gwaggo sunƙi amince wa da kai amatsayin wanda zuciya da gangar jiki ke muradin kasancewa tare da shi, ta yaya hankali na zai kwanta? kasan abin da ba zai ta’ba yiwu wa ba ne yaya Nasir”

Ta karashe tana mai share kwallar da ta gangaro mata zuwa kan kundugugin kuncinta.

Nasir ya kalleta cike da boyayyen tashin hankalin da ya sake yi masa ƙawanya yanzu,  tabbas suna son junansu sosai iya matuƙa gaya, shi kansa ba zai ta’ba san cewa ace yau basa tare da junansu ba in har dai ba mutuwa ce ta riski ɗayan su ba, sai dai yaya zai yi? yardar iyaye ita ce yardar komai cikin rayuwarsu.

Cikin tattausar murya ya ce ” Na sani my one, na san muna son juna sosai, sai dai ba yadda muka iya har sai iyayen mu sun yarda da maganar mu, har sai sun amince mana sannan zamu iya zama abu d’aya, amma insha Allahu muna tare da juna zasu amince mana babu kuma wanda zai rabamu”

“Shi kenan yaya Nasir na ji amma wallahi muddin Baffa da gwaggo suka ƙi amincewa to na rantse zasu sami gawata a koyaushe kuma a kowanne irin lokaci”

Cikin sauri Nasir ya tare da fadin, ” Haba my one , karki kuma fad’ar haka, Ni na san abin da su Baffa suke yi me kyau ne akan mu, dan haka mu jiraye hukuncinsu, amma kada mu yankewa kanmu danyen hukuncin da ƙarshensa ba zai yi mana kyau ba.

A hasale ta kalle shi tare da mayar masa da raddin…

 

Yawan comment, yawan typing. Ba Hannun banza gareni ba ehh.

 

Mai Ƙosai.

*ƘADDARATA CE A HAKA*

©Maryam Abdulaziz

MAI ƘOSAI

 

 

P__2

 

” Amma me? Yaya Nasir kada ka ce mini za ka rabu da ni, ka da ka ce min ka shirya rabuwa da ni plz don Allah, kar ka sake na ji wannan gubar maganar daga bakinka”

Nasir ya ce ” Haba my one ni fa ban ce zan rabu dake ba, kuma ban shiryawa hakan ba ko da da second daya ne, ina sonki my one har abada kece matata duniya da lahira kin ji share hawayen ki”  ya ƙarasa cikin sigar san kwanatar mata da hankali.

“Shi kenan har naji dad’i, da zuciyata ta fara harbawa da sauri da sauri, ni ma ina sonka kuma ko wanne bugun numfashina yana fita ne tare da naka”

Sai da ya ta’ba saitin zuciyarsa sannan ya ce ” Wow! Godiya nake yi sarauniyata, wai ina zuwa hakane ma? Ni ban tambaya tun farko ba”

Murmushi ta yi kana ta ce ” zanje wajen Inna, bari na wuce”

Shi ma murmushin ya yi kan ya ce,

” Ki ce za ki hana kakus sakat, to muje na dan taka miki”

Turo baki ta yi kafin ta ce,

” Au haka ma za ka ce, ba na son rakiyar ”

“Tuba nake ranki shi dad’e muje ko”

Har ƙofar gidan Inna ya rakata sannan suka yi sallama ya wuce shi ma yana jin cewar in sha Allahu babu wanda zai raba shi da my one ɗin sa.

Gidan ta shiga haɗe da yin sallama, zaune ta hango inna tana aikin gyaran lamsir dan Inna akwai masifar san kwaɗon lamsir shiyasa koyaushe take cikin cin sa da aikinsa.

Ƙarasawa ta yi wajenta tana fad’in ” Oh! Inna ke kam kullum cikin aiki bakya gajiya, yawan aiki fa yana jawo tsufa da wuri, ki bari ki tsufa ni kam ba ruwana wllh” ta ƙarasa tana dariya ƙasa-ƙasa.

Inna ta kalleta kana ta ce ” NURI kinci gidanku, yarinyar kamar Aku,  cha-cha haba ,yo to in ban yi aikin ba kanki zan yi , zama waje ɗaya ai babu dad’i ”

Haɗa rai ta yi kafin ta ce ” Ni dai Inna kinga kin yi fura ki ba ni. (tana tsananin San fura) kuma nasha gaya miki ni ba suna na NURI ba in ba za ki ce *NURIYYA* ba to ki barshi mana an yafe mene ne wani Nuri ko daɗin ji babu.

” Yo ni na ga ikon Allah haka nan na yi niyya kuma na iya faɗa, kisa zare da allura ki dinke bakin ka ji min ‘ya da tsurfa” Cewar Inna.

Nuriyya ta ce ” Ni dai ki ba ni fura nasha inda akwai” ta ƙarasa tana turo bakinta.

“In kuma na ce Babu fa” Inna ta fad’a.

Cikin washe baki Nuriyya ta ce “Ah! nasan ma akwai don Allah ki ba ni

Inna ta ce ” Allah ya aiki na yi ‘yar nema je ki dakko tana firinji”

Miƙewa ta yi ta ƙarasa falon ta bud’e fridge din ta dakko, ai kam ta yi sanyi sosai. Kusa da ita ta dawo ta zauna ta hau Shan kayan ta ba tare da ta ƙara cewa innar komai ba.

Sai da ta shanye furar tatas sannan ta kalli Inna ta ce ” Inna don Allah ina roƙonki ki yi mini wani abu guda d’aya, kinsan duk abin da za ki faɗawa Baffa ya yi baya tsallakewa, ke kaɗai za ki gaya wa Baffa yaji , don Allah Inna kisa baki ya amince da aurena da yaya Nasir don Allah”

Inna ta ce ” Me? In yi me ? Rufa mini asiri, kin san halin Baffan ki indai ya yi magana baya canzawa ko ni bana iya dakatar da shi, dan haka ki yi haƙuri ki rungumi ƙaddarar ki

Cikin marairaicewa Nuriyya ta ce ” Inna don Allah ki yi magana da shi nasan in kika saka baki to zai canza maganar shi”

Inna ta ce ” kayya dai ‘yar nan bar halin Baffan ki , ki yi dai haƙurin da na ce za ki ga riba mai yawa aciki”

“Inna ni fa na riga na gaya muku yaya Nasir nake so , kuma shi kad’ai nakejin zan iya rayuwa da shi, dan Allah Inna ki yi wani abu a kai”

“Allah me iko , har ya kawomu lokacin da yarinya za ta ce ga wanda takeso, mu sa’adda akai mana auren munsanma mazajen namu ne ma, kuma kinsan dai ba kyau karya alƙawari , dan haka kin san babu yadda Baffan ki zai karya alƙawarin da ya d’auka, ba dan ma tsaye-tsaye da shirirta irin tasa ba , da su dangin Idirisun sun so ace tuntuni aka yi auren, amma ya biye miki sai kinyi karatu ga shi nan ai”

“Inna ba alƙawari tsakanin aure, idan ‘ya’yan suka taso basason juna fa, haba inna yanzu zamani ya sauya, kuma idris ɗin da kike gani abokin yaya Nasir ne nasan zasu fahimce juna sosai, kuma ni Inna ba fa son shi nake yi ba, na riga na gaya masa tuntuni”

” Shi ke nan , naji Nuri ta, zan yi iyakar ƙoƙarina wajen shawo kan na shi”

Cike da farin ciki Nuriyya ta rungume Innar ta ce ” kai Inna wllh kin ga mai mini komai innata Allah ya tsundu min ke a aljanna”

Inna ta ce ” Naji ɗaga ni uwata, daman kinzo ne dan ki lallasani kawai ko”

Nuriyya ta ce ” Wa? Wace  ni? Ina sam, ni ina na kema da ƙwarin ƙashin da zan iya karya ‘yar tsohowa.

“Au haka kika ce to na fasa.” Cewar Inna.

 

Comment and share.

 

Mai ƙosai.

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment