Littafan Hausa Novels

Ibtissam Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Ibtissam Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

IBTISSAM

( A heart touching story of love and destiny)

 

Story & written

By

Mss Lee

 

 

Littafin IBTISSAM is now 300 , me bu’katar ya karanta littafin har ‘karshe zai iya biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha umar, sai a turo da shaidar biya ta wannan number 07041879581.

 

MARUBUCIYAR * Gidan Aunty * and now *IBTISSAM*

 

ALL PRAISES ARE FOR ALLAH IN ALL CONDITIONS .

 

O Allah ,ya hafeez , help and protect the people of Palestine 🇵🇸. O Allah, ya lateef ,ease their pain and suffering in Gaza . O Allah , ya Rahman,bestow your mercy on them . O Allah , ya Fattah,open the door of sustenance & provide relief to the besieged.

 

___ BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ___

 

BOOK 1

S____20

 

Lokaci d’aya gabaki d’aya wajan ya harzu’ke kowa ya soma ‘ko’karin cecar kansa , Harbin da yake ta shine yafi komai rikita mutanan cikin Wajan hatta wanda aka sarewa hannu fad’uwa yayi a ‘kasa sumamme, Abla kuwa tuni farar baturiyar data ri’kota ta hankad’ata Kanta ya bugu da jikin wani center ga mutane da suka dunga tattakata, ana cikin guje gujen har wani abu ya fad’o mata da gabaki d’aya ya rufeta ba’a ganinta.

The Choice I Made Hausa Novels Complete

Wani ‘kwararran harbi aka saka guda d’aya lokaci d’aya gabaki d’aya kowa na wajan ya tsaya, musamman turawan nan da suka fi shiga Tashin hankali , hatta mom da tayi ‘ko’karin guduwa saida ta samu harbi a ‘kafarta, shiyasa kowa ya ‘kara rikice wa , wasu mutanene suka shigo cikin wajan gabaki d’aya ba’a ganin fuskokinsu sabida shigar ba’ka’ken kayan dake jikinsu , cikin kakkausar murya d’aya daga cikinsu ya furta “ Every Body kneel!” Yana kai ‘karshen zancansa masu ba’ka’ken kayan nan suka saita su da bindugogin hannunsu, lokaci d’aya turawan nan sukai kneel down tare da Mayar da hannayensu zuwa kansu ko wannansu ya sunkuyar da kansu , hatta su momy irin abunda sukayi Kenan , matan da aka kama kuma suka cunkushe waje d’aya suna kuka , d’aya daga cikin su me sanye da ba’kin face mask ne ya cire p-cap d’in kansa , take a wajan mutanan nan suka sara masa , hannu ya saka tare da zare facemask d’in fuskarsa bakowa bane face Bobo sanye da wasu ba’ka’ken Kaya , wandan jikin sa duk bindugune a jiki ga wasu irin abun tashin bom da yake sanye dasu, fuskarsa gabaki d’aya babu fara’a kamar ba bobon da yake yawan murmushi ba , rai a ‘bace ya furta “ Arrest them all “ cikin Sauri d’aya daga cikin mazan ya dashi da niyar guduwa Bobo ya harbeshi a ‘kafa tare da karasowa inda yake , hannunsa d’aya ya dungule ya kaimasa naushi da har saida guy d’in ya saki ‘kara ganin yadda Jini ya fara fito masa daga hanci, a zuciye bobo ya ri’ke hannusa d’aya ya juyar dashi tare da kaiwa hannun naushi , lokaci d’aya kashin hannunsa ya bada sautin ‘kas kamar na karyewar abu, sosai ya fara ihu yana girgiza wa bobo kai ganin bobo yana ‘ko’karin karya masa d’ayan hannun , cikin azaba ya fara furta “ I surrender! I surrender “ ya dunga furtawa da’karfi sabida azabar ‘balla masa hannu da bobo yayi. Yana juyawa gabaki d’aya masu sanye da ba’ka’ken kayannan suka soma kamasu, cikin sauri Robert ya ‘karaso inda yake , batare da ya furta komai ba ya nuna side d’in da matan nan suka cinkushe waje d’aya , “ yes sir” cewar Robert , tafiya Bobo ya somayi kafin cikin kakkausar murya ya basu umarnin su ‘kona gabaki d’aya wajan . Hakan ne kuwa ya faru gabaki d’aya mutanan nan saida aka kama hatta mom da take kuka akan da ma batazo wajan ba gabaki d’aya sun ‘kara rikicewa musamman da sukaga za’a ’kona musu wajan da yafi shekara 20 da ‘kungiyar su take zama , hatta guy din da bobo ya ‘ballawa hannu da Wanda bobo ya guntulewa hannu Haka captain yajasu a ‘kasa babu ko d’igon tausayinsu a fuskarsa . Wasu matane suma sanye da ba’ka’ken kaya suka ‘karaso inda yan matan nan suke ,hannu d’aya daga cikinsu tasaka ta yaye abun fuskarta, ba kowa bace face LG Laura j.richardson Itama gabaki d’aya jikinta sanye yake da bindigu ga wasu ‘kananan binduga da ta ri’ke a hannunta “ Let’s go” shine abunda tace musu , da Sauri kuwa yan matannan suka tashi suka soma bin bayansu bayan su Robert sun fitar da su mom, suna fita daga wajan su Robert suka sakawa wajan wuta . Sosai wajan ya soma ci da wuta ga Abla da take kwance sai a lokacin ta farka yadda taga wuta na ci tako inane yasa ta mike a zabure tana neman hanyar fita amma duk inda tayi ‘ko’karin saka ‘kafarta sai wajan ya ‘kara ci da wuta sosai tsoro da tashin hankali ya kamata da ta soma neman zaucewa babu abunda take furtawa sai ya Allah sabida yadda haya’ki keshigar mata cikin hanci ta ko ina wutace take kamawa sosai gabaki d’aya sai ta hargitse tarasa hanyar fita , ganin bata da wata mafitane yasa ta fashe da kuka .

A waje kuwa gabaki d’aya cikin wasu ba’ka’ken motoci aka soma saka turawan nan , matan kuma LG laura ce take nuna musu motocin da za’a saka su, ga bobo da yake tsaye hannunsa kare da wayarsa da alama waya yakeyi. Ana cikin saka ‘yan matan nan a cikin mota bobo ya soma jin hayaniya na tashi kad’an kad’an, da ido yabi wajan gani wata budurwa na ‘ko’karin karasowa amma sojoji sun hanata , ita kuma ta dage akan sai ta shigo , hannu kawai ya d’aga musu , cikin Sauri suka matsa mata , ba kowa bace face Emma da ta ‘karaso Wajan sai faman haki take fuskar ta tayi ja sosai alamar kuka ta gama yi , cikin d’aga murya ta soma nuna musu cikin wajen da ya soma ci da wuta sosai “ She’s inside ! She’s inside” shine kad’ai abunda bakinta yake iya furtawa , kallan wajan bobo yayi kafun ya kalleta “ who’s inside ?” Ya tanbayeta, girgixa masa kai ta ‘karayi cikin turanci ta furta “ ba su kenan ba akwai ragowar macen da aka kawotanan , bata cikin yan matancan, please ku temaka ku ceci ranta” kallan robert yayi alamar ‘karun bayani , cikin girmamawa Robert ya furta “ sorry sir bamuga kowa ba a ciki shiyasa muka kunna wa wajan wuta” da karfi bobo har yana dukan motar gabansa ya furta “ are you guys fool? Me yasa baku bincika sosai ba ?”, sorry sir” gabaki d’aya suka furta cikin tsantsan girmamawa, batare da ya kallesu ba ya ajje phone dinsa akan motan tare da bud’e bayan wani boot ya ciro wani ba’kin Abu kamar blanket , cikin sauri sojojin nan suka d’auko wani abu baki suka barbad’a masa akai suma suka d’auko nasu gadan gadan sojojin nan suka tunkari shiga cikin wutar amma tun kafun su ‘karasa wajan wutar tayi wani irin ‘karan sauti ga yanda ta huro sosai kamar wacce ake ‘kara hurata, duk yanda Suka so shiga cikin wutar basu samu wannan chance dinba sabida yadda wuta take ci sosia , Bargon hannunsa bobo ya karba ya saka a jikinsa zai shiga ciki gabaki d’aya kowannansu lokaci d’aya ya furta “ sir” dan wallahi Suka bari bobo yashiga cikin wutarnan ko me yasamesa big boss bazai d’agawa kowa ‘kafa ba shiyasa hakan ya ‘kara razanasu ganin bobo yana ‘ko’karin tunkarar wajan, hankad’o ‘kofar wajan da akai da ‘karfine yasakasu gabaki d’aya tsayawa , cikin sauri sauri ya soma takowa gabaki d’aya lokaci d’aya suka ‘kame sabida tsantsan mamakin ganinsa , duk da ba’a iya ganin jikinsa ko fuskarsa Sabida facemask d’in dake face d’insa amma duk Wanda yaga sar’kar diamond d’in wuyansa ya shaida shid’inne ba wani ba, jikinsa sanye yake cikin ba’ka’ken kayan chanel ya nannad’e hannun rigar t-shirt d’in rigarsa da ya bawa farin hannunsa da bracelet d’in hannunsa guda uku fitowa ras dashi, daga kafad’arsa kuwa doguwar coat d’insa ce ‘baka da d’an tudu a jikinta kamar Wanda ya d’auko wani abu, gabaki d’ayansu kasa motsawa sukai daga inda suke sai ‘kara shiga taitayinsu da sukai musamman yadda ko d’ago face d’insa bayayi , hakan na nufin kuskure ya ke jira mutum d’aya yayi tak a cikinsu , hatta bobo mamakin ganinsa ne yasa ya kasa motsawa dukda yasan ‘karamin aikin big boss ne wannan . Babu Wanda ya kalla a cikinsu tun da ya soma taku gabaki d’aya sojojin wajan suka bashi hanyar wucewa kowa yana jiran wucewarsa, hatta LG laura sosai ta zuba masa idanuwanta kamar zata had’iyeshi musamman kafad’arshi kamar Wanda ya d’auko mutum lokaci d’aya taji saukar harbi adaidai saitin face d’inta da ya sakata ‘kamewa cikin Sauri ta sunkuyar da kanta dan tasan ko wanane yayi mata haka. Bata gama fad’awa shock ba sai lokacin da coat d’in Big boss ta d’an zame take awajan dogon gashinta yafito sosai har yana ‘ko’karin rufe masa fuska , d’an ‘karamun tsaki yayi lokacin da Victor ya bud’e masa motar Bobo, batare da ya kalli fuskar wanda ya d’auko ba kawai ya jefata cikin motar tare da coat d’in da ya lullu’beta, d’an d’agowa yayi kad’an ya zubawa bobo eyes d’insa da suka farayin ja na ‘bacin rai kafun ya juya cikin takunsa na izza ya shiga farar Audi Rs d’in da Anthony ya bud’e masa , cikin Sauri Victor da Anthony suka shiga cikin motar tare da barin wajan cikin mugun speed .

Sai a lokacin Bobo ya kalli car d’insa da Big boss ya jefa masa wacce ya d’auko daga kallan idanuwansa da yayi ya tabbata ran sa a ‘bace yake, gashin kansa ya shafa tare da nufar motar cikin sauri Robert ya bud’e masa , a kwance take fuskarta tayi rigingine sabida yadda dogon gashin jikinta ya rufe mata fuska, hannunsa d’aya ya saka ya d’an yaye gashin take a Wajan kyakkaywar fuskar Abla ta fito rass da ita , sosai zuciyarsa ta buga lokaci d’aya daya kalli fuskar Abla, rigar jikinta ya kalla ganin coat d’in Big boss sanye a jikinta gashi ko alamar motsi batayi, shikansa saida yayi shock d’in ganin coat d‘ in amma ya sani big boss akansa zai huce ‘bacin ransa sabida d’auko Wanda shi kansa yasan big boss ko kusa be kalli face d’inta ba, hannunsa d’aya ya kai wajan hancinta amma gabaki d’aya nunfashinta baya fitowa da alama suma tayi gabaki d’aya sabida yadda eyes d’inta suke a kulle ga innocent face d’inta da ya ‘kara fad’awa kad’an. Ko me ya tuna oho sai shima ya d’an ta’be bakinsa sosai kamar zaice LG Laura tazo ta fitar masa da ita daga cikin mota sai kuma ya fasa , batare da ya kalli Robert ba ya furta hospital lokacin da yake shiga d’ayan side d’in na motar, cikin ‘kan’kanin lokaci motocinsa da na sauran jami’ansa suka bar wajan , motar da aka kama turawan nan ma an tafi , sai motocin su LG da tun fitowar Big Boss ta kasa motsawa sabida yadda wani irin ba’kin kishi ya kamata ganin wata a kafad’ar Man d’inta ga coat d’insa da babu macen da ta isa ko ta’bawa amma yau ga wata banza ta samu damar da ta d’auki sama da shekara goma tana jiran irin wannan damar ko kad’an ce . Sosai kishi ya kamata takasa ko motsi har saida captain ya ‘karaso inda take “ Lokaci na tafiya” kamar bazata tanka masa ba , sabida yadda ta kasa motsi sai kuma cikin fusata rai a’bace ta shiga cikin motocin su tare da barin wajan dan har Emma sai da aka tafi da ita.

THE QEII HEALTH SCIENCES shine sunan hospital d’in da su bobo suka shigo, tun kafin motocin su suyi parking wasu doctors mata 2 da namiji d’aya Suka ‘karaso wajan tare da gadon d’aukar Mara lafiya , da hannu bobo ya nuna musu Inda Abla take a kwance , cikin Sauri matan nan suka sakata a gadon d’aukar Marasa lapiya suka bar wajan . Hannu Male Doctor d’innan ya mi’kawa bobo babu musu kuwa sukai shaking hannu , da turanci doctor d’in ya furta “ wacece ita sir !” , d’an kallansa bobo yayi na sakanni batare da ya damu da abunda zai furtaba ya furta “ she’s my sister !” Saurin washe masa baki doctor d’in yayi “ Okay sir , za’a bata kulawa sosai”, kansa bobo ya jinjina masa kafun ya soma tafiya “ ku bata kulawa sosai , zan dawo” , yana kai ‘karshen zancansa ya koma cikin mota Robert ya tayar da ita suka bar Wajan .

 

FLASH BANK

Abunda ya faru jiya bayan Big Boss da Bobo sun fita , details d’in wasu yan mata ne guda biyu da akai kidnapping d’insu a cikin New York , cikin ‘kan’kanin lokaci bobo ya bincika bayanan yaran har ya samu details d’in ’kasar da aka fitar dasu , wannan dalilinne Big boss ya basu umarnin zuwa Canada tun a daran jiya , shiyasa washe gari da sassafe Bobo dasu Robert sukabar New York , tsakanin America da Canada tafiyan hour 3 ne a jirgi kasantuwar private jet suka hau 2 hour 20minute ne ya kawosu kasar Canada . Wannan ne dalilin zuwan su bobo Canada shiyasa kowa yayi mamakin ganin big boss a ‘kasar dan babu Wanda yasan da zuwansa ko dalilin zuwan nasa hatta bobo yayi mamakin ganinsa a canada.

 

 

******

**********

9:01pm na dare motocin bobo suka danno kai cikin asibitin, Daidai parking lot motocinsu suka tsaya , cikin Sauri robert ya fito ya bud’e masa mota . A yanxu babu ba’ka’ken kayan d’azu sabida yanda ya canza dressing zuwa blue d’in wando da white shirt d’in Riga sai wata white coat dayake sanye da ita sabida sanyin da akeyi . Tun kafun ya shiga cikin premises d’in asibitin likitan d’azu ya fito cikin sauri ya ‘karaso Inda bobo yake , cike da girmamawa ya furta “ this way sir”, hakan ce kuwa ta kasance, bobo be shiga da kowa cikiba sai Robert da yake binsa a baya , shima bobo sabida facemask d’in face d’insa ne yasaka ya shiga cikin asibitin, sabida yadda asibitin ya d’au shiru sai d’ad’d’an kun mutane da suke giftawa. Kai tsaye floor 5 suka nufa cikin elevator , gabaki d’aya yanda wajan yake ba hayaniya ko kad’an ya tsarin wajan da ya banbanta da sauran zai tabbatar maka da waje na musamman suka shigo da bakowa ake iya kaiwa wajan ba , yar tafiya kad’an sukai kafun suzo Daidai wasu ‘kofofi guda biyu da suke nesa da sauran, tun kafun su shiga cikin d’akin suka soma jiyo murya kadan kadan daga ‘kofar hagunsu , cikin sauri doctor ya bud’e bobo ya shiga. Babban d’akin asibitine me girman gaske da kallon farko da mutum zaiyiwa d’akin zaisan bakowa ake kawowa ‘bangaran ba tundaga kan yanayin d’akin mutum zaisan a cikin d’akunan ma Wannan Vip ne .

Cikin Sauri doctor da bobo suka ‘karaso cikin d’akin ganin nurses a tsaye sai faman furta “ calm down” suke Sabida yadda Abla ta burkice gabaki d’aya sai kuka take tana ‘ko’karin cire ledar ruwan da aka saka mata, ga rigar big boss da tayi mugun yi mata yawa amma Sabida yadda bata cikin nutsuwarta taki bari a cire mata balantana Tasha iska . Cikin French doctor d’in yake tanbayarsu abunda yake faruwa, nurse d’in kusa da shine ta basa amsa da “ Dr taki tsayawa ta kwantar da hankalin ta, hakan kuma xai iya ja mata matsala a brain d’inta sabida allurar da aka dunga mata ba Bisa tsari ba “, kallan doctor bobo yayi alamar ‘karin bayani sabida maganganun nurse d’in nan duk a cikin kunnansa , yana ‘ko’karin masa bayani Abla ta ‘karasa sakin wani saban ‘kara muryarta har sha’kewa take wajan furta “ karku ta’bani ni banaso, ina ne nan ? Su wanene ku ?” Iya abunda Abla take furtawa kenan ga gashin kanta da ya rufe mata fuska ba’a ganin face d’inta sosai , ganin taki na tsuwane yasa bobo ya d’an daka mata tsawa kad’an lokaci d’aya kuwa tayi shiru kamar ba itaba, a hankali ta d’an d’ago da face d’inta basu sauka ko ina ba sai akan fuskar bobo da ya tsaya yana kallan ikon Allah , yadda ta tsaya tana kallansa ga gashi duk ya rufe mata fuskane yasa ya d’an harareta kafun ya nuna wa nurse akan suyi abunda zasuyi mata , da ‘kyar tabari nurse d’innan ta ta’bata Sabida ganin yadda bobo ya kafeta da ido, ga tsoro ya kamata sosai ganin fararan mutane cikin zuciyarta sai addua take ganin kyaun bobo ga shi dukda ba sosai take kallan fuskarsa taga ko murmushi bayayi, d’an ta’be baki tayi kad’an kafun ta furta “ mugu da alama maganin mutuwa zasu sakamun, ai gwanda na mutu ma kowa ya Hutu,” duk wannan zan tukan cikin zuciyarta take yinsu can kuma ta ‘kara ta’bile bakinta tana had’iye kukan da yake ‘ko’karin fito mata ga tsayuwar su bobo ko nunfashi sosai taji ja, “ yanxu shikenan uwar karuwai ta siyar dani wajan ‘yan ‘yankan kai?”yadda bobo ya kafeta da idone yasa ta ‘kara shiga taitayinta gabaki d’aya a tunaninta bobo shine shugaban yan shan Jinin shiyasa yake kallanta yana Tuna’nın yadda zai tsotse mata Jini.(😂😂😂wonder shall never end 😂😂 bobo ya zama shugaban yan shan Jini ).

 

Kallan Direction d’in doctorn bobo yayi kafun ya furta “ let’s talk” yana kai ‘karshen maganarsa bai jira jin amsar saba ya bar d’akin shida Robert , shima doctor cikin sauri ya bawa nurse d’in umarnin su kula da ita kafun ya bar cikin d’akin , koda ya fito be tarar da bobo ba shiyasa yayi Saurin

Bud’e office dinsa da ke facing d’akin da Abla take ciki, a zaune ya tarar dashi kan kujera yayın da Robert yake tsaye gefensa cikin shigar ‘ba’ka’ken kayansa, tun kafin ya zauna bobo ya kallesa alamar ‘karin bayani, wani files doctor ya mi’ka masa yana zama kan kujerarsa “ wannan details din tane, alamu sun nuna tana cikin matsananciyar damuwa da ta saka wa zuciyar ta , hakan kuma babban illa ne da zai iya sawa ta kamu da ciwan zuciya , secondly she have stomach ulser , hakan ya samone daga rashin abinci me lapiya da bata samu , ayyuka masu wuya da kuma rashin cin abinci akan lokaci hakan ne yasa ta kamu da stomach ulser me mugun hatsarin gaske da idan ba’a kula da abincinta ba zaiyi affecting kayan cikinta.” Sai kuma yayi shiru yana tantamar karasa masa zancansa, “ And?” Cewar bobo yana zuba masa idanuwansa , ajiyar zuciya doctor ya sauke “ alamu sun nuna cocaine d’in da aka sha’ka mata shine yake ‘ko’karin ta’ba mata kwakwalwarta , sannan akwai allura da akai mata da ta wuce ‘ka’ida ta maye , sai kuma wata allura last da akai mata me mugun illa da idan ta ‘kara 2 hours tana bacci bazata ta’ba tashi ba”ya ‘karasa a hankali yana kallan bobo, cike da mamaki bobo ya furta “Cocaine ? Wannan yarinyar?” Cikin tabbatar da bincikensu doctor ya furta “ yes sir”, bobo be kuma cewa komai ba ya tashi tsaye hannunsa d’auke da file d’in Abla , agogon hannunsa ya duba kafun ya mikawa doctor hannu sukai shaking , kai tsaye d’akin da aka kwantar da Abla bobo ya ‘kara komawa a wannan lokacin an tufke mata gashin kanta , amma yadda ta takure waje d’aya tana kuka ne zai bawa duk Wanda ya ganta tausayi , duk Wanda yaji sautin kukanta yasan daga ‘kasan zuciyar ta yake fitowa, yadda take kuka sosai bobo yaji ba dad’i cikin zuciyarsa da yayi sanadiyar ta’bo masa tabansu da bayasan tunawa a rayuwa , kujerar da take side d’in gadon ya zauna , yadda take ‘boye fuskarta cikin rigar big boss da ta kudun dune ne Yaso bashi dariya , musamman dramer da yake ‘ko’karin shiryawa da kaso 90 aciki yasan me wuyane sosai. Gabaki d’aya nuni Robert yayi wa nurses din akan su fita, suna fita shima be ‘kara one minutes ba ya bar d’akın yayi saura bobo da Abla kawai gashi ta sunkuyar da kanta ‘kasa taki yadda ta d’ago da fuskarta ya lura a tsorace take gabaki d’aya , mamakin abunda doctor ya fad’a game da lapiyar tane ya tsaya masa a rai haka kawai yaji yana san jin ko wacece ita, da inda iyayenta suke , yafi tsawan 5 minutes zaune a wajan be tankamata ba , shima Abla bata d’ago kanta va sai ma ‘kara tura kanta da tayi cikin rigar jikinta. Knocking d’in da akai ne ya bada izinin shigowa , LG laura ce sanye da wasu ‘kananan kaya a jikinta , gashin kanta ta d’aureshi ta baya sai faman lilo yake , kallan Abla dake kan bed tayi duk da bataga fuskarta ba taji ranta ya mugun ‘baci lokaci d’aya taji wani irin tsanar Abla ya shiga cikin zuciyarta , ji take kamar ta kasheta lokaci d’aya ta mutu musamman yadda taga tana ‘kara rirri’ke rigar big boss a jikinta “ in kin gama kallanta zaki iya bani abunda ya kawo ki?” Cewar bobo ya furta wa LG da French, da Sauri ta furta “ sorry sir” ta mi’ka masa ‘karamun book d’in da ta shigo dashi , har yanxu zuciyarta ta kasa ha’kura so take taga wata me zarrarce take ‘ko’karin wasa da ranta , ganin bobo ne yasaka bata d’au wani mataki akanta ba da tasan har da yarinyar awajan da babu abunda zai saka ta zuwa , mi’kewar bobo ne yasa ta sara masa duk da ba uniform a jikinta na sojoji, Daidai bakin gadon Abla ya nufa kafun ya d’an juyo Daidai saitin LG ya furta “ We’re going in not less than few minutes” sara masa tayi tare da furta “ yes sir” tana juyawa, koda zata bar d’akin sai da ta ‘kara jiyowa ta kalli gadon da Abla take Kai.

“ Hey !” Cewar bobo yana kalan Abla , da Sauri Abla ta zabura har tana bige hannunta , yadda fuskarta ta ‘bacı da hawayene yaso bashi dariya , gashi ta wani zaro masa ash eyes d’inta da ya cika da kwalla , kana ganin yanayin fuskarta zaka fuskanci ‘kiris take jira ta ‘kara saka wani kukan , “ quel est ton nom ? ( ya sunanki ?)”, cewar bobo , bin bakinsa da kallo Abla tayi a tsorace ko kwakkwaran motsi batayi , shi kuma bobo atunaninsa tana Jin French shiyasa yayi mata da yaran dan Abla gabaki d’aya bata kama da yan Africa,ganin tayi masa shiru tana binsa da manyan idanuwanta yasa a wannan karan yayi mata turanci “ what’s your name ?”, yanxu ma shiru tayi masa idanuwanta gabaki d’aya ya cika da kwalla, lokaci zuwa lokaci tana kallan gefenta, kamar ace mata takkk ta arta a guje , shigowar doctor ne yasa ya mayar da kallansa bakin door din har ya ‘karaso hannunsa d’auke da wata farar paper yana mi’kawa bobo, d’an kallan paper bobo yayi yana ‘kara kallan doctor d’in “ ta samu matsalar maganane?” Girgiza masa kai doctor yayi “ A tsorace take shiyasa , idan akai mata dole kuma zai sa mata ciwan kai”, kansa bobo ya jinjina masa , wayarsa da ta d’anyi Haske ne ya sa ya kalla kafun ya nufi kofar fita , doctor ma ya bi bayansa, yayi saura sai Abla kawai da ta ‘kara du’kun’kune kanta cikin doguwar rigar jikin ta da har yanxu ta’ki bari a ta’bata. 5 minutes later Bobo ya dawo cikin d’akin bayansa LG ce sai kuma doctor da Robert da suka shigo, yadda LG Laura take kallan rigar big boss kamar taje ta hankad’a wacce take sanye cikin rigar sa da ko ita da ta sansa sama da shekara 10 ko gashin kansa bata ta’ba ta’bawa ba sai yau wata yar iska ta nanuke rigarsa kamar zata had’iye , kana kallan fuskar LG yadda tayi jaa zakasan ranta a’bace yake tana ‘ko’karin dannewa ne kawai.

‘Dan gajeran murmushi bobo ya saki tare da zama akan kujerar kusa da gadan Abla da ta ‘kara ta kure jikinta , har zai mata turanci sai kuma ya fasa tuno yadda tayi Hausa d’azu , hausan da shi kansa yayi mamakin yadda akai ta ‘iya yinsa amma bashi da lokacin tanbayar yadda tayi shiyasa cikin cool voice ya furta “ ya sunanki?” Itama Abla da mamaki ta d’ago fuskarta ta zubawa bobo , bata san lokacin da bakinta ya furta “ shima farin meshan jinin nan ya iya Hausa ?” Da mamaki bobo ya kalleta sabida maganarta wato d’an shan jini ta d’auketa , “ lalle kina da aiki babba” cewar bobo cikin zuciyarsa . Be kuma ce mata komai ba ya mike tsaye tare da kallan LG cikin French ya furta “ ku taho tare da ita and ku rufe mata kanta bansan ganin gashi a waje , yana kai ‘karshen zancan ya bar d’akin, a zuciye LG ta matso gadon da Abla take, wani farin yadi da ta gani a ‘kasa ta jefa mata tare batare da la’akari da yaran da ta iya ba cikin French tace mata ta kulle kanta, dukda Abla bata gane me take nufi ba itama da Sauri ta d’auki farin mayafin ta yafa akanta tana ‘kara rike coat d’in jiginta gagam( Ni kam zan so Big boss yaga yadda ake cakud’a masa Riga ko tsarabar mari ne ta samu😹🥹). LG ta zo zata cire mata rigar Abla ta ‘kara ri’ke wa gagam musamman yadda batasan aga jikinta, a karo na biyu LG ta ‘kara saka hannunta azuciye zata cire rigar Abla ta gantsara mata cizo , zafin da tajine yasa ta tsinkawa Abla mari , itama bata sauke hannunta ba Abla ta daddage ta tsinka mata mari dama da hannu ( kowa yasan zafin hannun bahaushe ba irin na bature bane rainan madara da Milo) a gigice ta saka ‘kara sabida zafin marin da taji batayi aune ba Abla ta ‘kara bata wani tsaraban cizon da ya saka LG ware murya ta kwala ‘kara , sai kuma ta fara dukan Abla , itama Abla bata ‘kyaleta ba , duk da yadda LG ta fita girma da ta doketa zata saka hannu ta rama dan tayi al’kawari kafun su shanye mata jini sai ta Gana musu azaba. Da Sauri a ka tura ‘kofar shigowa , yadda yaga suna dukan junane yasa bobo ‘karasawa wajan ya ‘ban’bare Abla , be tsaya wani tunani ba ya d’auke fuskar LG da mari , itama Abla ya d’aga hannu zai Mareta yaga shatin marin LG a fuskarta shiyasa ransa ya ‘kara ‘baci , hannunta kawai ya kama zatayi masa musu itama ya daka mata tsawar da yasa ta kame bakinta , ko kallan inda LG take beyi ba suka fito daga d’akin, kai tsaye fitowa sukai daga cikin asibitin d’in gabaki d’aya ,yadda Abla taga zagara zagaran maza ko wannansu sanye da ba’ka’ken kaya da bindugu a hannunsu yasaka ta soma share hawayenta , jikinta har karkarwa yake sabida tsoron ganin ko wannansu da binduga datayi , sosai kirjinta ya soma sama da ‘kasa hatta tafiyar ‘ko’karin canzawa ya fara tana lumshe ido, yadda ta soma kakkare wa a bayan bobo tana kulle idanuwanta ne yasa ya d’an juyo ya kalleta , zai mata magana ta ‘kara firgita zata saka gudu Sabida bindugar da ta gani a hannun Robert , wani irin juwane taji yana ‘ko’karin kamata , ganin yadda take ‘boyewa abayansa ne yasa ka ya d’an jiyo ya kalleta , sosai ta runtse idanuwanta ko bud’e bata sanyi har suka ‘karaso wajan motar da Robert ya bud’e masa , nuni yayi mata akan ta zauna , ba musu kuwa ta zauna dan sosai tsoran mutanan da ta gani da bindugu ya kamata , ko d’ago da kanta batasan yi musamman yadda ta rintse idanuwanta dukda sanyin Acn da yake cikin motar Alba zufar tsoroce ta fara fito mata , babu abunda take nanatawa cikin zuciyar ta sai Innalillahi wa inna ilaihi raji’un , gabaki d’aya ta sada’kar shikenan ‘karshenta ya zo , lokacin shanye Jininta yayi , shima bobo ko sau d’aya be kalli side d’in da take ba da alama abu yake me muhimmanci a cikin wayar sa , direct Airport suka nufa , a wannan karan ma koda bobo yasata ta fito batayi musu ba amma ta ki kallan kowa sai faman kare fuskarta take hatta bobo ta’ki yadda ta kallesa , ana zuwa wajan shiga jirgi Abla ta d’ago da idanuwanta , karo na farko arayuwarta data fara ganin jirgi shiyasa tana kallansa ta fashe da kuka me tsuma zuciya , tana girgiza musu kai , muryarta har rawa yake wajan furta “ Dan Allah kuyi hakuri”, yadda tayi maganar sai ta baka tausayi , hatta bobo sai da yaji ba dadi cikin cool voice ya furta “ babu abunda za’ai miki kinji? Taho mu tafi” kanta Abla ta jinjina masa kafarta har rawa take wajan taka step din jirgi, LG tana bayansu gabaki d’aya ba’kin cikine ya kamata kamar zuciyarta zata buga sabida tsanar Abla da tayi Alwashin tunda bobo ya mareta sabida ita sai ta Gana mata azabar da sai ta kwammace bata duniya ( To faaa 🥱), suna shiga cikin jirgin yawanci sojojin bobone ko tsaye sanye da blank din kaya da Sauri ta matso inda yake dan harga Allah tsoran su Robert take , duk inda ya taka Abla tana binsa a baya , Adai dai wani waje me shegen kyau Bobo ya tsaya , kujerune sosai A wajan kamar ba a cikin jirgi ba , yadda tsarun kujerun suke sai sun burge mutum , yan mata biyu da su bobo suka taho dasu ko waccensu tana zaune kan kujera ta saka belt d’inta , itama Abla waje bobo ya nuna mata sai bin ko ina take da kallo tana zama ya saka mata belt d’in da Hausa ya furta “ kar ki motsa daga inda kike idan ba haka ba jirgin sai ya had’iyeki ya cinye ki” ya fahimci tsoran jirgin ta keji shiyasa ya fad’a mata haka , yadda Abla ta ri’ke kujerar jirgi sai ta baka dariya hatta bobo saida yayi murmushi kafin ya bar wajan , LG ma da wasu mata suma duk a wajan suka zauna , yadda Abla taji wani irin girgiza na tashin jirgi sosai hakan ya girgixa ta ware murya tare da kwala kara cikin Sauri kuma ta toshe bakinta hawaye na gangaro mata cikin zuciyarta har ta fara adduar shahada ganin shikenan ta tabbata kashesu za’ayi , tun tana tsorata yadda LG take binta da mugun kallo itama Abla taka take binta , ga tsoro ga masifa , yadda sanyin Ac take kad’a ko ina ne yasa Abla ba shiri bacci ya d’auketa .

 

2 hours 45 minutes ne ya shigo dasu ‘kasar U.S cikin Garin New York , da karfi LG ta d’akawa Abla duka da yasata zabura cikin sauri, a zuciye ta cire mata belt d’in jikinta tana bin fuskarta da wani irin kallan tsada , agadarance ta furta “ let’s go” kamar Abla bazata bisu ba ganin yadda sauran yan matan suka tashi yasa itama ta tashi ta soma binsu har suka sakko cikin jirgin, Bobo na tsaye sai su Robert da wata farar baturiya sai faman sakin murmushi take ita kadai , wad’an da Abla ta gani ne ya saka lokaci d’aya jikinta ya soma raba da Sauri ta koma bayan bobo tana karanta adduar da zata zo bakinta duk da a Wannan lokacin babu bindugu a hannansu , kallan farar matar bobo yayi bansan akan me suka tattauna ba illa “ dis is the girl” da bobo yace mata , yanxu ma murmushi ta ‘kara saki tana nufo inda Abla take ta kamo hannu, da Sauri Abla ta bud’e baki zatayi ihu bobo ya furta “ idan kika Kuskura kika mun ‘kara sai na tarwatsa kanki” ba shiri kuwa Abla tayi shiru tana zazzare idanuwa saida ya bata minute d’aya kafun ya furta “ babu abunda zata yi miki, tafiya kawai zatayi dake kika kuskura kika bud’an baki kuma..” ya ‘karasa yana d’auko wata ‘karamar bindiga, saura kad’an fitsari ya kwacewa Abla lokacin da ta ga bindigar jikinta har rawa yake lokacin da farar matar nan ta kama hannunta suka wata bakar mota , ko kwakkwaran motsi Abla ta kasa har driver ya tashi motar suka bar wajan .shima Bobo motar da Robert ya bud’e masa ya shiga , ragowar sojojinsu suma suka shiga cikin motocin su guda shida suka bi bayan motar bobo , ita kuma LG da wasu sojoji suka bita tare da ‘yan matan nan . Tunda motocin su bobo ta soma tafiya a kan babban titin da zai kaisu 5th Avenue lokaci d’aya motocin bayan bobo guda biyar suka fara ‘balle bottom d’in rigar su suna cireta sai bakar singlet da suke bari hatta ta kalman ‘kafarsu ko wannansu ya cire ya nannad’e ’kafar Wandunansu zuwa gwiwa ,tun kafun ayi horn aka wangale wa bobo babban gate d’in cikin gidan, Victor tsaye a wajan cikin girmamawa ya sarawa bobo , cikin Sauri Robert ya sara masa shima yana fitowa daga cikin motar , Victor ya shiga ya tada motar tare da barin wajan , lokaci d’aya gabaki d’aya sauran sojojin sukai parking d’in motocin su suka fito , tun kafun a basu umarni ko wannansu ya kwanta a kasa a jere cikin layi , lokaci d’aya suka soma birgima a kasa duk da Nisan da ke tsakanin first gate da second gate haka suka dunga birgima kamar wasu kifaye suna tunkarar gate 2, anan ma still gate aka bud’e musu suka cigaba da birgima zuwa babban gate din cikin gidan dukda daga second gate zuwa main gate ya fi nisa haka suka dunga birgima suna furta “ sorry sir “ har suka ‘karaso main gate kafun kamar wad’an da aka saka tsere suka soma zaga compoud din cikin gidan cikin gudu gudu .

Bobo kuwa direct main part d’insu Victor yayi parking motar sa yana fita Victor ya ja motar ya bar wajan cike da girmamawa , yana shiga cikin falourn ya tarar da ko ina shiru kamar babu mutane a cikin falourn, Adaidai lokacin da little da prince suka fito daga cikin wani ‘kofa hannun d’auke da coffee, little yana ganin sa yayi saurin zuwa Wajan da yake tare da hugging d’insa , shima prince hugging d’insa yayi kallan su yayi tare da kallan coffee d’insa hannunsu , fahimtar hakan little yayi ‘kasa ‘kasa da murya kafun ya furta “ big yaya bobo help us wannan shine coffee na 8 Kenan kuma yaya big boss ya hanamu hawa lifter ta step muke bi, please”, murmushi kawai bobo yayi yau big boss a sama yake kowanene tsautsayi ya fad’a bazai ji da dad’i ba . Coffee d’in hannu ya kar’ba kafun ya furta “ dare yayi kuje ku kwanta” cikin had’a baki suka d’an zaro ido take da furta “ yaya !” Shima nasan I don ya d’an zaro musu kafin ya furta “ shikenan ku kwana a tsaye , yana kai ‘karshen maganarsa be basu wani damar ba ya nufi elevator , direct part d’in big boss ya nufa , tun kafun yashi Wajan daddad’an ’kamshin turaran big boss ya Dakar masa hanci , murmushi kawai bobo yayi kafun ya saka turn print d’insa ’kofar ta bud’e , gabaki d’aya hasken corridor d’in an kashe su sai dumm light da aka bari, bobo be damu da rashin hasken Wajan ba ya nufi ‘kofar farko da bobo yasan big boss yana ciki, ko da ya shiga nan ma still dum light ne a wajan sai kamshin turaransa da yariga ya gama kama ko ina na cikin part d’in, kofar main falourn dinsa ya shiga bakinsa d’auke da sallama . Yana zaune kan kujera sanye da wasu fararan kaya masu laushi ga gashin kamsa da ya tufke waje d’aya a bayansa , fuskarsa a d’aure ko alamun fara’a babu, tunda bobo ya shigo be d’ago ya kallesa ba , cikin nutsuwa yake operating d’in system d’in gabansa har ya ajje masa coffee d’insa be kallesa, kusan tsawan 2 minutes ya dakata da abunda ya ke , fararan sexy eyes dinsa ya d’ago ya zubawa bobo tare da mi’ka masa farin hannunsa guda d’aya a hankali ya furta “ my coat” d’an zaro idanuwa bobo yayi shikansa besan lokacin da dariya ya kwace masa ba “ Haba mana big boss , Hakana da kudin da zaka siyo adadın da kake bu’kata fa “ d’auke kansa big boss yayi kafun ya furta “ bani dasu banda kud’ima” yanxu ma wani dariyar bobo ya ‘kara saki wai bashi da kud’i yadda yake dariya ne yasa ran big boss ya ‘kara ‘baci , cike da tsokana bobo ya kara furta “ Wannan ne karo na farko daga ka d’auko wata” be ‘karasa ba rai a ‘bace big boss ya kaimasa wani irin lafiyayyan naushi da bobo yayi saurin kauce wa , duk da haka big boss be barsaba ya ‘kara kai masa wani laushin still bobo kauce wa yayi, a karo na uku big boss rigar bobo ya dan ‘ka tare da d’aga hannunsa zai kai masa naushi , kamar little bobo yayi fiki fiki da idanuwa tare da karya wuya, hankad’asa baya big boss yayi ya fad’a kan kujera “ d’an iska kawai”, wata yar iskar dariya bobo ya ‘kara saki , bindigar gefensa big boss yazo d’auka bobo yayi Sauri nufar ‘kofa sai da ya daidaici kofa kafun ya furta “ yadda ka fito d’innan my man kamar wani…” wani waje big boss ya harba da yasaka bobo saurin barin d’akin yana dariya , big boss kuwa kansa kawai yake nodding rai a ‘bace ……

 

PAY YOUR MONEY INTO 2681892316, Aisha umar zenith bank sea a turo shaidar biya ta wnn number 07041879581.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment