Littafan Hausa Novels

Hamshakiyar Uwa Hausa Novel Complete

Yadda Ake Rikita Maigida Yayin Kwanciya
Written by Hausa_Novels

Hamshakiyar Uwa Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

HAMSHAƘIYAR UWA

 

 

*NA*

 

 

*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*

 

 

_PAID BOOK_

_Kuɗin Karatu 600_

_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank ko katin Mtn_

_Phone 08140004302_

 

 

 

_Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa mai komai,tsira da amincin Allah su tabbata ga annabi Muhammad(S.A.W)._

 

_Kamar yadda na fara lafiya,Allah ka bani ikon gamawa lafiya,Allah ka bani ikon faɗakarwa gwargwadon iyawata,Ya Allah ka yafe min duk wani kuskure da hannuna zai rubuta,Allah ka bani ladar faɗakarwar._

 

 

*DOKA*

_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_

 

*Free Page 1*

 

Kan shi a ƙasa bayan ya zube a gaban ta gwiwoyin sa suna ƙasa tamkar mai neman gafara. A hankali ya furta Hajiya Barka da dare.Ta ɗago kai daga kan TV da ke nanne a bango cikin wata ƙatuwar ma’ajiyar ta bango guda. Ta maida kanta gare shi ta na nazarin fuskar shi, sannan ta dubi yarinyar da ke zaune a ƙasa tana shafa mata man zafi a ƙwauri ta ce, “Azima ta shi ki je ki kwanta.” Cikin sauri yarinyar ta miƙe ta re da faɗin sai da safe Hajiya. Allah ya tashe mu lafiya, Hajiya ta furta a hankali. Ta maido kallon ta ga gareshi sannan ta soma magana cikin isa “Shamaki zauna da kyau Allah ya yi maka albarka.” Ya ce Ameen Hajiya. Ta ce “Bisa dukkan alamu ka ga wadda ta yi wa ranka, ko dai birgewa ko kuma ta baka shi’awa, faɗa min wani abu dangane da ita.”

Bibiyata Akeyi Hausa Novel Complete

Ya sake gyara zama bai yi mamaki game da kalaman mahaifiyar ta sa ba,domin ita mace ce mai tsananin basira tare da karantar ɗan Adam, in har za ku yi zaman minti talatin da ita ba ko shakka zata iya zayyana maka abubuwa da dama daga cikin ɗabi’u ko halayyarka. Sannan babu abinda tafi saurin ganewa irin ka yi mata ƙarya. Ya ce Hajiya so ɗaya na ganta zata je Islamiyya na tsaya zan yi mata magana ta ja tsaki ta wuce, maimakon in fusata sai kawai na ci gaba da bin ta a baya bata sani ba har ta shiga makaranta.

Na san cewa kamar shidda sun ta so na koma sai ban ganta ba, yau na bi ta layin da na ganta cikin sa’a sai na hange ta a wani shago tana siyayya,na jira ta gama na bi bayan ta na ga gidansu yanzu ina neman iznin zuwa ne in Allah ya sa an bani izni.

Hajiya ta yi shiru kamar ba zata ce komai ba, zuwa can ta ce “Je ka kwanta amma kafin hakan ina son ka yi sallar istikhara da safe ka zo ka kuma bani wannan labarin da ka bani.” Ya miƙe a hankali tare da faɗin na gode a tashi lafiya. “Allah ya maka albarka.” Ta furta tare da ɗaukan goran ruwa a gefen ta ta buɗe da zumar sha.

Firgigit ya farka ya na kallon ɗayan sashen da take kwance, mafarkin yana dawowa a zuciyar sa, babu ko shakka sai ya yi wanka domin ya cimma hakan a mafarkin sa, bai taɓa samun hakan ba duk zaman gauran takar sa, kila gara lokacin da ya ke saurayi farkon balaga. Ya yi addu’a a sallar sa, domin bai samu zuwa Masallaci ba sakamakon makara,ba zai iya tuna lokacin da ya rasa jami’in sallar asbahi ba. Ya jima kwance jikin sa lankwas wanda yin hakan ba al adarsa ba ce. Sai ya ji kamar wani ɗan zazzaɓi ya na sarfatar sa. Cikin hakan ya ji ana kwankwaso ƙofarsa, ya tashi zaune sannan ya bada iznin a buɗe. Ta turo ƙofar ta na sanye da kayan makaranta, Azima ce. Ta ce”Yaya Shamaki Hajiya ta ce in duba ka.” Ya ce ki sanar mata ina zuwa. Ya miƙe ya ɗauki jallaiya bulu mai gajeren hannu tasha aiki da sirfani mai ruwan zaiba ya saka.

Yana fitowa falonsa Meema ta na shigowa ta nufeshi da gudu tana faɗin “Dadi! Ya sa hannu ya ɗaga ta sama ya sata a jikin sa tare da faɗin Mamana Ina Mubina ina Anisa? Ta nuna mishi hanyar ɗakinsu tare da faɗin “Suna ciki Rahin tana shirya su.” Ya lakaci kuma tun ta ke fa? Ta ce “Ni’ma yanzu za ‘a shirya ni.” Ya dire ta to maza kar ku yi latti ki tafi a shirya ki. Ta ruga da gudu. Shi kuma ya nufi sashen Hajiya.

Tana zaune a kan sallayar ta ƙafafun ta a miƙe sanɓal ta rufe kanta da hijabi na alfarma ƙamshin ta na tun fil”azal ya na tashi tana riƙe da carbi tana lazimi. Ya samu gefe ya zauna zama irin na girmama wanda ka ke gaban shi. Ya kalle ta cikin darajawa tare da faɗin Hajiya ina kwanan ku? Ta sauke numfashi cikin ƙasaita, sannan ta amsa da “Lafiya lau Shamaki, me ya same ka yau ba ka je sallar asbahi ba?” Ta yi tambayar cike da kulawa. Ya sunkuyar da kai, jikina yau na tashi babu daɗi sam, kuma sai na makara. “Me ya biyo bayan neman zaɓin da ka ba Allah ajiya! Ka ji wata damuwa game da yarinyar ko kuma Allah ya haska maka wani al’amuri a cikin baccin ka?”

Ta jeho masa tambayoyi. Shamaki ya ce eto har zuwa yanzu ina jin ƙaunar ta kuma na yi mafarkinta. Ya sunkuyar da kai domin ba zai iya bada labarin mafarkin ba. Hajiya ta ce “Ina sauraron ka.” Ya sa hannu ya shafa fuskar sa sannan ya saci kallon ta ta tsira mashi ido,ba ko shakka so ta ke yi sai ta fahimci ko zai mata ƙarya. Ya ce cikin wani yanayi muka haɗu Hajiya Allah dai ya kyauta.

Ta yi ɗan murmushi da alamu ta fahimci ina ya dosa. Shike nan, ka sake bani labarin da ka bani jiya game da yarinyar. Ya gyara zama ya zayyana mata komai kamar jiyan. Ta numfasa tare da faɗin shike nan ka je ka fara bincike a kanta kafin ka je gurin ta. Sannan kar ka manta. da sharuɗɗa na akan duk wata mata da za ka aura. Bana son ka sake sakin mace daga guda ukun nan da ka yi, amma ka sa a ranka matan ka huɗu ne in Allah ya ƙaddara ina aɗdu”a. Kaje ka shirya yau kai zaka kai yaran ka makaranta domin tun jiya suka nemi alfarmar hakan.

