Littafan Hausa Novels

Jalila Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Jalila Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*JALILA*

*short story*

 

*story and writing by Ummu sultan [matar dan aljannah]*

 

 

 

_Alhamdulilahi rabbil’alamina, godiya ta tabbata ubangijin taliƙai allah yadda nafara lafiya kasa nagama shi lafya_

Matar Hariji Hot Romantic Hausa Novel

*banyi shi dan cin zafin wani/wata ba idan yayi daidai da labarin ku arashi ne*

 

*ga mai ɓuƙatar a tallah ta mai hajar sa ya tuntubeni a 08108353370 sai naji ku*

 

 

Bismillahir rahamanir rahim

 

*Babi na daya*

 

Tunda natashi yau ma da ciwon kai na tashi, amma duk da haka “inna bata tausayamun da aikin gida ba”!

 

Haka kullum nake rayuwa da bautar “inna” bani da wani lokaci nawa in bana taba, ina cikin aikin ne jiri ya kwashe ni na faɗi, bansan inda kaina yake ba saidai na farka nagan ni asibiti, doctor ya mun aune aune anan ne ya gano ina da ciwon zuciya amma bai yi nisa ba, idan nasha magunguna za’a dace; sallamata akai muka dawo gida “inna tace yanzu cikin ai yukan ki na cire maki ɗibar ruwa”!

 

 

Murmushin jin dadi nayi nace “inna nagode da kika mun haka ɗin ma nasan kina so na”..

 

Kallan banza ta watsamin, nai saurin ɗauke ido na na maidashi ƙasa ina murza ya tsun hannu na na,, muna nan zaune wata “ƙanwar inna”tazo gidan gaida ta nayi na tashi na basu waje..

 

 

Ƙanwar inna[ rabi] tace ke abu wannan yarinyar ba zaki kaita birni ba ai katau?

[Da yake tana kai yara birni aiki]

 

 

Inna tace uhmm “rabi” surutun jama’a nake gudu wallahi, koni da nayi tunanin nan amma sam bani da wata hujja ta kaita kinga dai malam bazai yarda ba!

 

“Rabi tace haba gun boka zaki kai shi, a kulle masa baki shi kenan fa sai yarda kika juya shi”.

 

 

Kuma kin kawo shawara, amma kibani sati ɗaya nasan abun yi.

 

Juga ta tai tayi, har tasha wo kanta ta amince akaini aiki

 

•••••••••••••••••••••••••••••••

 

Hisham” gaskiya bazan iya ba wallahi asan mai yiyuwa man, haba ace kullum nice yar fashin aiki na!

 

Kallan ta yayi yace yanzu mai kike so nayi ne??

 

Rumgume shi tai, tsam a jikinta tace kasamo mana yar aiki wacce zata runƙa kulamun dasu “mubin da mubina”!

 

Shi kenan abun da kike so? Sha kurumun ki madam ɗina zan je hajiya tasamo mana ita!

 

Kiss ta mashi a kumatu, ta wuce kitchen…

 

 

Yau kwana uku da yin maganar kaini birni aiki,, farko babana bai yarda ba sai da tabiyo Mai ta ƙarkashin ƙasa nan’ sati mai zuwa zan tafi aiki nayi kuka so ba adadi ace da gata na anma zani birni aiki wannan duniya da mai tai kama ne?

 

 

Idan nasamu dama ina zaga yan’uwan mahaifiya ta ina masu ban kwana,, ban faɗi ma kowa ga inda “inna zata kaini ba” ina tsoran kada wani ya ganta ya mata maganar!

 

 

“Hajiya” ce zaune a bedroom ɗin ta, tana karanta kur’ani sallama yayi ya shiga zama yai kusa da ita ta ƙarashe karatun tace “hisham yanzu ake tafe”?

 

Ehh hajiya barka da safiya..

 

Yauwa ya gida ya yara?

 

Alhamdulilahi suna gaida ki, hajiya maganar ar aikin nan dai da muka fara a waya!

 

To badamuwa zan ma wata “rabi” magana in sha allah

 

 

 

Mu hadu a next page bani da chaji ne

 

 

*domin shawara 08108353370

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment