Littafan Hausa Novels

Jikina Yake So Complete Hausa Novel

Siffofin Mace Mai Ruwa
Written by Hausa_Novels

Jikina Yake So Complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Jikina Yake So Complete Hausa Novel

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

 

Yarinya ce y’ar kimmata shekara tara taci ado cikin English wear na gown an tufke mata kai da baby pink d’in ribbon mai kyau.

 

Jikina Yake So

 

Ba wata fara bace cen amma ba laifi kakkyawa ce son kowa kin Wanda ya rasa, tana da dimple a kummatun ta da suke lotsawa a duk sanda take murmushi ko dariya hakan ba karamin kawata fuskan ta yake yi ba.

” Aunty aina!!!! Aunty aina ki bani chocolates d’in da uncle datti ya sayo min”, ta fad’a a lokacin da take nufar parlorn da mugun guru saboda har ga Allah tana mugun son chocolates hakan ya sa a kullum tazo gidan sai ta saka uncle Datti ya saya mata.

” Allah Khadija ba zan bayar ba, wai shin ba na hana ki shan zaki ba? ko zo kike yayi miki illah ne? ta fad’a a takaice tare da d’an had’e rai”.

 

 

Salon So Hausa Novels Complete

“Eeeyyaaaa aunty na yi hakuri ki ban, yau d’aya kawai ki ban nashi daga yau ban k’arawa.

 

” Hmmmmm nana kenan ke yarinya ce ba za ki fahimci illan shan zak’i ma mace ba but tunda kin ce haka mik’a min eye glass d’ina na saka sai muje na d’auko miki”, domin Rana mugun fama da chronic ciwon ido bata gani sai da glass medicated, idan babu wuri duhu baka kirin yake koma mata hatta tafukan hannayen ta ma.

 

 

Kamar dama jira take yi ta d’au glass d’in a kan glass table ta mik’a mata ta karb’a ta kafa daga nan ta jawo hannun k’anwar ta suka shige d’aki tace ta tsaya a waje dan kar taga mab’oyan.

 

Guda d’aya ta fito dashi ta mik’a mata ungo wannan tafi kar ki kuma damuna.

 

Maimakon ta k’arb’a ta turo baki ta tare da sakin kukan shagwab’a wai ita baza ta k’arb’a ba sai an kara mata.

Jin kukan nata yayi yawa uncle Datti ya fito ranshi a b’ace, shi dai bai san me ya saka saffffff baya k’aunar b’acin ran baby angel ba balle kukan ta, a duk ran da ta saki kukan rigima bai da tsukuni a zuciyan shi har sai ya biya mata bukatunta tayi shiru.

 

So tari idan yana rawar k’afa a kan Nana Aunty Aina har mamaki take wai shin tsakanin ita da Nana was yake aure? Me yasa baya tarairayanta kamar yanda yake yi mata? ko dai Uncle Datti son Nana yake, duk wannan tunanin su suke mata yawo a kwakwalwar ta ba tare da ta samo amsar su ba.

 

Gani tayi ya nufo wurin Nana ba duk ya gigice ya susuce kamar wani wawa yana lallashin ta” shiru, yi shiru my angel fad’a min me ke damun ki, wa ya tab’o min ke”, ya jero mata tambayoyi a tare.

 

Baki wangalau aunty Aina ta bud’e tana kallon shi da mugun mamaki, abunda ya dad’a bata mamaki ji tayi Nana ta kuma rushewa da kuka har tana shid’ewa ala dole ita tayi fushi shi kam sai ma gabaki daya ya fita a hayyacin shi ya rasa ina zai saka kanshi yaji dad’i.

 

Zumb’uro baki tayi cikin shagwab’ar ta tace “Uncle chocolate zan sha, aunty Aina tak’i ta k’ara min”, ta fad’a cikin kuka tana langab’e kai.

 

” To to to yi shiru zo muje na saya miki, fita suka yi daga gidan shi da Nana suka bar Aina a tsaye jigum kamar gawa tana mamakin Datti.

 

Da taga abun ba mai k’arewa bane ta fad’a kitchen ta dafa had’add’iyar shinkafa jelof wanda yaji kayan had’i, ga wani uban k’amshi da ya gama gauraye kitchen d’in, tana gamawa ta fad’a d’aki ta rage kayan jikin ta kana ta fad’a bathroom. Tana gamawa ta fito ta shirya tsaffff cikin leshi mai ruwan toka d’inkin riga da zani. Kallo d’aya zaka yi mata ka san cewa ta had’u ba k’arya domin kyaun ba daga kayan jikin ta bane daga itan ce, cuz she is a kind of beautiful.

 

Parlour ta koma ta zauna shiru- shiru babu su babu alamar su har aka fara k’iran sallar Magrib, tayi alwala ta gabatar da sallar ta, tana idar da sallar kenan sai taji sallamar Datti a d’akin ta, ta amsa tare da juyowa sai ganin Aina tayi da kaya niki-niki a laida ta tare ta da ido tana kallon ta”.

“Heeeee madam wannan kallon na mene ne?, Datti ya fad’a yana tapping d’inta da hannu.”

 

Ta d’an had’e rai tana kallon shi haba dear d’ina for how long zan fad’a maka cewa ka rage saya wa yarinyar nan kayan zak’i? You now it ba sai na fad’a maka dalilina ba sanin kanka ne cewa akwai mai ciwon Suger a family d’in mu and ance ana gadon ciwon ko ka manta ne”.

 

Come on wife……., ya fad’a tare da jan maganar, i know ina sane ban manta ba sanin kanki ne nima ba zan so abunda zai cutar da ita, ciwon suger bata kama yara under ages da zarar mutum ya doshi shekaru 40 a lokacin ne aka bata shawara da ta dinga kiyayewa.”

 

Amma duk da haka ka rage, kana shagwab’a yarinyar nan da yawa.

 

Murmushi yayi mata yana cewa” duk abun da nayi wa Nana ban fad’i ba jinin mu ce ita”.

 

Ganin yanda ta had’e rai ya san ya tab’o mutuniyar hakan yasa yace wa Nana ta je d’aki ta jira su, hakan kuwa aka yi bayan fitan ta ya rungumo abar shi zuwa jikin shi ya hau lallab’a da kalan soyayya har sai da ya tabbatar ta sauko.

 

Kasancewar shi ma’aikacin gomnati hakan yasa washe gari da safe ya shirya ya tafi Office dan akwai wani aiki a gaban shi da yake so ya kammala. Kwararren likitane asubitin Plateau Hoptil da ke garin jos, yana isowa ya tarar an kawo musu patient da za’ayi mata surgery breast d’inta wacce bayan gwaji aka tabbatar da tana d’auke da breast fibro domain”, haka suka shigar da patient d’in suka hau yi mata aiki, tun shigowan shi surgery room d’in sai wajen k’arfe uku kafin nan ya samo ya huta cuz aikin yau ba sauk’i mutane sunyi musu yawa”.

Bayan ya fito ne ya soma nema number d’in Aina a waya cikin sa’a ringing d’aya ta d’aga tare da yi sallama ya amsa mata”.

“Wife kin ji wajena shiru ko?

” ummmm”, ta amsa tana mai dad’a manna wayan a kunnen ta”.

” Baby angle d’ina fa it has been long to hear from her”.

“Tana room d’in ta she is busy playing with her teddy”, hmmmm wait kitso take mata”.

” Dariya mai sauti yayi kafin yace” baby angel kenan sarkin rigima any ways nima yanzun nan na kammala aikina yanzu ma haka gida na nufa, me zan taho muku da shi?”

“Komai muna da shi my man domin kuwa baka rage mu da komai ba”.

Tsintar kanshi yayi da jin dad’in maganar ta, Aina mace mai tattausan lafazi, ta san k’almar da zata yi amfani da shi dan ta faranta mishi.

Bayan sunyi sallama ya kashe way an shi daga nan ya shige mota bai zame ko ina ba sai family house d’in su ya tarar da kakar shi Hajiya Rahane wacce suke k’ira da tsohuwa tana kallo a talabijin tana yi tana karkad’a kai”.

Sallama yayi mata bata ji ba har ya zauna bata san da ma ya shigowa ba, tsinkayo muryar shi tayi yana cewa” tsohuwa kallo ake yi ne nake ta sallama baki ji ba?

Ta juyo a hankali tana kallon shi d’auke da murmushi a fuskanta” ai film d’in ne tayi dad’i da yawa, Allah idan ina kallo mai dad’i har ban so na daina”.

” Dariya yayi, ya mik’e ya d’auki goran ruwan faro ya b’alle murfin ya kafa a bakin ya hau sha, tsohuwa kan ci gaba da kallon nata tayi cikin shauk’i tana murmushi. Sai da ya sha iya shan shi kafin ya cire goran a baki ya maida muffin ya rufe yana cewa” affff ashe ma bamu gaisa ba, ya gaishe ta ta amma ba tare da ta d’auke idanuwan ta akan TVn ba”.

Da yake daffffff take da ta gama kallon haka shima ya zauna jiran ta amma shi ba kallon yake ba, fito da waya ya shiga gallery yana watching hoton baby angel.

Bayan ta kammala ne ta tattara dukkan hankalin tace” Abubukar”, ya d’ago da sauri yana kallon ta da mamaki ji yayi ta k’ira sunan shi gasau babu sakayawa.

” Ya baka taho min da y’ar jikalle na ba,? Tana nan sai rigima take yi kin san halin Nana”.

“Y’ar neman nan ba ta samu kana biye ta ba dolle yayi, ni dai ban san ranar da zata yi hankali ba”.

” Tsohuwa kenan, dai-dai da rana d’aya bana k’aunar b’acin ran Nana shi yasa nake biye ma fitinar ta”.

Haka dai suke ta hira kusan rabin hiran akan Nana ya kare, bai wani dad’e ba yayi sallama da ita ya nufi b’angaren mum d’in shi ya gaida ta kafin nan ya shige sauran sauran b’angarorin ya gaishe su daga nan kuma ya nufi gida a ranshi yana jin tsananin kewan Nana na kama shi.

 

eedatou muje zuwa…………..

 

*SHINNING STARS WRITER’S ASSOCIATION*

 

”’The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers.”’

 

*UNCLE DATTI

JIKINA YAKE SO!

©

*eedatou*

”’Follow and note me on Wattpad”’: *eedatou*

 

Page 3 and 4

 

Ba shi ya iso gida ba sai wajen karfe takwas da rabi na dare cuz of go slow din da yaci karo dashi a hanya.

Ko da ya iso ya tarar Nana a kan kujerar three seaters tana sharar barci sanye take da riga da gajeriyar wando wanda bai gama rude kanta ba, tsayawa yayi for some few seconds yana kallon ta murmushi ne ya d’an sub’uce mishi” lallai Nana sarkin kiriniya ji yanda take ta sharara barcin ta hankali kwance”, bin kayan jikin ta yayi da kallon sai yaga ta bala’in yi mishi kyau domin kuwa shekarun Nana bai hana bayyana kyaun surar ta ba, yanda jikin ta ya murje yayi b’ulb’ul zaka d’auka kamar ta yaran larabawa d’innan ne. Tsintar kanshi yayi da nufar wajen ta ya tsugunna dafff kunnen ta ya hura mata iskaaaa”, cikin barcin ta taji, ta d’an yi mik’a kamar zata rashi sai ta gyara kwanciya ta koma ta kwanta.

” Cije libs d’in shi yayi a hankali ya kuma kafe ta da ido, komai na Nana daban ne tana da kyau da kan diri, a hankali ya sa hannu biyu ya kinkime ta ya soma tafiya da ita, yayin da ya maida jakan shi da ya shigo da ita d’aya hannun nashi.

D’akin shi ya nufa ya dire ta a kan bed d’in shi kana ya lek’a d’akin Aina ya tarar da ita kan Sallaya ta idar da sallah kenan tana lazimi.

Zama yayi a kan tafkeken bed d’in ta ya jawo pillow ya kishingid’a yana jiran ta har ta idar ta ninke sallayar ta ajiye tare da zare hijabinta shima ta tana ninkewa lokaci guda tai murmushi tana kallon Datti” barka da dawowa mijina”, da murya mai zakin gaske ta fad’a.

Amsa mata yayi shima cikin murmushi kana ya d’an turbune fuska da tsigar wasa yace” shine kika bar min baby angel d’ina a parlour ita kad’ai ko? Wife mun kusa mu bata fa”,.

Ohhhhh damn it!!!!!!!!, na manta Nana batayi sallah ba take barci sai yanzu na tuno ma, mai baby angel tare muke da ita nima sallah ne ya shigo dani amma bari na tada ta”.

Kafin ya bud’e baki yayi magana tuni tayi hanyar parlour ko da ta iso bata tarar da kowa ba ta lek’e bayan kujera nan ma babu ita babu alamar ta, nan idanuwan ta suka cicciko kamar zata yi kuka? Ina Nana ta yi da daren nan ita da ta barta tana barci? Tsoro ne ya d’an kamata a lokacin da wani tunani ya fad’o mata ta safe kirji tare da waro ido waje” na shiga uku kar dai shigowa gidan nan akayi aka tafi da Nana”?

Kuka ta fashe da shi da gudu tayi d’akin ta ta tarar da Datti a inda ta barshi yana ganin yanayin da ta shigo a firgice yace lafiya kika shigo haka? Me ya faru? Banda kuka babu abunda take yi da kyau ta iya bud’e baki tace” banga Nana ba?”

“Kamar yaya baki ga Nana ba? Ya jefa mata tambaya fuskar shi na bayyana mamaki.

Wallahi na duba kafff parlourn nan babu Nana babu alamar ta, nafi kyautata zaton satota akayi”.

Sai yanzu ya fahimci inda ta dosa bai san sanda dariya ya subuce mishi ba har sai da ya kular da ita tace” wato baka damu da b’atan baby angel d’in da kake ikirarin taka ce ba shine ma na zama abin dariya?, ta kuma rushewa da kuka tana tunanin halin da y’ar k’anwar take ciki”.

Ganin abun nata dad’a k’aruwa yake yi gashi ko kad’an bai son jin kukan mace balle na wacce take da muhimmaci a rayuwar shi, wacce babu abunda zai iya saka mata da shi sai addu’a domin irin guduwar da ta bayar a rayuwar shi, ba shiri ya had’iye dariyar shi, cikin rad’a yace” yi shiru daina kukan haka matata idan ba su kike ki saka nima na taya ki ba, guess what? baby angel na d’akina tana barci.

Kuka mai d’auke da hawaye ne ya makale mata lokaci guda tace” Dan Allah? da gaske? ya d’aga mata kai alamar “eehh”

Zolayar ta yayi yana cewa” Ashe Ainata ma ta damu da baby angel d’ina amma tafi ganin ganin ina son baby angel fiye da kowa.

Kin san dalilin da yasa nake son Nana?

Ta girgiza mishi kai tare da yin kasa da kan ta tana murmushi kasa-kasa, ” sabo da wife d’ina tana sonta bayan haka jinin mu ce ma’ana soyayyar Nana a jinin mu yake”.

A tare suka kwashe da dariya daga nan suka d’unguma parlour ta serving d’in shi da abinci dan d’asu suka ci nasu da Nana suna ci suna hira har ya gama daga nan suka nufi d’aki suka shirya tsafffff suka kwanta tare da bama juna baya wanda ya kasance kamar al’adan su ne.

Tana jin Datti na ta sharara barci yana minshari, wannan wace irin bak’in kaddara ne? Anya zata iya cinye jarabawar da Allah ya rubuto mata kuwa? Wai ace aure kusan wata uku kenan su kwana ta tare su tashi tare babu abunda ke shiga tsakanin su?

Anya su Ummi sunyi mata adalci kuwa? Kaiiiiiii!!!!! Allah kana ji kuma kana gani……….., Allah kasa tsare min mutunci na kar biyayyar da nayi ma mahaifana na auren mijin da marar bukata wanda ko kad’an mace bata gaban shi ya yi silan jefa ni ga hallaka………, ka kare ni da mata masu irin matsalata daga sharin son zuci…………, tana kayo nan wani tsiririn hawaye masu d’umi wanda zafi da rad’ad’in kamar ana narka d’alma ne suka suma bin kyakkyawar round kuncin ta d’aya baya d’aya.

 

WAIWAYE ADON TAFIYA

 

Aina’u Muhammad Kabeer Danbaba da Nana Halima uwar su d’aya uban su d’aya kuma mahaifan su duk suna raye. Mahaifiyar su mutuniyar Katsina ce haififfiyar garin mamaga ce da ke karamar hukumar Jibia.

Mahaifin su Kuma Alhaji Abubakar haffaffen garin Bauchi ne su uku ne a wajen mahaifan su rak, yana da wa sunan shi Alhaji Isma’il wato mahaifin Datti da kuma autar su Hajiya k’arama usulin sunan ta Halima wato Nana sunan ta taci cikin su ita ce bata tab’a haihuwa ba”.

Datti wanda asalin sunan shi Muhammad wato shima sunan mahaifin Nana aka saka mishi, su hud’u ne a wajen mahaifan su, shine babba a wajen iyayen su, sai Ilham yayi aure a nan Bauchi take da zama a unguwar Federal low coast, sai Fu’ad wanda yannzu yaka yake zangon k’arshe a makarantar jami’a da ke Bauchi wato ABUBAKAR TAFAWA BALEWA UNIVERSITY, bayan haihuwar shi mahaifinyar su bata kuma samun ciki ba sai da Fu’ad ya kai shekaru goma sha d’aya kafin nan aka haifo Mardiya wace zasu yi sa’a da Nana”.

Sunan mahaifiyar su Datti Maryam ne amma ana k’iran ta da “umma” ita kuma mahaifiyar su Aina sunan ta Murja ana k’iran ta da “Ummi”.

 

Mahaifin su Alhaji abubakar wato Kabeer D’anbaba da kuma mahaifiyar su Sa’adatu wanda akafi dani da tsohuwa duk suna da ransu, kasancewar family d’in Kansu a had’e yake yasa suke zama a family house d’in su dan su kara dankon zumunci amma y’ay’an su kuma suka amince su zauna a duk unguwannin da suke so”.

Marsala ta farko da Datti ya fara fuskanta shine; so tari idan yana tare da friends d’in shi yana yawan jin labarin cewa duk namijin da balaga ya kamashi yana wet deals da dai sauran su, abunda yafi d’aure mishi kai tunda yake bai tab’a jin feelings, ko tayi wet dream ba, hasali ma mace bata gaban shi kuma bai d’auketa amatsayin komai ba.

Wannan marsala tun yana d’aukan shi k’arami har ta kai ta kawo ya girmama yafi k’arfin tunanin shi ya fara tunanin ko aljana ce ta aure shi, wannan dalilin ne ya saka har ya kawo munzalin aure bai tab’a yin budurwa ba, a gida anti anyi ya nemo mata a had’asu aure tun yana boye musu har ya yanke hukuncin Samar da iyayen shi halin da yake ciki game da mata.

Hankalin su ya matuk’ar tashi sosai da suka ji labarin babu kalar maganin da basu nemo ba da na gargajiya da na bahaushe duk sun nema amma shiru, gashi a lokacin yana aiki a asubiti suna gudun kar mutane su mishi mummunan fahimci kun san zaman namiji da kud’i babu mata ana d’auka fasiki ne, da wannan tunanin baban Aina ya yanke hukuncin nema mishi auren Aina a wajen baban shi tare da goyon bayan matar shi domin kare mishi kima da darajar a idon duniya.

Da farko mahaifin Datti bai nuna goyon bayan shi ba a cewan shi za’a cutar da yarinya ne a nakasa mata rayuwa daga k’arshe ya hakura ba dan komai ba sai dan su tsohuwa sun nutsar da shi a cewan su idan ba jinin shi ba wa zata amince ta zauna da namiji irin shi?

A haka har aka d’aura auren ya rok’a a bar mishi Nana wacce tun haihuwar ta taji yana son yarinyar sosai tamkar cikin su d’aya da ita.

 

************************************

 

CIGABAN LABARI

 

Rik’e yake da waya a hannun shi ya shafe kusan dakika biyar sai kai komo yake a d’akin shi kad’ai jefi-jefi yana cizon yatsa. Ba komai ne yake damun shi ba illa sanin kanshi ne tunda yake wato tun da ya fara falin balagan shi har zuwa yanzu dai-dai da kwana d’aya bai tab’a jin sha’awar mace ba, lokuta da dama idan suna hira da friends d’in shi har mamakin su yake wai idan suna kallon blue film suna jik’ewa amma gashi yau kusan goma kenan ya downloading yana kallo amma ko gizau bai ji ba.

Tsaki mai karfi ya sake tare da yin wurgi da wayan a kan gado ya d’au car key din shi ya bar gidan a gaggauce ya wuce chamber d’in su, a gefen wani garden ya tsaya yayi parking ya fito tare da yin ma mortar key, ya tarar da friends d’in shi su uku suna hirar su cikin raha, ko sallama bai yi ba ya nemo kujera ya zauna suna ganin su suka mik’a mishi hannu suna cewa” man yane ka shigo ba ko sallama”.

Tsaki ya kuma ja cike da takaici yana kallon su d’aya bayan d’aya” walle guys baza ku gane bane, kunsan ma me, na fi minti arba’in ina kallon blue film d’in nan amma ba wani feelings d’in da nake ji, kai like ma normal film d’in da babu romantic scene haka nake ji”.

“Whatttttt don’t say this please! cewar wani kenan wanda ake k’ira da Yusuf ya fad’a da mugun mamaki.

” haba man kar ka raina mana hankali mana, kana namiji ace ka kalli bf kace baka ji feelings ba? ko yaron da he is not well matured idan ya kalli bf dolle sai ya d’an ji canji a jikin shi balle kai da kake da mata? We taught duk wannan matsalar ya k’are a sanda aka maka aure ka gane ko so stop all this jokes we are no more kids”.

Sassauta murya yayi kamar zai fashe da kuka yace” wallahi billahil azim Yusuf da gaske nake Allah babu abunda ya janja har yanzu”.

A take suka tsura mishi ido da mugun mamaki, tunda suke basu tab’a cin karo da mai matsala irin na Datti ba, ba dan sun san halin shi baya karya ba da tuni sun karyata shi.

Can Usman ya nisa yace” tabbb inko haka ne ta yiwu ko haihuwar ka akayi da matsalar ko kuma matsalar jinnu ne?”

“No Usman bana tunanin hakan”. Fahad yayi saurin dakatar da shi, a iya tunanina may be process na maturity d’in shi ne ya zo da hakan it might be zuwa d’an wasu lokutan al’amuran zasu dai-daita.

To Allah yasa abokaina amma wannan matsalar babba ne ace kana namiji abu baka jin sha’awa, gayu akwai fa matsala fa”.

Haka ne amma da yardar Allah babu komai”, ya fad’a.

“Ni wallahi matar ka ce ta bani tausayi wallahi, duniya babu macen da zata amince a aura mata miji mai irin matsalar ka, say tari ma hakan ya kan yi silar kashe aure na sha jin labarin cewa mata da yawa sun halaka da irin wannan matsalar auren domin duk hak’urin mutum jiki da jini, ” Yusuf ya fad’a lokaci guda yana kakkab’e jikin shi yace” ku taso muje…………..

Mik’ewa suka yi su hud’u suka shiga mota ba su suka wuce ko ina ba sai club suka zazzauna suna chilling, kwalbar bear ne a jjjjugaban su suna sipping a hankali fahad, Usman da Yusuf suka mik’e suna ta rawa da yammata shi kuma Datti yana zaune a wuri d’aya yana kallon kywawawan samari da yammatan da ke wurin, ga mata iya mata wanda suka amsa sunan mata amma duk ba su ishe shi kallo ba, hasali ma bai ga dalilin da ya saka suka tsaya suna b’ata lokacin su akan mata ba shi ko kad’an bai d’auki jinsin mace a bakin komai ba, he is friendly to them amma kwata-kwata baya jin feelings balle ma mu’amala ya shiga tsakanin shi da mace.

Har ga Allah ba yana iya bakin k’ok’arin shi wajen tilas ta ma kanshi ko zai ji sha’awar Aina amma har ila yau baya jin komai game da ita, kuma yana sane da irin kawaicin da take nuna mishi a zaman su na aure, bata tab’a nuna ta kosa da shi, kuma bata tab’a neman shi da nufin kwanciyar aure ba shi yasa yake ganin kimar ta da darajar ta.

So tari yana tsananin tausaya mata da irin tauye mata hakkin da yake yi wanda shi kanshi ya sani halittane yanda bazai iya canja shi ba, da yana da wata dabara da zai biya mata bukata da tuni yayi, sometimes yana trying best d’in shi ya romancing d’inta amma duk da haka tamkar itace yake baya iya tab’uka mata komai, babu kalan romantic novels, blue films, din da bai nemo ba duk dan ya taimaka mishi wajen biyan bukatun shi amma abu yaci turaaa…., daga k’arshe ya rungumi k’addara ya zuba ma Allah idoooo.

What’s up guy!!!! cewar Usman kenan dan ya ga tund’asu yake zaune shi kad’ai.

Mtswwwwe ya ja tsaki lokaci guda yana lallon wrist watch d’in shi, saurin mik’ewa yayi yace” i need to get going guy”.

Why!!!!! Cike da damuwa Usman yayi maganar yana kallon Datti”.

“Nothing, kawai dai i can’t keep waisting my time ne a nan wajen, i see no reason da zan tsaya ina kallon abunda ma ba burgeni yake ba illa ma haushi da yake ban”.

Alrght, bye then zan fad’a ma guys d’in cewa ka wuce.

Owkkkkkkk yana fad’a ya bar wajen, gida ya nufa ya tarar da baby angel a kwance a kan cinyar Aina tana tsefe mata k’itso zata wanke mata kai, sallamar shi suka ji Aina tayi saurin sakin kan Nana a tare suka mik’e suka fad’a jikin shi suna dariya ya maida hannun ya had’e su waje d’aya kana Aina tayi saurin raba jikin ta da nashi tayi d’akin shi da sauri tana had’a mishi ruwan wanka.

D’ago da Nana sama yayi yana wasa da ita suna dariya sai ma ya ji moment d’in nan ma yafi mishi ganin matan da yayi a waje wanda yake d’auka marar amfani har Aina ta shigo ta tarar da su a hakan tace” dear d’ina wai baka gajiya da yarinyar nan ne? Shiga goma fita goma baby angel ni dai karta gajiyan min da kai.

Saurin sakin Nana yayi tare da mik’a mata tsarabar ta tayi d’aki tana tsalle kana ya yi wajen Aina ya lakaci hancinta da hannun d’aya yana murmushi wanda ya bayyana dimple d’in shi yace” Mrs complainer an bar miki mijin ki d’in what next”? ya d’aga mata gira.

“Take your bath”, cikin muryar shagwab’a sai ya tsaya yana kallon ta.

Me kake kallo bae?

Shagwab’ar ki ce ta burgeni?

How i wish i will have feelings for you da na gwada miki tsantsar soyayya, forgive me wife, ki yafe min na san na gaza ta wajen biya miki bukatan ki, saurin rufe fuskar ta da tafukan hannayen ta tayi, Aina………., ya k’ira sunan ta da daskararriyar murya tayi saurin cire hannun daga fuskar ta tana kallon shi”.

Ba laifi na bane da na zama rago a gare ki”………,

Ba laifina bane da na kasa cika miki mara da ruwa wallahi Aina da da hali da nayi ko zan samu sassauci a zuciya ta domin kuwa zuciyata cike take da tausayin ki da ni kaina”………

Tunda ya fara maganar kwalla ya soma zubo mata ya rungumo ta yana lallashin ta tare da fiddo da hanky yana goge mata a kunne kuma yana binta da tattausan lafazi har sai da ya tabbata ya saka ta dariya kafin nan yace mata ta taya shi wanka, ta waro ido tace” babbar magana!!!!! Ina zata iya cud’a datti sallon taje tayi gane-gene? Duk abunda take fad’a a kasan zuciyar ta ne.

 

Nace :lol kika sani ko daga nan ya wulla da ke duniyar dad’i? Abunda kike mafarkin samu ne fa.

 

Kamar ya gano ta ya d’an ja kunnen ta da k’arfi har sai da ta saki ihu a hankali mai d’auke da kissa da kisissina tace” ouch kunnena zafi!!! Zafi dear “.

” Saurin sakin ta yayi da sauri yayi hanyar d’akin shi kana ya juyo ya kashe mata ido d’aya yace” that’s your punishment for disobeying your husband, next time idan kika bijirema umurnina it will be more worsen than this”.

Ta marairace fuska kamar zata yi kuka ya kuma mata gwalo ya haura zaman bene da gudu yana waiwayowa yana mata gwalo.

Tana ganin ya tafi tayi d’an murmushi a ranta tace” Matar Datti kenan, zaman gidan Datti gwanin birgewa sannan kuma gwanin kunci, ba dan matsalar shi ba da zata iya cewa tafi kowa sa’an miji”.

Cije lab’an ta tayi na kasa ta bi bayan shi itama tana shiga ta tarar yana bathroom, direct wardrobe d’in shi ta nufa ta nemo mishi dogon wando da shirt baka ta d’ora zaman bed d’in shi, bata tsaya b’ata lokaci wajen nemo tuarare ba cuz shi kanshi kayan baya bukatan turare, cuz like b’arin turare akayi a jikin kayan saboda dukan su ma’abota tsafta ne shi yasa a kullum k’amshi kama jikin kayan su yake yi”.

Shelve d’inshi ta nufa ta d’auko novel tayi rigingine a kan gadon shi tana karantawa cikin nisad’i cuz story d’in ya d’auke mata hankali matuk’a haka kawai take jin shauki na kamata”.

Some parts na labarin dariya yake bata tayi ta tuntsirewa da dariya wasu kuma ya bata haushi, idan aka zo wajen tausayi tayi ta Jan majina da kyar tana kokarin hana hawaye zubo mata jim kad’an sai gashi ya shigo kugun shi d’aure da towel yana rik’o hand towel yana tsane ruwan jikin shi, kallon ta yayi yace” seams like u are carried away?”

Ta juyo tana fad’in” yeah”, it’s very interested”.

Mikewa tayi a hankali taje kan shelve d’in ta ajiye novel d’in a wajen da ta d’auko, ta d’auko kayan da zai saka tayi wajen shi a lokacin har ya gama yana shafa mai.

Sai da ta jira ya gama ta mik’a mishi ya k’arb’a yana mai zuba mata albarka tayi murmushi ta koma main parlour ta bashi wuri ya saka kayan.

Tarar da Nana tayi da Teddy d’in ta tana wasa tace zo nan na k’arasa miki tsifan, ba shiri Nana tayi wajen ta da sauri ta hau tsefe mata kan.

Da yake kad’an ya rage su gama hakan ya saka basu wani b’ata lokaci ba suka gama daga nan ta jata zuwa wajen da suka tanadar domin wanke kai ta wanke mata tsaffff da shamboo ta had’a da anti-dandruff tana gamawa ta hau drying mata kai da hand dryer.

Fitowan Datti kenan ya tarar babu kowa a parlour kamar zai yi d’akin Aina sai kuma ya fasa ko mai ya tuna ya nufi saloon d’in nan ya tarar da har Aina ta gama drying ma Nana suma tana tufke mata da baby pink na ribbon.

Babu abunda kan Nana ke yi idan banda k’anshin tsadaddun mayuka da kuma turare na kai, ga wani irin sexy shinning d’in da suman ke yi.

Waya ya fiddo a ya hau musu video yana tsokanar Aina wai zata kyau da aiki a saloon ji yanda ta dad’a hasko mishi baby angel d’in shi.

Dariya ta hau tace” na ga wacce zata k’ara tab’a kan Nana da sunan wanke kai tunda abun ya zama da tsokana”.

A wajen ne yake fad’a musu su shirya ya kaisu family house, sunyi murna sosai da d’oki har rige-rige suke tsakanin Aina da Nana shi kan me zaiyi in banda dariya har suka fito suka nufi hanyar fita a tare suka shige mota sai gida.

 

Ko da suka iso d’akin tsohuwa suka fara nufa suka tarar da Alhaji Abubakar(baba Karami) da wan shi( baba babba) suna hira da mahaifiyar su cikin shauk’i da jin dad’i.

Sallama suka yi suka shigo ko da tsohuwa ta gansu da sauri ta mik’e ta tare Nana tace” oyoyo jikalleta ta”, Aina tace” matsa ni kam tsohuwa na gaida iyayena kin tare min waje, Nana kad’ai kika gani a nan?, ta fad’a da tsigar wasa tab’a botsarewa.

“Iyeeeee ka ji min ja’ira kikayi wasa iyayen naki na naha su amsa gaisuwar taki naga ta fad’in k?”

Dariya Aina tayi” haba aminiyar ai bama haka da ke”.

Gara dai……., ta ja kwafaaa su duka suka saka da dariya banda Nana da tayi jikin baba babba ta fad’a tana cewa” oyoyooo babana.

Bayan duk sun shigo suka zazzauna, Datti da Aina suna zaune a kasa yayin da har ila yanzu Nana ke jikin baba Karami yana mata wasa yana cewa wai bata san ta fara girma bane?

 

eedatou…….

 

SHINNING STARS WRITER’S ASSOCIATION*

 

”’The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers.”’

 

 

UNCLE DATTI

JIKINA YAKE SO!

 

©

*eedatou✍🏻*

”’Follow and ✅ote me on Wattpad”’: *eedatou*

 

Masoya littafin Uncle Datti jikina take so bana ganin comments and votes d’inku shi yasa jikina yake mutuwa da yin typing Allah had na canja littafin na fara typing wani sabo sako muku ne kawai banyi ba. Ku daure ku dinga karfafa min gwiwa tunanina ya fara karkata na daina typing littafin UNCLE DATTI JIKINA YAKE SO.

 

5&6

 

Banga laifin kowa ba duk Datti ne ya gama sangarta ta, cewar tsohuwa kenan.

Turb’une baki tayi kamar zata fatsa kuka Datti na ganin haka ya taso har izuwa gaban mahaifin shi ya tsuguna gaban ta yana lallashin ta ita kamar dad’a k’ara ingiza ta yake yi” shtttttt shtttttt yi shiru mana baby angel kyale tsohuwa fad’a take nema, nan ne ya samu Allah ya taimaka ta maida hawayen da kiris ya rage su zubo mata.

Kwa dai ji da shi, ni kunga tafiya ta ba zan iya da shiriritar ku ba tayi hanyar d’akin maigidan ta.

Ganin haka ya sa su baba Karami da baba Babba suka mik’e suma” tunda kun kuran mana uwar mu muma kunga tafiyan mu.

Bayan fitan su suma suka mik’e suka yi cikin gida, Nana d’akin mahaifiyar ta tayi da gudu tana kwala mata k’ira ita kuma Aina tayi d’akin sirikarta, a parlour ta tarar da ita ta tsugunna har kasa tana gaishe ta. Cike da farin ciki ta amsa mata tana tambayar lafiyan su ta amsa mata da cewa duk suna nan k’alau.

Hamdala tayi kafin ta shiga yi mata nasiha sosai mai ratsa jiki Aina banda godiya babu abunda take mata.

Jimmm kad’an sai ga Datti ya shigo ya samo wuri ya zauna a gefen kujerar mahaifiyar shi tare da sakin k’ara washhhhh umma na gaji”.

Ta sakar mishi hararar wasa tace” ban son sakarci banza aikin me kayi?

Hira ne ya b’arke a tsakanin su har har Fu’ad wanda tun shigowan su yake d’akin shi bai sun zo ba ya fito yana latsa waya ya tarar da su, sosai yayi murnar ganin su dan shi mutum ne mai faram- faram da mutane saidai ko kad’an baya son raini ba kamar Murja ba wacce take miskila, idan ba wanda ta sani sosai ba bata fiye sakewa da mutum ba.

Laaa auty ashe kun taho? Ehhh wallahi Fu’ad yanzun nan ma kuwa”.

Nemo wuri yayi ya zauna ba tare da ya d’auke idanuwan shi a kan wayan ba”.

Wai ina mutuniyar ne ban ji duriyar ta ba? yana nufin Nana kenan, Datti yayi mishi harar k’asan ido yace” me zaka mata?

” Yaya kenan da ka tambayar wajen Nana sai kace me zan mata? Me ma nake dashi da zan bata”. umma ki ji min yaya fa? Ya juyo ya shagwab’e fuska yana kallon mahaifiyar shi wacce tun d’azu sai murmushi take yi.

“Hmmmmm ka ma dai da taka kalar fitinar, kai ma ka dai san halin yayan naka sarai, ni dai na ga ranar da Nana zata bar gidan nan ayi mata aure ko binta zaka yi gidan miji ohoo”?

Dariya suka saka su duka banda shi da

Rad’e rai yayi sosai, bai san me yasa ba yaji zuciyar shi ta tsaya cakkkk, ba komai ne ya ya sa hakan ba illa maganar umma, sannin kanshi ne duk son shi da Nana dole watarana sai tayi aure ta koma karkashin wani, to wai ma me ye na suka wannan tunani? Idan tayi aure me matsalar ka aciki? jefo ma kanshi tambaya yayi yana mai tuhumar kanshi.

Nana kam tana can b’angaren mahaifiyar ta tunda ta shigo gidan ta lik’e mata sai surutai take mata, Sallama aka yi aka shigo” Fu’ad ne ya shigo Nana ta wani had’e rai kamar wanda bata tab’a sanin shi ba, yana sane da hakan amma ya fuske cuz shi dai haka kawai yarinyar bata wani burge shi, ya rasa dalilin da yasa brother d’in shi ke nan da nan da ita tamk’ar duk familyn itace kad’ai gare su”.

Kallo d’aya yayi mata ya d’auke kai ya koma gefen ummi dama a parlour suke ya bi lafiyar three seaters ya kwanta tare da fad’in” Ummi yunwa nake ji ko zan samu ragowar abinci a wajen ki?

Murmushi tayi mishi tace” Fu’ad kenan me zai hana? Idan ma babu ai sai na saka Nana ta dafa maka”.

Saurin mik’ewa yayi ya zauna da mugun mamaki yace” what? Wata Nanar ba dai wanan ba?

” Ita d’in dai da ka gani a gaban ka?”

“Me wannan zata iya dafawa banda jagwalgwale?”

Dariyar sosai ta saka dama da wasa tayi maganar banda abunshi du-du-du nawa Nanar take da har zata saka ta dafa mishi abinci ita da ko tafasa ruwa ba’a koya mata ba?, mai da wukar wasa fa nake maka.” Ga mamakin su, ji suka yi Nana ta saki tsaki mai k’arfi duk suka bita da kallon mamaki, magana ce ta hau yi a zuciya bata sani ba ashe ya fito fili tana cewa”, Allah ya sawwake ma na dafa ma abinci, wallahi ko yunwar kashe ka zata yi ba zan dafa ma ba gara ka mutu…………ummi saurin buge bakin ta tayi da k’arfi tana cewa” ja’ira sai dai ke ki mutu amma ba shi, banda bakar zuciya ma d’an uwan ki kike ma fatan mutuwa?,

Sosai yayi mamakin rashin kunyar Nana yarinya k’arama kamar ita ace ta gasa mishi magana dan rashin kunya har da ja mishi tsaki? nan da nan yaji ranshi ya mugun b’aci idanuwan shi ne suka sauya launi saboda b’acin raiya, kyale ta kawai ummi zanyi maganin rashin kunyar ta, yaja kwafa ya koma ya kwanta”.

Ba tare da ta bi ta kanshi ba ta hau wa Nana fad’a ta inda take shiga ba ta nan take fita, Nana kam ta sa kuka da gudu tayi b’angaren umma, hira suke yi amma tun daga nesa yake jiyo sautin kukan ta yaji gaban shi ya mugun fad’uwa, iso wajen su tayi na ganin Datti ta dad’a k’ara saurin kukan ta ta fad’i k’asa tana birgima tana cewa” an tsane ta, dama ba son ganin ta make a gidan ba”, a rikiceyayi wajen ta da Sauri” ya Salam !!!!!! da wata irin dashashiyar murya yayi maganar me ya same ki kike kuka? Wa ya tab’o min ke? Yi shiru Nana ta ki fad’a min”.

Jawo ta yayi a jikin shi yana lallashin ta ita kam tamkar ingizata yake haka take ji, ta dad’a lafewa a jikin shi cike da shagwab’a ta cigaba da rera kukan ta”. Shiru yayi na y’an wasu dakika yana sauraran ta, yayin kukan nata ke dad’a rasa shi, k’irjin shi yayi mishi nauyi da yawa kamar an aza mishi dotse a ka. Ba komai ne yafi d’aga mishi hankali ba illa kukan Nana da ko kad’an baya k’aunar ji. Ganin ba zai iya jure hawaye a fuskar Nana ba yayi saurin raba ta da jikin shi ya dunk’ule hannun shi ya kaiwa iska naushi yana huci kamar mayunwacin , su ummi kam banda ido babu abunda suke binshi da shi, ita kam ba ma kukan Nana bane, yanda duk ya rikice akan ta ne ya mugun bata mamaki har ta fara zargin cewa gaba akwai kallo tsakananin su, ba dan Aina shakikiyar Nana bace wallahi babu abunda zai hanatayi zargin cewa Datti na tsananin son Nana, ba so irin na wa da k’anwa ba, so na auratayya”.

Hannun shi d’aya ya aza a saman kafadar ta, dayan kuma ya d’ora a saman lab’an shi yayi da tsigar lalashi yace” sheeeee……., kana ya tausasa murya a hankali yace” kukan ki nasa nima naji kamar nayi kuka angel, kina so nayi kuka ne Nana?

Ta girgiza kai tana sheshshek’ar kuka, to idan bakya so nima nayi dan Allah ki fad’a min, wa ya saka ki kuka?”

Sai yanzu ta samu damar tsagaita kukan nata, ta hau kora mishi bayani har ta gama, ji yayi ranshi ya kuma baci sosai fiye da na farko a zuciye yayi hanyar b’angaren Ummi duk suka bi bayan shi cuz a tsorace Duke da lamarin shi”.

Tarar da su yayi hankalin su kwance suna hirar su har ga Allah sun ma manta da mai ya faru dan Fu’ad had ya tashi ya sako abincin yana ci yana zuba santi wai ya rasa tsakanin ta da Umma wa tafi iya girki, banda tsiya da dariya babu abunda take mishi, ga zaton su sai ji suka yi Datti ya damko Fu’ad da k’arfi ya sharara mishi mari ji kake tasssssss, ya nuno shi da hannu yana wuci idanuwan shi had rufewa suke cuz of tsabar b’acin.

How dear you!!! Wa ya baka dama ka saka baby angel kuka?

Ba su umma kad’ai ba hatta ummi duk sun rikice sun rasa abun yi yayin Fu’ad ya dafa da kuncin shi yana murzawa ba kad’an marin ya shige shi ba, a take yaji ranshi nayi mishi suya, ji yayi ya tsana yarinyar tsana mai matukar gaske, a yanda zuciya ta d’ebe shi kamar ya kama ta ya nad’a mata duka dan ya wuce haushin tunda akan ta ne d’an uwan shi ya mare shi.

Ya had’iye miyau mai d’aci zuciyar shi cike da dafi yace” yaya akan Nana zaka mare ni? Me kuma tace nayi mata?

Yi min shiru munafiki ni zaka tambaya?

Shiru yayi tare da jefa wa Nana harar tsana ya ja kwafa ya fice daga parlourn abincin da bai gama ci kenan ba ya nufi main parlour ya zauna. A take yaji wani irin tukukin bak’in cikin ya ya kama shi, ba shiri ya ciro waya a aljihun wandon shi ya shiga failing numban friend d’in shi Kamal.

Bayan ya d’aga wayan ne ya shiga kora mishi labarin abunda ya faruwa yana gamawa yace” wallahi tallahi na sha alwashin sai na illata rayuwar rayuwar ta……….! sai na  maida  Datti abun tsana da kyama a waken al’umma……………, domin kuwa sai na d’auki fansar abunda yayi min…………bashi ne kuma sai ta biya, aka ce ramakon gayya sai tafi ta gayya zafi!!!!!!! kit ya kashe wayaan ba tare da ya jira komai ba”.

Abunda bai sani ba ashe a kunnen baba babba yayi maganar da ma ya part d’in tsohuwa ya so ya zauna a nan.

Kunnuwan shi na jiye mishi mugayen zantuka daga bakin fu’ad ya daka uwar tsawa yace” Baka isa ka cutar da Nana ko ka tozartata ba………..kuma ina mai tabbatar maka da cewa duk abunda ya same ta kaine sila!!!!

Shan jinin jikin shi yayi ,sumi-sumi ya mik’e ya bar parlourn.

 

B’angaren Datti kuwa bayan barin Fu’ad wajen ya ja hannun Nana keeee suka fita daga gidan Aina na ganin haka tabi bayan su da sauri gyale a hannu sanin kanta ne muddin ta bari suka tafi to sai dai ta taho a motar kasuwa, ko acab’a gashi a al’adar ta bata kaunar sa.

A mota kuwa masifa yake tayi har suka iso gida, yayin da take jero dankaren dana sani a zuciyan shi,” ji fa daga zuwan su ko minti talatin ya tabbata basu kai ba amma dan rainin yaron nan sai da ya sanya mishi angel kuka, Aina kam shiru tayi abunta gudun karya sauke haushin a kanta cuz kad’an daga aikin shi kenan, Nana kam ko a jikin ta sai ma dad’in da take ji a ranta musamman da ta ga ya mare Fu’ad dama haka take so cuz Fu’ad nayi mata shishshigi da yawa,

 

A raina nace; Nana at this aged kike cewa gardeden kato namiji kamar Fu’ad yayi miki shishigi?

Sati guda suka d’auka ba tare da sun waiwaye gidan ba cuz fushi sosai Datti yake da su ummi, a cikin satin ne ma ya neman ma Nana wani tsadadden makaranta cuz a wajen yake so ta zana jarabawar ta ta JSCE. ABUBAKAR TAFAWA BALEWA INTERNATONAL SECONDARY SCHOOL shine makarantar da ya samar wa Nana shi ke kaita ya d’auko ta, kuma ya nemar mata mai yi mata extra moral lesson zuwa wani watan za’a yifara mata lesson.

A ranar da ya kawo mata form d’in makarantar ba karamin murna tayi ba, kasancewar ba wani tazara sosai tsakanin gidan su da kuma makarantar. Ranar farko da Nana ta fara halartar makarantar ta ga sauyi sosai, tsarin makarantar kuya ya kayatar da ita matuk’a.

Principal office ya fara kaita yayi mata registrations both PTA da school fees d’inta, daga nan ya damkata a hannun principal na makarantar ya nuna mata ajin ta tare da introducing d’inta gaban sauran y’an uwanta students.

Bayan fitan shi ne wata fara tsiririyar yarinya mai tsawo kad’an, wanda shekarunta ba za su wuce na Nana ba ta taho ta zauna a kujerar ta, time d’in Nana na bud’e litattafan ta tana rubuta sunanta a jiki da kuma ajinta, JS2B shine ajin da naga Nana ta rubuta a kan littafin ta, tana jin zuwan yarinyar amma bata d’ago ta kalle ta ba balle ta sa ran zata kulata, ganin haka ya saka yarinyar ta bugi bencin a hankali lokaci guda tace” hi”, a sannan ne ta d’ago ta kalle ta d’auke kai tare da amsa mata ciki-ciki.

Ta so ta ja Nana da hira amma bata samu fuska ba, ba shiri ta koma seat d’inta da zauna dan ko kala Nana bata kuma furta mata ba, tana nan zaune ita kad’an ta har teacher ya shigo ya gabatar da darasin shi, a ranar sun sha darasi sosai almost duka periods d’in sai da aka shigo musu, Nana har gajiya tayi Allah cikin ikon shi closing hours na cika Lamar had’in baki sai ga datti ya parking mota a d’an nesa da ajin su kad’an yana jiran ya ga fitowan Nana.

Daga bakin ajin su ta tsaya tana kallon yanda mata da maza ke ta giftawa, duk ta kosa taje gida cuz yunwa ta kama ta sosai, kamar ance ta d’ago ta hangi motar Datti da sauri ta nufe shi, daga nesa ya hango ta ya tsare ta da ido, fuskar ta ya fara kalla ya ga tayi wani irin fresh zai oya rantsewa da Allah a kaffff makarantar babu wacce rayi na biyu balantana ta kama kafar Nana a kyau

Duk da karancin shekarunta bai hana ta fahimci cewa Uncle Datti ya gama nisawa a kogin tunani ba, ya kafe ta da ido gashi ya kasa d’auke su daga gare ta ya sa ta yin gyaran murya kamar wata babbar mace” eehheennn”, yayi firgigitttt ya dawo daga hayyacin shi tare da zira hannu a aljihun wandon shi ya fiddo da hanky yana share zufan da ya karyo mishi”.

Muryar ta ya ji ya daki dodon kunnenshi har ya saka shi saurin numshe ido kana ya bud’e su a hankali ya maida hanky. Ba komai be ta fad’a ba illa nuje ko?”, ta nufi kofar motar ta bud’e ta shige abinta, yana ganin haka ya shige mota shima a kasalance ya tada motar sai gida.

A parlour suka tarar da Aina tana cin pepper soup na kayan ciki ga fresh milk a gefen ta ta baje tana ci tana sipping at the same time kuma tana watching Hausa series film na Labarina wacce yake zuwa daga tashar Arewa24. Muryar Aina taji da sauri ta maida kofin fresh milk din ta ajiye dama ta kai baki kenan zata sha.

Murmushi tayi fuskar ta na bayyana tsantsar jin dad’in ganin y’ar uwar ta tace” maraba da zuwan student, har kun taso ne?”

Kai ta d’aga mata tare da zare site bag d’inta tayi jefi da shi kan kujera tayi kitchen da sauri ta d’au spoon ta zauna a gefen Auntyn tata itama ta hau ci, uncle Datti kam tsayawa kallon ta kawai yake yi, sai yanzu ya fahimci cewa dama can yunwa ce ta dame ta shi yasa d’an surutun da take mishi ma bata yi ba”.

Aina ce ta mishi barka da dawowa, ko zama bai yi ba ya sa kai ya fita yace ma Aina zai je ya dawo nan ba da dad’ewa ba.

Bayan sun gama ci Nana ta tattara plate d’in ta kai kitchen ta d’auraye sai ga aunty Aina ta shigo itama dama ta d’ora girki tuwon sakwara zatayi da miyar egwisi, har ta daka sakwarar ta ta nad’e a leda ta saka a flask saura miyar kenan ta gama had’awa shine ta koma kitchen ta zauna tana cin kayan ciki.

Nana na gama wankewa ta juyo tana kallon Aunty Aina da fararen idanuwan ta, tana kallon yanda take jujjuya spoon d’in kamar baza ta CE komai ba sai kuma naji tana cewa”, auty Aina girki nake so ki koya min”.

Dariya ta kusa ba ma Aina har sai da ta kusa sakin murfin pot din dan dariya ma har kwalla take fiddawa, da kyar ta iya tsagaita dariyar tata tace”Nana girki fa kika ce? Ina me ina iya girki yanzu dududu nawa-nawa like? Ki bari zuwa gama idan kika k’ara shekaru akan na yanzu sai na koya miki”.

Had’e rai tayi cikin rigimar ta ta cuno baki tace” Allah aunty da gaske nake, d’an rainin sense d’in nan ne fa ya yarfa ni gaban ummina yana cewa ban iya komai ba”, shi yasa nake so ki koya min cuz bana son raini”.

Da mugun mamaki ta tsaya tana kallon ta, ta fahimci cewa da Fu’ad take yi shi yasa manyancen ta ya mugun bata mamaki, tsawa ta daka mata tace” Fu’ad d’in ne kike gayawa haka? to shikenan bari na k’ira shi a waya na fad’a mishi ya min maganin ki ta yi hanyar d’aki ta sauri sai ga Nana ta bita a baya tana mata magiya, cuz cikin ta ya d’uri ruwa sosai, sanin kanta ne muddin Fu’ad ya ji wannan labarin to wallahi babu abunda zai saka ya zo har gidan ya b’abb’alata gashi wanda yake tsare mata fad’an baya ya fita.

Dan Allah Auntyna kar ki calling d’inshi…….., wallahi ban sake raina shi……., dan Allah mana auntyna…….., idan ya ji b’allani zai yi”.

“Ai gara yayi maganin ki tunda bakya jin magana,”Ta ciro waya ta wani dake tana latsawa ala ita da gaske take, Nana da tsoro ya gama kammata ta yi fici-fici da ido kamar wata munafuka, ta kwantar da muryar tace” haba Aunty Aina wallahi da gaske nake, Allah na ratse ban k’arawa, ta dakata da latsa wayar ta jan kwafa, Allah ya taimake ki da yau sai kin yabawa aya zakin ta, tana fad’a ta sa kai tayi kitchen Nana na ganin haka ya saki sassanyar ajiyar zuciya irin ta relief kana ta bi bayan ta, cikin rashin sa’a ta tarar har Aunty Aina ta gama miyar tana shirin barin kitchen d’in kafffff suka yi da Nana wacce take nokewa a bakin k’ofa.

Kamo hannun ta tayi suka nufi parlour ta suka zauna suka tarar ashe an gama shirin “Labarina”, Kamar dama da su aka canja program d’in aka saka “akushi da rufi”, program na yau dai akan miyar agusi za’a yi shi, murmushi Aunty tayi ta d’an gyara zama tare da kallon Nana wacce d’ungurugum hankalin ta na ajan Tvn bangon kana ta maida kai itama tare da tattara nutsuwar ta, a take aka hau gabatar da shiri tiryan-tiryan ake bayani da kuma gwada yanda ake sarrafa miyar duk inda Nana bata gane ba ta na tambayar Aunty Aina ita kuma ta mata bayani yanda zata fi d’auka.

A ranar kusan abinci kala uku Nana ta koya a wajen Aunty Aina sai bitar shi take yi a kwakwalwar ta tana imagination ga ta nan a kitchen tana dafawa.”

B’angaren Datti kuwa majalisar su ya nufa ya zauna a gefe shi kad’ai ya na sauraran maganganun abokan nashi”, shauki!!! shaushi shi yaushe zai ji shauk’in nan? Yaushe ne zai d’auke mace a matsayin abokiyar more rayuwa? Yaushe ne zai ji dad’in mace, ya nuta ta da ita, mace ta jiyar da shi dad’in da maza suke ji a jikin su? Yaushe ne zai ji son sexxx a ranshi?, tunowa yayi da Ainar shi mace mai kyau da kyaun diri amma ko kad’an baya jin sha’awar ta kamar yanda yake ji akan sauran mata, sosai ya nisa a tunanin ya gama mantawa a inda yake sai ji yayi an buge kafad’an shi, da sauri ya dawo cikin hayyacin shi yana bin shi da kallo. Mumin ya kayi shiru muna chatting ka matsa gefe kayi shiru kana tunani?” “Kyalle shi dai Yusuf kaima ka san halin mutumin namu, kulli yaumin zaka zauna da Datti amma baya cikakken minti goma ba tare da ya fad’a tunani ba”. Cewar Usman kenan cikin rashin jin dad’i da kuma tausayin abokan shi.

Kafe su da ido datti yayi kana yace” mene sha’awa? Yaya aje jinta, ma’ana alamomin ta? Kuma yaushe ake jinta? har zucuyan shi ya fad’a tare da jaddada k’almar a zuciyan shi”.

Tambayar ta daki zuciyan su sosai duk suka yi shiru aka rasa Wanda zai amsa musu tambayar, can Fahad ya ya ja dogon numfashi ya sauk’e a hankali yace” Sha’awa abu ne da kuma wajibi ne ga namiji da mace, wanda Allah(S.A.W) ya hallice su su bauta mishi sannan kuma ya saukar da sha’awa a tsakanin su domin suyi aure su hayayyafa ranar gobe kiyama yayi alfahari da su”.

Usman cikin dakewa yace” Alamomin sha’awa sun kasu kashi-kashi kuma kowa da alamar da take saukar mishi da sha’awa, ma’ana ga namiji akwai wajen da idan yayi arba da su yana saukar mishi da sha’awa ya ji idan ba ya kusance ta ba bai samun sukuni.”

About the author

Hausa_Novels

3 Comments

Leave a Comment