Littafan Hausa Novels

Jikar Maguzawa Hausa Novel Complete

Hausa Novels
Written by Hausa_Novels

Jikar Maguzawa Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

JIKAR MAGUZAWA

 

1-5

 

Official

By

 

AsmaBaffa

 

 

 

SHIN KIN SAN SHAHARARRAN GROUP ƊIN NAN DAYA SHAHARA WAJEN KAWO SHAHARARRIN FINA-FINAN DA SUKA SHAHARA WAJEN SAKA MA’ABOCIN KALLONSA A CIKIN NISHAƊI DA FARIN CIKI?

IDAN HAR BAKI SANI BA LALLAI KUWA ANA YI BABU KE!

KODA YAKE HAR YANZU AKWAI BABBAR DAMAR ZUWANKI DON A CIGABA DA DAMAWA DA KE IDAN HAR KIKA JONE DA MU!

 

Kuna ina ma’abota kallon shirye-shiryen Arewa24 na ƙasashen waje da suka fara ba su ƙarasa ba? Yi Maza ka garzayo wannan maƙala don ƙarasq kallon shirye-shiryen.

 

Kuna ina ma’abota karatun lobayya wato ma’abota karatun littafan hausa? Shin na tambayeku akwai wani novel da kuka karanta har yau baka samu karashensa ba? Ko kuwa akwai novel ɗin da kake nema ruwa a jallo ka rasa? To kaima garzayo wannan maƙala domin dacewa da haziƙan fasahan littattafai.

 

‘Yan gayu sam! Bamu barku ba! Kina son koyon kwalliya ɗaurin dankwali kala-kala? Yi maza ki jone da mu kin ji? In sha Allahu sai dai ki koyawa wasu, domin an tanadar muku kyawawan vedios wanda zasu taimaka ki koyi kwalliya da kanki, ki koyi ɗauri da kanki.

 

Anzo wajen! Wato fannin girki! Ayyuriririiiii!

Duk kyan mace sai ta iya girki ta cika sunanta kyakkyawa! Maza-maza yar’uwa ki jone da mu don kuwa muna kawo manyan-manyan girki masu daɗi da ɗanɗano wanda ba su da wuya balle ma ace sai ankashe musu kuɗi. Ke dai shigo ki ganewa idonki!

 

Ƙarshen-ƙarshe kenan! Wato ba anan fa aka tsaya ba akwai wani babban albishir ga masu son group ɗin, shi ne babban tanadin da akai don kawai a faranta muku! Tanadin kuwa shi ne, akwai haɗaɗɗan novel da ya haɗu iya haɗuwa ya tsaru iya tsaruwa da aka yi shi musamman dan ku, wato wanda ake sakinsa a iya group ɗin kacal, wanda wasu manyan marubuta ne ke rubuta su, duk dai sai kin antayo zaki ganewa idonki. Wannan ma na ɗaya daga cikin littafan.

Kalli katsa kaɗan!

 

Galadima Family Hausa Novel Complete

 

*TSARE TSAREN WOMEN24 TV WHATSAPP DA WOMEN24 TV VIP👇🏾*

 

DAURE KI KARANTA DAKYAU

 

Akwai groups guda biyar(5) da muke tura littafi wanda marubuta keyi kyauta da kuma littafin da Sai a group ɗin zaki iya samu sannan da wasu groups ɗinda muke tura videos na makeup, daurin dan kwali, girke girke, Indian Hausa da shirye shiryen AREWA24

 

Group ɗin akwai na *MATA* daban sai na MAZA daban bama hada *MAZA* da MATA a group saboda tsaro

 

*KUDIN WOMEN24 TV VIP*

Sannan maza su *#500* zasu bada mata kuma *#500* zasu bada

Wannan group in duk littafin da kika gani a ciki toh anan kadai zaki iya samun littafin inkin gani a wani guri toh na sata ne

 

*KUDIN WOMEN24 TV*

*#300* na masu karamin karfi shikuma shikuma *free book* kadai muke turawa wanda koh zaki iya samu a wasu groups in

 

Inkin biya *#500* zan saki a dukka groups in women24 tv VIP da women24 tv

 

 

*GROUP DIN YAKASANCE KAMAR HAKA*

 

1.WOMEN24 TV VIP NOVELS

2.WOMEN24 TV VIP AUDIO NOVELS

3.WOMEN24 TV VIP DOCUMENTS

4.WOMEN24 TV VIP VIDEOS

A wannan group in zamu dunga tura maku Videos na Makeup, Girke Girke, Daurin dan kwali, Indian Hausa da films inda *AREWA24* sukeyi irinsu Dadin Kowa, kwana chasa’in, Rayuwata, Ajeeb Akushi da Rufi da dai sauransu

 

5.WOMEN24 TV VIP MUNSAN JUNA WANNAN GROUP IN NA HIRA NE

Kinajin sunan groups innan kinsan meye za’a dungayi a groups in

DARI BIYAR (#500) zaki bada insaki a dukka groups dinnan guda takwas.

 

Account number.

 

 

2065301650

Zubairu Hayat Iman

Uba bank.

 

 

Number waya.

09030159301

 

 

 

 

 

Inbaki da Bank account zaki iya turo da katin MTN

 

Kada kibari gara basannan ta wuceki.

 

Yan Niger ku nemi wannan number

+227 90 79 59 39

 

 

 

Sadaukarwa ne ga

 

ZAINAB GARBA BUTALAWA

 

 

 

Page na farko na

AUTA ne

 

 

 

 

Bismillah

 

 

 

Mutane cike suke a bakin wani katafaren gida ana Zaman makoki kana ganin irin yawan mutanen kasan babban mutum ne ya mutu,ga yan samari duk suna Kama baza su wuce shekaru Sha shida Sha bakwai ba a kalla sunkai su hudu,wani Handsome matashi zai Kai 28yrs Yana zaune da samari matasa da alama abokansa ne harda dan guntun hawayensa,cikin matasan wani Asif cike da tausayawa yace Hakuri zaka Yi Jawad dukkan Mai rai mamaci ne kowa na haka ne,Jawad ya daga Kai sama Yana dan maze damuwarsa

 

Cikin taron masu gaisuwar wani Dattijo ne yake ta kururuwar kuka babu ji babu gani,wani yace haba Alhaji Nasir hakuri akeyi an San ka rasa dan uwanka kaninka amma Addua ce ta kamaceka,Alhaji Nasir ya nuna yaran nan Yan maza yace ba kukan mutuwar Alhaji Muhammad nake ba kalli bataliyar da ya mutu ya barmin ya sake fashewa da kuka yace babu fadan da ban Masa ba akan ya daina auri saki yaki ji gashi kowanne yaro uwarsa daban kadan ne suke a dakinsu su biyu kowa uwarsa daban ga Yara Mata Suma dukkansu Yara ne basu Isa aure ba a bala’in rayuwar nan da ake ciki yasan ni bana son haihuwa a duniya

 

Kuka ya sake fashewa da shi yace Yara na uku kacal a duniya sabo da gudun rayuwa na kayyade iya yaran da Zan Haifa a duniya sabo da rayuwar yanzu ni ko badan rayuwa ba bana kaunar Yara da yawa yau gashi tawa bata ja min ba ta wani ta ja min,Ina fada masa Muhammadu ka daina tara Yara ka daina auri saki ko wacce tazo sai ta haihu sannan ya saketa ashe ni ake tarawa yaran ban sani ba wayyoooooo Allah Muhammadu anyi dan banzan yaro Muhammadu ya jawo min dole Yara su zauna a wajena na basu tarbiyya idan banyi ba duniyace zata zageni Alhaji Nasir Yana ta sambatu

 

Wani dan uwansu yace kayiwa Allah kayi Shuru a gaban mutane duk an tsaya Kai kadai ake kallo Wai to ba Yana da Babban da ba ance tunda ya auri wata Yar labenon wannan yaron ai Mai kudi ne ance me zuciya ya gaji arzikin mahaifiyarsa,yace gashi can ai baiyi aure ba,Kuma ai yaro ne ko yayi aure Ina raye ai baza a Kai Masa Yara sunfi ashirin gidansa ba,gashi me Kama da bature sannan Ina zai iya wani tarbiyya bai dade da dawowa kasar ba,shi kanshi tarbiyyar yake bukata a bashi,Jawad dake jinsu yayi shuru kawai mutuwa ce a gabansa.

 

Cikin gidan Kuwa dangi ne da abokan arziki ana ta zaman makoki matar Alhaji Nasir tana zaune sanye cikin zundumemen hijab hannunta dauke da carbi mutane yan Uwa da makwafta Mata cike a palon ga Yara marayun da aka mutu aka bari Mata rututu duk Yan Yara Wanda suke 12yrs sune manyan ma ko kuka basa yi suna zaune harda matansa biyu da ya mutu ya bari duk shayarwa sukeyi suna zaune Suma suna kuka sosai,Hajiya A’i tana jijjiga yarinyarta da take shayarwa sai faman kuka takeyi ga zafin mutuwa ga kukan yarinya wacce tana rarrafe ma hakan yasa takaici ya isheta ta fara dimawa Yarinyar duka a baya ana bata hakuri,Wata dattijuwa tace haba ke Kuwa A’i ita yarinya me ta sani haka dai ta lallashi yarinyar, suna zaman makoki har akayi sadakar bakwai.

 

Mutane ne talakawa masu yawan gaske iya kallonka gasu Nan da miskinai da Wanda talauci ya musu muguwar Shaka manya da Yara wasu da yaransu sun cika inda aka tanadar musu sabo da wannan bawan Allah mai taimakon talakawa zaizo ya raba taimako sannan zai saurari matsalolin bayin Allah ya tallafa musu,mutanen Nan rana tana dukansu amma sun cika makil duk securities sun shirya su sunyi layi sahu sahu ana jiran wannan bawan Allah.

 

Wasu jibgan jibgan motoci ne na Alfarma guda Uku inda aka tanada Suka Yi parking, cikin kwalla kwallan motocin Wanda securities ne suka fito motar da tafi kowacce kyau Suka zagaye ga yaransa na jikinsa duk matasa Wanda baza su wuce 29 to 30 yrs ba duk sun dau wanka,kana ganinsu kasan suna cikin hutu da Jin dadi.

Motar data fi kowacce kyau aka bude wani sanyi da kamshi ya feso wajen farar kafarsa ya zuro waje yasha uban takalmi na nunawa sa’a,Fitowa yayi gaba daya kowa ya saki baki Yana kallonsa duk da cewa wasu sun taba ganinsa,ya gaji da haduwa cikin wata almurar shadda Fara kal,dinkin Kamar a jikinsa aka dinka shi ya zuba uban kyau,gashi Kyakyawa na gaban kwatance,tun daga kan tsayinsa dai dai,sannan ba siriri ba baza a kirashi da me kiba ba,gashi fari kal skin dinsa Banda sheki ba abinda take,gashin Kansa Baki wuluk kamar na larabawa ya tarashi an Masa aski na Yan gayu Kamar a film, hancinsa normal ba me tsayi da yawa ba Kuma ba gajere ba haka ba siriri ba sannan ba me Fadi ba,bakinsa karami me dauke da jerarrun hakoransa masu kyau farare tas,gashin girarsa me yawa baki wuluk,idonsa madaidaita farare tas suna wani lumshewa Kamar zaiyi bacci .

 

Kowa dake wajen kallonsa yake ana murnar ganinsa talakawa sai daga Masa hannu sukeyi suna sowa da ihu ana ta faman gaisar da shi,cikin tafiyarsa me Jan hankali ya fara taku Yana bin sahu sahu da kallo Yana daga musu Hannu,layin karshe na Mata ya tsaya layin da na taho da gudu Zan Shige Ina magana da karfi Ina furta a taimaki marainiya,Marainiya ta ajin karshe,duk wani maraya a ajin farko yake ni Ina ajin karshe na Shige cikin layi tare da cukulewa ba mutunci,Ina tsaye Ina fushi na fice a layin na tsaya a gefe sabo da sun dade suna jira yaki zuwa ya sallamesu gashi har nima na zo shi yasa naji haushinsa

 

Kallo daya ya min ya juya tare da yiwa yaronsa magana cewar a maida Ni cikin layin duk Maganar nan da yakeyi babu Wanda yaga murmushinsa wannan shine karon farko dana taba zuwa karbar kudinsa labarinsa Kawai nake ji a layinmu shi yasa nazo nima,yaronsa ne da sauri ya bude mota ya ebo kudi masu uban yawa ya Mika Masa ya karba Ina kallo Yana bi layi layi Yana rabawa dubu biyu biyu dubu uku uku,idan kana da babbar matsala ka fada Masa zaice ka koma gefe ka jira shi, wata cikin mutanen tace dan Allah ka taimaka min kudin gidan hayata ya Kare gani da Yara su biyar marayu babansu ya mutu ya barmu,Nan take yace wacce sana’a Zaki iya Yi? Tace Ina siyar da su maggi,wake da manja tare da sauran kayan kanti,ba tare da ya kalleta ba ya tambaya Nawa ne kudin gidan? Dubu dari, yace alright yanzu za a Baki dubu dari biyu dubu dari kudin jari dari Kuma kudin hayar,a kasa ta zube tana kuka tare da sa Masa albarka yaronsa Kuma abokinsa Asif yace bata kudin Nan take ya sallami matar.

 

Haka ya dinga rabon kudin Yana sauraren matsalolin mutane Yana Sallamarsu har yazo layin karshe wasu Yan Mata suka ce aure za musu babu katifa Nan take ya bada kudin suka tafi su ma har aka karaso inda nake na karaso da sauri tare da durkusawa har kasa Kamar yanda naga sauran sunyi Yana sauri ya fara irgo dubu uku zai bani nace Nifa waec da Neco Zan zana bamu da hali Kuma naga kana Shirin bani wasu dubu uku na karasa da shagwaba kamar Zan narke,ba shiri ya kalleni haka bai saurare ni ba yace nawa ne? dubu talatin da bakwai na furta nan take ya irgo ya bani nace Saura kudin Uniform Yaya nawa duk sun rube,kallo daya ya min wai yaji na ce masa Yaya yace Nawa ne? 7k ya irgo ya bani na karba nace na gode ya juya zai tafi nace na manta takalmi na Wanda nake zuwa school duk sun lalace Asif ya kalla tare da cewa karasa sallamarta mu wuce flight dina ya kusa time is going,Asif ne ya Kara min 10k yace gashi nan,nace rayuwa tayi tsada fa bawan Allah har school bag zan siya,Asif ya bude baki yana kallona yace ke Wai baki to tarbiyya ne daga taimako sai kace kudin ubanki sai matsaloli kike kawowa kina ta karbar kudi dama irinku ne bata gari da kuke hana bayin Allah taimako

 

Na kalle shi nace Kai kudinka ne to ai sai ku rage min hanya ku sauke ni a layin gidanmu dan Allah da nisa Sabo da Takaici Asif juyawa yayi Kawai ya shiga dalleliyar mota Suka Yi gaba,suna tafiya Jawad ya dafe kai yace Asif Ina magani na?wani wuri ya jawo ya bude a motar ya dakko Masa wani magani dake cikin Yar farar roba ya dauki daya tare da korawa da ruwa

Kallonsa Asif yayi ya furta ranka ya dade ko mu Shiga asibiti a duba ka? no need yace a hankali,sai da yaji kansa ya daina ciwo sannan yace mu biya naci abinci but nafi son fura kawai,Asif yace a Ina zamu samu fura to me kyau? Driver yace nasan wani gida amma mun bar layin a baya matar me tsafta ce sannan da Engine take komai na furar Kamar ta kamfani,Jawad Yana Jin haka yace muje please,motar ya juya sauran motocin ma na securities suka bi bayansa a nutse zuwa wata tsohuwar unguwa ta talakawa layin baida kyan gani ko kadan kamar ba a cikin birni ba.

 

Ina zuwa kofar gidanmu na iske motocin Jawad Wanda ya gama raba Mana kudi Ina murna nayi mamakin ganinsu a kofar gidanmu amma bai fito ba,duk suna cikin motocinsu,Wucewa nayi abina Zan Shiga gidanmu naji an kwala min Kira ke Marainiya,da sauri na juyo naga Asif,dawowa nayi Ina gyara wuyan hijab dina red, yace a nan ake siyar da fura? da sauri nace ae Mamata ke yi,a kawo mana,Murmushi na saki nace ai wannan salon a baku kyauta ne kawai taimakon da kuka bani a baku fura ta kudinku,Asif share ni yayi yace jeki da yawa za a kawo kiyi sauri to na furta na Shiga gida da gudu

 

Ina Shiga Ina haki nayi sallama na iske Ummiya a kitchen tana wanke abinda ta hada furar,nace na dawo Ummiya gashi na samo kudi da yawa sun Isa na biya kudin school mutumin me kirki gasu sunzo siyen fura da yawa sunce da yawa hope tayi sanyi? Na fito da kudin na bawa Ummiya baki ta bude tace Ashe taimakon da gaske ne? Ei baki gani ba nayi ta shagwaba ana Kara min kalla ki gani,Ummiya tace ai nasan sai kinyi Iskanci an gode Allah ya biya sa a lahira yanzu a Kai musu furar ai baza mu karba kudinsa ba,Nace sai mun karba so kike su karya Mana jari su tafi,furar na jera manyan ledoji roba roba irin ta Rufaida na fito da manyan ledoji har biyu Ina Fitowa numfashi na ya dauke ganin Jawad da nayi a jikin mota a tsaye Yana kallon layinmu,sai da na saki salati sabo da tsabar kyawunsa,a hankali na karasa gabansa da ledojin a hannuna.

 

Asif ne yazo ya karba yace tsaya musha muji irinta idan bata Yi ba baza mu siya ba,Ni dai ban ce komai ba haka ya dauki roba daya ya bude tun a Ido kasan tayi Spoon ya sawa Jawad yace taste,a hankali yasa hannu ya wani dan ebo a spoon ya Sha yaji shegen Dadi yace tayi let’s go ko kallona baiyi ba tunda nake sintiri a wajen bai ko kalle ni ba,Asif yace ta Nawa ce duka nace ta dubu buyar, kacal? Ya tambaya na kalleshi nace dan Allah ka dinga rage Fadin rai kai ba me kudin ba harda wani kacal,sai lokacin Jawad ya kalleni a ransa yace bata da kunya Asif zata Kira da me Iyayi, Asif zaiyi magana Jawad ya furta don’t, let’s go please,Nace ya sunan Ogan naku? Asif ya kalleni sannan yace Jawad sunansa,Kai na girgiza tare da cewa nice name sunansa Zan sawa Dana na fari idan nayi aure,Asif yace babanki fa? nan take na bata Fuska nace idan yaci sa’a zan maida shi akan Dan Auta na,ai sai dai yazo a Dan Auta Maybe,Farko idan Namiji ne Jawad sabo da ya taimakeni,idan macece Ummiyata Baba Kuwa ai ya samu sa’ar gaske yazo a Dan Auta,Asif ya dinga dariya yace shi kuwa Baba me ya Miki haka baza a sashi a Kan arziki ba har sai Dan Auta,nace ai Dan Autan ma ba guarantee watakil nace,Jawad Yana jinsu Yana karanta Jarida ta bashi dariya sosai,Asif yace ke mun tafi tace ku gaida tsofaffin kace da Oganka godiya dubu dubu kace Yana da kyau ya dinga Sallar dare Yana godewa Allah shi kadai ne baida damuwa a duniya komai an bashi,jarabtarsa Kawai akan fura ne duk inda take sai ya nema,Asif mota ya shiga kenan Nace kudin fa ku Kuna da karfi ba sai an Muku mutunci ba ku biya kudinku,Asif Yana dariya ya zaro kudin ya Mika Min na karba ta window

Suka ja motocinsu sukayi gaba nima na shiga gidanmu Ina murna.

Ummiya sai fada take min me yasa na karbi kudinsu,Haka Muka gama tsara kudin ya zamuyi da su har na school dina an ware,sabo da mijin Ummiya yace dama shi bazai iya daukan nauyin agola Yar wani ba in zata iya wahalar to ko ubana mahaifi yayi dawainiyar yarsa shi yasa ko sana’ar da Ummiya ke Yi sabo da ni takeyi,shi yasa ko yaushe adduarta Allah ya fito min da Miji na gari da wuri ta aurar dani itama ta huta,Nima dake da kuruciya son auren nakeyi ni koma waye na aure shi,akwai Saurayina Salisu da ya nace min to bashi da kudin aure yaro ne Nima ba wani damuwa nayi da shi ba

 

Bayan kwana Uku na fito nace Ummiya zan tafi cewata a kalla bazan wuce 18yrs ba,Matashiyar dattijuwa Ummiyata a kalla bata wuce 37Yrs ba dauke da katuwar Leda ta fito a hannunta ta mika min gashi Najla ki gaishe su kafin na Zo ki samu Mahaifiyata a sirri ki fada mata ba kudi a hannuna shi yasa ban Zo ba,sannan na fada miki in kinje Kwana Uku karki wuce haka sabo da yanayin aikina kin San teaching a private school ba sauki Kuma Kinga akwai aiki a gabanmu kin sani,Najla nace Inshaallah ina gyara Hijab dina me hula har kasa,Ummiya ta sake furta Kinga kin girma Saura kije naji ance anyi fada dake a gidanmu dai gidan yawa ne Kuma kin San part dinmu ne kawai musulmai ki taka a Sannu kin San halinsu,Dariya nayi nace Yau akwai danna ashariya wallah Ummiya gidanku baiyi ba ga shegen yawa sunayensu ba dadi ga Sallamarsu in ba ashar ka dura ba babu me kulaka,bana son shegen surutu a dawo lafiya kar naji anyi fada dake Najla na fada Miki duk inda Kika je Sai kinyi rashin mutunci ki kiyaye.

 

Na furta Fada Ummiya ai kamawa take

Okay wato baza kiji magana ta ba ko? Naji mana duk da na saka Hijab ai kunne na yaji,

Kwafa Ummiya ta ja tare da furta ko Zaki Fara shiga gidan Mahaifinku ku gaisa daga nan ki gano lafiyar kannenki? Fuska na murtuke nan take,Ummiya tana kallona tace tafi ko na dura Miki ashar Allah kuma ya shiryeki jeki dan Allah lokaci na kurewa,sallama nayi Mata na wuce abina.

Tasha na wuce Ina zuwa motar Sumaila Shiga Muka dauki Hanya,ba bata lokaci na sauka a daidai kusa da kauyen YarKaya nabi Yar hanyar da zata sada ni da kauyen,wani machine na hau ya kaini har kofar gidan kakannina,katon gida ne na kasa Amma duk an sumulmule ko Ina da siminti baza kace na kasa bane ginin,yaran gidan na iske a waje suna wasan kasa tsalle suka Shiga Yi ganina tare da rungumeni sannan Suka fada gidan da gudu suna ga Fara tazo

Gidan na shiga nasan babu batun sallama Ina Shiga na duro wata uwar ashariya da karfi,Wanda suke tsakar gida manyan Mata da maza Suka dage Suma tare da narko tasu ashariyar suna murna Suka tarbe ni barka da zuwa Fara, yanda suke gaisuwarsu ba girmamawa ba komai Haka na musu sannan na shiga sashen kakannina Wanda su musulmai ne a gidan da sallama na shiga,na Iske Kakanni na duk suna Nan,Bayan mun gaisa na shiga cikin daki na ajiye kayana sannan na fito zuwa babban tsakar gidan nabi sashi sashi Muka gaisa sannan na koma sashen mu aka kawo min abinci wake da Mai da yaji waken manya manya ya birgeni ya Sha man gyada naci na koshi sannan nayi Sallar la’asar na fito tsakar gidan duk sun dora girkin dare ko wanne waje ga Yan matan gidan sun dawo Nan Muka kafa daba Muna hira,Matasan mazan ma Suka shigo a Naroro yana ganina nazo ya dawo kusa dani ya zauna Yana Kare min kallo Kamar tsohon maye Wai so na yake muyi auren zumunci

 

Kwance yake saman luntsumemiyar kujera kusa da wata tsohuwa me kwari gabansa kwanikan abinci ne na alfarma,kallonsa tayi tace Jawad Nifa bana son shegen baccin Nan naka kamar me cutar bacci da an Fara Hira sai bacci, Murmushi ya sake saki tare da lumshe kyawawan idanuwansa ya furta ke zancenki Kaka baya wuce na aure ku dai ayi aure,Jawad talaka marar sana’a shi ake hanawa aure amma Kai ka girma ga kudi Allah ya baka me ya rage maka cika babban mutum aure darajarka dakin matarka,yanzu da matarka ce sai ka kwanta a cinyarta ta Sanya ka nishadi ta lallaba ka,kefa kaka? Allah kiyashe ni cinyata tunda tayi rashin Shureim shike nan ba wani Kato da zai sake daura Kansa a kanta,Dariya Jawad yayi yace kina missing abinki kenan? Kwarai kuwa wannan uban gemun naka sai kake Kama da shi,ai na dauka ku bakwa son gemu?cewar Kaka, Inji uban wa Yara kuci gaba da ajiye gemu ni kaina a baya idan Ina ganin na Shureim sai naji na sake kaunarsa wata sabuwar kaunarsa nake ji cewar tsohuwar farar, Murmushi Jawad yayi kawai tare da gyara kwanciyarsa yayi matashi da cinyar kakarsa,kafarta ta zame tace baka Isa ba kayi aure ka kwanta a ta matarka,Ni din? Ae Kai din Mana yace Zan Kuma komawa Kano bazan sake siyo Miki fura me Dadi ba,ai nasan dole sai ka siyo min ma amma dai kwanta badan halinka ba,Dariya yayi ya kwanta abinsa sai bacci.

 

Muna tsakar gidan tare da Yan matan gidan Muna hira masu girki suna yi muka ji ashar ta fara tashi da bala’i a sashen Nomau,Gwamma tace Nomau kaji kunya Kai Kam kayi asara,ace Yar cikinka zaka aura wannan yarinyar me ta Isa me ta sani kamarka katon gardi ga tsufa baza ka hakura da mu ba,Nomau cikin bala’i yace dama duk Wanda ya ajiye wata a gidansa ya shiga Uku shi da baccin rana sai dai ya gani anayi gaba daya Kun maida ni banza wofi nan ya fara ashar kala kala,muna ji muna kallo.

 

Asif ne ya shigo palon kaka ya iske tana kallo,sallama yayi ta amsa da fara’a bayan sun gaisa tace Yana ciki dazu nan yaje samansa haurawa yayi saman ogan nasa Kuma dan Uwansa,Yana Shiga ya iske shi daure da towel ya fito a wanka,Fuska Jawad ya bata tare da furta Malam basai ka jirani a palona ba Kawai sai ka shigo min yanzu da tsirara nake fa ya furta a gajiye,Dariya Asif yayi tare da Zama a gefen bed dinsa sannan yace ai sai na Sha kallo kawai wani yace ka tube,ya ake ciki ranka ya Dade zamu je Kano din ne gobe? kamar bazai Yi magana ba ya furta Inshaallah,Man ya kamata fa kayi aure ga kudi ga komai ko ni da nake yaronka Ina da Mata sai Amarci nake Sha wallahi kayi aure kaji dadi ana ta barinka a baya,juyowa Jawad yayi Yana goge gashinsa ya furta baka da aikin yi ka taba Jin Ina ko kula wata? Wallahi da me fura ma ka aura sai Naga Kuna Kama kalli yarinya kyakyawa ta kirki wannan matar manya ce,da Alama ma tana da hankali Ni nayi maka sha’awarta Kun dace,wannan ta samu Hutu sai an kalleta cewar Asif, Jawad Yana fesa body spray yace dama naga alamar sonta kake Yi in kana so ka Kara ta biyu Malam karka dameni ni bata yi min ba, wannan yarinyar Zan aura ai Kuwa da nayi asara me ta sani me zata iya nafi marfinta sai na sata yoyon fitsari nafi karfinta,dariya Asif yake tare da cewa kasan Kuwa Mata? Wannan zaka sa yoyon fitsari? Tsaki Jawad ya ja ya furta please ka kyaleni ko ka barmin room,Shuru Asif yayi yaci gaba da kallon wani Indian series a katuwar plasma din dakin Jawad.

 

Jawad ma Zama yayi suna kallon film din ana zuba love budurwar tana wani fari da iya zance murmushi Jawad ya saki ya kalli Asif yace karya sai film wace zata zauna tana uban wannan love din,Asif yace kayi aure ka gani wallahi abinda yafi haka Mata nayi Jawad yace Indai zata min haka kana ganina ka kirani da Sallau wato sallamamme kenan ko ka dinga kirana da Dan bila,Bila babban bawa to nine Dansa kaga Danbila kawai,Asif ya dinga dariya kamar ba gobe

 

Asif yace idan ka sake ka auri Yar Kauye wacce bata waye ba to ba Kai ba Jin sweety sai dai kaji ana Kiran wasu banda Kai,Jawad Yana Murmushi yace Ina son mace me iya zance wacce zata dinga tsarani ,wannan sai Yar birni gogaggiya cewar Asif,Jawad yace wa yake zancen ta kauye na aurota haihuwa daya ta ragargaje haka zaka ga nononta da wuyanta da cikinta duk sun hade sun Zama Kai daya na kasa gane Ina nono Ina wuya Ina cikinta musamman kibarta tayi yawa bada Ni ba,nafi son wayayya Yar birni,suna ta hirarsu suna nishadi har magrib suka fita Sallah masallaci.

 

Washe gari da wuri suka bi flight zuwa Kano inda zasu raba kudin a kauyuka Yankin Kano ta kudu Inda Suka nufi Secretariat dake garin Takai kafin su je an gama shirya mutane da komai,Babu bata lokaci Suka Isa cikin motocinsa na alfarma da sauri ya fara sauraron matsalolin mutane Yana sallamarsu lokacin Najla suna Kauyen ‘Yar Kaya kusa da Yankin Sumaila sunyi kwalliya ana ta Shan biki wata ce tazo da labarin rabon da akeyi a cikin kawaye,tace bayin Allah ana ta rabo babu mu wani me kudi ne yake fitar da zakkah duk shekara gashi wannan lokacin dama ance a jahar Kano zai yi suna Takai local gamman kuyi sauri muje,Amarya me Suna Tanoma ta zaro Ido tace Al’quran kuzo mu tafi baza a barni a baya ba, Nima idan na karbi kaso na ai hike nan ko jari na kafa,ta durma min duka a baya tare da furta hegiyas tahi muje,haka na mike Muka yafa gyalenmu duk mun Sha anko kana ganina kasan Ni daga birni na fito ba kalarsu bace,haka muka cika wata karamar mota Gulf wasu akan cinyar wasu Muka tafi.

 

Har inda ake rabon aka shigar da mu nan take Jawad da mutanensa Suka zubawa motar Ido Saura kadan ya gama sallamar mutane sabo da dama mutane masu matsala ake tara Masa ba kowa da kowa ba,ai kallonmu suke dukkanmu da anko muna ta dirgowa daka cikin mota,Muka biya kudin mota muka tafi gabansa da sauri Amarya tana gaba Tanoma jiki na rawa tace dan Allah ka tallafa min da jari,Jawad ya Mata wani kallon Iska ya ebeta ya watsar tare da dora idonsa a kaina mamaki ya kamashi shi wacce ya sani a birni take ba shiri yace ke ba kece ta rannan ba har Muka siyi fura a gidanku ba,nunawa nayi ban San zancen ba nace laaa ni kuma? ba ni bace gaskiya Ni sunana Fara a Kauye nake Ina da Yar uwa dai a Kano sunanta Najla

 

Asif ne ya matso yace ke amma ku Yan biyu ne? Da sauri na daga Masa Kai nace ae Najla a hannun Maman mu ta girma ni kuma a wajen kakannina,Asif yace ohh shi yasa naga kinfi ta birni nutsuwa amma gaki a Kauye Kamar ba Yar can ba

Gado nayi kasan mu kyawawa ne jinin mu haka muke ga farin jini Allah ya bamu duk inda muke sai an so mu sai anji kaunarmu sai shegen bala’i gare mu wannan gadon Yana damuna,Asif yayi dariya yace naji ance Fara ke sunanki ne Kuma Fara? Ae da yarenmu ne duk macen da aka haifa wacce ba baka ba Indai Fara ce to sunan Kawai za a sa Mata,kaga wannan Yar uwarmu ce ita Kuma sunanta Tanoma an haife ta ana noma,Asif yace amma maguzawa ne ku ko? Nace ae,ai Jawad kakarin amai ya fara Yana masifa dama sister dinki ba Yar Fulani bace naje na Sha furarsu? Najla tace yo wa ya kaika yanzu ai an daina tantancewa,Asif ya kalleni sosai yace kamarku tayi yawa wannan ankon fa biki kuke Yi? da sauri Tanoma tace musamman muka dinkashi sabo da zuwan Oganku me rabon kudi sabo da nuna farin cikin ganinsa,Nace in kaje kauyenmu kace ankon Jawad zaka ji ance mune Muka fitar da ankon sabo da murnar zuwansa,Kadada kanwar Amarya itama tace ai na zuwanku ne,Asif ya nisa shi dai bai yarda ba amma yayi shuru,yana Gama sallamar kowa sannan ya dawo kanmu bai ko kalle mu ba ya irka 10k ya bawa kowacce,Kadada tafi ta fara kowa a cikinmu Suka hau tafi banda Ni,Tanoma ta rangadawa Jawad guda duk Yan matan sai guda suka cika wajen da sowa da guda Ina ta kallonsu Tanoma ashariya ta duro tana irga kudi kutmar doson uwa……tace dan ubanki Kadada irga kudin kwanon masara ashirin,Kadada ma ta daga nata sama tare da furta burar…..shi Jawad ma Dariya suka bashi ya murmusa sun zagaye shi suna ta faman guda mota ya shiga abinsa Suka wuce Asif har da cewa ki gaishe min da Najla,nace zata ji Inshaallah

 

Cikin Kano Suka wuce direct Tahir guess palace Suka Yi masauki shi da Asif,mu Kuwa mota muka Shiga sai kauyenmu,muna komawa gida Babba wato Wanda yafi kowa tsufa a gidan ya rufe Amarya da fada sai danno ashariya dan kutmar…..Burar….yace gidan Ubanwa kuka je ana Neman ki za a Mika ki dakin mijinki,Tanoma ta bada hakuri sannan ta shirya aka dauki Amarya zuwa gidan mijinta wani bamaguje Dan uwanmu gidanta ba nisa da nasu.

 

Washe gari da Yamma Muka je gidan Amarya Tanoma muka isketa tana kuka

Nace Amarya lafiya Ta noma tana shesheka tace abun ba dadin ji Kawai abar kaza cikin gashinta,ashe Nasafiya Dan iska ne, dodo yayi maganinsa babu ni ba shi ni da shi mun kulla gaba sai nayi wata biyu bana magana da shi

 

 

 

 

BANA BUKATAR GODIYA SHARHI NAFI SO DAN ALLAH FANS

 

 

 

 

 

AsmaBaffa

10/6/22, 22:01 – Buhainat: 🌏JIKAR MAGUZAWA🌏

 

6-10

 

Official

 

By

AsmaBaffa

 

 

 

 

SADAUKARWA NE GA

 

ZAINAB GARBA BUTALAWA

 

 

Wannan Novel a

WOMEN 24 TV kadai za a iya samun ci gabansa

 

SHIN KIN SAN SHAHARARRAN GROUP ƊIN NAN DAYA SHAHARA WAJEN KAWO SHAHARARRIN FINA-FINAN DA SUKA SHAHARA WAJEN SAKA MA’ABOCIN KALLONSA A CIKIN NISHAƊI DA FARIN CIKI?

IDAN HAR BAKI SANI BA LALLAI KUWA ANA YI BABU KE!

KODA YAKE HAR YANZU AKWAI BABBAR DAMAR ZUWANKI DON A CIGABA DA DAMAWA DA KE IDAN HAR KIKA JONE DA MU!

 

Kuna ina ma’abota kallon shirye-shiryen Arewa24 na ƙasashen waje da suka fara ba su ƙarasa ba? Yi Maza ka garzayo wannan maƙala don ƙarasq kallon shirye-shiryen.

 

Kuna ina ma’abota karatun lobayya wato ma’abota karatun littafan hausa? Shin na tambayeku akwai wani novel da kuka karanta har yau baka samu karashensa ba? Ko kuwa akwai novel ɗin da kake nema ruwa a jallo ka rasa? To kaima garzayo wannan maƙala domin dacewa da haziƙan fasahan littattafai.

 

‘Yan gayu sam! Bamu barku ba! Kina son koyon kwalliya ɗaurin dankwali kala-kala? Yi maza ki jone da mu kin ji? In sha Allahu sai dai ki koyawa wasu, domin an tanadar muku kyawawan vedios wanda zasu taimaka ki koyi kwalliya da kanki, ki koyi ɗauri da kanki.

 

Anzo wajen! Wato fannin girki! Ayyuriririiiii!

Duk kyan mace sai ta iya girki ta cika sunanta kyakkyawa! Maza-maza yar’uwa ki jone da mu don kuwa muna kawo manyan-manyan girki masu daɗi da ɗanɗano wanda ba su da wuya balle ma ace sai ankashe musu kuɗi. Ke dai shigo ki ganewa idonki!

 

Ƙarshen-ƙarshe kenan! Wato ba anan fa aka tsaya ba akwai wani babban albishir ga masu son group ɗin, shi ne babban tanadin da akai don kawai a faranta muku! Tanadin kuwa shi ne, akwai haɗaɗɗan novel da ya haɗu iya haɗuwa ya tsaru iya tsaruwa da aka yi shi musamman dan ku, wato wanda ake sakinsa a iya group ɗin kacal, wanda wasu manyan marubuta ne ke rubuta su, duk dai sai kin antayo zaki ganewa idonki. Wannan ma na ɗaya daga cikin littafan.

Kalli katsa kaɗan!

 

 

 

*TSARE TSAREN WOMEN24 TV WHATSAPP DA WOMEN24 TV VIP👇🏾*

 

DAURE KI KARANTA DAKYAU

 

Akwai groups guda biyar(5) da muke tura littafi wanda marubuta keyi kyauta da kuma littafin da Sai a group ɗin zaki iya samu sannan da wasu groups ɗinda muke tura videos na makeup, daurin dan kwali, girke girke, Indian Hausa da shirye shiryen AREWA24

 

Group ɗin akwai na *MATA* daban sai na MAZA daban bama hada *MAZA* da MATA a group saboda tsaro

 

*KUDIN WOMEN24 TV VIP*

Sannan maza su *#500* zasu bada mata kuma *#500* zasu bada

Wannan group in duk littafin da kika gani a ciki toh anan kadai zaki iya samun littafin inkin gani a wani guri toh na sata ne

 

*KUDIN WOMEN24 TV*

*#300* na masu karamin karfi shikuma shikuma *free book* kadai muke turawa wanda koh zaki iya samu a wasu groups in

 

Inkin biya *#500* zan saki a dukka groups in women24 tv VIP da women24 tv

 

 

*GROUP DIN YAKASANCE KAMAR HAKA*

 

1.WOMEN24 TV VIP NOVELS

2.WOMEN24 TV VIP AUDIO NOVELS

3.WOMEN24 TV VIP DOCUMENTS

4.WOMEN24 TV VIP VIDEOS

A wannan group in zamu dunga tura maku Videos na Makeup, Girke Girke, Daurin dan kwali, Indian Hausa da films inda *AREWA24* sukeyi irinsu Dadin Kowa, kwana chasa’in, Rayuwata, Ajeeb Akushi da Rufi da dai sauransu

 

5.WOMEN24 TV VIP MUNSAN JUNA WANNAN GROUP IN NA HIRA NE

Kinajin sunan groups innan kinsan meye za’a dungayi a groups in

DARI BIYAR (#500) zaki bada insaki a dukka groups dinnan guda takwas.

 

Account number.

 

 

2065301650

Zubairu Hayat Iman

Uba bank.

 

 

Number waya.

09030159301

 

 

 

 

 

Inbaki da Bank account zaki iya turo da katin MTN

 

‘Yan Niger ku nemi wannan number

+227 90 79 59 39

 

Kada kibari gara basannan ta wuceki.

 

 

 

Page naki ne

UMMIN SADIQ

 

 

 

Jawad hakimce yake a palon Yayan mahaifinsa Yana jiransa kannensa Marayu Mata da maza sai Fitowa sukeyi suna gaida shi tausayinsu ya kamashi,wata Yar karamar yarinya wacce da kyar take tafiya tana gwaranci ta fito da gudu tare da hayewa jikin Jawad ya dauke Yana Murmushi bai San hawaye yana digo Masa ba,sai Yarinyar ce tace Yaya mene? Babba Yana kuka dama? tana dariya Babba Yana kuka tana tafi,da sauri yasa handkerchief tare da goge hawayensa da sauri ya daga Meenat sama Yana Mata wasa

 

Duk sai kannen nasa sukai ta fitowa Mata da maza kowa yace Yaya Nima dagani sama haka ya dinga faman dagasu,Samarin masu dan hankali hannu ya basu Suka tafa da kowa

 

Sai bayan minti biyu Abba ya fito sanye da jallabiya ya bata rai Yana hararar kannen Jawad,duk suka mike tare da komawa dakinsu,Jawad ya dan duka tare da gaisa shi ya furta Abba gani kace kana nema na,zama Abba ya gyara sannan ya kalli Jawad yace Jawad Kai Kam me ka rasa a duniya da ka kasa yin aure komai Allah ya baka ga kyau ga kudi ba wacce zata ce bata sonka amma ka zauna shashanci ni Kuwa ko matan banza kake bi bamu sani ba?

 

To ka sani baka da Uwa baka da uba ga uban tarin kanne an Haifa maka an Kuma mutu an bar maka,tunda Kaine Babba ya Zama dole kayi aure ka maida yaran Nan karkashin matarka…

 

Ni wlh bani aka barwa ba matata tace baza ta iya rike dan wani ba kaga ba yanda zanyi Alfarma daya Zan maka kayi aure cikin gaggawa ka kwashe yaran nan su koma gidanka sannan matan babanka sun ce su gidansu zasu tafi baza su rike kowa ba aure zasu je suyi har Yan yaran nan da suke Shan Nono tsige su zasu yi su bamu su tafiya zasu yi

 

Jawad hankalinsa ya tashi ransa Kuma ya baci da Maganar Yayan mahaifinsa ya kalle shi yace yanzu Abba Kuma ka yarda matarka tace Haka Kuma ka amince? To ya zanyi da ita muna zaune lafiya so kake na saketa munafuki,ya za ayi a daura Mata jego ita bada haihuwa ba yaranta Uku azo a bata wahala da Yara gasu nan sunfi goma Sha,Amma Abba kasan Kaka ma ta koma Labenon ni kadai a gidan a Sai Yan aiki ya za ayi na auri mace Kuma na bata jegon Yara yarinya matashiya haba Abba,kaga Jawad nima matata baza tayi Jego ba sannan bazan bari kakarka ta wajen uwa ta rike mana Yara ba ko a kasar nan take zaune bazai yuwu ba Kayi aure ka Karo masu aiki su taya matarka raino Allah ne ya Dora ma,Nima Kaka ko tana nan bazan bata jego ba bare ta koma kasarta ma ta gado,Baki Abba ya tabe yace itaku Kuma wannan Ni ba ruwana in zakayi aure kayi na baka Yan satikai ko na Kori yaran nan daga gidana,Mahaifiyar taka kafin ta rasu wani abin arziki ta shuka, Jawad ransa ya Kara baci yace ba matsala Inshaallah Zan kwashe su dama yanzu duniya ta lalace Dan uwanka Uwa daya uba daya in ka mutu bazai iya rike maka da ba,Rayuwace shima Daddy maganinsa kenan da aure aure kayi ta haifar yara gasu nan Kuma Abba kaci Amanar zumunci wlh ya mike sanye cikin danyar shadda Yana baza kamshi ya fice,Abba yace kaji shegen yaro to bazan rike ba bani nace ya tara yara ba,farko ma dana ce Zan rikesu zafin mutuwa ne yanzu Kuwa na fasa.

 

Jawad Yana fita compound Hafeez dan Babba da shi yace Yaya Jawad cak ya tsaya da tafiyar da yake zuwa wajen motocinsa har Hafeez ya karaso yace ka gama tafiya zaka Yi,? Jawad yace ae Hafeez ko da matsala?Hafeez yace kudin abinci zaka Bamu Umma iya yaranta ne kadai suke ci suna koshi wallahi mu sau daya take bamu abinci Kuma shima da rana Kawai kwana muke da yunwa har su Meenal,me yasa baku fada min da wuri ba? ya school fa? Hafeez yace a taxi nake zuba kowa mu tafi motocin gidan nan Umma ta Hana driver ya kaimu sai yaranta kudin hannuna ma ya Kare jiya bamu je school ba,ni kadai naje sabo da final Exam takaici ya Kama Jawad yaji tausayinsu Nan yace Kuma baza ka kirani a waya ba Zan kwasheku very soon ku Kara hakuri kunji yace to Yaya,biyoni mota suka jera har mota ya fito da dubu dari ya bashi yace ka boye ko Mene kuyi da shi idan ya Kare ka min waya a kula dasu Meenat sune Yara ku kula da komai nasu kaji, Inshaallah Hafeez yace ya koma ciki Jawad ya Shiga motarsa driver yabawa Umarni ya wuce da shi Office .

 

Yana Office Asif ya shigo ya zauna a kujera Yana Masa barka da aiki Jawad ya kwashe yanda sukayi da Yayan mahaifinsa ya sanar da Asif da komai ma dake tafiya,Asif yace abinda nace maka kenan Sir kayi aure komai kankantar mace tana da amfani yanda aka maka rashi aka bar maka marayu in ya kamata ace kana da Mata duk ka kwashe yaran su koma gidanka tana kula da su tare da Yan aiki suna taimaka Mata is better basai kana sonta ba a samu me hankali ko biyanta kudi ne sai kayi a aureta ta kula da Yara Kawai ta zauna tare da yaran ko da rayuwar aure bata hadaku ba sai a dinga biyanta,Jawad yace wacce marar gata ce zata yarda a aureta sabo da bautar yaran wani,ai biyanta zaka Yi ta Fadi Nawa zaka bata gaba daya daka Kai sai ita zaku San haka,Jawad yace to wa ka hango? Asif direct yace Fara Jikar Maguzawa naga tafi Najla hankali Yarinyar da muka siyi fura a wajensu da to Yar uwarta wacce ke kauyen Fara alama tana da hankali sannan suna bukatar kudi da gudu zata amince, Jawad yace amma kaje wajen Yarinyar Kai kuyi magana idan ta Amince fine cewar Jawad,Asif ya furta an gama next week zanje Inshaallah.

 

Umma tana kitchen ana hada abinci tare da Yan aiki tuni iya yaranta su Uku Rayyan, Affan da Nabeela Suna Dining suna breakfast da dankalin turawa da kwai ga shayi me kauri da farfesun kaji suna breakfast shima Abba Yana palonsa a can yake karyawa da lafiyayyen abinci,Kannen Jawad Kuwa tana kitchen din ta sa an dafa musu farar taliya ko wanne ta zuba plate Yar kadan kadan ta kalli me aiki tace to asabe ni nayi na Allah muna da yaji ai sai ki soya musu manja kowa ki zuba Masa ki basu suci su tafi school Kar ki manta Kar Wanda ya bude min fridge ya dauki lemo ko ruwa uban kowa cikinsu ya Sha na pampo,Asabe tace an gama Hajiya,Umma ta fice tare da haurawa saman palon Abba a can itama ta karya da farfesun da bread ga tea hadin kauri,Yaranta Kuwa tuni driver ya tafi kaisu school,Su Meenat Kuwa taliya Suka ci yaran da kansu suka shirya kansu,akwai Nawwara,Asmau da suma da girmansu zata Kai 13yrs itace ta shirya Yan yaran ta hada kansu kaf bayan sunci taliyar irin su Meenat su dama ba a saka su a school ba sunyi kankanta su biyar ne Wanda ko maganar kirki basu iya ba a gida ake barinsu Bayan an musu wanka an shirya su cikin kayan gida sai a barsu a gidan,Hafeez kafin ya wuce School sai da ya yiwa kannensa take away abinci lafiyayye Suka tafi da shi school shi Kuma ya dawo gida ya wuce bangarensu ya bawa su Meenat Suka ci sannan ya gyara su ya samu Binta me aiki duk cikin Yan aikin gidan itace kadai me tausayinsu tare da kula da lamarinsu Yaran ma itace take kula da su a boye,Hafeez godiya ya Mata ya Kara rokonta ta kula dasu Meenat kafin su dawo tace ba matsala sannan ya fita.

 

Umma Kuwa suna karya wa da Abba a palonsa tace yaran nan naka basu da godiyar Allah ace wai har Taliya nake sawa a dafa musu sabo da cikinsu ya dauka idan sunje school Kar su ji yunwa amma Wai Hafeez shine zai zageni su a gidansu basu San Mai da yaji ba,nace Hafeez Lagos garin arna ne kasuwanci ne ya kawo iyayenku Kar kuce lallai ku sai rayuwar Yan garin zaku dauka bai dace ba,ai sai Kuwa Asmau ta ja min tsaki Wai ai ba gidan ubana bane nan take Hajiya Barira Umma ta fashe da kuka,Alhaji Umar Dankoli Abba ya rikice Yana bata hakuri yace kiyi hakuri Hajiya Bari su dawo daga school zanyi maganinsu

 

Hajiya Barira tana hawayen karya tace Alhaji ka kyalesu ba komai Zan rike yaran nan idan Jawad yayi aure Naga gidansa ya hadu ka duba gidan da ya kera kamar wani Dan kwallon kafa duniya guda me zai hana mu koma can ni da yarana ya bamu part Daya ya saka matarsa a part daya da kannensa tana kula da su kaga zai Fi yarinya karama zai aura baza ta iya tarbiyyarsu ba,Abba yace gidana Honey me kyau ne Ina samu dai dai gwargwado me zai sa na koma gidan yaro da Zama Ina Yayan mahaifinsa,Amma kasan Jawad ya fika kudi ko wallahi in ya kawo wata Bamu San azabtar da yaran nan da zata Yi ba amma idan Muna kusa shike nan kasan rayuwa sai ta mallake shi yanzu Mata mallakar Miji sukeyi suna jefa shi a bala’i da asiri,Nan take Abba yace hakane Kuma bari zamu koma gidan idan zancen auren ya taso Umma Murmushi ta saki tace Alhmdllh ko kaifa shi yasa nake sonka ka waye da yawa Dariya suka Yi gaba daya

 

Meenat ce tayi kashi a wando ga me dan kula dasu bata kusa Umma ta hanata shiga part din,Fitowa Meenat tayi Kashi na bin cinyoyinta Lokacin Umma ta fito taji wari ta kalli Meenat tana rakubewa a bango jikinta ya hau rawa cikin maganarta da bata iya sosai ba tace dan Allah kiyi hakuyi Umma,Umma wata uwar tsawa ta buga Mata Kashi dan ubanki Kika Yi a wandon yau Zaki ci ubanki dake kabari, cikin Yan aikinta Binta ta kwalawa Kira ta fito da sauri tace wankewa Yarinyar Kashi da kayan jikinta ki gyara ko Ina data bata sannan ki kawo min ita main Palo,Hajiya me gadi ta Kira tace tsinko min bulala lafiyayya maza ka kawo min ya fita da gudu ya samo ta bishiyar dalbejiya katuwa me kauri ga tsayi ta karba tace good tare da kwalawa Asabe Kira Tace kawo min man shanu a kitchen Asabe ta kawo da sauri Umma ta dangwali man shanu ta shafe jikin bulalar da shi tana maiko tace tafi zafi ance,Asabe maida man kitchen

 

Kamar yanda tace haka Binta ta gama ta kawo Mata Meenat tana kuka Binta tana Jin tausayin Yarinyar ya ta iya,Meenat tuni ta fara tsaga ihu Umma ba tausayi ta cire Mata kayan da aka sa Mata Yan kanti ta bar yarinya tsirara tare da riketa Kam ta fara shafda Mata bulala tana ihu sai da ta farfasawa Meenat jiki sannan ta hankadar da ita ta Fadi bakinta ya fashe,Hajiya bulalar ta jefar sannan ta wanke hannunta tare da haurawa sama ta kwanta a makeken bed dinta bacci ya kwashe ta,Meenat tana Palo tana birgima tana ihu gashi Umma tace Kar wani me aiki ya taba ta suna ji Binta harda kuka ta fita daga part din gaba Daya sabo da tausayi.

 

Tana fita Jawad ya shigo gidan a motarsa ta Alfarma Fara tas yau shi ke driving Kansa sanye cikin 3qutr da t-shirt masu tsada sai shining yake Yana kamshi tun daga compound yake Jin kukan Meenat da sauri ya karaso cikin palon ya isketa tsirara jikinta yayi rudu rudu wani wajen ma ya fashe abinka da me haske ganin Jawad zumbur ta Mike tare da fadawa jikinsa tana rusa kuka,Tausayi ta bashi ya tuna matan Babansa duk da ba yaransu bane dukkan yaran sun hada sun rike babu wacce take zaluntarsu duk da kusan kowa Mamansa daban daban amma ba a samu muguwa ba kowacce Daddynsa ya aura tana rike yaran da Amana,daukan Meenat yayi Yana lallashinta

 

Sorry my Angel waye ya dukar min ke Haka? tana shesheka tace um..Umma ce akan nayi Kashi a wando Kuma babu me kaini toilet shi yasa,eyya sorry idan kina Jin Kashi daga yau ki fadawa me aiki kinji tace ai ban gansu ba,yace to kiyi a pow din Ayanah kinji Kai ta daga masa, ransa ya baci sosai da irin dukan da aka yiwa Meenat Yarinyar da bata San me take ba ko ba kanwarsa bace dole me Imani yaji tausayi

 

Yace Ina Ayanah fa? an kunna musu Cartoon let’s go na gansu,dakinsu ya shiga ya iske shi kaca kaca babu me kulasu Binta ce ma take dan gyara su kullum tana kula da su duk sunyi bacci su hudu,kowacce a kasan tiles ga uban ac,Jawad Kansa ya daga sama yace dole nayi aure ko hayar Mata zanyi dole nayi,Meenat ya ajiye tare da sa Mata kayanta tace Yaya yau abinci me Dadi muka ci Yaya Hafeez ya siya Mana,Sauran yaran ne Suka tashi su ma duk Kamar Meenat suke Ayanah ce Bata kaisu ba,na kusa saku a school Kuma ai kunyi wayo murna Suka Fara suna tsalle,bedroom din ya gyara musu da Kansa ya shirya komai neat sannan ya dauki Ayanah ya Mata wanka da ruwan zafi ya ajiyeta a saman bed,ya dauki Nee’ema itama ya wanketa tas ya ajiyeta ya dauki Ameera ya Mata sannan Khairat da Meenat ya musu su biyar duk ya shirya su harda gyara musu gashi suna ta murna sunyi kyau suna ta kamshi,Binta ya Kira yace ta taho Masa da sauran a mota shi Kuma ya dauki Ayanah da Meenat ya sa su a Bayan mota,Umma ce ta fito da sauri ta karaso compound din wajen motarsa tace yanzu Jawad ka shigo baza ka tsaya mu gaisa ba sabo da Allah hakan ya dace?

 

Jawad ya sake daure Fuska ya ja Tsaki ko kulata baiyi ba har Binta tazo ta zuba Masa yaran a bayan mota su biyar yace da Binta Shiga gaba keda Ayanah itace karama ta Shiga Kuwa shima ya kunna mota Yaja Suka fice abinsu,Umma tace Binta Binta Zaki dawo ki sameni ku Kuma nasan bazai wuce shopping zai Kai ku ba wato ni bazai jira ya hada da yarana ba Yan guda uku sai dai iya kannensa sune Yan Uwansa zaka gani ai zaka dawo ka barsu dani wulakancin daka min a kansu Zan fanshe Dan banza marar tarbiyya duk kasar waje ta lalata shi dama dan wata sadaka yalla ne zai gaji arziki,Wai wani Yan Lebonon a gidan uban wa we shall see taja Tsaki tare da komawa part dinta.

 

Jawad Kuwa yawo ya kaisu suka je wuraren shakatawa da yaran tare da Binta Yar aiki 2pm suka Yi lunch a wani Eatery sannan ya musu shopping na kayan ciye ciye na Yara suka dawo gida suna parking a mota ya iske dukkan kannensa sun dawo daga school ga Salamatu matar Babansa da Aziza itama Amaryar Babansa ce Yara ne matasa Salamatu shekararta ashirin da takwas da yaronta data yaye Abeed while Aziza 24yrs take da yarinyarta Humaira itama nono take Sha amma an kusa yayeta

A Palo ya iskesu dukkan kannensa suka dinga fitowa Mata da maza suna gaisar da shi yana amsawa mazan Kuwa Hannu ya basu suna ta tafawa tsarabarsu ya basu sannan suka gaisa da matan Babansa Ya zauna Ayanah tana jikinsa Aziza tace dama wajen Abba da Kai muka zo duk da cewa kullum kana zuwa gida Kuma komai na Abinci da sutura babu abinda ka Gaza mana Alhmdllh mun gode,Jawad ya kallesu yace amma fa Kuna takaba ai da Kiran mu kuka Yi gidan,Salamatu tace a’a dole ce taso mu,Suna Haka sai ga Abba ya shigo palon

 

Karasowa yayi ya zauna bayan an gaisa yace Salamatu lafiya dai ko Kuna takaba zaku fito bai dace ba wallahi yanzu ana Wasa da addini ana Wasa da takaba ko Idda wanne irin abu ne zaisa sai kunzo nan,Yara ne munga sun muku yawa a halin da kuke ciki na rashi duk da nasan dan uwan nawa baza ku shekara biyu a gidansa ba tare da ya sakeku ya auro wasu kamar yanda ya Saba,ana baku ci da sha me kuke nema? Allah yasa ba kudi kuka Zo Nema ba daga mutuwa an tara muku kudin sadaka mene sai Kun dakko kafa Kun taho gidana to ku sani bani da kudin da zan baku kuci ku koshi ku zauna lafiya ga gida nan tangameme sai nan gaba za a raba muku gado..

 

Aziza baki ta tabe tace Allah sarki ai dai ka bari kaji me ya kawo mu ko,Umma ce ta fito tasha wanka cikin lace fari tayi kyau dama gata kyakyawa Zama tayi kusa da mijinta tana Jin zance,Aziza tace dama mun yanke hukunci kowacce gidan Iyayenta zata tafi mu karasa takaba a can,gida mu kadai kamar mayu baza mu iya ba kowa tana da iyaye gabansu zamu koma ya halatta idan da dalili me karfi mace ta fita ta karasa Takaba a gidan Iyayenta ko Yan uwanta sabo da Haka duk mun yaye Yara har Humaira na tsigeta a Shan nono zamu ajiye muku idan mun gama takaba Aure zamu Yi.

 

Nan take Hajiya Barira tace wallahi bazanyi jego ba bazan karba ba yawwa ba dai a part Dina ba wancan ma yaran masu girma sun isheni Allah ya gani,Abba yace to Kai Jawad kaji baza ta iya ba ya za kayi kaifa aka mutu aka barwa ka shiga Uku da kazo a Da na farko babba,Jawad cike da bacin rai yace ba damuwa ku ajiye yaran kuje,Umma Zan kawo Nanny Guda biyu masu kula da yaran kafin nayi auren, duk da haka Umma Fuska ta bata tace kayi sauri gaskiya bana son Jin kukan yaro wannan ma sun isheni mutunci Kawai nake muku,Salamatu ce ta ajiye Abeed itama Aziza ta ajiye Humaira yaran suka hau ihun kuka sabo da kiwa amma haka su Aziza suka fice tare da barin gidan abinsu duk da cewa a ransu son yaransu da tausayinsu sun cika musu zuciya amma hakan bai hanasu tafiya ba,Abba yace Kai wannan Yara da kukan tsiya suke yaja Tsaki ya tashi tare da haurawa sama abinsa,Umma ma mikewa tayi tare da kallon Humaira data Fadi sabo da kuka tana Mika Hannu inda taga mamanta ta bi,Tsaki Umma taja tace yarinya ki dinga kuka haka sai kace ana yankaki shegen Kai kamar na kwado,Jawad ka sani ko ka dauki Nanny dole fa sai kayi aure sabo da Nanny akwai mugun hali ni dai bazan iya ba amma Kai dai ka sani tana fadar haka ta wuce sashen mijinta aka bar Jawad da Yara suna uban kuka a palo.

 

Binta me aiki ya kwalawa Kira tare da daukan Abeed ya lallashe shi tare da mikawa Binta shi ya dauki Humaira,yace Zan biyaki kudi masu yawa duk runtsi ki kular min da kannena,Binta tace zanyi kokari duk da cewa Watarana Umma tana hanani Shiga dakin yaran,kiyi kokari dai please tace Inshaallah,dubu talatin ya bata ta karba tana godiya fita yayi direct Office ya wuce…

Hadadden Building dinsa yaje Wanda ke Lekki Lagos yana zuwa ya sallami kaf ma’aikatansa sannan ya Shiga lift zuwa Hawa na hudu inda Office dinsa yake.

 

Ba karamin haduwa Building din yayi ba komai glass da glass office dinsa Kuma komi na ciki fari ne kal ko Ina kamshi da sanyi ke tashi,Office dinsa katon gaske harda Palo da bedroom tare da toilet,wasu takardu ya kwashe Kawai sannan ya fito ya bar Office zuwa gidansa dake Banana Island Lagos unguwace ta sai Wanda ya Isa ya gagara,Yana driving Yana Magana shi kadai,Ido ya lumshe tare da furta Wai aure zanyi? Jawad da aure duk adana jikina da nake Tsaki ya ja kawai sannan yace ko na dakko Nanny ba Kamar matar gida ba,matar gida itace me sa Ido me Nanny zata musu haka ya dinga zance shi Daya har ya Isa katafaren sabon gidansa Da ya gama tsara shi Yana zuwa duba gidan yayi kafin ya zuba furniture ya fito

Ya Shiga mota me gadi ya bude Masa gate ya fita ya koma Ikeja GRA inda yake zaune a hadadden gidansa yan aikin gidan dukkansu maza ne me girkinsa ce kawai mace yare ce me suna Dina Yana Shiga ya iske ta shirya Masa abinci dining ya wuce Bayan yaci lafiyayyen Abinci samansa ya haura tare da sheka wanka ya dauro Alwala ya shirya cikin jallabiyya sky ya wuce masallaci sabo da magriba ta gabato.

 

Najla tuni na bar kauyen Kakanni na na koma cikin Kano gidanmu har munyi nisa ma da Fara Zana ssce exam.

Yau Friday bamu da Exam Ina zaune Ummiya ta fita unguwa Daddy Yana wurin aiki sai ga Kawata Farisa da Hamziyya sunyi sallama sun shugo,Ina murnar ganinsu nace daga Ina haka mu shiga Palo,Farisa tace ke dakata kiji Jawad me sadakar kudi a company dinsa dake kano gobe za ayiwa mutane interview zai dauki ma’aikata masu degree da NCE,kinsan abin farin cikin? Nace Yi sauri dan Allah ki fada min dama Ina Neman kudi Ido rufe,Farisa tace abincin Yan gayu ake bayarwa a ciki duk abinda mutum yake so kyauta zai karba Indai interview yaje,Naman kaza kala kala,kwai,zabi,friedrice,sakwara,snacks ke abinci dai ance a reception din cikin building din ba abinda babu Kuma Indai kaje interview kyauta zaka ci ko Mene,Hamziyya tace baza taje ba tsoro take ji ko secondary Exam Bamu gama ba da me zamuje interview.

 

Dariya na saki Ina murna nace kin tabbatar kyauta ne? Yayana yaje fa last year shi ya bani labari,yaushe za a fara? Monday 9am,nace ki zabo kayan Sallah mu shirya muje kin tabbatar abincin Yan gayu ne kuma har da nama? tace ae,Hamziyya tana kallonmu tace Allah ya shiryeku nace Ameen,Kinga Farisa Ni zanje Interview da takardu ,ke ki dauki Certificate dinki ko ma na Mene mu samu file me kyau mu zuba muje,sannan mu dau wanka sabo da raini nan muka gama shirye shiryenmu Hamzy sai dariya take Mana.

 

Ko da Ummiya ta dawo ban fada Mata ba Allah yasa satin kaf bamu da Exam,ranar Monday da wuri na gama aikin gida naci wanka na shirya cikin wata Atamfata sabuwa dinkin riga da skert maroon and black color nasa takalmi da jaka black da mayafi na ebo takardu biyu na zuba a file dina,Ummiya bata da teaching ranar, Kallo na tayi tace Ina zuwa haka? nace makaranta zamuje za a Mana wani lesson mantawa nayi ban fada Miki jiya su Farisa suka zo Suka fada min,Ummiya ta yarda da ni tace a dawo lfy nace Ameen ta bani dari biyar kudin Napep dana abinci na karba na fita,ban tsaya ko Ina ba sai gidan su Farisa.

 

Ina zuwa na ganta ta fito ma ta Sha lace dinta itama tayi kyau ta dakko takardu a file nace wanne takardu kika dakko ke? tayi dariya tace Jssce certificate na dakko da Indigene form sai birth certificate,Nace Ni Kuma commern Entrance ne sai birth certificate da state Indegene,Dariya Muka sheke nace shi yasa yau banci komai ba zamu ci kaji,tafawa mukayi sannan muka tafi tare da Shiga Napep.

 

Muna zuwa muka iske

Mutane dukkansu maza ne ba Mata sai mu sun cika bakin gate securities basu bari sun Shiga ba,ya hadu wajen sosai muna tsaye muma ka rantse takardun arziki Muka ebo mazan har wani magana ake Mana Kuma interview kuka Zo?nace ae wlh gashi ma Naga ba a bude ba Allah yasa Kar a barmu jira,suka ce haba ai oga Yana zuwa za a bude Mana Allah yasa muka ce,Bamu dade ba sai ga wata mota me rai da motsi ta yanko ciki ana cewa ga Oga nan haka aka wangale Masa gate driver dake driving ya shiga da mota,Bayan 15mnt aka Bude Mana gate tare da cewa masu interview su shiga,muka Shige ciki wani hanya aka bi damu Muka haura sama mutane ko Hamsim bamu Kai ba,sama aka hau damu muna ta kallo Farisa tace ko yanzu kasuwa ta tashi Dankoli yaci riba munsha kallo,wani wajen cin abinci aka kaimu akace kowa ya karya,Farin ciki ya kamani,Muka zazzauna katon wajene hadadden restaurant kujeru da Table hadaddu ma’aikatan suka Zo suna tambayar kowa abinda za a kawo masa,suna zuwa kanmu nace Kai bawan Allah ka tattabar akwai lunch? Yana Murmushi yace sosai ma Kuwa nace kawo Mana komai na wajen

 

Baki bude yace komai? nace ae komai da ake ci kowacce ka zuba Mata a gefe,to yace ya tafi ba a dauki lokaci ba sai gashi ya dawo da katon plate kowacce shake da abinci iri iri,Chips a gefe,yam and Egg with souce a gefe,ga wani pepper chicken, wani snack kala biyu a gefe ya ajiye Mana ya koma ya shako wasu plate din da abin ci iri iri ya ajiye Mana,ya koma ya kawo wani plate din na farfarun Naman rago daban, yace an gama Hajiya ya juya zai tafi Farisa tace tea din fa? yace sorry ya koma ya kawo Mana,nace Juice da karfi,ya kawo Juice da ruwa,sai kallonmu akeyi ana gulmar mu muna ta washe baki nace Farisa mu Fara? tace tsaya a irga uku tace 1,2,3 start muka Fara duri da Bismillah nace muyi Adduar abinci,Allah kasa abinci ya zauna lafiya a cikinmu,ya Mana amfani sai muka shiga ci ba ji ba gani,Ina cin kaza nace Kar mu bar komai sai munyi kara’i muci yanda ko tunawa muka Yi said mun dinga Jin dadi

 

Farisa tace ai gyatsa ma idan nayi sai naji kamshin Naman Nan,banza ta fadi naji ance sai yayi sati Yana interview kullum sai munzo don irin wannan abinci, Muna ta ci na kalli daya daga cikin ma’aikatan nace Karo Mana ac,ya Kuwa Karo karfinta,muci wannan muci wancan sai da Muka cinye komai tas Muka shanye komai ruwa ne kawai bamu sha ba, toothpick na dauka Ina sakace hakorana na kuskure bakina da ruwa sannan muka zauna Muna hutawa,cikin mazan suna ta Mana Dariya mun lashe komai wasu suna ta mamaki,sai da Muka huta sosai sannan nace a kawo Fruits salat na kwala da karfi masu bada abinci Suka sake kawo Mana,Farisa tace mene ya rage bamu ci ba? nace Coffee,Nan Tace a kawo Coffee Suka kawo Muna korawa a hankali yayinda tuni an tafi wajen interview, fitsari tuni ya fara kamani Amma na daure abina Muka tafi inda ake Kiran mutane suna shiga sharp sharp ya gama da mutane Suka tafi yin lunch sai mu kadai akace mu shiga,Farisa tace wlh bazan iya Shiga ba ai abin kunya ne dama Ni girki ne ya kawoni nace tab ai Ni sai na shiga ko banza na bata Masa lokaci na tsani naga me kudi Yana hutawa, Farisa dariya tayi na mike na Shige da takardun primary dina

 

Sallama nayi tuni tsaruwar office din kamshi da sanyi sun ratsani har wani bacci na Fara ji,Yana hakimce yasha wata shadda sky ya zuba kyau sai sheki yake ban San Sanda nace Jawad Fariyar Shadda, ya ganeni tsab ya nuna bai Sanni ba har gaban table dinsa na karasa Yana zaune a kujera tana jujjuyawa, tsugunawa nayi nace Ina kwana mun ga abinci kala kala mun gode Allah ya biya ka ci da marainiya Allah ne yasan irin ladan daka samu yau,wlh baka ji farfesun Nan ba dadi har yanzu shinshina hannuna nakeyi Ina Jin kamshinsa,Dan Allah wannan kajin amma daga kasar waje kasa aka kawo,ko kulani baiyi ba Yana ta rubuce rubucensa,nace an gode shayinma ice ko da Madarar Dano aka Yi sa ai kasan dano ta kasar Denmark ko? Hannu ya Miko min yace sit ga sit nan Miko min documents naki

 

Mika Masa nayi nace Allah yasa ka bani babban matsayi a nan,bai min magana ba ya duba file dina tunaninsa ma NCE nayi lokaci guda Naga ya dago ya kalleni a fusace tsoro ya kamani fitsari na ya fara damuna dama matsewa nayi nan take nace zanyi fitsari dan Allah,bai kulani ba nace dan girman Allah,takarduna ya watso min yace get out,rokon sa na Fara na mike tsaye Ina matse kafafuna nace Dan Allah zanyi fitsari a wando dan Allah,takalmana na cire sabo da yanzu Saura kadan na Fara Yi a wando tsalle na fara Ina Kai kawo a office din nace wayyo Kawai na hango wata kofa a Office din da sauri naje na Murda handle na shiga sai Naga bedroom komai yaji,na duba naga wata kofar na bude Ina shiga Naga lafiyayyar toilet sai kamshi ke tashi komai clean kofa na kulle da sauri nayi fitsari na a nutse nayi tsarki da ruwa me dumi sannan na shirya kaina nayi flushing tare da wanke hannuna na fito,Karo naci da shi a room din tsoro naji yace koma ki wanke min toilet,nace ban bata ma ba bani da Infection, wani kallo ya min ba shiri na koma ciki komai a kwai haka na wanke Masa sannan na fito nace angode na fice da gudu na kwashi takarduna na fice Ina haki na manta da Farisa sai data rike ni sannan na tsaya cak nace wayyo muje dan Allah,tace Naga kin dade nace muje wajen lunch first Zan Baki labari, Sallah Muka je mukayi ta azahar lokacin har 2pm tayi,

 

Sai da Muka koma wajen lunch mutane har sun gama sun tafi Muka je aka kawo Mana friedrice taji Hadi ga Rabin kaza kowa,juice da ruwa aka kawo Mana wani irin girki na Yan gayu haba nan ma muka Fara duri sai da Muka cinye Muna hutawa Nan na bawa Farisa labarin komai tana ta min Dariya,daga nan nace da masu abinci su zuba Mana take away,Ina fada sai ga Jawad ya fito cikin takunsa na kasaita Farisa ta rude da haduwarsa aka zuba Mana take away sai Naga Jawad an zuba Masa wani Kalar lemo na Apple Nan take aka Masa nace laaaaaaaaaa da karfi sai da kowa ya juyo sun zaci wani Abu ne har Jawad sai da ya juyo nace dama akwai irin juice din Oga Nima a hada min irinsa,Nan take wani ya dinga masifa yace tunda kuka Zo komai sai kunci to irin wannan na Oga ne ba a bawa kowa,nace to jaraba munji karka damemu,Farisa tace muje gida,nace Kinga oga Yana Sha ki tsaya ko zai rage na Sha irin nasa,wani waje na daban ya zauna Yana Sha Yana latsa waya.

 

Wayo nayi nace bari na dan taka ko Zan samu cikina ya samu space na fara dan zagawa a wajen da wayo har naje kusa da Jawad,idan Naga zai ganeni sai na juya naci gaba da tafiya haka na dinga yawo a wajen a dole dan motsa jiki nakeyi,Tsaki Yaja ya tashi ya bar abin da yake Sha ya fita Yana waya na zaci ya gama Sha ya tafi na dauke na kwankwade na ajiye Masa cup din,Ina juyowa Zan tafi nagan shi a bayana ya dawo, tsoro da kunya yasa na arce da gudu nace Farisa muje Muka kwashi take away dinmu nace dan Allah kayi hakuri Kai masu aiki ku hada Masa sabo me yawa yafi na baya Dadi,na kalleshi nace sorry sir zasu maka wani Wanda yafi na da Dadi da kauri Yi hakuri kaji bazan sake Sha maka abinka ba.

 

Jawad shi Dariya ma na bashi na maida shi yaro Tsaki yaja Kawai ya Kira driver yace su wuce Airport,mu Kuwa Muna fita Napep muka shiga Muna ta tafawa nace wallahi dole mu dinga zuwa duk ranar Interview har Muka rabu Muna Jin dadin girkin mu,Ina komawa gida na bawa Ummiya take away nace a wajen me makarantar mu yazo ya raba mana tace to mashaallah ke baza kici ba? Nace naci acan Kawai kici

 

yau Saturday bani da Exam Ummiya ta fita teaching da takeyi a private school nice a gidan nake ta aikina komai sai dana gama na hada furar siyarwa sannan na hau keken dinki ina taya Ummiya dinkin mata,Sallamar Daddy naji ya shigo mikewa nayi tare da amsawa nace Daddy Sannu da zuwa ashe yau zaka dawo,yace yawwa Najla ya aiki ya makaranta? Nace lfy Alhmdllh Maman naki tana makarantar ne? nace ae na mike na karbi ledar hannunsa da jaka ta kai masa daki ta kawo Masa ruwa da lemo,me Kika dafa ne? Nace shinkafa da Miya da salat bari na kawo maka,da sauri na shiga kitchen na hado Masa na kawo Masa Palo yace Allah ya Miki Albarka na amsa da Ameen sannan na koma naci gaba da aikina,Kira ya kwala min na tashi na koma yace na manta kinyi bako Yana kofar gida,mamaki ne ya kamani Wai bako ni inyi bako sabo da kwar jinin Daddy mayafin doguwar rigata maroon na yafa sannan na fita

 

Ina fita naga mota baka mamaki ya kamani sabo da nidai duk kyau na ban taba samun saurayi me Mota ba tunda mu talakawa ne a unguwar Talakawa na taso haka na karasa jikin motar Ina zuwa naga ya bude kofar motar ya fito Asif na gani Nan take nayi Murmushi tare da furta Barka da rana ya aiki? Alhmdllh ya gida ya su Mama? Lfy suke yace good,Nace Ina Ogan naku? Yana garinsu Lagos,Ido na zaro na tambaya dama dan Lagos ne? ae mana nace Masha Allah,Furar kazo siya ne? Ya kalleni ya saki Murmushi yace wlh sabo da Yar uwarki ta Kauye nazo tun daga Lagos har nan,sai lokacin na tuna karyar da nayi musu a Kauye nace ba nice Najla ba Yar uwarta ce a Kauye sunana Fara,Allah yasa lafiya? Yace hmmm abinda nazo da shi deal zamuyi a biyata kudi,baki na washe nace kudi za a bani ka tabbatar? Yace bafa ke ba kanwarki Fara ta kauye me hankali,nace oh to,fada min ko Mene ai yanzu Maganar kudi ita ake ji duk na rude na gigice nace ai yanzu harka Indai da kudi Kuma ba kisan Kai bace ai ita Fara Shar da ita, Asif ya saki dariya yace be calming down please You have to calm down,nace wace calm down ai nutsuwa ta Kare Ina jinka wanne deal ne?

 

Ogana Jawad….dakatar da shi nayi da Hannu nace Wai…. Wai ma da Jawad zasu yi deal din? Yace kwarai,me kudin fa? Ae Mana yace,nace angama dama naga Yana da hankali mutumin kirki ne ga hakuri ba ruwansa da duniya duk kudinsa,Asif ya sheke da dariya yace farko fa cewa Kika Yi baida mutunci he is not romantic,nace son zuciya nayi lokacin dama ba gaskiya nake ba Ina jinka fada min Zan sa ta Amince ta aureshi ko zata mutu sai ta aureshi, Asif yace amma Kamar Yan biyu ne ku Sam ba a gane ku,nace baka kula bane ta Kauye Fara tana da digon tawadar Allah a goshinta guda biyu a jere, yace okay ya fara bani labarin Jawad

 

 

About the author

Hausa_Novels

2 Comments

Leave a Comment