Littafan Hausa Novels

Humaira Hausa Novel Complete

Yadda Ake Rikita Maigida Yayin Kwanciya
Written by Hausa_Novels

Humaira Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

HUMAIRA

 

_A Sympathetic And Love Story_

 

 

*CREATED AND WRITTEN*

_BY_

🥰 *UMMEETA* 🥰

 

 

*🌙MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION🌙*

We shine all over the world

 

 

 

بِسم الله الرحمن الرحيم

~~~~~~~~~~~~~~~~

 

**PAGE 1**

 

**UNITED STATE**

 

Wani babban ɗaki ne da yake ɗauke da madaidaitan gadaje guda uku, ba wani dogon tarkace a cikin sa, komai a kimtse yake, a taƙaice dai kallo ɗaya za ka ma ɗakin ka fahimci ɗaki ne na kwanan ɗalibai, na shahararriyar jami’ar karatun law, HARVARD UNIVERSITY dake UNITED STATES (US)

 

Ba kowa a ɗakin sai wata fara, kyakkyawar budurwa, son kowa ƙin wanda ya rasa, kai wannan ɗin wanda ya rasa ma yana so, kyakkyawar gaske ce, sai dai a ce masha Allah. Zaune take kan ɗaya daga cikin gadajen da ke ɗakin, ta sa akwatinta a gaba wanda ta kama haɗa kayanta gaba ɗaya

Zan Jiraka Hausa Novel Complete

Hawaye ke bin fuskarta tana gogewa a hankali, wayar da ke gabanta ta ɗauka ta sake kiran wata number a karo na ba adadi, duk da ta san ko ta kira ba samu za tayi ba, amma hakan bai sa ta fasa ba, dan in da sabo ma, ta saba da jin abunda baturiyar wayar ke gaya mata

 

Wata balarabiyar budurwa ce ta shigo, kai tsaye wurinta ta nufa ta zauna, a hankali ta dafa ta, ta ce “HUMAIRA”

 

Ɗaga ido tayi ta kalle ta bayan ta share hawaye, ta ce “Maryam, har kin dawo?”

 

“Eh….wai dan Allah Humaira zuwa yaushe za ki daina wannan kukan? Shekarar mu huɗu a tare, ba ranar da za ta wuce ba tare da kin yi kuka ba, har ranar graduation ɗin mu ma sai da kika yi kukan nan, sannan ba ki taɓa gaya mun dalilin kukanki ba, what’s wrong with you?”

 

Sake share hawaye Humaira tayi, ta ce “kiyi haƙuri Maryam, na san kin damu da ni ne, amma ai komai ya zo ƙarshe tun da gobe za mu rabu, kowa zai koma ƙasarsu”

 

“Yeah, komai ya zo ƙarshe, but i’m seriously worried, ke ko irin murnar nan da kowa ke yi na zai koma gida after all these years, ke ban ga alamar hakan a tattare da ke ba”

 

“Maryam, duk waɗanda kika ga suna murna, sun san me za su koma gida su riska, ni kuma murnar me zan yi tunda ban san wa zan haɗu da shi ba idan na koma, ina fargabar komawa Nigeria Maryam” wasu zafafan hawaye suka sake gangarowa

 

“Ban fahimta ba Humaira, ba kya da kowa ne a Nigeria?”

 

“I don’t know Maryam, kafin in bar Nigeria na san ina da waɗanda nake kira da ahalina, amma yanzu da nake kiran numbern nan kullum ba na samu, ba zan iya cewa ina da kowa ba ko kuma babu”

 

Shiru Maryam tayi tana mamakin wannan al’amari na Humaira, kamar ya za ta ce ba ta sani ba ko tana da ahali ko ba ta da su ba? Irin kukan da take yi ne ya sa Maryam ta ja ta jikinta tana rarrashinta, ita kanta ta gama sabawa da kukan Humaira, damuwarta ɗaya gobe za su rabu amma ba ta san me ke damun ƙawarta ba, fatanta shi ne Allah ya zama gatanta a duk in da take, a kowane irin hali take ciki kuma

 

Washe gari da misalin ƙarfe ɗaya na rana, Maryam ta raka Humaira zuwa airport bayan tayi sallama da sauran abokanan karatunta, kasancewar Maryam jirgin su sai ƙarfe huɗu.

 

Maryam na riƙe da hannun Humaira, ta ce “Humaira zan yi kewarki da yawa”

 

“Nima haka Maryam, you mean alot to me, sai dai ga shi ba ƙasarmu ɗaya ba”

 

“Haka ne, amma Humaira idan da gaske ne i mean alot to you, meyasa ba za ki iya gaya mun damuwarki ba?”

 

Numfashi ta sauke ta ce “ba wai ba zan iya gaya miki ba ne, a halin yanzu ba na cikin natsuwar da zan iya gaya miki damuwa ta, amma ki taya ni da addu’a dan Allah”

 

“Ina yi miki kullum, Allah yana tare da ke Humaira, just have faith in Him”

 

Jinjina kai Humaira ke yi tana share hawaye, Maryam ma share hawayen tayi, suka rungume juna kamar kar su rabu, amma dole suka saki juna idanunsu cike da hawaye. Haka Humaira ta ƙarasa ciki, aka gama binciken da za’a yi mata, sannan ta shiga jirgin, kujerar kusa da window ta zauna tayi shiru tana ta lissafin rayuwa, Maryam kuwa ba ta bar wurin ba sai da jirgin su Humaira ya tashi

 

**NIGERIA**

 

Ƙarfe uku da ƴan mintuna kaɗan, jirgin su ya sauka, cike da murna mutanen cikin jirgin suke fita ɗaya bayan ɗaya tare da gode wa Allah.

 

Humaira tayi nisa a duniyar tunani, sam ba ta san jirgin ya sauka ba, kusan kowa ya fita sai ita kaɗai da ma’aikatan jirgin, wata ma’aikaciya ta zo kusa da ita, ta ce “Baiwar Allah” kusan sau biyu, amma ba ta ji ba, hakan ya sa ta taɓa ta

 

A firgice ta dawo hayyacinta dan tayi nisa sosai, ma’aikaciyar ta ce “kiyi haƙuri idan kin tsorata, na ga kowa ya fita ke kaɗai kika rage”

 

Buɗe ido Humaira tayi tana leƙan window, kafin ta kalle ta, ta ce “lafiya? Har mun yi landing ne?”

 

Murmushi tayi, ta ce “eh mana, muna Nigeria yanzu”

 

Daga jin ta ambaci Nigeria, gabanta yayi mummunan faɗuwa, a hankali ta ce “innalillahi wa’inna ilaihi ra’jiun” sannan ta miƙe ta fita jiki a mace

 

Tafiya take a hankali tana jan akwatin ta, wanda ta gani ne ya sa ta tsayawa cak, hawayen da ba ta shirya ma zuwansu ba, suka biyo kyakkyawar fuskarta, gaba ɗaya ta kasa motsawa

 

Matashin saurayi ne ɗan kimanin shekaru talatin da ɗaya, ba fari ba ne sosai amma ba za’a kira shi da baƙi ba, yana da matsakaicin tsayi, yana da kyau dai-dai gwargwado. Sanye yake da farin wandon da ya matse shi, sai farar riga t-shirt da jacket shi ma fari, sarƙa biyu ne a wuyansa na ƙarfe, cikakken gaye ne mai ji da kansa sosai

 

Yana tsaye ya jingina da jikin ƙatuwar motarsa baƙa, yana hango Humaira ya sauke madubin idanunsa yana murmushi, ganin ba ta da niyar ƙarasowa ya sa shi matsawa, sai da ya gama zagaye ta kafin ya fuskance ta ya ce

 

“Welcome back Baby!!” Ya ƙarasa maganar yana wani kashe ido

 

Hawaye ke ta gangarowa kan fuskarta, ta kasa cewa komai, murmushi ya sake yi ya ce “these tears doesn’t suits your sexy eyes dear, ƙaddara ce ta riga fata, kuma na sha gaya miki i’m your husband amma ba ki yarda ba, right? Kina tsammanin ya fi ni sonki ko? The truth is ba ya ƙaunarki shiyasa yayi making wannan simple deal ɗin saboda kawai ya rabu da ke…..Baby, you have no choice but to follow me”

 

Kuka take yi sosai yanzu, tana kallonsa, ya ce “oh no Baby, meye haka?….well zo mu bar nan first, mu tafi gida” ya sake kashe mata ido kafin ya ja jakarta ya wuce yana pito, wanda ya zame masa jiki

 

Har ya shiga mota tana kallonshi kuma ba ta daina kuka ba, ta kai mintuna uku a wurin, daga ƙarshe ta fahimci ba ta da zaɓin da ya wuce ta bi shi, kamar me ciwon ƙafa haka take tafiya har ta shiga motar, yayi murmushi ya ce “Good, Baby” sannan ya ja motar

 

Gaban wani babban gida ya tsaya, tun da ya shigo layin mai gadin ya buɗe mishi gate, shiyasa kai tsaye ya danna motar ciki yayi parking. Sai da yayi da gaske kafin ta biyo shi suka shiga cikin parlour

 

Wata babbar mata ce a ciki, tana da ƙiba sannan ba ta da wani tsayi, fara ce amma ba sosai ba, daga ganinta za ka san tana jinkanta, zaune take kan cushion ta ɗora ƙafa kan ƙaramin table tana shan fruits, wata mai aiki na zaune a ƙasa tana tausa mata ƙafa

 

Ganin shigowarsu Humaira ya sa ta ajiye bowl ɗin gefe sannan ta miƙe bayan mai aikin ta sake mata ƙafa, tana murmushi ta ce “your welcome My boy” ta rungume shi, kafin ta kalli Humaira da har yanzu kukan take yi, ta ce “meye abun kuka kuma daughter in-law? Ki godewa Allah da ya kawo ki gidan nan, don’t stress yourself, okay?”

 

Ta mayar da kallonta kan shi, ta ce “SHA’ABAN, ka kai ta ɗakin da za ta zauna kafin auren, ta samu tayi wanka sai ta sauko ku ci abinci kafin in dawo”

 

“Where are you going Mom?” Cewar Sha’aban

 

“Zan je in fara shirye-shiryen bikin naku mana, ka manta na gaya maka immediately tana dawowa za’a fara shirin biki!? Kuma nan da one week in Allah ya yarda”

 

Cike da murna ya ce “are you serious Mom? One week?”

 

“Of course My son, anything for you”

 

“Thank you” ya faɗa yana sake rungume ta

 

“Don’t mention, yanzu dai je ka raka ta, ta yi wanka, bari in je in shirya ni kuma” daga haka ta wuce ɗakinta

 

Humaira jiki a sanyaye take bin Sha’aban, gabanta sai faɗuwa yake yi musamman da ta ji abunda mahaifiyarsa ta faɗa

 

Har cikin ɗaki ya kai ta, kafin ya ce “freshen up Baby, yanzu zan dawo” ya fita yana pito

 

Zama tayi kan gado kusan mintuna goma tana kuka idanunta sun yi ja, da sauri ta ɗauki wayarta ta sake kiran numbern duk da ta san ba lallai a ɗaga ba, har ta tsinke kuwa ba’a ɗauka ba, sake gwadawa tayi a karo na biyu

 

Abunda ya ba ta mamaki kuma ya sa ta matuƙar farinciki, shi ne ɗaga wayar da aka yi, ba ta jira ta ji wanda ya ɗaga ba, cikin rawar jiki ta ce “Ya…what… where are you? Why do you let this happen? Why do you do this to me? Why do you abandon me for so long? What have i done wrong? Sai da na gaya maka don’t make this deal, kar kayi, but you refuse to listen to me, ka ga abunda ya faru ko? Na san waye Sha’aban shiyasa hankali na bai kwanta ba, yanzu ga ni nan a gidansu, kuma mahaifiyarsa ta ce nan da one week za’a mana aure…..i won’t be able to survive idan har na auri Sha’aban wallahi” ta ƙarasa tana kuka mai cin rai

 

Tun da ta fara maganar ba ta tsaya ba bare ta ji me za’a ce, sai da ta kai ƙarshe sannan ta tuna ba ta ji muryar kowa ba, duba wayar tayi ta ga har yanzu yana ongoing call, ta sake mayarwa kan kunnenta, a hankali ta ce “Hel….Hello!? Are you there?”

 

Sha’aban ne ya turo ƙofar ɗakin, ganin yanda take kuka ga waya a kunnenta, ya sa kai tsaye ya nufe ta, ya fizgi wayar, ya ce “da wa kike waya?” Ya tambaye ta rai a ɓace

 

Duk da cewar tana matuƙar tsoron Sha’aban ko da kuwa yana cikin farinciki ne bare kuma idan ya ɓata rai, amma kawai ta ji tsoron ya rage, tayi ƙarfin halin ce wa “ai wayar na hannunka, ka duba”

 

Sai da ya mata wani irin kallo, wannan kallon yana daga cikin abunda ke ba ta tsoro na Sha’aban, sannan ya duba wayar, cikin mamaki ya ce “MIRAJ? Da Miraj kike waya?”

 

Ba abunda ta ce mishi, ya juya a haske ya fita, sai da ya sauka parlour kafin ya dauki waya ya kira wani layi, bugu ɗaya aka ɗaga

 

Daga ɗayan ɓangaren aka ce “Sai Oga, wani abu kake buƙata ne kuma?”

 

A tsawace ya ce “come on keep quiet, simple thing ma kun gagara kuyi shi ne kake tambayar me nake buƙata? Ya muka yi da kai jiya? Ba gaya mun kayi ka kashe Miraj ba?”

 

“Ƙwarai kuwa, yana barzahu”

 

“Kar ka raina mun hankali Rilwanu, yanzu fa na ga Humaira tanawaya da shi, amma za ka ce ka kashe shi? Yaushe ka fara mun ƙarya? Ka san tun ranar da na nemi Gogo na rasa, kaine wanda na aminta da shi, kai ma yaudara ta za kayi?”

 

Cikin da girmamawa Rilwanu ya ce “ba ma haka Oga, kai ka san ba zan yi maka irin na Gogo ba, wallahi da gaske nake yi na kashe shi, sai dai idan wani ne ya ɗauki wayar ta shi, amma tabbas na kashe shi, kuma a irin kisan da na mishi, wallahi Oga ko ran ƙarfe ne da shi ba zai rayu ba, ka yarda dani”

 

Shiru Sha’aban yayi yana nazari, tabbas bai ji muryar kowa ba, kuma a irin yanda ya ga Humaira tana kuka, in da a ce da Miraj ne ba yanda za’a yi tayi kuka haka, wataƙila an sanar da ita labarin mutuwarsa ne, ajiyar zuciya ya sauke ya ce “shikenan, sai na neme ka”

 

Kashe wayar yayi kafin ya ce “na yarda ya mutu, amma ba zan yi sake ba, i must do something”

 

Hakan yayi dai-dai da saukowar mahaifiyarsa, ta gama shirinta cikin atamfa da mayafinta za ta fita, ya tsayar da ita ya ce “Mom”

 

“Ya aka yi ne Son?”

 

“Mom, kin ce nan da one week za’a yi bikin nan, i’m not comfortable with it gaskiya, ina so a fara events ɗin nan daga gobe”

 

“But why Son? Na ga ka yarda fa, kuma me ma zai ɗaga maka hankali yanzu tunda ga ta nan a cikin gidan nan, kuma ka san ba yanda za’a yi ta gudu”

 

“I know Mom, amma ni dai kawai kiyi yanda na ce, i know you can do it, kin ce fa anything for your son” ya ƙarasa maganar yana ɓata rai

 

“Kwantar da hankalinka yaron Mom, daga gobe za’a fara shirin biki, jibi a fara events, hope you are okay with it?”

 

Shiru ya ɗan yi kafin ya ce “shikenan, it’s ok”

 

Murmushi tayi mishi kafin ta fita, shi kuma ya zauna a wurin, har kusan mintuna ashirin amma Humaira ba ta fito ba, yayi yunƙurin komawa ɗakin amma ya tarar da ta rufe daga ciki, dole ya haƙura ya dawo parlour

 

Da daddare bayan magrib, Mom na parlour a zaune tare da wata mata, Mom ta kalle ta, ta ce “ki sha ruwan mana” tana nuna mata drinks ɗin da aka ajiye mata

 

Girgiza kai matar tayi ta ce “ba shi ya kawo ni ba, ki gaya mun dalilin kira na yanzu” ta faɗa fuska ba yabo ba fallasa

 

Murmushi Mom tayi ta ce “wai ni Farida meyasa har yau kin kasa haƙuri da tsarin Ubangiji ne? Na daɗe da sanin tun farkon aure na da Yayanku ba kya so na, har bayan rasuwarsa ma ba kya so na, to kiyi haƙuri ki so ɗan sa mana”

 

“Har yanzu ba ki gaya mun dalilin kira na ba” ta faɗa ba tare da ta damu da abunda take faɗa ba

 

Numfashi ta sauke ta ce “well…dama na kira ki ne akan auren Sha’aban, ina so mu fara shiri ne daga gobe saboda jibi zala fara events”

 

Sai yanzu ta kalle ta da kyau, a hasale ta ce “da wa? Wai kina nufin da ni za’a yi shirye-shiryen bikin Sha’aban? Kin yi kuskure Hajiya Harira, wallahi matuƙar da wannan yarinyar ne za’a yi auren Sha’aban, to ba da ni ba, dan wallahi ba za’a haɗa hannu da ni ba wajen lalata rayuwar ƴar mutane saboda kawai ba ta da gata, ba ta da mai tsaya mata, ina da ƴaƴa mata, wata rana zan mutu, ba zan yarda hakan ya faru kan nawa yaran ba, yarinya natsatsa kamila mai hankali amma kike so ki haɗa ta da wannan lalataccen ɗan na ki, to wallahi i’m out of this”

 

A tsawace Hajiya Harira ta ce “ke dakata Fadila, ɗan nawa kike kira da lalatacce? Kar ki manta matsayi na a wurinki, ni matar Yayanki ce, kuma dole ki ɗauki Sha’aban a matsayin ɗanki”

 

Cikin ɓacin rai Anty Fadila ta ce “me zai sa in ɗauki Sha’aban a matsayin ɗana? Lokacin da Yaya ya rasu yana da shekaru uku a duniya, ai ɗaukarsa kika yi kuka bar garin nan sai da kika gama lalata shi kika sangarta shi, ba ki ɗora shi kan kowa ce irin tarbiyya ta musulunci ba sannan kuka dawo, kika tsaya tsayin daka ba wanda ya isa yayi mishi faɗa bare ya hukunta shi idan yayi ba dai-dai ba, kika hana kowa iko da shi kika ce ɗanki ne ke kaɗai….to wallahi ba ruwa na da abunda ya shafe ku ke da shi, kuma wallahi idan kuka cuci ƴar mutane Allah ba zai ƙyale ku ba, na dai gaya miki” daga haka ta fita a fusace

 

Jinjina kai Hajiya Harira tayi, ta ce “shikenan, na yarda ba za mu taɓa shiryawa da Fadila ba, kuma za ta gane, daɗin abun ba ita ba ce za ta aurar da shi, ƙanin mahaifinsa yana nan, Malam Sa’idu, zan neme shi, auren Sha’aban da Humaira ne dai sai an ɗaura ko za’a mutu” ta jingina jikin kujerar tana huci………

 

 

 

 

 

**WACE CE HUMAIRA? MEYE LABARIN TA? MEYASA BA TA SON AUREN SHA’ABAN? WANE IRIN DEAL NE MIRAJ YAYI DA SHA’ABAN WANDA HUMAIRA BA TA SO? WAI MA SHI MIRAJ ƊIN YANA INA?….DUK WAƊANNAN AMSOSHIN ZA KU SAME SU, AMMA IDAN KUKA CI GABA DA BIBIYAR LITTAFIN HUMAIRA, ZA KU SHA LABARI**

 

 

 

*LIKE*

*SHARE*

*COMMENT*

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment