JARIRI HAUSA NOVEL COMPLETE
Jariri Hausa Novel Complete
JARIRI
Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM
SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP
GARGAƊI
BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
1&2
Fuskar Halifa ɗauke da damuwa yace, “Inno gaskiya zuwa gidan Nusaiba da matsala saboda ko kaɗan banasan tayi nesa dani, na shaƙu da matata banasan ko nan da cen taje kawai kuyi haƙuri ku barta a nan” Inno ido ta zura masa tana ganin rashin kunyar ƴaƴan zamani ido biyu, kafin tayi magana Goggo ta karɓe zancen da, “Ka ji mun yaro da sabuwar salawaitun fitsara ido biyu, mu zaku gwadawa fitsara da rashin kunya? Munga tantabaru ma wajen soyayya yaran yanzu da komai sai sun nuna rashin kunya a ciki, mun ƙi mu bar maka ita sakarai kawai” Inno ta ce, “A’a barshi Hansai ya nuna mana ya kusa haɗa kafaɗa da mu, tunda ya kusa ajje ɗa kinga mun haihu shima ya haihu ai mun zama ɗaya da shi, fitsararre mai idanun marasa ɗa’a dubi yadda yake fiƙi-fiƙi saboda ɗiban albarka” Nusaiba da ke gefe ta zumɓuri baki gaba ta ce, “Ni dai gaskiya Inno ku ƙyaleni a nan inyaso wani a cikinku yazo ya zauna mun”
Nusaiba na rufe baki Goggo ta ce, “La’ilaha’illallahu Muhammada ɗan Abdullahi, Inno kinji ɗibar albarka da yarinyar nan zatayi mana irin ta yaran zamani, kinji Nusaiba ta zaɓi miji akan gidan ubanta, ke dan Ubanki ni zaki nunawa rashin kunya ido biyu, idan ban kwashe miki albarka ba kice bani bace?” Halifa ya ce, “Goggo abun fa bai kai haka ba, saboda Allah zuwa gidan nan yayin haihuwa ba fa dole bane ku barmun matata a gida mana, ina jin ɗumunsu ita da abinda zata haifa amma kunzo sai kwashe mana albarka kuke, a haka zan barta taje wanka gida kuna kwashe mata albarka? Haba ina dalili.”
Fataucin Mata Hausa Novel Complete Documents
Wannan karan Inno ce ta kuma rafka salati ta ce, “Tir da wannan halin naka na rashin ɗa’a amma dai Halifa na sai na kwashe maka albarka, wato jarabar taka ido biyu har agabanmu dan rashin ɗa’a? Wato mu bar maka yarinya inyaso ko arba’in bazatayi ba ka nuna rashin ɗa’a mujita da wani cikin ko?” Halifa hannu biyu yasa ya rafka tagumi saboda tsofaffun ba ƙaramin caja masa kai suke yi ba, cikin damuwa ya ce, “Inno wai dan Allah me yasa kunfiya matsala ne? Ni fa shiyasa wani lokacin ko ziyararku banaso saboda ba’a kwashewa ta daɗi da ku”
Inno daƙuwa ta watsa masa ta ce, “Ubanka Salisu shine me matsala, kuma wallahi kamar a kunnensa zan kira uban naka a waya naji ko shi ya baka lasisin da zaka ɗebe mun albarka” tashi yayi ya fice daga falon dan yasan indai ya cigaba da biye musu to tabbas zai hau sama da su.
Nusaiba da sauri ta tashi tabi bayan mijinta bisa tsautsayi ta harɗe ta faɗi, nan take ta fara naƙuda ba shiri suka fara ƙwala masa kira, hankali a tashe ya dawo suka kamata suka sakata a mota suka wuce asibiti.
Zuwan su asibiti da awa guda Allah ya sauki Nusaiba lafiya ta haifo ɗanta namiji kyakkyawa da shi, Nurse ɗin data karɓi haihuwarce ta fara goge jaririn amma wani abu daya ɗaure mata kai, yadda jaririn ya ƙura mata idanu ba kiftawa har hannu tasa ta rufe masa ido amma ƙir idanunsa a kanta, idan ba musu idanunta suke yi mata ba kamar ma harararta ta ga jaririn yana yi. A haka ta samu ta gama gyarashi da gurin aka sa masa kaya Nusaiba ta rungume abinta suka koma bacci, kafin wani lokaci tuni ƴan uwa sun cika asibitin kowa xai zo hannunsa ɗauke da kullar abinci yake shigowa, gudun hayaniyarsu yasa nurses suka hanasu shiga ɗakin da Nusaiba take saboda karsu hanata bacci.
Bayan wani lokaci, Nusaiba ce ta tashi gabaɗaya yunwa takeji cikinta kamar anmata yasa, batasan da kawo abincin da akayi tana bacci ba dan haka ta ƙwalawa Nurse kira, tana zuwa tace ta kira mata su Inno da sauri ta fita ta sanar musu da saƙon Nusaiba, su Inno tare da sauron ƴan uwa ne suka shigo ɗakin fuskarsu ɗauke da farinciki, wasu daga ciki ne suka ɗau jaririn, Nusaiba a shagwaɓe ta ce, “Inno yunwa fa nake ji ku haɗa mun ruwan tea” Inno ita da goggo da ƙarfinsu suka nufi wajen kullar amma tunkafin su buɗe sukaci karo da tsottsatssen ƙashi da wanda aka taune akan murfin kular, suna buɗe ƙatuwar kular abinci yace ɗaukeni inda kuka ajiye.
Ledar ƙaton buredin ma cen ƙarƙashin gado suka hangota, da alama anciye biredin iskar fanka ce ta tura shi cen ƙasan gadon, mamaki ne ya kamasu amma babu wanda ya magantu a cikinsu, Inno ce ta ɗakko flask ɗin shayi shima ta jishi shafal ba komai a ciki, a hassale ta fara magana. “Yau naga rashin ɗa’a ido biyu ni za’a gwadawa ɗiban albarka. Waye ya cinye abincin da shayin gurin nan?” Goggo ta ce, “Gane mun hanya yarinya ta haihu madadin taci ta ƙoshi gashi wasu ƙarti sun cinye”
Da mamaki Mahaifiyar Nusaiba ta ce, “Inno duka abincin kulolin aka cinye? To Nusaiba ko kinci abinci ɗazu?” Nusaiba ta girgiza kai, Inno ta ce, “Banda rashin ɗa’a Nusaiba duk cinta ai bazata iya cinye cooler uku ta abinci ba, maza kiramun masu fararen kayan cen gabaɗaya sai na kwashe musu albarka banda su babu me aikata wannan rashin ɗa’ar, yara sai rashin ɗa’a da ɗiban albarka kamar ƴaƴan mayunwata.” Mami mahaifiyar Nusaiba ta nufi mazaunin Nurses ɗin ta kira suka taho tare dan su a tunaninsu wani abun ne ya samu Nusaiba, suna zuwa Inno ta kalle su ɗaya bayan ɗaya ta ce, “Ina kuka kai abincin gurin nan saboda ɗiban albarka yarinyar nan ko loma ɗaya batayi ba, idan sha’awa ya baku basai ku tambaya a baku ba amma zaku nuna mana halin rashin ɗa’a wato sai kunci na Allah ya isa ko?” kallan juna suka farayi kamar haɗin baki suka ce, “Wane irin abinci ana zaune ƙalau kamar wasu mayunwata” Goggo kulolin ta janyo tana cewa, “Gasu naga ɗazu ke kika taya ni shigo da wata” ɗan zaro Ido sukayi suka ce, “Duka abincin cikin kular aka cinye” Inno ta ce, “Kiji mun shakiyyan yara marasa ɗa’a tambayarmu ma kuke yi, wallahi ko ku fito dashi ko na ɗebe muku albarka ku bi duniya”
Ɗayar nurse ɗin ce ta ɗan fara ɗaukan zafi ta ce, “Iya wai me kuka ɗauke mu ne saboda kuma muna ma’aikatan jinya duk wata ƙura aka ɗebo sai a watsa mana…” Inno a hassale ta katseta. “Amma kedai wannan yarinyar anyi maras ɗa’a wallahi idan baki rufen baki ba zan kwashe miki albarka ki ɓalɓalce ” ganin abun na nema zama faɗa Mami ta sasanta tare da yin waya gida akan a ƙara kawo musu wani abincin.
A yammacin ranar aka sallami Nusaiba ita da Jaririnta, tun a asibiti ake taƙaddama akan zaman Nusaiba a gidan ita Mami ma shiru tayi saboda yadda su Goggo suke ja’ina da Halifa amma fir yaƙi yarda. A hassale Goggo ta ce, “Rakiya wai dole sai mun bi ta yaron nan ne? Shi da ita duk jikokinmu ne me zamu zauna muna bi ta tasu, ni idan ya bari idanma bai bari ba zan ɗauke ta na wuce gurina da ita.” Inno sheƙeƙe ta ce, “Hansai au ke zaki tafi da Nusaiba? Wallahi bazan yarda da wannan ɗiban albarkar ba nice na haifi Uban Halifa ni nake da iko da wannan maganar” Goggo ta ce, “Rakiya wallahi baki isa ba nina haifi Uban Nusaiba dan haka nina fi dacewa da tafiya da ita” Inno ta ce, “Ahayye Allah na dawo inji kishiyar me yaji, wallahi baki isa kizo mun da wannan rashin ɗa’ar ba, ninan gurina zan wuce da ita.” Halifa ne ya shigo yaji yadda suka fara hawa sama a tsakaninsu dukda sun kasance ƴan uwa kuma aminan juna, Halifa ya fahimci sarai inda maganarsu ta dosa yace,”Nifa gaskiya babu wanda zai ɗaukarmun mata wai magana ɗaya ayita yinta har a asibiti ina dalili, idan fa kuka takura zau ɗauke matata na kaita wani gidan nawa inyaso na samu wacce zata dinga kularmun da ita ” Inno ta ce, “Oh La’ilaha’illallahu muhammad rasulillahi sallallahu’alaihi wasallam, oh ni ɗiyar mutum huɗu ba ko ɗaya naga abinda ya tsirewa kakata Laure ido, yanzu ɗibar albarkar da zaka mun kenan Halifa wani bari ubanka ya zo ya shata mun layi da kai, kai anya ma wannan ba’a sauyawa Salisu kai a asibiti ba?” Mami ce ta ce, “Inno dan Allah kuyi haƙuri ku bar masa matarsa tunda har yace bayasan taje gida wanka, shawara ɗaya zan bayar gabaɗaya kuje ki zauna mata ai ina ga hakan yayi?” gabaɗaya sun aminta da shawarar Mami, Inno ta ce. “Hansai kinga gwara da akayi hakan dan kinsan ni yanzu bana iya aiki a bakin wuta, na dinga kula da aikin cikin gidan kina ɗora garwan wankan mejego da jaririnta idan ba haka ba kar naxo na aikata rashin ɗa’a” Goggo ta ce, “Eh kuma fa hakane Rakiya kinga zamanmu bibbiyunma zaifi.”
Da wannan shawarar suka tarkata zuwa gida tare da ƴan uwa da abokan arziki.
A daren ranar da suka koma da daddare kimanin karfe biyun dare Inno ce ta fito fitsari ahanyarta ta dawowa, ta hango ƙaƙanin abu na tafiya idan yayi gaba sai ya dawo baya ya rangwaɗa kai gefe. A ɗan tsoroce Inno ta ce, “Toooo yau wacce irin ɗiban albarka nake gani da tsohon daren nan” ta ƙarasa magana tana haskashi da ƴar fitilarta.
A zabure ta ja baya ganin jaririn Nusaiba ne tumɓur ko wando babu, washe mata baki yayi ya dafe ƙeya yana wani irin layi kamar wanda yasha ya maku, cikin wata irin murya ya cafe irin maganar Inno yace, “Tooo yau wacce irin ɗiban albarka nake gani da tsohon daren nan” tana faɗa yana wani irin tsalle kamar zai faɗo kan Inno, wurgar da butar tayi saboda tsoro ta fara gudu. Tsalle yayi ya caɓe zanin Inno har ya taɗe ta ta faɗi da rarrafe ta dingan rarrafawa tana ƙwala ihu, lokacin da ta ƙarasa ɗakinsu tuni ta daɗe da wurgar da zani daga ita sai ɗan fatarinta.
[…] “Jariri Hausa Novel” is a well-known Hausa book. As two young lovers elope and embark on a number of adventures, the story follows them. Both romance and suspense are prevalent in the book. […]
[…] “Jariri Hausa Novel” is a well-known Hausa book. As two young lovers elope and embark on a number of adventures, the story follows them. Both romance and suspense are prevalent in the book. […]