Littafan Hausa Novels

Ido Hudu Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Ido Hudu Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

IDO HUƊU

 

 

By A.A

 

Free Page

Book 1 Ep 1

 

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

 

Ma sha Allah.

Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki me kowa me komai.

Ya Allah yadda na fara lafiya ka bani ikon kammala shi lafiya kuskuren da ke ciki ka yafe min.

 

(Gaisuwa nake ga Masoyana *INDO CE* Kullum ku na raina kuma ƙara ƙaunarku nake, Zaku ga na cire INDO CE na saka A.A Sabuwar inkiyata kenan😻)

 

 

Bismillahirrahmanirrahim

 

 

 

 

 

Ruwa me ƙarfin gaske da Iska me matuƙar tasiri Gami da tsawa me matuƙar kaɗa dukkan halittun da ke wannan yankin, a cikin wani dare wanda ya kasance me matuƙar duhu, Walƙiyar da Gagarumin hadarin dake Ruwan ya ke yi ce kawai ta ke haska sararin samaniya, dare ne me cike da firgitarwa tin daga kan Mutane har zuwa halittu Daban-daban wanda hakan ya sa wasu su na ta barin Sheƙarsu domin neman tsira.

Ashe Dangin Juna Muke Hausa Novel Complete

Hanƙoro gami da Wani ƙugi babban Tafkin Ruwa ya ke yi, yadda yake kantsamewa ya na rimi kamar fusata za ta sa ya fito ya cinye ƙasar hakan kaɗai ya isa karyar da Zuciyar Ɗan Adam.

Duk wannan yanayin bai sa ta tsorata ba sannan ba ta fasa yin abin da ya kawota gurin ba.

Ruwan sama ya na dukanta yayin da na ƙasa ke ƙoƙarin haɗiyeta amma hakan bai sa guiwarta ta sare ba, ta na tsaye cokam a gaban Tafkin ta zuba masa idanu kamar me yi masa kallon ƙarshe, ta kwashi lokaci me tsayi kafin ta ja dogon Numfashi sannan ta fara magana.

“Ya Allah ka fini sanin abin da ke ɓoye a cikin Zuciyata kuma ka fini sanin abin da zai faru da wanda ya faru, Yaa Ubangijin sammai da ƙassai kai ne wanda kai mana Ni’ima da kowace irin kyauta, kai ne Ka saukar da wannan ruwa daga sama sabi da ƙarfin Izzarka Ya Allah, Ina roƙo gareka ka sa yadda wannan Akwati ta tafi ta tafi da dukkan IZZA da SARAUTA da JIN KAI na wannan Masarauta me cike da abubuwa da yawa, Ya Allah ka sa Tafiyarta ta kawo Alkairi a tare da ni da duk wanda Akwatin ta shafa, kuma ina roƙonka ka kare min ita da dukkan wani haɗari ko na Mutum ko na wata halittar ko da kuwa na Ruwan da Akwatin ta ke akansa ne.”

 

ta na kaiwa nan ta fara Ambaton sunan Allah cikin rintse ido numfashinta ya na ƙoƙarin barin gangar jikinta, har sai da ta kai ƙasa ba Alamar numfashi a tare da ita sannan bakinta ya dena Ambaton Allah.

 

Tsaye take a bakin Taga da ke a sama ta na kallon Mutanen da ke hidimominsu a ƙasan, Tunani me zurfi Zuciyarta ta tafi yi hakan ya sa ba ta ji shigowar Mai-Martaba ba.

“Sarauniya Ameenaa” shine abinda bakinsa ya furta cikin girmamawa.

Juyowa ta yi ta zuba masa Jaruman idanunta kafin ta ce “Salam-alaik Sarki Zunnur.” jinjina kai ya yi alamar ya Amsa. ta keɓe ta kusa da shi ta wuce cikin takunta irin na Giwar Mata.

“Da Alamun fushi akan fuskar me Babban Ɗaki” ya faɗa tare da tsirawa bayanta ido.

Cak ta tsaya kafin ta ce “Tabbas Ina cikin rashin jin daɗi kasancewar Gimbiya ba ta cikin farin ciki, ko Abinci ba ta tsayawa ta ci.”

“Ni ma ba na jin daɗin hakan, amma ba yadda za’ai da ita.

“Ya kamata ka gane Muhimmancin Amira domin kuwa a Mata ba mu da tamkarta, ka sani ita kaɗai ce Jarumar Gimbiyar da Masarautar Moomin ta Mallaka, akan me ba za ka dinga jiɓantar lamarinta ba, shin ka na mantawa ne kai ne Mahaifinta?”

“A’a, Ban taɓa mantawa ba, tuba na ke ya Ke Sarauniya Ameenaa, sai dai Gimbiya ta na da taurin kai da kuma jijji da kai, ni kuma hankalina ba ya ɗaukar wannan, ina da Izzar da zan iya sa wa a cire mata wuya idan ta kuskure min.

Cikin tsananin ɓacin rai ta ɗago hannu da nufin sharta masa Mari amma sai ta fasa sabi da tuna wani abu da ta yi.

cike da Zarra ta ce “Ba kasancewarka Sarki ce ta sa ba zan mareka ba, kai ɗin Mijina ne, Lallai ka gyara kuskurenka kafin ka yi tuntuɓe da Hukuncina.”

ta na gama faɗen haka ta ɗan ɗage Doguwar rigarta ta ci gaba da tafiya. Ya raka bayanta da ido cikin mamakin yadda akai shi ya zama Shugaban Mutane ita kuma ta zama Shugabarsa.

 

Masarautar Munwaz.

Cikin Takunsa irin na cikakkun Jaruman da su ka ga yau su ka ga Jiya kuma su ke sa ran ganin baɗin-baɗaɗa ya shigo Turakarsa wadda ta sha Adon Zinare kala-kala har da na gumaka. zabgegiyar Takobin da ke hannunsa ya ajiye a mazauninta kafin ya juya da nufin ci gaba da tafiya don hutawa.

“Rai nawa ka kashe da Takobinka a yau?”

Rubaina ce ta jefo masa tambayar bayan ta tsirawa Takobin Ido.

Kallonta ya shiga yi kafin ya kauda kai gami da cewa “Waɗanda Hukuncin kisa ya dace da su.”

“Na sani, Sarki Zamwaal ya na kiranka”

“Aikin me Hadimanki su ke yi da za ki taso da kanki?”

ta ɗan murmusa kafin ta ce “Uhmm ina son ganinka ne, kuma ka riga ka sani ba na son na ga wata mace ta doshi inda ka ke.”

Ido ya tsira mata kafin ya taka da nufin yin gaba ta yi saurin shiga gabansa tare da cewa “Wuce ni za ka yi?”

“Ina son rage yawan kayan jikina ne, kuma kinsan yanzu lokacinki gareni ki maida Saƙon kirana da Sarki ya ke yi zuwa ba zan zo ba”

murmushi ta yi kafin ta yi taku biyu cikin zallar jin kai, kamar wadda aka tilastawa yin magana ta ce “Duk matsayin lokacina bai kai na Mahaifinka ba, ka je ka ji me ya ke so gareka.”

Da ido ya amsa mata sannan ya yi hanyar fita ba tare da ya ce komai ba, ta bi bayansa ta na murmushi sabi da shaukin Sonsa da ya ke ƙara ruɗarta.

 

“Akhi”? Yarima Rooh ya kira sunan ɗan uwansa cikin sigar tambaya kamar yadda ya saba.

cike da kulawa Farin Matashin da ke kan farin Doki ya kalli Ƙanin nasa don jin abin da zai faɗa.

sanin ba amsawa zai yi da baki ba ya sa Yarima Rooh ya ci gaba da magana, “Ka ce Tsere za mu yi zuwa cikin Masarauta kuma kasan ba zan iya ba.”

Tattausan murmushi ya saki wanda ya ƙara fito da ainahin kyawunsa cikin sanyi ya buɗe fararen haƙoransa ya yi magana fuskarsa ɗauke da murmushi “Akhi Rooh ko ba za ka iya ba sai ka yi, daga bakin wancan Tafkin za mu fara”

Yarima Rooh ya zaro ido a tsorace ya ce “Kasan dai Dokin nan ban iya sarrafa shi sosai ba tin da ba nawa bane, ka bari mu je gida sai mu dawo”

“Zan baka wannan”

“A’a gaskiya ai Dokin Jarumi sai Jarumi kawai dai mu tafi a hankalin”

tsayawa ya yi cak kafin ya dire daga kan dokin cikin maganarsa me ɗauke da izza ya ce “za ka karɓa ne ? ” kamar zai yi kuka ya ce “Irin halinka dokin nan gareshi akwai gardama da kafewa akan ra’ayi ɗaya don haka gwara wannan ɗin, amma da sharaɗi, ni zan fara yin gaba sai na yi nisa sai ka tawo”

Yarima Salaah bai ce komai ba sai ci gaba da shafa Dokinsa da ya yi.

Yarima Rooh ya sauke ajiyar Zuciya kafin ya gyara zamansa ya tattaro duka Jarumtarsa sannan ya ce “Akhi sai mun haɗu a Turakar Sarki ” da murmushi kawai Yarima ya bi shi don kuwa ya san halin kayansa.

Sai da ya yi nisan da ba ya iya hango shi sannan ya koma kan Dokin nasa cikin ƙwarewa ya ɗau hanya.

A matuƙar Gajiye Yarima Rooh ya isa Cikin Masarauta ya haɗa gumi ga wata muguwar ƙishirruwa da ya ke ji sai Numfarfashi ya ke yi.

Ya na sauka daga kan Dokin ya ji an cafki Dokin gami da yi masa magana. Zaro idanu ya yi kamar za su faɗo ƙasa cikin disasshiyar murya ya ce “Akhi! wai shin kai Aljani ne?”

Girgiza kai Yarima ya yi alamar a’a

kamar Yarima Roooh zai yi kuka ya ce “kuma na ga ka rigani Zuwa har ka huta kuma na ga kai ba ka gaji ba, kullum fa haka mu ke ni dai ba na taɓa yin Nasara, shi ya sa Ummi Ba ta sona ta fi Sonka”

riƙo hannunsa ya yi cike da kulawa ya ce “Ba wai ta na ƙin ka bane, a koda yaushe Muradinta ka zama Jarumi har ka fi ni Jarumta, ranar da ta ga hakan nasan za ka ga gata kala-kala a gurinta , nima ba wai finka Nasara ko wani abu na yi ba, ka dage ka zama Jarumi kawai , Gobe In sha Allah zan fita Farauta nasan za ka bi ni, ina so ka bani Mamaki.”

Ƙasa ya yi da kai baya son sare masa guiwa don haka bai musa ba, cikin sanyi ya ce “Akhi! me ya sa naga Kai Ummi ta fi sonka Abhi kuma ya fi sona duk da cewar kai Jarumi ne?”

Shafa kansa ya yi cikin sigar tausasawa ya ce “Akhi Roohh , kar ka tsawaita tambaya akan hakan, Duniya ma ta shaida akwai bambance-bambance na ra’ayi tsakanina da shi, tayuwu hakan ne ya sa kake ganin kamar ba ya sona, kamar yadda Ummi ba ta son ragontarka haka shima akwai abin da ba ya so daga gareni, sai dai ni kuma kaifi Ɗaya ne .”

 

 

 

Paid Book ne

 

Book 1 VIP 300 NOMARL 250 Idan Kati ne 300.

 

Book 2 VIP 300 Nomarl 250 Kati 300.

 

COMPLETE 1-2 500

 

Don ƙarin bayani 09079885632

 

 

Ayeesha Abdulkareem

*A.A*

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment