Littafan Hausa Novels

Jemage Hausa Novel Complete

Babbar Yarinya By Oum Aphnan
Written by Hausa_Novels

Jemage Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

https://chat.whatsapp.com/FR8O5JHbv39ABdnE6uV8yN

 

🦇🦇🦇 *JEMAGE.* 🦇🦇🦇

 

 

 

Jemage Hausa Novel Complete

_MALLAKIN._

*ZAHRA ABDUL M AHLAN.*

 

*PAID.*

BOOK.

3/2/2023🪄

 

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’

 

 

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*

 

 

 

*____________________________________*

 

_da sunan Allah mai rahma mai jin kai, tsira da aminci su kara tabbata ga shugaba ja gaba Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa sallam da iyalan gidansa da Sahabbansa da shehunnai da ma magoya baya bakidaya har izuwa ranar sakamako, Ya Allah ka bamu ikon gama wa lafiya yadda muka fara lafiya alfarman Ahalil baitin Nabiy Rasulillahi S,A,W

 

Buri Uku Hausa Novel Complete

_~AMINTATTU GUDA UKU DAGA AMINAN JUNA UKU~_

*AISHA A YABO FULANI*

*RASHIDAT USMAN OUM NASMAH*

*ZAHRA’U ABDUL M AHLAN*

_PAID BOOKS CIKIN FARASHI MAI SAUKI_

_GUDA ƊAYA #200 GUDA BIYU #300 GUDA UKUN #500, AMMA PAYMENT TA KATI YA SHA BAMBAN DA TA ACCT, GUDA DAYA #300 BIYU #500 UKUN #600, BIYA KUDIN KARATUN KU TA WANNAN ASUSUN BANKI 0006064512 Rashida Usman JAIZ BANK ko kuma katin waya ta daya daga cikin waɗannan lambobin_

08147537180

08162576936

08165550116

*Masu turo da evidence of payment wadanda suka yi transfer to acct ku turawa ɗaya daga cikin mu, don girman Allah banda vtu inde kika yiwa ɗayan mu vtu to kinyi sadaka Anty☺️ muna godiya gareku masoya*🪄

 

 

_SADAUKARWAR LITTAFIN *JEMAGE* GA KAWALLIYA *RASHIDAT USMAN UWAR NASMAH* INA MIKI LUV DOMIN ALLAH, BABBAN KAUNA ZUWA GAREKI AMINIYA *AISHA FULANI* RABBI YA BARMU TARE_

 

_LITTAFIN *JEMAGE* KYAUTA CE GA SISINA KUMA TAWAN *KHADIJA SANI JOURNALIST* INA MIKI SAHIHIN KAUNA TAWAN INA ROƘON ALLAH YA SHIGA LAMARIN KI,ALLAH YA IYA MIKI ALLAH YA DAFA MIKI ALLAH YA BIYA MIKI BUKATUNKI NA ALKAIRI FIDDUNYA WAL AKHIRAH, ANA UHIBBUKI YA UKHTY

 

 

*SHINFIƊA*

_LITTAFIN *JEMAGE* KIRKIRARRIYAR LABARI NE, DA FATAN ZA A DUBA DARASIN DAKE CIKI_

 

*GARGAƊI*👂🏼

__BAN YARDA A JUYA MINI LABARI TA KO WANI SIGA BA, BAN YARDA A ƊORA MINI LITTAFI A YOUTUBE CHANNEL BA TARE DA IZININA BA, SO PLS A KIYAYE._

===========

Follow me on my wattpad @Fateemah0.

==============

*MARUBUCIYAR.*

1-HALITTA DAGA ALLAH NE.

2-GUDU A JEJI.

3-SHUHADA.

4-NIDA ƘANNEN MIJINA.

5-WA’YA KASHE ZAHRA’U? #200.

6-COLONEL UBAIDULLAH.

7-ITA CE ZUCIYATA #200.

8-SAMIMA (MACIJIYA CE).

9-DA NA SANI NA.

10-GAWURTACCEN SOJA #300.

11-BADAWIYYAH.

12-AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE) #300.

13- AHLAN #200.

14-DSP ALIYU HAIDAR.

15-SARKIN RUWA #200.

16-MAMIYOTA CE #200

 

 

 

 

∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆

 

 

FREE PG-1️⃣▶️2️⃣

 

 

 

Wanka take yi amma sam ba hankali a tare da ita kana ganinta zaka san a zabure take, da shi ke irin bayin nan ne na talakawa wanda ake zagayewa da falange amma shi wannan ginewa aka yi amma saman washar yake ba komai, tana cikin wankan ne taji saukowarsa ya ɗirka a ƙaramin bishiyar dake bayin nasu,bishiyar tana da ɗan tsayi dan har ta zarce katangan bayin, nan take ta ga duhu sakamakon diran fuffukensa, ai bata yi sanya ba tasa hannu ta fizgo zaninta ta ɗora jikinta duk kunfa ta taƙarƙare ta kurma ihun tashin hankali zata fice taji fuffukensa ya riƙeta sake takarkarewa tayi tana sakin wani ihun a karo na biyu tana faɗin.

“Inna! Inna! Inna! Don Allah kizo ki ganshi wallahi ga shi nan ba karya nake yi ba Inna!!!” Inna wacce tun ihun da *RASHIDA* ta yi ta ji ta take ta alla-alla ta sallame sallan la’asar ɗin da take yi ai kuwa tana sallamewa tayi wuff ta fito tana salati tana ambatar sunan Rashida ɗin, jin muryar Inna ya saka shi tsalle ɗaya ya tashi kan Inna ta shigo bayin babu shi babu dalilinsa 6acewa ya yi ne yaya ne oho sai Rashida da jikinta ke kakkarwa haƙwaranta na haɗuwa da juna tsananin tsoro nan take taji numfashinta ya sarƙe yayi sama idanunta suka hau kesfewa, salati Inna ta saka tana faɗin

“Rashida! Rashida! Ke Rashida! Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Malam! Musa! Abdul!” duk Inna ta ruɗe kiran sunayensu kawai take yi tana jijjiga Rashida wacce idanunta sun kammala rufewa jikinta ya tsandare, Musa da shigowarsa kenan rataye da fatanya a kafaɗarsa yaji sautin kukan Inna a kewaye saurin ajiye buhun hannunsa ya yi ya zo jikin bayin yana faɗin

“Inna lafiya kuwa kike kuka a bayi!” jin muryan Musa ya sa Inna faɗin

“Yawwa Musa shigo don Allah Rashida bata numfashi” jin an ambaci sunan Rashida yasa da sauri Musa ya shigo ya ga Inna durƙushe ga Rashida a sume wacce duk kunfa a jikinta.

“Don Allah Musa taimaka mu dauketa mu kai ta gidan Malam mai Allo” da sauri Musa ya cincibi Rashida ya fito da ita, sai da Inna ta canza kaya sabida durƙusawa a ca6in bayan gida da tayi ta saka wa Rashida riga da dogon hijabinta na islamiyya Musa ya sanyata a akori-ƙura suka turata duk inda suka zo wucewa sai an bisu da kallo da haka suka ƙarasa gidan Malam mai allo suka yi sallama a zaure aka amsa sai zuwa can aka basu izinin shigowa, Musa ya sake cincibar Rashida wacce har wa yanzu bata farfado ba suka shiga suka zube gaban Malam mai allo wanda yake ta faman rubutu a allo ya kalli Inna ya kalli Rashida ya kuma kalli Musa ya ce.

“Dawowa ku ka kuma yi!?” Inna cikin kuka tana sake sa guiwarta a ƙasa tace

“Don Allah Malam mai allo ka taimakeni kar na rasa ‘yata Rashida ita ɗaya ce mini Allah ya bani a duniya, tana wanka ne na ji ihunta tana faɗin ga shi nan ni kuma a lokacin ina sallah sai da na sallame na shiga kewayen amma banga kowa ba daga nan na ga idanunta nayin sama don Allah ka taimakeni” Inna ta fashe da kuka matsinaci, cikin alhini da lamarin Rashida ya ajiye allonsa a gefe ya dauko wani ruwan rubutu a kwarya ya yi addua ya yayyafawa Rashida wacce da kyar taja numfashi alamun zata farfaɗo wacce a farfaɗowar ne ta sake ganin gilmawar fuffuke ta sake saka ihu ta miƙe a birkice da sauri Musa ya riƙe hannunta yana faɗin.

“Rashida ki natsu! Ki natsu!” cewar Musa yana jijjigata

“Wallahi Allah da gaske nake yi na gansa yau ma na gansa babba ne Yaya Musa fuffukensa ma haka ku yarda dani mana haba taya zan muku karya Inna ke ma shaida ce bana miki karya a islamiyyar mu ance karya babu kyau, kullum sai Malam Sabitu ya yi mana wa’azi akan karya, wallahi shi din babba ne na gan shi ban taba ganin halitta mai muni kamar shi ba halan ma so yake ya kasheni don Allah ku yarda dani ku ceceni” nan ta hau sambatu gwanin ban tausayi inda ganin ba na kare bane yasa Malam mai allo bata ruwan rubutu wanda ba jimawa bacci ya kwasheta ta koma sauke ajiyar zuciya, bayan tayi baccin ne Malam mai allo ya dubi Inna ya ce.

“A gaskiya kamar yadda na gaya miki na zata aljanu ne suka shafi Rashida amma tun ranar da na yi mata hayaki na ga babu aljanu a tare da ita, amma yanayin zaburan da take yi da faɗe-faɗen da take yi lamarin akwai ɗaurewar kai da ruɗani” majina da hawaye Inna ta shar6e da gefen hijabi ta dubi Malam mai allo tace

“Malam ko dai Rashida ta zauce ne? da fari ko ni nayi zatan aljanu ne suka shafeta sabida yawan zuwa ƙauyen bishiyar kuka da suke yi duk dare wai sun tafi dandali, dan suna son zuwa dandali duk dare ga hanyar sai a hankali tunda anyi ittifakin aljanu ne maƙel a hanyar kauyen bishiyar kuka da ma ita karan kanta dandalin dan akwai katon bishiyar kuka, amma a yanzu na fahimci duk ba wannan bane a tare da Rashida,to malam ko dai ta taka musu ɗan aljani ne suka haukatar da ita?” girgiza kai Malam mai allo ya yi ya ce.

“Da ace aljanu ne kamar yadda na gaya miki kin ga wannan hayakin? Ko da ba a jikinta suke ba wani mugun abin suka yi mata ina mata wannan hayakin zasu bayyana,amma a gabanku ba wani abu da ya bayyana sai ma cewa da take yi ita da hankalinta tana cikin hayyacinta da gaske take yi ta gan shi”

“To Malam miye abun yi?”

“Ni ina ga a shawarce kafin abun ya fi haka tunda a yau har suma ta fara yi kawai a fara yi mata rubutun maganin wankin kwakwalwa” a zabure Inna da Musa suka kalli Malam

“Wankin kwakwalwa kuma? Hauka fa ke nan? Rashida ta haukace tana zabura tana gane-gane?” Inna ta faɗa cikin sabon kuka.

“Hakan zai fi gaskiya tun kan wata rana abin ya buga mata kai ko ta mutu ko ta fi haka zautuwa”

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! wannan wace iriyar jarabawa ce ke tunkaro mu haka gadan-gadan Ya Allah!” cewar Inna tana kuka wiwiwi,shi ma Musa jikinsa ya yi sanyi.

“Shikenan Malam mai allo a fara yi mata ɗin kafin nan zan sanar da mai gidana” Inna ta faɗa a sanyaye tana ta aikin face hanci da hawayen da suka gaza tsayuwa. Nan Malam mai allo ya basu wasu ganyen magunguna dasu rubutu suka yi masa godiya Inna tace zata aiko Abdul da abin sadaka ya ce ba komai, Musa ne ya kara daukar Rashida ya sake turota a akori-kura suka dawo gida, koda suka dawo suka iske Malam Yahaya wato Baban Rashida da Abdul ma sun dawo, ganin yadda Musa ya turo Rashida ya sa suka tabbatar da eh lallai fa akwai matsala da sauri Baba ya miƙe shi da Abdul

“Rashida ta rasu ne?”

“A’a Malam bata rasu ba, Musa kai ta ɗakinta ka kwantar da ita” Musa ya amsa da to ya dauki Rashida ya shige ɗaki ya kwantar da ita ya fito. nan suka zauna a barandar wajan ɗakuna da saman shi akwai rufi na falange akan tabarma suka yada zango jikinsu duk a sanyaye, Baba ya ce.

“Wai meya faru ne na gan ku haka?” zube masa magungunan da Malam mai allo ya bada tayi ta kalli Baban Rashida ta ce

“Malam dazu ina cikin sallar la’asar na ji ihun Rashida tana ga shi nan nazo na gan shi,koda nazo ni banga kowa ba sai Rashida” nan ta ba shi labarin abinda ya faru a yau din da yadda suka yi da Malam mai allo, shuru Baba ya yi yana mai dafe kansa jin yadda kan na shi ya sara, rintse ido ya yi yana waswasin Allah yasa ba shi bane makasudin ummul’aba’isin abin da ke faruwa da ‘yar shi ba tilo, gabaɗaya jikinsu ya mutu murus, Inna ta ce.

“Malam baka ce komai ba fa?” saurin kallon Inna ya yi sai kuma ya muskuta yana gyara zamansa yasa hannu ya riƙe ha6a yana duƙar da kan shi kasa kafin ya ce

“Lamari na Rashida a yanzu tsoro ya fara bani Salame” ajiyar zuciya Inna ta sauke a yadda suka zauna suka jeru tamkar mutuwa aka yi suna jimani, har aka yi kiran sallar magriba Malam ya miƙe ya kalli Musa da Abdul ya ce

“Ku tashi mu tafi sallah” miƙewa suka yi da kyar suka bi bayan Baba, a hanya Musa ya ce

“Baba anya babu saka hannunmu a matsalar Rashida?” saurin kallon Musa ya yi sai kuma ya kalli Abdul dake tafiya a hankali da alama bai ji abinda Musa ya faɗa ba, da ido Baba ya yiwa Musa magana da ya bar zancen, Musa ya sunkuyar da kai bai kara cewa komai ba.

Bayan fitar su Mama ta tuna da ruwan tuwon da Rashida ta ɗora ta shiga wanka, sallah Inna ta yi kafin ta shiga madafin ta samu itacen ya cinye wutar ta mutu ruwan ya tafasa har ya ƙone a fili ta ce.

“Kai tashin hankali babu dadi Allah ya so bata yi talge ba da an 6ata gari dan ƙonewa zai yi” sake hura wuta Inna tayi ta fara hada-hadan yin sanwa, tana yi tana duba Rashida dake bacci tana so ta tasheta tayi sallah amma tana jin tsoron yadda zata farka, rabuwa tayi da ita har ta farka da kanta kawai ba sai ta tashe ta ba.

Tana cikin girkin ne ruwa ya kare dole yasa ta dauki hijabi ta fito domin zuwa dibo ruwa tunda dama ta sani ba lallai bane su Musa su shigo har sai anyi isha’i idan suka zo daukar abincin Malam zasu kai majalisa.

 

 

 

 

Tafiya suke yi su biyu ku san kan su ɗaya suna hira, wasu yan mata uku ne suka sha gabansu, kallon su suka yi da son jin dalilin da yasa suka sha gabansu, ɗaya daga cikin ‘yan mata ukun ne ta kalli ‘yan mata biyun da suka sha musu gaba ta ce

“Shatu! Fatu? baku san abinda ya faru da ƙawarku ba ko?” hada baki suka yi wajan faɗin

“Kamar ya?”

“Cab kuna nufin ku ce ba ku sani ba! Labarin da duk ya baza ƙauyen nan ba wanda bai sani ba, dazu aka kai Rashida gidan Malam mai allo kamar gawa Musa yana turata ita da Inna, jita-jitan dake yawo ma kamar ance Rashida ta haukace ne”

“Kee Lantai ki iya bakinki wallahi,hauka ki gan shi a gidanku amma wallahi ahir dinki ba akan kawarmu ba” cewar Shatu tana riƙo ƙugu cikin masifa dan su Lantai sun jima suna neman su da tashin hankali a kauyen nan lokaci ya yi wallahi da zasu ci uban su Lantai.

“To karya aka yi ne dan an gaya muku gaskiya” Fatu ta ce.

“Oh har dasu kaza a cin danƙo? Ke Bishira ki fito idanuna na rufe dan wallahil azim ke huri ɗaya zanyi miki da iskar bakina ki faɗi ƙasa kina tafiya kina fama da yunwa jiki duk kasusuwa zaki 6allo watan bakwai ki bari dai Lantai da Harira da suke da dan kumari su yi dan suma ba sha zasu yi hannunmu ba”

“Wai ku me ku ka dauki kanku a ƙauyen nan zatonku kun fi kowa ne!?” cewar Harira a fusace zata yi kan Fatu da sauri Lantai ta riƙo Harira Fatu ta ja layin dambe tana fadin

“Barta ta shigo na yi mata 6arin makauniya a shirya nake wallahi!” su Lantai ganin da gaske zasu lanlasu a hannun su Shatu da Fatu yasa suka zame suna fadin idan su Shatu sun isa to a haɗu a filin shege ka fasa, Fatu ta daga murya da yake sun yi gaba tace

“Ko a filin dan iska ka fasa ne zamu zo ba a shege ka fasa ba” hannun Fatu Shatu taja tace

“Dama ai gidansu Rashidan zamu je kinga muje mu dubata, wallahi kauyen Mani da Iyah ta aikemu ne yasa idan wani abu ya faru ba lallai mu sani ba tinda dawowarmu kenan” tafiya suke yi da sauri suka nufi gidan su Rashida tun kafin su karaso sauron gidan suka ji yo ihun Rashida tana fadin

“Wayyoo! Wayyooo! Waayyo! Me nayi maka kakeson cutar dani! Don Allah ku zo ku gan shiii! Inna! Babaa! Yaya Musa! Abdul!” da mugun gudu Fatu da Shatu suka nufi cikin gidan har suna bangaje juna suka yi dakin Rashida dake kwance tana ta birgima tana buga kanta da banko da alama mugun mafarki take yi duk ta haɗa uban gumi,

“Rashida? Rashida? Fatu dibo ruwa” cewar Shatu duk sun ruɗe da gudu Fatu ta fito ta nufi katon tulun ruwa amma ba komai a ciki, zagaye gidan ta hau yi tana neman ruwa babu kamar daga sama Inna tayi sallama tana dauke da ruwa a saman kanta, Fatu bata yi wata-wata ba na wafci ruwan da ke saman kan Inna ta nufi dakin Rashida Inna ta bita a baya dan tana tafiya tana zance zuci sai yanzu taji gurnanin Rashida, Fatu na shiga dakin bata yi ala’akari da jiƙa ɗakin da zata yi ba ta sheƙawa Rashida ruwan gabaɗaya a jikinta ta duka, a zabure Rashida ta farka tana tattaba jikinta ta kalli ƙawayenta aminanta sun zuba mata idanu cikin tashin hankali suna kallonta kuka ta fashe da shi ta faɗa jikinsu, Inna na tsaye daga bakin kofa ta ma kasa shigowa cikin dakin tana riƙe da labule, kukan da Rashida ke yi ne yasa Fatu da Shatu fara tayata kukan sai da suka yi mai isar su tukunna Shatu tace

“Rashida wai meke faruwa dake ne?” ɗagowa tayi idanunta jajur tace.

“Nima ban sani ba Shatu, ban sani ba amma wallahi ina ganin *JEMAGE* ba irin ƙanana ba katoto duk yadda zan fasalta muku girman shi ya fi haka duk yadda zan fasalta muku muninsa da kalar tsoronsa ya fi haka” hannunsu ta kama ta ce

“Na san ko da ba wanda zai yarda dani ku Aminaina zaku yarda dani haka ne?” suka gya ɗa kai suna mata kallon tausayi, Shatu ta ce.

“Amma kinyi sallah Rashida?” girgiza kai tayi alamun a’a, tashi suka yi suka kamo hannunta suka fito Inna dai bata ce komai ba dan ji take yi kamar ta yi ta kuka ko zataji saukin abinda take ji a ranta, ruwa Fatu ta hau nema Inna tace

“Ba ruwa fa a gidan,ruwan kenan na dibo kika karba Fatu”

“To don Allah Inna ga Rashida bari muje dibo ruwan” cewar Shatu,

“To yaran albarka” cewar Inna, daukar abin dibar ruwa suka yi suka fita suna tafiya suna tattaunawa akan matsalar da ta kunno kai wa aminiyar su.

Basu dade ba suka dawo da ruwan inda Fatu ta sanya wa Rashida a buta, riƙe hannun Fatu Rashida tayi tace

“Don Allah Fatu ki rakani kewaye” zaro idanu Fatu tayi zata yi magana Inna tace.

“Raka ta”

“To Inna” cewar Fatu suka nufi bayi da kyar Rashida ta shiga Fatu ta juya baya, sai da ta rintse ido ciki tsoro ta kama ruwa suka fito Fatu na tsaye Rashida tayi alwala suka shiga daki ta kabbara sallah, Shatu kuwa ci gaba da dibo ruwa tayi tana taya Inna girki har suka gama a lokacin anyi sallar isha’i, Fatu suka yi wa Inna sallama zasu tafi, sai albarka Inna ke sanya musu suka ce zasu biyowa Rashida gobe zuwa makaranta idan jikin nata da sauki.

 

Bayan tafiyarsu Musa da Abdul suka shigo, Abdul ne ya karbi abincin Baba ya tafi kai masa majalisa, kallon Rashida Musa yayi ganin yadda ta takure gabaɗaya ya ji hawaye a idanunsa, Inna tace

“Musa ga abinci”

“A’a Inna bana jin yunwa” yana gama faɗi ya fita waje yana fadin

“Mu muka jawo mata mune sila! Mune sila” ya naushi iska…..

 

 

 

 

 

 

#COMMENTS#SHARE

#MomAhlan🪄

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment