Jinkirin Aure Hausa Novel Complete
_JINKIRIN AURE_*
*_Ƙalubale ga ƴammata_*
*By*
*Oum Hairan*
*Dedicated to*
Dr Mass Agadas son so for ever.
*P 1-2*
Iska ce ke kaɗawa ta damuna me cikakken sanyi da sanya zuciyar da take cikin kwanciyar hankali a nishaɗi, yayin da zuciyoyin da suke cike da zullumin damuwa suke kasancewa da sassaucin yanayi.
Saidai a gurinta itan wannan yanayi yafi mata kowanne yanayi zafi, rayuwarta ta ƙuntata hawayenta ya yawaita ƙuncin zuciyarta ya ƙaru a yayin data keɓance kanta ita kaɗai a madaidaicin office ɗin nata me ɗauke da table me kujera ɗaya, gabanta cike yake da files-files na petiant ɗinta na yau data gani inda gabadayan hankalinta yabar gangar jikinta a zaune saman kujerar lokaci zuwa lokaci hawayenta ba diga saman takardar dake gabanta.
Ƙwankwasa ƙofar akayi har karo uku dake hankalinta baya jikinta batasan anayi ba, jin shirun ne yasa me neman izinin turo ƙofar tare da sallama ta shigo cikin office ɗin ta tsaya ta zubawa Mamallakiyar office ɗin idanu tana mamakin abinda yake sanyata shiga matsananciyar damuwar da har hankalinta yake gushewa haka.
Dukan Table ɗin Dr Zaheera tayi abinda ya dawo da wadda ke zaunen cikin nutsuwarta tayi saurin sa handcap ta share idanunta ta ɗagosu ta zubasu kan Dr Zaheera itama ita take kallo harta isa ga wata kujerar ta zauna suna facing ɗin juna.
Dr Zahira ce ta kawar da shirun da cewa “Kullum kin kasance cikin damuwa kin takuri kanki kin tsawwala kanki Dr Madinah meye yasa hakan ne? Meyesa kike mantawa duk abinda ba’a fareshi akanka ba bazaa ƙare shi akanki ba?”
Manyan fararen idanunta ta lumshe ta kwantar da kanta saman kujerar da take kai hawaye na tsiyaya daga kwarmin idanunta tasa tisue ta goge dogo hancinta
“Meye ne matsalata meye ne aibina meye yasa kyawuna ya kasa samar min da mijin aure, meyesa kullum al’umma basamin adalci suke ganin cewar nice naƙi aure bayan Nima nafi kowa son na ganni cikin dausayin sunnar ma’aikin Allah???
Tambayar da kullum nakewa kaina kenan”
Mijin Kwaila 2 Complete Hausa Novel
Cewar Dr Madinah dake ɗagowa tana zuba idanunta akan ƙawarta Dr Zahira, shiru Dr Zahira tayi na ɗan lokaci sannan ta buɗe baki tace.
“Dr Madinah ba jama’ar gari da suke ganinki daga nesa ba ni kaina da nake da kusanci dake lamarinki yana bani mamaki gani da sani a damuwa da tunanin meye dalili? Madinah kyawunki yakai ace kina juya ragamar maza a hannunki sai kuma ya kasance maza sune ƙaddararki, ta yaya zan yarda ace mu da bamu kai ba maza na zumuɗi akanmu ke da kika wucce kice babu wanda ya taɓa cewa yana sonki?”
Murmushi me ciwo Madinah tayi tana kai dubanta ga agogo ta miƙe ta fara harhaɗa files ɗin ta sanyasu wajen adanasu ta ɗauki jakarta ta dubi Dr Zahira tayi gaba tana cewa “duk sanda na tsaya tuntuntunin abinda kike tunani yanzu Zuciyata zafi takeyi Zahira ni kaina na fara tsoron kaina ina tunanin to ko wani abune ke gareni abin gudu da Ni na kasa ganewa, Zahira shekaruna sun fara tafiya a matsayina na ɗiya mace ba namiji ba ace na zubar da shekaru talatin da biyu batare da aure ba wannan abu da cin rai yake…..”
Isa sukayi bakin titin suka tari ɗan sahu suka hau ya fara sauke Zahira a kwanar unguwar su sannan ya wuce da Madinah tasu unguwar ya sauke ta ta fito tana gyara mayafin data yafa saman uniform ɗinta na aiki ta nufi unguwar tasu lokaci zuwa lokaci suna gaisawa da dattijan unguwar dake zaune a ƙofar gidajensu.
Gidansu ta shiga da sallamarta babu kowa a tsakar gidan hakan ya bata damar nufar ɗakin mahaifiyarta ta daga labulen tana cewa “Ammi sannu da gida” Ammi dake zaune a tsakar ɗakin ta ɗago tana duban tilon ɗiyar tata mace tace “Yawwa Munau Jaɓɓama” guri ta samu ta zauna tana yage mayafinta tace “Yau na gaji da yawa Ammi me kuka girka mana?” Numfashi ta sauke tace “Abinda kika tsana” dafe kirji tayi tace “Nashi na Ammi don Allah meye yasa kukayi alale?” Tana maganar tana kwalawa me aikinsu kira Bintalo ta ta rusuna a gabanta tace “meye kikeyi Binta?” Tana wasa da yatsunta tace “bsbu abinda nakeyi Uwarɗakina” fasali taja tace “ki samamin abinda zanci insjin yunwa gashi ku kun tashi kunyiwa mutane Alele” miƙewa Bintalo tayi ta fita bata jima ba ta dawo ɗauke da tire shaƙare da kwanuka ta ajiye mata a gabanta ta fara budewa tayi murmushi tace “wato wanani Ammi kikayi niyyar yi ashe ma My Favorite kukayi” murmushi Ammi tayi ta zuba mata ido tana kallon yanda take cin abincin a nutse da alama yunwa ta yini da ita yau.
“Munau” Ammi ta kira sunanta ta ɗago tana ajiye cokalin ta mayar da hankalinta ga mahaifiyar tasu Ammi tace “Wato Madinah kullum da wannan tunanin nake kwana nake tashi kullum da tunanin lokacin aurenki nake bacci nake tashi Madinah kullum shekarunki tafiya sukeyi girma ƙara sauko Miki yakeyi ke kuma abinda yake aranki shi kikeyi baki tunanin gobenki kin kasa tsayar da hankalinki ki samarwa kanki abokin rayuwa ki inganta kanki, Munau meye ne a gabanki daya danni sunnar ma’aikin Allah da tunaninki baya baki dacewa da cancantarki na kiyi ta? Aure shine martaba da mutuncin kowacce ƴa mace aure shine daraja da ƙimar kowacce mace ke ba iya mace ba hatta namiji aure shine ƙimarsa”
Idanunta da suke tsiyayar da hawaye ta sadda ƙasa taci gaba da kukanta me tafasa zuciya, wannan ya tashi hankalin Ammi tace “Ina mamakin yanda da zaran nayi Miki magana akan ingancin rayuwarki kike sanyani a gaba kinamin kuka Munau idan har maganar da nakeyi Miki ce bakiso zan iya tattarawa na daina amma ki sani da gaske ganinki a gabana bayamun daɗi kamar kowacce uwa Nima nafison ki rinƙa zuwar min da yawo kina komawa ɗakinki”
Hannu tasa ta tsane hawayenta ta ɗago cikin raunin murya tace “Wlh Ammi kullum ina addu’a mafarki da fatan zuwan wannan ranar amma taƙi zuwa, Ammi ya zanyi wannan rana tazone? Nima na zama matar aure cikakkiyar mace me ƴanci sannan me ji da alfarmar aure, Ammi ki daina ganin laifina kiyimin addu’a don Allah kema gani kikeyi kamar nice banason aure bayan auren ne yaƙi zaɓata Ammi kinsani tun kafin wannan lokacin wallahi tallahi bansan wani namiji ɗaya daya taɓa tarata ya buɗe baki yacemin yana sona koda wasa ba bare da aure, wai Ammi ya akeyi ake samun mijin auren nan ne Nima nayi ko na samu ki daina kallo na a me laifi….”
Ta ƙarashe maganar tana sakin wani kuka me gunji tare da kifa kanta a kafaɗar Ammi, cike da tausayawa Ammi ta shiga bubbuga bayanta da sanyin yanayi na mahaifiyar da taga ɗanta cikin halin tsanani tace “Shikenan Munau na fahimceki ki daina kukan haka Allah yanaji yana gani zai kawo mana mafita da yardarsa zanci gaba da yimiki addu’a kema karki gajiya wannan ita ce ƙaddarar mu, yawwa ɗazu baffan ku Sunusi yazomin da maganar haɗin aurenki da ɗan uwanki Khamal…”
A firgice ta ɗago tace “Ni kuma Ammi habadai Khamal kin manta waye Khamal Ammi ƙungurmin ɗan taba sannan ɓarawon kaji da awakin unguwa ace shine mijina? A’a nikam wannan zaɓin baimin ba nidai a tayani da addu’a nasan Allah bai manta dani ba Ammi”
[6/2, 9:15 PM] AM OUM HAIRAN: *_JINKIRIN AURE_*
*_Ƙalubale ga ƴammata_*
*By*
*Oum Hairan*
*Dedicated to*
Dr. Mass @gadas son so for ever.
*Free P 3-4*
_Normal 300 VIP 600 PC 1k acct details 3184512451 Fauziyya Tasiu First bank._
Tashi tayi ta nufi ɗakinta ta cire kayanta ta nufi bayi ta watsa ruwa tayi alwala tayi sallar magrib ta zauna tana karatun Kur’ani tana sharar hawaye, a wannan yanayi taji an buɗe ƙofar dakin nata an shigo an nemi guri an zauna bata ɗago ba Saida takai aya sannan ta rufe Kur’anin ta shafa addu’arta ta juyo tare dayin kasa da muryarta cikin girmamawa tace “Yaya Mus’ab kaine a daren nan ga gari yanata cida alamun ruwa zai sauka”
Fasali yaja yana cire hularsa yace “To ya zanyi Madinah kece kinƙi barinmu mu huta Baffa Sunusi ne yaje ya dameni da maganar aurenki da Khamal kuma yacemin lallai kafin azumin bana sukeson ayi komi a gama shiyasa nazo naji meye kike ganin zai yuwu?”
Tunda ya fara maganar take kallonsa tana girgiza kai batare da ta katseshi ba har ya gama sannan tace “Yanzu Yaya Mus’ab wannan shirmen maganar har takai ka hana kanka kwanciya cikin iyalinka ka fito da wannan tsohon daren?”
Murmushi yayi yace “Kullum ke raayinki bambam yakesha da mutane Ni abinda yasa naga dacewar nazo mu tattauna naga ba duka abinda rai keso take samu ba musamman a wannan bigiran Madinah kinsani ni bana cikin mutanen da zasu kawo Miki mafita domin cutarwa a gareki, nayi ɗawainiya da rayuwarki tun yarinta kawo lokacin da kika zama mutum kike iya yiwa kanki abubuwa da suka shafi rayuwarki.
Inason ki tsaya ki ɗauko hankalinki ki tattarashi waje guda ki duba yanda rayuwar take tafiya kiyi hƙr ki karɓi wannan zaɓin kiyi addu’a wata ƙila shine alkhairin daya hana wani zuwa ke kuma kikaƙi karbarsa tun kina ƙarama”
Idanunta ta ɗago daya ciko da kwalla tace “Shikenan ashe dama idan Allah ya jarabci bawa da wata ƙaddara saiya manta da faɗin ma’aiki (S.A.W) da yake horonmu da mu zaɓawa ƴaƴanmu iyaye na kwarai, Yaya Mus’ab wanne ɓangare zan nuna idan na karɓi Khamal a matsayin miji nace shine alfahari na? Please Yaya Mus’ab na rokeka a matsayinka na gatan daka tsayawa rayuwata kayiwa girman Allah ka shigemin gaba wajen bijirewa auren Khamal baiyimin ba bayan haka Nima banyi masa ba Yaya Mus’ab abinda Khamal yake faɗa min kullum shine shifa duk da lalacewarsa yanaji a ransa taimakona zaiyi idan ya aureni saboda naje na zubar da darajata irin mazan da nakeso na tsaya ruwan idanu nayi musu tsufa bazasu iya aurena ba Yaya Mus’ab kullum haka yake faɗamin Ni ban kalleshi da aibinsa ba sai shine yake cusguna min da naƙasun da bani nayiwa kaina ba….”
Ɗaganta hannu Yaya Mus’ab yayi yace “Shikenan ya isa Madinah Allah yayi zaɓi na alkhairi yanzu ya batun komawarki karatun? Dr Shafi’u abokina yace akwai wata jami’a a Rasha da suke bada horo na musamman akan duk wata matsala data shafi ƙwaƙwalwa to ke kuma naga kinada interested akan wannan ɓangare shiyasa nace zanyi Miki magana ko zakije ki ƙara samun gogewa”
Ƴar ƙaramar dariya tayi tace “Shiyasa nake sonka Yayana duk abinda da zai kawowa rayuwata haske shine burinka Yaya Mus’ab Allah yaja kwana ya ƙara arziki, ka bincika min shi abinda tafiyar zataci da inason na biya kudin aikin hajji amma tunda hakane bari na tura gaba tunda dai Ammi tayi Ni daga baya naje nayi, Yaya nifa Research kawai akan abinda ya shafi brain yana mugun sani nishaɗi”
Dariya Mus’ab yayi yace “Autar Ammi kenan waye zaiƙi farin cikin Ammi ai dole mu ƙarfafa Miki gwiwa munyi waya ma da Khamis shima ya bada goyon baya Salees ne dai da Aminu suke ƙorafin wai mune mukeja ake zaginmu ana cewa mun ɗaure Miki gindi kina yawo da sunan karatu ni wani lokacin gwiwata har sanyi takeyi”
Kwantar da kanta tayi jikin bedside tace “kuyi hƙr No condition is permanent Ya Mus’ab wata rana sai labari Allah shaida ne bana aikata abinda mutane suke zargina dashi Yaya duk wata mace da wannan ƙaddarar ta faɗa mata dama sociaty dinmu kallon ƴar iska gantalalliya watsattsa sukeyi mata hatta da Allah ya hukunta zai aureta bayajin a ransa budurwa zai aura, nifa da wannan surutun da nakeja muku wlh ko za’a bani sadakin bazawara indai nagartar mijin takai gara na karɓa indai yayi albarka Shikenan”
Murmushi yayi ya miƙe cike da tausayin ƙanwar tasa yace “Insha Allahu komai zai wucce ki kwanta goma ta wucce gashi gobe talata” fatan alkhairi tayi masa ya fice tare da ja mata ƙofar ta miƙe tayi mata key ta shiga bayi ta dauro alwata ta kwanta daidai lokacin da aka kece da wani ruwa me ƙarfi ta kunna MP tana sauraron ƙira’a tare da tsunduma duniyar tunanin rayuwar baya.
Kamar yanda ta saba yauma ganin zata raba dare bacci yakasa ɗaukarta tana hasaso lkcn da zata kwanta kusa da mijinta ta tayi matashin kai da ƙirjinsa ta shafa sumarsa taja gemunsa, wannan rana ji takeyi dama zata iya kissimo irin nishaɗin da zata kasance dama tazo mata nan kusa dama zata buɗe idanu taga ba ita ce Madinan da abu ɗaya ya zamewa tsaiko cikin rayuwarta ba.
To wai meyene abinda ya zame mata katanga da samun abokin rayuwa ne? Tambayar da kullum takewa kanta da makusantanta kenan amma ta kasa samun amsa saidai ace mata tayi hƙr lokaci ne idan ta hƙr ta cire komai a ranta kuma sune waɗanda zasu fara cewa da ita “Madinah wai yaushe zakiyi aure ne?” Wannan tambaya tana dagula lissafin ta da ace mutanen duniya zasusan ƙuncin da take shiga a dalilin wannan tambaya da sun daina yi mata ita.
Zuwa yanzu abubuwa sun fara yi mata nauyi sha’awar kasancewa da namiji abokin ɗebe kewa tana yawan bijiro mata takan raba tsayin dare bata iya bacci ba saboda ciwon mara idan abin ya ta’azzara har fita takeyi daga hayyacinta sai likita ya tsaya a kanta sannan take dawowa daidai.
Sai bayan sallar asuba sannan ta koma ta kwanta bacci me nauyi ya dauketa dake yau ba itane da dutyn safe ba tanada isasshen lokacin bacci ba ita ta farka ba sai 12:21pm ta farka shima tashinta akayi ta buɗe idanunta kan Ƙawar tata kuma abokiyar aikinta Dr. Zahira murmushi sukayiwa juna Zahira tace “Tunda nayita kiran wayar ki najita a kashe nasan kinanan kina sana’ar saiki tashi mu fita inaso zaki rakani unguwa”
Miƙa tayi tare da salati ta diro a katifar Zahira tabita da kallo tana cewa “Kaga manyan mata masu manyan kaya matan me rabo wato Dr. Komanki abin sone ga kowanne lafiyayyen namiji wlh Ni kaina da nake mace halittarki na birgeni an baje fasaha wajen ƙeraki ke gani kin zamewa mazaje ƙwalele ya Allah karka kasheni sai naga wannan me rabo da zai huta da jikin nan”
“Amin ta amsa dashi tana shigewa bathroom ta sakarwa kanta ruwa ta sulla wankanta ta ɗauro towel ta fito ta tsaya jikin mirror tana shafa ta bata kusan rabin awa wajen shafa mai fesa turare gyara gira sannan ta koma ta ɗauki wata baƙar atamfa tasa abinka da kyakkyawar nandanan ta ƙara wani kyau na musamman ta ɗauki mayafi Milk kalar zanen jikin atamfar da takalminta da jakarta duk kalar mayafin ne ta dauki system nata da wayoyinta suka fice.
A tsakar gida suka ishe Ammi tana gyaran ƙumba ta dubesu tace “Ai dake kece kinga ta fito Zahira ni tun asuba rabona da Munau tanacan tana sana’ar bacci kamar kasa” dariya tayi har Saida dimpli ɗinta ya lotsa tace “Ayyah Ammi wlh banyi bacci da wuri ba jiya don Ni a yanda na kwanta ma sai biyu zan fita a gdannan to wannan uwar ƙwarzabar tazo ta tasheni wai zataje unguwa kuma saina rakata”
Tsugunnawa tayi tace “Ammi na tuba wlh na horu a taimakeni da key ɗin motar Allah bazan kuma bige kowa ba” harararta tayi zatayi magana tace “Wlh Ammi tsautsayi ne bazan kuma ba da abin hawan kafi kwarjini kinsan yanayin aikin mu…..”
Cilla mata mukullin tayi tana cewa “Yar ƙaniya jeki nikam Allah nunamin ranar aurenku na daina ganinku kuna shigemin gaba” addu’a ce Ammi tayi amma Saida ta sanyaya mata jiki, har suka isa kango jikin gidan nasu dake dama tun jiya tace da maigadin ya wanke mata motar shiga kawai sukayi ta sallameshi suka fice suka dauki hanyar asibitin da suke aiki.
Dr. Zahira ce ta kawar da shirun da cewa “Na fahimci kinsa damuwa kwana biyu a ranki Dr. Meye yasa Ni da nake bazawara bana damuwa kamar yanda kike damun kanki?” Dr. Madinah akwai arhar hawaye nandanan suka shiga zarya a idanunta ta buɗe ƙaramin bakinta tace “Saboda ke kin taɓa yi kinada yaranki ko yanzu kika mutu kinada masu ɗaga hannu suce Allah ya jiƙan Umman mu Dr. Ni banyi ba banida kowa sai Ammi, kwana biyun nan ta matsa da maganar aurena sai nakejin dama zan iya aurar kaina kodan na faranta zuciyar mahaifiyata”
Cikin tausayawa Dr. Zahira tace “Dole zata damu Dr. Ko kinsan yanzu a unguwar nan taku shafinki aka buɗe jiya Husain ƙanina yazo yake cemin wai ke meye ya hanaki aure ne? Na dubeshi da mamaki shine yake cemin yaji a majalissar Bala me Youghut anata zaginki wai karuwanci kikeyi har wani dillali yana cewa shi yama taɓa kaiki gurin wani mai gidansa…..”
[6/3, 7:14 PM] AM OUM HAIRAN: *_JINKIRIN AURE_*
*_(Ƙalubale ga ƴammata)_*
*By*
*Oum Hairan*
*Dedicated to*
Dr. Mass @gadas son so for ever.
*Free P 5-6*
_Normal 300 VIP 600 PC 1k acct details 3184512451 Fauziyya Tasiu First bank. Shaidar payment ta wannan number 09013718241_
Murmushi takeyi wanda da ka gansa kasan na ciwo ne irin wadannan ƙananun sharrikan suna damunta amma yanzu sun rage yi mata zugi a zuciya ta saduda tunda ita dai ta tabbatar da bata taɓa aikata abinda mutane suke kallonta dashi ba, ta sani Allah zai wanketa tsaf idan lokacin wankewar yayi.
Da wannan suka isa sukayi parking bata iya cewa komai ba suka fito kowacce ta wucce office ɗinta da wuri tayi ƴan aikace-aikacenta ta sallami petiant ɗinta yawanci duk waɗanda zasu ƙara karɓar magani ne da kuma ganin yanayin jiki dake azumi ta ɗauka yau ɗin sai uku ta fito daga nata office ɗin ita dama Dr. Zahira ta jima da tashi a aiki suka kuma ficewa, lalle sukaje da kitso Zahira aka yima kitso Madinah ba ma’abociyar kitso bace tafi ganewa ta gyara sumarta ta daure dake Allah yayi mata baiwar sumar.
Biyar suka ɗauki hanya wannan karon Zahira ke jan motar suka shiga unguwannin cikin gari ƙofar nasarawa sukaje wani gida Zahira ce ta kira wata number bugu biyu aka ɗaga suka gaisa ta sanar dashi suna ƙofar gidan yayi musu izinin shiga Madinah na mita tana cewa ta gaji da yawon zuwa gurin ƴan tsubbu da Zahira ke sata ita ta barta taji da damuwarta basai ta ƙara mata wata ba.
Da wannan suka shiga cikin gidan a aljihun zauren suka ishe babban mutumin malami ne babba da tarin littafai a gabansa yana duba wani littafi a hannunsa ya dago ya amsa sallamarsu tare da nuna musu gurin zama suka zauna da gaisawa Zahira ta fara yi masa bayani tace “Mal wannan ita ce Dr. Madinah wacce jiya na fara baka labari wato Mal wani abune me bam mamaki da ɗaure kai yake faruwa nikam abin yana bani mamaki matuƙa, Mal babu muni babu matsalar tarbiyya babu jahilci babu gigita ta talauci amma rayuwar taƙi tayi haske kullum cikin damuwa take hatta Ni kaina abin ya fara sani a damuwa, Mal mijin aure ya gagara ga Dr. Madinah gashi shekaru har sun fara nauyi kullum abu sai ƙara nisa yakeyi Ni raina ya fara faɗamin anya babu sa hannu ko na mutum ko na shaiɗanu?”
Zubawa Dr. Idanu yayi kanta na ƙasa tana wasa da yatsunta can ya numfasa yace “Allah ya shiga lamarin Madinah” shiru ta tsawaita can ya dago yace “Babu matsalar jinnu cikin lamarin nan kuma babu sa hannun kowa Madinah kawai lokacine baiyi ba amma insha Allahu zamu duƙufa tayaki addu’a Allah ya jinkirta zama ya kawo abokin rayuwa na kwarai yanzu abinda nakeso daku ga wata addu’a da zan baki yau daren Laraba ƙarfe biyu ki tashi kiyi alwala kiyi sallah raka’a huɗu kowacce ki karanta mata fatiha ƙafa ɗaya da kulhuwallahu 40 kowacce raka’a har ki idar kiyi istigfari adadin 100 kiyi salatin annabi ƙafa ɗari shima kina me tawassali ga Annabi Muhammad (S.A.W) bayan kin gama ki faɗi bukatar ki ta zaɓin miji na kwarai abin alfaharin kowacce mace sai ki rufe da istigfari 100 salati 100 saiki tashi ki koma ki kwanta kiyi haka na tsayin kwanaki bakwai bijahi Rasulullah sai Allah ya waiwayi lamarinki domin kin haɗa shi da wanda bazai iya juya baya ga bukatar wanda yaje masa dashi ba wato Muhammadur Rasulullah, Madinah idan kinyi haka duk abinda alƙibla ta nuna to dole ki karɓe shi koda kuwa ɗan uwan naki Khamalu ne idan kuma akasinshi ne to dama fatan da mukeyi kenan, aje a dage Allah zai duba buƙata”
Gdy tayi masa sosai suka ajiye masa sadakar Naira dubu goma suka tafi hakanan taji malamin ya kwanta mata domin a kalaminsa akwai tawali’u sosai cikin lamarinsa, suna tafe ne tafiya irin ta kurame can Madinah tace “Dole zan bar ƙasar nan cikin yan kwanaki Dr. Saurin cin birki tayi tace “What happen Dr. Madinah da zakice zakibar ƙasa bayan kinsan yanayin da muke ciki yanzun?” Numfashi ta sauke tace.
“Shine dalilin da zaisa nabar ƙasar Dr. Zahira yau ina zaune a office Baba Sunusi ya kirani zagin da yayimin akan nace banada ra’ayin aure da Khamal ko karen gidansa baitaɓa waba har yana kirana ƴar matsiyata taka hayen arziki……” Kukane yaci ƙarfinta ta rushe da kuka tace “Wai meye laifina ne da Alƙasim ya haifeni da Adiyyah? Dubanta Zahira tayi tace.
“Na dade da fahimtar family ɗinku kuna rayuwa a cikinsu ne kawai amma basa kaunarku Dr. Don Allah yau dai ki bani labarinki ko a takaice ne wala Allah ta yiwu inada rawar takawa Dr tun muna school of nursing na fahimci halin da kuke ciki amma abin baiyi tsamari irin yanzu ba don Allah Please Dr. Ba’a ɓoyewa abokin kuka mutuwa”
Ajiyar zuciya ta rinƙa jerawa sannan tace zan baki labari na Zahira kiyi hƙr tun a baya ba rashin cancanta ce tasa nake basarwa ba rashin lokaci ne yanzu kuma inada lokacin da zamuyi amfani dashi yanzu muje gidan Mama mu ɗauki izini saimu kwana a gdanmu”
Haka akayi gidansu Zahira suka fara zuwa Mama bata hanasu ba don tasan shakuwarsu musamman da sukace zasuyi wani aiki ne suka dungumo suka taho Sheka lokacin Ammi ta gama haɗawa autarta kayan shan ruwa suka baje a tsakar gida suka huta lokacin sallah yayi sukayi Saida sukayi Isha sukayiwa Ammi sallama sukayi shirin kwanciya dake katifar ta Dr Madinah babba ce by six ce me tudu, duban Dr Zahira tayi tace “kin shirya jin labari na?” Jinjina kai tayi Madinah tayi murmushi tace “kin shirya zubar da hawaye kenan zan baki labari kamar yanda kika buƙata amma idan bukata ta samu zan tashi” amincewar Dr Zahira yasa Madinah gyara zamanta ta kurɓi coffee ɗin hannunta ta fara da cewa.
*** *** *** ***
Madinah Alƙasim, shine cikakken sunana Wadda a yanzu duniyar likitoci musamman wanda suka shafi ƙwaƙwalwa a ƙasata Nigeria sukafi sani da Dr. Deenah, Mal Buba shine wanda yayi silar tsatsona domin shine ya samar da Alƙasim da ƴan uwansa Sunusi Nuhu da Kabir sai mata biyu Gwaggo Hajara da Yakumbo Harira, Baffana Wato Alƙasim shine daban a cikin biyar ɗinnan kuma shine ɗa na uku a wajen Mal Buba ya kasance Sunusi da Nuhu sune kawai a samanshi sauran duk ƙasanshi ne.
Mahaifina ya taso da rangwamen gata saboda mahaifiyarsa ta rasu ne tun yana shekara uku a dalilin haihuwar ƙanwarsa inda suka tafi tare ita da jaririyar data haifa, saiya kasance ruƙon Kasim ya koma hannu Inna Mai koko wadda ita ce uwar su Sunusi. Inna mai koko batason Kasim ko kaɗan hakan yasa suma yaranta suka taso da aƙidar ƙiyayyar Kasim inda shi kuma Mal Buba ganin yanda suke nunawa ɗan marayan zakin nasa kyara da tsangwama yasa ya ɗauki kulawa da soyayyar duniya ya ɗora masa.
Sai ya kasance duk inda zasuje tare suke zuwa dake Mal Buba bafulatanin Gwangola ne dake cikin taraba a yanzu ya taso da yawon kiyo da fatauci har kawo lokacin da girma ya fara riskarsa, yaso ya ɗora Babban ɗansa Sunusi akan wannan tafarki amma sai Innan mai koko tayi tsalle ta dire tace ƴaƴanta karatun boko zasuyi ba gantali ba shima da yake ya jima da zare lissafinsa akansu yasa yaci gaba da rainon Kasim akan harkarsa har Kasim ya saba fita kasashen Afirka shine Chadi Ghana Cameron Mali Senegal Togo kai dama kasashe da yawa na Afrika irinsu Rwanda da dai sauransu.
Daga baya ne kuma karatun bokon yaƙi ga ƴaƴan Inna taso su koma harkar fatauci abin ya faskara domin ba’a rainesu a cikinta ba Baffa Kabir ne kawai ya ɗan yi abin arziki lokacin da Mal Buba ya dawo ya zauna su kuma sukaci gaba da fafatawa a zahiri Kabir ba irin zuciyar yan’uwansa ne dashi ba shi yanason Kasim musamman yanzu da kusancinsu yake ƙaruwa suke yawon kasashe tare.
Kasim baiyi ilimin boko mai zurfi ba iyakarsa Firamare irin ta wancan lokacin bata yanzu ba amma yanada ilimin muhammadiyya fiye da yan uwansa dalilin da yasa komansa ya zama cikin nutsuwa da dattako, Wata shekara harkar kasuwancinsu takaisu Ethiopia a hanyarsu ta shiga garin Ethiopia ne sukayi kicibis da wani ayari na ƴammata sun dauko ruwa dake suna kusa da wani ƙauye ne.
Nan suka isa garesu suka rokesu su sammasu ruwa su sha su wanke fuska kasancewar tafiyar Sahel ga rana duk sun galaɓaita, sai waɗannan ƴammata sukaƙi basu wannan ruwa guda ɗaya cikinsu da tafi kowacce kyau ita ce ta tsaya bayan yan’ uwanta sun tafi ta basu ruwan nata sukasha sukayi alwala suka bata tulun ta juya ta koma.
Kasim ne ya dubi Kabir yace “Bantaba zuwa garinnan ba amma naji labarin abinda ke faruwa mubi yarinyar nan kada matasa su keta mata haddi” babu musu sukabi bayanta ilai kuwa batayi nisa ba wasu matasa su biyu suka fito cikin rairayin Sahel suka tareta sunayi mata dariya ɗaya cikinsu yakai hannu ya dumbuli nononta aikuwa ta ƙanƙame jikinta yana rawa tanayi musu magiya da yanayin tashin hankali kamota ɗayan yayi daidai lokacin da Kasim ya iso da sauri yakai hannu zai ƙwaceta suka kama kokowa da matasan har suna yankarsa daƙyar ya ƙwaceta a hannunsu y haɗata da Kabir shi kuma yaje ya ɗebo mata ruwan ya dawo ya ishe su tana ganinsa ta rinƙa murmushi da kanta tayi musu jagora har gdansu mahaifinta tsoho ne sosai shi kaɗai ne a bukkar tasu sai wata bukkar dake rufe a gefe.
Da mamakinsu sukaji yayi musu magana da fullanci suka amsa masa yayi musu tambayoyi suna bashi amsa can ya dago yace musu “Adiyyah tayi miji yau zan daura maka aure da matarka ka dauketa ku tafi” Saida gaban Kasim ya faɗi ya ɗago zaiyi magana ya ɗaga masa hannu yace “yaro tsayin lkc ina jiran zuwan mijin Adiyyah baizo ba sai yanzu ka bayyana tabbas kaine zabin da Allah yayi mata kayi hkr ka karɓi al’adarmu a yanda tazo maka zakaji dadi kuma zakayi alfahari da auren Adiyyah gatanan na baka ita halak malak bayan Ni baka da wani gata saikai daga bayyana yanzu”
Kasim baiso karbar wannan aure ba haka Kabir ya rarrasheshi aka ɗaura wannan aure Adiyyah tayi murna shikam Kasim sama-sama ce murnar shi a ranar kaka Hakeem ya bawa Kasim wannan bukka dake rufe wai ya kwana da matarsa shi kuma zasu kwana da Kabir, wannan shine asalin haɗuwar Kasim da mahaifiyarmu Ammi kenan.
Cikin ikon Allah watansu biyu a wannan ƙauye suna shiga cikin gari suyi sarinsu har suka gama ana saura kwana uku zasu tafi ne ciwon ajali ya riski tsoho Hakeem a daren ya rasu sarai Adiyyah taji mutuwar mahaifinta maiyi mata gata dake su can ba kamar mu ba basa zaman makoki kwana biyu da rasuwar suka dauko hanyar Nigeria birnin Kano kasancewar kasuwanci ya jima da dawo da Mal Buba Kano ganinsu da baƙuwar fuska yasa bayan Oyoyo akayi cirko-cirko ana jiran aji abinda suka zo dashi Kabir ne yayi masu bayanin komai Mal Buba ya jinjina lamarin ubangiji shi nan har yayiwa Kasim mata a can Gwangola ashe matarsa tana Ethiopia, shikam baija da lamarin ba Inna me koko ce dai a lokacin ta rinƙa faɗa tana cewa wannan ai irin tsiya da masifa aka dauko musu ƙasar da akace da karuwanci suke samun kuɗin shiga shine zaaje a kwaso musu don a lalata musu nasaba.
Shi kuwa Sunusi baƙin ciki ne kawai na ganin zukekiyar matar da ƙaninsa ya samu a sadaka yasashi ƙyashi da baƙin ciki gashi shi ya bige da yar tallan shinkafa da wake. Gidan da Mal Buba ya ginawa Baffa Sunusi nan yasa aka gyarawa mahaifina da mahaifiyata Mal Buba da kansa yaje kasuwar Rimi ya siyo musu katifa da pillow da duk wani abu da yasan zasu buƙata, aka fara rayuwa a wannan gida Jamila matar Baffa Sunusi da Indo matar Baffa Nuhu suka hadewa Ammi na kai ya zamana ko fitsari a dole Ammi na take fitowa girki kuwa kafin ta gama tayi kuka yakai sau nawa don sun rinƙa kallonta suna zundenta suna mata habaici tare da dariya suna cewa da ita karuwa matar cushe ko kuma su rinƙa cewa da ita yar cirani kayy har mayyah sunsha ce mata wai kyawun banza kyan ɗan maciji…..
[6/7, 8:29 AM] AM OUM HAIRAN: *_JINKIRIN AURE_*
*_(Ƙalubale ga ƴammata)_*
*By*
*Oum Hairan*
*Dedicated to*
Dr. Mass @gadas son so for ever.
*Free P 7-8*
_Normal 300 VIP 600 PC 1k acct details 3184512451 Fauziyya Tasiu First bank. Shaidar payment ta wannan Link ɗin👇🏼._
Zahiri irin kalaman da suke amfani dasu wajen cusgunawa Adiyyah sunyi tasirin hanata walwala ta rinƙa rama babu dalili wannan ya ɗaga hankalin Alƙasim musamman lokacin da Adiyyah ta samu ciki me laulayin gaske ya kasance komai sai yayi mata kafin ya fita daga gidan hatta da girki.
Wannan ya ƙara rura wutar ƙiyayya tsakanin Adiyyah da matan yayan mijin nata wato faccalolinta ya kasance ko maganarta babu me amsawa Adiyyah zuciyarta me tsarki ce shiyasa wannan yanayi ya dami rayuwarta a haka a daddafe tayi haihuwarta ta fari ta haifi Yaya Shamsu koda akazo batun zaman biƙi Inna me koko ita ke daukan duk surukanta amma cewa tayi bazata iya wahala mara amfani ba.
Baffana yaji ciwon wannan magana haka ya tafi Yola dangin mahaifiyarsa ya dauko wata dattijuwar ta kula masa da matarsa lokacin da sukayi arba’in tsohuwar ta tafi ya hadɗanta sha tara ta arziki, rayuwa taci gaba da tafiya babu wani daɗi indai kaga Adiyyah na walwala tsakaninta da mijinta ne ko kuma ɗanta, na manta ban faɗa miki ba a wannan lokacin Sunusi da Nuhu basu haihu ba Sunusi nada shekara bakwai da aure Nuhu yanada huɗu ga Alƙasim shekara ɗaya da rabi an sankato masa ɗansa namiji.
Aifa sai aka ƙara ɗaukar tsana aka ɗorawa Adiyyah da ɗan ta kinsan abin yaro kuma lafiyayye lokacin daya fara rarrafe Adiyyah na can na aiki saidai ta jiyoshi ya canyare da kuka tana fitowa sai taga ko Jamila ko Suwaiba wata ta make mata ɗa haka zata ɗauki abinta tayi ciki dashi ta rarrasheshi, yaron nan har wuta yasa hannunsa Jamila na girki a Madafi amma bata iya hanashi ba, wannan ta wucce wata rana Adiyyah ta shiga wanka tabar Shamsu na bacci a ɗaki ashe tana fita ya tashi ta yayo waje lokaci an siyowa Suwaiba kalanzir zatayi girki a robar swan kawai yaron ya ɗauka ya kyankyaɗa Suwaiba da Jamila suna ɗaki suna kallonshi yanata kakari da fitar da dafara babu wacce ta fito Saida Allah ya jeho Baffanmu ya ga ɗansa a wannan hali ya isa gareshi da gudu shida Baffa Kabir suka ɗaukeshi Baffanmu yana kwalawa Adiyyah kira ta fito a gigice taga halin da ɗanta ke ciki aikuwa ta fasa ihu sukayi waje a guje kafin suje asibiti rai yayi halinsa.
Sosai wannan abu ya girgiza Baffanmu take ya yanke shawarar barin wannan gida aikuwa bayan bakwai ya samu wani gidan haya shi kadai da matarsa suka shiga ciki babu daɗewa kuwa Allah ya ƙara basu rabo ta kuma haihuwar namiji shine Yaya Mus’ab ɗina da zakiji ina yawan ambato gatana masharin kukana Yayana kuma abokina me share damuwata.
Zakiji yanda akayi ya samu wannan matsayin da darajar a gurina a hankali,
Haka rayuwa taci gaba da tafiya shekarar Mus’ab biyu aka haifi Yaya Salees shima shekararsa biyu aka haifi Yaya Khamis sai yaya Aminu, Ni kuwa Saida yaya Aminu ya shekara tara sannan aka haifeni, Zahira haihuwata tazo da wani irin yanayi me gigita tunani domin tun kafin a haifeni komai ya janyewa mahaifinmu Mal Buba ya karɓe duk wani abu da yake nasa a hannun Baffanmu sakamakon sharrin da Sunusi da Nuhu sukayi masa dalilin siyan wani gida da yayi akusa da wanda muke ciki ya haɗe da namu dake dama ya daɗe da siyen wanda ya kama hayar ya gyareshi, bansan wanne tudu wanne gangare akabi aka sauko ba duk wannan yardar da nasamu labari dake tsakanin kakana da Baffana ta gushe ba ya zamana ko gaisheshi Baffanmu yayi baya amsawa rayuwa tayiwa Baffanmu kunci gashi bai iya komai ba sai fatauci ga babu jarin juyawa sannan ga yan’ uwansa duk babu wanda zai raɓa yaji daɗi sai Baffa Kabir shikuma shima ba wata power ce dashi ba domin shima yan uwan nasa da suke ciki ɗaya sun barranta kansu dashi saboda yana tare da Baffanmu.
Tun cikina yana wata biyar Baffanmu ya kama wani ciwo ne kama da hauka sakamakon wani hatsari da sukayi shida Baffa Kabir a hanyarsu ta dawowa daga Gwangola, a wancan lokacin babu wadatar na’urorin bincike sannan su kansu likitocin kwakwalwar sunyi ƙarancin da ba kowa ne yake da halin zuwa ya gansu ba saboda Ammi na ta sanar dani a wancan lokacin saidai aje Lagos ko Port-Harcourt sannan za’a sami damar duba mutum indai matsala ce data shafi ƙwaƙwalwa don ko likitocinmu na arewa sunce zasuyi ƙarshe sai sun turaka can.
Tun ciwo yana ƙarami haka Ammi da Baffa Kabir sukayita fafutuka suga abin bai girma ba amma abu yaci tura karshe kan Baffanmu ya rinƙa kumbura yana wata irin firgita ko bacci baya iyawa saidai damuwa kullum cikin kuka yake kamar ƙaramin yaro idan an tambayeshi mene sai yace Adiyyah yake tausayawa ranar da baya raye gashi Mus’ab da Salees da Khamis basu kawo ƙarfi ba bare su taimaketa gata ita ba kowa ba a Nigeria idan tace zata koma Ethiopia ma can ɗin ma ba gatane da itaba tunda shima babanta Hakeem a irin yanayi da Baffanmu ya taso shima ya taso gata ita kaɗai kacal ya haifa kamar rai mace yayyanta biyu maza Daga yawon almajiranci basu dawo gida ba har aka auradda ita Tsoho Hakeem ya rasu.
Cikin dare Adiyyah ta fara naƙudar haihuwata har wayewar gari Baffana da baason shigarsa damuwa kuma dama baa cikin lafiya yake ba domin a lokacin kansa yayi na mutum uku lafiyayyu saboda kumburi shine yaketa kaiwa da komowa sai kuma matar Baffa Kabir da tazo tun daren kiran sallar farko yayi daidai da dirowata duniya zuwa lokacin Baffana ba’a barinsa fita shi kaɗai saboda kowanne lokaci yakan iya samun gushewar hayyacinsa ashe ba’a sani ba ya fita a titin sheka anan wata motar yan sanda ta kwankwatse min Baffana!!
Dakatawa tayi tana sharar hawaye sannan ta ɗora da cewa ashe duk sauran ƴan uwana gata suka samu nice ƙaddarata tazo a juye.
Zahira tunda Baffa Kabir da Yaya Mus’ab dake da shekaru sha bakwai a lokacin suka fahimci Baffanmu ya fice suka bazama nemansa, basuyi nisa ba suka ishe wannan mugun ganin da bayanin wasu mutane dake gurin sanda abin ya faru suka gane shine aikuwa sun shiga tashin hankali, aka ɗauki gawarsa bayan an shigar da duk wani bayani daya kamata aka wucce da ita gida.
Wayyoh wannan rana zo kaga tashin hankalin da Ammi ta shiga sumanta uku har asibiti ta kwanta yau Shikenan ta fito rana mijinta me ƙaunarta da son ganinta cikin walwala wanda yafita sonsa ya ɗauke wannan shine ga ƙoshi ga kwanan yunwa ga burinsa ya samu ɗiya mace da yake burin ganin ya haifa ashe bazai ganta ba gatan da yake alwashin bata da ilimin da yake burin bata da muradinsa na ganin ta zama likita duk ba tabbatattu bane……
Wannan mutuwa hatta makota ta girgizasu shi kansa Mal Buba ya kaɗu da jin rashin daya tafka ɗansa mai biyayya a garesa da gudun ɓacin ransa Mal Buba yayi kuka har hawayensa sun kafe ya zama na zuci yana hasaso daren jiya wajen tara yana zaune a tabarma a aljihun zauren gidansa yaji an shigo, yace waye can ya jiyo shassheƙar kukan babban mutum ya taso ya fito yaga ashe Alƙasim ne mamaki ya kamashi yace “Ƙasim meye ya fito dakai yanzu?” Cikin kukan ya durƙusa ya riƙe ƙafarsa yace “Banida lafiya banida hankali Baffa amma hakan bai hanani jin tausayin kaina ba idan na mutu kana fushi dani akan laifin da zargine sharri ne Baffa kaji ƙaina ka tausaya min kace ka yafemin wlh tallahi inajin kamar bazan kai gobe ba…
Duk sanda yazo yanayi masa wannan magiyar sai yakanji kamar ya yayyafa masa fetur ne to jiyan ma abinda ya faru kenan yana masa kuka yana magiya haka Mal Buba ya tsallake ya shige daki ya barshi shidai baisan sanda ya tafi gidansa ba ashe rabuwar ƙarshe ce.
Kuka sosai Buba yayi yana cewa “Na yafe maka Alƙasim wlh nasan bazaka aikata min ba kuma Kabiru ya faɗa min bakada hannu a cikin wannan sata da akayi ƴan fashi ne suka tareku suka kwashe komai…. Wayyoh Alƙasim ka yafemin Nima na yafe maka!”
Saida ƴaƴansa suka haɗu suka ɗaukesa a gurin aka ɗauki Baffanmu aka kaishi makwancinsa sannan akaci gaba da karɓar gaisuwa, adalci ɗaya da gwamnati tayi mawa su Ammi ta bawa Ammi jari sannan an ɗauki nauyin karatun Yaya Mus’ab da Salees zuwa jami’a hakanan Ammi ranar suna tasa aka Samun Madinatul Munawwara sunan kakata wacce ta haifi Baffa kenan, nan akaci gaba da raino na kyawu na biyu na haɗa na mahaifiyata Ammi da kuma na Kakata wacce naci sunanta domin itama waɗanda suka santa suna fadin kyawunta asalin bafulatanar Adamawa ce cikin garin Maybalwa.
Kyau yana jawa yaro farin jini matuƙa musamman ni nawa daya haɗu da tsafta nan a unguwar mu aka rinƙa rububi da tururuwar zuwa ɗaukata Deenah shine sunan da ɗan Baffa Kabir ya raɗamin Shikenan Deenah ta bini Babu jituwa tsakanin yayyena da ƴaƴan su Baffa Sunusi amma ta dalilin haihuwata sai ga Khamal Naseer da Hussain dan Baffa Nuhu suna tururuwar zuwa gdanmu Hussain ne me ɗan banzan karambani har ɗaukata yasha yi ya tafi dani gdansu haka iyayensa zasu koromu karshe Suwaiba tace indai ya ƙara dauko mata wannan aljanar yarinyar irin tsiya da jaraba saita sa an yankashi.
Dake ba wani girma yayi sosai ba haka ya hƙr ya barni saidai yazo gdanmu yayita yimin wasa sai yamma ya tafi, soyyayarsa gareni yasa Ya’ya Mus’ab ɗaga masa ƙafa.
Inada saurin girma kamar kazar gidan gona shekara ta biyu aka sani a makaranta da yake wayona yafi na shekaru na saiya zamana a makarantar ma na samu karɓuwa matuƙa da gaske ina karatuna shaƙuwata da Hamma Hussain na ƙara shiga jikina da koyamin damuwa dashi har takai duk ranar da Banga Hamma Hussain ba bana samun nutsuwa,
Saida takai duk masifar Suwaiba da Baffa Nuhu Saida suka sallama lamarin Hamma Hussain gareni, ya garace yaje makaranta a dake shi daya tafi da wuri bai ganni ba.
Inada shekara goma na gama firamare lokacin Yaya Mus’ab ya gama jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya ya dawo gida gadai kwalin amma babu aikin yi dake akwaishi da zuciyar nema haka zai ta buga-bugarsa shine gini shine dako duk don ya samo mana abinda zamuci shida Yaya Salees da wannan suka samamin secondary na ɗora itama ta kuɗi ce kuɗi sosai nake kwasa a wannan makaranta da nakeyi daɗinta dake ba asarar kudin akeyi ba ina kwashewa.
Inada shekara sha huɗu wata rana muna zaune a tsakar gida nayi matashin kai da cinyar Hamma Hussain yanamin tsifa a lokacin shi kuma yana karatunsa a Bayero University Kano, hira sukeyi suna tattaunawa akan irin wahalar da Baffanmu yasha nan Hamma Hussain yake cewa ai wani lakcaransu yayi musu bayanin yanda ciwon yake samuwa matsalar jijiyoyin ƙwaƙwalwa ne”
Nan na fara tambayarsa abinda ya shafi ciwukan da suka shafi ƙwaƙwalwa dake yana bawa duk abinda ya shafeni muhimmanci ya zauna yanamin bayanin abubuwan daya sani a matsayinsa na ɗaliban ilimi nan take naji inada soyayyar karantar bangaren kodon na gano yanda za’a magance ciwon daya zama sanadin kashemin mahaifina da kuma wani yaro a maƙotanmu me suna Hashim da shima akace tun wani hatsarin mota da akayi dashi yana ƙarami ya samu wannan matsalar.
Ina tashi na zura da gudu Hamma Hussain ya bini ban zame ko inaba sai gdansu Hashim, Hashim ya girmeni a haife amma yanayin lalura yasa yake abubuwa kamar yaro ƙarami nan na kama hannunsa muka zauna nace masa “Aboki nice zanyi maka maganin ciwonka zakaji sauƙi zaka warke ka koma kamarni kamar Hamma Hussain” dukkansu waɗanda suke gurin kama daga babar Aboki Hajiya Sakina da kuma Babansa Alh Musa da kuma yayyensa suka kama yimin dariya Hamma Hussain da Yaya Mus’ab sune kawai suka zubamin idanu sun sani a rayuwata banson dariya hakan yasa ina ɗagowa Hamma Hussain yayi sauri cewa “Hakane Dr. Deenah Matar Dr. Hussein insha Allahu saikin zamo silar warakar Aboki” ……….
[6/7, 8:29 AM] AM OUM HAIRAN: *_JINKIRIN AURE_*
*_(Ƙalubale ga ƴammata)_*
*By*
*Oum Hairan*
*Dedicated to*
Dr. Mass @gadas son so for ever.
*Free P 9-10*
_Normal 300 VIP 600 PC 1k acct details 3184512451 Fauziyya Tasiu First bank. Shaidar payment ta wannan Link ɗin👇🏼._
Tsalle nayi na faɗa jikin Hamma Hussain ina dariya ya ɗagani muka fita duk da shekaruna sun fara nauyi ina da kusan 15 years Amma har yanzu ban girma da ɗauka gurin Hamma Hussain ba baya gajiya da hidima dani baya gajiya da wahaltamin baya gajiya da jiɓantar al’amura na.
Muna rayuwa da taimakon Ubangiji dayake kawo mana ɗauki cikin nasara Yaya Mus’ab ya samu aikin campany ya fara shikuma Yaya Salees yaci gaba da buga-bugarsa shine acaɓa shine kwandastan mota ita kuma Ammi takanyi funkaso da safe da rana kuma tayi lemon ginger da kunun aya haka Allah ya rinƙa tallafarmu munaci gaba da rayuwa cikin ƙaramin yanayi Ni da yayye ba biyu muna karatunmu wani lokacin kudin school fees ɗinma sai anyi kamar anayi kafin asamu a biya.
Zahira a mafi yawan lokuta ma Hamma Hussain shine yake biyamin kuɗin makarantar, shekarata sha bakwai na gama secondary A wannan lokaci idan kika kalleni zakice nayi shekaru ashirin da biyu saboda cikar zati na da halitta ta.
Tabbas na amince Zahira ni babbar yarinya ce matar manya a hankali mukayi wata shaƙuwa da ta rinƙa rikiɗa tana zama soyayya amma a ɓangaren Hamma Hussain nikam bantaɓa jin so na soyayya tsakanina da Hamma ba saidai kawai nasan duk cikin ƴan uwana inajin Hamma Hussain a raina fiye da kowa.
Lokaci da zamuyi candy Hamma Hussain ya kashemin kudi bana wasa ba domin a lokacin ya gama karatunsa dake zuwa wannan gaɓa Allah ya ɗaga mahaifinsa da Baffa Sunusi sun shiga harkar siyasa gadan-gadan wannan tasa baisha wahalar samun aiki ba, kuma baya ƙyashin kashemin ko nawa ne ga Yaya Mus’ab shima komai ya samo Deenah komai ya shigo hannunsa nawa ne wannan tasa na zama ƴar gata abu guda ɗaya yanzu daya kutso cikin rayuwa shine masifar son karatun likitanci kamar yanda naci buri itakuma Ammi tunda na taso taga yanda nake girma kamar kazar gidan gona bata da burin daya wucce taga ta auradda Ni.
Muna zaman jiran jarabawa Kusanci na da Hamma Hussain yana ƙara ƙarfi duk dangi kowa yana kallon mu matsayin masoya Mal Buba shine ya shiga cikin maganar dakansa yasa aka kira Baffa Nuhu akan maganata da Hussein tashin farko abinda Baffa Nuhu yace ya girgiza Ammi na sanda taji wai Baffa Nuhu ne yace shi indai shine ya haifi Husain to bai amince masa aure na ba harma da ƙarin cewa shi ai baima yarda muɗin halattatun ƴaƴa bane don har Ethiopia yaje ba’a nuna masa limamin daya ɗaura mawa Baffanmu da Ammi aure ba.
Tun daga wannan lokaci aka jingine maganar auren to dama dake ba wani damuna maganar tayi ba haka naci gaba da harkokina ranar da jarabawarmu ta fito Hamma Hussain ne yaje ya dubo min yazo da murnarsa jarabawa tayi kyau na samu duk abinda ake buƙata ranar Ya Mus’ab har goyani yayi saboda murna ya tsugunna gabana yace “Uktee me kikeso yanzu bayan fitowar jarabawarki?” A dan ɗarare saboda Ammi bata bani da sauƙi idan nace mata karatu nakeso nace masa.
“Hamma Mus’ab don Allah kar ku watsawa muradina ƙasa kune kukace shine burin Baffanmu akaina koda baya raye zaku iya cika masa burinsa, inason nayi karatu burina shine na zama likitar ƙwaƙwalwa please Ya Mus’ab…..”
Ɗaukeni naji anyi da marin da Saida bakina ya fashe Ammi tace “Karatun ubanki zakiyi Munau Ni kwadantaki zanyi inci da zansaki a gaba in kalla Mus’ab na faɗa maka ka daina biyewa shirmen yarinyar nan…..”
Cikin sanyin jiki Yaya Mus’ab ya ɗago yace “Ba haka bane Ammi yawanci tunanin yaro shine nasararsa Kinga yanzu kece da kanki kikace mubar maganar auren Hussain da Madinah to me zamuyi da ita Ammi babu amfani zaman Madinah a gida gara ta tafi makarantar wala Allah karatun shine alkhairin rayuwarta kuma ai karatu baya hana aure tana karatun ta idan Allah ya kawo mijin sai tayi aurenta”
Barin gurin Ammi tayi Yaya Mus’ab yabita nikuma na nufi ɗakina nasa tisue na goge bakina ina tunanin idan Ammi taƙi amincewa da muradina ya zanyi Allah ya sani ina matuƙar son karatu bazan iya hƙr da karatun ba, na kusan raba dare ina juyi ranar ko islamiyyarmu ta dare banje ba har na saduda na haƙura da lamarin karatun amma kullum raina a kunci yake banida sakewa damuwa ta aure ni gashi Hamma Hussain ya daina zuwa zuwa gdanmu Baba Suwaiba da Baffa Nuhu sunce idan bai hƙr daniba zasu cireshi cikin jerin yaransu.
A zahiri ya nuna musu ya haƙura saidai a bayan fage yanata yimin hidima adashi Yaya Mus’ab ya ɗauka a gurin aikinsu yaje ya yankarmin Form na Jamb bansan anayi ba sai saura sati ɗaya za’ayi jarabawar na samu labari murna a gurina kamar anyimin Hajj da Umrah lokacin jarabawa yayi muka zana cikin kokwanto ko mu dace ko mu faɗi tunda mun riga mun san halin ƙasar mu, bayan kammalawa muka dawo sati kaɗan Jamb ta fito komai na cikin nasara na samu abinda kowanne dalubi yake nema, nan aka shiga fafutukar yanda za’ayi a biyamin kuɗin jarabawa a Jami’ar Adamawa aka samamin admission Yaya Mus’ab yasai da machine ɗinsa da system dinsa ya gamamin komai dakansa yakaini makaranta ya kamamin hostel muka fara rayuwar karatu da ɗalubai yan’uwana anan muka haɗu dake in baki manta ba.
Tun a wancan lokacin kyawu na yake firgitani kinsan meye yasa kyawuna yake firgitani? Tunda na taso na mallaki hankalin kaina bayan Hamma Hussain babu wani namiji daya taɓa kallona ya furtamin kalmar nan me tsada a gurina kuma me arha a gurin ƴammatan da suka amsa sunan su mata musamman kyawawa kamata.
Zahira kinsani tun a wancan lokacin Ni dake zamu fito daga makaranta za’a ganmu tare a tsaya ace ana sonki saidai Ni bantaɓa samun wannan gatan ba muna wannan rayuwar kikayi aure kika auri Daddyn Noor har muka gama makaranta mukayi duk abinda ya dace muka dawo garinmu kikaci gaba da rayuwa a gidan mijinki nikuma naci gaba da rayuwata tare da mahaifiyata da ƴan uwana.
A wannan ƙadamin ne kuma idanun jama’a yayo kaina musamman da naje karatu na dawo su Baffa Sunusi sune suka fara buɗe fagen da cewa Ammi ta mayar dani karuwa taki barni bayi aure saboda tana morar kyauna tana samun abin lasawa.
Wannan maganganu sune suka rinƙa tunzura zuciyar Ammi takan cemin Munau ki hƙr da makarantar nan tunda kin samu abinda kika samu kiyi aure ko dangin mahaifinki sa daina zagina da ganin laifina” a duk lokacin da tayimin wannan bayanin nakanyi dariya nace “Ammi kenan duk fa wanda ya zageki haƙƙi ya rage Miki tunda kinsan baki aikata abinda suke zarginki dashi ba kuma ma Ammi shi aure ai mutum biyu akeyinsa Ni kinganni fah wlh tunda na taso babu wanda ya taɓa cewa yana sona shima Hamma Hussain da kuke gani wlh bakina da nasa baitaɓa kallona yacemin Deenah inasonki ba kawai abu daya dana sani zanyi aure idan lokacinsa yayi, kiyi hƙr Ammi banason zaman banza shiyasa kikaji muna zancen juyawata karatu tunda mijin auren baizo ba”
Jinjina kai Ammi tayi tace “Shikenan Munau Allah ya taimaka ya kawo miji na gari” amsawa nayi da Amin na tashi na ɗauki handbag ɗina dana aje na shige ɗakina na cire kayana na fito na shiga bayi na watsa ruwa na sanya kayan bacci naci abinci na kwanta Zuciyata cunkushe da tunanin ta inda zan fara neman abokin rayuwa raita tana faɗamin to nayiwa Hamma Hussain magana mana aikuwa na daga waya na kirashi ya dagamin babu wani jinkiri kamar yanda na saba nace “Hamma!” Numfashi ya sauke yace “Na’am Ɓingel” yanayin yanda naji muryarsa yasa gabana faɗuwa sai nayi shiru da furta ƙudurina har Saida naji yace “Deenah meye yake faruwa ne yau na yini zirga-zirga akan sharafin karatunki harma an gama komai zaki fara karatu a Skyline university dake nan Kano makarantar tanada kwararrun malamai shiyasa na zaɓa Miki ita kuma shi kinsan wannan ɓangaren da kika ɗauka bangare ne me wahala harkar ƙwaƙwalwa har tafi ta zuciya wahala shiyasa naga gara ayi abin da gaske, to alhmdllh dake Ɓingel ɗin tawa akwai kwazo result ɗinki ya tsallake harma ya zarce kin sami gurbin karatu a cikinta saidai matsalar kuɗi amma karki damu zanji da komai tunda mun gama magana da Yaya Mus’ab komai zai yiwu da yardar Allah”
Numfashi na sauke cikin raunin murya nace “Hamma Ni na hƙr da karatun Ammi aure takeso taga nayi saboda maganganun da aketayi akaina, Hamma kawai muyi aure idan da rabon nayi karatun nayi a gaba….” Wannan magana dana faɗa masa ba ƙaramin jefashi a tashin hankali nayi ba ashe abinda yake addabar zuciyarsa kenan shiyasa farkon kirana naji kamar bashida lfy.
Numfashi ya sauke cikin son kwantar min da hankali yace “Kullum shine burina Deenah karki damu lokacin ya kusa insha Allahu gobe kafin na tafi aiki zanzo gidan muyi magana da Ammi”
Haka mukayi sallama ko babu komi na ɗan samu nutsuwa inaji a raina nakai kukana inda za’a sharemin hawaye, kamar yanda ya alƙawarta min da safe kafin in tashi yazo gdanmu shine ya tasheni da tausasan yatsunsa da naji suna yawo a fuskata yana huramin iskar bakinsa na buɗe ido ina miƙa na manta a yanayin da nake ciki, ya kuwa kafeni da idanunsa ina sauke nawa akansa ai ban gama sauke idona akansa ba na yayumo bedsheet ɗin na rufe jikina ina cewa.
“Wayyoh Oh God sorry please Hamma….” Lumshe idanunsa yayi ya kwantar da kansa jikin bango yana sauke wani wahalallen numfashi na figo hijjab ɗina nasa na miƙe zan bar gurin ya riƙoni na faɗo jikinsa ya saukemin hucin numfashinsa a saitin fuskata a wahale yace “Harda ƙwalele Deenah meye yasa kikeson tsokanata da jikinki wlh kina cutar dani shiyasa na ɗauki matakin ƙaurace Miki saboda banason ayi abin kunya”
[…] Jinkirin Aure Hausa Novel Complete […]