Halin Rayuwa Hausa Novel Complete
HALIN RAYUWA
1
NA
07035586299
HAJ. HAFSAT C. SODANGI
(Mrs Yunus Abdullahi Dabai)
1
Hakkin Mallaka [m]
Hakkin Mallakar littafin na Haj. Hafsat C. Sodangi ne
GODIYA
Godiyata har kullum ga Allah take Subhanahu
ta’ala mai kowa mai komai, Makadaici, Mahalicci wanda a ke nufa da dukkan bukatu gwani mai hikima wanda yayi halittarsa bisa tsari na aure wato mace da namiji.
Tsira da aminci su kara tabbata ga cikamakin
Annabawa, shugaban Manzanni Annabin karshe
Muhammad (S.A.W) da alayensa da sahabbansa da
wadanda suka bi ma tafarkinsa na gaskiya har zuwa
ranar karshe, wato ranar rarrabewa tsakanin karya da
gaskiya (AIkiyama), Ubangiji yasa mu dace.
Har wayau ina mika godiyata ta musamman ga
daukacin makaranta littattafaee cikin kasa da waje,
Ubangiji ya saka da alheri ya kuma kara karfafa
zumuncin da ke tsakaninmu.
Na gode, Haj. Hafsat C. Sodangi
6/7/1434
GODIYA
Godiya mai dumbin yawa gare ki.
Rabi’atu Faruk Jauro (Ministry of Commerce and
Industry Yola, Adamawa State) Da Zainab Sunusi Kofar
Gabas Danbatta, Zainab Abarshi Yawuri
2
HALIN RAYUWA
A duk sanda naci karo da wata kalma da
ta danganci rayuwa gabana kan fadi in
tsinci kaina cikin wani matsayi na tsoro da
razana, wani lokaci ma in ji na samu kaina cikin
halin da zuciyata kan samu kanta cikin yanayi na
kaikawo saboda tunawa da al’amuran da suka
shafi jiyana da yau dina, in suke jin wani
mummunan faduwar gaban idan na tunan ba ni
da tabbatas ko masu niya bisa gobena.
A mafi yawancin lokaci kuma in har nayi irin
wannan tunanin to nakan samu kaina ne da yiwa
gwanin halitta godiya da bai sanya mana wani
tabbataccen al’amari ba in dai cikin wannann
rayuwar tamu ne ta wannan dunyar, duk abinda
ka gani zai wuce.
Farin ciki ko bakin ciki yana da lokaci, komai
yayi farko wata rana zai yi karshe. Wani karin
maganar ma sai ya ce abin da ya baka tsoro a yau
babu mamaki gobe ya baka tausayi, wasu ma da
suka yi wa rayuwa irin fahimtar da suka yi wwa
rayuwa irin fahimtar da suka yi mata sai suka ce
wai ita din tamfar hawainiya ta ke, ta kan iya
canza launinta a kowane lokaci.
Al’amuran da na gani a shekaruna na
kuruciya sun sanya ni son bayar da labarina ga
na kasa dani ba don wani labarin dadin bayarwa
3
ke gare shi ba, a’a sai dai don ya zamo hannunka
mai sanda a gare su. Ya zamo musu wani darasi
da za su rika don su kauce daga aikata kurarai
irin na kuruciya kurarai da kan zamo tanfar na
tsalle daya mai jefa mai shi rijiya.
Wannan labari da nake nufin bayarwa a yau
labari ne da ya danganci halin da rayuwata ta
kasance shekaru talatin baya da suka wuce a
lokacin da na ke da shekaru tara kacal a duniya.
Ni Maryam Abubakar, na taso ne a gidanmu
gaban iyayena uwa da uba cikin gata kulawa da
kuma tarbiya, a wantcan lokacin da nake magana
a kai iyayena uwa da uha suna matukar sona
musamman ma Babana wanda Sunan
Mahaifiyarshi ke gare ni bisa hakanne ma bai
fadin sunan nawa sai yake kirana da kalma ta
Yacuwuna’ kalmar da ke nufin ohaifiva ko
uwa cikin harshen barbarci.
Wani dalilin da ya kara tsananin soyayyarshi
gare ni ko in ce muni da Yayata Khadija wacce
take ta girme ni da yawa, don a lokacin da nake
da shekaru. taranne a ka yi bukinta da wani
saurayinta da suka so juna tun suna ‘yan yara,
Ibrahim shi ne din bai da kowa sai mu, nai da
dangi ko kuma in ce ya dade rabonshi da yayi
mu’amalla da su ba ya ma maganarsu.
4
Nasha jin Innata a wancan lokacin tana ce
mishi Mallam ko ba don mu ba kai ni wurin ‘yan
uwannan namu in gano su saboda yaran nan su
gansu su ban iyayensu da danginsu saboda in mu
ne yau ba mu ne gobe ba, su kuwa dangi
musamman na uba ko don maganin gori a neme
su.
A mafi yawancin lokaci ta kan yi irin
wadannan maganganunne har ta gama ba tare da
ya tanka mata ko ya ce mata uffan ba. Sai dai
wannan bayani da nayi a kan Babana bai hana
shi zamowa daga cikin mutanen kirki ba, mutumn
ne mai tsananin hakuri mai gudun bacin ran
wani, mai girmama makwabci wanda ba ya shiga
harkar da ba tashi ba, ba mai yawan magana ba
ne mafi yawancin lokaci hirarshi takan yi nisa ne
kawai da makwabcinshi Mallam Hodijo wanda
suka zama tanfar yan uwa shi da shi ga shi
kuma sai aka yi dace Babana Babarbare ne
wanda ko zanen da ke fuskarshi ya isa ya
bayyanar da asalinshi.
Haka shima Mallam Hodijo Bafulatani ne da
bai bukatar sain an tsaya bayani a kan shi, don
haka sai abin nasu ya kara zamowa gwanin
sha’awa kullum a cikin zolayar junansu suke
suna raha tare da barkwancin wasan fulani da
5
Barebari, haka kuma alaka take tsakanin Innata
da matar Mallam Hodijo mai suna sumaye.
Wani dalilin da ya karawa Babana sonmu ni
da ‘yar uwar tawa shine, kasancewar matarshi
mata mai wabin ‘ya’ya cikin haihuwa bakwai da
aka yi ne aka samu mu biyun muka rayu.
Rashin sanin dangin Babana ko rashin
mu’amallar da su bai hana gidanmu zamo wa
gidana Jama’a ba Innata mai ‘yan uwa ce ban da
haka kuma mata ce da ta iya mu’amalla da
mutane da ke kuma iyakacin kokarinta wajen
kiyaye hakkin makwabtanta.
Ita din kuma mata ce da yawan mu’amallarta
da ‘ya’yan da ba nata ba, ya zamo dalilin da ta
zamo uwar yara da yawa maza kuma da mata
kanana da kuma ‘yan samari.
Gwanar kitson ce da kuma lalle bata laima da
kwiya kan hakan sannan bata taba damuwa dayi
don a biya ta ba, don haka kullum ta zaunar da ni
da nufin yi min kitso ko lalle to zata hada ne da
duk yaran da muke wasa da su a wannan lokacin
tayi mana kitso da lallen tare da wannan dalili sai
tayi sabo da iyaye da yawa na yaran da take yi
mana kitson nan ko lallen tare wasu daga uwa
godiya bayan sun aiko mata da abin hasafi ta
mayar su biyo baya.
6
Wasu yaran da ta zamo uwa gare su kuma
musamman yan mazan daga yawan ciyarwarta
ne tana ganin yaro cikin wani zata zaunar da shi
ta zuba mishi abinci in har ya yarda yaci zata
gaya mishi gobe ma kazo daga haka har sai zuwaa
wurin nata ya zame mishi jiki ko kuma dabi’a,
don haka a ko ina yara suka ga Inna za ka ji suna
Mama’ Mama ina za ki? Mama kin dawo?
Mama kin ga wane ko? Hatta wasu iyayen yaran
da suka san Inna uwa ce a wurin ‘ya’yansu, za ka
ji suna gaya mata laifin yaran nasu don nufin ta
taya su yi musu fada kan laifuffukan nasu kko
kuma kin da suke yi wa makaranta.
Cikin yaran da Inna ke yin mu’amallah mai
karfi da su akwai Mubarak da Mansur wadanda
su ba suna zuwa wurinta don cin tuwonta bane
a’a sukam ma yan gata ne a gidajensu
musamman Mubarak wanda shi shi kadai ne da
namiji a gidansu a wurin kuma ubanshi Alhaji
Mühammadu wanda a unguwar tamu duka babu
maigidan da ya kai nashi girma da kuma kyau.
To haka shima Mansur ko da suke da yawa a
gidansu gidan nasu na rufin asiri ne, su suna
zuwa wurin Inna ne kawai saboda gidannata ya
zamo wurin zuwan yaran unguwar har kuma sai
ka ji suna tambayarta Mama da wani abu ne mai
dan dumi in akwai ta ce akwai in babu ta ce sai
7
Raino ne sila Hausa Novel Complete
garin rogo, wani lokacin ma har sai ka ji tana yi
musu fada kan abin da tasan suna yi musamman
Mubarak, kusan kullum ya shigo za ka ji tana
tambayarshi kaje Makarantar ko yau ma ba ka je
ba? In yaje ya ce yaje in bai je ba ya dan tsuke
fuska yana yi mata bayani Mama ke ba za ki
gane ba ne? ta ce Eh, ba zan gane ba in ba ka
gaya min damuwarka ba amma in har za ka bude
baki ka gaya min ai zanfahimci daidai
gwargwado, tayi mishi nasiha
lyayena ba masu hali ba ne, amma a cikin
rufin asiri muke rayuwarmu, sana’ar Babana
sana’a ce ta rufin asii, kayañ miya yake sayarwa
a saman layinmu ba sni da tsawwalawa.kan
kayanshi, don haka wurin nashi matattara ce ta
cinikin yara.
Mallam ban tumatir, Mallatu han attarugu,
Mallam ban alayyaho, aikin ke nan. Don naka
inhar ban je Makaranta ko gidan Yaya Dijah ba
to yawanci na kan je wurinshi ne in rinka taya
shi in yana bada kaya in rinka karbar mishi kudi
saboda wasu yaran da tarbiya bata ishe su ba
sukan karbi kayan miyan su tafi ba tare da sun
ba shi kudin ba saboda ganin hankalinsi ya tafi
wajen masu kokarin ya ba su nasu.
Babana ba mutum ba ne mai dogon buri ko
mako game da kudi, don hakan kullum ya dawo
8
daga kasuwarshi ya kan tattara duk cinikin nashi
ne ya mika mata ko kuma ni ya miko min in
shirya su in je in ajiye su a inda nasan tana adana
kudi.
Shi kuma ba mai yawan sa ido kan abubuwa
ba ne, balle ka ji shi yana kididdiga ko tuhuma,
don haka kusan komai Inna ce take tafiyarwa
tana ganin wani rami a çikin gidanmu za ka ji ta
kira wani daga cikin samarin da suke shigowa
wurinta ta basu kudi ta ce maza suyo siminti ka
toshe mnin wannan wurin.
In kwata ce take nema ia cika zata sa su nemo
mai kwasheta ya gyara suyi ciniki ya kwashe ta
basu kudin suje su biya haka nan rufin kwano in
ta hango alamar zuwan damina zata basu kudin
foti su sayo su nemo mata mai hawa kwanon ya
kara bin kusoshi da fotin din maganin yoyo.
Haka nan kuma ko wata hidima ce ta taso
bata jiran Babana sai dai ta ce mishi an yi kaza
an yi kaza ko da kuwa ta sallah ce ko azumi ya
ce mata to, ko da kuwa a kan shi ne zata yi tayi
mishi tuni musamman da sallah, Mallam in fa
baka sayi yadi ka bada dinkinka yanzu ba zaka
rasa dinki, ya ce mata to don na rasa dinki
menene tunda dai ke da yaran kun samu ai shi ke
nan.
9
Tayi murmushi ta ce, Haba Mallam ana
hidimar sallah ai zan so nima in ga mijina fes in
Rara jin dadi da yiwa Ubangiji godiya, yayi
kamar bai ji ta ba. Inna da makwabciyarta Babah
Sumaye wani irin zama suke yi da yafi na ‘yan
uwan da babu fahimta da kauna ta zumunci a
tsakaninsu dadi.
Kusan kullum sai wata fa shigo wurin wata
duk abin da suka girka sai sun aikewa juna, wata
rana ma ka ji daya tana cewa dayar in za ki yi
girki kiyi tare da nan gidan, don kasala nake ji ko
kuma aiki zai yi min yawa-za a yi abu kaza da
kaza su ce to.
To haka Babana yake da mallam Hodijo
ko’ina za su suna tare ko da kuwa Masallaci ne
kullum kuma naje karbo cefanen gidanmu, to
nakan hado ne da na gidan su Babah Sumaye.
Innata ba wata jaruma ba ce in dai a kan
neman kudi ne bata da wata sana’a da take yi ta
maida taro ya zama sisi anima tana cikin wadata
saboda halin mijinta na komai nashi a wurinta
yake ajiye shi bai da kuma matsala don ta ce
mishi ta kashe kaza kan abu kaza na hidima da
ya taso haka nan ita din gwana ce kwarai ta
shirya abinci mai dadi aci shima Baban nawa
mai son cin dadin ne.
10
Sannan ta iya zama da shi ta iya tarairayarshi
da tattalinshi duk da shi ba mai yawan magana
ba ne, ko yawan dariya amma in suna tare shi da
ita fuskarshi bata rabo da murnmushi, bini-bini
kuma za ka ji shi yana yawan ambaton sunanta
Ramatu.
Gidanmu karamin gida ne dan madaidaici,
dakuna hudu ne a ciki, ciki da falo guda daya
wanda ni da Inna muke ciki, sai dai-dai guda
biyu, daya Babana daya kuma tarkace na
kwandunan tumatir din Babana da sauran
kayayyakin Inna na aiki, kullum ka shigo
gidanmu daga zauren gidan ka ke soma shakar
kamshin turaren Innata.
Ana cikin hakanne aka wayi gari a gidan
namu Inna tana wani irin rashin lafiya da Babana
yayi ta zarya yayi ta zirga-zirga da dawainiya
mai yawa a kai, cikin wani irin farin ciki da
zumudi mai yawa.
Haka nan itama Babah Sumaye tayi ta hidima
aikin gidanmu gaba daya ya zama nata, ta rinka
kai kawo tana ta faman murna ashe, ashe wai
Innar tawa wani cikin ne da ita, ni kam nayi farin
ciki saboda ganin zan samu kani wata kila mace
watakila namiji, wanda dama nasan Babana yana
Son samunshi.
11
Sai dai kuma gabana ya fadi da na tuna da
irin haihuwar da Innan tayi shekara guda da ya
wuce inda ta kubuta da kyar.
Kankana, abarba, lemo da ayaba basa
yankewa a gidanmu, saboda kullum sai Mallam
Hodijo ya kawo ya ce a kawo mata saboda abin
sana’arshi ke nan a bakin asibitin garinmu.
Haka a ka yi ta fama da ita har dai ta samu
sauki ta wartsake ta koma kan al’amuranta.
Muna nan a haka har cikin Inna ya bayyana
ya fito sosai, dama kuma ita din mai katon ciki
ne ina jin ta rannan a hirar da suke yi tana gaya
mishi ni dai ban taba jin ciki irin wannan ba
Mallam, ko kuma don mutum ya fara girma ne
yake jin hakan oho.
Yayi murmushi ya ce, “Ramatu ke nan, kina
yar shekaru talatin da biyar kina gayawa kanki
girma da kuma ni ne nayi kuskuren ba ki nace
miki kin girma da kin ce.na hango wata yarinyar
ne a waje yáa sani kiranki tsohuwa.”
Tayi murmushi ta ce, “Uhun! Mallam ke nan,
to tunda a ka yi auren yarinyar nan kuwa har
gata yanzu da juna biyu ai dole in kirawa kaina
girma ni da kaina.”
Ya tayata murmushin kafin ya sake kallonta
Cikin natsuwa ya ce mata, ai ba Dija ce mizanin
da za ki rinka dubawa wajen gane girmanki ba,
12
ni za ki rinka dubawa ai ni ne ma’aurinki ya ya
ki ke a wurina? Shi ne maganarki, ya ya nake
kallonki? Shi ya kamata ya zama abin lurarki,to
in kuwa ni ne ban taba kallonki na gane
canzawarki ko bambancin da ke tsakaninki a yau
da na ranar da mahaifinki ya kira ni ya ce min in
dawo da yamma inga ‘yar da yake da ita in tayi
min in kawo sadaki a daura min aure da ita babu
wata rana da nake wayar gari ko zan wayi gari
ban yi wa wannan mutumin kirki addu’a ba
Ramatu.”
Ta kalle shi ta dan yi murmushi ta ce, Uhun
kai Mallam babu halin in kawo maka wata
magana sai ka kawo wannan zancen ya ce, Eh ai
bana gajiya da bada labarin ne saboda ya bani
abin da ban taba tsammanin samu ba na kar6i
aurenki cikin tsananin tsoro saboda nayi zaton za
ki bijire sai kuma ki ka zamo yarinya mai
albarka mai ladabi da biyayya, mai sanin darajar
iyaye da aurenki.
Tunda ki ka zo wurina ban taba ganin wani
al’amari daga gare ki ba sai na alheri.” Shiru
Inna tayi tana sauraronshi sai da ya gaji ya canza
zancen don kanshi ni nafi zaton canjin da kike ji
din wata kila da namiji ne ai kin san gaba daya
haihuwar nan da a ka yi in ban da na farin sauran
13
shidan duk mata ne amma tunda kin ce kina da
damuwa to tashi kawai muje asibiti.”
Tayi maza ta ce ka ji Mallam kuma shekaran
jiya ne fa naje awo suka kuma ce min babu
matsala, iyaka dai in dan rage cin gishiri da
barkono.”
Haka rayuwar Inna da Babana take kullum a
cikin ganin alherinta yake, bai daga ido ya kalli
wani al’amarinta ba balle ya gano kuskurenta
baida wani labari wanda ya wuce na fadin
alherin mahaifinta saboda ba shi ita da yayi ba
tare da shi din ya neme ta ba ya kuma ba shi ita
tana da shekaru goma sha biyar a duniya, bayan
kuma gata da manema masu yawa da suke fatan
ganin an ba su aurenta.
Kullum Babana a cikin sayayyar haihuwar
Inna yake komai ya gani ya bashi sha’awa zai
sayo yazo da shi gida, rannan ina jin ta tana ce
mishi wannan kayan fa Mallam yawansu ya isa
haka.
Kuma ma ni sai nafi son a hakura da sayayyar
haka sai an ga an yi haihuwar tukuna saboda ni
dai Mallam zuciyata a tsinke take game da
haihuwar nan.
Yayi maza ya dago ido ya kalleta za ki fara
ko Ramatu? Kin san irin fadar min da gaban da
kike yi kuwa idan kina furta irin wadannan
14
kalaman? Kin sani sarai ai kin uma san abinda
kike yi in yi kike yi don in ji dadi kin sani, in ma
don me kike yi kin sani.
Kin sani sarai bani da kowa bani kuma da
yan ‘ya’yannan naki amma sai ki rinka gaya
min maganganun da zan rinka hawa gadona da
daddare ina kasa yin bacci saboda lissafe-
lissafen al’amura. Tayi murmushi ta ce, “To kayi
hakuri Mallam bari in je in kawo maka
abincinka.”
Bai saki fuska ba ya ce, To wane abinci kumna
zan ci ni yanzu bayan kin gaya min wannan
maganar.”
Ta sake yin wani murmushin ta ce, “Kayi
hakuri Mallam ba zan sake yin ba amma da
wannan katon cikin nawa da wannan kwalliyar
da nayi don ka ji dadi in girka abinci don kai ka
ce ba za ka ci ba ai kai ma kasan in na soma
fushi zan dade ban huce ba, burabusko fa nayi
maka da miyar yakuwa, ta kuma sha kashi da
tantakwashin ga kuma nama ka gani?”
Ta zauna kusa da shi tana nuna mishi in zuba
maka? Ya ce To ko don tsoron kar kiyi fushi ai
zan ci Ramatu amma in don yunwar da na dawo
da ita ne ai ta tafi tunda taji irin kalaman ki tayi
maza ta ce ai ba zan sake ba kayi hakuri ya ce ya
wuce Ramatu.
15
Anyi hakan bai dauki wasu kwanaki da suka
zamo masu yawa ba na farka cikin dare naga
kofar dakin Innata a bude alhalin sanda zamu
kwanta ni da hannuna ne na rufe kofar har na
sanya mata salanta nayi kamar in gyara ruhuwata
da na fahimci zamewanta ne yayi dalilin
farkawar tawa saboda tsananin sanyin da a ke yi
har na juya da nufin komawa baccina sai kuma
na tuna ai ban ga Innata a wurin kwanciyarta ba
da sauri naji baccin ya sake ni nayi mika na bude
idanuwa sosai a kasa na ganta a durkushe da
gwiwoyinta a kasa ta dafa wata kujera ‘yar
tsugune wacce dama ta zamanta ne a kicin
nantake na karan wartsakewa ina kara bude ido
don in ganta da kyau har nayi nufin saukowa in
da take sai ga Babana ya shigo dakin cikin sauri
rike da kwanon sha karami a hannunshi alamar
rubutu yaje ya yiwo mata daga wannan rubutun
dai Ramatu in bai yi ba sai kawai mu tafi asibiti
kin ga nakudar tayi tsawo kar muzo muyi irin na
wancan karon shima asibitin yana da amfaninshi
ai duk rama ce ta Ubangiji ta kawomasu bata dai
tanka ba.
Ya isa gare ta ya durkusa a gabanta shi ma
kan gwiwoyinshi karbi ki sha rubutun nan
Ramatu, bata motsa ba daga yanayin ta na
16
sunkuyar da kan da tayi tana kallon ‘yan
yatsunta.
A hankali cikin matsananciyar taushi da
laushin murya ta ce mishi ka yafe min abubuwan
da nayi maka Mallama.
Ya kara zuba mata ido watakila ba wannan
ne karo na farko da tayi mishi irin wannan rokon
ba saboda jin da nayi ya ce mata, To ni wai me
kika yi min ne Ramatu da ki ke ta nanata min
wannan maganar? Ai ni ban san komai ba game
da ke in ban da alherinki shekaru ashirin din
aurena da ke sune shekaruna na jin dadi da
samun farin cikin rayuwa in ban da ke da wata
kila ban taba sanin jin dadi ba, na zauna da ke
kina yi mini biyayya kina tattalin farin cikina,
kina kyautata min, ban taba yi miki umarni kin
ki bi ba, ban taba cewa ga yanda za ki yi kin ce
a’a ba.
A kullum ckin kiyaye bacin raina ki ke, to me
zan ce miki? In har akwai abin da ki ke yi min da
ki ke kuntatawa rayuwata ai bai wuce irin
wadannan kalmomin naki ba, tunda kin san me
suke nufi a gare ni, kina yi min nuni ne da zan
iya komawa in da na baro har gara ma wancan
lokacin ban taba danddanar wani madandani da
ya kwadaitar da ni son rayuwar duniya ba kamar
yanzu, to suma na yafe miki tunda nasan kina
17
cikin wani hali ne yasa ki ke yi mini hakan.
Ubangiji ya raba ki da wannan ciki lafiya.
Ni da nake kwance shiru a kan gado nake ta
faman kukan sharbe na kasa saukowa daga kan
gadon saboda tsoron kar a ce min in fita waje ba
wai don tsoron daren ba sai don tsoron kar a
hana ni ganin halin da Innata ke ciki saboda
nasan a duk lokacin da Babana ya shigo dakin
Innata ba a barina in shiga in ma ina ciki zan yi
sauri in tashi in fita tunda nasan ko ban yi hakan
ba ita Innan zata sani ni ce cikin zuciyata na
amsa addu’ ar tashi na ce amin.
Mallam yayi maza ya ce na’ am Ramatu me ki
ke son 6aya min? me ki ke so in yi miki? A
hankali ta ce mishi Mama ce. Gabana ya yanke
ya fadi jin ta ambaci sunana. Cikin natsuwa ya
ce mata “Eh, me Maman nawa tayi?
Ta sake rage murya kafin ta ce mishi, ka
baiwa Innata rikonta zata rike maka ita kamar
ina raye.
Cikin nutsuwa ya ce mata, In har ina raye to
a’a duk inda zan shiga zan shiga ne tare da ita,
zata rage min kewarki yayi maza ya share wasu
zafafan hawaye da suka zubo daga idonshi. Ita
din ai kama da ke take yi, kina raye ma nakan
kalle ta in yi mamakin kamanninta da ke balle
kuma in kin tafi kin bar ni.
18
Wasu hawayen suka ci gaba da zubowa daga
idanunshi har suna jika rigarshi, ban taba yi miki
karya ba, ba zan yi miki a wannan lokacin ba,
zan dai yi miki alkawari a duk lokacin da na
hango wata alama ta katsewar rayuwata, to cikin
taimakon Ubangiji zan mika mata ita.
Yana gama fadin hakan yayi maza yà miko
wata Jaka ya dauko wacce yasan nan Inna take
tara kayan haihuwarta yana cikin haka sai ga
Babah Sumaye da Baba Hodijo sun shigo alamar
kofar gidanmu ma a bude take sun kuma san da
abinda Inna ke ciki.
Mallam Bukar ga motar nan fa a waje mun
samota, da sauri Babana ya ce, To mu tafi.”
Yasa hannu ya daga Inna ya tsaida ita, Babah
Sumaye ta daura mata zani tana fadin “Iko sai
mai shi.” Gaba daya cikin ya tattara ya dawo
kirjinta.
Tuni na sauko daga kan gadon ina ta faman
kuka ina rike da hannun Innata wacce itama ta
kama nawa hannun ta kankame a cikin nata.
“Sake ta mu tafi, muje ki shiga gida ki samu
Jumare ku kwanta tare tazo tana nan a ciki, ki
kuma daina wannan kukan da ki ke yi, kiyi mata
addu’a kawai in Ubangiji ya kawo saukin
lamarin da sassafe sai ki ga mun dawo tare da
19
sabon yaronmu ko yarinya. Ki samu wata ‘yar
uwar.
Wadannan duka kalaman Mama Sumaye ne
don haka na dan samu natsuwa har na wuce na
shiga cikin gidan nasu naje na samu Jumare
muka kwanta mu kuma namu gidan aka sa
kwado a ka kulle shi.
Jumare ‘yar kanwar Babah Sumaye ce da ke
yawan zuwa wurinta, ta girme ni da shekarun da
suka kai hudu, don haka ta fini wayo tana ganina
ta ce min ke share hawayenki kizo muyi
kwanciyarmu haka ake yi in za a haihu gobe za
ki ga sun dawo da sabon yaro ko mace ko namiji,
wanne ki ka fi so?
Na dan yi shiru wai zan yi zabi, nan da nan
kuma naji bani da wani zabi bana ma dokin
abinda za a haifan tunda naga wahalar da take
ciki, bukatata kawai in ganta ne ta dawo gida
lafiya.
Duk da kalaman da aka yi min na Inna
haihuwa zata yi ba daga kwanciyata nayi bacci
ba saboda na riga na tsorata da abinda na gani,
daga baya ne kawai da yake shi bacci 6arawo ne
ya sadado yazo ya dauke ni.
Farkawa nayi daga baccin nawa a dalilin nayi
ya ishe ni ga kuma hasken rana da ya cika dakin
da sauri na diro daga kan gadon na fito dakin da
20
gudu, gidanmu nake nufin zuwa inga o zanga
Inna da sabon yaron da aka ce kan safiya zata
haife shi Jumare na gani a zauren gidan ta rabe
tana leke.
Nima na tayata yin leken don in ga abin da
take gani, cincirindon jama’a ne gaba dayansu
kuma maza babu mace ko daya gashi kuma
yawan nasu yakai inda ya kai.
Can gefe ga yara ‘yan saffa suma maza mafi
yawancinsu kuka suke yi. Da sauri na kalli
Jumare meye a ke yi? Ta kara lekawa tana
kokarin tantancewa kamar fa rasuwa a ka yi
amma ban sani ba.
Muna cikin haka sai ga makara an fito da itaa
daga cikin gidanmu da mutum shimfide a ciki,
ina kallo a ka yi sahuana sallar amma wai ban
gane Innata ce a ciki ba, ina ji Jumare tana gaya
min wanda ya rasunne a ciki, na kuma ga zanin
Innata lullube kan likafanin amma kwata-kwata
ban kawowa kaina cewar ni ce na rasa Innata ba
saboda ban taba zaton zan rasata a wannan
lokacin ba, ban taba zaton zata daukan min
mahaifiyata ta raba ni da ita kamar yanda tayi wa
daruruwan yaran da ba za su kidayu ba.
“Waye ne ya rasu Jumare? nayi tambayar
cikin tsananin tsoro da firgita ba wai don ina
zaton abin ya kasance ne a kan Innata ba, sai dai
21
kawai don naga abin da ban taba gani ba, wanda
kuma yayi matukar tsorata ni.
Na sake yi mata tambayar mai yawa na sake
yi mata tambayar da sauri ta ce min, “Ke ban
sani ba. Saboda itama ta shiga wani yanayi na
kuma yarda har a yau dinnan na yarda Jumare
bata san Innata ake sallata ba.
Ban san yanda aka yi ba ina ganin an dauki
makarar nan an tafi da ita din, bin Jama’a sun bi
bayanta cincirindon yara suka yi ta dalewa kan
manyan motoči za su bi don yi mata rakiya na
kama kuka sosai da sosai Jumare tana bani
hakuri.
Daga baya ne kawai na soma jin matan da ke
wucewa ta bayangidan za su shiga gidanmu,
suna fadin “Ikon sai Ubangiji! Ashe Ramatu ce
ta rasu?
Ban san yadda a ka yi ba, ganina kawai nayi a
cikin gidanmu Yaya Dijah tana kankame dani a
jikinta tana ta faman kuka, bai yiwuwa in tsaya
kwatance ko bada labarin abinda ya faru. illa
iyaka dai kawai an yi zaman makokin Ina na
kwana uku cikin matsananciyar kewa da jimam
da addu’o’i ba daga wurin mu ya’yanta ko
mijinta ko danginta ba kawai. Har daga wurin
Jama’a masu yawa da suka santa ko suka Ji
22
labarinta wurin kira da mutanen da suka san
rayuwarta.
An watse daga zaman makokin Inna, ‘yan
uwa da abokan arziki duk suka watse aka bar mu
daga mu sai mu a gidanmu, ina nufin daga
Babana sai ni sai ko Yaya Dijah da take nan bata
koma dakinta ba.
Muna zaune gaban Babanmu ni da Yaya
Dijah da take tashe da tsohon cikinta in ban da
kuka babu abinda take yi, ni kam nayi kukan na
gaji na bari watakila don ban gama fahimta ba
ko gama gane girman abinda ya same ni shi yasa
na hakyra da kuka na koma zare ido.
To yaya za ayi ai sai hakuri kawai, ita kam ai
ta huta wajen haihuwa.ta rasu banda haka kowa
alherinta yake fada, dubi kuma irin mutanen da
ta samu, kiyi hakuri kawai ki bar kukan muyi ta
addu’a Ubangiji ya gafarta mata, muka ce
Amin.
Duk da hakurin da Babana ke ta bayarwa na
muyi hakuri sau biyu ina ganinshi ya buya a
dakinshi yana nashi kukan.
Rannan da safe Yaya Ibahim yazo gaishe mu
dama kuma tunda a ka watse zaman makokin bai
taba fashin zuwa gaisuwar ba, suna gama
gaisawa da Babana yayi tasa mishi albarka. Da
zai tafi kuwa sai ya ce mishi in ka taso daga
23
kasuwar ka biyo ta nan ka tafi da matarka taie
gida ta huta a dakinta, sai kayi ta hakuri da ita.
Ya ce, To Baba yayi mishi godiya ya tashi ya
tafi, rannan da yamma Yaya Dijah ta koma
dakinta ba a wani dade ba kuwa ta haihu, ya
mace ta haifa, Yaya Ibrahim ya sanya mata
sunan Innarmu daga mu har Babanmu muka yi
murnar alherin da yayi mana.
Babah Sumaye ce taje ta zauna mata tayi
mata biki har tayi arba’in saboda Yaya Ibrahim
da iyayenshi sun ki yarda da dawowanta gida
suka ce tunda babu, Inna to me za ta dawo gida
kuma tayi?
Sannu a hankali sai mutuwar Inna ta rinka
shigarmu tana ratsa tsoka da kashi da bargo da
zukatanmu, gaba daya ta makurkusa mu ta canza
mu daga yanayin da duk muke tun ma dai ba
Babana ba.
A farkon al’amarin ni kam ma gani na rinka
yi tamfar karya ne tana can asibitin. ne kawai
watarana zata dawo wani lokaci kuma in rinka
jin tanfar wani mummunan mafarki ne da zan
farka in ga al’amarin ya sauya in da duk abin ba
haka ba ne amma ina?
Sannu a hankali sai kwanakin suka fara tafiya
daga daya har a ka je uku a ka yi bakwai har aka
kwana arba’in ban ga Inna ta dawo ba, babu ita
24
babu dalilintà sai dai yan uwanta da abokan
arzikinta su dan zagayo su duba mu a duk sanda
za su tafi kuma hakuri ne dai suke ba mu tare da
fadin Ubangiji ya jikan Ramatu da rahamarsa, ya
kuma sa alherinta ya bita, amma ita kam shiru
kake ji.
Wannan shi ne abinda yafi komai ba ni tsoro,
a wannan lokacin sai na zama babu abinda nafi
so irin in zauna in yi ta kuka saboda na riga na
fidda ran sake ganinta tunda ban taba ganin
randa tayi tafiyar da ta wuni ta kwana ba tare da
ta tasa ni a gaba ta tafi dani ba.
In ban da kewarta da kadaicin babu abin da
yafi komai damuna, ko ina yayi min fadi gani
nake tanfar ni.kadai ce a raye babu wani abinda
nake ji in ji na gani su balle in ji dadinshi in
tsaya bayani, na kewar da Inna ta bar mu a ciki
ma to na 6ata bakina ne na kuma san duk yanda
nakai da jin wani abu’ kan rasata da aka yi to
Babana yafi ni, illa iyaka dai kawai shi baya
cewa komai.
In bani nayi mishi maganarta ba, ba ya yi
mini. In na cika kawo mishi zancenta ma sai ya
ce min yawaita yi mata addu’a zai fi yawaita
hirarta amfani in ce mishi to.
Tunda Inna ta rasu ba mu taba dora tukunya a
gidanmu da sunan yin girki ba, Babah Sumaye
25
ke sanya mana abinci rana da dare kamar yanda
ta rinka yi sanda Innarmu ke rashin lafiya.
Abin karyawa kuwa sayo mana nake yi wata
rana koko da kosai, wata rana waina da miya
wata rana shayi da burodi.
Kullum dai ni Babana yake tambaya me nake
so? In gaya mishi ya ce in je in da kudin suke in
dauko inje in saya, in na tati kan in dawo sai in
samu yayi sharar tsakar gida da kicin har da
wankin bayan gida muna gama karyawar sai in
tattara kwanukan da muka yi amfani da su in
wanke su in kife in uye ruwan wanka in je in yi.
Innata ma mata ce mai matukar tsabta, don
haka har bayan bata nan din ma ba ma iya barin
gidanmu da datti, kullum ka shigo tšab zaka
ganshi, kamshin turarenta ne dai a yanzu babu
shi a gidan.
Gidanmu gida ne na Jama, 8, kafin rasuwar
Inna amma a yanzu da bata nan wuni muke yi a
ciki babu wanda ya leko mu har yaran ma sun
daina zuwa dan gara gara ma Mansur jifa-jifa ya
kan shigo ya gaida Babana, ni kuma ya kawo
min dan wani abin lasawa.
Don haka nima ban cika zaman cikin gidan
ba in Jumare tana nan in shiga gidan Babah
Sumaye in bata nan in je wajen Babana in taya
shi sai da kayanshi sai ya taso in debo mishi
26
kwanduna mu dawo gida in shiga wurin Babah
Sumaye in karbo mana abincinmu mu zauna
muci tare a kwano daya ni da shi.
A duk ranar Juma’a kuma yakan sani in
shirya in je in gaida dangin Innata mafi yawanci
nafi zuwa gidan Yakunbo Halima wacce ita ce
yar Inna da take bi in naje wurinta wannan
Juma’ar sai wata Juma’ar, kuma in je wajen
Yaya Dijah.
Babana yana mutunta Yakunbo saboda sona
da take yi, sai dai duk da haka bai yarda ya bata
rikona ba duk da har turowa tayi a rokar mata
shi ya bata ni.
Sai ya ce a bata hakuri gani nan dai a tsakani
ai duk na ishe su. Tunda Yaya Dijah tayi arba’in
kusan duk sati sai tazo gidanmu sau biyu in zata
zo kuma takan zo mana da lafiyayyar miya
wacce take yi mana da naman kaji ko kayan
cikin saniya wata ran har ta kirbo mana sakwara
wai mijinta ne yake yin cefanen ya ce tayi ta
kawo mana mu rinka ajiyewa ko biredi ma rinka
ci da ita shima zuwanshi biyu wurin Babana kan
maganar ya basu ni.
Ya kalle shi yayi murmushi ya ce to in baku
ita Ibrahim kai da matarka ga kuma ‘yarku sai in
kara muku da ita ni fa? In zauna ni kadai? Ai ba
zan iya ba.
27
Surukuta mai dadi Babana yake yi da Ibrahim
da kawai ya maida shi saboda yayi sa’a shima
Ibrahim din mutumin kirki ne ga sanin darajar
surukuta.
Don haka Baba yana sonshi yana kuma son
diyarshi da ya yi wa Innarmu takwara da ita ba
kadan ba har ma sai yayi mata lakani yake
kiranta da suna.
Rannan ina jin Babana yana cewa Ibrahim
din ka gayawa Dijah ta daina zirga-zirga da
yarinyar nan a kan hanya tana diban mata sanyi,
ya dan yi murmushi cikin girmamawa ya ce, Ai
ba komai Baba, Babana ya ce a’a ta zauna aa
dakinta kawai zuwan nata ba wani dadi ne da shi
ba tunda maimakon tazo ayi wata magana da ita
sai tazo ta wuni tana kuka gara ta hakura kawai
ta zauna a dakinta ya ce to Baba, ya tashi ya tafi
tun daga nan sai ya zama kannenshi ne suka
kawo mana duk wani abin da za su aiko mana da
shi ita kuwa ta koma zuwa jifa-jifa.
Inna ta rasu ne cikin watan Jimadah Thani,
sannu a hankali sai gamu mun iso cikin watan
Sha’aban har shima ya kusa zuwa karshe mutane
sai shirye-shirye da dokin isowar Ramadan suke
yi mukam a gidanmu ba a shirin komai.
Da Inna tana nan da mu ma muna nan muna
ta shirye-shirye abinda zuciyata take ta gaya min
28
kenan sai dai ban gayawa Babana ba saboda
yawan ce min da yake yi mata addu’a yafi yawan
hirarta amfani.
Ana gobe za a fara Azumi Babana ya bani
sugar mudu bibbiyu da madarar (Peak) dozin
dai-dai ya sani na bi yayun Inna mata da ke
gidan aurensu na kaiwa kowacce nata na gidan
Babanta kuwa shi da kanshi yaje ya kai musu
haka nan gidan Baba Hodijo.
Yaya Dijah kuma mu ma ta aiko mana da
abubuwa masu yawa kala-kala kuma masu dadi
na kamun Azumi.
Washegari kuwa mai alfarma Sarkin Musulmni
ya bada sanarwar ganin watan Ramadana mai
albarka don daukacin Musulmi maza da mata
suka yi niyyar daukan Azumi.
Sanda Inna ke raye na kan yi Azumin amma
ba mai yawa ba, ban san dalili ba a wannan
lokacin sai Babana ya ki yarda sai da nayi tayi
mishi kuka ya bar ni na dauka har watan ya kai
ashirin kuwa ban yi abin da yafi guda bakwai ba.
Shiga goman karshe da aka yi ne ya nuna
gabatowar sallah karama daga ko’ina sai aiken
kayan sallah ake yi min dangin Inna maza da
mata zai wuya a ce ga wanda bai yi min ba, sai
dai kawai na wani yafi na wani haka kawayen
Inna da Iyayen ‘ya’yan da ta saba yi wa kitson
29
sallah da lalle kyauta, Babah Sumaye ma Yaya
Dijah da mijinta kam ba a maganarsu ga kuma
Yakunbo.
Babana ya tara kayan a gabanshi yana
dubawa, idanuwanshi suka cicciko da hawaye ya
ce, Wannan duk arzikin Ramatu ne Ubangiji ya
gafarta mata na ce mishi amin Baba.
Mun wayi gari a gidanmu ranar sallah kamar
yanda ta kasance a gidajen sauran Musulmi baki
daya, sai dai mu kam maimakon walwala da
farin ciki irin na sallah samun kanmu muka yi
cikin matsananciyar kewa.
Mutuwar Inna ta zamo mana sabuwa saboda
ganin babu kowa cikin kicin din gidanmu, da
yanzu tana nan tana fama da cincirindon yaran
dake karbar abincin sallah a kofar kicin dinta
wanda yawanci burabuskon gero take yi da
miyar yakuwa saboda shi ne mafi soyuwar abinci
a wurin Babana, sai kuma tayi masar shinkafa da
miya don rabo na sosai da sosai wanda ni zata yi
ta aika ina mikawa sai wadanda suka san da
burabuskon nata ne zaka ji suna aiko ni ki
gayawa Ramatu ta fa sanmun burabuskon nan
ina so, in ce musu to.
Yau kicin dinmu shiru babu kowa a cikinshi,
na shiga cikinshi har na gaji ina ganin kamar zan
30
ganta a mazauninta ban ganta ba, babu ita babu
dalilinta.
Ga fa kwanukan abinci nan an tara mana zo
ki zabar mana wanda zamu ci ki fitar da saura ki
samu masu ci ki basu don kar ya lalace nayi
maza na ce to Baba.
Nazo na dudduba na dauko kwanon
Yakunbo, tuwon shinkafa ne miyar kuka da man
shanu da yaji, ga kuma naman da nayi zaton na
Talo-Talo ne a ciki na ce mu ci wannan Baba ga
kuma masa da miya.
Mansur ya kawo na Yaya Dijah, kwan doya
ne da cincin mai nama da gasasshiyar kaza, sai
miya a wani kwano su na adana mana sauran
zan fitar in baiwa yaran da suke so ya ce, To.
Duk da lodin kayan sallar da ke gare ni ban
wani yi kwalliya ba,bayan wankan da nayi sai da
Babana ya ce min to gyara jikinki mana
Yahcuwuna kiyi kwalliya kamar sauran yara,
sannan naje nayi.
Nayi kyau ba kadan ba, ga kitsona da Babah
Sumaye tasa a ka yi min sun sauka har kafadata
na shiga gidan taga kwalliyata ta kuma aike ni
gidan su Jumare na kai musu abincin da tayi har
da gidan Yakunbo saboda mu’amallah sosai suke
yi a tsakaninsu.
31
Kwalliyar sallah sosai na rinka yi muka kuma
yi yawon sallah ni da Jumare wacce take ganin
ita din budurwa ce tunda ‘yanmata a wancan
lokacin sha hudu ne sha biyar in an yi tsanani
sha shida wacce ta makara sosai sha bakwai.
Har gidan zoo Jumare ta kai mu muka kuma
samu goron sallah, osai wurin dangi da kuma
masu son Jumare.
Tun sanda Innata ta rasu ban sake zuwa
Makarantar boko ba, ko kuma ta Alkur’ani, ina
zaune ne kawai a gida bana komai tanfar dai a ce
da gani har Babana nawa mancewa muka yi da
ana zuwa Makarantar sallah da sati guda.
Ina tare da Babana, labarin yawon sallarmu
da Jumare nake ba shi yana jinjina kai cikin
yanayi na nuna alamar murna da gamsuwa don
dai ya kara min jin dadi da na gama sai ya kalle
ni ya ce min, gobe kuma ina za ku ke nan?
Nayi dariya na ce babu, ai hidimar sallah ta
Kare tunda yau sallah na da kwana bakwai.
Ya sake kallona ai kuwa dai haka ne hidimar
sallah ta kare kenan, na ce eh Baba. Ya ce, To ai
ina ganin sai kiyi shiri ki soma zuwa
Makarantarki, kin ga kin dade ba ki je ba, in ma
kin ga ba za ki ta bokon ba shi ke nan amma ta
allo kam da ta Asuba sai ki rinka zuwa na sake
ce mishi to Baba.
32
Jimawa can ya sake kallona cikin natsuwa ni
a ta bokon aji nawa ki ke ne? a wancan lokacin
da ba a cika sanya yara a Makaranta kafin
cikarsu shekaru bakwai ba, saboda bin ka’idar
hannun dama ya taba kunnen hagu kafin a dauki
yaro a Makaranta sai na ce mishi aji uku.
Yayi maza’ya ce, A’a to ashe ma kin fara nisa
ina ganin har ita sai ki koma don ki samu ki
gama aji shidan ki koyi karatu da rubutu da dan
turancin kai yara asibiti.
Ban amsa ba saboda jin nauyi a dalilin gane
in da maganar tashi ta dosa, iyaka dai nayi shiru
don komawa kan karatuna da na bari nima yafi
min don zai rage min zaman kadaicin da nake
ciki.
Kwana biyu bayan nan na soma zuwa
Makarantar boko wanda sai da naje ta allo kafin
nayi hakan gab ake da fara jarrabawar canjin aji,
a lokacin da na koman sai, dai da yake dama can
ina cikin yaran ajin masų fahimta gashi kuma ina
da kawata da muke benci daya Hasiya Jibrin, sai
na samu hayewa zuwa aji hudu.
Rannan na dawo daga Makaranta na shiga
wajen Babah Sumaye karbar abincina na zauna a
nan wurinta ina ci muna hira tana bani labarin
al’amuran da take ganin ya kamata in sani, na
gama na mike na kai kwanon gun wanke-wanke
33
na hada da kwanukan da na samu a wurin na
wanke su tas, na kife na wuce bandaki nayi
wanka na fito na wanke uniform dna na shanya.
Na shiga dakinta na shafa mai na dauki
kayana da ke wurinta na fito ina rungume da
allona, na ce mata za ni Makaranta Babah, ta ce
a’a sai kin karbo min cefane, ajiye allon anan
kiyi gudu ki karbo min cefane ki kawo min sai ki
tafi, na ce mata to. Nayi yanda ta ce din kafin na
tafi makarantar.
Mu’amallah ta uwa da ‘yartga Babah Sumaye
take yi dani, yanda take tafiyar da ni sanda
Innata take raye haka a!’amarin yake, har yanzu
sai dai ma kari.
Don yanzu tana sa ido sosai a kaina hada
kayanki kiyi wanki, in ce to. Dauki kibiya ki
tsefe kanki, tunda ba wani son kits ake yi ba
in ce mata ban iya ba ta ce in gama abinda nake
yi in kawo kibiyata tayi min tsifan kowane
lokaci a cikin yi min fada take, sai dai in bata ga
nayi laifi ba ko da kuwa a gaban waye.
Ina ganin har dan hakanne yasa Yakunbo bata
dadewa bata zo wurinta ba, in tazo kuwa ta rinka
yi mata godiya ke nan, ita kuwa Yay. Dijah
kusan kullum in zata zo zata riko mata wani
abun hasafi ko dai sabulun wanka dana wanki ko
kayan tea.
34
A wannan lokacin a gida na daina barin
Babana yana sharar tsakar gida da kicin, ina idar
da sallah nake fita in yi komai in gama abin da
ke bukatar wanki in wanke na gyarawa in gyara
tunda ba wani kwanannen datti ba ne a gidan.
Sai kaga nan da nan nayi na gama na shiga
wankana, yawan abubuwan da Yaya Dijah kke
kawo mana kwana da yawan maganar da take yi
min kan fita kullum aje sayen abin karyawa
kowa yana gani yasa na rage sai in ce Baba muci
abu kazan da muke da shi kawai ya ce min to.
Kullum na gama shiri zan tafi Makaranta sai
Babana ya ce min matso nan in gyara miki hodar
nan taki, in ce to. In matsa yasa gefen rigarshi ya
goge min fuskata kafin ya umarce ni dasa hannu
in dauki Naira daya a cikin kudin da suke dakin,
lokacin nan kuwa Naiara daya ba karamin kudi
ba ne a wurin yara, don kuwa tana iya sayen
waina ta sayi biskit har ta hada da kwalbar lemo
wani lokaci ma har da alawa don haka kudi sosai
nake zuwa da su Makaranta.
Ina tare da Babana a gida duk da Innata ta
rasu yana matukar kula da ni, wai abin da yake
yi min din ma sanda Inna take nan bana samu,
don kuwa ita mai kwaba ce mai kulawa kuma da
tarbiya, iyaka dai kawai zama kusa da Inna da
35
yunwa yafi zama a inda bata nan cikin daula da
da na sha.
, Babana ya dawo daga Masallaci sallar asuba
ya zauna ya gama laziminshi da addu’ar da zai yi
ya gama ya shafa nima na shafa tunda a kusa da
Sinl nake zaune na soma gaishe shi kasancewar
ranar ta Lahadi ce ya sani gyara zama kusa dashi
tunda ba Makarantar boko zani ba.
Zan gama abin da zan yi ne in tafi makarantar
allo wannan kuwa sai wajen tara. Daga ido nayi
na kalli Babana cikin natsuwa na ce mishi Baba,
ya ce Na’ am Mamana, na tambaye shi yanzu duk
addu’o’in da muke yiwa Inna suna zuwa inda
take?
Yayi maza ya gyada kai tare da fadin da
yardar Ubangiji kuwa, kin san ai akwai wasa
ayyuka na sadakatul jariya masu gudana da dan
Adam kan bari a duniya ladar ta rinka kaiwa a
gare shi a bayan rayuwarshi daga cikin irin
wadannan ayyuka da ladansu bata yankewa
akwai ‘ya’ya na gari.
Ba kina sallolinki a kan kari ba? Nayi maza
na ce mishi eh babu, ba kya kuma sabon
Ubangiji da gangan, na girgiza kai nuna lamar
a’a, ya ce To in sha Allahu in kin yi addu’a ladan
zai kai gareta ga kuma Yayarki da take zaune a
dakin aurenta, tunda a ka yi aurenta ba’a taba jin
36
wani abu na rashin jin dadin game da ita ba, kin
gani? Cikin yardar Ubangiji addu’o’inku za su1
rinka kawai gare ta.
Na sake kallon shi a hankali na ce mishi
menene sabo Baba? Ya zuba min ido kafin ya
gano ta inda zai Bullowa lamarin, irin su karya,
gulma da shiga harkar da ba taka ba, da
bijirewa iyaye ko zina da makamantansu kin
gane?
Nayi maza na ce na gane, kusan kullum sai na
lissafawa kaina laifuffukan da Babana ya lissafa
min a matsayin zunubi ko sabo, don kar in aikata
su saboda kar in aikata su su zama sanadin da
addu’o’ina za su daina kaiwa ga Innata.
Kusan kullum na zauna tare da Babana muna
hira zai yi min nasiha da cewar in kasance mai
gaskiyaa kan al’amurana in kuma tsare
mutuncina kar in yarda wani yayi min wayo duk
abin da na gani naji ina so in gaya mishi ban da
karbar abin hannun wani ita mace bata da wata
daraja komai kyanta in har bata zama mai kamun
kal da tsare mutuncin rayüwarta ba, in ce mishi
to din ba tare da na san mé maganar tashi take
nufi ba har na gane komai.
Rannan na idar da sallar Asuba ina ta doki da
zumudin Babana ya shigo in ba shi labarin da ke
37
Cina a raina, yana shigowa na soma gaishe shi ba
tare da na jira ya kai mazauninshi.
Cikin natsuwa na kalle shi na ce mishi Baba
zan yi sadaka yau, ya kalle ni cikin natsuwa ya
ce sadakan me kike son yi uwata? Na ce ko na
meye ma Baba jiya da daddare nayi mafarkin
Inna wai tazo gidannan na ganta lullube da
fararen kaya tana kallona tana ta faman
murmushi ni kuma sai tambayarta nake yi Inna
dama ashe za ki iya zuwa wurinmu shi ne tunda
kika tafi baki taba zuwa kin duba mu ba, ni da
Babana?
Ina maganar tana kallona murimushinta kawai
take yi ni kuma ina kurarin matsawa kusa da ita
don in taba ta ina cewa Inna kiyi mini magana
mana har zan taba tan sai kawai naga ta 6ace sai
kuma kawai naga ra farka daga baccina.
Cikin natsuwa ya zuba min ido a allona
lokaci mai tsawo bai kawar da idamuwanshi daga
gare ni ba har na fara jin tsoro ko yayi fushi ne
saboda maganarta da nayi mishi tunda ya sha ce
min in an tunata ayi mata addu’a kawai basai an
yi zancenta wani ba har zan buda baki in bashi
hakuri tare da alkawarin ba zan sake yi mishi
hirarta ba sai naji ya ce min jiyan da kika yi
mafarkinta ai jiyan ta shekara.
38
Nayi maza na daga ido na kalle shi a firgice
saboda razanar da nayi sai ya ce min kin gani in
ha ki manta ba ta rasu ne ranar sha tara ga waran
Jimada Thani, to yau ma ai shataran ne ko
ashirin ga watan.
Na ce Haka ne Baba, lokaci mai tsawo ya
dauka yana yi mata addu’a tare da sauran
Jama’ar Musulmi da suka rigaye mu baki daya
in kuma tamu cikawar tazo to Ubangiji ya
azurtamu cikawa da kyau da Imani.
Nayi maza na ce amin Baba tsawon lokaci
muna zaune shiru babu wanda ya sake furta wata
magana sai na bude baki da nufin fadin abinda
ke kai kawo cikin raina a hankali na soma yin
maganar cikin yanayin girmamawa da tsoro don
kar ya hana ni abin da nake nufin fadin tunda
yasha gaya min cewar maimakon yawan
ambaton Inna da yawan maganarta mu rinka
yawan yi mata addu’a kawai.
Zuba min idon da yayi yana kallona shi ne ya
kara tabbatar min da cewar ni yake sauraro, don
haka cikin natsuwa da ladabi sai na buda baki
nace mishi Baba tafiyar ta Inna ta fara nisa duk
da a lissafi ne kawai Inna ke da shekara guda a
yanzu in a kewa da kadaicinta ne mun kai wani
matsayi da ba zai yiwu mu kwatanta ba.
39
Duk da haka shekara gudan lisafin ma lokaci
ne mai tsawo da yawa in ban da tafiyar tata bata
dawowa ba ce da yanzu ta dawo ko kuma damun
soma sa rai da dawowan nata.
Cikin natsuwa ya ce min eh, Maryam ai tafiya
taia wata irin tafiya ce da dadewa bai sawa a
dawo da dadewa kansa a dawo ai da mu ma
iyayenmu sun dade da dawowa.
Nayi maza na ce haka ne Baba, kamar in yi
mishi wata maganar sai kuma naga to bari kawai
in ja bakina in yi shiru.
Kamar in sake yin wata maganar sa kawai
naga bari kawai in ja bakına in yi shiru.
A wannan lokacinne na shiga aji shida na
Makarantar Primary na fara girmia har Babana ya
fara barina ina tafiya gidan Yayc Dijah ni kadai
don yi mata wuni. Ina matukar son awa gidanta
saboda yanda na lura na gane bata da wani
wanda take so da kyautatawa irina.
Kullum naje gidanta to bata gajiya da tattalina
da tarairayata komai na ce mai kyau ne cewa
take yi in dauka tana ganin na kwana biyu ban je
ba zata shiga aiko kanen mijinta suzo su ga
lafiyata, in kuwa naje bayan aiken nata zan
gamu da fushinta kan dadewan da nayi ban je ba
kullum a cikin yi min nasiha take tana ganin zani
aikata kuskure zata yi maza ta gyara min.
40
Yanda Yaya Dijah ke sona da ji da ni haka
shima mijinta yana ganina zai fara murmushi ina
Inna take? Zo maza ga Mamanki tazo.
Sanin da yayi kullum naje gidan Yaya Dijah
zata tasa ni a gaba da aikace-aikace har da su
hidimar girki wai kar in girma ban iya aikin
mace a gidanta ba, yasa yana ganina zai je yayi
sabon cefane ya kawo ko da kuwa ba a ranar
suke bukatar cefanen ba sai ya ce in na girka in
tafi mana dashi gida muyi amfani da shi ni da
Baba.
Ina son Yaya Dijah da mijinta ina kuma
matukar son ‘ya’yanta Inna da Abbati, ina son su
irin son da ba zai kwatantu ba, saboda gani nake
tamfar su din su kadai sune dangin da nake da su
sai kuma nake kallonta kallo irin na uwa, ganinta
nake tamfar ita ce madadin Innata da na rasa.
Dangin mijinta kuma ‘yan uwa saboda suna
sonta kowane lokaci kaje’gian sunanan aurenta
aure ne na soyayya, fahimta da kuma kyautatawwa
juna, don haka gidanta gida ne na farin ciki da
kwanciyar hankali, kudi masu yawa ne kawai ba
su da su amma suna cikin rufin asiri.
Ni da Yaya Dijah kamannin da ke tsakaninmu
ba wasu masu yawa ba ne, ba su wuce wadanda
zaman ciki na kasancewa shakikai ke haddasawa
41
ba, yayin da nake matukar kama da Innarmu ita
kuma kama da Babanmu take yi.
Haka nan ko a halayenmu mun bambanta
mace ce mai matukar hakuri bata kuma da
kwaramniya.
A wannan lokacin saboda na riga na fara yin
wayo na fara fahimtar me nake ciki sai na zama
babu abin da nake so nake fata da buri irin in
ganni nayi haddar Alkur’ani mai girma a dalilin
kullum sai Malaminmu na Alkur’ani yayi mana
bayani kan falala, girma da kuma darajar
mahaddata Alkur’ani a ranar alkiyama su da
yayensu.
Sai na zamo ina matukar kwadayin nima
iyayena musamman ma Innata da nake rayuwa
cikin tsananin kewarta da begenta su samu irin
wannan matsayin a gobe kiyama.
Kowane lokaci a cikin taka tsan-tsan nake na
kauce wa aikata laifi musamman yin karya da
duk wani abin da Mallaminmu ya ambata cewwar
laifi ne don in samu in zama ya ta kwarai
saboda ya ce mana ya’ya na kwarai suna daga
cikin sadakatul jariya da mutum ke bari a duniya
wanda ladansu ba su yankewa a gare shi.
Rannan ina tare da Babana a cikin gidanmu
da daddare a kishingide yake a kan tabarma
yayin da yake jan carbinshi a hankali cikin
42
natsuwa idanuwanshi a kaina suke tare da
natsuwar shi saboda sauraron haddar da nake
kawowa na suratul ‘ANKABUT”.
Sai da na kai karshe na sake kallonshi cikin
natsuwa kan in gaya mishi abinda nake nufin
gaya mishin sai ya ce min kina da murya ta
karatun Alkur’ani Maryamu, kar ki yarda ki
daina, kar ki yarda kiyi wasa ta basirarki na ce
mishi to Baba, kan in yi wata magana sai ya sake
bani umarmi na in maimaita surar, ya ji ta dá
kyau.
Sau biyu na maimaita sannan yayi murmushi
ya ce a’a lalle hadda ta zauna sai kiyi ta tilawa
kar ki yarda kina yin sake don shi Alkur’ani
kana barinshi sai shima yayi nesa da kai, don
haka ki dage da tilawarshi. nayi maza na ce to
Baba. Yi mana addu’a, na sake cewa to nayi
muka shafa sannan muka je muka kwanta.
Rannan da safe muna aikace-aikacenmu a
gida ni da Babana kafin ya fita kasuwarshi nima
in tafi Islamiyyata tunda ranar ta Asabar sai naji
ya ce min ni Mero ba ki iya komai ba ne cikin
girke-girken da ki ke cewa ‘yar uwarki tana nuna
miki?
Nayi maza na bar abinda nake yi na kalle shi
Cikin natsuwa da zumudi na ce mişhi Baba duk
abincin da nake zuwa da shi gidan nan fa ni nake
43
yi Yaya Dijah zama kawai take yi tana kallo in
taga zan yi wani abu ba daidai ba ta gyara min.
Shiru yayi yana kallon wuri guda nuna alamar
a cikin tunani yake, na bar abinda nake yi na
sake kallonshi tare da tambayarshi mene ya
faru Baba? Kaji miyar bata yi dadi ba ne?
Yayi maza ya gyada kai uh’uh ba haka ba ne
Mero tunani dai nake yi na in har ke ce da gaske
ki ke yiwo mana wannan girkin to ai gara in
hutar da wadannan yan uwa namu da suke ta
faman dawainiya damu shekara guda har da
wasu watanni tunda mahaifiyarku ta rasu ba su
taba hutawa da hidimarmu ba.
Don haka in har za ki iya to sai in sauke musu
nauyin girkinmu su rinka.yin nasa kawai in rinka
kawo cefanenmu kina yi mana.
Nayi maza na ce eh Baba gara kawai muyi
hakan can cikin zuciyata murna nake yi da
zumudi saboda babu abin da nake so nake kuma
sha’awa irin in ganni ina girki ni kadai ba tare da
ana nuna min ba wai ni a dole na iya.
Wannan maganar da muka yi da Babana bata
wani dade ba don ko kwana bakwai bata yi ba,
naje karbo cefane kamar kullum yanda na saba
ni ke zuwa wurin shi in karbo cefanen kayan
miya gami da su manja ko man gyada da maggi
44
in kai ma Babah Sumaye shikuma Baba Hodijo
yayi abin da ya saura tare da hatsi.
Ina tsaye ina jiran ta gama hada min in dauka
in kawo mata sai kawai naga ya miko min ledoji
guda biyu, ungo ki kai mata daya ke kuma ki
girka mana daya.
Gabana ya yanke ya fadi tamfar dai’ ba ni ce
na ce mishi na iya girkin ba. Zaro idanuwa nayi
ina kallonshi yayin da shi kuma ya ci gaba da yi
min bayani, na riga na yi wa Mallam Hodijo
bayanin komai, don haka kaiwa ita uwar taki
kunshi daya ki rike daya.
Kije ki girka mana abinda ki ka san shi ki ka
fi iyawa kin gane ko? Na ce mishi to Baba, na
kamo hanya ina dawowa gabana sai faduwa yake
yi ban taba yin girki ni kadai babu wani babba a
wuri ba hasalima kafin rasuwar Innata bana
shiga kicin da sunan ya yi girki ko da kuwa na
wasa ne.
Babah Sumaye ta zubawa cefanen ido tana
kallo yanzu nan bawan Allahn nan da gaske yake
yi sai ya raba girkin nan? Ta dan gyada kai tare
da fadin to ai shi kenan tunda haka ya gani
daya,
amma menene’? Ai mun riga mun zama
dan abincin da a ke sa mishi guda nawa yake?
Ban da haka ma kullumn fa cefanen nan a
wurinshi ake karbo shi amma ya ce wai
45
dawainiyar da ake yin tayi yawa, ni dai nafi
zaton ko subutan bakin da nayi na ce a gaya
mishi ga wata bazawara na saman mishi ne duk
ya kawo hakan.
Ni kuma ba nayi hakan ne don na gaji a sa
mishi tuwo ba a’a ko kadan ba haka ba ne nayi
mishi tallan bazawarar ne don ganin hankalinta
da natsuwarta shi kuma yana ta zaune a haka yau
kusan shekara daya da rabi da rasuwar Ramatu,
wanda wasu da kyar suke jira ayi arba’in sai
kawai ka ji sun daura aurensu.
Yanda dama ban san anyi wannan magana da
Babah Sumaye ta rattaba min ba haka a yanzun
ma da ta rattaba min ban nuna naji ko na gane
inda Zancen nata ya nufa ba, balle in furta wata
kalma.
Sa hannu kawai nayi na dauki leda guda daya
na juyå da nufin fita daga gidan saboda nima ban
san dalili ba sai naji maganar ta dan sosa min
zuciya ina fita daga gidan dai ina jinta tana cewa
bai fahimce ni ba ne, ban gaya mishi hakan don
ban damu da rashin da aka yi ba sai dai don
sanin da nayi cewar yanda duk muka kai da son
Ramatu to babu yanda za muyi tunda ta riga tayi
tafiyar da babu dawowa a cikinta sai dai kawai
muyi ta binta da addu’a.
[…] Halin Rayuwa Hausa Novel Complete […]