Sannan in kaji zazzaɓin zai matsa sai ka sha magani, duk da nafi zargin zazzaɓin na soyayya ne. Ta kai ƙarahen maganar da ‘yar dariya irin ta manya cikin ƙasaita.

Ya shafa kanshi tare da yin murmushi mai sauti,ba ko shakka zolayar sa Hajiya ke yi.

Ya ɗan rusuna. zan yi yadda ki ka ce insha Allahu Hajiya. Sanna ya miƙe ya nufi ciki. A mota tare da ‘yan yaran sa mata su uku, Meema da ke zaune a gefen shi ta ce “Dadi za ka dawo ka ɗauke mu?” Ya dube ta sannan ya girgiza kai, Bazan dawo ba Mamana zan tafi kasuwa ne fa. “To zaka raka mu har ajin mu?” Ya kai hannu ya shafi kanta me zai hana zan raka ku in kuna so. Anisa ta sako hannuwan ta daga can baya ta shafo kumatun sa, Dadi muna so ‘yan ajinmu suna cewa basu taɓa ganin Babana ba. Mubina ta ce Nima haka Dadi za ka raka mu kowa ajinta. Ya ce to shike nan sai mu fara kai Anisa ita ce Smaller ko sai mu kai Mubina, sai in kai Anty Babba ko Meema? Cikin jin daɗi ta ce e Dadi na.

Sun yi kamar yadda suka tsara da ‘ya’yan na sa sannan ya ciro kuɗi ya raba wa malaman sannan ya tafi suna ta godiya sannan ya kama hanyar kasuwa.

Tun da ya zauna a ofishin sa da ke babban reshen manyan katunan sa wato Zeena Galary da ke ƙatuwar plazarsa mai suna Gidan Zeena a babbar kasuwar kwari da ke Kano. Dukan yaransa na katin sun fahimci ya na da ‘yar damuwa, kasancewar ba haka ya saba zuwa ba. Shi kansa tunda ya ke bai taɓa samun kansa cikin wannan yanayin ba game da matansa da ya aura a baya. Ko matarsa ta fari bai ji irin abinda ya ke ji a wannan lokacin ba. Yana jin in bai fita ya nemo yarinyar nan ba kafin yamma akwai matsala.

Suna idar da sallar Azahar ya cire agogo da zobe da duk wani abu da zai nunashi a mai kuɗi, ya fita ya saka salifan da ke ƙofar banɗakinsa na ofishin ya fita ba tare da ya yi wa kowa magana ba, ya je titi ya tari ɗan sahu ya hau tare da faɗin kaini Ɗan a gundi. Dai dai bakin lungun ya tsaya ya ciro kuɗi Naira ɗari biyar ya miƙa masa sannan ya sa kai cikin lungun, shi dai Ɗan sahu ya ciro canji ya ɗago kai ya ga baiga Alhaji ba, cikin jin daɗi ya yi tafiyar sa.

 

Na siyo gawayi ina sauri zan dafa mana taliya ‘yar murji ni da ƙannai na kasancewar Umman mu bata nan taje awon ciki. Na taka dakalin ƙofar gidanmu sai naji ance “Salamu alaikum. Na waiwayo sai naga wani Mutum wanda wanda ba zan iya siffanta shi a take ba. Na amsa sallamar ina jira ya min tambaya domin dai ƙila wani gidan yake nema a lugun namu.

Ga mamaki na sai naji ya ce “Zan iya magana da ke?” Me zai hana.Na bashi amsa ba tare da na fahimci me ya ke nufi ba. Ya ɗan ƙara matsowa ya dafa bangon gidan mu ya soma magana “Sunana Aliyu amma anfi sani na da Shamaki, kusan kwana uku baya na ganki kuma gaskiya ba wata kwana Ni ina son ki!” Na ɗan ja baya da sauri domin ban zaci inji haka daga gare shi ba,hasali ma ni ba a taɓa furta min kalmar so ba,dan haka sai na rikice ina sake kallon shi. Ya ce ,”Na ga kin firgita da gaske na ke yi.” Zan shige gida ya ce “Tsaya mana ya kamata ki bani amsa ko da rashin amincewa ce.” Na ce abinci zan dafa wa ƙannai na suna jin yunwa. “In dawo anjima da dare?” Ya tambaye ni da sauri. Na sake duban fuskar sa, nifa bantaɓa zance ba,bansani ba ko Abban zai bari. “To ki tambaya in sun dawo amma zanzo anjima ɗin.” Na ce to shike nan.

Ina girki ina tunani, duk da mutumin ba yaro bane amma naji ya birgeni, sannan kalmar so da ya furta a gare ni ta zama baƙuwa a gurina, dole ma in amsa masa ko na shiga sahun ‘yammata da ke zance a lungunmu bayan wasu ma na girme su nesa ba kusa ba. Shekaruna ashirin da haihuwa jarabawar kammala Sakandire muke yi, a Islamiya ina ajin sauka, amma ban taɓa samun wanda ya ce yana sona ba ko da sunan wasa ba. Na sha kallon kai na a madubi duk da ban kasance fara me shegen kyau ba,na tabbata ba za a sakani a layin munana ba, kuma dai dai gwargwado ina da hankali da kamun kai.

Cikin wannan yanayi na gama girki amma sai na kasa ci, haka a Islamiyya yau sai tambayata a ke yi lafiya kuwa. Domin na zama shiru sai tunani, in har iyayena sun laminci in yi soyayya da shi ba shakka zan ji daɗi domin har na fara jin cewa na ƙosa in sake sauraron muryar shi.

Bayan magariba Umma tana zaune kan tabarma ta idar da salla ta na cin ɗata, na zauna kusa da ita na ce Umma ɗazu wani mutumi ya zo ƙofar gidan nan wai gurina ya zo. Ta ɗago kai da sauri “Me ya ce miki ?” Na ce wai yana so na, nace sai in na faɗa.a gida. “Ɗan ina ne?” Ta tambaye ni, na ce wallahi bansani ba, ya ce dai zai dawo da daren nan. Tace Allah ya sa dai na gari ne,dama ranar nan sai da Umman su Fati ta gwaɓa min magana wai an saka ranar Fati ita dake suyar awarar dare, masu zuwa haddar Kur’anin dare shiru. Kuma nasan ta gwaɓa min maganar ne saboda na ce ta hana Fati yin dare sosai a gurin tuyar awara wani lokacin har shaɗayan dare take kaiwa Abbanku in ya zo sai ya yi ta faɗa. Wai an bar yarinya gurin daga ita sai yaran nan maza marasa kunya. Na ce ai yanzu faɗar gaskiya ta zama matsala Umma. Ta ce haka ne ke dai ki kula da kanki in ya zo ki fita ki saurare shi in kuma Abbanku ya dawo kafin lokacin zan faɗa masa.

Jamila ƙanwata ta matso kusa da mu tace Umma Yaya Baby ce zata fita zance? Na ce to sarkin tsegumi. Umma ta ce “Menene a ciki in kin faɗa mata, Jamila ai ƙawa zaki maida ita,na faɗa miki komai ki ke yi tare da ita shekarunta sha bakwai fa yanzu.” Na kalleta nayi murmushi tare da faɗin to ƙawata baƙo zan yi. Ta ce Allah na gode maka mu ma Allah ya sa ayi biki a gidanmu. Umma ta ce “To kije kiyi wanka ki gyara jikin ki.” Na ce har sai na yi wanka kuma, na yi da safe fa. Jamila ta ce, au da me ki ke nufi, haka zaki je kina zufa? Na tashi na je na ɗebi ruwan sanyi abinda bana wanka da shi amma dan zumuɗi na faɗa banɗaki na yi wanka aiko ina ta atishawa, cikin zuciya ta kuwa fargaba ce tana saƙamin ko ma dai ba zai zo ba.

Na idar da sallar Isha’i a ɗakin Umma na zabga tagumi gefe ga kayana sabbin na sallar bara da Umma ta ce in saka. Jamila kuwa ta tasani agaba sai fadi ta ke “Anty Baby ki tashi ki saka kayan kar ya zo baki shirya ba.” Na ce Jamila ni yanzu fargaba ke duka zuciya ta,ji na ke kamar ya fasa zuwa,kila ma ya canza shawara.Ta ce “Karki faɗi haka Anty, shifa ya zo da kansa tun farko ba ke ce ki ka nemo shiba.” Sauke ajiya zuciya ta sun zo dai-dai da sallamar Abbanmu. Umma ta amsa tana masa sannu da zuwa, muka leƙa muka yi masa sannu da zuwa ya amsa. Nace to Jamila bari in shirya ɗin,ke ki je ki kaiwa Abba abinci. Ta fita tare da faɗin “To.”

Ina jiyo Umma ta na sanar da Abba game da baƙon da zanyi,na yi kasaƙe inji me zai faɗa,sai ga muryar wani yaro ta ratso gidan da sallama. Umma da Abba suka amsa. Ya ce,”Ana sallama da Abban gidan nan inji wani mutum.” Abba ya ce to ka ce ina zuwa. Umma ta ce baka tambaya ko waye ba,yace Malam Sani ne mun yi da shi zamuje wani aiki gobe,to nasan kan maganar ne,kinsan yadda rayuwa ta ke yanzu in ka samu aiki ƙoƙari ka ke ka je in ba haka ba sai aba wani. Ta ce “Haka ne Allah yasa mu dace.” Ya ce Ameen bari in dawo yanzu.

Na gama cire rai da zuwan mutumin har takwas da rabi na yi danasani da ban saurare shi a lokacin ba, na kwance ɗankwalin da na ɗaura dan ya soma damu na,nafara ninke shi sai naji sallamar Abbanmu. Ya na kuma tambayar ina Baby?” Da sauri na amsa gani Abba, ya ce “Kije baƙonki yana waje yana jiran ki.” Gabana ya yanke ya faɗi, na ce to.Jamila ta miƙo min yar kwalba tare da faɗin ga Humra ta Umma ce ki shafa ajikin ki. Na ɗan goga na fita da sauri. Umma ta ce “Baby in kinje fa ki gaida shi .” Abba ya ce haba kema dai yaran yanzu kar suke kallon kowa. Umma tace kasan wannan ce farkon fitar ta zance dole a tuna mata. Abba ya ce “Jamila kai masa tabarma. Can na tsaya a bakin ƙofa ina shaƙar ƙamshi turare mai daɗi irin wanda na ji ɗazu, yana can gefe jingina da bango sanye da farar shada riga da wando ba hula a kanshi, gefen shi ga keke irin mai kwando a gaba na manya ya jingina. Jamila ta shimfiɗa tabarma a kan dakali sannan ta gaishe da shi ta koma ciki. Na taka a hankali na isa kusa da shi,nace sannu da zuwa Yaya. Basan lokacin da baƙi na ya furta hakan ba. Cikin yanayin jin daɗi ya amsa da “Yawwa ƙanwata.” Na nuna kishi tabarmar Yaya ka zauna. Ya ce to, ya isa bakin dakalin ya zauna,na tsugunna a gefe ya ce, ,”kema dawo nan ko ki hau sama ko ki yi irin zaman da na yi.” Na zauna sannan na rusuna na gaida shi,ya amsa “Hajiya ta ce in gaishe ki, na ce ina amsa wa amma, sai kuma na yi shiru. Ya ce amma me? Na ce nayi mamaki ya aka yi ta sannu. Yace, “Ta sannu tun ranar da na fara ganin ki, tasan na yi magana da ke ɗazu, kuma ta san ina nan yanzu.” Na ce Allah sarki to ina gaishe ta in ka koma. Sai da tuni zuciyata ta shiga fargaba e ko matar sa ce Hajiyar domin daga ganinsa ka san dai yana da iyali.

Ya katse min tunani da tambaya. “Baby Ya sunan ki na gaskiya? Saboda ko sunan ki Ni bansani ba yanzun da na yi sallama da Abba na ji yana cewa Baby.” Na ce Amira, amma na asalin gaskiya Rabi’atu sunan Maman Abbanmu ne, sai ake ce min Amira,Baby kuma Ummanmu ta ke faɗa min sai kuma ya rinjaya. Ya numfasa. “Ni ma dai Babyn ya fi min daɗi, amma zan kira kowanne in na so ko?” Na Ɗaga kai alamun eh.

Ya yi ‘yar gyaran murya “Baby gaskiya ina son ki kamar yadda na faɗa ɗazu, in har ki na sona to aure ya kawo ni kamar yadda na faɗawa Abba ɗazu. Sanna bazan ɓoye miki komai ba,ina da yara uku duka mata,kowacce mun rabu da mahaifiyar ta… Saboda me? Na jeho masa tambaya ba tare da na sani ba. Ya ɗan yi dim, sannan ya ce “Saboda Allah, kar ki damu sannu zaki san komai. Ya ci gaba Ni ƙaramin ɗankasuwa ne ina tsare shagon mai gidana a Kantin kwari. Fatan kin fahimta?” Na ɗaga kai tare da faɗin umm. Take zuciyata ta sare kuma ta soma tuhumarsa. Mata uku, kuma ba ko ɗaya yanzu, gaskiya ya kamata insan dalili. Ya katse min tunani da cewa, “Baby ta bakin ki na ke son ji ko kina so na kuma za ki iya aure na? Ni dai komai na ki ya yi min. Na numfasa cikin sanyi jiki na to gaskiya ni dai bansani ba ko ina son ka domin ban taɓa samun kaina a cikin shi ba to bansan ya yake ba. Sannan magana aure Allah shine mai ƙullawa, in har ya ƙaddari hakan zan amsa hannu biyu. Yace “Har yanzu dai ban samu amsa ba,amma zan baki zuwa jibi, kiyi nazari kuma ki ƙoƙarta ki gano ko kina so na.” Na ce, to na gode kuma zanyi yadda ka ce. “Bani lambar wayar ki zan kira kafin jibin inji wannan sanyayyar muryar.” Na ce sai dai in baka ta Ummanmu, saboda har yanzu Abbanmu bai sai min ba, yace sai mun gama walimar saukar ƙur’ani. Yace to bani ta ta ɗin, na faɗa masa sai ya yi flashin yace, “Inkin shiga sai kuyi sebin domin inna kira kai tsaye kinsan ni ne.” Nace, to. Yace “Nine ɗan auta a gurinta, kuma ni kaɗai ne namiji, yayinda huɗu duk mata, Yaya Zainab ce babba,sai Maryam A’isha da Fatima duk suna aure a nan cikin gari.” Na ce masha Allah kaji daɗinka. Ni kam bani da yaya hasalima ni ce ‘yar fari sai ƙanena uku Jamila da Jafar da kuma Habu,sai wanda za a haifa mana yanzu. Yace “Allah ya sauke ta lafiya dama ina ganin Abba na raya a zuciyata cewa ƙila ke ‘yar fari ce.” na ce Ameen, gani ka yi ba tsoho ba ko? Na tambaye shi ina ‘yar dariya. Yace “E mana.” Shima cikin dariya ya amsa. Nace, haka in ‘yan makarantarmu suka zo sai su ce wai Ummanmu Antinmu ce. Muka ƙara yin dariya tare. Ya ce “To Ni dai bari in zo in tafi kar dare ya yi sosai,na kalli kekensa nace danma kana da abin hawanka balle ma ka ce zaka rasa ɗansahu. Yace haka ne.” Nace, Ka gaida Hajiya da kyau. Ya faɗaɗa fara’a “Zan faɗa mata Insha Allahu.” Shine ya nannaɗe tabarmar ya tako har bakin soro yana faɗin in gaida su Umma

 

Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA

 

 

*NA*

 

 

*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*

 

 

_PAID BOOK_

_Kuɗin karatu ₦600_

_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank ko Katin Mtn_

_Phone 08140004302_

 

*DOKA*

_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_

 

 

*Free Page 2*

 

Har tsakiyar dare bacci ya ƙi zuwa min sai juyi na ke akan “yar katifarmu Jamila ta na ta baccin ta, tufka na ke ina warwara abu biyu ke ɗaga min hankali,menene dalilin rabuwa da matansa? Kuma komai nasa dole sai Hajiya ta sani? Zuwa yanzu nasan cewa Hajiya dai ba matarsa ba ce, ko dai mahaifiyarsa ko kuma uwar ɗakinsa. Da safe ina raba mana abin kari awara ce da koko duk muna tsakar gida harda Abbanmu. Umma ta dube ni,”Ke kuma lafiya duk jikin ki a sanyaye?” Nace, lafiya lau, kawai yau kasala nake ji. Ta dubi, Abbanmu tace, “Abban Baby kace ka yaba da saurayin nata jiya?” Ya ce gaskiya Salamatu na yaba sosai, in har sun dai-daita zanyi farin ciki domin alamu sun nuna shi mai hankali ne.Umma ta ce “To ɗan unguwar nan ne?” Yace, A a yace min shi ɗan Gama ne can aka haifeshi amma yanzu suna nan haka ko gurin Janbulo ne, ya ce da ɗan gidan sa a gurin da ya gina suna zaune da mahaifiyar sa. Kuma yace a kwari yake tsaron shagon wani mai gidansa, amma yace asali su ‘yan Gaya ne. Umma ta ce “To, Allah ya daidaita su.

Ni dai bance komai ba,mutumin ya maƙale a zuciyata duk yadda na auno matsaloli sai zuciyata ta kawo wani uzri ta wanke shi. Haka nan har naje makaranta na dawo ina tunanin Aliyu Shamaki.

 

Da dare muna ‘yar hira da Umma, ta tambaye ni da cewa “Ni ko Baby mutumin nan ya yi miki kina ganin cewa zaki iya aurenshi?” Na ce to Amma Ni dai ina ta waswasi. “Game da me?” Ta katse ni da tambaya. Na ce aurensa uku duk sun rabu da matan, ‘yayansa uku duka mata kuma duka sunan mahaifiyarsa ya saka, sai ina jin tsoro ko mahaifiyarsa ce bata barin matan. Umma tace “Karki fara lamarinki da zargi, tabbas dole ki damu game da rabuwa da matansa, shawarar da zan baki shine ki sa hankalin ki sosai ki gano raunisa da fushin sa, ta haka zaki iya samun zaman lafiya da shi. Baby a irin tarbiyyar da nake baku ina sa rai ko mutum yana fidda wuta ta baki dan bala’i za ki iya zama dashi, haka duk wata kissa ko kisisina, ko shirka bai kamata kiji ɗarba.” Na yi ‘yar dariya haka ne Umma.

 

wayar Umma ta yi ringin Jamila tace Yaya Baby lambar jiya ce da kika ajiye. Gabana ya faɗi harda juyawar ciki,take naji banɗaki kawai na ke son shiga. Na amshi wayar na shige ɗakin Umma ina jinshi yana sallama, sai da na zauna sannan na amsa sallamar da wata murya da bansan ina da itaba. Na gaida shi,ya amsa na tambayi Hajiya da yara,yace duk suna lafiya. Yace, “Shine ko ki kira ni kiji ya naje gida jiya.” Na ce to kayi haƙuri amma gaskiya na so in kira ka sai kuma na yi tunanin kar kana kan Kekenka kuma in tsaida kai, har kuma bacci ya ɗauke ni. Ya numfasa “To na amshi uzrin ki, amma ya kike gani zuwa yanzu a zuciyarki ta kuwa fara sona?” Na kwanta tare da ƙara manna wayar a kunnena. Ba zan iya tabbatar da haha ba Yaya,sai dai ka faɗamin yaya son ya ke ko zan gane.

 

Ya yi yar dariya. “Bani labarin bayan rabuwa kin tuna da ni? Sau nawa? Kina tuna hirar mu? Wacce a ciki?” Na numfasa, gaskiya na tuna ka sosai amma ban lissafa dadin ba. A hirar mu dai nafi tuna batun auren ka guda uku,sai in ji fargaba. Yace, “Alhamdulillah Baby kin fara so na, karki damu da maganar matan da na rabu da su, ko tunanin dalilin rayuwar mu, zai fi kyau ki maida hankalin ki akan irin rayuwar auren da za mu yi. Zanzo gobe,ki tanadi labari mai daɗi da za ki bani.” Nace,to Insha Allahu Allah ya taimaka a gaida Hajiya. “Zan faɗa mata.” “Yaran ki fa?” Cikin sauri na ce agaida min su don Allah, koda bansan sunayen su ba. Ya ce “Haka ne ban faɗa miki ba, dukansu sunansu Zeena.” Kamar yaya na tambaye shi cikin rashin fahimta. Yace Ƙwarai kuwa duk sunan Hajiya suka ci, amma kowace da laƙaninta Babbar Meema, mai binmata Mubina sai ƙaramar su Anisa.” Na sauke ajiyar zuciya, gaskiya abin ya birge ni kuma har naji ina son in gansu. “Karki damu ke da ‘ya’yanki kuma ke ma zaki haifa mana wata Zeena ɗin ko?” Kunya ta sa na yi saurin faɗin sai da safe, na kashe wayar sannan na yi rigingine a gadon ina jin farin ciki gami da fargaba. Dole in yi magana da Umma.

 

Kamar kullum ya zauna a gefe yana jan carbi yana jiran Hajiya ta gama addu’o’inta kafin ya gaida ita kuma su yi ‘yar hirar da suka saba. Bayan ta kammala suka shafa tare, ya matsa gabanta sosai ya rusuna ya gaishe ta. Ta amsa tare da kai hannu ta shafa masa kai tana faɗin “Allah ya albarkaci rayuwarka, da ta ‘ya’yanka, ya yi albarka a cikin neman ka, ya albarkaci abinda zaka samu. Allah ya tsare ka daga dukkan sharri mutum ko Aljan da duk wani abinƙi.” Shi kuwa yana ta maimaita ameen. Bayan sun kammala sai ta gyara zama sannan ta ce, “Jiya Maman sani ta zo game da maganar abincin sadaka na ranar juma ‘a wasu abubuwa sun ƙare, na ce ta lissafi kamar yadda aka saba, kuma ina son wannan karon za’a saka sunan mutum ɗari a kayan salla yara marayu, sai mu ba Zeena Foundation dama su nemo yaran da suke dace da buƙatar tallafin nan a ba su. sannan ɓangare kayan ɗaki Amina ta. Kawo sunan mutum biyu kuma sun gama bincike tabbas yaran mabuƙata ne duk marayu ne na ce taje gandu su yi magana a Zeena funitures da manajan kamar dai kowane lokaci. Ya ƙara yin ƙasa da kai cikin girmamawa to Hajiya duk yadda ki kayi dai-dai ne. Ta dubi fuskar shi, “Baka sanar da ni ko ka tattauna da yarinyar nan ba.” Eh na samu ganin mahaifinta kamar yadda ki ka bani shawara, kuma ya min ‘yan tambayoyi kafin daga bisani ya shiga ya turota. “Kamar wace tambaya ya yi maka?” E ya tambayi unguwarmu sannan ya tambaye ni game da addini da sana’a da aƙida. Ya gamsu duk da ce masa da na yi ni yaron shago ne, yace buƙatar kawai ace da sana’ar komi ƙanƙatar ta Allah shine mai buɗawa in yi magana da ita in har mun sasanta ya bani ita. Hajiya ta ɗan yi jim,sannan ta ce, “Mecece hikimarka ta ɓoye matsayinka? Ya gyara zama, Hajiya ina son in samu soyayya ta tsakani da Allah bata abin hannu na ba, ina son in shimfiɗa sabuwar rayuwa ba irin ta baya ba.” Ta yi ɗan murmushi cikin ƙasaita ta ce “Wannan yaro na ne, tabbas akwai hikima cikin abinda za ka yi. Na amince da haka, to ita yarinyar ta karɓe ka ya kuka yi?”. Ya sunkuyar da kai,to har yanzu dai ban same ta sosai ba, na yi mata uzri yarinya ce sosai yanzu ne zata gama Sakandire su za suyi sauka a Islamiyyar su, haka nan kuma ni ne saurayin ta na farko. To ta kasa gane ko tana sona. Hajiya ta yi hiru cikin nazari, sannan ta ce Allah ya zaɓa mana abinda yafi zama alkhairi, za mu ci gaba da addu’a.” Ya ce Ameen ina godiya sosai. Haka suka kasance cikin tattaunawa har zuwa lokacin da Juma ta shigo ta na jera flas na ƙosai da hankali da wainar ƙwai da na ruwan zafi ga kunun gyaɗa ga kuma kayan shayi. Shamaki da kansa ya Haɗawa Hajiya Shayi mai kauri kamar yadda ta buƙata, ya shirya mata komai sannan ya saka abinda kanshi ke so ya shiga ci suna ƙara tattaunawa.

 

 

] Ummi Tandama*HAMSHAƘIYAR UW

 

 

*NA*

 

 

*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*

 

 

_PAID BOOK_

_Kuɗin karatu 600_

_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank ko Katin Mtn_

_Phone 08140004302_

 

*DOKA*

_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_

 

*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*

 

 

Mamakin kansa ya ke yadda ya ƙosa dare ya yi yawan murmushin da ya ke in ya yi shiru ya sa yaran kantin suka soma tsegumin cewa maigida ya faɗa soyayya, musun da suka yi ya sa ɗaya daga cikin yaran mai suna Ɗahiru ya ce bari ya gwada shi. inhar haka ne zai gane. Ya kunna waƙar Hamisu Breaker ta soyayya. Yaje ya zauna a bakin Office ɗin yana ci gaba da shi’anin gaban sa. Daga ciki kuwa Shamaki ya yi tsam da ransa yana sauraron yadda mawaƙin ke yin falsafa akan so, sai kawai ya ƙwala wa Ɗahiru kira, ya amsa ya shigo cikin girmamawa yace “Gani Alhaji.” Wai ku bakwa rabo da jin wakane duk da ita wannan naji ta yi daɗi da ma ‘ana, amma waye ya yi ta ne, tura min ita a waccan wayar in yi wani nazari a kanta. Ya ɗauki wayar ya fita yaje yana basu labari suna dariya. Ranar haka ya yini jin waƙar. Da yamma ya kira Malam Bala direbansa ya ce a wanke mota zai fita bayan Isha’i. ya kuma fara lissafin zai bi ta Zeena Store ya kwashi alawoyi yaje Zeena Factory ya haɗa mata kayan ƙwalam na Snacks. Kamanta gurin wa zaka kuma wane matsayin kake a idon ta? Zuciyarsa ta jeho masa tambaya. ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya ce sai dai in nemi ɗata ko yalo? Ɗan tsaki ya saki sannan ya yi maganar da ƙarfi Ayaba da Lemo zan siya. Hassan dake cikin Office ɗin yana rubuta wani rasit ya ce “Karɓo wa za ayi Alhaji?” Ya dubi Hassan me nace? Yace,”Naji kana maganar Ayaba da Lemo.” Ya yi ɗan tsaki eh da za a karɓo ne amma bari sai na fita sai in siya kawai.

 

Nikam kafin Isha’i na shirya tsaf, ba sallah zan yi ba don haka na kame ina jiran zuwansa, gabana kuwa sai faɗuwa yake ina ayyana yadda zanji idan mun kasance muna hira,ina ta baiwa kaina shawarar ya kamata ace ina zaɓo kalamai inzan furta masa,sannan kuma kar inyi masa magana da irin muryar da nake yi wa kowa hakan zai sa in ƙara birge shi. Take na gamsu da hakan,kuma na yarda shi na musamman ne.

Shamaki ya wahala kafin ya samu kayan da za su nuna shi a talaka,suma dai yadine fari mara nauyi, yanada mugun tsada amma ba kowa zai iya gane hakan ba sai wanda ya san kaya. Ya zube wayoyinsa guda huɗu a kan gadonsa, sannan ya saka mai boturan wadda ya sawa sabon layi domin ita kaɗai a alajihu agogo da zobe na azurfa duk ya zube su. Ya nufi sashen Hajiya.

Ta ƙare masa kallo sanna ta amsa gaisuwarsa. Ya ce zanje gurin Rabi a ne kamar yadda na sanar da ke tun shekaran Jiya. Ta ce “Na fahimta,kaje Allah ya bada nasara,kuma ka ce ina gaisheta. Sannan ka tabbata ka sami zuciyarta a yau,domin na lura kana matuƙar sonta. Allah ya yi muku albarka gabaɗayan ku.” Ya ce Ameen sannan ya miƙe ya fice da sauri. Ta bishi da kallo a fili ta furta akwai matsala ya kamu da yawa, ni da nafi son ya samo wadda ta fi son sa dole inyi wani abu.

Ya dubi Malam Bala yace, in ka isa gurin masu Lemo na ɓawo za ka karɓo. Da suka isa ya rasa na nawa ya kamata ya siya yace Malam Bala ga dubu biyar su yi kashi biyu. Da aka kawo ya ga da yawa yace Malam Bala ka dauki kashi ɗaya. Sai da suka gota lungun sannan ya sauka,yace ka je zan kira ka nan da awa biyu. Ya taka da ledoji biyu a hannunsa ya dawo ya shiga lungu.

Jafar ya shigo da ledoji suna rinjayarsa, yace Umma wai gashi inji wani mutum wai yace Yaya Baby taje. Cikina ya juya da sauri na ɗauki buta zan shiga banɗaki, Umma ta ce “Ke dakata lafiyarki da tun ɗazu kuna zaune sai da yazo zaki tarki shiga banɗaki?” Nace wallahi Jafar yana faɗa sai naji cikina ya juya, na shige da sauri. Ina jiyo Jamila tana tsaki tana mitar “Yanzu da wari zaki gunsa?” Na fito na sake shafa turare sannan na fita na samu har Jamila ta shinfiɗa masa tabarma ta aje masa ruwan fiyawata.

Cikin girmamawa na gaida shi, na kuma tambayi Hajiya da yara. Yace tana gaida ni kuma duk suna lafiya. Nace shine harda wata ɗawainiya haka? Ni fa karka matsawa kanka a irin wannan yanayin ba sai ka min wata ɗawainiya ba. Ya ce “Karki damu, ina da halin yin hakan ne, yanzu ki bani labarin soyayyata. Na ƙosa mu soma musayar ta ni da ke, domin har na soma zama wawa ina kasa jurewa tunaninki.” Nace koda bansan so ba, na tantance kai na musamman ne, duk wani kai kawo nawa kana zuciyata kuma na kasa gano aibunka, zuciyata tana faɗa min cewa in maka uzri kuma in amince ka zama mijina. Na gamsu sosai da shawarar zuciyata kuma na amince ka zama mijina in ina gidanka sai ka koya min soyayyarka. Na kai ƙarshen maganar tare da rufe ido. Ya ce “Alhamdulillah wannan yanayin da ki ke ji shima alamun so ne Baby, yanzu sai mu yi maganar aure, zuwa wane lokacin ya kamata mu zama miji da mata?” Nace ai wanna da su Abba zaku yi magana. Ya numfasa “An saka ranar da zakuyi walimar sauka?” Nace har an fitar da katin manyan baƙi an raba tun wancan satin. Na mu sai wannan satin insha Allahu zan baka ina fatan zaka zo ka ga karatunmu? Ya ce “Ai ina tunanin a haɗa bikinmu da saukar ki… Kai! Na katse shi. Na yi ƙasa da murya. Saura sati biyar fa ayi walimarmu yaushe aka shirya? Ya numfasa “Wane irin shiri kike magana a kai?” Na sunkuyar da kai, yaushe ka kawo kuɗi har aka sa rana, kuma ga maganar lefe su Abbanmu ga maganar kayan ɗaki abin da za a ci abiki, kaga duk abin dubawa ne. Yace “Kinyi gaskiya, amma zan ɗauki wani kuɗin dashi na zan bada kuɗi cikin satin nan a kawo dubu hamsin, sannan nasan dai ko ba lefe zaki aure ni ko?” Har a zuciyata zan iya hakan Yaya, sai dai matsalar iyayena basu da halin yimin kayan ɗaki a cikin wata guda, yanzu ma suna ta abinda zasu fiddani kunyar walimar saukar nan da zamuyi. Yace to ke da me za kuyi a saukar? Nace walima ce kawai a gida, ya ce nawa zaki kashe… Na katse shi da A a bazan ɗora maka nauyi ba, kar ka rene ni da haka, kabari in saba da yanayinka na asali,ka koya min yadda zamu rayu a lokutan akwai ko na babu. Ya ɗaga hannunshi ɗaya tare da faɗin kinga dakata kiji. “Inada shine shiyasa, kuma ba roƙona ki ka yi ba, kawai ki faɗa min nawa zai ishe ki ko inje in ɗauki kuɗin da zan kawo miki na aure inyi gaban kai na da su.”. Na ce Umma za su min faɗa, duka yau ne zuwan ka na biyu fa, kuma… “Kuma me?” Nace shike nan dubu uku ne. Ya ce “To zan baki sai kuma me?” Na ce shike nan. Yace “Ankon walima da hijabi Lemo da kalanda kinsan dai nima na taɓa saukar nan nasan ya ake yi. Na ce ai duk Abba da Umma sun sai min. Ya ce to shike nan zan kawo miki dubu uku jibi mu koma kan maganarmu in turo a kawo kuɗin ko?”Nace bari in faɗawa su Umma, yace don Allah da kin shiga ki sanar musu,kuma zan kira komai dare yau inji ko sun amince.” Na ce to shike nan, amma nima zan nemi wata alfarma a gurinka. Ya tattaro hankalinsa gurina “Faɗi da sauri in har zan iya kin samu.” Ina son in ci gaba da karatu ko da makarantar koyon aikin jinya ne. Ya yi shiru can yace “Bazan miki alƙawari ba,saboda wasu dalilai amma mu aje maganar zuwa gaba.” Nace to shike nan. Ya kwai kwayi muryata “Na gode Babyna.” Na sa hannu na rufe fuska ta. Yace to bari in tafi, nace yau naga baka zo da Kekenka ba? Ya ce tayar ce ta yi faci ɗazu ina hanyar dawo wa daga kasuwa, na ce to Allah ya tsare ya ce “Ameen muka yi sallama cikin shauƙi da ƙauna.

Na samu Abba yana ta faɗa wai ko dai nice nace wa Aliyu zan sha Lemo domin yaran zamani ba abin yarda bane. Na zauna na ce Abba wallahi ban roƙeshi ba yanzu ma dan baku san ya mu ka yi da shi ba ne, cewa ya yi in faɗa masa abinda zan kashe a walima lokacin sauka zai bani kuɗin nace a a ya bari shine ya ji haushi. Umma tace “Abban Baby na faɗa maka ko Jamila bazata yi roƙo ba, bare kuma Baby, duk da ba ‘a shedar ‘yan zamani akwai abinda zaka shedi ɗanka dashi, yace “To Allah ya muku albarka dukanku har da ke Ummar ta su,domin tarbiyyar ki ce, shi kuma Allah ya saka masa da alkhairi ya jiƙan magabata.” Muka ce Ameen ya ce “To sai a yanka aba kowa, ku rage akai gidan Yaya ba ma ci mu kaɗai ba.” Jamila ce me yankawa Ni kuma na yi zugum ina tunanin ta ina zan fara sanar da iyayena saƙon shi. Umma ta ce, lafiya ke kuma ai Abban na ku ya gane ba roƙarsa aka yi ba. Nace ba wannan ba ne, haka ya ce wai a satin nan za a kawo kuɗi, kuma wai in kun yarda za a yi biki tare da walimar saukarmu… Tarin Umma ya sa nayi shiru ta ƙware da ayabar da ta ke ci, na tashi da sauri na kawo mata ruwa ina yi mata sannu.Abba ya taso shima cikin sauri yana mata sannu. Bayan ta samu kanta tana maida numfashi tana magana, “Baza a yi gaggawa ba gaskiya sai anyi bincike, kuma bamu da halin biki a wata ɗaya.” Abba ya ce ki daina magana kin ƙware ki yi shiru tukunna. Sai da ta samu natsuwa sannan Abba ya ce, “Inda haka zata samu zanfi kowa murna ace na aurar da Baby a ranar saukar ta. To amma hidimar da yawa ga haihuwarki ko yau ko gabe.” Umma tace, ta haihuwa mai sauƙi ne, ba taron suna zanyi ba Allah dai ya sauke ni lafiya. Abba ya ce “Ameen, dama tun farko ya faɗa min aure ya zo, sannan ya taɓa aure kinga dole ya buƙaci aure da wuri, ina ga abinda za a yi mu amince su fara kawo kuɗin sai mu yi maganar da ta dace.” Umma ta ce to shikenan ke sai ki faɗa masa in yazo. Na sunkuyar da kai na ce yace infaɗa masa a waya zai kira a ta Umma in yaje gida. Abba ya ce to. Sai ki sanar dashi. Da wayar Umma na shiga ɗakinmu ina ta jiran kiransa har bacci ya kwashe ni.

 

Shamaki ya ƙosa ƙwarai ya sallami mutanan da yakan gansu in an idar da sallar Isha’i, suka tsare shi, yana sauraron buƙatunsu wanda zai yi a gurin kamar kuɗi marasa yawa ya basu wanda sai ya tura su je Zeena Foundation sai ya tura su. Ya ƙagara sosai dan tun jiya ya so jin yadda Baby suka yi da mahaifanta, amma da yaga dare ya yi sai ya barwa yau. Ya dubi Malam Sabitu wanda shi ne limamin masallacinsu da ke jikin gidansu ya ce, Malam zan shiga gidan gobe zan baka kati ka ba mutumin sai a kaishi Zeena Hospital za su min magana game da abinda za’ a biya. Ya ce “To Allaji Allah ya ƙara arziƙi muna godiya.” Shamaki cikin ƙosawa ya ce ba komai, Malam Aba sauran jama’a haƙuri ina da uzri a ciki. Liman ya ce “To insha Allahu Ubangiji ya rufa asiri.”

Kamar ya wuce amma dole ya shiga gurin Hajiya, tana lazimi, Azima tana gefe tana jira ta kammala dan ta mirza mata manta na ƙafa. Ya zauna shima yana jira, zuciyarsa ta tafi matuƙa ga tunanin Baby, nan da wata ɗaya tana gidansa zai bata rayuwa mai kyau, zai maida ita sarauniyar shi.,.. Yaya Shamaki! Muryar Azima ya ji ta kira sunan shi da ƙarfi, a firgice ya waiga ya dube ta tare da faɗin Baby lafiya?” Sai kuma ya dawo cikin hayyacinsa ya dubi Hajiya wadda ta tsare shi da ido, yace sannunku Hajiya. Bata amsa ba sai ta kalli Azima tace je ki dawo. Ta maido duban ta gare shi, “Aliyu.” Ta ambaci sunan sa, ya ɗan zaro ido kafin ya zabura ya amsa da cewa na am Hajiya. Cike da Tsoro ya ke Domin a duk ranar da ta ambaci sunansa to ya tabbatar ranar ya kai maƙura gurin ɓata mata rai. Ta numfasa “Faɗa min tunanin me ka ke yi?” Yace ba wani abu bane waya nace wa yarinyar nan zan mata tun jiya to ban samu na cika alƙawarin ba. Ta nuna shi da yatsa shi yasa ka shigo gida da wuri ba domin ka gama jin matsalolin mutanan da ke da buƙata a gurinka ba? Ni kuma ka zo ka tasani ka faɗa kogin tunani, to in na janye amincewa ta da wannan yarinyar ya zaka yi kenan?” Gaban shi ya yi mummunar faɗuwa cikin sauri yace, Nasan baza kiyi haka ba Hajiya! Ta kuma zaro ido cike da mamaki, abinda ta tsammani zataji shine Duk yadda ki ka yi daidai Hajiya. Ta lumshe ido cike da damuwa, can ta ce “Shikenan yau nasan baza muci abincin dare da kai ba,bare muyi wasu bayanai ko wani lissafi,ka tashi kaje ka yi wayar.” Ya san gatse ta yi masa,dan haka sai ya ce, za muyi lissafi Hajiya, abincin ne yau cikina duk a cushe ya ke. Ta kuma yin shiru tabbas ko ita yau abincin nan ba zai ciyu a gareta ba, ta numfasa sannan ta kai hannu ta ɗauki wayar ta a gefe ta shiga neman Hassan. Ya ɗauka cikin girmamawa suka gaisa, ta ce dama zan tambaye ka yau da aka kawo abinci kasuwa Shamaki ya ci Hassan ya ce “A’a kayan marmari ya ci sosai yau.” Ta ce to na gode. Ta sake maida kallon ta ga Shamaki, tashi kaje za muyi magana da safe, yanzu kam bana zaton kana iya fahimtar duk abin da zan ce maka.” Ya ce haba dai Hajiya karki tashi hankalin ki, wallahi abin ba kamar yadda ki ka zata bane. Ta nuna masa hanyar sashensa “Je ka yi waya.” Tsam ya miƙe cikin sanyin jiki ya ɗan kuma risnawa tare da faɗin mu tashi lafiya Hajiya Allah ya huci zuciyarku. “Allah ya maka albarka.” Ta furta cikin kallon gefe. Ya tafi ta bishi da kallo ranta ya sosu ƙwarai in da ne Shamaki ba zai tafi ba da tace ya tafi, zai tsugunna ne yana bata haƙuri ƙilama sai ya zubar da hawaye har sai ta huce, sannan zai ci abincin ko da baya jin yunwa,haka kuma za suyi lissafin kamar yadda suka saba. Lallai dole ta ɗauki dukkan mataki kafin abin ya wuce gona da iri, ta koma ta jingina sannan ta ɗauki waya ɗaya a cikin wayoyinta. Ta danna kira, suka gaisa da malamin wanda shine yake taya su da addu’o’in neman tsari da samun kariya. Ta ce Malam akwai wata matsala da ta soma tunkarowa cikin ahalina yaron nan Shamaki ya faɗa soyayya da wata yarinya, yadda ya koma kamar wawa abin ya tsorata ni. Ina son amin bincike shin ba wani abu yarinyar ta yi masa ba! Kuma tsakaninsu ina son in sani akwai alkhairi ma kuwa!Malam yace “Insha Allahu Hajiya za kiji sakamako zuwa gobe, za ayi bincike sosai zamu iya samun sunan yarinyar?” Hajiya ta ɗanyi shiru sannan ta ce ina zuwa. Ta katse layin ta soma kiran wayar Shamaki, ya gama shirin kwanciya kenan yana ta sauri dan ya kira masoyiyarsa, cikin sauri ya ɗaga kiran Hajiya gaban shi yana faɗuwa. Tace “Ya sunan yarinyar da kake so?” Cikin sauri yace Baby Amira ko Rabi atu duka suna kiranta da shi. Ta kashe layin ba tare da tace komai ba. Sai da ya gama komai sannan Ya danna kiran layin wayar mahaifiyar ta sannan ya kwanta a kan tsakiyar gadonsa ƙafafun sa na ƙasa.

Na jigata sosai da tunanin abinda ya hana Yaya Aliyu kira na, sai naji kamar in kira shi sai kuma wata zuciyar ta hane ni,har na kasa cin abinci a yinin na kuma shiga kaiwa Allah kuka in har da akwai matsala ina roƙon Ubangiji ya kauda matsalar, yanzu kam na samu tabbacin cewa ina son Aliyu har lokacin da muka je makwanci banji sautin wayar Umma ba, na sadaƙar cewa ya canza ra’ayi. Ƙarar kiɗan Nokia ya tashe ni zaune, na kasa kunne inji ko Umma zata kira ni, har kiran ya yanke, na tashi da sauri na fita, daidai lokacin da wayar ta sake daukan kiɗan na yi sallama a ƙofar ɗakin ba a amsa ba, na shiga Umma bacci ta ke wayar na caji Abba kuma bai shigo ba, na ɗauki wayar da sauri na nufi ɗakin mu ta kuma katsewa kafin in ɗaga, na fara danna lambobin cin bashi amma sai kira ya ƙara katse hakan, da sauri na faɗa kan lamammiyar katifar sannan na manna wayar a kunne tare da sallama. Ya amsa tare da tambayar ko dai har na yi bacci? Na ce masa e bacci ya fara ɗauka na. Ya ce “Ki min afwa abubuwa sun sha kaina ban kira ba kamar yadda na yi alƙawari.” Na sauke numfashi hakan kuwa ya yi matuƙar ɗaga hankali na, na yini a damuwa ko dai ba lafiya ne, in kuma na yi kamar in kira ka, sai zuciyata ta faɗa min cewa in kana cikin wani uzri fa, yanzu dai da tunanin haka na kwanta. “Alhamdulillah! Ina da tabbacin kina so na a yanzu, kuma naji daɗi dan Allah karki dinga ɓoye min duk yadda ki ka ji a kaina ko daɗi ko akasin haka ina son wannan kinji Baby?” Nace To zan ke faɗa maka Yaya. ya ce “Yanzu faɗa min ya kuka yi da su Umma?” Na ce sun amince ka kawo kuɗi amma kamar yadda na faɗa maka baza su amince da auren lokacin walimar saukarmu ba, domin yanayi,kuma kai ma bana son ka takura kanka, kuma malamai suna cewa gaggawa yawancin ta daga sheɗan ne, abi a sannu. Ya numfasa “Gaskiya kika faɗa Rabi’atu amma ina son ki gane wani abu, na taɓa aure nasan daɗin shi kuma ina buƙatar shi. Bazan jure dogon zama ba, tunda har zaki iya sadaukarwa game da lefe, me zai hana ni ba zan sadaukar game da kayan ɗaki ba. Ko ba domin ni za ayi ba?” Na ce domin kai za ‘ayi mana,amma kasan mutane akwai su da munafinci sosai za ayi ta gulma cewa ko kayan ɗaki iyayena ba su sai min ba. Lefe kuwa zamu iya cewa ankai ajiya. Yayi murmushi mai sauti, “Gadon ma sai muce kafinta bai gama ba.” Ya faɗa cikin yanayin nishaɗi. Na ce in har su Umma za su yarda da haka ni bani da matsala kaine abinji nan katifar da nake kwance da kaɗan ta fi tabarmar kauri. Ya saki dariyar da sai kuma naji kunya ta kamani. Yace “Ina da katifa babba kuma Hajiyata ta na da tukunyar girki dan haka ni matata kawai na ke buƙata.” Wani daɗi ya tsirga min da ya ambace ni da matarsa. Allah ya nuna min na faɗa a zuci, “Ameen Babyna.” Nace kai araina nayi addu’arfa. Yayi “yar dariya,araina na amsa fa ke ma kinji ne?” Nace e mana, yace “A lallai mu na musamman ne gaskiya kunnuwanmu suna iya sauraron abinda zukatanmu suke faɗa kenan gaskiya mu gode wa Allah. Yawwa Baby in tambaye ki wani abu?” Na lumshe ido na sake yin ƙasa da murya domin bacci yana ɗan bibiyata. Na ce tambayi ko me ka ke so. “Zaki iya zama da uwar miji?” Cikin sauri na wartsake, a son zuciyarta shi ne ‘a ‘a bisa ga yadda na ga Umma tana fama da kiyayyar dangi Abba, kuma ta bamu labarin abin ya fara ne tun daga tsanar da mahaifiyar Abba tayi mata kafin ta rasu. “Kinyi shiru Baby.” Yafaɗa da sanyi jiki. Nace mamaki na ke yi da wannan tambayar kuma ina nazarin dalilin yinta. Yace “Kar ki damu da dalili, ki faɗa min me kike mamaki.” Nace to ya zaka tambaye ni cewa zan iya zama da mahaifiyar da ta haife ni? Na marairaice murya ina magana cikin yanayi shagwaɓa. Yaya in har yadda nake jin ka a zuciya shine so to tayaya Mahaifiyar ka baza ta zama tawa ba? Sannan in har wani zai tambaye ni cewa zan iya zama da mahaifiyata me zai hana in so jin dalilinsa cikin mamakina? Ya yi shiru Yarinyar ta gama gigita shi ta sukurkuta shi,dan haka ya fara da faɗin “kiyi haƙuri Babyna nasan mata da yawa suna gudun zama da Uwar miji wannan shine farkon matsala ta da matata ta fari Maman Meema, amma ba wai dan wani abu na yi wannan maganar ba.” Nayi ɗan murmushi domin ganin na soma gano wasu abubuwa game dashi, kuma rauninsa ba zai min wahalar ganewa ba. Ya katse ni da cewa “Kin lashe babbar jarabawar da na fara miki kuma zan turo ranar Lahadi ni kuma zanzo jibi in kawo miki dubunki uku ta walima.” Ba gobe kace min ba a jiya? Na katse shi, Ni ba damuwata kuɗin ba domin sai da na sha faɗa akan Lemon da ka kawo jiya, Abba yana zargin ko dai roƙon ka na yi ka siya min, Ni kuwa ina jin daɗin hirar da kai ne kawai ina son in ganni gani ga ka.” Ya katse ni da cewa “Alhamdulillah na ci nasara Baby wallahi kin kamu da sona Baby dan Allah ki furta ki ce Aliyu ina sonka dan Allah! Ki faɗa inji.” Na sunne kaina cikin ɗan yamusashshen filo na Na ce wayyo Allah Yaya kamin afwa zan faɗa maka amma banda yanzu. Ciki shagwaɓa yace haba Babyna.” Gyaran muryar Abbanmu naji banji sallamar shi ba, nasan zai zo ne ya duba mu kamar yadda ya saba,don haka sai nace Yaya Abba ya shigo sai goben ka yi haƙuri, na kashe wayar ya taɓa ƙofar na yi laf, ya haska sannan ya yi addu’a ya tofa gabas da yamma kudu da arewa na ɗakin, sannan ya ja ƙofar ya fita.

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment