Littafan Hausa Novels

Hot Romantic Hausa Novel Complete Wattpad

Romantic Hausa Novels Complete
Written by Hausa_Novels

Hot Romantic Hausa Novel Complete Wattpad

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Hot Romantic Hausa Novel Complete Wattpad

*BISMILLAHIRRAH MANURRAHIM*

 

K’irk’irar_ren labari ne, a kan Wasu k’ananam yara guda biyu ‘‘Marayu”, akwai Darusa Acikin sa, Sun tashi basuda kowa basusan kowaba Sannam Bawanda Yake kuladasu Ta dalilin haka Aka samu akasi kash!.

 

1=2

 

‘‘Rayuwa sirrice iya magana Baiwace, Hikima Jigo ce Hankali ma’auni ne Hak’uri Gurbi ne, Fushi Kuma Dana sani ne. Kowa kagani Yanada rana, Zama na kowa Yawan Fushi Bana bane, Duk rintsi ka Kyauta_ta wa Mahaifan ka Zasuji Dadi, Duk wanda ya iya zama da mutane ko a ina zakagan shi daban Na.

‘‘Ruwa Ake zubgawa kamar da bakin k’warya, yara subiyu mace Da namiji kyawa_wa Macen tafi namijin itace rik’e da Leda ta rufe musu jikin su Kafafuwan su ko takalmi babu.

 

Bayan ruwa ya dauke Ta bude Su, tace ‘‘Ismail” Yaya naga kayi shiru maiya same ka ya girgiza kai tace Haba Kayi magana mana kodai yunwa kake ji yayi murmushi ta girgiza kai, tayi murmushi tace To Ga ragowar Abunda yake jikina Jirani bari na siyu maka Kosai Kaji?.

 

Ya girgiza kai yace to yaya ta tashi ta ruga da gudu Ta tafi gurin wata Mata mai tuyar ‘‘KOSAI” ta tsaya A gefe ta mik’a kudinta matar Tace Koma gefe zan Sakamiki karki kashe min kasuwa Tace To ta koma gefe tana ta kar_kar wa rawar d’ari, Tana kallo tana ta sallamar mutane Chan ta saka mata A takar da tace zoki karba, Ta mik’a mata ta karba ta ce na gode, ta ruga da gudu, Mata mai tuyar k’osan ita da kanta ta ce Allah sarki Gata kya_kyawa Ga kyan hali Ban kyauta mata ba, ta tsallako titi da sauri.

 

Ta Kari so gun k’anin ta harya fara bacci tace ‘‘Isma’il” ya bude ido tace ga kosan bayawa kaji Ya k’arba tana kallon shi ya raba k’osan biyu Dama guda hudu ne, yace Yaya ganaki nima ganawa tace A’a kaci nibana jin yunwa kaji?, yace to kici d’aya ta dauki guda d’aya ta ci sauran ra gowar ‘‘isma’il” ya cinye sauran.

Yace Yaya nikam yaushe Baba zaizo nam ya dauke mu ne? Tayi murmushi tace Ai baba da mama suntafi gurin da ba’a dawowa Sai dai muyi musu A’du’a kaji ‘‘ISMA’IL” yace to yaya Tace tashi Mutafi kaji Yace to ta rik’e hanun sa Sukaci gaba da tafiya k’afar su ko takalmi babu Sunacikin Tafiya Wata mata ta yiyo siyayya a kasuwa ta gansu ta tsayar dasu taje ta nema musu kaya da takalma ta basu tace maza kukoma gida kukoma makaranta kudena yawo Akan titi kunji, Macen ta ce to Suka saka kayan gwanin burgewa ‘‘ISMA’IL” yace Yaya kayan nam sun miki kyau, tayi murmushi Tace Kai ko ismail surutun ka yayi yawa Yayi dariya ta ja shi suka cigaba da tafiyar su idan ka gan su Kamar yan biyu.

 

Suna cikin tafiya Sai ga motar Sojoji tazo wucewa Ta gefen su isma’il yana ganin su ya fizge daga hanun yayar sa Birki Aka taka Kowa dayake gurin yagama zata An taka yaron Wani sojane, captin 3 sters, yafito daga motar Isma’il ya nufi gunda yake, Da gudu Yace Soja.

 

Capting din sojannam Yayi mamaki sosai yayi murmushi yace Kai K’anina bakajin Magana ko?.

“ISMAIL” ya dafa kafadar sa yace Nima ina son soja, Yace To fa kanason soja Yace A yayi murmushi yace To kabari Sai ka girma zan zo na dauke ka da kaina kaji ko ismail yace To ya juya yayi tafiyar sa Yana zuwa gun yayar sa harta d’aga hanu zata mare shi, sai sojan ya daka mata tsawa yace Zo nam ta taho yace Karki taba shi kinji Tace Yaya baya jine.

Captin na sojannam yace Yana son soja Inane Gidan ku tayi shiru, Abunka da yaro yace ta ho kusa dashi yace Yaya itace take min komai Bamuda kowa.

Sojannam yayi shiru Yace Ina iyayen ku suke tace Gabad’ayan su sun rasu Kuma bamuda kowa Sojan nam yace A’a tana hawaye yace zaku bini mutafi tare tayi shiru, ‘‘ISM’IL” yace yaya zamuje gida ne, Tausayin ismail ne yasata tace A ya saka su A mota Yatafi dasu.

 

Tafiya suke yana tamabayar su zasu iya gane Garin su macen tace A’a yace Allah sarki, Karkuda mu Zan Aje ku A guna Kaikuma zan saka A makaranta Bakace kanason Ai kin soja ba?.

 

Ya na isowa Gida ya faka motar sa Awaje Ya shiga yna rik’e da hannayen su, yayi sallamah Ta amsa Yana shiga dasu Ta bata rai, Yace, ‘‘Khadija” ta amsa Yace Zomana zamu dan tattauna dake tace toh ta taho ta zauna Yace khadija Wa dan nam yaran Inason Ki rik’e mini su marayu ne basuda kuwa zasu zauna Anam tashi tayi tace Bazai taba yuwuwa ba nazama baiwar su Kaje chan dasu amma nikam karkayi tinanin Zan lura dasu kanaji ko?.

 

Ya kalleta yace marayune fa, ta tintsire dadariya tace, A’a “ya”yan hauwai niya ne su karshen marai ci Ya daka mata tsawa tace A’a kazaba kawai koni kosu?.

Hot Romantic Hausa Novel Complete Wattpad

Rek’e kai yayi yace Shikenam ‘‘Amarya” kisani fa A idon su kike furta wa ‘yan nam munanam magan ganun ta yi tsaki, tace to sai me ta kallesu tace tabbas wahala zakusha Idan har Kunzabi zama agidannam, Cikin bacin rai ya fusata zai daketa yaji an k’an kame kamar sa yarinyar tace A’a yaya (Balaifin bane), Kabar mu kawai Daman munsaba da fadi tashi Ahaka ta kama hanun‘‘Isma’il” tace zo mutafi yace To yaya taja k’anin ta suka fice, daga gidan Ismail yace Yaya kowa baya son mu Yayi murmushi, Tace A’a ismail Kadaina damuwa Ai ganinam zan share maka hawayen ka kaji, yace to yaya!.

 

Ismail shekarun sa bakwai dawatani Ne Amma bai kai shekara takwas ba, ita kuma yayar tashi Shekarun ta tara ne tana cikin na shiga na goma.

 

Ahaka sukacigaba da rayuwar su, Duk Dan Abunda wani Daga cikin su yasamu Baya ci sai ya ragewa d’an uwan sa Abun tausayi! Har Ismail ya cika shekara 12 da haihuwa, ita kuma Addar tashi Ta cika shikara 15 da hai huwa.

 

Ismail Abunda yake yafara Damun Yayar tashi, Watarana Suna zaune Ismail yace Yaya tace na’am ismail Meyasa bakaji Nekam Yakamata Ka fara nituwa Yayi dariya yace yaya kenam Ai ni Zan iya komai dan ganin ki cikin farin ciki, Bazan juri ganin Kina cikin damuwaba tayi murmushi tace Haba Kai kuwa Ni ai yanzu Abunda kake ne Bana so naji labarin Kwanaki Kaje kayi fada dawani Daya daga cikin Abokan ai kina kaga dan wankin nam danake agidan hajiya Ai yana rufa mana asiri, Ahaka mukeci muke sha Kadaina Rikici da muta Idan harkana ganina cikin farinciki Yace Shikenam Addata nadaina, Tace yauwa daman inaso Zan maka rijister yakamata kashiga makaran ta Ya juya ya kalli gefe yace A’a ni yaya bana so, Ta lallabeshi sannam yace to tace To zan koma nacigaba da aikin da Tajuya zata tafi, Yace Yaya kibani Kudi yunwa nakeji Ta biyu shi da gudu yace ya ranta da gudu Ya yi tafiyar sa.

Babbar Yarinya By Oum Aphnan

Tana shiga cikin gida ta tatar da hajiya Tana ganin ta tace, ‘‘AISHA” kinsam akwai aiyuka da yawa a gaban ki kika tafi shashan cinki ko?.

Tace A a Hajiya Daman Ismail naje na duba kwana biyu banaganin sa tace to daga yau duk abunda zakiyi sai da sanini kinji tace to Hajiya Ta tashi ta ta kinkimo dilar wanki, Ta fara tafito Cikin rana tanata Wanki Gaba d’aya ta jike jagab Da gumi Tanata wankin Ta jitayi Anyi Sallamah ta Amsa Wani Matashin saurayi ne ya shigo, Sanye sa wa’yan masu kyan gaske, har wani shek’i suke, Yazo yawuce ta kusa da zainaba, Ta durk’usa ta ce sannu da zuwa ya bita da kallo yace yauwa.

 

Yaja Jakarsa yashige cikin gida yanazuwa, Yace mama ta fito Tace A’a An samu hutu kenam yace A mama yace mama nikam Wacece A waje kitake miki wanki, tayi tsaki tace maza kaje Ka aje kayanka Kahuta, kaji yace to mama, Ya tafi Amma hankalin sa gabaday’a nakan ‘‘AISHA”, Yanazuwa daya aje kayan sa ya zagayo ta baya yataho yace da ita sunnu cikin rawar jiki tace yauwa, Yace Maiya faru nagan ki A tsorace tace A’a bakomai, yace yaya sunam ki?.

Hot Romantic Hausa Novel Complete Wattpad

Tace ‘‘Aisha” yace Gaskiya zanyiwa mama magana a na rage miki Aiki za’a nemo mai tayaki, ya sa hanu ya fara wankin shima bai wuce kala biyu ya wankeba yace kai Aisha gaskiya naggaji Gaskiya kina k’ok’ari sosai Allah sarki dazan iya dana taya ki, Tace ba komai Ka tafi kar hajiya tazo nam tasa meka Kaji, yace A’a zan tayaki hira Zuwa kigama wankin kinyi k’ok’ari sosai ai tayi murmushi, tana cikin wankin Tafara jin hajijiya tace wallahi Hajijiya ma nakeji, Ta nemi gu ta zauna take ta fara gyan gyadi, Bacci ya fara daukar ta shikuma tashi yacigaba da shan ya mata wa ‘yan da ta wanke.

Hajiya ta fito ta rik’e baki Ta dau ko ruwa a bokati Ta shek’a mata take ta farka daga baccin da take, tace Ok dan nawa kika mayar Bawan ki ko?.

Tace A’a hajiya kiyi hakuri, Yana tahowa yace haba mama kina tausaya mata Aikin yamata yawa ta hararre shi Yasan bacin ranta ya sshige cikin gida. ta taho da dinga rankwashin ‘‘Aisha” tanacewa kekam Ba naga alama koranki zanyi daga gidan nam Ta kukkun bura mata fuska.

 

Ta window ya lek’o ya girgiza kai yace gaskiya mama bata kyau tawa, Tana juyowa suka hada ido, Tace ‘‘HASSAN” bakajin magana ta ko, Ya koma ciki Ta cigaba da wanki, Ta kammala baki daya, Ta koma gefe ta zauna, Tayi tagumi! Awannam rana hajiya Ko lomar Abinci D’aya bata bataba, ‘‘HASSAN” daya fahimci haka ya Raba Abincin sa gida biyu A plate Ya taho tana zaune, Yace Aisha tace na’am ta share hawayen Fuskar ta yace Kiyi hak’uri kinji?.

 

Ya mik’a mata Abin ci Taci rabi Ta rage Yace kicin ye mana, duka tace A’a yace saboda me to naga a bin in madam me?.

Tace Inada k’ani Sunam shi, ‘‘ISMA’IL” shi naragewa Yakalleta yace Allah sarki! Sunacikin maganar Sai tace Ana buga k’ofa tace to gashinam Ma ya zo tatashi da sauri, Ta bude K’ofa Tace gashi bayawa Abincin Yau take yaci ya cinye Abincin Yana daga kai ya kalleta yaga gaba d’aya fuskar ta a kuk_kun bure!.

 

Yace Yaya Mai ya same ki A fuska?.

Ta Shafa fusrkar tace ba komai, kawai nad’an buge ne, Yayi murmushi yace Adda kenam Wannam Ai dukane, Bazan iya jurar ganin Abun da Ake miki A gidan nam Ba, Yaya Insha Allah zan saya mana gida namu Na kan mu, Ta kalleshi ta yi murmushi tace Ismail kenam Tayaya zaka saya mana gida Bayan Bakada sana’a Nikam banga ta inda zaka saya mana ba?.

 

Yace Yaya daman Akwai Wani Abokina Dayace Zamuna tafiya Aiki tare dashi, Gashi Ma yasaya mini waya harda Layi, Ya mik’omata yace gashi Ki rik’e ta In munje chan zanna k’iran ki insha Allah Zan saya mana gida kinji yaya ta tace to bazan hanaka ba Amma ka kiyaye, Sukayi bankwana ya yi tafiyar Sa.

 

Coming Soon, Yananam Tafe.

 

3=4

 

 

Sukayi bankwana ya yi tafiyar Shi, Har ta juya tafara k’ok’arin Rufe (Gate), ya juyo ta sake bude Masa tace Yaya naga kadawo ismail? Ya girgiza kai Yace Yaya jinake Kamar Karna tafi Na barki Tayi murmushi, tace Haba d’an k’anina Insha allah Zakayi Nasara Kokatafi Ai gawaya Zamu na gaisawa Karkadamu kaji ko?.

 

Yace To yaya ‘‘Hassan” ya taho Yana zuwa Yace, wannam shine k’anin Naki Tace A yace Yaya kake?, ‘‘Ismail” yace lafiya k’alau yace Dan Allah ga yayata Kadinga kulamin da ita Har zuwa lokacin Da allah yayi Tawowa ta, Yayi murmushi yace ba komai Allah yabada sa’a ismail yace Amin yajuya zai tafi, ‘‘AISHA” ta dakatar dashi ta ciro wasu ‘yan kudade a ak’ulle Gefen (ZANINTA),ta mik’ama ismail tace Gawannam zasu yima amfani ko a hanya kaga abunda kake so sai ka saya kace, yayi murmushi hawaye ne suka fara zubuwa daga idon sa, Ta saka Hanun ta ta goge masa, tace Bana son ganin Wannam hawayen Yimaza katafi kaji, yace to Shikenam tace katafi nace yace A’a saidai ku juya bayan ki muddin ina ganin fuskar ki bazan iya tafiya ba.

 

Tayi murmushi ta juya baya sannam yayi tafiyar shi, ta juyo ta duba taga har yayi nisa, saita maida k’ofar ta rufe ‘‘Hasan” Irin yadda yaga Suke Ma’a malar su ta burgeshi, yace Aisha wannam Abun naku najima banga shak’uwa irin wanna ba tayi murmushi, tace Ai koda kaine dole kasa d’an uwanka wanda duk fadin duniyar nam bakada kowa sai shi ‘‘HASAN” yace hakane kinyi gaskiya.

 

Tace hasan kagadai abunda ya faru dazu karhajiya tazo tasake tarar dakai Anam kaga kayan nam yanzu Sun kusam bushewa tana tattabasu tace Ai harma sungama bushewa ta tattaro su ta Nufi d’akin ta Ta rubesu kan latsatsiyar katafar ta, Shikuma ‘‘HASSAN” yayi ficewar sa yawo gurin Abokan shi.

Ta taho k’ofar hajiya tayi Sallamah, ko Amsawa batayi ba Cikin fushi ta hantare ta, tace Uwar me kikazo yi nam kuma yanzu?, cikin rawar jiki ‘‘AISHA” tace hajiya daman kayan naki ne Sun bushe ‘‘DUTSEN GUGA” nazo k’arba Tace Ok to shigo kizo kidauka gashi nam A gefen (TV) ‘‘AISHA” ta shigo kanta a sunkuye ta dauko dutsen, Ta juya kenam k’afar ta ta harde ta taho yif! Sai kan k’afar hajiya Ta tashi dasauri tace Hajiya kiyi Hak’uri Ta ciza baki Ta saka k’afa ta harbeta ta Kai mata mari, ‘‘AISHA” tana durkushe Harta rufe idon ta sai taji marin bai iso fuskar taba tana bude idonta bawanda ta gani face ‘‘HASSAN” yace mama kiyi hak’uri yace ‘‘AISHA” Tashi kije tatashi tayi tafiyar ta.

 

‘‘HASSAN” yabawa hajiya hak’uri sannam ta hak’ura, ya taho ta bayan ‘‘AISHA” a hankali tana guga.

 

Ya sauna, tana k’ok’arin Jona (DUTSEN), a soket Tana share hawayen Fuskar ta tace Ba laifin mu bane, Allah yaka yaso ya ganmu, ‘‘HASAN” yayi magana yace Kik’ara hak’uri da hajiya kinji, Ta juyo tayi murmushi tace Bakomai, Yana Gyara mata kayan ita kuma tana ta goge su Sukacigaba Da tad’i tamkar Ba itaba, Harta gama Goge kayan Baki Dayan Su, Ta ninke su ta tafi Bangaren Hajiya tayi Sallamah hajiya tana harara ta Ta jera kayan Kowanne A inda yadace.

 

Ta juya zata fice hajiya tace Duk abunda yasameni Kisani bazan barkiba, Batace komai ba ta fito Tana zaune wayar Ta tafara ringin, tana dauka ‘‘Tace ismail” yace na’am Tace dafatan kun kama hanya ismail yace A’a tukunna tafiyar dazamuyi Sai dare saboda Hanyar Da rana ana yawan tare mutane, Tace to Indai kasan Da matsala kawai kadawo yayi dariya yace haba Yaya ta Ai insha allah Sai nacika burina, Tace to Allah ya shige mana gaba, Yace Amin Ya kashe wayar Sa.

 

Washe gari;

 

DA safe, ‘‘Aisha” ta na zaune Tana Goge_Gage A falon hajiya, Ta goge komai ya fita tass, Tana murna Wata ya k’are zata Samu Albashi Tana gamawa Ta zo gefen Hajiya tatsugu na, Hajiya ta kalleta tace kin gama Aikin naki ne? Tace A nakammala komai Hajiya ta bude jakar ta ta ciro kudi, Ta lissafa su ta raba biyu ta mik’awa ‘‘Aisha” ita kuma ka karba ta lissafa Tace Hajiya dubu Bakwai ne, (7000), Hararar tayi tace A haka naga daman Baki, naraba kudin ki biyu (2), dashi nake zuwa gun doctor Ko kinada wata magana ne, ‘‘AISHA” ta girgiza kai tace A’a hajiya, Ta nuna mata k’ofa da yatsar ta tace Kifice min Daga Dakin nam, kafin ranki ya baci.

 

‘‘AISHA” Ta tashi ta yi fitowar ta waje Taji zafin Abunda hajiya ta mata ta daga kanta sama tana hawaye tace Bakomai, Nadan Wani lokaci ne insha Allah, ji tayi Ta bayan ta Hajiya tace zagina ma kike ko ‘‘AISHA” dan bakida mutumci ko?.

‘‘idon ta ya cic_ciko da k’walla tace A’a hajiya Kiyi hak’uri Ta ciza baki hajiya tace Allah yasoki, Dana babbalaki Agidannam Naga kamar ‘‘HASSAN” ne yake D’aure miki gindi ko? To shima shima baifi k’arfin na gindaya mar dokaba, tafi kibani gu kar Raina yabaci.

 

Tafito tana share Hawayen Fuskar ta,jeta Gindin ‘‘Fanfon ruwa” ta kunna yana zuba shaaa… Ta sa fuskar ta ta kama wankewa, ‘‘HASSAN” ne yashigo cikin gida Yana ta dariya, Harya kwanta k’asa ‘‘Aisha” ta tsaya kallon shi Ta kashe Fan fon tace To lafiya kai kuma nagan ka kana dariya?.

 

Ya ce lafiya, ‘‘AISHA” wata ce Taci kwalliya tana tafiya Kawai wani Mai mota ya wanketa da ruwan kwata, Kawai ta fashe da kuka nayi nayi Na danne dariyar amma hakan ya k’agara gaskiya taban tausayi.

‘‘AISHA” tace oh! Shine kake mata dariya yatashi kenam San tsi ya debeshi ya zame, Yafad’i kasa fuskar sa duk Toka, kamar dodo ‘‘Aisha” tatasam lokacin data tintsire da dariya ba, Shima ya kama dariya Sai kuma ‘‘AISHA” taji kunya ta juya tayi tafiyar ta.

 

‘‘HASSAN” yashiga cikin ‘‘GIDA” yana ta dariya Hajiya tafito tace Hassan mai zangani Haka ta tintsire dadariya Shigewa Fanin sa, yayi ya Watsa ruwa Yafito, yayi Dresing na kayan wasan kwallo, Yafito Yace Mama sai na dawo tace to Adawo lafiya, Ya fito wajen gida da kwallon sa yana dan bubbugawa.

 

Dukan tambalar yayi da k’arfi, ‘‘AISHA” ta shawo kwana kenam sai A fuskar ta Gau! Ta tsala wani irin I hu ta fadi, K’asa hancin ta ya fara zubda jini, Taken Hankalin ‘‘HASSAN” ya tashi ya taho da gudu, ya dagata Jini na zuba ta hancinta, Tana murmushi, Ta tashi Tana tafiya Ta yanki jiki tafadi, K’asa.

‘‘HAJIYA” tafito dasauri ta ce Kai ‘‘HASSAN” meya faruda ‘‘AISHA” tazo ta d’aga hanunta ta tab’a ta ko motsi batayi, ida nun ‘‘HASAN” suka k’ara girma suka zazzaro, Yace Mama kodai mutuwa tayi ne kam?.

 

 

Too been continue….

*BISMILLAHIRRAH MANURRAHIM*

 

K’irk’irar_ren labari ne, a kan Wasu k’ananam yara guda biyu ‘‘Marayu”, akwai Darusa Acikin sa, Sun tashi basuda kowa basusan kowaba Sannam Bawanda Yake kuladasu Ta dalilin haka Aka samu akasi kash!.

 

5=6

 

ida nun ‘‘HASAN” suka k’ara girma suka zazzaro, Yace Mama kodai mutuwa tayi ne kam?.

 

Dora ha nun ta tayi Akai, Tace A’a suma tayi, ‘‘Hassan” Hankalin sa gaba d’aya yatashi, Yace haba mama Yanzu Mukaita Asibiti Mana, ta ha rare shi, Tayi tsaki, tace Ta mutu mana, Daman fa batada kowa! ‘‘Tsayawa kan lonta yayi, yace Mama kenam, Koda batada kowa ai gamunam Baikamata muna wulakanta ‘‘AISHA” ba k’anin ta kafin yatafi, yacemin Murik’e masa ita Amana, mama karkiyi haka tatashi, tace Ok! Na fahimceka Gabadaya Bakada tinani, So kake Tasamana guba ta kashe mu gaba d’ayan mu ta mallake mana dukiyar ko?.

 

Yayi murmushi, Ya tafi bakin Fanfo, ya kunna ya taro ruwa a hanun sa ya yayyafa mata afuska, Hanun ta ya fara motsi, Daga bisani, ta bude idon ta sai, ta kama hawaye, Ganin ta farfad’o ‘‘HASSAN” yaji dadi sosai, yace Aisha sannu ta girgiza kai, ta mik’e ta zauna, hajiya kallonta tayi tace Dakin yi niyyar tafka mana sharri ko, Ace mumuka kasheki, Zakiji da munafurcin ki, tayi tsaki Tayi komawar ta cikin gida.

 

‘‘takalli hasan tace Hassan hajiya Batason zamana agidannam kaikadai ne kake nunamin kulawa agidannam, nagode sosai ya girgiza kai yace A’a Aisha kiyi hak’uri da abunda mama take miki, insha allah komai zai wuce.

 

Wayar hassan tafara ringin, Yana dubawa yaga, ‘‘SARDAUNA” yayi murmushi yadaga yace saudauna, Kunga bansamu halattar ball ba ko? Yace A kasan wannam wasan dazamuyi wasa ne mai mahimmanci, idan bakazoba Komai zai iya faruwa Bamutaba zuwa wannam matakin na (final) ba ka k’okarta kazo Dan allah, Yayi murmushi ya kalli ‘‘AISHA” ta kallishi itama tace wannam wasan nada mahimmanci, kadai ji Abunda sardauna ya fada Yakamata ka k’okarta kaje ka hassan?.

 

Ya kalleta yace A’a yanzudai kizo nakaiki karamin Asibiti na bayan mu abaki maganai, na hak’ura da wasan namu, ta kalleshi tace A’a jeka inyaso inkadawo ka siyo min maganin bakomai Tatashi ta zauna, taje bakin fanfo ta cika bokati daruwa Tace Dan allah katafi Inaso kuci kofin nam Idan har kukaci Nikaina zanyi farinciki sodai Saikadawo.

 

‘‘HASSAN” yayi mamaki sosai yayi murmushi, Ya shiga ya fito da mashin, d’in sa yahau, Betsaya ko inaba sai, Babban filin kwallon ‘‘GARIN MAIDUGURI” yana zuwa yasamu kocin su zaune yatabashi, Yamasa magana yna ganin ‘‘HASSAN” yace haba kazo a k’urerren lokaci gashi harsun saka mana kwallo 3 a ragar mu, Amma bakomai ayayi chanji, Hassan nashiga, Ya zura kwallo daya a ragar Abokan karawar tasu, daga bisani ya kara tabiyu, Aka tafi hutun tak’aitaccen lokaci na minti shabiyar, Aka dawo ‘‘HASSAN” ya kara samusu kallo a ragar su yazamana ana kunen doki,.3=3 uku da uku.

 

Saura minti Biyu A hura tashi, ‘‘HASSAN” ya k’ara saka musu kwallo ta hudu, Fili yacika da masu murna, Aka tashi Hassan aka masa kyauta ta musamman, Ya natahowa yanata murna, Yanazuwa ya wuce Wani babban asibiti, ya karbawa ‘‘AISHA” ma gun_gu na.

 

Ya nadawowa gida ya tarar da ‘‘Aisha” zaune tana kuka, Yayi shiru ya taho da sauri, yace Aisha maiyafaru Ta nuna masa hanun ta Ta k’one gun yayi yajuya yasiyo mata wani maganin, ya dawo tamika masa hanunta ya saka mata magani, Ya bare mata magun gunam ya kuma diba mata ruwa yabata tasha.

 

Yace Agarin yaya naga hanun ki ya kone tace Nazo girkine Abincin ya zubemin A hanu, ‘‘HASSAN” ya kalleta tace yaya ina fatan kunyi Nasara kam ko?.

 

Ya gyara zama yace Tabbas munyi nasara ‘‘AISHA” tace to alhamdulillah, Yaciro Wani kyauta na musamman da aka bashi, Yace gashi na baki kyauta, tace A’a nikam ai ba abunda zai min koda na karbi wanna Abun nagode.

 

Maida Kayan shi yayi Aljihu, Yana juyawa Suka had’a ido da mahaifiyar sa, tace hassan inason magana dakai, Yace to mama Yana zuwa tace hassan Nayanke Shawarar Goben nam zaka koma makaranta, Yace Haba mama saura 2weeks fa, Take yaji mari tasssss a fuskar, yasa hanu yana shafa gurin yace to mama naji amma saboda me bazaki bari na k’ara miki koda 1 week bane?.

 

Tace banaso banason ganinka tareda wannam yarinyar tukunna ma kai bakada tinani ne, Naga tanason rabani dakai ne, ‘‘HASSAN” yace to mama naga batada kowa ne shiyasa nakeson tazauna A gidan nam Zatana miki duk wasu ayyuka muddin muka bar ‘‘AISHA” mama bazamu samu madadin ta ba, kiyi tinani.

 

Sallamah sukaji, Tace to kaje ka lek’omin Kaga suwaye ne, ‘‘HASSAN” na sako kai ya hanngi wata Hadaddiyar ‘‘YARINYA” tace sannu yace yauwa Tace ‘‘HASSAN” ko? Yace A ta miko masa jaka tace Maza kashiga min da ita kafin nanuna maka fushi na, yayi murmushi yadauka suna shigowa Tatafi da gudu, Ta rungumi hajiya Tace yaukam dai gani nazo miki Hajiya tayi murmushi, tace Yaya hanya Tace lafiya k’alau ta haye kujera ta zauna, ‘‘HASSAN” na kallonta yace mama wannam fa wacece ta kalli hasan tace ‘yar uwar kace tazo nam ne ma saboda kai, Hassan yace saboda ni kuma mama to ai ni bansan da zuwanta ba, zaraf tasa baki tace A nazo ko dawata magana ce, ya girgiza kai yace A’a.

 

Tace Brother ‘‘HASSAN” inason zamuyi yawo da kai idan Allah ya kaimu gobe, Yace tab to ai kin makara nidazan koma school gobe, tace tab! Ai dasauran kwanaki, Ba inda zaka koma yace to fa kekike da iko dani ko mama, yace to mama ce tace zan koma, tace mama wai haka akayi tace A amma andaga tinda Bak’uwa tazo musamman dakai.

 

‘‘HASSAN” ya ce to ni kinganni banida kudi, tace to ai dakudina nazo dan haka Duk abunda nake buk’ata shi za’a yi da kudina yayi murmushi yace to Allah ya kaimu goben Yayi tafiyar sa yayi Alwala yatafi masallaci, Yaje yayi sallah yadawo Bayan Anyi sallar isha’i Sun hadu za’a ci Abinci yace Au mama ni kirabamin nawa biyu, Zan bawa ‘‘AISHA” tace to fa bayaddaba yace Mama kidinga tausaya mata, mana ta k’one Ahanunta bazata iya girkiba pls mama, Bak’uwar dasukayi ne ta ce A’a mama ya san mata Yadibi Abincin yatafi ya buga mata k’ofa tana budewa ya mik’a mata taja k’ofar ta ta rufe, yadawo suka ci abincin su, aka kunna kallo kowa daya gaji yatafi fanin sa washe gari.

 

 

DA safe misalin k’arfe 10:30 am nasafe.

 

‘‘HASSAN” ya fesha wanka, ya saka turare na musamman, Ya fito da babur din shi, ‘‘AISHA” tafito ta ga yana goge ta tace Inazuwa yau koma hassan?.

 

Yace Zani Wani guri ne Wallahi, Tace Allah yatsare, Tayi komawar ta tacigaba da Aikace_aikacen goge_gogen ta, Ta, wayar ta ne, tafara ringin Tana dubawa, Taga ‘‘ISMA’IL” ne cikin fara’a tadau wayar suka gaisa, Yace Yaya Alhamdulillah Komai sun Fara Dafiya daidai, Ta daga hanu ‘‘AISHA” tace Alhamdulillah.

 

Hajiya ne take tahowa tace zankiraka anjima yace to Takashe, wayar Hajiya nazuwa tace Au Aiki zaki tsaya yi ko Waya, Wannam yarinyar kunen ki na k’ashi ne ko?.

 

‘‘AISHA” tace A’a hajiya cikin zafin nama tacigaba da goge gogen ta, Bak’uwar budurwar nam ce ta fito tana tafiya kamar bazata taka k’asa ba, ‘‘AISHA” ta bita da kallo tazo ta wuce ta kusa da ita ‘‘AISHA” tace sannu ta sauk’e Tabarun fuskar ta tayi tsaki, tace Ke ni Sa’ar kice Ni bana son Haka, ‘‘AISHA” tace Allah yabaki hak’uri, Laifi nane, harta juya zata tafi ta dawo tace ke ta kai hanu Ta mare ta tass, ‘‘A idon hassan, yataho A fusace Ya kai hanu Zai Mare ta ya fasa yace Meyasa zaki Mare ta.

 

Budan bakinta tace Oh! Haba dan na mare ta wani Abune Nifa Ban son raini ne, Yayi murmushi, Yace ‘‘AISHA” kiyi hak’uri, tace Bakomai Yadawo kanta yace Kibata hak’uri, Tace Hmmm Ni Hakan bazai taba yuwuwa ba, ‘‘HASSAN” yace to nikuma idan baki Bata Hak’uri ba nafasa fita dake ‘‘AISHA” tace Aa hassan Karkayi haka bakomai, dan allah Kuyi tafiyar ku, Kaji Hassan, Ya fusata yace to kinci Albarkacin Tasa baki, natafi Idan kinga dama Kizo mutafi?.

 

Ranta ya baci, tace Dakata Hassan Dalilinka nazo gidan nam amma Abunda zaka sakamin dashi kenam A idon wannam k’azamar zaka ci mutuncina to tafiyar ma na fasa ta, ta juya taje Ta zauna Kan babbar wata kujerar( 3sitter), Tana ta ciza yatsa Hasan ya zauna gefe ya kunna kallo ‘‘AISHA” na gefe tana goge,gogen ta, Yasaka tashar (HAUSA) sun saka wani film yanacikin kallo.

 

Kawai yaji An zauna agefen sa Ta dau remote ta saka Music wak’ar ’‘koredo Bello” Takama mamin Ta koma gaban tv tacigaba da rawanta Gogan naka ko kallon ta beyiba, Ta matso sitin shi taci gaba da rawanta, ‘‘AISHA” data gama mofin ta yi tafiyar ta.

 

Tayita tik’ar rawar ta harta gaji ta wuce ta dauko drinks dinta ta bude tasha tasha ta k’oshi, Tace ‘‘HASSAN” rawar ya burgeka ko, ya kalleta yak’ara hade fuskar sa, tace Ai nasan ta burgeka, Ta zauna gefen shi tace dan uwana pls ka saurare ni dan Allah, Ya ce to ina sauraron ko, Tayi murmishi Tace nazo garin nam badan komai ba sai dan kai Hassan d’ina Yayi dariya yace hassan dinki kuma, Tace yes kwarai da gaske Ai mutu karaba Nidakai, Tashi yayi zunbur yace tab, Ni karatu ne Agabana kinji Danasan Zkizo. Da kuwa bazan dawo gidan nam nam kusa ba.

 

Ta yi murmushi, Tace Ai aikin gama yagama Ni banida wanda ya kwanta min A raina kaf duniyar na Face Mumtum, d’aya Ba kowa bane sai kai, Masoyi na ‘‘Tayi murmushi ta nuna shi da d’an yatsa, yace Tab! To ai kin makara Ni Inada wacce na keso, Tatashi tace Wht…. Tana girgiza kai tace Wacece Haka, Ai kuwa Ta tara wa kanta bala’i Inka isa kafada min ko wacece ita, Ta juya tasake juya tace Kakalleni sama da k’asa ba A yi macen dazata hada nema dani ba, ya yi murmushi yace to na yaushe kuma Ai aikin gama yagama.

 

Tsabar kishi Jikinta karkarwa ya fara yi, take Aljanunta suka tashi, Hankalin hassan yatashi Ya tafi da bibo ruwa a k’aramin kofi yayi adu’o’i Ya tafo mata A ruwa Ya fesa mata Take Ta zube Kan kujera Ta zauna, Tayi shiru Yazauna gefen ta yace sannu Tayi shiru batace komai ba, Hassan Tace ki dan kwanta ki huta, kinji ta kishi gide bacci ya dauke ta Shi kuma ya koma cikin d’akin sa ya zauna yayi shiru yayi ta gumi Abun tausayi !.

 

 

To bee continue……

7=8

Tsabar kishi Jikinta karkarwa ya fara yi, take Aljanunta suka tashi, Hankalin hassan yatashi Ya tafi da bibo ruwa a k’aramin kofi yayi adu’o’i Ya tafo mata A ruwa Ya fesa mata Take Ta zube Kan kujera Ta zauna, Tayi shiru Yazauna gefen ta yace sannu Tayi shiru batace komai ba, Hassan yace ki dan kwanta ki huta, kinji ta kishi gide bacci ya dauke ta Shi kuma ya koma cikin d’akin sa ya zauna yayi shiru yayi ta gumi Abun tausayi !.

 

Sak’e_sak’e yake A cikin ‘‘ZUCIYAR SA” shin wannam yarinyar mai takeso danine kam?, A firgice Ya juya Boka k’ofar sa Akayi Yataso Ya bude, Yaga mahaifiyar sace, Tace ‘‘HASSAN” lafiya naga ‘yar uwar taka kabarta ita kadai A falo tana bacci, ya girgiza kai mama lafiya k’alau wallahi, Tace to Kazo daman inada magana dakai, cikin ladabi da biyayya yace to mama, Yabiyota abaya suna tafe Har suka k’ariso falo ta zauna shikuma na zauna ya durk’usa A gaban ta Yayi shiru, Ta ce to Kaganta nam yar uwar kace Dan kai tazo gidan nam dan haka ka kula da ita sosai, Ina fatan ka fahim ceni yace to mama, Sunacikin tadin su, tafar ka daga bacci tayi mik’a ta bude idon ta tace A mama yaushe kika dawo?.

 

‘‘HASAN” kuwa ya sunkuyar da kansa K’asa ta kallishi tace Marar gaskiya dole ka sunkuyar da kanka ai, Tatashi tayi shigiwar ta bayi tafesa wanka tafito tana kamshi.

 

Tace Mama Zan d’an fita nazaga gari, tunda yaya ‘‘HASSAN” yak’i yawo dani, Zafar yayi yace Allah yakiyaye Hanya, Tace Amin Ai kamin Komai dakace Allah yakiyaye Hanya, Mahaifiyar sa tayi murmushi tace to Kikula karkiyi Nisa fa kinga garin namu Balafiya sosai yanzu kinji ko?.

 

Tace to Mama, ta yi ficewar ta ta barsu agurin suna ta hirar su.

 

‘‘AISHA” kuma tana komawa bangaren ta tacika alk’awarin da tadauka ta kira numbar d’an uwanta, ‘”ISMA’L” tanashiga yace tab! Sai yanzu zaki k’irani Ko nayi fushi Tace a’a yi hak’uri ina sauraron ka bani labarin gurin Aikin naku?.

 

‘‘HASSAN” yace Ai alhamdulillah komai na tafiya yanzuhaka Nasamu alheri sosai, Zan turo miki da kudi, Tace A’a kabarshi kawai bana buk’ata kaidai shawarar dazan baka karage rigimar kannam Yace To shikenam Yaya Insha allah bazan baki kunya ba, Kota wace hanya indai zaki ji dadi koda ni zansha wahala bandamu ba tace a’a gaskiya kana ji da yayar kannam to Allah ya kiyaye min k’anina yace amin, Wani ne ya kwala masa k’ira kai hassan kazo mana kacigaba da aikin da kake yi yace to ganinam ina zuwa tace ana k’iran ka ko yace A tace to sai anjima ya tafi cikin sauri, yace Maigida Kayi hak’uri Nayi waya da gida ne.

 

Ya Kama kwale_kwale ya haye sukacigaba da tafiya, Har suka iso wani K’asur gumin daji, suka tsaya ya fito dawani k’aramin akwati yace gashi Kana zuwa kan wannam Dutsen ka jefa shi k’asa kayi maza_maza ka dawo kaji kam idan kuma ka bata lokaci duk abunda ya faru dakai to nifa baruwana.

 

‘‘HASSAN” yadauka yayi tafiya mai nisa yajefa akwatin Kamar yadda maigidan nashi ya umurcesa Ya juyo yana tafiya Sai ya hangi jikin wata bishiya kamar mutumne Yake d’aga masa hanu yace kai Karkuma naje Maigida yatafi yabar ni, Yace kai sainaje naga ko menene, Yatin karo gurin Sai yaga wata Kya_kyawar mace ce, Tana ganin shi tace Dan allah ka taimakeni na maka alkwarin Ko nawa kake buk’ata nikuma zan baka.

‘‘ISMA’IL” yayi shiru ta sake maimaita abunda take fad’a yace Naji Zan tai makeki amma saikin fadamin Dalilin Zuwan ki wannam dajin.

 

Tace naji zan fad’a maka amma ka tafi dani daganam idan har sukazo dagani harkai bawanda zasubari, Yace suwaye ne haka, tace Kaidai bakasan suba Amma kayi Abunda na umurceka, Yace to tashi mutafi Ta mik’e Sai ta fadi tace bazan iya ba sai ka talkafamin yataho tadafa kafadar sa, Ya cigaba da tafiya da ita yana zuwa dai_dai inda Maigidan shi yake, ya tarar ba kowa yace Shikenam kin ruguzamin lissafina nayiwa yaya ta Alk’awari Amma gashi zata daukeni Mak’ar yace Kuma duk kekika jawo, Tace nawa yake biyanka nizan biyaka fiye danashi idan har kafitar dani dawannam dajin, yace Ta ina zaki iya biyana tace Kai kam bana maka alk’awariba Yace to naji zakai zubanyamini kudin da suke biya na sau biyu tace A yace suna biyana Naira dubu d’aya ne duk Bayan kwana d’aya, Tace naci nikuma zan baka dubo goma duk Kwana d’aya, take ‘‘ISMA’IL” yace shikenam Namiki alk’awarin Zanyi iya ka k’ok’arina amma ina so kibani Labarin Abunda ya jawo zuwanki wannam dajin?, tayi murmushi tace Aikin kud’i zakayi Idan kudin bemakaba nizan k’ara maka sannam zanbaka labarin zuwana nam wajen Amma sai munbar yankin Dajin nam.

‘‘HASSAN” yace to Naji Amma nima bansam hanyar dazata bulle mana zuwa Inda kikeson zuwa ba, tayi shiru tace Gama ga Allah Kaodai mubar Gunnam, sukacigaba da tafiya sunyi Tafiya mai Nisan gaske wanda hassan ya lura yarinyar nam bata saba wahala ba gashi kafafunta duk sun Far_fashe da kyar take tafiya, Sunacikin tafiya Wanta iska mai k’arfin gaske ce take tin karo su hassan yace kidaga k’afa kafin iskar nam ta cin mana, tace toh suna tafiya tana yamutsa fuska, Har zuka iso Daidai wata k’atuwar bishiya wacce gefen ta akwai wani K’aramin kogo, Hassan yace dakata Barin duba mana nam kila ma pake A nam, tace to ta nemi gu tazauna Hassan yaciro wayar sa ya haska gurin daga bisani yasaka hanun sa yashare ciki tass ya karyo wasu itatuwa ya had’a Abun kwanciya guda d’aya da kuma na zama yataho gunta yace zamu iya fake wa, ta tashi ya tallafa mata Ta zauna kan gadon daya hada na karare Ta mik’e kafafun ta Hassan ya kalli k’afafuwan ta suna jini, Yace Sannu tace yauwa Ya hada itatuwa Ya dauko duwatsu guda biyu yayi ta gurzasu har saida yasamu wuta ta kama, Tayi mama kin hassan sosai, Suna cikin wannam yanayin ne Wata iska tazo ta tirnik’e sannam aka sake ruwa anyi Awanni Ana zabga ruwa, Har bacci Yadauketa, shikuma hassan yana zaune, Ahaka ya kwana cir da idon sa batare da ya rintsa ba.

 

Ta na tshi ta nemeshi, bata jishiba saita farajin takun sawu, tayi shiru Ganin mutum tayi yashigo Da Wani katon tsun_tsu a Hanun sa, Taga Abokin tafiyar ta ne sannam hankalinta ya kwanta Ta ce Ina kaje haka yace Abinci naje ne mo miki, Tayi murmushi, Ya fige Tsun_tsun tas..

Sannam Yaciro Wata wuk’a ya fede shi ya gyara ya sake hada wuta ya gasashi ya gasu sosai, Ya mik’a mata tace ai ni banacin naman nam, yayi murmushi yace To ya yaga naman biyu yasa abakinsa yanaci, yace mata kice mana Kar yunwa ta galabaitar dake, Bataso hakadai ta karba tafara ci dataji dadin naman tacinye tass ta koshi, Yace Ya sa hanun sa ya dibo mata ruwa tak’afa kai tashi yanazuwa yana dawowa harta koshi, Tace Na gode Yayi murmushi yace Ba komai, Yanzu zamutafi kokuma tace duk yanda kace, Yace Yanzu dai k’afar kinnam Barin nemo wani magani Yakama mu zauna anam har kidan samu sauk’i naga kafar taki duk ta farfashe, tace Karsuzo su samemu nake tsoro yace A a kikwantar da hankalin ki insha allah ba yadda za’a yi susame mu.

 

Ya ta shi ya fice ta dinga ballo ganyayen ”ya”yan itatuwa har kusan kala goma sha, Sannam ya taho dazu Yasamu wani itace yayita rarake sa har saidayiyi gurbi inda zaka zuba ruwa sannam yayita murza ganyayen har saita suka fitta ruwa yasa ta mik’e kafafun ta ya zuba mata ruwan tace wayyo allah akwai zafi yace Daman dole zakoji zafi allah yabaki lafiya.

 

Akwana na a tashi sukayi kwana hudu, Kafar ta ta dazo ragas kamar bata taba jin wani kunburi Ba, Tayi mamaki sosai, Tace Gobe in allah ya kaimu da rai da lafiya zamu bar nam gurin kaji, Yace to Ai ni sai yadda kikace, tayi murmushi ta e meyasa Kakeson tara kudi, ne kam?.

Yayi murmushi yace‘‘BALAIFIN MU BANE” dolece ta sa mu Sonake Zan ginawa yayata gida Tazauna itama kotasamu sawaba a rayuwar ta Tayi murmishi tace lallai Kanason yayar kannam zan so nima na ganta, Yace dagaske tace A yace to shikenam zan nuna miki ita, Tayi murmushi.

 

Washe Gari DA safe suka sake shiga cikin Daji Tsundum, suna cikin tafi sukaji wani wari Na dosusu, suka toshe hanci, suna k’arisowa suka tarar da gawar wakin mutanene Ankashesu Har sun rube, Hankalin ‘‘ISMA’IL” ya tashi, suka wuce gurin sunyi tafiya mai nisa sun zauna suna hutawa yace mata kai ni hankalina baitaba tashiba irin wannam yawan gawar wakin danagani an koshesu, to wana laifi sukayi haka dan allah kai Duniya abun tsoro ce?.

 

Murmushi tayi tace Hmm ai ni nasaba da hakan, Nima kaina bansam dalilin dakkoni wannam dajin ba, Haka suke kashe mutane ba gaira babu dalili, tafashe da kuka.

 

‘‘ISMA’IL” ya rarrashe ta yace Shin maiya kawo ki wannam dajin yakamata yau kam ki sanar dani kadam dagacikin labarin ki? gaskiya tace to shi kenam.

 

 

Nakasan ce ‘yar gata mahaifina mutum ne mai tarin Arzik’i yanada dukiya sosai, wacce shi kansa bai san adadin ta ba.

‘‘ISMA’IL” Yace allah sarki ina sauraron ki? Gaskiya Amma dai shikenam.

Tgirgiza kai tace, Natashi cikin gata Sannam mahaifina Bayason yaga Kana rena na gaba dakai, sannam kullum cikin taimakon talakawa yake, watara yana zaune Al’umma sukayi gangami sukace, Suna son yashiga harkar siyasa dan taimakon marar sa k’arfi, ‘‘TALAKAWA”yace A’a bazai shiga harkar siyasa ba saboda Siyasa tana zubar wa da mutum kimar sa da darajar sa, sannam kuma duk yanda kayi bazaka iyama mutane ba, Yak’ara dacewa tabbas dazan shiga siyasa watarana kuzaku fara zagina Ni kubarni banason shiga harkar siyasa, sukayi sukayi Yak’i Amincewa.

 

Bayan yadawo gida ya Zauna gani gashi ga mahaifiya ta yanemi shawara Agunmu muma mukace, A’a bamason yashiga siyasa Abukamar wasa Wasu sukayita sukan mahaifina Abun yana matuk’ar bata masa rai sosai Amma shi mutum ne mai Hak’urin gaske.

 

Saboda kullum idan muna zaune dashi yakan cemana nida mahaifiyata muzama masu hak’uri Zamuga cigaba sosai A rayuwar mu.

Tafashe dakuka! ‘‘ISMA’IL” ya rarrashe ta tayi shiru, Yace mata baya ganam kuma sai me ya faru?.

Tayi murmushi! Tacigaba da bashi labari, Tace Watarana ‘‘FAMILY” namu mun hadu Manya da yara daman munsaba duk Bayan wata muna Shirya Zama na musamman Duka dangin mu Mukan hadu manya da yara Mutattauna Abubuwa Na musamman Dangane Da abunda ya shafemu, Akan tara kudi Kodan gaba buk’atar wani ko Rashin lafiya Acikikin wannam Gidauniya ta ajeyar Ake komai, mahaifina shine Babba, Kowa yana bashi girman sa dai_dai misali, Bayan Angama Taro Munyi rakiyar Masu Tafiya Muna dawowa Kawai Aka tare mu Ahanya Mahaifina yanaji Yana gani Akaciro ni a mota mahaifiyata tana kuka shima yana kuka, Sukace Yana yunkirin wani Abu sai sun kashe ni.

 

Haka suka rabanidashi Kuma suka karbe wayata Sannam suka yi awun gama da mu bani kadai bace munada yawa Mutanen nam basuda imani kisan killa suke wa mutane Suba kudi suke bukata ba Nina gaga fahimtar wa’yanna irin mutanene su.

 

‘‘ISMA’IL” ya kalleta ya girgiza kai yace Gaskiya natausaya miki Ta girgiza kai tace Ko, ‘‘ISMA’IL” yace yanzudai to sai kitashi mu kama tafiya nasan lallai suna nam suna bibiyar mu, Begama rufe bakiba yace Ance ai gata chan, Idanun ta suka zazzaro, Suka Kama gudu, kafin kace Mai Antare su tako ina, Rik’e kai tayi tazauna a k’asa tafara kuka tace Wayyo Allah Bakasan komai ba gashi na jefa ka cikin damuwa.

‘‘ISMA’IL” yadaga Kansas ya k’are musu kalla shima ya durk’usa yace K’addarace Bayanda muka iya hakan Dole sai ya faru, Karkiji komai Allah Natare damu….

9=10

‘‘ISMA’IL” yadaga Kansa ya k’are musu kallo shima ya durk’usa! yace K’addarace Bayanda muka iya hakan Dole sai ta faru, Karkiji komai Allah Natare damu….

 

Fuskokin su gaba d’aya a rufe, Da kagan su kasam Ba imani A tattare Dasu, wani bushe_she ne Ya taho ko wanne daga cikin su ya yakoma gefe ‘‘ISMA’IL”, yaka kallon sa, ya daka masa tsawa, Kai yaga ko gizau beyiba, ya tuntsire da dariya yace lallai wannam Hatsabibi ne kai Har Ka isa Ka dauke wannam (YARINYAR)?.

lallai ka aikata babban kuskure Ita wannam dakake gani ‘yace Gawani Attajirin mutum kuma shi mutumne mai taimakon Al’umma, Munbi duk wata hanya Domin Nakasar dashi, Amma shidin Mutum ne me tsananin k’wazo, Yagagare mu, ‘‘ISMA’IL” cikin tsaurin ido da rashin tsoro Yace, Maizai hana Ku karbi dukiya Ku rabu da ita?.

 

Cikin mamaki, yace Ai muba dukiyar bane Abun daya dame mu, ‘‘ISMA’IL” yace to me ya dameku Naga duk wani Mutum a duniyar nam bawanda za’a masa tayin zunzurutun k’udade wanda yasan idan har Yasamesu zai koma cikin mutane yacigaba da yaruwar sa cikin kwanciyar hankali, Shugaban tsagerun nam yace wannam kai ya dama kagan ninam wannam yarin yar Kawai burina, Ganin ta bata numfashi a doron k’asa.

 

Dajin wannam Batun nashi, sai ta fashe dakuka, tace Dan allah karkukashe ni, Kufadi duk Abunda kuke so na muku Alk’awarin zan baku.

 

Murmushi, yayi yace Ai badaga ni bane nima umur ni Aka bani Dan haka dole Zan zartar da kukunci Lokaci kawai nake jira Ana bani umur ni Tabbas Zan ai watar, ya daga bindiga sama yayita Harbata har Sai da harsashin da suke cikinta suka k’are tass!.

 

Sake fashewa da kuka tayi, ’‘ISMA’IL” yace haba kidaina kuka, ya share waye fuskar ta tace, Dole na nayi kuka saboda yanzukam nasan tawa ta k’are, ‘‘ISMA’IL” yayi murmushi ta kalle shi tace kai gaba d’aya naga hankalin ka kwance, Isma’il yace ai ni nasaba dan Wani namin barazanar mutuwa Abun bai damuna, saboda ni natashi cikin k’uncin rayuwa Bawanda yake tallafamini sai ‘yar uwa ta guda d’aya tilo, Nayi Alkawarin fuskantar duk wani k’alubane Idan har ita zata kasan ce cikin jin dad’i da kwanciyar hankali, Ta share ragowar hawayen fuskar ta tace Allah sarki!.

 

‘‘ISMA’IL” ya k’ara gyara zama yace mata ki kwantar da hankalin ki idan har kina tare dani Insha Allah, zamu samu mafita, Kinji kidaina Tada hankalin ki, Nam da wa ‘yan su yan kwanaki tace to shenam.

 

‘‘AISHA” kuma tanachan ta shiga damiwa yau kimanin Sati biyu kenam, babu labarin k’aninta ‘‘ISMA’IL” tana zaune tayi tagumi, Abakin gate Da yamma liss! ‘‘HASSAN” yafito yayi shiru yatar da ‘‘AISHA”tayi tagumi ya zauna agefen ta yana kallon ta ya k’ura mata ido yace ‘‘AISHA”tinanin me kike haka?.

Tayi murmushi tace kade bari kawai, Yau sati biyu kenam lambar ‘‘ISMA’IL” ko na k’ira bata tafiya shine gaba d’aya nashiga cikin damuwa saboda shikadai ya ragemini Bana so na rashi banason wani abu ya sameshi amma baya jin magana haka yayi nisa dani, ‘‘wani mirmushi ‘‘HASSAN”yayi yace haba kidaina wani sama kanki damuwa insha allah yana nam lafiya kinji Aisha.

 

Gyad’a kai tayi tace Amin, turo gate Akayi da karfi Sanadin hakan, Yagauce daga inda yake, ‘‘ISMA’IL” yace ‘‘AISHA” maza ki gudu gate, Ina kafin ta yun k’ura Ya jubgo Akanta, inda take ya nufa da gudu ya tura gate din gefe da karfin tsiya, Ya samu ya jawo ‘‘AISHA” ko motsi batayi, Yana juyawa ya dan ganin waye ya tab’a gate dinnam har hakan tafaru, Ganin mitumiyar sa yayi Agefe yace dama kece kika taba abunnnam Amma ke gaba d’aya banga amfanin zuwanki Gidan nam ba, Take ya daga wayar sa ya k’irawo Abokin sa yataho da mota sukadauke ta Abun tausayi suka sak’ata amota Suka wuce da ita Asibitin (Fravet) suna zuwa aka karbe su hanu bibbiyu, Likita na zuwa ya ce, Za’a mata aiki Amma lallai sai kun biya kudi kafin A fara, ‘‘HASSAN” yace nawa ne, Likita yace Su nemo naira Dubu Dari Da hamsin, Dajin wannam kudaden sai k’irjin Shi ya buga yace to likita zandawo yanzunnam.

 

Kama hangar Vida yayi yshigo A gigice, ya durk’usa a gaban mahaifiyar sa yace Mama ki bada kudi Za’a yiwa ‘‘AISHA” ai ki wani irin kallo ta masa tace nikuma ina ruwana tunda ba’a bunda yasameka To ai Alhamdulillah, Ni banida kidi, ‘‘HASSAN” yace A’a mama karkice haka, itannam fa mareniya ce mama tace dakata Ba’a bunda zanbaka saidai tamutu ni baruwana, Rik’e kai yayi ya tashi, Ya fice waje Ya tura mashin Din sa, Waje Ya yi buga buga ya sayar da ita naira dubu d’ari, ya koma asibiti yace likita gawannam dan allah a fara mata aiki dan allah likita take yanke, Suka shiga da ita d’akin Taimakon gaggawa,(imagency), sun bata fiye da awad’aya ‘‘HASSAN” Kuma yanata sintiri yaje yadawo yaje ya dawo, likitocin ne suka tafito babban likitan yace, An samu Nasara, Amma saidai Kanta ya dan bugu, Amma zata samu lafiya, farinciki ya kama ‘‘HASSAN” aka chanja mata d’aki hassan yana gefen ta tana ta bacci bata far kaba.

 

‘‘ISMA’IL” yaji wani Abu a jikin sa, Yace to kodai wani Abu yafaru Da ‘yar uwa tane Dole yaukam insha allah zamu nemi mafita A daren yau ko mu tsira kokuma sukashe, Tabbas acikin biyu za’a yi d’aya.

 

 

To bee continue…..

 

‘‘ISMA’IL” yaji wani Abu a jikin sa, Yace to kodai wani Abu yafaru Da ‘yar uwa tane Dole yaukam insha allah zamu nemi mafita A daren yau ko mu tsira kokuma sukashe, Tabbas acikin biyu za’a yi d’aya.

Murmushi, Tayi tace Haba kaiko, Nikam banga wata hanyar dazamu tserawa wannam gun_gun ‘yan tadddan ba, Kasan sun ‘kara saura komai.

 

murmushi ! ‘‘ISMA’IL” yayi yace Idan harkin amince shikenam, ta girgiza kai tace Na amince Dare ya raba, Misalin k’arfe, 12:17am Tana bacci ‘‘ISMA’L” ya tatta ba ta ta farka, Ya ce gawannam Ki wanke fuskar ki, Ta karbi ruwa ta wanke fuskar ta Ahankali Suka Fita Suka yita gundun tsira sun dau sa’o’i suna gudu, Ta kama Haka, tace ‘‘ISMA’IL” zan mutu bazan iya guduba na gaji, Ya tsa Sukayi ‘yan mintoci, Sannam sukacigaba da tafiya, suna cikin tafiya ‘‘ISMA’IL” yace lokacin Sallah yakusan k’aratowa gare ya kusan wayewa, koda sun taho bazasu cinmana ba saboda mun musu nisa, sa hanun shi yayi A aljihun sa, Yajire yayi shiru, Tace yaya naga kayi shiru, ‘‘ISMA’IL” yace Wallahi Na manata wayata A baya amma bakomai damuwata daya ne, ‘‘AISHA” amma bakomai sukaciga da tafiya Suna tafiya “ISMA’L”, yadaga gansa yace (ALFIJIR) ya fara ketowa muk’ara sauri, Suka cigaba da tafiya, Hamma tafara yi, Tace ‘‘ISMA’IL” yumwa nakeji, ‘‘isma’il” yace Ai yazama dole na nemo miki Abunda zaki sa Acikin ki amma mudan k’ara gaba tukunna.

Sunacikin tafiya, ya hango wata bishiyar (TUFA), Yace jirani Anam ya na k’arisawa ya hau ya tsinko, Ya taho Ya bata gaba d’aya guda biyu taci taji to k’oshi, Suka tashi sukacigaba da tafiya tafiya suke har gari ya gama Waye wa, Suna isowa Wani kogine, Iya ganin ka, Tsayawa sukayi, ‘‘ISMA’IL” yace to fa, Yanzu yaya zamuyi kenam, Wannam ruwan Kodai zamu shiga ne, Ta girgiza kai tace a’a gaskiya Mu dakata ko Allah zai Kawo mana mafita, ’’ISMA’IL” ya kalleta yace to shikenam, Suka nemi gu suka zauna, Isma’il yace Nikam Inane Garin nam Naku haka?.

Tace, (ADAMAWA), Mubi yayi murmushi yace insha allah kamar kin koma gida Amma dan Allah Kicika min Alk’awarin da kika dauka, Karki Karya zuciyar Maraya, tayi murmishi, Tace Ai nina maka Alk’awari, karkaji komai.

Hot Romantic Hausa Novel Complete Wattpad

Sunacikin Maganar Saiga wani Yataho da ‘‘KWALE_KWALE” isma’il yawota yayi harta yunk’ura zatayi magana janta gefe yayi suka labe, kwale_kwalen Yana isowa Mutumin ya fito ya jawo kwale_kealen, yayi fito sau uku, Ya sauk’e wani Akwati, isma’il ya rufo da gudu yana ganin isma’il ya tsaya yace kai Meya kawo ku wannam gurin Isma’il yace Ka tai makemu Akwai Masu bibiyar mu, Yayi mirmishi, Yace Nima ina musu Aiki Amma idan Har kunada kudi Ba’abunda bazan mukuba, Isma’l suka kalli juna, Isma’il yace Bamuda kudi gaskiya, Mutumin Ya fara kunce kwale_kwalen shi, Harya hau zai tafi, yayi murmushi yace kozo kushiga wani farin ciki Isma’il besan lokacin da ya taho ya rungumi mutuminnan ba tsabar murna, Yashiga ta taho ya rike hanun ta mutumin ya tada ingin girgin ruwan nashi, Sukayi ta tsula gudu, Sai da sukayi Kwana uku akan ruwa suna tafi, Sannam sukazo wani giri na musanman, A tsakiyar ruwan.

 

Ya umurci su da su buya inda baza’a gansuba, yafita bewuce ‘yan mintoci ba, Ya dawo ya tada ingin nashi, suka cigaba da tafiya, Wuni sukayi kass! Sannam suka iso bakin ruwan suna sauk’a isma’il yadinga masa godiya, Mutumin yace bakomai karkudamu Allah ya k’iyaye hanya har sun Kama hanya isma’il ya jiyo yace Malam karkagaji dani, samu A hanyar dazata kaimu Adamawa, Mutumin yayi shiru yak’irawo wani yace ciri wasu kudade yace Inaso sai ka ke bodar ADAMAWA, ka nuna musu kabar su, Anam kaji cikin girmamawa, yace to Sukajuya Yasaka su Awani kwale_kwalen, Sunata tafiya Har dare ya musu Suna tafiya ga sanyin tsiya, ‘‘ISMA’IL” yacire rigar sa ya lulluba mata, duk da haka tanata kar_karwa.

 

Kwanwa sukayi, Gadari ya waye Yana zuwa daidai_wani Guri ya Ajesu ya nuna musu, Yace Daganam Zanbar ku akwai jami’in tsaro A gunnam, Isma’il suna tafiya Daga nesa wani soja ya daka musu tsawa, Isma’il yadakata yanazuwa yace ina katin dan kasar ka, Isma’il yace Katsaya zan maka bayani, Kafin kace me yayi wani yare sojoji suka dawo kan isma’il tare da yarin yar nam Sukace bamu yadda dakaiba sato ta kayi, dan ta’adda ne kai.

 

Ita kuma gasanyi ga cizon sauro ga wahalar da tasha, ‘‘ISMA’IL” yana kallonta kawai ta zube ta fadi k’asa maza maza aka dauketa Shikuma isma’il Suka kamashi, Aka daure shi suka masa dukan tsiya sai ya fada musu Yanda yayi yasato Yarinyar nam Yace, nima Kawai tsautsayi ne ya had’ani da ita, duk abunda isma’il ya fad’a basa yadda.

 

Daga karshe Aka juya kan isma’il Aka sa mar Bindiga Akayi Daya dagacikin sojojin Yace Zamukashe ka tinda ka k’i fada mana gaskiya bakin isma’il yana murmushi Bakin sa najini Yace Gaskiya ta kenam, Wannam zalincin da mai yayi kama, ‘‘AISHA” nagaza cika miki burinki Ya fashe da kuka, sojojin suka tin tsire da dariya sukace dan soyayya kenam.

 

Tau! Tau!! Tau!!! k’arar harbe kakeji, sau uku, Cikin firgici ‘‘ZUBAINA” ta farka, Tana bude ido ta kama hawaye, Tace A ina nake, Wani soja ne A gefen ta yace kikwantar da hakalinki, Azzalumin War haka ya shek’a kiya farat tayi tace ! Kar ku aikata kisan kai ‘‘ISMA’IL” Ba dan ta adda bane. Sojon yace Ai war haka ya mutu harbin nam daya tashe ki Ai shi A ka harbe, Dur k’usawa k’asa tayi takama kuka, Tana cewa Da nasan haka zata faru dashi Da tun A baya nina mik’a kaina sun kashe ni, Yanzushikennam ai kun kyauata, Ta tashi tana kuka ta fito.

 

Tace Wayyo ni ‘‘ZUBAINA” dawana ido zankalli ‘yar uwar ‘‘ISMA’IL”. Na jawo An kashe mata dan uwa.

 

Fitowa ‘‘ZUBAINA” tayi A gigice Tace Wayyo ni ‘‘ZUBAINA” dawana ido zankalli ‘yar uwar ‘‘ISMA’IL”. Na jawo An kashe mata dan uwa Tanata famar rusa kuka, Jim kadam, Sojan dayake kusa da ita ya daka mata tsaya, Ta firgita Ta tashi zata gudu ya dakatar da ita, yace Hak’uri zakiyi ki dau dan gana ba kuka zaki tsaya yimana anam ba, Ya sakota a gaba sukazo har wajen da Ragowar sojojin suke, Kyalla ido tayi taga Ba ko gawar isma’il ta kama bude_dube tamkar wata mahaukaciya, Chan ta hango shi A kwance yana numfashi sama_sama.

Tahowa tayi dagudu ta juya shi, ya kallita yace, kibani ruwa k’ishin ruwa nakeji Hankalinta ya kara tashi, Ta hango wani Rowa A kan wani tiburi, ta ruga aguje Ta dauko, Ta fara bashi yana sha kenam wani fusataccen soja yayi boll, da robar ruwan,‘‘ISMA’IL” yace kinga yanda rayuwa ta kasance dani ko?, (BALAIFIN MU BANE) bamuda kowa Allah ne kadai gatan Mu, Burina koda na mutu bana so kisanar da ‘yar uwata hakan, ‘‘ZUBAINA” tafashi da kuka!.

 

Wani Soja ne, Ya sauk’o a wata motar yak’i Suna ganin shi, gaba d’ayan su suka k’ame, ‘‘ZUBAINA” tata ho da gudu, ta durkusa, Harwani soja ya kai hanu zai dakatar da ita Ya nuna mar yatsa, ya koma gefe Ta ce, Ka taimakeni Yanda allah ya taimake ka, Dan uwanane Bashida laifin komai, yayi murmushi ya kalleta, Yace kekuma to meya biyo daku nam hanyar?, ta ke ‘‘ZUBAINA” tafara bashi labari sai da yayi kwalla, Yace maza maza A na baku umurni A kula da yaronnam take yanke, Su kauko ‘‘ISMA’L” zubaina tayi mamaki sosai, tace yallaboi nagode sosai, Banzaci akwai wanda zai taimake muba sai gashi Allah ya kawo ka, ‘‘ISMA’IL” shi mutum ne mai tausayi bashida kowa marayane kaga duk abunda ya faru dashi nice sila, Bayan Wasu ‘yan Sa’o’i gaba d’aya dakarun sojojin suka taru, Kowa ya tsume, Shi babban nasu ya dinga musu fada, Daga bisani ya umurci kowa ya koma bakin Aikin sa, Ya dawo inda zubaina take ya zauna gefen ta ya tam baye ta ke ‘yar wana garine, ‘‘ZUBAINA” tace ni yar Ada mawace Nida mahaifina da mahaifiyata muna zaune a garin (MUBI), yace Allah sarki Muje wajen d’an uwan naki, tace to sukakama hanya, suna tafe tare da ita Duk wajen daya wuce k’ananam sojoji sai sun rasa masa, kai Gidan soja Akwai Biyayya, Shiga sukayi ‘‘ISMA’IL” yana bacci harda munshari ‘‘ZUBAINA” tana ganin shi taji sanyi A ranta tayi murmushi ta koma gefe tayi zaman ta a kusa da ‘‘ISMA’L”, Haka suka yita samun kulawa a wajen babban sojannam har na tsahon kwana bakwai(7), ‘‘ISMA’IL” yayi garau kamar bashi ba.

 

‘‘ZUBAINA” tana zaune tayi tagumi! ‘‘ISMA’IL” ya hangota suna hira dawani, jami’in (SOJA), Yataho wajen ta, ya zauna gefen ta, yadau k’ananam duwatsu guda biyar zuwa shida, yana d’an jefa su nesa, yace me ke damun ki ne kam?.

 

Tajuyo tace o ‘‘ISMA’IL” kenam abunda kedamu kawai, dai bazai wuce nagani Gani ga mahaifina ba, ga Mamana ‘‘ISMA’IL” yayi murmushi yace karkida mu ai zamu tafi nam bada dad’ewa ba kinji?, ta gyada kai tace shikenam.

Suna zaune suna ta hirar su, suna ha go shugaban sojojin sukatashi.yace a’a kiyi zamku nazo nima tataku hirar ne.

 

”ISMA’IL” Yace bakomai. Suna zauna hira takai hira sojan nam yace,Abokina ”isma’il” kake dasuna ita kuma,”ZUBAINA” ko?. murmushi yayi yace Gaskiya da jarumine yanzu, Kai baka tsoron Yar uwar taka ta rasaka?, murmushi ismail yayi yace haba yallabai… Idan har zata kasance kikin farinciki tabbas ba komai burina yacika, murmushi, sojannam yayi ta tafa wa isma’il, yace wannam shk’uwar ta ku bazata misal tuba, na jinjina maka haka akeson dan uwa yabamu da ahalin sa, bawai ya watsar da suba ‘‘ZUBAINA” wani murmushi tayi tace nima sonake naga wannam ‘yar uwar tashi dayake ta bamu labarinta gaskiya.

 

Wata motar sojojine ta taho ta faka, wasu sojojine na musamman suka fito suka tinkaro inda babban maigidan nasu nake zaune, cikin girmama wa suka sara masa sukayi wani yare wanda bakowa bane yasan abunda suke nufi ba sai su ya su, Rungumar juna sukayi, Ya gabatar da isma’il tare da ‘‘ZABUAINA” yace dasu yaukam yakamata ashiga daku cikin garin (ADAMAWA) mubi, take wani farinciki ya lullube zubaina, tace isma’il gaskiya ina cikin farin ciki, kallonta yayi kawai yayi murmushi, Sukayi bankwana, Gafe da gefen su, Sojojine Akamusu rakiya har izuwa cikin garin (ADAMAWA), aka sauk’e su Anam kuwa suka zama abun kallo, isma’il yace ‘‘ZUBAINA” kinga bamuda kudin motar da zamu tafi izuwa garin mubi, yanzu yaya zamuyi kenam, gashi wayata tana chan ta salwanta, Yana tinani yataba aljuhun rigar sa futu_futu, Yaji nauyi kamar kudi, yaciro yace la ikon allah duba kiga kudi ya lissafa su naira dubu goma sha d’aya, yayita tinanin a ina yasamu k’udaden nam, sai yayi murmushi, zubaina tace fadamin naga kayi murmushi yace bawanda zai mana wannam abun fa ce, sojan nam kai Allah ya masa albar ka, isma’il yace yanzu ya kamata mu sayi kaya dazamu saka kafin nam nushiga motar dazata kaimu zuwa garin ku daganam ni sai kisallame ni nakama gabana, shiru tayi tace yanzu shikenam muna zuwa garin mu mun rabu kenam, isma’il yace A mana ta gyada kai tace to shikenam, take suka sayi kaya kala biyu, Na naira, dubu uku da d’ari biyar.

 

‘‘ZUBAINA” tafito tayi kyau sosai, tace da isma’il kayan nam basumin kyau ba gaskiya ko, yayi murmushi yace In ba keba ina mukaga lokacin wani Gaye nima kayan gwanjo nasaya riga da wando, Kingan su zasujima ina saka kayana ni baruwana dawani kyale_kyale tayi murmushi tace to shikenam, suka kama hanya Suka shiga mota, Sunata tafiya sunyi tafiya mai nisa sosai Anzo wani waje ‘‘ZUBAINA” tatiwa matuk’in motar magana tace Sauke mu Nam ALHAMDULILLAH, ‘‘ISMA’AL” yace kai garin nam Naku Gaskiya Ya burgeni sosai, murmushi Zubaina tayi tace(MUBI) garin Dadi kenam ta nuna Masa wata hanya tace idan muka bi nam Har Gidan mu, Tana murmushi suka kama tafiya Wani gida suka iso Kaf Illahirin Ayarin jerin Gidajen Wajen Ba gida kamar Wannam Kuma Cikin TALAKAWA, mamaki ‘‘ISMA’IL” yake yace zubaina Gaskiya Dazan ce wani Abu amma na fasa, murmushi tayi tace Kaiba Ko.

 

Suna zuwa dai_dai (Gate) na gidan Ta kwan_kwasa, Ta juya furkarta Tace Nasam Mom dina ce zata fara fitowa Tana zuwa zan rungume ta, Murmushi isma’il yayi Ta juya Wata mata tazo tana bude (gate), Ta juyo Isma’il gani yayi ta tsaya yace ‘‘ZAINABA” yaya naga kin tsaya tayi shiru tace Tabbas Basa gidan nam Ta fashe da kuka isma’il ya rarrashe ta suka zauna A k’ofar gidan, Isma’il yace to Mezai hana ki neme su Awaya Tace A’a so nake sai dai kawai suganni A gida Amma gashi kuma basanam To meya faru, Duk wanda yazo wucewa sai ta ce yar alhaji Lafiya kuwa yau a anguwar nam Tabbas Basu kyauta wa Mahaifin kiba, Ko ina ya shiga sai Allah.

‘‘Duk wanda yazo wucewa sai yayi mamaki ya ce yar alhaji Lafiya kuwa yau a anguwar nam Tabbas Basu kyauta wa Mahaifin kiba.

 

‘‘ISMA’IL, kallon Zainaba yayi ya gyada kai, Yace Hmmm to Mahifin ku kuma mai ya faru dashi, Gashi kuma Shi mutum ne Mai Taimako, hmm Allah sarki Daman A rayuwa Duk Abunda za’a kiwa Mutane Wani Lokacin Basa yiwa mutum uzuri Tabbas Akwai Abunda Ya faru, ‘‘ZUBAINA, murmushi tayi Tace Nidai fatana Allah yasa Mahaifina Nacikin kwanciyar Hankali Koma me suka Masa Allah Zai saka mana, Ta fashe da kuka!!.

 

‘‘ISMA’IL, ya rarrashe ta yace zubaina Mezai hana Ki nemi lambar Mahaifin naki, ki ji Ina ya koma, ta yi murmushi ta ce Shikenam yanzudai Mu k’arisa ‘Kofar gidan su, ‘‘AINA’U, tana tafiya isma’il na biye da ita K’ofar wani Gida suka zo Wacce ko k’ofa babu A mashigar gidan Wani Buhu a ka saka mai makon k’ofar suna zuwa isma’il yana tsaye Awaje Tayi sallama, Isma’il yana daga waje ji yayi Gidan ya rude da shewa yayi murmushi.

‘‘AINA’U, ta ce zubaina Ashe da rabon zamu sake ganin guna, ikon Allah, suka sake rungumar juna, ‘‘ZUBAINA, tace Muje waje Suka fito ta nunawa aina’u ‘‘ISMA’IL, Ta ce wannam dakike gani ya taimake ni sosai suka gaisa, sunacikin tad’i zubaina tace Nikam k’awata mahaifina tashi sukayi daga anguwan nam ne?.

 

Murmushi ‘‘AINA’U, tayi tace Allah sarki Alhaji Ya kwan biyu da Barin anguwar Nam sai da yatafi Daga baya Kowa Ya gane kuren sa, A yankinnam Gaskiya Ba a kyau ta wa mahaifin ki ba, Murmushi zubaina tayi tace Nikam meya faru k’awata ki fadamin gaskiya karki boye min komai duk da nasam mahaifina shi mutum ne mai hak’uri da kawai ci.

 

Murmushi ‘‘AINA’U, tayi ta ce Watarana mahaifin ki yana zaune A k’ofar gida yana karatun, (ALQUR’ANI) mai girma Wata mata ta ho da gudu Tafad’i Gaban shi tace ALhaji Katai makamin kamar Yanda ALLAH ya taimake ka, Yata ce Gata chan Na Kowa ya k’i kulata A garin nam, Kuma haihuwa ce tazo kowa ya guje mu, Dukda ta gane kuren da tayi Bekamata A juya mata baya ba, Bawanda ya fi k’arfin hakan ta faru dashi, Take yace jirani ina zuwa, Ya shiga cikin gida ya ajiye ALQUR’ANI, mai girma shida mahaifi yar ki suka fito, Ya umurci matar ina ‘yar tata take, suna zuwa ya kalleta cikin tausayi yace Maza Mahaifiyar ki ta sakata A mota shikuma ya shiga mota, Suka kai ta (ASIBITI), cikin ikon Allah ta sauk’a lafiya ta samu d’an ta namiji Ya musu tara ta Arzik’i.

 

Bayan Sati d’aya da faruwar hakan matar tazo da d’an nata tare da mahaifiyar ta, Sukayi sallamah Mahaifinki Ya musu iso suka shigo Suka zauna k’asa suka gai she da Alhaji, Nam ma ya musu tara ta arzik’i matar tace Alhaji Kai tayiwa ta kwara, farin ciki Ya kashi Ya ji dadin hakan harya karbi, Yaron Ya rik’e A hanun sa ya nuna wa mahaifiyar ki, Ta kalli yaron ta fashe da kuka, tace Idan na kalli Jariri Sai hawaye yazomin ina tinawa da ‘yar mu guda d’aya tilo mun rasata ita muke gani Tana saka mu farin ciki.

 

Dajin wannam Batun, Mahaifiyar yaro tace Alhaji Idan kuna bukatar shi Bakomai zan baku shi, Dan zaman shi A gurin ku zaifi samun kulawa fiye da gun mu, Da jin wannam, batun Alhaji yace to idan har Uwar gida ta amince ba komai, Murmushi tayi tace Na amince Amma sai ya isa yaye idan kin yaye shi, Sai kikawo min shi, ta ta shi tashiga dakinta ta dun k’ulo kudade ta mik’a musu sunkak’i karba tace A’a kodai kunre nane sukace A’a hajiya.

 

Hakadai Alhaji yasa aka ginawa matar nam gida mai kyau, Suka tare ciki, To tindaga wannam lokacin mutanen garinnam sukafara jifan mahaifin ki da munanam maganganu akan Shine asalin mahaifin Wannam yaron Amma angagara samun wanda zai fadawa alhaji ido da ido, Watarana Yafito ya tarar da manyan anguwa a k’ofar gidan sa, yana fitowa ya musu sallamah suka k’i amsawa wani daga cikin su yace haba Alhaji Abunda kayi a matsayin ka na mai fada aji Kana aikata irin wannam Abun to yaya kake tsanmanin sauran al’ummar ka na wannam gari?.

Hot Romantic Hausa Novel Complete Wattpad

Murmushi yayi yace ba laifi bane, Dan ka taimaki wanda yake buk’atar taimako. agaji a kan gab’a, kukan ta ta kawomin nikuma na share musu hawayen su, shin hakan danayi laifi ne?.

 

Sukayi shiru, Daga bisani Wani yace Alhaji wai ace kaine da aikata (ZINA) a boye hartakai ga ka dauki nauyin magaifiyar yaro da mahaifiyar yarinyar girma yafadi, dagin wannam maganar alhaji yaji zafin maganar sosai Amma ya danne zuciyar sa yace Abunda zaku saka min dashi kenam na gode ya juya zai shiga gida suka mar ihu!.

 

Yajuya ya shiga gida yasanar da mahaifiyar ki, Daga k’arshe ya yanke shawarin barin garin (ADAMAWA) baki d’aya, Washe gari da safe Ya tattara duk wasu abubuwan sa masu mahimman ci, ya shiga motar shi ya fito zai tafi matar nam tataho da gudu tace Alhaji Meyasa baka fahimtar dasuba, yayi murmushi yace Ba komai yasake murmushi yace kukula min da mai sunana, ya sake dunkulan wasu kud’ade ya bata.

 

Yaja motar shi sukayi tafiyar su, Bawanda yasan taka mamai inda alhaji yake, ‘‘ZUBAINA, ta sunkuyar da kanta tace Bakomai tabbas watarana gaskiya zata fito, Sukayi bankwana da k’awar ta tace To nabar ki lafiya mukam zamutafi, suka rungumi juna tace K’awata zan kawo miki ziyara watarana amma Badan naso ba saboda garinnam Inaganin sa tam kar Wuta bazan iya zama na wasu minto ciba, Ta umurci ‘‘ISMA”IL, da su bar garin haka kuwa akayi sukakama hanya tana kallon garin tana girgiza kai har suka bar cikin garin (MUBI) adamawa.

‘‘ZUBAINA, ida nunta duk sin cic_ciko DA hawaye, suna tafiya isma’il ya lura DA hakan yayi murmushi yace Dan Allah kidaina bana son ganin ki cikin damuwa kinji zubaina, ta goge hawayen ta ta ce shikenam, Yanzu ina zamu nu fa gashi bansam ta inda zamu Fara Neman mahaifina Ba, ta yi murmushi tace nasamo mana mafita, kasam yaya za’a yi kuwa isma’il?.

 

Gyada kai yayi yace sai abunda Kika ce, wani kallo ta mishi ta yi murmushi tace munemi wayar wani sai mu k’ira lambar su, Haka kuwa akayi wani bawan Allah yabasu waya, ‘‘Zubaina, sau hudu ta k’ira amma ba’a gada wayar Ba tsumewa tayi ta mikawa me wayar kayan shi, tace Malam mungode. Ya juya zai tafi akabiyo shi ya daga yace, ke ga shi ank’ira dasauri ‘‘ZAINABA, ta haho ta karbi wayar ta Kara A kunen ta.

 

‘‘kara wayar tayi A kunne, tayi magana tayi magana taji shiru tace To wata’kila dai mama bata gane Zainaban ta bace ke magana, Ta kashe wayar tana hawaye aka sake kira ta daga tace mama ki daga murya bana jinki zainaban kice mama na, shiru kawai ta kashe wayar aka sake ‘kira kawai ta mi’kawa mai wayar tace mun gode Malam Ya karbi wayar sa ya sakata a aljihun sa.

 

‘‘ISMA’IL, kallon fuskar ta yayi yai murmushi! Ta juyo suka had’a ido yace bata jinki ne gyada kai tayi tace A mutafi kawai, kama hanyar su suna tafiya Isma’il yace gaskiya, Ni abunda yake damuna ‘‘Farinci kina ma’ana yaya ta kowana hali take ciki se allah.

 

Mai sauroro Shin Aisha yayar ‘‘isma’il, dai mun barta a baya tana gadon Asibiti muje zuwa dan jin yadda zata kasance?.

 

‘‘AISHA tana zaune tayi tagumi tayi shiru, ‘‘HASSAN, Ya taho yace yaya yace wai ke haryanzu baki daina wannam tinanin nakiba,?. Adu’a zakiyi Allah ya bayyana manashi, Gashi gobe zan koma makaranta Amma naji Labarin kamar wai An kwara mana Hutun (SATI BIYU), juyowa Aisha tayi ta ce saida na fada masa karya je gunnam amma yak’i to ai gashinam Abunda ya faru, Wayar sa ma ta daina shiga.

 

Tagama rufe bakinta kenam hassan Yaga inuwa ta bayan sa, yana juyawa Yayi murmushi ya ce haba malama Ni bayadda za’a yi na zauna da ke kiyi hak’uri Inafatan kingane tsaki tayi tace Malam kokaso koka k’i dani za’ayi Kasani Ita kuma wannam Korar kare zan mata Agidannam Matsiyaciyar Banza Marar asali, Juyowa ‘‘AISHA tayi ta ce Allah baki Hak’uri Insha Allah duk lakocin Da nima yayana yasoko k’afa cikin gidannam Insha Allah zan barmiki gidan ku kinji?.

Hot Romantic Hausa Novel Complete Wattpad

Hassan kallonta yayi yayi murmushi yace Ba laifin mu bane, Haka itama ba laifin ta bane, Ke meyasa ba kya gane wa ne kam, Tin tsirewa tayi dadariya ta ce, ni ‘‘SAUDAT” ina da tsananin kishi Zan iya Abunda baka tsammani Akan Abunda nake so, Daka mata tsawa yayi yace malama barkai na ta juya tayi tafiyar ta.

 

‘‘ISMA’IL tare da zainaba sukayi landin cikin garin barno, Da yamma Kai tsaye isma’il ya kwan_kwasa (gate), zainaba tana zaune ta taho dan ganin waye yake buga gate tana hada ido da isma’il, A fusace ta tafka mar mari Tasss sai da yatsun ta suka fiffito a kumatun sa, Daga bisani ta rungumeshi, zainaba kuma kallon ikon allah kawai take ta sake Baki, Aisha ta Ce k’anina kayi Hak’uri bacin raine idan banyi hakan ba bazan huce ba murmushi yayi Yace To Ai sai a sakeni ko?, k’ara k’an_k’ame shi tayi.

 

Bayan ‘yan mintoci ta sake shi ta Ce wannam fa ina kasa mota?, murmushi yayi ta ce kodai itama batada kowanne kam? Ya ce A’a Ina hassan ne kam?.

Cikin farin ciki ta ce yananam gaskiya yakamata kayi masa godiya Da badan shiba da sai dai kazo kasamu ‘yar uwar ka ta zama gawa.

 

Isma’il ya ce subahanallah Mushiga ciki, Kutsa kai sukayi, Isar su kenam, Saudat Ta fito ta ce mezan gani har ‘yan iska kike kawo mana Gida laillai yau zaki bar gidannam, k’iran hajiya tayi suka fito tareda hassan, Hangosu hassan yayi yana isowa ya mik’awa isma’il hanu suka gai sa, Hajiya tace kai yaya zaka shigo mana gida kafita kona maka ihun barawo na tara maka jam’a hasan zaiyi magana ta dakatar dashi.

 

Ta ce dole seya fita, ya juya ya fita ‘‘Zainaba” ta juya zata bishi ya ce Kekam zaki iya zama tare da Aisha, Juyawa tayi ta k’arewa hajiya kallo tace haba da girmanki kina maganganun batanci Kan mutumin kirki Wana bolar gidan naku, A wannam lokacin Ran hajiya ya baci tace To na yanke hukunci Aisha ma ta tattare kayan ta ta bar gidannam Ta ke hassan yace haba Mama bekamata Kiyi Haka ba, Juyowa kan shi tayi Ta ce yau Zan baka zabi daya kazaba ko wannam Karuwar Ko ni shiru yayi yace A’a mama hak’ikanin gaskiya Ina son kowannen ku.

 

Ta ke Aisha ta tattaro ko matsen ta ta kama hanya zasutafi Ta juyo tayi murmushi, ta ce Hajiya Nabar ku lafiya Hassan ya kalleta tana kallon shi yagagara cewa komai fita sukayi Bakin Gate din Gidan.

 

Suka yi tafiya mai nisa Gabadayan su sungaji, Aisha ta ciro wayar ta tace K’anina kasaida wayar nam Musamu musamu Dan abunda zamu sa A cikin mu, Daganin wayar Zainaba ta ce Akwai Kati ne A wayar Ta ce Akwai ragowar Nera Hamsin, ta ce mik’omin mik’amata tayi ta karba tasaka lambar wayar mahaifin ta tayi ringin Jitayi An dagawayar akace Yana sallah, Ta ce Idan ya idar da Sallah Kace Ya k’ira zainaba ce.

 

Haka suka zauna sunata hamma, Yamma lis taji Kira tana dagawa tace Alhamdulillah, Mahaifina ne yake k’ira Sallamah yayi Jiyayi Ance Baba, ya ce muryar wa nakeji kamar zainaba na, Tana shekar kuka ta ce Baba ita ce, Yace kina ina ne tace Gaskiya Baba, yace a’a dakata yanzunnam zan turo A daukeki duk inda kike abunka da mai Hali, take ya sa cibiyar Sadar wa ta binciko masa inda ta ke, Yace Kashewayar Yanzu za’a zo A daukike karki damu ki kula, Minti shabiyar Jimkadam wa ta mota ce ta faka A ka dauke su Dukanin su su Uku, motar duk abinda kake bukata Akwai shi tindaga Abunci da gun kwanciya.

 

Bude k’ofa akayi Suka fito Jirgine na musamman A kadauke su, Ya tashi Dasu betsa ko Ina ba Sai Cikin babban birnin tarayya (ABUJA). Jigin ya sake su wata mota ce Ta alfarma Tazo ta fa ka, Nam ma sukashi ga, basu wani dau lokaci mai tsahowa ba se ganin su sukayi cikin wani gida Mai kyan gaski, Daga ka gidan kasan bana k’aramin mutum bane.

 

Tindaga mashigar gidan Mutanene Kawai inata hidinmar Buki, Aisha ta ce to wannam Shagalin fa kuma, Isma’il ya ce nake ga kamar na nakine ranki yadade, tayi murmushi Ta ce Mukarisa Tafiya suke Abi nam dasu Ashiga chan dasu, Daga ne sa ta hango mahaifiyar ta ta taho da gudu suka rungumi juna.

Tindaga mashigar gidan Mutanene Kawai su nata hidinmar Buki, Aisha ta ce to wannam Shagalin fa kuma, Isma’il ya ce nake ga kamar na nakine ranki yadade, tayi murmushi Ta ce Mukarisa Tafiya suke Abi nam dasu Ashiga chan dasu, Daga ne sa ta hango mahaifiyar ta ta taho da gudu suka rungumi juna.

‘‘Kuka kawai suke, Bayan wa ‘yan su mintoci, Mahaifiyar zainaba ta juyo ta kalli mutane guda biyu mace da namiji, Ta ce Farincikina wa ‘yan nam fa?.

 

‘‘ZAINABA” ta k’irawo su ta ce Yaya isma’il ku k’ariso mana, Tahowa sukayi suka gaida mahaifiyar Zainaba, Hajiya ta ce Sudin kuma suwaye ne?, Zainaba tayi murmushi, Ta ce Yan zudai so nake A basu masauk’i na musamman Zuwa gobe Zan fayyace miki komai sudin marayu ne basuda kowa, Hajiya ta ce Allah sarki!.

A ta ke Aka kaisu wani Fanin daban Aka ajesu I dan Kaga wajen cewa zakayi Anya kuwa wannam Gurin A nageriya Ya ke kuwa?, Kale_kale suke Aisha ta kalli isma’il ta ce k’anina ina ma A ce Wannam Gidan Mallakin mu ne, Gaskiya Ina matuk’ar son wajen nam Amma nasam Na ‘yan wasu kwanaki ne, Zamu fita.

 

Washe Gari Da safe, zainaba ce da kanta ta garzayo Har wajen Da su Isma’il, daganin ta suka tashi Ta ce A’a kuzauna kusaki jikin ku Nam Ai gidan kune Zaku samu kulawa sosai Yanxuma haka Alhaji ne Yakeson zai tattauna tare Da ku na gama bashi Labarin komai Tin jiya da dare, isma’il ya tashi suna biye da zainaba A baya Har suka zo farfajiyar Alhaji, Sukayi sallamah ya amsa, Yana karatun Alqur’ani mai girma, Ya ajiye yace Ko iso Isma’il suka zauana kasa yace A’a tashi ku hau kujera, Isma’il yace Ba komai Alhaji hakan ma yayi, murmushi yayi ya ce.

 

Isma’il ba abunda zance maka saidai nace Allah ya biyaka da gidan Aljanna bisa taimakon da kamini Tabbas Kayi Abunda ka chan_chan ci yabo da jinjinar ban girma, Saboda yanda Kanuna kulawar ka sosai kan ‘yar mu zainaba, Naji ta ce Kunyi da ita akwai Wa ‘yan su kudade dazata baka ladan Taimakon da ka mata ko?.

Gyada kai isma’il yayi ya ce tabbas munyi haka da ita Amma ni har azuciyata kawai na tai maketa ne saboda Allah, Bana buk’atar wani Kudin ladan Hakan Abud’aya kawai nake buk’ata farin cikin yaya ta na mata Alk’awarin Gida na musamman Alhaji Wannam Alk’awarin nakeson Cika mata Sai kuma gashi Hakan Ya gagara, Alhaji yayi murmushi Yace Isma’il kenam.

 

Idan har kunada Buk’atar zama tare da mu Na bar muku Wannam fanin da aka kai ku jiya A matsayin ma sauk’i sannam Acikin gidaje na Dana ke dasu na mallaka muku guda biyu kai d’aya yar uwar ta ka d’aya besan lokacin da isma’il ya fashe da kuka ba ya ringa wa alhaji godiya.

Hot Romantic Hausa Novel Complete WattpadHot Romantic Hausa Novel Complete Wattpad

Sannam Yace sannam zan sama maka Aikin yi da zaka dogara da kanka, kaji karkada mu, zainaba kuma na gefe tana ta murmushi Tana kallon isma’il Daga bisani Ya salla mesu, har sun fita zainaba ta dawo daga baya ta durk’usa gaban mahaifin ta tace Baba Dan Allah banaso isma’il yayi nesa da mu.

 

Kallonta yayi yai, murmushi yace to shikenam kuje ku sasan ta kawunam ku Ai bazan hanaki Abunda kike soba, Kunya ta kama zainaba ta rufe idon ta Tatashi ta fita.

 

Tsahon watanni Uku kenam, Isma’il tare da zubaina soyayah tayi k’arfi sosai, Ita kuma Aisha Kullum cikin tinanin ‘‘HASSAN” ita da hasan suna son juna amma kowa yana boye wa dan uwan sa Akwana atashi Watarana Zainaba tare da isma’il ana zaune suna hira suna bada labarain wahalar dasuka sha A rayuwar su, zainaba sai Hawaye ta ke tace Yanzu daman Yaya isma’il da kai ka yanke hukuncin Zama Bata gari ko?, ya tintsi re da dariya yace A mana to kowa ya k’i taimakon mu gashi dalilin haduwa ta dake ya zame mini Alkhairi ai, suka tintsire da dariya, Sakon (message), ne ya shigo wayar Aisha kamar haka:

 

Assalam dafatan kina lafiya Aisha Sarkin hak’uri Na dad’e cikin dakon son ki da kaunar ki cikin zuciyata, amma nagagara samun Gurin dazan sau k’e shi Cikin zuciyar ki, sena taho zan sauk’e Se na gagara sau k’ewa kuma kinsan da hakan Amma kuma ina ji ina gani Haka kika tafi kikabar ni, Tsahon wata daya kenam da wasun ‘yan kwanaki, Aisha Giwar mata, Tabbas nikam Tinda jimawa na kamu Amma ina da tabbacin kema hakan take, ina mai baku hak’uri da ke da isma’il bisa ga abunda ya faru Abaya, Tabbas hajiya bata kyauta miki ba Idan bazaki damuba ina so muhadu dake zan idan har kin huce Ina jiran sakon Amsar ki daga ‘‘HASSAN” muhuta lafiya murmushi tayi ta ce, ‘‘Isma’il Aunt zainaba” ina neman shawarin ku, Gyara zama suka yi su ka ce to muna sauraron ki, Aisha.

 

Dariya Aisha tayi ta ce inada wani wanda na dade tare dashi Amma kuma ina matuk’ar ji dashi sosai Amma kuma mahaifiyar sa ta gasa ni sosai A baya sannam kullum shi cikin kare ni yake A gunta dukda yasan Nine mai gaskiya Amma duk da haka yana daraja ni nima ina mutun tashi sosai amma kwatsam rana daya mahaifiyar sa tamini korar kare Tun lokacin da na bar gidan Naga ranshi baiji dadin hakan ba kwatsam seyayito ro mini sakon Yana mai bani hak’uri kan Abunda ya faru baya.

 

Shin wace shawara zakubani?.

Shiru isma’il yayi ya ce Aisha kinsam bazan juri ganin wani abu ya sameki ba Amma idan har kin yadda da shi ba komai, kinji ‘yar uwata farin cikina murmishi tayi ta turawa isma’il sak’on sunam Anguwar da suke, Da lamabar gidan da suke, Washe gari da misalin k’ar fe Goma zuwa shad’aya na safiya, K’iran hassan ne ya shigo Tana amsa k’iran yace Ga ninam na iso ki taho ki mana jagora, Ta taho tare da Aisha suka tari Hassan tare da mahaifiyar sa.

 

Daganin Aisha mahaifiyar Hassan ta gagara had’a ido da ita rik’iya ta musu har wajen hajiya suna zuwa aka musu karba ta musamman, Hassan na kallon Aisha yaga ta k’ara kyau sosai fiye da yanda yasa ba ganin ta da chan baya.

 

Zainaba ta fahimci hakan setayiwa aisha rad’a a kunne Ta ja ta suka fita ta barsu daga ita sai, hajiya se shi hassan, Hajiya ta ce Hassan zamu baka Aisha Amma da sharadi idan har abunda ya faru a baya ya kuma faruwa bazakar be ‘yar mu, mahaifiyar hassan ta ce A’a insha allah hakan ma bazai sake faruwa ba insha Allah, Munmiki Alk’awarin Hakan Hajiya ta ce to shikenam suntashi zasu tafi ta ce tafiya da wuri haka Isma’il ya ce A hajiya Sunkama hanya Suna tafiya Aisha tare da Zianaba, suka musu rakiya, Suka shiga mota sukayi musu by_by.

 

‘‘Suntafi da Sati uku se gasu Da jerin motaci, Iya kallon ta, *HASSAN* na waje Yana ta lek’e_leke Kozaiga *Aisha*, Ya k’ira wayar ta ba ta tafiya, K’iran ‘yar uwar sa, yayi Wacce da take mutu k’ar son shi, tana zuwa tace mekuma zann maka *Dan uwana* yayi murmushi yace “AISHA* na ke buk’atar Gani tayi murmushi ta ce zan jarraba ko zata fito Amma gaskiya shikenam, Bakomai.

 

Ta juya, tayi tafiyar ta, mahaifiyar zainaba da ‘yan uwanta ne Sunata lissafa kayan *LEFE* ‘‘MAIJIDDA” ta yiwa mahaifiyar Hassan rada Akunne, Tayi murmushi, Ana ta lissafa kayan lefe tace Ina amaryar ta mu ne Kam?.

Hajiya, Uwani, Mahaifiyar ‘‘ZAINABA” ta yi murmushi tace tana d’aki tare da yar uwar ta, K’aramar yatinya ce Ta ce Bari na k’irawo ta, Jim kadam *Asha* ta fito Daga nesa wani k’am shi ne ke tashi wanda ya bude kaffatanin gidan da k’amshi..!

 

Tana zuwa a durk’usa hark’asa ta sunkuyar da kanta ta gaishe da mahaifiyar *HASSAN* hajiya maijidda tare da ‘yan uwanta.

 

Sannam ta wuce ta bude Wayar ta, Tama gama kunnuwa, kiran Hassan tagani, tayi murmushi, Ta ce, kallagaban ka Ganinam ina kallon kak’ariso mu gaisa.

 

Murmushi yayi ya garzayo gurin aisha, Sunfi minti biyar suna hira Daga bisani Ta ce to ni zan koma, ta juya zata tafi, Hassan ya bita da kallo ya ce dakata…!

Kafin kitafi Ai ko murmushi Kya mini Kozanji sanyi A raina tayadda harna koma gida ina cikin shauk’i, ta juyo tayi murmushi ta ce kaji Dashi…!

 

Tayi tafiyar Ta,

 

Rana d’aya Aka saka, Daurin Auren ‘‘ISMA’IL” ta re da ”ZAINABA” haka ‘‘HASSAN” shima tare da‘‘AISHA”.

 

RANAR 22/GAWATAN SATUNBA/2019.

 

‘‘ISMA’IL” na dawowa da dare, zai wuce bangaren sa, ganin Zainaba yayi a zaune Beyi k’asa a gwaiwa ba ya toho Inda take, ya tsuguna A gafen ta Ya ce, Zainaba lafiya kuwa na ganki A zaune Kuma gashi lokacin sallar isha’i yayi, murmushi tayi ta ce wallahi bana jin dad’i ne, Isma’il yayi murmushi ya ce sorry, Be tsaya ko ina ba ya wuce Wajen ‘‘HAJIYA UWANI” yayi sallamah ta Am sa ya zauna gefe d’aya bayan ta idar da sallah, Ta juyo kan sa tayi murmushi, Ta ce To gata bata jin dad’i Anbata magani ta k’isha, Juyawa isma’il yayi ya ce Haba Zainaba Se kace wata k’aramar Yarin ya, Ya tashi Ya je Ya dauko magani Yana tahowa ta ce Akwai d’aci bazan iya shaba, Isma’il ya taho yadinga rarrashin ta har seda ta sha maganin, sannam ya debo mata zuwa a but tayi Alwala tayi sallah, Data Idar ta kalli isma’il tayi murmushi..!.

 

Ya kalleta ya ce Meya faru, Zainaba ta gyada kai ta ce ba komai, Kaje Ka huta Kaima, Sukayi ban kwana ya wuce Bangaren Sa, Akwana atshi ranar da aka saka ta buk’i Saura kwana uku.

 

Tin ranar Laraba Aka fara Shirye_shiryen buki, Ranar Asabar aka daura Aure, Da misalin K’arfe Hudu na yamma, Aisha ta na cikin d’aki tare da zainaba se rusar kuka ta ke…!.

Akazo Daukar, Amarya Isma’il ya taho Ya kamo hanun ta, Ta k’an k’a meshi Tanata famar kuka Yayita rarrashin ta, Yana kuka, Zainaba na kuka Aisha na kuka, HAJIYA ce da kanta tare da ‘yan uwanta Suka raka ta har izuwa wajen mota, Hassan na gefe Yataho suka gaisa da isma’il, Isma’il ya ce Hassan Zainaba Tana sonka sosai Dan allah ka rik’e mini ita amana Hassan yayi murmushi ya ce, isma’il Insha allah zan rik’eta Karkaji komai, Haka suka tafi Tana kuka ana rarrashin ta har izuwa Gidan ta.

Isma’il kuma suka tare da amaryar sa shima, Alhaji Yayiwa isma’il tara ta arzik’i Haka suka cigaba da Rayuwar su ba tsangwama, ba nuna warayya.

Anam littafin *BALAIFIN MU BANE* ya k’are, Se kun sake jina a littafina nagaba, Anam *kamal* yake cemuku Muhuta lafiya.

*DOMIN YIMIN GYARA KO WANI ABU MAKA MANCIN HAKA ZAKU IYA TUN_TU BATA TA A *WHATSAP* TA WANNAM LAMBAR*

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment