Littafan Hausa Novels

Izzar Sarauta Page 1 To 10

Written by Hausa_Novels

Izzar Sarauta Page 1 To 10

 

 

 

 

 

 

IZZAR SARAUTA*

 

 

 

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

🎐 “`G•W•A
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

 

 

*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* ✍

 

*DEDICATED TO..*
*MOM IRFAAN*
*Nagode sosai da irin gudunmawar da kike bani Allah ya* *k’ara zamunci*

 

ALHAMDULILLAH!
ALHAMDULILLAH!!
ALHAMDULILLAH!!!

Mairo Yar Baka Hausa Novel Complete

_Allah na gode ma da ka k’ara bani damar fara wani littafin ya Allah yanda na fara lafiya Allah yasa na gama lafiya._

 

_Masoyana a kullum Ina k’ara gode muku da irin gudunmawar da kuke bani, gashi Allah ya sake dawo dani na sake kawo muku labari mai nishadantarwa soyayya da kuma IZZA Allah ya bani ikon isar da sak’on da yake ciki._

 

“`DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN K’AI, NAKE FARA WANNAN LITTAFIN NAWA.“`

 

 

📝 *Page* 1⃣⏩2⃣

Kyakyawan saurayi ne Wanda ashe karu bazai wuce ashirin da takwas ba, yake saukowa daga matattakalan jirgi cikin IZZAR SARAUTA da kuma mulki gaban shi akwai masu tsaron shi haka ma bayan shi.

Da ka ganshi kaga jinin larabawa, yana gama sauka k’asa wasu mutane suka zo da sauri suka tare shi, motoci ne jire a k’alla zasu Kai takwas aka bud’e mai daya daga ciki ya shiga Suma suka shiga da sauri suka tada motar.

Da gudu suke tafiya a titin Wanda in mutum beyi Wasa ba zasu iya taka shi, mutane na gannin haka suka fara fad’in, “YARIMA Dameer ya shigo gari kenan?”.

Daya daga cikin mutanan yace, “ga zahiri ai in dai ya shigo gari haka zaku ga motoci na tafiya”.

Dayan yace, “to ai IZZAR SARAUTA kenan” haka dai suke ta magana tsakanin su.

Tunda ya shiga motar ya daura kan shi jikin kujeran motar yake tunani da ya zamai mai jiki, har suka iso wani babban Gate Wanda daga gani kasan na masarauta ne.

Busa da kid’ed’e ne kawai ke tashi tunda suka shigo babban Gate d’in badawa duk sun fito sun tsatsaya suna jiran fitowan yariman daga mota.

A dai-dai wani dan madedecin part suka tsaya da sauri na cikin motar suka fiffita suka bud’e mai sai da akai wajan minti goma sannan ya zuro k’afar shi ya fito a motar.

Dan madedecin part d’in ya dosa nan ma da sauri daya daga cikin fadawan ya bud’e mai ya shiga, direct bedroom d’in shi ya huce.

Yana shiga ya cire takalmin shi ya haye kan Bed d’in, gaba daya ya rasa mai yake mai dadi a duniya tunanin shi kawai yaushe mahaifin shi zai fara nuna mai kulawa irin ta d’a da mahaifi.

 

Yasan da mahaifiyar shi na Nan bazai tab’a zama cikin wannan k’uncin ba, can dai ya Mik’e toilet ya shiga shower ya sakan ma Kan shi.

Ya Kai tsawon minti talatin sannan yayi wanka yayi alwala ya fito, gaban miroo ya tsaya Yana goge jikin shi da towel Yana gama wa ya zura jallabiya ya shinfid’a sallaya ya tada sallah.

 

Wata mace ce kishingid’e kuyangu zagaye da ita kowa da aikin da yake mata, alama tayi da hannu da a miko Mata apple cike da girmamawa.

Daya daga cikin kuyangun ta miko mata, amsa tayi ta fara juya shi a hannun ta Sannan tayi wani k’asacan murmushi ta kalle daya daga cikin kuyangun ta tace,

“Ke marina” cike da girmamawa da kuma tsoro tace, “Naam ranki ya dade uwar gidan sarki fulanin sarki Allah yaja da ranki”.

Juya apple d’in hannun ta tayi sannan tace, “yau Dameer ya dawo masarautar nan Ina so a fadawan jakadiya karta Bari ya samu ganin mai-martaba har sai ya shigo ya gaishe Ni”.

 

Cike da girmamawa marina tace, “an gama ranki ya dade” sannan ta tashi ta fita dan isar da sak’on uwar gijiyar ta.

 

Girgiza Kai tayi sannan ta saki wani makirin murmushi tace, “tunda ban bar uwarka ta zauna a masarautar nan ba Kai baka Isa ka zauna ba masarautar MURI ta ‘yaya’na ne”.

Gimbiya haleematun sa’adiya kenan uwar gidan sarki Fahad Abdullah kenan kuma fulani a yanzu.

 

 

Bayan ya idar da sallah shiryawa yayi cikin milk d’in shadda an Mata Zane da bakin zare, hannun shi daure da agogo bak’i haka hulan kan shi ma, shigar tayi mutukar fito da ainiyin kyau shi na jini larabawa.

 

Fitowa yayi daga part d’in nashi da sauri masu tsaron shi suka taso daga musu hannu yayi alaman baya buk’atar su.

Da kanshi ya shiga mota ya tada sai babban fadan masarautar, Yana Isa yayi parking ya fito kofan da zata sada shi da fadan ya nufa.

 

Zai shiga kenan yaji jakadiya na magana, “Allah yaja da ran yarima Dameer mai-martaba Yana da bak’i yanzu, Amma zaka iya shiga gurin fulani”.

 

Bece Mata ufan ba ya juya zai tafi ko mai ya tuna kuma sai ya juya ya shiga part d’in gimbiya haleematun sa’adiya fulani kenan.

Noking d’in kofan yayi daga can wata kunyanga ta fito taga ko waye sai da ta gaishe shi sannan ta juya duk da dai ta san ba samun amsa zata Yi ba, fulani ta fad’a zuwan nashi sannan tace, “a fad’a Mai ya shaga” shiga yayi.

Da sallama a bakin shi, tana ganin shi ta saki fuska ta fara washe bak’i, “Aa kaga mutanan saudiyya lallai my son shine baka sanar Dani zuwan naka da wuri ba ai da an..”.

 

Katse ta yayi da cewq, “ba komai Momma nima haka kawai naji Ina son zuwa na ganku shiyasa tafiya ba shiri”.

Tab’e Baki tayi tasha be ganin ta sannan tace, “ka shiga gurin mai-martaba kuwa Dan nasan dai-dai lokacin na Yana fada”.

Girgiza Kai yayi kawai sannan ya tashi Yana cewa, “yanzu Zan shiga na barki lafiya” be jira amsar ta ba yayi ficewar shi Dan d’an maganan nan da yayi Kan shi har ya fara ciwo.

Da harara tabi bayan shi har tabar gannin shi sannan tace, “very soon Nigeria zaifi karfin ka”.

Yana fita be shiga shashin mai-martaba ba ya hau mota ya fita a masarautar gaba daya.

 

“Deeyanah, Deeyanah” Amma kenan take Kiran Deeyanah wacce aka kira da Deeyanah ta fito da sauri tana cewa, “Amma ganinan fa uniform d’in makaranta na nake ninkewa”.

 

Murmushi kawai Amma tayi sannan tace, “Deeyanah kenan sarkin karatu ya Allah ka bamu kudin da zakiyi karatu”.

Ita ma wacce aka kira da Deeyanah murmushi tayi sannan tace, “Ameen Amma in nayi karatu na zama yar jarida ai Amma mun gama talauci a duniya”.

Girgiza Kai kawai Amma tayi sannan tace, “Allah yasa Deeyanah Allah ya cika Miki burin ki na ganin kin taimaka mana a rayuwa”.

Murmushi kawai Deeyanah tayi sannan ta cigaba da taya Amma wanke kayan miyan da take.

 

 

*Vote*
*Comment*
*&*
*Share*

 

 

*Aunty baby ce* ✍
[1/6, 10:37 PM] Mum Irfaan🤱🏻: 🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚

🤴🏻 *IZZAR SARAUTA*🤴🏻

 

 

 

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

🎐 “`G•W•A“`🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

 

 

*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* ✍

 

 

*DEDICATED TO..*
*MOM IRFAAN*
*Nagode sosai da irin gudunmawar da kike bani Allah ya bar zumunci.* 💖💕💖

 

*BISMILLAHIR* *RAHMAIR RAHIM*

 

 

📝 *Page* 3⃣⏩4⃣

 

 

Tunda ya fita daga masarautar be sake dawowa ba sai k’arfe goma na dare plazan shi da ke cikin birnin taraba ya je duba yana yin masu kula da wurin.

 

Direct part d’in shi ya huce dan ba karamim gajiya yayi ba, yana shiga parlour shi yaga an jera mai kala-kala abinci.

 

Tab’e Baki kawai yayi dan yasan wacce ta aiko da abincin bata huce Amaryan mai-martaba ba, bedroom d’in shi ya huce kan Bed kawai ya haye ya kwanta.

 

Wayan shi yaji na ringing sai da yaja dan tsaki sannan ya dauki wayan dan yaga mai kira, my Jadda ya gani Dan murmushi gefan Baki yayi sannan ya dauka.

Cikin larabci ta fara mai magana yana mayar mata harda suka gama wayan sannan ya kashe ya gyaran kwanciyar shi ya rufe I duk da dai ba baccin yake ba tunanin rayuwa kawai yake.

 

Sai kusan k’arfe shi-biyu ya samu bacci yayi gaba da shi.

 

Mai-martaba ne zaune a kilisar shi kad’an-kad’an yana tauna tuffa a bakin shi, jakadiya ce ta shigo cikin girmama ta zube gaban shi tace,

 

“Barka da hutawa mai-martaba Allah ya ja da ran sarki gimbiya Marwa tana neman iso”.

Kai ya d’aga mata alaman zata iya zuwa sannan jakadiya ta k’ara mai kirari ta fita dan sanar da gimbiya Marwa Amarya gun sarki Fahad Abdullah kenan.

 

Gimbiya Marwa ce ta shigo cikin kwaliya ta sanye da alkefba ta samu kusa da mai-martaba ta zauna sannan ta duka ta gaishe shi.

 

Ya amsa cike da fara’a, fira suka fara cikin kwanciyar hankali da nuna so da kauna Dan duk cikin matan shi ya fi son gimbiya Marwa shiyasa ita ke damawa.

 

 

 

*Asalin labari*

Wanene sarki Fahad Abdullah, sarki Fahad Abdallah ‘da ne ga sarki Abdullah Muhammed Abdullah adalin sarki ne duk cikin sarakunan taraba da suka shud’e shine Wanda al’umma suka fi so da nuna Mai gata.

 

Sabida shima yana kyautatawa al’umma da kuma talakawan garin, sarki Abdallah yana da mata uku, gimbiya Maimunatu ita ce babba Allah ya azurtata da ‘ya’ya biyu duk maza,

 

Fahad shine babba sai Aliyu, matar sarki Abdallah ta biyu kuma bata tab’a haihuwa ba Mai suna gimbiya Ameena, sai matar shi ta uku gimbiya Mabaruka tana da yara uku,

Duk mata Hadizato, sai kuma ummu-salma, suke nan Allah ya azurta da shi, sarki Abdallah yaran shi biyar kenan, sarki Abdallah gwarzon namiji ne a cikin gidan sa shiyasa kan yaran shi ya zamo a had’e.

 

Fahad yana kula da k’annan shi hudu sosai baya cire Hadizato da ummu-salma a cikin duk abinda zai ma Aliyu a haka har suka girma suna bashi girman shi sosai kuma iyayan su ma haka sai dai Dan abun da ba’a rasa ba.

 

Girma ya zo ma Fahad lokacin kuma sarki Abdallah yayi marabus da mulki ya danga wa dan shi Fahad, a lokacin an daura wa sarki Fahad aure da gimbiya Halimatun-sa’adiya.

 

Halimatun-sa’adiya ‘ya ce ga wazirin sarki Abdallah lokacin da za’a ba sarki Fahad mulki bashi da wacce yake so sai waziri yace ga halimatun-sa’adiya diyar shi sarki Abdallah beyi musu ba aka hada aure da nadin sarautan sarki Fahad.

 

Anyi bikin aure da sarauta lafiya an tashi lafiya, nan kuma ba’a fi wata biyu da hawa sarautar sarki Fahad ba Allah yayi wa sarki Abdallah rasuwa.

 

Rasuwan da ta ratsa duk wani mahaluki na cike da wajan masarautar, haka sarki Fahad ya cigaba da mulki kaman yanda mahaifin shi yake yi.

 

Ya bud’e makarantun islamiya dana boko duk kyauta, ba k’aramin Dadi talakawan gari suka ji ba ganin ya cigaba da abunda mahaifin shi yake.

 

Sannan kuma ya cigaba da kula da iyayan shi Mata da kuma k’annan shi mata uku da kuma kanin shi Aliyu, har suka isa aure duk sun ukun ya auran da su.

 

Matar shi halimatun-sa’adiya ta kasance mace mai kishi gashi kuma kullum zancen mutanan fada ya k’ara aure sarki ba’a San shi da mata daya ba.

 

A haka wata tafiya ta kama shi zuwa saudiyya zaiyi wata biyu k’iri da muzu gimbiya halimatun-sa’adiya taki bin shi Ita a dole tana laulayin cikin ta na fari.

 

Maman shi tace, “to ya barta tunda wata biyu ne ba matsala Allah ya dawo dashi lafiya”.

Haka ya shirya da yan rakiyan shi suka tafi saudiyya, satin shi daya a saudiyya wani abokin shi balarabe da sukai makaranta tare ya gaiyace shi gidan su.

Ya shirya shida fadawan shi suka je gidan wannan aboki nashi mai suna……

 

 

 

*Vote*
*Comment*
*&*
*Share*

 

*Aunty baby* ✍
[1/6, 10:37 PM] Mum Irfaan🤱🏻: 🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚

🤴🏻 *IZZAR SARAUTA*🤴🏻

 

 

 

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

🎐 “`G•W•A“`🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

 

 

*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* ✍

 

*DEDICATED TO..*
*MY SUMY*
*Marubuciyar* *k’awar’yata ce* 💕💕💕

 

*BISMILLAHIR RAHMAIR RAHIM*

 

 

📝 *Page* 5⃣⏩6⃣

 

 

Mai suna Al’mustapha an musu tarba ta mutunci da karramawa dan larabawa ba daga nan ba wajan tarban bako.

Iyayan Al’mustapha sun yaba da hankalin sarki Fahad Abdullah sosai suka saki jiki da shi, ya dade a gidan sannan suka shirya zasu tafi.

 

Sallama sukai da iyayan Al’mustapha sannan ya fito raka shi har sunyi sallama zai shiga mota ya hango wata kyakyawar balarabiyan yariya wance baza ta huce shekara goma sha-bakwai ba.

 

Da gatawa yayi daga shiga motar har yariyar tazo ta huce ta gaban shi ta shiga gidan su Al’mustapha da kallo ya bita Al’mustapha da yaga yana kallon yariyar sai ya dawo yake tambayar shi lafiya kuwa.

 

Girgiza kai yayi kawai yace, “lafiya” sannan ya shige mota da tunanin yariyar a ran shi to a ina take shidai bega fuskan ta da kyau ba balle Amma kuma yaji gaba daya son ta ya shiga zuciyar shi.

 

Har suka isa masaukin su tunanin yariyar yake ji yake kaman ya koma gidan su Al’mustapha dan ya gano wannan yariya amma ba dama.

 

Haka nan ya kwanta cike da tunanin yariyar nan, washe gari haka ya tashi sai tunanin yanda zaiyi ya koma gidan su Al’mustapha yake, can wata dabara ta fado Mai.

Ya dauki wayan shi ya kira Al’mustapha bayan sun gaisa yake fad’a mai ya manta da zuban azurfan shi a gidan kuma mai-martaba ne ya bashi yana son zuban azurfan sosai to zai dawo gidan ya duba.

 

Al’mustapha yace, “Aa abokina zan duba na kawo ma”.

Da sauri sarki Fahad Abdullah yace, “Aa shi zai zo ya duba” haka nan Al’mustapha yace, “to shikenan sai ya zo zai fara duba mai yanzu ma”.

 

Suna gama wayan ya tashi ya shirya cikin kayan sarauta yayi kyau sosai sannan suka tafi zuwa gidan su Al’mustapha.

 

Gidan su Al’mustapha kuwa sai duba mai zube ake har Al’mustapha yasa k’awar shi mai suna Khadija suna ce mata khaujut ita da matar shi su shiga D’akin da sarki Fahad ya zauna su duba.

Hakan kuwa akai suka shiga suna ta dubawa basu gani ba a haka har sarki Fahad ya iso, kaman jiya haka aka tarbe shi cikin mutunci.

Al’mustapha ya tambaye khaujut akan sunga zuban suka ce basu gani ba haka nan yace, “to taje ta kawo ma abokin shi shayin gahawa” ta huce kitchen ta hado komai da komai sannan ta shigo D’akin dan ta ajiye Mai.

 

Tunda ta shigo D’akin yake binta da Ido Sai yanzu ya tuna Al’mustapha ya tab’a gaya mai yana da k’anni mata, ajiyewa tayi sannan ta fita nan d’in ma binta yayi da Ido.

 

Sai da Al’mustapha ya tabo shi tukun ya dawo daga duniyar tunanin da ya shiga, ajiyar zuciya ya sauke sannan yace, “my friend wannan k’anwar kace? “.

 

Murmushi Al’mustapha yayi sannan yace, “eh sunan ta khaujut”.

Jinjina Kai kawai yayi yana sak’e-sak’e cikin ran shi yasan dai abunda yake tunani bazai tab’a yuhuwa ba larabawa baza su taba daukan Y’ar su su bashi ba yanda suke gannin yan Nigeria k’ask’antu.

 

Al’mustapha ne ya kalle abonkin nashi ganin ya tafi duniyar tunani kuma yaga kaman akan k’anwar nan tashi ne, gyaran murya yayi sannan yace, “abokina ya akai ne naga kayi shuru? “.

Shurun ya k’ara yi dan besan abunda zaice mai ba can dai yace, “Bari in tafi dan ina son yau in shiga harami”.

Al’mustapha taso wa yayi daga kujeran da yake zaune ya matso tashi ta zauna ya dafa kafad’ar shi yace, “abokina ya kama in wani abu kike so a cikin gidan nan ka fad’a min ko ma menene zanyi ma insha Allah in dai befi karfi na ba”.

 

Ji yayi maganar tayi mai nauyi ya fadawa Al’mustapha Ita sai kawai yace, “ba komai my friend”.

Murmushi Al’mustapha yayi sannan yace, “In kai ka kasa fad’a min ni bari in fad’a ma son khaujut kake tun jiya naga alamun haka sannan kuma zuben da kike cewa ka manta da shi a gidan Nan to ka manta baka cire shi a hannun ka ba da zaka tawo Nan gidan dan haka na gano ka kawai” ya karashi zancen cikin tsokana.

 

“Innalillahi ” ya fad’a Yana dariya yace, “kai fa Al’mustapha Daman haka kike duk abunda mutum yake Kare wa sai ka gano shi to Alhamdulillah da yasa ka gane Wallahi tun jiya da nagan ta naji gaba daya sonta ya shiga zuciya ta pls my friend ka taimaka min”.

 

Girgiza kai Al’mustapha yayi sannan yace, “abokina akwai aiki babba sabida iyayan mu da wuya su yarda duk cikin mu sunfi son khaujut, amma zanyi kokarin ganin na taimake ka dun gaskiya nasan kana da hankali munyi zama da kai na tsahun shekara biyar nasan halin ka to amma khaujut yariya ce Bata wuce shekara sha-bakwai ba”.

 

Murmushi sarki Fahad Abdullah yayi sannan yace, “Ni ba son khaujut nake dan komai na rayuwar ta ba sonta nake tsakani da Allah Wallahi ban taba soyayya kuma ban taba jin Ina son wata yariya a duniya ba irin khaujut”.

 

Al’mustapha yace, “na sani abokina amma kuma ya matar ka? “.

Sarki Fahad yace, “tana Nigeria amma kuma kasan Nigeria duk in kana da mulki a hannun ka ba mata daya zaka aura ba dole biyu zuwa uku”.

“To shikenan na maka alkawari zuwa gobe zan fada ma yanda mukai da family mu akan maganar” cewan Al’mustapha.

 

“To nagode my friend Allah ya bar zumunci” haka sukai ta firan su sannan Al’mustapha raka shi ya tafi cike da murna.

 

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment