Littafan Hausa Novels

Halin Kishi Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Halin Kishi Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

DANDANO DAGA LITTAFIN HALIN KISHI

 

Seda ta tabbatar da Mama ta shiga bandakin tajiyo qarar ruwa alamar ta fara uzurin daya shigar da ita kafin ta sauke qafafunta qasa dakyar saboda yanda gaba daya jikinta yayi mata nauyi.

 

A yanda take bazaka taba zaton zata iya motsawa ba amma da yake ita ta saka kanta se gashi cikin abinda be wuce minti biyu ba cikin sanda ta fice daga dakin ta taki sa’a kuwa harta salallaba ta bar ward din bata hadu da kowa ba saboda dare ya rigada ya tsala Asuba ma ta fara kawo kai daga Marasa lafiyar har ma’aikatan da yawa sun samu bacci se masu jiran kiran kota kwana acan dakin su.

 

Qarfin hali kawai take tana daga qafa har ta fice daga get din Asibitin, zuciyarta ta qeqashe babu alamar tsoro ko fargabar wani abu musamman a irin yanayin da ake ciki na rashin tsaro da garkuwa da mutane haka Umaimah ta ringa tafiya a cikin daren nan a matuqar galabaice ga tsohon ciki seda ta kwashe kusan minti Arba’in kafin ta kai layin gidan nata zuwa sannan ikon Allah ne kawai yake tafiya da ita dan tamkar zata mutu haka ta zube a bakin Get din layin tana bugawa.

Soldiers Family Romantic Hausa Novel

Masu gadi ne suka taso da dalleliyar fitilar su suna tambayar waye, Sammani me gadin Gidan su ya gane ta, da sauri ya bude mata Get din yana mata sannu qasan zuciyarsa fal mamakin ya akayi ta taho daga Asibiti a wannan yanayin?

 

Dazu fa da sukaje ko motsi batayi kai shi tunda uwarsa ta haifeshi be taba ganin mace tamkar Aljana irin Hajia Umaimah ba, haka ya ringa binta da sannu har ya rakata cikin gidan, daga bakin qofar palour ya tsaya ta shige ya jawo qofar, a ransa yana Addu’ar Allah yasa a kwashe lafiya.

 

Kai me ma ya kaishi barinta ta shiga gidan be fara sanar da Alhajin ko ya kira Hajia Babba ba? Tunanin abinda kaje ka dawo ya sakashi runtumawa da gudu ya nufi bangaren Hajia Babba beyi la’akari da cewa dare bane ya ringa buga musu qofa jikinsa har rawa yakeyi dan se a sannan ya gane qatuwar wautar daya tafka kuma duk abinda ya faru yanzu shi za’a fara ganin laifi.

 

Ganin yana ta bugu ba’a bude ba ya sakashi zagayawa ta baya inda window dakin Halifa yake ya zuge Net ya shiga kwala masa kira yana cewa

 

“Halifa, Halifa ka tashi ga Hajia Umaimah can ta dawo ka tashi dan Allah kar ayi kisan kai a gidan nan ace da sa hannuna”.

 

Halifa daya farka da niyyar qundumawa duk uban da yake buga qofa Ashar da sauri ya wantsalo daga gado yana raba ido, Anty Umaimah kuma matar da suka baro a Asibiti bata hayyacinta waya dawo da ita gida toh?

 

Da gudu ya fice daga dakin ya nufi Sama gurin Hajia, a matattakala suka hadu tana shirin saukowa Habiba na biye da ita a baya kana ganinsu kasan hankalin su a tashe yake.

 

“Yawwa Halifa kaima kaji bugun kenan, muje mu duba wanene a wannan lokacin Allah dai yasa lafiya” ta fada tana qarasa sakkowa.

 

“Hajia Sammani ne wai Anty Umaimah ce ta dawo gata can ta shiga gida” Halifa ya fada yana yin gaba se Hajia ta dafe qirji tana cewa

 

“Umaimah? Umaimah kuma yaushe ta dawo ita da bata da lafiya waya dawo da ita gida? Kai Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un wannan bala’in har ina Umaimah bazaki kashe ni da raina ba” da wannan surutan suka dunguma bangaren Khalil sedai suna zuwa suka tarar da qofar palour a datse.

Sammani ya saka muqullin hannunsa amma yaqi buduwa alamar an rufe qofar ta ciki kenan.

 

Halifa ne ya koma cikin gida da gudu ya dakko wayarsa ya shiga kiran Yayan nasa, Hajia na tsaye ta kasa cewa komai, Addua kawai takeyi Allah ya tsare mata Dan nata da Marainiyar Alah.

 

CIKIN GIDAN

 

Humairah tana kwance lamo akan gado idan ka kalleta zaka dauka bacci take yi amma idonta biyu, ita kadai na san abinda take ji a jikinta bisa sabon al’amarin daya sameta. Sam Yaya Khalil be tausaya mata ko ya dubi qarancin shekarunta ba seda ya gurjeta son ransa tamkar me biyan bashi kafin ta samu kanta a hannunsa.

 

Yanzun haka da tana da qarfin tashi da barin masa dakin za tayi dan bata san abinda ze biyo baya ba idan ya fito daga wankan da yakeyi, bata tunanin ze barta ta huta duba da yanda dakyar da sidin goshi ya barta ta fito daga bandakin kafin ya shiga yin nasa wankan.

 

Idanuwanta da sukayi laushi tubus suka qanqance saboda kuka ta lumshe tana jin wani bacci bacci yana fizgarta amma bata so tayi tunda asuba ta kawo kai gara idan sukayi sallah se tayi baccin amma in Yaya Khalil ya bata dama kenan.

 

Juyawa tayi daga rufda cikin da take zuwa rigingine wanda yayi daidai da bugun da akayiwa qofar dakin da take cikin wani irin tashin hankali kamar za’a balla qofar idan ba kunnenta bama harda kururuwa take jiyowa daga wajen.

 

A firgice ta yunqura tana cije baki ta miqe zaune, jitayi bugun yana qara qarfi, ta waiwaya ta kalli qofar bandakin a daidai sanda Khalil ya fito daure da babban towel fari a qugunsa yana goge fuskarsa da wani qarami yana cewa

 

“Badai bacci kikayi ba yarinya dan yanzu ma aka fara…” se maganar sa ta maqale saboda bugun daya jiyo anayi tareda hargagin daya tabbatar na Umaimah ne ba shiri ya wurgar da towel din hannunsa ya nufi Humaira data dora hannu biyu aka tuni hawaye suka balle mata, zatayi magana ya dora hannunsa a kan lebe alamar tayi shiru seta shiga girgiza masa kai.

 

Seda yaja numfashi ya ajiye zuciyarsa na tsalle saboda tsoro kafin ya nufi bakin qofar ba shiri Humaira ta kwasa da gudu ta shige gurin walk in closet dinsa ta fara neman gurin buya. Ita dai tana ga ajali ne yasa ta auri Yaya Khalil dan dai bata ga alamar tana da rabon komai a cikin zama dashi ba sena wahala.

Ta tabbata ko Umaimah bata kashe ta da hannunta ba kamar yanda ta dade tan iqirari to kuwa tabbas fargaba da tsoratarwar da take mata zasu saka zuciyarta tayi bindiga.

 

Khalil kuwa seda ya gyara muryar sa kafin a shaqe kamar wanda ya tashi daga bacci ya ce

 

“Waye wannan yake bugamun qofa a daren nan Sammani wane irin rashin hankali ne me ya faru zakazo kana mun bugu yanzu?”

 

“Kutumar bura ubanka ce ta faru Khalil, ka bude mun qofar idan ba haka ba wallahi har kaje lahira kana dana sanin abinda zan aikata maka Maci amana Macuci” Umaimah ta fada cikin hargagi.

 

An rigada an kai gabar da bayajin komai dan Umaimah ta zageshi, a yanzu tashin hankalin sa daya ne, idan ya bude qofar ta shigo taga Humaira besan me zata aikata ba haka idan yaqi budewar nan ma besan me zata yi ba waima ta yaya akayi ta farka har aka sallameta daga Asibiti tsakar daren nan wannan wane irin bala’i ne haka.

 

“Khalil bazaka bude bako? Shikenan ka zauna a ciki kaida Yar iskar Karuwar da ka dakko amma ka jirani na dawo zakaga abinda zanyi” Umaimah ta sake fada kafin ta juya dakyar take daqa qafa ta sauka qasa. Tana jin ana buga qofar kuma ta tabbatar da Sammani ne ze taso yan cikin gidan amma bata kukasu ba ta wuce.

 

Kitchen ta nufa, zuciyarta ta rigada ta gama qeqashewa abinda ta ayyana mata tayi kawai shi zatayi kota mutu ko ta rayu wannan duk ba damuwarta bace amma dole ta koyawa Khalil hankali na cin Amarta da yayi.

 

ASIBITI

 

A nutse Mama ta fito daga bandaki bayan data dauro alwala taja qofar ta rufe a hankali gudun karta tashi Umaimah. Kai tsaye idonta ya sauka akan gadon da Umaimah take kwance se taga babu kowa, da mamaki ta qarasa Gurin ta daga bargon dai dagaske bata nan.

 

Hijabin ta ta zura ta leqa waje ta tambayo ko Ma’aikatan ne suka dauki Umaiman tunda daman sunce akwai gwajin da za’a mata amma ta dauka ai seda safe.

 

Bacci sosai ta tarar da Nurses din sunayi abinsu, seta qarasa kusada wadda take kula da Umaimah ta shiga tashin ta, Nurse Halima ta farka bakinta dauke da salati ganin Mama a tsaye yasakata wartsakewa tana cewa

 

“Aa Mama badai jikin Umaiman bane? Muje na dubata mu gani se a taso likita”

 

“Ba ku kuka dauketa ba ne Nurse? Na shiga alwala na fito yanzu banganta a dakin ba” Mama ta fada cikin firgicin jin maganar Nurse, to ina Umaimah zata tafi a daren nan ita da ba lafiya ba?

 

Kafin kace me Asibiti ya hargitse ana neman Umaimah daki daki, da yake Asibitin  ba wani girma ne dashi ba cikin dan lokaci suka bincike ko ina amma babu Umaimah babu me kamar ta har Get an tambayi masu gadi sukace basuga fitar kowa ba zuwa sannan tuni Mama ta fara kuka, wayarta ta dakko ta shiga kiran Abba ta gaya masa halin da ake ciki seda ta kira sau biyar kafin ya daga wayar.

 

GIDAN ALHAJI SABO

A daidai sanda Mama take kira Anty Saratu ta farka yin fitsari, da yake wayar a vibration take bata ji ba, seda ta yiwo fitsarin ta dawo, dakyar take bude ido saboda bala’in baccin da take ji to kusan kwana biyar kenan a jere baccin su ragagge ne ko yau din se gurin qarfe daya suka dawo gida daga Asibitin kafin ta kwanta biyu tayi.

 

Hasken data hango wayar Abba tayi ya saka ta miqa hannu tana hamma ta jawota dan tasan qila Alarm din nasa na fama ne ze fara kadawa ya hana mutane bacci, sunan Maman Yara da ta gani ya saka fara tashin Abban ya yi juyi yana cewa

 

“Ohni Saratu wai me kuma kike so dan Allah ki barni na huta mana idan dai ba so kuke ku qarasani na mutu kawai ba”

 

“Alhaji Maman ce take kiran ka a waya, ina ga jikin Umaimah ne fa” ta fada tana miqa masa wayar, seya karba da sauri ya saka a kunne, Mama ta fashe da kuka tana cewa

 

“Alhaji An sace Umaimah, daga na shiga Bandaki nayi Alwala na fito babu ita a dakin gashi mun duba ko ina amma ba’a ganta ba”.

 

“Kamar yaya ba’aga Umaimah ba? Ita Umaiman Allura ce ko me da za’ace ta bata wannan ma ai zancen banza ne, jira gani nan zuwa” Alhaji Sabo ya fada yana miqewa tsaye, jiri ne ya jashi ya koma dabas ya zauna da sauri Anty Saratu ta taro shi tana cewa

 

“yi a hankali Alhaji kasan kaima fa ba lafiyar ce dakai ba”

 

“Ba’a ga Umaimah ba Saratu, wannan abu har ina daga wannan tashin hankali se wannan kai Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, miqomun riga ta muje Asibitin mu gani”.

 

“Ba’a ganta ba kodai wani gurin ta shiga taya za’a ce baa ga mutum ba a Asibiti Ahaji sudai duba dakyau ko bayan gida ta zaga” Anty Saratu ta fada tana miqa masa jallabiyya se ya karba ya hau kici kicin sakawa amma ya gagara saboda yanda jikinsa yake rawa.

 

“Saratu bane babbar riga ki gani na dora zata fi mun sauqi” ya fada yana zama a bakin gadon ya dafe kansa da hanna ye biyu, al’amarin Umaimah nema take yi ta kashe su kawai ta huta dan ya tabbatar yanzun da kanta ta tashi daga Asibitin wannan kadan ne daga aikin ta.

 

Tareda Salman suka fito daga gidan, Salmanun ne yake jan motar. Seda suka hau titi ya kalli Abban yana cewa

 

“Abba ya kamata a sanar da Yaya Khalil fa yasan halin da ake ciki?”

 

“A kyake shi kawai Salmanu muje mu gani idan ba’a sameta ba sannan se mu sanar musu” Abba ya fada yana rufe baki wayar Salmanu da take gefensa ta fara qara, seya cirota yana duba.

 

“Lah Abba kaga Yaya Khalil din nema qila toh yasan abinda yake faruwa” Salmanu ya fada yana daga wayar ya sakata a speaker.

 

“Salman ku taimaka mana, ga Umaimah nan tazo ban san me zatayi ba tace na bude qofar dakin da muke ciki idan ba haka ba se tayi abinda har naje lahira ina dana sani. Tsoro nake ji karna bude tayi mana wani abun kuma idan ban bude din ba bansan me zata aikata ba” Khalil ya fada cikin rawar murya dan da gaske ya gama karaya da lamarin Umaimah. Ya shaida yar daba ce ta gaske, a HALIN KISHI irin nata za ta iya aikata masa duk abinda zuciyarta ta raya mata tunda ai ba yau ta fara ba.

 

“Muje gidan, bari na kira Maman ku na gaya mata, yanzu ita wannan yarinyar bazata bar rayukan mutane su huta ba ko? Ai Shikenan” Abba ya fada yana latsa waya.

 

Sanda suka isa sun tarar dasu Hajiar su Khalil a tsaye har sannan Sammani da Halifa na qoqarin buge qofar amma abu ya gagara saboda qofar ba ta wasa bace, Cikinsu Salmanu ya shiga suka ci gaba da kici kicin, Abba na kusada Hajiya da ta kasa cewa komai ya na bata baki.

 

Kamar an ce Habiba ta waiwaya ta hango haske ta gurin qofar Kitchen ta baya, hannun Hajiya ta janyo da qarfi ta nuna mata suka yunqura zasu tafi gurin Abba ya dakatar dasu da yi musu alamar kar suyi motsi ya fara sanda a hankali har ya isa gurin da Umaimah take kiciniyar kunna cylinder Gas saboda duk dare suna kashe ta ne daga wajen idan zasu kwanta gudun tsautsayi, ko wani abun zasuyi sedai suyi amfani da electric.Abba na zuwa kuwa ya shammaceta beyi wata wata ba ya dauke ta da marin da seda taga taurari a idonta Halifa dake bayansa yayi azamar kashe Gas din data kunna dan sosai suka jiyo qarar fitar sa daga Kitchen din alamar ta zare pipe din ne yana fita kaitsaye.

 

“Me kike yi Umaimah” Abba ya fada ciki matuqar bacin rai yana dubanta.

 

“Igiyar Gas na cire daga jiki, zan sake shi ya cika gidan sannan na kunna mana wuta dani dasu dukka mu qone dan wallahi da nayi zaman KISHI da wata mace akan Khalil gara mu mutu, kuma yanzun ma ba fasawa nayi ba, ko ba yau ba wallahi se na kashe ta, na kashe Khalil sannan na kashe kaina” Umaimah ta fada babu alamar wani tsoro ko nadama a fuskarta.

 

Duka Abba ya sake kai mata a zuciye kafin ya angizata suka shige cikin gidan Hajia ta tare tana cewa

“Kayi Haquri Alhaji kodan halin da take ciki, Umaimah me yasa kike haka me yasa bazaki bar mu mu huta ba ki dauki haquri da dangana dan Allah?”

 

“Karki sake taba ni munafuka Annamimiya, idan da kina so na haqura ai tun farko seki hana danki yin auran tunda yana jin maganar ki amma saboda baqin munafunci kika mara masa baya yanzu kuma kizo kina bani haquri se kace ke har naki mijin ya mutu kin bari anyi miki Kishiyar.

To wallahi bazan fasa abinda nayi niyya ba kuma duk wanda yayi yunqurin hanani se ta shafe shi Idan yaso kowa ma ya mutu a huta” Umaimah ta fada tana fizgewa daga ruqotan da Hajia tayi, ta sake yunqurawa kafin su ankare har ta kai matattakalar benen kai bazakace ciki wata tara ne a jikinta ba a yanda take tafiya.

 

A daidai lokacin Khalil ya fito tareda Humairah dake sharbar kuka a bayansa ta tsorata sosai ta gama saddaqarwa yau kwananta kawai ya qare a gidan, Umaimah na hangota ta kai mata wata muguwar cakuma ta goce, mantawa tayi da duk wani ciwo da take ji a jikinta ta ware qafa uku uku ta hada matakalar ta diro qasa tana ganin mutane da mugun gudu tayi bayana Hajia tana sauke numfashi.

 

“Ka fito ko to kuwa ka shirya baquntar lahira yanzu Khalil sena kashe ka” Umaimah ta fada tana daukar Abin flower da yake akan benen ta nufi Khalil da yayi mutuwar tsaye gadan gadan, tana dagawa marata ta katsa mata ba shiri ta wullar da abin hannunta ta dafe ciki tareda durqushe wa Khalil yayi kanta kafin ya qarasa taja baya tana cewa

 

“Karka taba ni munafuki karka kuskura qazamin hannunka ya tabani kuma ba barinka nayi ba se naga bayanka da duk wata mace da kace zaka hadani da ita”

 

“Kai Khalil wuto daga nan ka rabu da ita” Abba ya daka masa tsawa kafin da kansa ya hau benen ya kamo hannunta, tana tirjewa da komai seda ya direta a tsakiyar palour sannan ya qyaleta.

 

Idanunta da suka rigada suka qeqashe ta daga tana binsu daddaya da kallo kamar yanda suma suke kallonta ko wanne da kalar tunanin da yakeyi akanta.

 

A saitin Khalil ta tsayar da idonta se kawai ta fashe da kuka tana cewa “Kasan ina kishinka Khalil me yasa? Me yasa zaka hadani da wata Mace dame na rageka da zakayi mun kishiya Khalil me nayi maka” ta qarasa cikin daga murya tana sake rushewa da kuka.

 

Halifa ne ya matsa kusada Hajiya qasa qasa yace “Anya Hajia Anty Umaimah bata da motsi a kwakwalwarta nidai ina ga akaita gurin likitan kwakwalwa dan abinda takeyi ya fi kama da na masu motsi a kai”

 

“Uwarka Aisha gata nan a kusa da kai itace take da motsin kwakwalwa, se kaje ka tono ubanka Ummaru a kabari yazo yayi mata magani” Umaimah ta fada idonta cikin na Halifa babu ko dar da tunanin matsayin uwar tasa da ta zaga a gurinta.

 

“Umaimah ashe baki da mutunchi har haka? Hajiya Aishar kika ambata kika zaga harda Mijinta da yake kabari saboda ke baki da mutunchi kin kuma zubar da tarbiyyar da muka baki a titi ko kin kyauta nace kin kyauta, ki tashi ki wuce mu koma Asibiti ga motar Ambulance nan sunzo da ita zasu dauke ki” Mama da shigowarta kenan ta fada cikin tsananin fushi tana qarasawa inda take ta kama hannunta. Seta fizge tana cewa

 

“Wallahi babu inda zani, indai kuma ana son zaman lafiya se dai Khalil ya saki yarinyar nan. Ba’a halicce shi dan kowacce mace ba bayan ni dan haka bazan taba raba shi da wata ba”.

 

“Ke a wa? Yanzu har kin isa mace da zaki tsaya kice baza’ayi miki kishiya ba ko kuwa kenan har wata macece data san ciwon kanta balle tayi kishin mijinta? To bari kiji kishi ba hauka bane idan zaki dawo hankalin ki tun wuri ki dawo saboda kinga ana lallabaki ya saka kike botsarewa ko to daga yau zanga uban da ze sake lallabakin, ki tashi ki wuce muje aure kuma Khalil da Humaira har mutuwa idan yaso baqin ciki ya kashe ki shasha sha mara tunani” Mama ta sake fada a mugun fusace.

 

Se Umaimah ta miqe tana cewa “ai ko baki fada ba nasan kina baqin ciki da zama na ni kadai a gidan mijina ina yin yanda naga dama bayan ke kina da kishiya dole kiyi murna tunda anyi mun, to wallahi daga ke har ita Hajiyar baku isa ba, naga itama ba ayi mata kishiyar ba shine ni zaku taru ku hada baki ayi mun ko to sedai ya zaba koni ko ita,

 

Idan kuma ita ya zaba to se na kashe shi in yaso kowa ya rasa”

 

Mari Mama takai mata kafin ta rufeta da duka tana cewa

“Kaiconki Umaimah kaiconki, wallahi da ba’a gida na haife ki ba tabbas zance ke ba yata bace ba jinina bace dan kaf ahalina dana Ubanki babu me mugun hali wanda be dauki kalmar kisa a bakin komai ba irin ki, kafin ki kashe shi ni gara na miki dukan daze lahantaki Muguwa me baqar zuciya”

 

“Aa Hajiya ki bari ki dena jifanta da wadannan kalaman yawun uwa kaifi ne dashi akan Da, Ke kuma Umaimah kiyi haquri mu bar komai zuwa safiya in Allah ya kaimu” Hajiya Aisha ta fada tana qoqarin janye Umaiman ai kuw ata hankada ta da yake a bazata abin yazo mata se gata tim a qasa ta bugu da qugunta sosai har seda tayi qara.

 

“Karki sake tabani munafuka tun farko ai komai yana hannunki da kinso ki gyara da ba’a zo haka ba se yanzu ne zaki ce na bari da safe toh an qi a bari din” Umaimah ta fada tana zarewa Hajiya data zuba mata ido kawai tana kallonta ido.

 

Khalil kuwa runtse idonsa yayi, Allah kadai yasan irin daci da qunar da zuciyarsa takeyi masa a duk sanda Umaimah ta zagi mahaifiyarsa amma yana danne zuciyarsa ne ya hanata aikata mata abinda take raya masa saboda yana mata uzurin me rangwamen hankali, kishi ya taba mata kwakwalwa qari kuma da cikin da take dauke dashi.

 

Yasan Umaimah nada kishi amma be zata zata bari hankalinta ya gushe ta ringa abu irin na mahaukata ba akan abinda ita ce silar faruwarsa, meye lefinsa dan yayi aure bayan ita ta bashi qofar na yaje yayin sannan yanzu zatazo tana tambele da rashin hankali har tana iqirarin zata kashe shi?

 

Hadiye wani abu daya tsaya masa yayi ya bude baki dakyar yana nufar ta yace

“Duk abinda zakiyi Umaimah ni zakiyi wa ni nayi miki laifi karki sake zagin Mahaifiyata ko wani akan wannan abun ina kuma yi miki uzurine kawai saboda halin da kike ciki a yanzu”

 

“Ni kake yiwa uzuri Khalil? Idan ka sakeyi mun uzuri kai ba dan halak bane, idan baka dauki mataki akaina ba to Aisha da Ummaru shegenka sukayi kai ba dan halak bane

 

Sannan kace karna sake zaginta ko? (Seta waiwaya ta kalli Hajiya datayi suman zaune tun dazu kawai tana kallon Umaimahn) tace

“Aisha kinci uwarki, Khalil ka tsireni na zageta kayi abinda zakayi”

 

A mugun fusace Halifa yayi kanta amma se Hajiyar tayi saurin riqe shi tana cewa

“Barta Halifa wannan ba Umaimah bace, na tabbatar idan ba shafar Aljanu ba to ta samu tabin kwakwalwa amma wannan ba Umaimar da muka sani bace”

 

“Uwarki ce mahaukaciya bani ba” Umaimah ta sake fada kafin ta rufe baki Abba ya kai mata wata mahangurba ba shiri ta durqushe a gurin ko ihu ta kasayi saboda yanda duka ya shigeta .

 

“Khalil kana tsaye, mace ta zagi uwarka a gabanka kana tsaye baka dauki mataki ba Hajiya ko dai bake kika haifi Khalil ba?” Mama ta fada cikin kidima tana tafa hannaye,

 

Khalil da idanunsa suka rine zuwa ja jijiyoyin kansa gaba daya sun tashi ya kalli Mama yace

 

“Mama dagaske wannan ba Umaimah bace, ko dai kwakwalwarta ta tabu ko kuma mugayan Aljanu ne suka shafeta amma kema Mama kinsan wannan ba Umaimah bace, kowa ya sani ina son Umaimah itama tana sona na tabbatar ba a hayyacinta take wadannan abubuwan ba”.

 

“Allah ya wadaran soyayya irin taka Khalil Allah kuma ya wadaran zuciyarka zuciyar da kana tsaye matar aurenka zata zagi uwar data haifeka ka saka mata ido ba tareda ka chanza mata kamanni a bugu daya ba, Umaimah ko dai kin siyar da Imaninki kin bi bokaye ne ban sani ba dan dai wannan yafi kama da zuciyar wanda aka tsafance Dodo ya cinyeta dan Ubanki me kika aikata masa?

 

Ko da yake ba banza ba, tun tuni ya kamata na fahimci cewar Umaimah kin bar turbar Allah da Annabi amma ban gane, taron qawayen da kullum nake harqilon rabaki dasu inda ya kaiki kenan wayyo Allah na ni Malika ubangiji ka yafe mun ka sassauta mun wannan jarabta da kayi mun da kangararriyar yarinya da take neman kaini kabari” Mama ta fada tana fashe wa da kuka, se ta sake kallon Khalil tace

 

“Saketa mara zuciya, ka saki Umaimah yanzun nan Khalil”

 

“Mama mu fara mayar da ita Asibiti a bincika kwakwalwarta, idan basu ga komai ba se mu tafi gurin Malam Ishaq qila a can a dace amma nasan ba yin kan Umaimah bane dole akwai abinda yake zungurinta” Khalil ya fada cikin rawar Murya kamar yanda jikinsa ya dauki rawa lokaci daya.

 

“Wallahi seka saketa Allah yasa Dawanau ce ita ko kuma kukar bulukiya, kai ko kashin awaki na haife ku yau Khalil seka rabu da Umaimah idan kai baka san darajar kanka ba to ni bazan zuba ido yata ta wulaqanta uwar mijinta ba nima na haifa, na kuma san zafin abinda takeyi idan ni akayiwa bayan saki wallahi se na saka an hada mata dan bura uban duka ta yanda ko akuya bazata sake yiwa tsawa ba bare ta zagi bil’adama” Mama ta sake fada cikin hargagi.

 

“Ai wallahi ko be saketa ba a yau se Alqali ya kashe auran nan, ni kaina da zan iya canzaki daga cikin Ahalina da a take a yanzu zanyi dan banyiwa iyayena haka ba ban san dalilin da yasa Allah ya jarabce mu da ya irinki ba amma muna roqonsa ya kawo mana dauki” Abba ya fada cikin qololuwar bacin rai.

 

“Abba Mama dan Allah kuyi haquri, ku bari muga safiyar nayi alqawarin idan har aka tabbatar lafiyar Umaimah qalau a take zan rubuta mata takaddar sakinta” Khalil ya fada yana kallon Hajiyarsu da sigar roqo, Hajiya da kwallar baqin ciki ta zuraro mata ta kauda kai, ta bakin na Mama ne itama ta fara zargin shikansa Khalil din ba kansa daya ba, duk yanda akayi da gaske an bawa Dodo zuciyarsa ya cinye in ba haka ba wannan abu har ina?

 

Kai da Fata Mama da Abba suka dage se Khalil ya saki Umaimah da tunda tasha marin Abba ta durqushe bata sake dagowa ba saboda wani Azababben ciwon mara da kai da suka dirar mata lokaci daya.

 

“Shikenan, taje na saketa saki daya” Khalil ya fada kamar wanda ze fashe da kuka.

 

“Uku zaka mata ka yanke duk wata alaqa da take tsakanin ku yanzun nan” Mama ta sake fada,

 

“Hajiya dayan ma yayi ba se ya qara ba” Hajiyar su Khalil da tunda ta fadi bata sake magana ba ta fada

 

“Wallahi se ya qara Hajiya ko beyi uku ba se ya mata biyu” Mama ta sake kafewa dole Khalil ya sake qarawa Umaimah da tayi mutuwar zaune jin wannan Drama da ake tsarawa.

 

“Durun uwar nan, ka sake ni Khalil a maimakon ka saki wannan Yar iskar daka auro? To wallahi dani da kai da ita sedai duk ayi biyu babu” Umaimah ta fada tana miqewa, dukda azabar da take ji a jikinta da a kwayar idonta ma kana iya karantar halin da take ciki haka ta yunqura, kafin kowa ya ankara ta finciki wani flower vase da yake kusa da ita babu bata lokaci ta saukewa Khalil a daidai Mazantakarsa, ihu daya ya kwalla ya fadi wanwar a gurin.

 

“Shikenan ta kashe shi, Ta kashe Khalil dama ta fada gashi kuwa ta cika ku riqeta Salman Na rantse da Allah yanda kika salwantar da ransa Umaimah da hannuna zan miqawa Hukuma ke” Abba ya fada cikin tashin hankali yana Kallon yanda Salman da Halifa suka rufu kan Khalil daya ke nan babu alamar rai a tattare dashi……

 

KISHI ABU NE DA UBANGIJI YA SAKAWA KO WACCE HALITTA, SEDAI A DUK INDA AKA GUDANAR DASHI DA UMARNIN ZUCIYA KADAI BA BISA DORON HANKALI BA TOH TABBAS ZE KAI MUTUM GA FILIN NADANAR DA BATA DA AMFANI

 

UMAIMAH TA KASAN CE DAGA CIKIN MATA MASU TSANANIN KISHI, AKAYI RASHIN DACE TA ZAMO DAGA CIKIN MUTANEN DA BASU DAUKAR KOMAI DA MUHIMMANCI A RAYUWARSU. TA YAYA ZATA KASANCE MACE DAYA TILO CIKIN RAYUWAR Architect Khalil Umar Bayero?

SABUWAR TAFIYA ME DAUKE DA SABON SALO DA BAZAKUSO AYITA BA TAREDA KU BA

 

WANNAN KARON MA ALQALAMIN MARYAMA YA SAKE ZUWAR MUKU DA DADDADAN LABARI DA ZE QAYATAR DAKU,KU ILIMANTU KUMA KU NISHADANTU

 

Kudai ku gyara zama ku sanya tabarau dan wannan tafiyar ba kalar sauran bace

 

Littafin HALIN KISHI ze fara zuwar muku ranar 7 ga watan May akan manhajar WhatsApp da kuma Arewabooks

 

Ga masu buqata

Naira 500 ne kacal

Akwai farashin masu siya su tura a group

Masu Audio Novel Mallakin Zaria TV ne kadai

 

A tura kudi a asusun

8142548705

Maryam Umar Farouk

Opay Digital services

 

Se a tura shedar biya zuwa ga

07061838488

 

First Lady Hajia Ma’un Yusufa tace ku garzayo kuzo ayi wannan tafiya tare daku, da Excellency Yusuf ne ze dauki nauyin biya muku baki daya se kuma yace yana so yaga ruwan qaunar da kuke musu shida Ma’unsa, Engineer Malam Bashir ma ba’a barshi a baya ba yace yau ga ranar biyan tsinuwar daya sha a hannun ku.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment