Littafan Hausa Novels

Jalaluddeen Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Jalaluddeen Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Jalaluddeen Hausa Novel Complete

Na *AYUSHER MOHD*

 

 

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai.

Yanda zan fara rubutun nan lafiya, ina rokon Allah dayasa in gamashi lafiya, sannan abinda ke ciki na kuskuren Allah ya yafe mana, wanda muka fad’a daidai kuma Allah ubangiji yasa masu karatu su amfana dashi(Ameen).

 

 

 

Ina godiya ga masoyana akan kullawar da kuke nunamin.

Hope zaku biyoni danjin wannan labarin…………luv u all

 

 

 

Episode 1⃣

 

 

 

 

Wani irin ihu ta sake mai tsananin kara, duk mutanen dake cikin gidan sai da hankalinsu ya tashi, mazan dake zaune a dinning suna breakfast suka kalli juna sai kuma suka mik’e da gudu sukai sama, masu aikin gidan suma duk suka hau gudu sai rige rigen hawa beni akeyi, mutum d’ayace bata ko d’aga kafar taba bare insa ran zatasa gudu kamar kowa, tsaki ma naga taja ta wuce d’akinta.

 

Zuciyar Mutum Hausa Novel Complete

Sukam duk sun isa kofar d’akin da ake ihun suka shiga knocking jin kofar a kulle, babban cikinsu wanda ina tunanin ma mahaifinsune ya matso jikin kofar yace “my swthrt open the door please. ”

 

Daga cikin d’akin cikin wata murya mai sanyi akace ” Dad kaga fuskata kuwa? Banasan ganin kowa.”

Kallan juna sukai shida mazan dake gun guda 2 sukai murmushi, wanda takira da dad d’in ya kalli wasu turawa dake sanye dakayan aiki kana ganinsu kasan masu aikine garin irin kayansu, ya musu alama da kai yace “Spare key.”

Cikin sauri sukace “ok Sir.”

Suka juya.

 

 

Basu dad’e ba sai gasu sun dawo, dasauri suka mik’a makullin.

 

D’an saurayin cikinsu ne wanda da alama shine karami ya amsa tare da bud’ewa, suka d’uru cikin d’akin dukansu, azaune suka ganta a kasa ta rufe fuskarta ta hannunta biyu.

 

 

Dad yai murmushi ya karasa kusa da ita yace ” My Swthrt meke ya faruwa? Bazaki bud’e ido ki kalli fuskar Dad d’in naki ba?.”

 

 

Cikin shagwab’a ta sauke hannun tare da bare baki tasa kuka tace ” Dad kalli fuskar Princess d’inkafa?”

 

Dariya suka kunshe dukansu, d’ayan namijin yace ” Wai! Wai! Wai! Seemah kin ganki kuwa? gaskiya na tausaya miki.” Yafad’a tare da kunshe dariyarsa.

 

Seemah ta kalleshi tace ” Yaya Janaid da gaske?” Takalli dad takara sa kuka tace ” Dad dama na fad’a maka shi yasa banso kuka ganni ba.”

 

 

Dariya karamin yai yace ” Ohhhh ni yazanyi? Kanwata takasa girma,” ya fad’a tare ta tab’a kasan id’anta ya lakutu bakin abu, yace ” wannan ba Mascara bane Seemah? ”

 

Sai alokacin ta kalleshi tace ” do u think so?”

Ya d’aga mata kai alamar eh,ta kalli masu aikin tare da mik’ewa taje kusa dasu, ta tsaya a kusa da d’aya tace “Anna mascarar dana sa jiyace tamin haka?”

 

Anna tace “Sorry Madam it’s my fault.”

 

Seemah takarasa jikin madubi ta kalli kanta kamar wata aljana da sauri ta rufe fuska takalli karamin saurayin tace ” Ya Ammar to ya akai hakan ta faru dani? Jini fa? Zai fita ma kuwa?”

 

Dariya sukai su dukansu, dad ya kamota ya zaunar a bakin gado, yace “Anna zo ki gyara mata fuska. ”

Dasauri tace “ok sir”

 

Ammar yace “amma meyasa kika kwana da kwalliya?bana hana ba?”

Ta turo baki tace “laifin Anna ne kullum in nai bacci ita take zuwa ta gogemin, amma shine jiya bata gogemin ba.”

 

Junaid yai dariya yace “da alama da asuba dakikai alwala duk ya zazzago miki, ke kuma shugabar bacci baki kulaba ki ka kwanta bacci.”

Tace” I think so yaya.”

Dariya sukai dukansu.

 

Dad ya mik’e ya kalleta yace ” Swthrt zamuyi late bari mu fita.”

Tai murmushi tace “nima inada lectures yanzu zan shirya.”

Shafa mata kai yai yace “yauwa baby na.”

 

Suna fita Anna tashigo ta goge mata fuska sannan Seemah ta shiga wanka.

 

 

 

Su dad na sauka kasa suka taradda matar d’azu ta fito daga d’akinta, ran dad ya b’aci ya kalleta cikin b’acin rai kafin yai magana su Ammar suka ja jakarsu sukai waje gun mota, ya kalleta, itama tsoron mai zaice take.

Ta d’aure tace “bakuyi breakfast d’in ba? na shiga toilet ne sai yanzu na fito.”

 

 

Dad ya maka mata hararra yace ” Yanzu in wani abu serious ne yasamu Seemah sai ki wuce toilet?” Ta d’aure tace ” it’s a relief ai tunda ba serious bane.”

 

Yace ” oh da kikai kamar baki sani ba? Kin kyauta.” Ya fad’a tare da yin kwafa ya wuce waje.

 

Tabishi da kallo tace yau koma me za’amin na tab’o ‘yar gwal? Sun bar yarinya duk tagama sangarcewa, datayi magana sai yacemata kar ta manta aurantama dayai saboda Seemah ne, tsaki tai ta wuce kitchen.

 

 

 

Seemah na fitowa daga wanka ta kure disco tana rawa tanasa kaya, Anna na tayata shiryawa, riga da wando tasa sanna ta zura suwaita doguwa a sama tasa karamin nayafi ta yane kanta, ta fito tare da d’aukan karamar jakarta.

 

 

A hankali ta sauko kasa ta kalli dinning kamar yanda masu aiki aka umarcesu, sun jera mata nata kayan abincin, ta karasa dinning ta bubud’e kwannukan, ta kalli matar dake zaune itama tana nata breakfast d’in tace ” Small Mom banajin zan iya cin abinci, in dad ya kira ya tambaya please kicemai na ci.”bata jira amsar taba tai waje, tana gyad’a kai.

 

Haushi yakamata tace “Small mom? Da haka ki kirani da sunana mana Sadiya”

 

Seemah na fita ta taradda driver ya gama goge mota yana tsaye yana jiranta, ta kalleshi tace ” da wace mota zamu? ”

Dasauri ya nuna mata wanda yake tsaye, tsaki tai tace “ni bana santa kujerar cikinta basu da laushi sosai, muje a waccen.” Tafad’a tare da nuna wata.

 

Da sauri yace to madam.

 

Kallan garin tai tace ” it’s snowing.”

 

Takarasa ta shiga mota suka fita daga gidan.

 

Garin England yau sun tashi ana ruwan kankara sai dai sukam mazauna garin sun saba da wannan rayuwa, hada_hadar su kawai sukeyi, nikam banda rawar sanyi ba abinda nakeyi, nace kaii! Ina zan iya rayuwa a nan? Seemah na kallah dako ajikinta, nace uhmm keda aka haifeki anan dama…….wayarta ce takatseni datai kara, da sauri Seemah tad’aga ganin sunan dake jiki Big Bros.

 

Cikin shagwab’a tace ” Yaya Habib.”

Yace ” Princess dafatan kin tashi lafiya?” Tace “lafiya lau Bros bayan kak’i zuwa?”

Ya kalli matarsa dake kusa dashi yace “Ai zuwa zai ban wahala yanzu d’an company d’in dad na bukatata sosai.”

Seemah Tace ” dama za’a barni inzo im ganka, If you think it yaya ban tab’a zuwan garin iyayena ba, gashi kai yanzu ka koma can, sannan su Ya Junaid da Ammar suna zuwa duk bayan 5 month haka ma Dad amma ni bandani.”

 

Habib yai murmushi yace “gaskiya kam, kunyi hutun skul?”

Cikin zumud’i tace “yau zamu gama exams, kasan kuma inmun gama shikenan an gama zuwa sai an dawo.”

Yace “Good, zan ma Dad magana yabarki kizo ko 1 month ne kimana.”

 

Dakarfi tace ” *YESSSS* Kai Bros shiyasa nake sanka sosai.”

Nan sukai sallama akan sai ya tambayi dad.

 

*************************

Seemah cikin farin ciki ta isa makaranta, ra k’osa taga ya Nigeria take, suna isa ta sauka daga motar tare da shiga cikin skul d’in, tana taka kafa zata ciga class d’insu taji ansa ihu ana fesa mata spray, mamaki ya kamata ta kallesu zatai magana taga abokinta Alex yazo kusa da ita yayi knell down tare da miko mata flower, yace ” Seemah will you date me?”

Ihu yan class d’in suka sa suna tafi suna cewa ” ACCEPT IT!!!!!!”

Kallan Alex tai cikin mamaki tace ” Alex what’s going on? ”

 

Ya kara m’iko mata flower yace ” Seemah please accept my love.”

Kallansa ta sake yi ta d’an tab’e baki tace ” Alex will you stop all this drama?”

 

Alex ya mik’e tare da cewa ” Seemah!!!”

Hararsa tai sannan tace ” do I look easy to u? Meyasa kowa yake neman raina min hankali? Rannan Abokin ka yazo min da zancen yana sona, yau kuma kai? Am I a toy to u? ”

Alex zai yi magana ta amshi flower hannunsa ta kalli wata mate d’insu datake sanshi, kowa na skul d’in ya sani har shi Alex d’in ta ajiye mata flower a gabanta sannan ta kalleshi ta wuce ta zauna, Alex ya bita da kallo, abokanansa sukace kaima kasani ai yarinyar nan datakejin kanta kamar ‘yar gidan sarauniyar England itace zata so ka? Get a hold of yourself buddy!!!…….

 

 

 

 

Tana zama waya ta d’aga tama Ammar text, tana ajiye wayar ya kira, yace ” Princess ya akai? Ki kace wani ya miki proposing?”

 

Tace ” eh mana yaya wai kuma ka san wa? Alex fa?”

Dariya yasa yace ” yanzu ya akai?” Tace ” ya akai kuwa? I reject him kaima kasani yaya Alex is not my type.”

 

Dariya Ammar yai tace ” nifa yaya wanda zan aura dole ne sai ya cika abubuwa guda 5, na farko kyau, na biyu ya d’inga bani respect, na uku bai isa yamin abinda zai b’atamin raiba, na hud’u ya zama mai kud’i d’an ni ban taso a babu ba, na biyar in har nace kaza to lalai sai an min.”

Ammar yasa dariya sosai yace ” anya kuwa zaki samu duka?” Tace “umm wait an see yaya I will definitely find him.”

 

Ammar yace kai amma na kosa inganshi.

Dariya itama tai tace “yaya plz kasa baki a barni naje Nigeria. ”

Yace “ok ba matsala, ai kin kai 20yrs ya kamata dad ya barki.”

Tace tnx Yaya

 

Ammar yace “ki share kiyi exams d’inki a nutse.”

Murmushi tai tace “ok tnx Oppa”.

 

♡♡♡♡♡♡♡♡♡

 

Zaune yake a gaban mahaifiyarsa ga kanwarsa dake kwance bata da lafiya, tun tana ‘yar shekara 10 ciwo ya kamata, take a kwance har yau Allah bai bata damar mik’ewa ba, komai yi mata ake.

Goge mata bakinta yai da miyau yake zuba, ya kalli umma yace ” umma ina tunanin tau zan koma.”

Tace ” Jalal in ka tafi wannan karan ka d’inga bari sai sati bibiyu, daga Abuja zuwa binin_gwari da nisa.”

 

Murmushi yai yace” zan duba, amma Abba fa? Naga har zan tafi bai dawoba.”

Tace “yaje kai Zainab kauye ne gun iyayenta, ta damu tanasan zuwa,” tai shiru can tace jalal nikam har yanzu baka duba maganar dana cema ba? Na auren Zainab? Kaga ‘yar uwace gata ba ruwanta.”

 

Jalal ya mik’e tare da cewa ” Umma bari na wuce, zan kiraki a waya.”

Takalleshi tare da cewa “to Allah ya kiyaye hanya.”

 

 

*Jalaludeen* kenan talakawa ne sosai sai dai mutum ne shi da bayasan a rainashi dan bashi da hali, kuma baya tab’a kaskantar da kanshi akan wani mai hali, baya d’aukar raini, ba kuma ya so a rainashi.

 

 

**************************

 

 

Seemah na gama exams da sauri ta shige mota dan batasan su had’u da Alex tana shiga, ta kira yaya Habib, yai murmurshi yace ” lalai na yadda kanwar nan tawa ta kosa tazo ta ganni”

 

Seemah tace ” yaya ya kukai da dad?” Yace “ya ce ba matsala indai zan kula dake.”

 

Ihu tasa tace” wow yaya amma nifa tunda na gama exam so nake a satin nan, in fact gobe ko jibi na k’osa inganka.”

Habib yace ” bakomai zan duba flight na kusa nima na k’osa inga my kanwa.”

 

 

 

 

 

 

 

 

By[truncated by WhatsApp]

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

🐾 *JALALUDEEN*🐾

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

 

 

 

 

 

 

Na *AYUSHER MOHD*

 

 

 

 

No 2⃣

 

 

 

 

Seemah tana isa gida a falo ta tarad da Matar babanta tana kwance ta mik’e akan kujera, ta saka apple a gaba tana ci, haushi ya kama Seemah itakam yanda matar takeyi yana bata haushi sam bata santa, ita tanaso taga mutum ya damu da ita bakamar wannan ba.

Shiga tai tare da tsaya a inda take kwance, ta kalleta tace “Small mom bakiga na dawo bane?”

Tad’aure ta d’an kalleta kasa kasa tace ” to in kindawo Seemah so kikeyi in mik’e in shiga tsalle? Ga ‘yar shugaban kasar England ta iso?”

Kallaman sun ma Seemah ciwo ta kalleta tace ” a gurin iyayena na fi wata sarauniyar England matsayi, amma ina tunanin dole yau injira Dad yazo d’an ya tabbatar miki da hakan.”

Tana kainan ta juya tai d’aki ta fad’a gado, d’an shagwab’a irin na Seemah ta hau kuka baji ba gani, sai data daidaici lokacin dawowar dad ta sake ware murya tana kuka.

 

 

Itakam mata hankalinta ya tashi, gashi batajin zata iya ba Seemah hakuri.

 

Dad tare suka dawo su 3 kamar yanda suka fita, haka suke dawowa kullum.

Dad na shiga ya kalli falon ya saba yana shigowa Seemah zata rugo da gudu ta rungumeshi, ganin ba ta nan yasa ya kalli matarshi yace ” Sauda ina Seema?” Cikin rawar murya ta nuna sama, dasauri dad yai hanyar suma su junaid suka bishi.

 

Seemah kam jin motsinsu yasa takara sa kuka da sauri suka bud’e kofar, dad ya karasa tare da cewa ” Baby menene? Waya tab’amin ke?”

Seemah Cikin kuka tarik’e hannun dad tace ” Dad tambayar ka zanyi, tsakanin ni da sarauniyar England wayafi matsayi a gunka?”

 

Da sauri Dad yace ” wace irin tambaya ce wannan Seemah? Wake wani zancen sarauniya bayan ni kece sarauniya ta?”

Ta kalli junaid tace kaifa yaya?

Ya kalleta yace ” Haba princess yama za’ayi ki mana wannan tambayar? Ai ko d’an sarauniyar ne ya nemi yana sanki saboda matsayinki bana jin zamu iya amincemai har sai ya yadda da dokokin mu bare kuma ace matsayi.”

 

Dariya tai tace ” yaya Ammar fa?”

Dariya yai ya matso tare da rik’e kunnenta kad’an yace ” waye ya miki wannan banzar tambayar ke kuma har kika rik’e a ranki?”

Tad’anyi kara tare da kallan Dad tace ” Small mom ce.”

 

A zabure Dad ya mik’e ranshi ya gama b’aci ya juya yai waje da alama gun matar tashi zai je.

 

 

Ammar ya kalleta yace “da baki fad’aba Seemah, Dad bazai mata dasauki ba dama ta b’ata mai rai da safe.”

Seema ta murgud’a baki tace ” wayace karta d’inga kula dani? Ni fa yaya banasan mutumin da bai damu dani ba, nafisan kowa na duniyarnan ya soni kar kowa yad’inga nunamin halin ko in kula.”

 

Dariya Junaid yai yace ” lalai Seema ai kuma hakan bazai yiwo ba, tunda mu muna sanki ba shikenan ba? Karki damu dan wani bai damu dake ba.”

 

Kallanshi tai tadai jishi amma bata aminta ba, itafa tafisan kowa ya sota yakawai……

 

Nikam nace tab da matsala……..

 

***********************

Dad kam yana fita ya tarad da Sauda a tsaye a kasan beni, ya kalleta yace ” waya baki izinin kid’inga had’amin ‘yata da wasu can mutane? Harki samin ita kuka?”

 

Tai shiru can tace” Alhaji bafa haka bane kasan me?….”

Katseta yai cikin zafin rai yace ” bansan komai ba, kuma banasan insan komai, abu d’aya nakeso in sani, a wani dalilin kike samin ‘yata kuka? Ko d’an ke bakisan darajar d’a ba? ”

 

Cike da mamaki ta kalleshi tace “Alhaji yazaka fad’amin wannan kalmar? Abinfa bai kai nan ba.”

 

Yace ” what? Bai kai nan ba? In bai kaiba meyasa ‘yata na sameta tana kuka? Karki manta zan iya jure komai amma banda hawaye daga idan ‘yata, banga d’an Adam d’in dazai wahalarmin da ‘ya ba nikuma in kasa d’aukar mataki ba, na aurekine d’an ki kularmin da ‘ya kuma akan haka kuka amince daga ke har iyayenki, kukace ku kuma so kuke in barki kiyi karatu a nan kasar na aminta, sannan ni na cika nawa kin gama masters d’inki sai nine bazaki cika min ba?”

 

Sauda ta had’iyi wani abu, ta d’aure tace ” kayi hakuri, ba da wani abun na fad’aba amma tunda abin ya kai haka amin hakuri.”

 

Dad baice komai ba ya juya ya hau sama, ta bishi da kallo ranta yakai matuka gun b’aci, tasan sarai me yake nufi da ya hau sama wato ta biyoshi ta bada hakuri.

Itakam ta rasa wani irin so sukema Seemah, itakam da Seemah gwara a mata kishiyoyi guda 3 su zama su hud’u, in kishiyoyine bata tunanin zasu samu wannan damar, haka ta d’aure tahau sama.

 

Seemah na zaune suna hira da shewa sai labarin abin dariya suke bata, itakuma tanayi, can ta d’aure tace “Dad please ka barni inje Nigeria. ”

 

Dad yace ” Seemah mu jira sai wani hutun, ban shirya missing d’inki wannan hutun ba.”

Turo baki tai cikin shagwab’a tace ” Dad please ka barni, bafa dad’ewa zanyi ba, sannan ga waya.” Tafad’a tana d’aga wayarta.

Ammar tad’an kalla da alama magana tamai ta ido, shima yace ” eh Dad ka barta please ko d’an taje ta gaida su Inna.”

Dad zaiyi magana sallamar Sauda ya katseshi, suka amsa ta karaso ta tsaya a kusa da Seemah, ta saki murmushi tace ” Haba Princess daga wasa ashe kinji haushi? Na d’auka tsakanin d’a da mahaifi akwai lokacin wasa?.”

 

Seemah ta kalleta zatai fitsara Ammar yai saurin toshe mata baki yace ” Aunty ba komai ya wuce.”

Takalleshi tace ” Seemah ina kike san zuwa nazo shigowa naji ana zancen.” Tai maganar tana murmushi.

 

Seemah tai shiru can tace” gun Yaya Habib nakesan zuwa amma naga Dad kamar bayaso.”

 

 

Yanda tai maganar ne yasa tabasu dariya, junaid yace ” da alama yau zamu ganku a rana Dad.”

 

Hawayene ya zubo mata tace “dad kaji ko? Gashi ka bari su yaya Junaid zasu mana dariya.”

 

Da sauri ya jawota ya rungume yace ” barshi da gulmarshi, so yake yaga munyi fad’a tunda bai tab’a gani ba, zuwa gun Habib kuwa na amince.”

Ihu tasa ta kara rungume dad tace ” Dad shiyasa nake bala’in sanka.”

Dariya suka mata Dad yace ” Amma in zaki inaji sai na had’aki da securities da zasu d’inga kula dake, haka kawai Habib na can gun aiki ke kuma kina guri ke kad’ai bazan bar hakan ta kasance ba.”

 

 

 

Ta kalli Ammar tad’an lagwab’ar dakai kamar zatai kuka Ammar yace ” Dad amma ina ganin kabari kawai in yaso in taje can sai a sanar da Habib ya samarmata bodyguards dazasuna kula da ita. ”

 

Dad ya kalle Ammar yace “kana ganin hakan ya fi?” Dasauri Seemah tace eh mana Dad.

 

 

 

 

 

Nace uhmm………………

 

****************************

 

Yau Seemah tun Safe akai wanka dan flight d’in sukai booking, Sauda tafi kowa murnar wannan tafiya d’an ko Seemah dazatai tafiyar ta fita murna.

 

Seemah ta shirya cikin riga da wando d’an ita banaji akayanta akwai atamfa ko ince bata tab’a gwada sawa bama, bayan tasa riga da wandon sai kuma ta d’auko rigar sanyi tasa, d’an garin sai da rigar sanyi, ta yi kyau Anna ta kalleta tace ” Madam I will miss you.”

Harararta Seemah tai tace ” bayan yanzu kin rage damuwa dani?”

 

Anna ta karaso ta rungumeta a hankali kwalla ya zubo mata, Seemah ta juyo tace ” wasa nake Anna na sani kin damu dani sosai, tun ina karama, nima I will miss u.”

 

Tare suka fito Anna na rik’e da jakarta, a falo sukaga Sauda sai murmushi take, suna saukowa ta kalli Seemah cikin tsananin farin cikin da kana gani zaka gane tace ” Seemah yanzu tafiya zakiyi? Sai kuma yaushe?”

 

Seemah ta kalleta ta had’e rai tace ” Small mom nasani kinfi kowa murnar tafiya tai, sai dai ba dad’ewa zanyi ba.”tana kainan tai waje gun dasu Dad ke jiranta a mota.

 

 

Kowa yana zaune a cikin motarsa da driver d’insa, ta kallesu tare da sa dariya tace ” Dad ahaka za’ayi rakiyar? Kowa na motarsa? Nima in shiga tawa?”

 

Junaid yace ” to a ya za’ayi?”

 

Ta bud’e motar junaid tace yaya fito, junaid ya fito, ta bud’e motar Ammar tace bros kaima fito, shima ya fito, sukace me za’ayi? Motar Abba ta bud’e ta gaba tace Ya junad shiga nan, ya kalleta yace tohh.

Nan ya shiga ta kalli driver d’in Dad tace fito shima ya fito ta kalli Ammar tace bros jamu………tafad’a tare da shiga kusa da Dad.

 

 

Dariya sukai nan suka shiga tare da fara tafiya, Dad yace ” kai Seema zamuyi missing d’inki, baki tab’ayin tafiya ba tunda aka haifeki.”

 

Tai raurau da ido tace ” yauwa, dole ne kowa a rana ya kirani sau 5 in ba so yake muyi fad’a ba.”

 

Haka suka cigaba da tafiya ana raha, Dad yace” na fad’ama Habib ya kularmin dake sosai duk abinda kikeso a tabbatar an miki shi.”

Dariya tai tace ” inada Dad irinka me zai dameni?” Sun isa takira Habib tafad’amai zasu taho.

 

Sai da aka gama musu checking suka shiga jirgi sannan suka juya zuciyarsu duk ba dad’i.

 

 

 

**************************

 

 

 

Habib na isa company d’insu ya fara shiga meeting, sun dad’e kafin su gama suka fito sukai sallar azahar, ya duba agoggo akala saura hour d’aya su seemah su iso, yana komawa yataradda wani aikin ya kara tasowa dolene su shiga wani meeting d’in gashi baisan sanda zai fito ba, Secretary d’insa ya kalla yace ” Kanwata tana hanya gashi zamu shiga meeting kasa wani ya je airport nan da minti 30 ya jirata ta iso ya tahomin da ita nan, sunanta Seemah, ka tabbatar wanda ka tura mutum ne mai hankali yakuma je ya jirata yanda tana isow zai kawomin ita.”

 

Secretary d’in ya amsa da to, nan ya shiga tunanin wazai tura, abokinshi ya tuno, dasauri ya danna number, daga can aka d’aga yace ” ya akai Sagir?”

 

Sagir yace ” Jalal please kataimakamin meeting zamu shiga da Chairman to kuma kafin mu fito kanwarsa ta iso shine ya keso a taimaka d’aukota, nikuma banyi tunanin kowa a company d’in nan ba sai kai.”

 

Jalal yai tsaki yace ” ta hawo taxi mana? Dole sai an d’aukota? Ni ma aiki nakeyi.”

 

Sagir yai dariya yace ” Taxi jalal? Kanwar Chairman d’in company d’inmu fa nace? Kuma bana tunanin ma ta tab’a zuwa kasar'”

 

 

Jalal ya nisa yace” to kanwar Chairman tafi karfin taxi?”

“Nidai plz kataimakamin abokina d’an Allah, sunnanta Seemah, bari na shiga meeting zan ba da makullin motar chairman d’in akawo maka, nan da 30mins zasu iso.”Sagir nakainan ya kashe wayar.

 

Tsaki Jalal yai sannan ya kalli takardun da aka bashi yai sorting, shifa baisan rainin hankali, shi driver ne? Dandai Sagir ne amma da ina…………..

 

 

 

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment