Littafan Hausa Novels

Idan Ba So Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Idan Ba So Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

IDAN BA SO

 

*NA*

~AYEESHERT KAY~

 

 

 

 

_Gargadi banyarda wata ta sauyamin labari ba ta ko wacce siga ba tare da izini na ba in kunne yaji gangar jiki ta tsira_

 

꧁BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM꧂

 

£p1

 

 

DUBAI

Jumeairah is the one of the most richest estate in Dubai,wani building ne wanda duk cikin estate din yafi ko wanne kyau da tsaruwa kai kace nan ne masarautar sheikh Mohammed ibn rashid wato sarkin birnin Dubai tsayawa fadan tsaruwan gidan ma bata lokaci ne cikin garden din gidan ne wata kyakyawar mace wacce shekarun ta bazai gaza ashirin da biyar ba tana da dan jiki fara ce kana ganin ta ka ga jinin Larabawa waya take cikin harshen Larabci hadi da turanci da take saka wa ji fa jifa

 

“Am so excited girlie anyi fixing din date dina da *Ahzan* can’t even tell you how happy am i right now promise me that you will attend my wedding please bestie!!”

 

Daga cen bangaran ne wacce take waya da ita ta ce

 

“OMG babe am so happy for you Sai ki bari mu miki murnar ai amma yanda kika san auran aka daura muku wow congrat my love insha Allah zanzo ko da school sai na zo I promise you that hh but baki fadamin date din ba?”

Akanshi Hausa Novel Complete

Ware madaidaitan idanunta tayi tana kallan wayan kamar mai rad’a ta gyara airpod din kunnan ta tana fadin”next month girlie buh gani nake yayi nisa da yawa!”

 

“Huh! Next month soon ohright Allah ya kaimu can’t wait let chat dear zan shiga leacture”

 

“Ok bye!!!!”

 

“Aunty *Layla* kina nan I have been looking for you since dama nanny tace bazai wuce kina garden ba”

 

Wacce aka kira da Layla ta yatsine fuska kana tace”yeah ina nan maiyafaru kike nai mana?”

 

“Haba aunty kinfa kusa tafiya ki barni kuma haryanzu baki daina min wan nan halin naki ba atleast be nice before you leave”

 

Layla ta tashi tana fad’in”ok ma’am i will try dama nasan baki da abin fada yanzu haka wani gulmar ce ta kawo ki”

 

Tana gama fad’in haka ta wuce.

 

DINNER

Zaune suke kan katafaran daining table din suna cin abinci Alhaji Farish ibn rashid yayi gyaran murya kana ya ce”princesses na baki babban company dina da yake africa wato golden star da zaman da zaki ringa yi a gida kinga saiki ringa zuwa the rest of the company’s sai ya zama kina handling din su”

 

Langwabar da kai tayi kamar wata yarinya karama ta ce”you don’t have to do that Abbie”

 

“I have to! My dear”

Ya fada yana kora wine din hannunsa ameesha ce tace”awwn see love am so happy for you again”ta fad’a tana kada spoon dinta saman glasse cup din dake gabanta murmushi Layla tayi kana tace

“Well thanks for that first love”

 

“You are welcome”

Baban nasu ya fada yana cin abincin sa Layla ta ajiye spoon din tana motsi da bakin ta kana ta ce

 

“Ameesha abbie i want my weeding to be loud to be the most talkative weddings ever i want everything to be classics and expensive huh!….”

 

“Even more than that princesses”

 

“Hhh thanks abbie Ameesha you should call pinnacle couture ina bukatan ganin su dan sumin selecting kayan da zansa and jewels”

 

“You don’t have to stress your self ma’am i will handle it”

 

Wata baturiya da take tsaye a gefe ta fad’a Layla ta kalle ta kana tace”ouh yes you!”.

 

Nigeria

White house_president

“Habib aje akai abinci gidan marayu duk almajirin da kuka gani a hanya wala babba wala karami a bashi dubu biyu,yau ranar murna ce addua ta ta karbu *Ahzan* zai yi aure zai auri irin wacce nake so yar babban gida”

 

Hajia Ramlat ce zaune a parlourn ta take maganar cike da farin ciki dauke akan fuskarta

 

“Ah lallai abin nayi ne har za a ciyar da talakawa da marayu ko tun yaushe mutanan suke kwana da yunwa baku basu ba sai yanzu da kike cikin farin ciki ko danki zai auri yar balarabiya yar masu kudi da mulki to bama lada zaki samu ba danma kiji da kyau”

 

Hajia babba ce take magana wacce ta shigo parlourn wato sirikar hajia ramlatu

 

“Kilama ke kika tilasa mai dan banga yana rawar kai a auran ba farin cikin nan ma da sabon ango yake bangan shi a tattarre dashi ba dan fuskarshi kamar kullum haka take har yanzu ba fara’a uwa na shanu,yarinya ta makyale mai kema kinga daula kin na ce ki bari dan mutane ya auri mace wacce ta kai mace zaa bashi mai kirar maza,ah to mai kirar maza mana tunda ni dai banganta da suffar wata babbar mace ba a tattarre da ita!”

 

Hajia Ramlat ta hade rai kana tace”hajia naga shi ya kawo zancen yarinyar nan na goyamai baya bafa ni na kawo mai ita ba nace ya aura”

 

“Ke dalla cen rufemin baki mai za ayi ga wanda yarinya zubar da mutumcin ta tayi fa tace tana son shi amma ina Ahzan ina tambadaddiyar yarinyar nan tir wallahi ko kun aura mai ita sai na auramai wacce ta fita ehhe”

 

Hajia babba ta fice daga parlourn ba tare da ta jira cewar Ramlat ba ta tafi tana mitar ta hajia ramlat ta tabe baki ta bita da harara”basai kiyi ba ai daga *Layla* kofa ta rufe wallahi yanda ubansa bashi da raayin auran mata fiye da d’aya shima haka nashi ra ayin yake auran Layla ne dai ba bashi mu zuba da ku shege ka fasa har akwai ma wacce ta isa ta hana wan nan abun arzikin ai duk girman kogi yana bukatan d…..”

 

Bata k’arasa ba afusace taja uban salati ta tashi part din kusa da ita ta nufa tana zuwa ta banka kofar hayakin parlourn da warin ya daki hancinta ta yatsine fuska da sauri ta shiga dakin ta banko kofar cikin masifa ta fara magana

 

“Afreen mai kike so ki zama ne kina so ki zama dani uwar banza ce a gidan nan ko mai kinfi kowa sanin halin hajia babba basai na fada miki ba kuma ba sai ba tuna miki yanzu ta dawo gidan nan da zama bane taya zaki ringa shaye shaye a parlour bama a bandakin ki ba yanzu da badan ni naji ba ya kike gani in wanine acikin gidan nan yaji to maza wallahi ki tashi ki kwashe kayan tsiya dinnan ki saka Roomfreashner”

 

Afreen da take kwance akan rog ta bude gajiyayyun idanunta tana kallan hajia Ramlat cikin muryar maye ta ce,”mumcy bross Ahzan ya dawo ne?”

 

“Eh ya dawo dan ubanki zaki tashi ko saina rotsa miki kwalbar lemun nan”

 

A firgice ta tashi zaune tana zare idanu”na shiga uku mumcy ya dawo shine baki aiko an fad’a min ba kina jin warin weed?allah yasa bai jiba”

 

“Kaji yar banza wato shi kike tsoro bama ubanki ba kinsan Allah duk lokacin da suka san kina wan nan badalar hum sorry for your self karma ki ambaci sunana a ciki dan wallahi sai na Batam da ke”

 

Afreen taja guntun tsaki ta tafi luuuu ta koma ta kwanta murya kasa kasa tace”plz leave me alone ki kira maid ta gyara i can’t do anything right now dama nasan ai he is not back yet”

 

“Yarinyar nan fa bata da hankali wallahi bari na kira zuwai ta gyara dan na kara minti biyu anan amai zanyi……”

 

Area madalla_

“Boka so nake duk abinda za ayi kar ayi auran nan!”

 

Boka ya gyara zamansa ya watsa dutsunan hannunsa akan wata jar‘kyalle kana yace”auran nan fa ba fashi sai an yi shi sai dai ki fadi wata buk’atar”

 

“To shikenan tunda abin yazo da haka kayi min abinda ko anyi auran ba zaman lafiya ka cusa mai son yasmeen ko ta yayane itama ya aure ta! dan ni yanzu burina kawai Ahzan ya auri yasmeen”

 

“Baki da matsalar wan nan sai dai abubuwan da muke bukata zaki kawo”

 

“Boka ni bazan iya wan nan siye siyan ba zandai baka kudi kayi abinda ya dace”

 

Washe gagayen hakoran sa tayi yace,”kudin ba ai zasu karba miliyan daya ta isa nan da bayan bikin ki dawo zan baki wasu magunguna da zata yi amfani dashi”

 

Makudan kudin dake jakarta ta fito dashi ta zube mai tana fad’in”To shikenan Allah ya kaimu”

 

Wani tsawa ya daka mata wanda yasa hantar cikin nata kadawa “karki kuma kira mana Allah anan indai kina son aikin ki ya tafi yacce kike so”

 

Da sauri cikin rawar murya ta tashi tana fad’in”amin afuwa to bazan kuma ba”.

 

Bayan ta koma gida ta tarar da yasmeen a parlour tana faman kuka tsaki tayi ta wurgar da jakarta jefe tana fadin”auu kuka kike yi bana ce ki daina kukan nan ba indai Ahzan ne zaki aure sa meye naki na daga hankalin ki kina zubar da hawayen ki a banza”

 

Cikin fushi yasmeen ta ce,”mai yasa bazan yi kuka ba mama kinsan yanda nake son shi wallahi indai har ban aure shiba bazan iya auran wani ba haka zan mutu banyi aure ba!”

 

“Ai kuwa sai dai ki mutu babu auran banza mara kamun kai shashasha wacce bata san mai take yi ba bata son mutumcin kanta ba”

 

“Wai dama kana cikin gidan nan take wan nan kukan meye kuma na zagin ta tunda dai ba lanlashinta zaka yi ba”

 

“Wallahi suwaiba kika kuma fadamin maganar da bata gamshe ni ba sai ranki ya b’aci kwadayayyu ke zaki kai arki ga halaka wallahi tunda baki da hankali ku ci gaba kema ki ci gaba da son ma so wani inba lalacewa ba har ki tsaya gaban uwarki kina ce mata wani in bashi baza ki iya rayuwa ba tarbiyya kenan banda lalacewa da iskanci mu zuba ni da ku acikin gidan nan”…

 

Yana gama fad’in haka ya fice daga gidan suwaiba ta bishi da kallo dogon tsaki ta ja ta karasa wajen yasmeen wacce kukan nata ya koma ciki ciki ta ce,”haba yar autata ki share hawayenki karki biye maganar ubanki kinsan dai halinshi kinsan yanda yake bari kiji naje wajen boka na zubamai makudan kudi da zai mana aiki yace auranki da Ahzan ba fashi sai kin shiga gidan nan”

 

Cikin shagwaba tace,”To mama auran sa da mayyar balarabiyar nan fa?”

 

Dan Jim tayi kana tace”yasmeen ko ya auri layla fa bashine zaisa yaki auran ki ba”

 

Fashewa da kuka tayi kana tace,”sai anyi auran kenan ashe momcy ramlat ba so na take ba!”

 

“Haba haba auta ko kowa yace haka ai baza ki yarda ba karki manta ramlat fa yayata ce uwar mu daya uba kowa da nashi amma inba na fada ba waye yasan ma ba uban mu d’aya ba kiga fa itama yacce ta so auranki da Ahzan shigowar yar iskar yarinyar nan ce duk ya jagula lissafi,amma Nace ki kwantar da hankalin ki zafa ki aure shi kisa ranki cikin ruwan sanyi karki je ki rame a zo aurar akai ki jiki duk k’ashi”

 

“Naji”ta fad’a a takaice tana turo baki ta tashi ta shige dakin ta tabar hajia suwaiba zaune a parlourn.

Wan nan kenan

 

White house_

Tv gabanshi yake kallo kafin ya ja tsaki ya kalli wanda yake kusa dashi cikin b’acin rai yake magana

 

“Ya akayi haka Vice President 1week kawai nayi a dubai amma har mutane sun fara korafi yaushe har mai ya hau haka am not aware of it how comes?”

 

Vice President ya numfasa kana yace”well kasan yacce abubuwa suke dole petroleum shima ya tashi”

 

“As in nasan yanda abu yake my dear i don’t care dole fah mu kyautatawa mutane meye amfanin mulkin namu in har mu baza muyi adalci ba baza mu kyautata musu ba sai dai mu miji dadi kenan su suna cen suna shan wuya?”

 

“Ba haka bane I was thinking tun acen ka sani saboda hajia tace zata sanarma da komai kar a bari ka sani harsai ka dawo kuma billion Dayan da kake magana da aka cire a public bank ita ta cira akan za tayi amfani dashi”

 

“What!!? Billion daya bama a bank dinta ba ko na gida To tayi mai dashi? A month din nan a kalla ta kashe 4billion mai take dasu ina take kaiwa?”

 

Vice President ya daga kafada akan bai sani ba

 

“Shikenan you can leave ka sanar gobe da safe akwai meeting banason ganin dan jarida daya har sai anyi settling din issue din nan”

 

“Ok his excellency na barka lafiya”

 

Ya fad’a cikin girmamawa baifi minti uku da barinsa wajen ba hajia ramlat ta shigo sai kamshi take zubawa kamar anan kamfanin turaran yake sallama ta yi ta naimi wuri ta zauna a kusa da kujerar da yake

 

“Sannu da hutawa my excellency naga Vice President yazo da fatan komai lafiya”

 

Yana rike da kanshi wanda ya saramai tun shigowarta fuskarsa a tamke ya ce

 

“Ramlat wan nan turaran naki nace ki daina sa shi yaci ka karfi yanxu haka kaina ciwo yake,ramlat mai kikayi da kudi har billion hudu ga maganar tashin…”

 

Rik’e mai hannu tayi tana murzawa cikin kissa ta ce”haba masoyina dan kawai na yi amfani da billion hudu shine zaka daga hankalin ka uzurin gaba na nayi dashi fa!”

 

Rasa gane kansa yayi da k’yar ya iya cewa”kaini daki ramla am feeling dizzy”.

 

Wani guntun murmushi tayi mai dauke da ma’anoni da yawa ta bishi da harara azuciyarta tace

 

”ni ce maganin ka zaka bi ka dagawa mutane hankali baka da aiki sai maganan hakkin talakawa mu zuba mu gani ni da kai da waccen munafukar uwarta ka!”.

 

Washe gari

Breakfast

Suna zaune gaba dayan su suna cin abinci akan daining table *Ahzan* ya fito daga shashin sa sai daya k’araso inda suke zaune ya gaishe da ko wanne daga cikin su afreen tace

 

“Ina kwana bross”

 

Bai amsa ba yace”amm zan wuce office!”

 

Afreen ta tabe baki azuciyarta tace”karka amsa mutum sai shegen miskilanci”

 

Hajia babba ta ce,”auu abincin ma baza ka ci ba ko da yake Ina kaga ta cin abinci zaa maka auran dole ni wan nan abu ai ni aka cuta iyyee”

 

Alhaji suhail ya kalli Ahzan kana yace,”Ahzan mai hajia take cewa auran dole dama za’a maka ba kai bane kace a tura a nai mar maka auran Layla?”

 

Hajia babba ta yi mistimisti da idanu ta ce,”kaii Ahzanu kaji tsoran Allah ka fadi gaskia karka cuci kanka inaji yarinyar nan ita tace tana sonka ta makyale ma?”

 

Ahzan daya kurawa hajia babba idanu cikin cool voice dinsa ya ce

 

“Hajia yaushe muka yi haka dake?ta ya zaki ringa cewa bana so bayan nina kawo ya da kaina nace kuma aje a nai ma min auranta”

 

Mumcy na jin haka ta sauke ajiyar zuciyata hajia babba ta tabe baki kana ta ce

 

“Kaji karyar banza ai ni daga yanayin mutum ma nake gane shi tunda ka biyewa son zuciya irin na uwar ka ai shikenan”

 

A hankali Alhaji suhail ya tashi “major bari mu fita tare i have a meeting also”.

 

Wan nan kenan.

 

 

 

_in naga ruwan sharhi kuma zaku ga next Page da wuri_🤸🏻‍♀️

 

 

~Comments and share plz~

 

09126276630 kay…✍🏻

[08/12, 6:03 am] +234 912 627 6630: ☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

 

*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*

 

IDAN BA SO

 

*NA*

~AYEESHERT KAY~

༺(っ◔◡◔)っ༻

 

 

 

 

꧁BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM꧂

 

 

£p2

 

 

____________Kano,bakar mota ce mai kiran Range Rover ta yi parking a gaban wani matsakaicin gida wanda kana ganin ginin ka san irin na da ne dan gidan ya tsufa duk ginin ya fara tsagewa tsabar dadewa da rashin samun gyara

Bud’e murfin motar ta yi ta zuro da fararan kafafunta waje tafi minti uku a haka da alama magana ta ke da mai tukin motar tana gama wa ta fito rik’e da leda har biyu a hannunta “sai da safe take care” abinda ta fad’a kenan kafin ta k’arasa kofar gidan ta tura kofar kwanan da ya kusa cire wa shima ba tare da tayi sallama ba ta shiga cikin gidan kai tsaye tana waka tana danna wayarta mai kiran 13promax d’aga labulan d’akin ta yi ta na haska wa da wayan ta kana tace

 

“*Sulty! Sulty!!!* am back home baby hope ba dai bacci kika yi ba!”

 

Da sauri ta karasa cikin dakin inda ta kira Sulty din tana kwance tana rawar sanyi ta takure a waje d’aya cikin firgici da nuna damuwa tsanta akan fuskar ta ta talla fo yarinyar tana shafa jikin ta

 

*Sultana* are you sick baki da lafiya ne mai ya same ki ooh my God tashi mu tafi hospital”

 

Sultana da tak’e k’okarin raba jikin ta da na ta amma ta kasa ta bud’e idanun ta da suka mata nauyi tana kallan ta cikin dashashiyar tsiririyar murya ta ta ce

“Ni bazan je ba am fine ba abinda yake damuwa ki kyale ni bacci nake ji i have school tomorrow!”

 

“Are you serious? Ni kike wa magana haka harda wani na k’yale ki my friend u are not ok tashi mu tafi kinga time na tafiya karmu rasa abin hawa”

 

Cikin muryar kuka Sultana ta ce”so kike a kama mu wani abin hawa zaki samu by this time it’s late already karfe 12:51 rashin lafiya ta bai wuce damuwar ki ba ce Aunty Ummita banason daran nan da kike kaiwa mutanan unguwan nan na zagin mu inna fita ai tamin habaici har da masu kira na karuwa k’anwar karuwa masu zaman daduro!”

 

Ya fad’a cike da tausayi har hawaye na gangaro mata akan farar kuncin ta Ummita ta tab’e baki ta ce

“Karki bari yanzun nan na hau ruwan cikin ki Sulty wai nawa ki ke mai kika sani a rayuwar duniya ke ki bar mutum ko kayi zagin ka zai yi hakama in baka yi ba zaginne zai biyo baya ballan tana nasan suna ganin mu ni da ke kawai a cikin gida ai sai abinda muka gani muka ji sai dai mu toshe kunnuwan mu na ce ki daina sa wan nan acikin ranki Sulty i want you to studie to have a good health and life in ban fita na samo ba waye zai samu kinsan dai bazan tab’a yin abinda ba shikenan ba dont you trust your sister ko ke ma kallar yar iskar ki ke min?”

 

“God forbid Aunty duk da nasan kina da male friends da yawa ban tab’a miki kallan haka ba saboda nasan you will never do that but kinsan ko yane in an fada maka irin wan nan dole kaji ba dad’i kuma kinsan yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba”

 

“Hhhhm wow nice one mutum ake kiwo ba dabba ba Sulty Ina kika samo wan nan Karin maganar lallai kin girma”

 

“A makaranta mana dama ke kike kallo na as a baby but shekara na 17 fa kinga ai na girma”

 

“For me you are still a baby my princess ok yanzu ki daina sa wani abu a ranki soon zamu siyar da gidan nan mu kama wani a unguwar da babu mutane babu sa ido kinji!”

 

Cikin farin ciki Sulty ta ce”Masha Allah dagaske can’t wait Aunty Ummita”

 

Ta fada ta na mai rungume ta “yeah insha Allah yanzu bari na samo miki magani amma before than sai kin fara cin abinci tukun”

 

Fara bud’e ledojin ta yi inda ta fito mata da takeaway daya ta bud’e chips ne da gashashen kifi with onion sauces sai dayar ledar da take dauke da katon kashashan kaza sai ledar yoghurt da drinks ta tura mata gaban ta tana fad’in

 

“Maza kici rabi kafin na dawo bari na shiga toilet”.

 

Washe gari…..

Oxford Academy ss1 class ajin sai surutu suke saka makon free class da suke dashi,Sultana tana zaune a class kanta akan desk din dake gaban ta tana wasa da bairo din hannun ta fuskarta dauke da damuwa jifa-jifa tana kallon yarinyar da kujerar ta yake kusa da nata caraf suka hada ido Marwa tayi guntun murmushi lokacin data taso ta dawo kujerar da Sultana ke zaune cikin rawar murya kamar wacce ta ke son yin kuka Sultana ta ce

“Mai yasa kika daina kulani kika daina min magana kika daina biyo min school da islamiyya mai na miki?”

Marwa ta dafe kai tana fad’in”please ki rufamin asiri karki min kuka a dauka wani abinne ni had’ina dake kenan wallahi saurin kuka ba fah laifi na bane yayana ne ya ce na daina kulaki saboda wai ‘yan unguwa na zagin ku da karuwar ‘yan zaman daduro…”

“Ke kinga hakanne Marwa Ina tunanin ko kowa zai mana zagin nan zai yarda banda ke tunda kinsan ni na fad’a miki rayuwar mu iya wanda na sani dama mutane kuma baa raba su da gulma sharri k’azafi kala kala in kana rayuwa ba abinda baza ka gani ba!”.

 

“Well Sulty the problem is not from you daga sis Ummita ce ita ce ke ja miki zagi ke lalata muku suna wan nan fitan da ta ke tana barin ki ke kadai ta wuni sai cen dare ta dawo dole a zarge ta ki ga fa mutane daban daban ne suke mai do ta gida acikin manyan mota kala kala….”

 

Da sauri cikin b’acin rai Sultana ta d’aga mata hannu tana fad’in

“Hey hold it please!! Ouh kuma zargin na ta kuke kenan dan tana fita tana dadewa ana kawo ta a mota hakan na nufin iskanci kenan ta ke tafiya yi Marwa kinsan ni kinsan halina in ina abun da bai dace ba kin sani Marwa kuma kowa da irin kaddarar sa mai yasa baza abi mutum da addu’a ba sai dai ai ta gossiping akan mutum!”

 

“Sultana karki min wata fahimta mai yasa kike son ke ma ki danne gaskia bayanis kinsan komai”

Da sauri sultana ta matsa gab da ita ta dauke kanta daga gare ta tana kallan window”mu bar wan nan maganar ki bi maganar yayan ki is almost time for test ki koma sit dinki kafin su shigo”

 

Cikin sanyin jiki da rashin jin dad’in abinda ya faru tsakanin su ta ce”owk am sorry”ta fad’a yayin da ta tashi ta koma wajen ta da zama

 

Bayan tashin su makaranta Sultana ko tsaya Marwa bata yi ba kamar yacce suka Saba tafiya tare da yake unguwar su d’aya napep ta tara ta wuce gida,bayan dawowa ta gida ta tarar Ummita na shirin fita

“Yauwa Sulty dama ke nake jira am about to go out sannun ku da zuwa how was the test”

Fashewa da matsanan cin kuka Sultana ta yi ta zub’e a fashashen sumintin gidan cikin kuka ta ke magana

“Ummita ni fa banson fitan ki haka kullum sai kin fita ne na gajia da surutun da unguwan nan suke yi in ke baya damun ki ni wallahi ya na damuna kawai mu bar unguwar nan mu koma wacce ba mutane ko kimin aure ko na huta!”

 

Ummita bin ta tayi da kallo kamar wata doluwa ta tafa hannun ta biyu tana salati”na shiga uku ni Ummie wai yaushe kika zama mara kunya hakane nawa kike harda zan miki aure kina ma da bakin maganar aure do you know anything about it ne?ko da yake kin shiga ss ai dole ki sani wajen friends,dan uban ki in ban fita na samo ba da mai zamu ringa cin abinci school fees dinki waye zai biya ko kinfi so in an koroki ki zauna a gida kina tak’umi da karkata kai aiki fa nake zuwa sultana ba wata uwar ba! Kuma nace ki bari inna samu yanda nake so an samu wanda zai siya gidan zamu tashi daga gidan”.

 

“Har zuwa yaushe Aunty?baza su tab’a gane aiki kike zuwa ba promise me that zaki ringa dawowa da wuri please!!! Sister”

“Kinga tashi kije kiyi wanka kici abinci fitan ma yau na fasa tare zamu wuni a gida muna hira hope that will make you happy tashi tashi”

 

Ta fad’a tana taso ta ranar duk wani damuwa na Sultana sai da Ummita ta mai da shi farin ciki saboda a kwai kauna sosai tsakanin ‘yan uwan biyu.

 

After 1month and 3weeks

DUBAI

Hayaniya ne ke tashi daga bakin gate din wasu ‘yan aikin gidan suna daga gefe suna tattauna abinda ya faru cikin harshen turanci”Miss Layla bata kyauta ba ace kina soyayya da mutum har na tsawan shekara uku dan kin samu wani sai ki kyale waccen”

 

D’ayar ta ce,”yaudara kenan tsantsa ko dan irin masifan son da yake mata ai bai kama ta ace ta rabu dashi ba just like that gashi wanda zata aura dinma ance wulakanci yake mata ba wani son ta yake ba!”

 

“Kaii Angela a ina kika ji wan nan zance”

 

Angela ta tab’e baki kana ta ce,”ranan da nake gyara parlour naji suna maganar da Miss Ameesha”

 

Muryar Layla da suka ji shiya sa ko wannan su saurin barin wajen

“Who the hell is he harda zai zo mana bakin gate yana haushi kaman kare kuma kuna kallan sa baku yi magananin sa ba ko an gaya mai gidan zoo ne nan”

 

Ta k’arasa wajen gate din ta lek’a tana kallan shi cike da ban tausayi ya had’a hannayen sa yana fad’in”please Layla habibty kiyi hakuri ki fadamin abinda na miki Kika min haka wallahi i still love you karki bari duk abinda da muka yi planing ya tafi a haka all the memories try to remember Layla duk time din da muka d’iba years haba Layla please come back I need you!”

 

“Heeys please na maka kala da wacce in tabar abu tana dawo wa taya ma za a ce zan bar Ahzan na dawo gare ka do you know who’s Ahzan ka tab’a ganin sa kuwa bansan ma at the first place wani tsautsayinne yasa na fara soyayya da kai just look at your self huh disgusting dama ance so makaho to shine ya rufe min idanun nawa a farko da bansan da wa nake soyayya ba amma daga baya na sani so please ka bar kofar gidan nan kafin na sa guards su maka koran kare”

 

Hawaye ne sosai yake zuba a idanunsa kamar wani k’aramin yaro yayi guntun murmushi na ta kaici kana ya ce”well tunda haka kika ce naji zan rabu dake haka Allah ya baku zaman lafiya ya bani wacce ta fiki”

“U must be sick Zaid harda kake tunanin za ka samu wacce ta fini never and ever and hakurin da tun farko ka bawa kanka da ya fiye ma dan ko a mafarki bazan tab’a dawo maka ba ballan ta na a gaske hey gate man close the gate my party is about to start ko shirya wa banyi ba zai b’atamin lokaci”….

 

Cikin sanyin jiki da takaici had’i da b’acin rai zaid ya bar wajen ranar ba karamin kuka yayi ba dan bai tab’a tunanin haka daga Layla ba duk irin soyayyar da suka sha ba wanda bai son tarihin soyayyar su ba!”.

 

Ta kai taccen barin su Layla__

Alhaji Farish ibn rashid babban attajiri ne yana da kudin da shi kansa baisan iya adadin sa ba yana zaune ne a k’asar DUBAI ya yi auran sa na farko inda ya auri yar turkey hasiya shekaran su biyu ta rasu wajen haihuwa

Ya dau 1year kafin ya auri Layla yar sarkin Dubai auran soyayya suka yi bayan sun d’au shekaru wajen hudu san nan Layla ta yarda ta samu ciki saboda ba ya da ra’ayin haihuwa da wuri bata da kuma son yara sosai ta samu cikin ta na farko na miji tun yana garirin yace ga garin kunan saboda rashin nonon da bai samu ba acewar ta sai dai a bashi madara ita baza ta iya bada nono ba dan bata so su lalace da wuri ran Farish ba k’aramin so suwa yayi ba yayi kuma kamar ransa zai fita amma saboda tsananin son da yake mata haka ya hak’ura ta d’au 2years kafin ta samu cikin Layla wanda ya bata wuya sosai harsai da ta kusa zubar dashi dakyar da lallashi ta yarda ta barshi bayan haihuwar na tane Farish ya sa mata sunan Layla shiyasa yake kiranta da princess

Ba k’aramin gata suka nuna mata ba ballan tana Alhaji Farish wanda ya d’au son duniya ya d’aura mata baya son yaji laifin ta ko da a makaranta ne aka bata mata rai to aranar zaije ya musu rashin mutumci kuma a cire ta daga makarantar tana da shekara biyar ta samu cikin Ameesha wanda hakan ba k’aramin d’agawa Layla hakanli yayi ba acewar ta daga Layla baza ta kuma haihuwa ba shima haka aka sha fama da ita har hawan jini mai karfi ya kama ta wanda yasa duk ta kumbure ta dawo wata kala bayan ta haifi Ameesha ne tace ya garin ku nan

Alhaji a Farish shi yai ta kula da yaransa da taimakon nanny’s din daya d’auko musu ba tare da ya kaisu wani wajen dangi ba kuma bai yarda ya k’ara aure ba’Layla ta samu karatu kamar yacce uban yake so yanzu haka tayi degree dinta zata tafi na gaba tun kafin ta fara school suke ta re da Zaid wanda suka nuna wa juna tsantsar soyayya sun kusa maganar aure wani business ya kai ta paris anan ne suka hadu da Ahzan ta makyale mai harta bayyana mai tana son shi Layla kyakyawar macece wacce ba wanda zai samu yaki karba bayan haka ne ta fara yiwa Zaid rashin mutumci har ta yaki ce shi!”.

Wan nan kenan

 

Bayan Aure

Anyi biki na gani na fada dan duk wani mahaluki da yake duniya yasan anyi auran *Ahzan Suhail Mohammad* da *Layla Farish ibn rashid* kudi yayi kuka kamar yayi magana,tsayawa ma fad’an abubuwan da ya waka na a bikin b’ata lokaci ne

“In Banda iskanci a kawo amarya jiya dadaddare a kasa kawo ta wajen kakar miji ahh lallai iskancin na ku ya kai Ramlatu kin nuna min ni ba kowa bace a gidan nan ko kece banza wallahi”

 

Hajia babba ce a babban parlour ta ke faman masifa yar aikin ta ne da take biye da ita ta ce,”ki kwantar da hankalin ki hajia zauna kafin su fito!”

Tana gama k’ara she maganar sai ga mumcy da alhaji sun fito

 

“Hajia lafiya kike hayaniya da sassafan nan?”

Alhaji ya fada yayin da yake kokarin zama kan kujera tsuke fuska tayi tana ka banka wa mumcy harara wacce ta ke gaishe ta

 

“Ina kwana hajia ya gajiya?”

 

A fusace hajia ta ce”da ban kwana lafiya ba zaki ganni haka gajiya kuma wan nan sai dai na tambaye ki kai kuma da kake tambaya haka nace yan kaiwa matar gidan amarya da yake ta fini mutumci ko shiyasa ba’a kawo ta waje na ba ta kwashi gaisuwa”

Mumcy taja dogon tsaki a ranta a fili kuma ta ce”hajia nima bata zo wajen na wa ba….”

 

“Daka ta bada ke nake ba uwar iyya Ina jinka!”

Ya sauke ajiyar zuciya kana ya ce,”hajia sai fa karfe dayan dare suka iso shiyasa nace su bari gobe sai tazo ta gaishe mu da safe a parlourn ki sai a musu dan fad’an da za a mata,”

 

“Ah to ni dai nace dan ya kamata yanzun ma yaci ace sun zo ai”

 

Afreen da ta shigo tace,”kawarta ta suka zo tace bata tashi daga bacci ba yanzu na fito daga part din!”

 

“Bata tashi ba karfe goman ah lallai kika bibiya ma bata yi sallan asuba ba ke naji kince k’awa ba manya bane zasu kawo mata ko na su tsarin kenan?”

 

“Nasu tsarin kenan hajia”

Afreen ta fad’a tana zama a two sitter da hajia ta ke zaune hajia ta jinjina kai kana ta ce,”ah Lallai Allah yasa dai ba muna musulmai bane kar tazo ta ringa nuna mana halin yahuda wa Ina Ahzan din yayi ko shi ma bai tashin ba?

Alhaji ya ce,”ai ya fita suna da yaro yau tun 8 ya fice daga gidan”.

Ok”

 

Wajen 12 Layla da babbar kawarta da suka zo wato bilkisu suka je gaishe su ba yabo ba fallasa hajia babba ta karb’e su suka mata fad’an da zasu mata

Bayan sun koma d’aki Layla ta yi saurin cire hijabin jikin ta tana mai da numfashi”huh gaskia daga yau bazan kuma sa hijab babba ba is not easy”

 

Bilkisu ta kwashe da dariya ta na fad’in”aikuwa ki d’au damara da dressing dinsu dan ma babban gida kika zo ko Ina ac ne”

 

Layla ta tab’e baki tana fad’in”chab kinsan bazan d’orawa kaina abinda bazan iya ba”

 

Bilkisu ta gyara zaman ta tana fad’in”babe howfar kina tunanin anya major ba zai gane disvirgin ce ke ba”

Da sauri Layla ta kalle ta ta ce”as in disvirgin sau d’aya fa muka tab’a s** da Zaid kuma it been almost 3years now am normal kuma taya ma zai gane in dai dama ba d’an iskan ba ne shima!”

 

“Hhh you are so funny Layla Major din kike cewa dan iska yeah gaskia bazai gane ba tunda sau d’aya ne kuma an jima”

 

“Hum can’t wait to see him tonight!!!”Layla ta fad’a tana farin da idanu bilkisu ta ce,”kinsan night flight ne da ni zaki bani labari a wata tomorrow morning!”

“Dama in ban baki labari ba wa zan bawa karki samu damuwa”.

 

 

 

 

 

*more comments more typing….*✍🏻

 

Share fisabillah🙏🏻

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment