Littafan Hausa Novels

Hanan Hausa Novel Complete

Sirrin Doguwar Mace
Written by Hausa_Novels

Hanan Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

[22/02, 11:40 pm] +234 813 298 6866: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„

*_HANAN_*

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

_By maman noorul_

_Hudah_

 

_Tsokaci_

 

*Wanan littafin kagagen labarine banyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba in yayi dai’dai da rayuwarki kiyi hakuri Yar uwa domin akasi aka samu*

 

_Warning_

*Ban yarda wani ko wata ta ta juya min labari ba ko a canzata ta ko wata tsiga ba a kiyaye please*

~Godiya~

_Alhamdullilah godiya ta tabbata ga madaukakin sarki daya sake bani daman rabuta wanan littafin,sanan Ina godiya ga masoyana Wanda a kullum suke bani karfin guiwa da goyo min baya Ina son ku sani da bazarku Nike taka rawa Allah ya biyaku ya Baku duk abinda kuke Nima na alkhairi_ Amin ya rabbi

 

Paid book ne

 

 

πŸ…ΏοΈ1️⃣▢️2️⃣

 

Bismillahir Rahmanir Rahim

 

Babban falo ne wanda ta ji kayan alatu da kayan more rayuwa

 

Kallo d’aya zakawa falon ka Gane na masu hanun da shuni ne domin kuwa wanan falon Yana cikin daya daga cikin faloli dake gidan babban d’an Siyasar Nan ne me suna senator sani Bello Ndaman Wanda a yanzu Haka yake niman takarar shugaban kasa

 

Tsayuwa a falon kadai ya Isa yasa me hankali tunanin mutuwa,domin kuwa in Kana ciki baka gane yanayi da ake ciki ko zafi ne ko sanyi ne ko Kuma damina,sanan Kuma baka sanin lokaci ko Rana ne ko darene ko Kuma safiya ne domin Yana bada yanayine na daban sai ka kalli agogo zaka Gane lokaci,duk wanan dukiyar da aka narkar anan din b’angaren amaryasa ce watoh ba indiya wacce ya aurota a India,matar senata uku ta farkon hajiya Aisha cikakkiyar Yar Niger ce banufiya kamar inda shima senator ya kasance banufe ne tun kafin ya tafi jami’a akayi musu aure da Aisha had’in iyaye Kamar inda dai nufawan sukeyi kafin ka auri wata yare sai ka Fara auren yarenka

 

Aisha batayi karatu ba Dan ko aji Bata tab’a zuwa ba suna tare ya Shiga jami’a Yana gamawa ya Niki soja Allah ya dafa me ya samu ya dade a Nigeria army kafin daga baya yayi resign ya shiga politics

 

Shigarsa siyasa yasa ya auro wata Yar maduguri hajiya Rabi wacce master ce da ita kyakyawar gaske wacce zai iya nunawa duniya ga matarsa domin akwai Jin turanci ga Kuma kyau duk wani harkokinsa na siyasa itace me tsaya masa,Amma ba Yana nufin yana wulakanta uwargidansa bane asalima duk wacce tace”zata Raina me Mata zai rabu da ita kusan nufawa da kabilanci ai,ita Aisha ma kasancewar akwai Hutu ga kudi ba abinda ta rasa baka tab’a sanin batayi karatu ba Dan kuwa idanunta a bude yake akwai wayewa a tare da ita domin babu kasar da Bata zuwa in taso Kuma yanzu ma ta Kan picking wasu abubuwa a bokon Saidau turancin ne babu ya’yanta 6 da senator ita kuwa Rabi biyar kyawawa dukkninsu Amma duk basa kasar suna turai senater me kudi ne Dan shekaransa ashirin a Senate so biyar ana zabarsa kasancewar Yana zuba aiki a zone dinsa yanzu haka ma shine Senate president saidai kujeran shugaban kasa yake so….bayan auren Rabi da tayi haihuwa uku ya auro wata ba indiyiya Wanda a UK Suka had’u me suna Hanaz wacce ta tab’ayin miss word sun Fara soyayya da yike Yana da kudi ya aureta anan fah ta ture gwamnatin hajiya Rabi domin senater ya daina yayinta hanaz ce Kan komai ya’ daya ta haihu dashi domin Yar gayu ce Bata son tayi haihuwa dayawa ya b’ata Mata shape,ranan suna Yar ta ci sunan mahaifiyarsa hauwa sai suke Mata alkunya da Hanan yanzu tana da shekara goma Sha tara,tana da shekara goma Sha biyu ta bar Nigeria zuwa karatu yanzu ta Gama ta dawo Kamar inda akeyi da ka Gama karatu zaka dawo ya’yansa biyar Mata suna gidan miji uku na nnagi Aisha Kamar inda yaran gidan ke kiranta biyu na ummi watoh Rabi maza uku Suma sunyi aure Amma duk suna kasar waje da matansu domin a can suke aiki matan ma cikinsu akwai Wanda Suke kasar waje yanzu Yara uku ne a gidan Hanan ce auta

 

HANAN ba abinda ta baro na mahaifiyarta tana da Asia’s look kana ganinta ka gan india,zamanta a kasar waje ba abinda ya tsinana Mata sai koyo rashin kunya da yawo clubs da Kuma abota da maza ba ruwanta,itace most popular and famous yar’sa a media domin ita media person ce me tarin followers a media shiyasa da tayi laifi kad’an za a buga a jarida harda kari,itace ciwon kan mahaifinta Dan ba zagin da Baya Sha ana cewa Wanda beyiwa yar’sa tarbiya ba bazai mulkesu ba politically tana janyo me matsifu shikuma baya son komai ya Shiga tsakaninsa da abinda yake so itako ko a jikinta wallahi harkarta takeyi ba ruwanta rayuwar turai take ko Niger garin kakaninta Bata son zuwa bare a Abuja suke Zama

 

Itace ciwon idon hajiya Rabi ta tsani mahaifiyarta da ita kanta Hanan din domin su Suka ture gwamnatin ta a zuciyar senator shiyasa da Hanan ke misbehaving Dadi take ji mussaman in mahaifinta na mata fad’a Dan ma kwanaki cewa yayi zai tsine mata yayi disowning dinta hakan ya farantawa Rabi Rai Amma ita hanan din ba ruwanta da wanan,nnagi Aisha ce kadai me nuna Mata soyayyar gaskiya

 

 

__________

 

Cikin kuzarin da Allah ya hore Mata take saukowa daga stairs rike da makullin mota

 

Sanye take cikin matsatsiyar cinos baki sai wata Yar Riga jumper iya cibiya flat tummy ta a waje ga kugun Nan ma Sha Allah hills ne kafarta me tsini sai tayi parking sumanta a tsakiyar Kai sai bakar gilashi da ta rufe rabin fuskarta ta fito a zazzafanta

 

Saukowa take hade da gudu kamar ba hills tasa ba har ta Kama handle zata bude kofar taji muryar mahaifiyarta na cewa Ina Kuma zuwa???”

 

Juyawa tayi ta zubawa mahaifiyarta dake sanye cikin atamfa doguwar Riga tayi kyau sosai ta saki murmushi tace”kawata ce zatayi birthday shine zani mu Fara shiryawa da wuri Dan muna expecting guest daga kasashe duniya our old friends are cominb

 

B’ata Rai mother tayi kamar inda take kiranta tace”no Hanan you are not going anyway wallahi na gaji Zaki fita ki d’auko min magana mahaifinki ya dawo Yana min matsifa Kuma fa karki manta rantsuwar da yayi miki akan duk Randa Kika sake jawo me magana zai aurar dake ga Maigadi and you know he meant I……”

 

Bata karasa ba Hanan ta karasa gun mother ta Kai Mata kiss a kumatu tace”sai na dawo “tana fadin hakan ta Kara sauri ta fita mother ta bita da kallon mamaki,ta rasa ya zatayi da yar’ta kullum cikin jawo mata magana take kishiyoyi na goranta mata ta rasa taya zata bullowa Hanan ta daina abubawan da takeyi

Sai Baba Buhari Hausa Novel Complete

__________

 

HANAN na fitowa gun motan ta tayi direct ta bude murffin ta shiga tayi Masa key Daman megadi na ganinta ya wangale gate Dan yasan halinta dukda Haka be tsira ba data fizgi motar saura kad’an ta kwashe shi yayi tsalle yayi gefe

 

Gudu take shararawa abinta a titi kasancewar layout dinsu babu hayaniya tana kokarin fita a anguwan su wata mota ta fito daga wani gida tana reverse a ka’ida sai ta jira ya Gama sanan ta tafi tunda ya rigada ya danno Kai Kuma an rufe gidansu bazai yiwu ya koma ciki ba Amma saboda matsifa irin ta Hanan kin ja baya tayi ya samu wuri ya fita sai ma horn da tayi ta Masa Kamar zata kashe Masa kunni

 

Da mamaki ya kalli madubi Suka had’a Ido domin itama kallonsa take irin kallon raini abin sai ya bawa Habib mamaki ya Danna Mata horn itama horn ta Danna me fiye da nasa

 

Tsaki yayi a fusace ya fito a mota,ganin Haka itama ta fito tana tafiya cikin taku

 

Yace”keee miye Haka

 

Hayewa saman bunnet tayi tace”malam in kasan abinda yayi maka kyau shine ka koma ciki in wuce in ba Haka ba saidai muyi ta Zama wallahi Dan baka Kai in baka hanya ba

 

Yace”Haka Kika ce??”

 

Tace”Haka nace

 

Yace”ok shikenan we shall see ai titin bana uban wani bane”

 

Tace”Amma ubana ne yayi titin Kuma kowa yasan duk layin Nan Babu Wanda ya kaisa kudi so ban gan abinda zaisa in baka hanya ba

 

In Banda rashin respect ka ganni ka nimi in baka hanya wallahi baka Isa ba

 

Tsaki yayi ya koma ya zauna a mota kafafunsa na waje ya dinga latse waya

 

Itako ko a jikinta radio ta kunna na motarta tasa kida ta Fara rawa abinta

 

Tun Habib baya kallonta har ya Kai ga Yana

 

 

Maman Nur

[22/02, 11:40 pm] +234 813 298 6866: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„

_*HANAN*_

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

By maman noorul

Hudah

 

 

Paid book

 

πŸ…ΏοΈ3️⃣▢️4️⃣

 

Bismillahir Rahmanir Rahim

 

Rawar da brick and lace sukayi a love is wicked take tana kad’an kugu yariyar ta iya rawa

 

Satar kallonta yake Yana Jin haushinta a take yayi Mata kallon Mara kamun Kai,abinda ya tsana a rayuwarsa kenan ya gan mace Bata da kamun kai

 

Sun dade a Haka Allah ko yasa babu wata motar da ta Zo wucewa ganin fah ko kwana zasuyi ba tashi zatayi ba kawai sai yayi tsaki ya Kira megadi ya bude Masa gate yayi ciki Yana jiyota cikin gurb’atacciyar hausarta tana cewa ka taimaki kanka malam”sanan tayi cikin motar ta tayar ta bar unguwan shima ya fito ya fita

 

Hotel din da za a shirya party tayi direct ta tarar da kawayenta Mata da Maza sai Suka hau shirya komai

 

BΓ yan duk an Gama wata shirye shiryesu inda Suka Kama domin a kusa da swimming pool zasuyi party suka Shiga ciki domin shiryawa

 

Fitowa tayi cikin bikini pant da bra ta saka wata katuwar hat da flat takalmi ga Kuma uban eye glass sai kamshi take

 

Lucy Yar minister da sukayi karatu tare a kasar waje itace me birthday din sai Suka kunna radio Suka Fara rawa

 

Hotona ake kashe musu dukda tasan Yan jarida ne da gulmarsu bata dameta ba she don’t bloody care sunfi maida hankali akanta kodan saboda babanta na niman president ne oho

 

Tana kwance a kujera Dake kusa da pool din tana waya sai ga abokansu na nesa sun Fara isowa ganin shalo wani best friend dinta ya sata mikewa ta saki wani irin ihuuuu tana cewa shalo Kaine a gari saukar yaushe

 

Ya saki murmushi tare da cire gilashi idanunshi yace”babe kece Kika canza haka?”

 

Murmushi tayi ta juya me baya wanan pant din da Bata da maraba da babu bama abinda ta rufe saima raba duwawun da tayi ya shige ciki

 

Wani ihhuuu shalo yayi itako karasawa tayi ta rungumeshi ta Haye jikinsa yace”it been long babe kin Kara kayan Dadi

 

Fari tayi da Ida tayi pecking dinsa hagu da dama sanan tayi kissing lips dinta dukk wanan abinda ake ana Mata video Kuma ta sani ba abinda ya dameta Bata b’oye hallayenta

 

Sauka tayi daga jikin shalo tayi kissing sauran friends dinta har mata

Karasowa wani Dan jarida yayi kusa da ita yace”Hanan ”

 

Ta juya tana me kallon banza,be damu ba yace”me Zaki ce akan wanan Shiga da kikayi kina Yar musulma Kuma Yar Dan takara shugaban kasa Wanda Kuma zai fad’a aji ayi koyi dashi ”

 

Cire hat din kanta tayi tace”while mahaifinah ke niman shugaban kasa bani ba, so kaje ka samesa I have a life to live that is what iam doing,iam enjoying life to the fullest so kaje ka sameshi not me”

 

Yace”ok,but Baki tunanin zai iya affecting dinsa mutane na Miki kallon Mara tarbiyya wacce Bata san darajar kanta ba dayawar mutane na cewa bazasu iya zaben Wanda beyiwa ya’yansa tarbiyya ba ”

 

Tace” Ina da right nayi abinda na gan dama Dan mahaifinna na niman mukami ban gan dalilin da zaisa in kuntata kaina ba saboda wani tsoho can da beda godiyar Allah me wanan tsohon zai Nima a gurin allah,Yana da dukiyar da har generation100 bazasu Gama dashi ba, madadin ya koma gefe young generation su samu wuri no he want to hijack the public property,,i don’t know why this old men are greedy and selfish”ta fad’a tana yatmusa fuska ta maida fuskarta Kan wayar hanunta irin ko a jikinta dinan shiko d’an jarida yayi dip da alamu maganar ta Dake shi

 

Wani ne ya Zo ya rungumeta ta baya ta kyalkyale da dariya

 

Dan jarida yace”please Zaki iya min suratul fatiha?”

D’agowa tayi ta zuba me harara tace”suratul fatiha,suratul fatiha….Kai da ka ganni ka ga alamu Zan iya?”

 

Wani irin salati ya sake tayi tsaki ta bar wurin rungume da wani Abba ba shalo ba

 

Daya daga cikin d’an jarida ya karasa inda ta zauna a cinyar Abbati zaiyi magana ta mike ta wanka me Mari tace”Wai Kuna da hankali kuwa ku barni in sarara Mana”

 

Rike kuncinsa yayi yace”Kika dake Ni?”

 

Ta jawo kwalbar wine din da suke Sha ta fasa a tebu zata Kai kansa shalo ya rike Mata hanun tare da dakawa dan jarida tsawa yace”live

 

Barin wurin yayi Yana juyawa Yana kallonta Yana tunanin irin rashin mutunci da zai Mata wallahi

 

Bayan shalo ya lallasheta kawai sai ta kyalkyale da dariya ta fad’a ruwa sai Suka Fara shashacinsu,duk abinda take ana d’auka ta dade suna wanka da kawayenta har mazan kafin ta fito tayi cikin hotel din ta Shiga room dinta tayi wanka ta saka burshot da wata Yar vest ta fito suka cigaba da party

A ranan Hanan Bata koma gida ba

 

____________

 

Abba ne tsaye rike da newspaper tunda sanyi safiya ya shigo d’akin mother ya tashe ta ji yaje kamar yayi hauka saboda Hanan ta Gama dashi bashi da sauran kima a idon duniya

 

Mother data gan Bata fahimtar maganarsa ta lumshe Ido Bata son hayaniya tace”sweetheart calm down please explain in Gane abinda yake faruwa

 

Ya daka Mata tsawa yace

 

 

Maman Nur

About the author

Hausa_Novels

2 Comments

Leave a Comment