Littafan Hausa Novels

Halin Girma Hausa Novel Complete

Auren Yarinta
Written by Hausa_Novels

Halin Girma Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Halin Girma Hausa Novel Complete

HALIN GIRMA!*

 

®Hafsat Rano.

 

FREE PAGES!

 

(1)

 

 

 

 

 

(1)

 

***Komai na rayuwa na tafiya ne bisa tsari da kudurar ubangiji, komai ya faru da bawa dama tun fil azal hakan na cikin kaddarar sa, Wala kaddara mai kyau ko kuma akasin ta. Yarda da Kaddara me kyau ko mara kyau na cikin Imani!

 

A tsaye take gaban sink din cikin toilet din tana wanke kananan kayan da ya kasance mallakin Maama da Zeenat, lokaci zuwa lokaci tana cire hannun ta tana yarfe shi saboda sanyin da ake zugawa kasancewar karshen December ne a lokacin da ake zuga sanyi. Dauraye kayan tayi ta yi saurin fitowa ganin haske ya hudo ta window din toilet din. Karfe shida da rabi agogon falon ya nuna, tayi saurin karasawa kitchen din domin dora abin karin kumallo kafin ahalin gidan su tashi.

 

Allah Ne Sheda Hausa Novel Complete

 

Tun kafin asubah take fara ayyukan gidan wani lokacin har karfe tara na safe bata kamalla wa, duk kuwa da tana iyakar kokarin ganin bata wuce taran ba saboda karatun ta na islamiya da take zuwa duk weekend, tana ganin shine kadai gatan da zata yi wa rayuwar ta a halin da take ciki a gidan mahaifin ta. Bata fatan wani ya shiga irin rayuwar da take ta kunci da tsantsar makirci, babu wanda ya san halin da take ciki balle ya kawo mata dauki, bata isa ta bud’e baki ba saboda kowa ganin kirki da karamcin Maman yake, mace ce me masifar kirki, me haba haba da saka duk wani abu nata gaba da na duk sauran yayanta a idon ahalin gidan,a badini kuwa bata da maraba da bola.

Kowa kallon mara dadin zama yake mata ko kuma mara godiyar Allah saboda rashin walwalar da take fama da har ya shafi kaso mafi rinjaye na rayuwar ta, zaka dauka bata dariya ko doguwar magana sai dai bata da sukunin yin kamar sauran yan matan gidan nasu.

Kowa kallon wadda tayi sa’ar uwar riko yake mata, ayi ta sakawa Maman albarka da yabo a gabanta tana amshewa amma a bayan idon mutane! Bakar wahalar da take sha ba zata misaltu ba.

Da tunanin ta kammala aikin ta dauraye hannayen ta sannan ta fito ta jera musu a saman dining ta dauko nata a dan plate ta wuce zuwa dakin su.

 

Bude kofar da tayi ya farkar da Zeenat, a zafafe ta dago ta watsa mata kallon banza gami da jan d’an karamin tsaki tana sake rufe kanta da katon duvet din da take kanannade a cikin sa. Cikin nutsuwarta ta karasa shigowa d’akin tana dora plate din saman d’an madaidaicin mudubin dake cike da kayan shafe-shafe ta soma gyara wajen data tashi. Katifar ta fara daukewa ta kaita chan store sannan ta dawo ta share dakin a hankali gudun magana taci abincin a tsaitsaye ganin lokaci na neman kurewa tayi saurin watsa ruwa a gaggauce ta fito.

Dogon hijabin ta ash colour daya kasance a matsayin uniform din islamiyar tasu ta saka bayan ta gama shiryawa ta dau yar madaidaiciyar jakarta me dauke da Al-kurani me girma da sauran littafan addini ta fito.

Habib na zaune saman dining da alamun zaman sa kenan ta gaishe shi a nutse sannan tayi masa sallama ta wuce islamiyyar dake chan kasan layin su inda take zuwa duk asabar da lahadi da safe sai sauran ranakun da yamma amma banda juma’ah.

 

 

 

*Babban gida ne irin wanda zaka kirashi da Family house, bangarori ne da dama a ciki wanda yake dauke da gidaje guda shida dake kunshe da mutane cikin su suna rayuwa irin wadda suka zaba ma kansu. Duk da kowanne bangare na da tsarin da yake tafiyar da rayuwar sa akai amma kuma suna tafiya ne da ra’ayoyin juna, daya baya taba zartar da hukunci be sanar da daya ba, sannan duk abinda suka zartar din dole ne ya samu amincewar mahaifiyar su Hajiya Fatima wadda suke kira da Gaji.

Gidan ta ne a tsakiya in da sauran gidajen ke kewaye da ita, galibin yan matan family din suna tattare ne a shashen nata da ya zama tamkar matattarar su, yanayin haihuwa a family din na tafiya ne kusa da kusa, inda zaka samu yawanci sa’oin juna a kowanne gida.

Duk da basu da tarin dukiya irin me yawan nan amma suna da rufin asiri daidai gwargwado, sannan ana damawa dasu a duk bangarorin ilimi na Islama dana bokon hakan ma bangaren kasuwanci da siyasa duk babu wanda basa tabawa.

Zamu iya cewa kowanne a cikin yayan Gajin yayi sa’ar abokiyar zama ta kwarai dan babu wanda yake kuka da abokiyar zaman sa, daidai gwargwado suna zaman su lafiya suna kuma mutunta juna suna girmana Gaji da duk wata bukatar ta.

Muguwar mace me kinibibi da kissa zai yi wuya ka gane alkiblar ta farat daya, komai su kayi daidai ne suna kuma da kokarin kyautatawa kowa, suna kokarin boye aibun su suyi amfani da hakan wajen muzgunawa wanda basu so, idan yayi korafi a bashi rashin gaskiya saboda kirkin su.

Alhaji Muktar shine Babban dan Hajiya Gaji bayan Babbar Yayar su mace da suke kira da Hajiya Babba dake zaune a Sheffield dake birnin London tare da family dinta , sai me bi masa Dr Ibrahim, sai Abba Usman sai Abba Musa sai dan auta Abba Kabir.

Dr Ibrahim dan boko ne sosai dan har ya kai matakin associate professor in da yake lecturing a halin yanzu. Matar sa daya ta aure Maama wanda zamu iya cewa kaf family din babu wanda baya kaunar ta saboda kirkin ta. Yaranta uku da Dr, Habib ne Babba, sai Zeenat sai karamin kanin su Marwan. Sai dai shi yana da ya daya daban wadda suke haifa da matar da ya aura a lokacin da yaje karatun sa na Masters a University of Michigan, anan suka hadu har sukayi aure suka haifi ya daya me sunan Gaji (Fatima-Iman) a lokacin ne kuma suka rabu saboda wata babbar matsala da ta taso tsakanin shi da family dinta, dan dama basa son auren, yana ji yana gani ya rabu da ita, ya dawo gida. Fatima na yin wayo suka kawo masa ita inda ya dauki rikon ta ya damka a hannun Maama wanda a lokacin take goyon Zeenat itama. Bata taba nuna masa komai ba ko a fuska kuma be taba ganin wani banbanci tsakanin Fatima da Zeenat ba, shiyasa ya kara bata mazauni me girma a zuciyar sa.

 

***Daidai layin su ta hangi Zeenat tsaye da Bashir, dan dam taji a zuciyar ta kasancewar ba wannan ne karo na farko ba, duk wanda yace yana son ta in sha Allah ba za’a dau lokaci ba zata same shi tare da Zeenat shikenan kuma ta ta maganar ta sha ruwa. Zeenat yar uwarta ce amma duk da haka tana jin babu dadi, sai dai bata bar hakan yayi tasiri a zuciyar ta ba, ta dau hakan a matsayin wata jarrabawar rayuwar ta. Daidai in da suke tsaye tazo zata wuce Zeenat din ta kira sunan ta

 

“Iman!” Tsayawa tayi chak, ta kalle su kad’an sannan tace

 

“Sannun ku.”

 

Murmushi Bashir din yayi mata sannan yace

 

“Malamar islamiyya, sannu da zuwa.”

 

Bata amsa masa ba dan yadda yayi maganar taji akwai alamun rainin wayo

 

“Ya akayi?” Tace tana kallon Zeenat.

 

“Babu!” Ta dage kafadar ta.

 

“Ok!” Tace tana cigaba da tafiyar ta, tana jin sanda suka kwashe da dariya, ta dan ji babu dadi a ranta amma ta danne, ta karasa gidan duk ranta babu dadi. Da gaske ta ji zuciyar ta, ta amince da Bashir farkon magana da yayi mata har tana addu’ar Allah ya tabbatar mata dashi, sai gashi tun ba’a je ko ina ba, ya koma wajen Zeenat wadda ko da ace da wasa yaje wajen Zeenat din toh babu ita babu shi har abadah.

 

A gate taci karo da Maryam, a kalla ba kamar sauran ba, Maryam ta fuskance ta, shiyasa tasu tazo daya sosai, duk da ba wata doguwar hiraa ce ke hada su ba amma ta kan sake da ita fiye da kowa. Bikin su za’a yi su hudu a gidan. Maryam din sai Bilkisu, Aysha da Amina. Daga su sai ita da Zeenat da yar gidan Abba Musa Rabi’ah sune a layi, duk cikin su babu wanda bashi da me son shi amma banda ita da ta gagara samun wanda ma zai tsaya din.

Bangaren Gajin suka wuce tana mata hira akan shirye shiryen bikin, rabin hankalin ta baya kan Maryam din har suka karasa, suna shiga ana kiran sallar magriba sai kawai suka wuce sukayi alwala.

Bayan sun idar ne Gaji ta kalle su tana kan abun sallah kamar zatayi magana sai kuma ta fasa. Sai da ta gama ta tashi sannan tace

 

“Maryama daga ina haka ke da alhuda-huda?”

 

“Daga islamiyya Iman take ni kuma na fito zan taho nan muka hadu.”

 

“Toh ku tashi ku dubo min ko an gama tuwo dan cikina ya soma kiran chiroma.”

 

“Wai Gaji wasa wasa fa kina da ci wallahi.”

 

“Saukin ta ba kowa ke siyan kayan abincin ba ‘yaya na ne, ko zaku hana su bani ne?”

 

Rik’e baki Iman tayi tana dariya Maryam tace

 

“Bamu isa ba ai Gaji, aci dadi lafiya lokacin ki ne.”

 

” Yafi muku sauki dai, kema alhuda-huda kin fara zama su balki ko? Kika biye musu baki da bakin da zaki iya karawa dani atau.”

 

Shiru tayi bata ce komai ba, suka zagaya kitchen din Gajin da ke baya suka hado mata abincin suka kawo mata sannan suka zauna suka ci tare, lokaci lokaci Maryam na tsokanar ta, ita dai Iman jin su kawai take har aka gama suka tattare kayan sannan Maryam ta tafi ta barta a nan, sai kawai ta zame tayi kwanciyar ta a saman doguwar kujerar ta fad’a kundin tunani kamar yadda ta saba.

 

“Yaya Iman kizo inji Maama, zamu ci abinci kar ya huce baki ci ba, kiyi sauri.”

 

Muryar Marwan ta iso daidai kunnenta, da sauri ta tashi zaune, sai kuma ta mike da sauri tana jin sanda Gaji tace

 

“Hajara ba dai kirki ba, yadda kike kula da yarinyar nan ubangiji Allah ya kula miki da naki yayan.”

 

Wasu guntayen hawaye ne taji suna neman zubo mata, tayi saurin maidasu ta kara sauri zuwa shashen nasu domin amsa kiran Maama.

 

 

 

1/2/22, 22:47 – Buhainat: *HALIN GIRMA!*

 

©®Hafsat Rano.

 

FREE PAGE

 

(2)

 

 

*****

Takalmin Abban su da ta gani a kofar shiga falon yasa ta sauke ajiyar zuciya, ta bud’e labulen hade da sallama, idonta ya sauka a cikin na Mama da take kallon kofar, tayi mata wani kallo me cike da ma’anoni da ba kowa ne zai gane ba sai ita kadai da ta san manufar sa.

 

“Abba barka da gida.” Tace tana zamewa k’asa

 

“Yawwa Uwata, kina ina haka mamanki na ta neman ki kinsan bata so kici abincin da ya huce ko? Ga yanayi na sanyin nan ba komai ne yake rik’e zafin sa ba.”

 

“Ina wajen Gaji ne.” Tace tana sake yin kasa da kanta.

 

“Toh dai a dinga kula ana abinda ya kamata kinji? Allah yayi muku albarka.”

 

“Amin.” Tace tana mikewa ta shige dakin su da dan sauri tana avoiding idon Maman da ta rakata dashi. D’are-d’are ta tarar da Zeenat a saman gadon tana waya, wuceta tayi ta bud’e jakar kayan ta, ta sauya kayan jikin ta da wasu ta ninke Hijab din sannan ta dawo ta saka abun sallah a k’asa ta zauna ta ciro littafin da akayi musu a islamiya ta soma karantawa a hankali.

 

“Malama kina distracting dina.”

 

Ta zare wayar daga kunnen ta tayi maganar a chunkushe. Banza tayi mata ta cigaba da karatun ta ba tare da ta daina ba.

 

“Mtsww!.” Ta ja dogon tsaki

 

“Baby bari zan kiraka ina zuwa.*

 

“Owk dear, ina jira.”

 

Katse kiran tayi ta zuro kafafunta daidai wajen da Iman din take zaune

 

“Malama duk karatun da kikayi a islamiya be ishe ki ba, sai kinzo kin cika mana kunne mu san kina zuwa makaranta, bayan kowa yasan dalilin da ya saka kika nace da zuwa ko kya samu ya sayyadi ya ce yana so.”

 

Bata tanka mata ba, hakan ya sake kular da Zeenat din, ta saka hannu zata warce littafin tayi saurin janyewa ta mike tsaye,

 

“Wallahi sai dai ki hakura da karatun ko kije chan kiyi, naga ma aiki ne gaban ki kin sani tsabar kinibibi so kike sai ya jiyo ki kina karatu. ”

 

” Kinga duk abinda kike yi bana taba tanka miki, ba wai don ina tsoron ki bane ko wani abu, kawai bana son tashin hankali ne da hayaniya. ”

 

” Toh ki tanka min ma mana, wallahi yanzu zanje na hado ki da Mama.”

 

Bata sake magana ba ta fice daga dakin dan ba karamin aikin Maman bane ta hanata zuwa makarantar na wani lokaci, sai kawai ta zarce kitchen ta tarar da kayan wanke-wanke tuli guda, ta nannade hannun ta tasoma wankewa. Abincin da ta gani a tukunya ta san nata ne, yayi mugun sanyi ita kuma a ka’idar ta bata cin abinci me sanyi, ko ruwan sanyi bata sha a rayuwarta balle yanzu da ake zuga sanyi sosai., gudun ta barshi bata ci ba gobe a hanata yasa ta samu leda ta juye a ciki ta wanke tukunyar ta goge gas da k’asan kitchen din ta gyara komai tsaf sannan ta fito da ledar ta zagaya ta kofar baya ta fita zuwa part din Gaji, ta samu me aikinta ta bata sannan ta dawo ta dauko katifar ta a store ta wuce dakin.

Har lokacin Zeenat bata gama wayar ba, toilet ta wuce ta dauro alwala tazo tayi shafa’i da wutri sannan ta kwanta ta rufe kanta gaba daya da dan yalolon zanin gadon da duk ya yayyage ta gefe da gefe ta kudundune da haka bacci ya dauke ta.

 

Da safe ta tashi kamar kullum tayi ayyukan da suka zama wajibi akanta, kasancewar litinin ce sai ta yi wanka kawai ta wuce shashen Gaji bayan ta tabbatar da fitar Mama tun sassafe, a chan taci abincin ta sannan ta kwanta bacci. Sai da rana ta soma dagawa sannan ta koma ta daura girkin rana,ta gama kafin lokacin tafiya islamiya, ta dauki na Gaji ta kai mata ta sake zama tana jiran lokacin ya cika.

 

“Yaki takwara ta, zo nan.” Gajin tace tana daga zaune a in da take

 

“Me yake damun ki?”

 

“Na’am?”

 

“Fad’a min idan kina da wata matsala ne, na dade ina lura da yanayin rashin walwalar ki, sai dai na kan dauki hakan a matsayin halitta, amma kuma jiya sai abun yazo kaina, na dinga tunanin ko dai kina da wata damuwa ne? Da kika kasa sanar wa wani kika barta a ranki.”

 

“Babu komai Gaji, yanayi na ne a haka amma ni babu abinda yake damuna.”

 

“Kin tabbata.”

 

Daga mata kai tayi tana jin kamar ta saki kuka, ga dama ta samu amma bata da ikon furta wa, toh tace mene ma wai? Hakan ba shi zai hana Mama ta daina muzguna mata ba, Kai tsaye zata kare kanta da zarar Gajin ta tuhume ta karshe kuma abun ya koma kanta kowa ya cigaba da mata kallon marar kirki ko kuma wadda bata san halacci ba. Shiyasa ta zabi yin shiru kawai dan fadar ba zata sauya komai ba, su duka sun yarda da Maman yarda irin ta ban mamaki.

 

“Ai nasan bangaren Hajara baki da wata matsala dama, na dai zata ko damuwa ce dai irin ta rashin maman ki kusa dake, duk da bani da haufi akan kulawar da kika samu iyakar abinda zaki samu kenan ko da ita mahaifiyar taki ce.”

 

“Haka ne.” Tace a kasalance

 

“Yawwa ki dinga dan daurewa kina shiga cikin yan uwanki kinji? Zaman shirun da kike babu dadi.”

 

“In sha Allah zan gyara.”

 

“Yawwa… Haka nake son ji.”

 

“Ya batun yajin aikin nan kuwa? Kun dauko karatu tiryan tiryan yajin aiki ya tsaidaku da tuni wata maganar ake ba wannan ba.”

 

“Wallahi shiru ba labari, muna dai ta addu’a Allah ya sa a daidaita.”

 

“K’asar nan kenan ai, dan karatun ma yanzu nema ake a hana dan talaka yin sa.”

 

“Wallahi.”

 

” Allah yayi mana maganin abinda yafi karfin mu.”

 

” Amin ya Allah!”

 

” Shiyasa nace duk ku fidda mazaje kawai da zarar wadanchan sun tafi kuma azo ayi naku zaman haka nan ba zai yiwu ba.”

 

Shiru tayi gabanta ya fadi, bata son taji ana maganar auren su, gashi kuma taga alamar ba za’a dauki lokaci ba za’a ce su fidda mazaje, ya zatayi da ranta? Da ganin suna makaranta yasa maganar ta lafa amma yanzu yajin aikin da aka tafi da ba’a san ranar dawowa ba ya saka iyayen nasu yanke shawarar suma su aurar dasu kawai sai karasa karatun a dakin su.

Tashi tayi tayi ma Gajin sallama ganin lokaci yayi, taje tayi alwala ta saka Hijab dinta ta fito, a falo ta tarar da Mama tayi saurin tsugunnawa ta gaishe ta

 

” Mama barka da gida.”

 

” Saura idan an tashi ki tsaya shiririta a hanya ko ki tsaya gidan Gaji karki zo kiyi abinda ya dace, jiya kam kinci darajar babanku yana nan.”

 

“In sha Allah.” Tace sannan ta mike ta fice Maman ta rakata da harara.

 

****Sati biyu tsakani aka fara bikin gidan nasu, duk yadda taso gujewa wasu abubuwan amma Maryam bata barta ba, komai idan za’a yi sai ta sakata a ciki, haka kunshi da gyaran kai tare suka je da wata kawar Maryam din.

Alhamis suka fara bikin, a compound din gidan Anty Mabruka sukayi bridal shower iya su da kawayen su, juma’ah akayi kamu asabar aka daura aure hade da yini, lahadi aka kai kowacce gidan ta.

Ranar litinin suka tashi gidan da sauran bakin da basu riga sun tafi ba wanda yawanci dangin Gaji ne, a babban kitchen din gidan suka hadu aka hada breakfast Masa da miyar taushe, har rana tayi sosai basu kammala ba hakan ya sake haifar mata da wata irin gajiya bayan wadda take fama da ita, tasan halin Mama sarai idan ta makale taki fitowa ayi aikin da ita duk da akwai masu yi din amma dolen ta ne ta fito, duk da hakan ba karamin taimaka mata yayi ba wajen gogewa da kalolin girke-girke mabanbanta. Sannan uwa uba girkin mutane da yawa wanda ba kowa bane ya iya.

Da saurin ta, ta karasa dakin su, ta kwanta a gefen gadon saboda wani irin sanyi da take ji alamun zazzabi ne ke neman rafke ta, rawar sanyi ta fara hakoranta suka shiga haduwa waje daya, ta saka hannu da k’yar ta jawo bargon Zeenat din ta lulluba.

Shigowar ta kenan ta tsaya daga kofar

 

“Kut! Lallai ma.” Tace tana karasawa ciki, ta fuzge bargon da karfi

 

“Dan Allah zee ki kyale ni bani da lafiya.” Tace muryar ta chan ciki. Shiru Zeenat din tayi tana kallon ta, sai kuma ta sakar mata bargon ta juya ta fice daga dakin. Har dare zazzabin be sake ta ba, babu kuma wanda yazo neman ta. Tayi tunanin Zeenat din zata fad’a wa Maman ne duk da bata saka rai ba, amma jin shirun ya tabbatar mata da ta fad’a mata dan da ba haka ba da tuni Maman ta turo neman ta akan wani aikin.

Wajajen Tara Zeenat ta dawo dakin, ta kalle ta a zaune saman abun sallah ta kudundune, juyawa tayi ta fita ta dawo da paracetamol a hannun ta da ruwa ta mika mata. Karba tayi da sauri tayi mata godiya, bata amsa ba ta sake fita sai gata ta dawo da katifar Iman din, ta shinfid’a mata sannan ta dauko bargon ta, ta dora mata akai ta haye gadon ta kwanta ta rufe idon ta. Sosai Iman taji dadi a ranta, ko ba komai tayi mata abinda bata taba ba, tashi tayi da k’yar ta lallaba ta fita kitchen ta hado tea sannan ta dawo ta sha da k’yar ta sake komawa ta kwanta ta kudundune.

Kwanan ta uku a haka, har ta soma samun karfin jikinta, Mama ta shigo sau daya ta bata anti-malaria shima dan tasan Abban zai iya tambaya ne, shima da tasan zai shigo ya duba ta ne, tana jin sanda take ce masa sun je asibiti ma kuma jikin da sauki.

 

***Karamin daki ne da yafi kama da shago, katifa ce karama irin ta yan boarding school sai jakar kayan sa a gefe, bayan haka babu komai a dakin sai wani dogon mudubi dake rataye jikin bangon dakin.

Tsaye yake a gaban mudubin yana duba fuskar sa dake cike da kasumba ko ina har baka iya ganin komai na fuskar tasa sosai, kansa rufe yake da katuwar hular sanyi, ya nannade wuyan sa da abu, kafar sa da hannun sa duk rufe suke cikin hular sanyi, idan ka cire fuskar sa da itama kasumbar bata wani bari a ganta sosai, babu wani abu na jikin sa dake a bud’e. Kayan jikin sa a wanke suke tsaf, sai dai sun tsufa sosai, har da wata yar bula a jikin hannun rigar.

A ko da yaushe yakan tsaya ne a daidai hanyar da take hucewa idan ta dawo daga islamiyya, amma kuma kwana biyu ya rabu da ganin ta, shiyasa ya yanke shawarar zuwa gida duk da yasan ba tsarar sa bace amma zai gwada sa’ar sa.

 

 

 

 

Hafsat Rano

 

3

 

****

Tsaye yayi jikin gate din gidan yana kare masa kallo, tunanin ta yadda zai fara shiga yake musamman da ba sanin sunan ta yayi ba, ya dai saka mata suna da zuciyar sa kuma be taba yunkurin tsaidata balle yaji sunan ta ba.

Lekowa maigadin gidan yayi, ganin mutum a tsaye yasa shi fitowa gaba daya

 

“Sannu.” Yace masa yana kokarin daidaita muryar sa

 

“Yawwa sannu, wa kake nema?” Maigadin ya tambaye shi yana kare masa kallon cikin rashin sani.

 

Nan fa ake yinta, shiru yayi kamar me nazari shi kuma maigadin ya kafe shi da ido yana son jin abinda ya kawo shi.

 

“Am… Amm nazo wajen…”

 

“Malam Iliya.” Zeenat dake fitowa ta kirashi tana leko wa.

 

“Na’am ranki ya dade!”

 

“Siyo min kati na 500 kayi sauri dan Allah.”

 

“Yanzu kuwa, ga wani bako nan bansan wajen wa yazo ba dai kin tambaye shi.”

 

Yayi gaba, kallon sa tayi tun daga sama har kasa a wulakanci ta yatsine baki tace

 

“Wa kake nema kai kuma Malam?”

 

“Yar uwarki nake nema dan Allah, wata me zuwa islamiya kasan layin nan doguwa haka fara.”

 

“Waye kai a wajen ta?”

 

Kallon cikin ido yayi mata, ta ja tsaki tana juya fuskar ta

 

“Ban fiye son kallo ba Malam, ka shigo ciki bari na tura maka ita dama ai sai dai ita din…”

 

Gaba tayi tana cigaba da sababi

 

“A kaf gidan nan wa zai kwaso mutum irin wannman dan Allah! Ji shi kamar wani mahaukaci.”

 

Sai ta kwashe da dariya tana sake daga kafa.

 

A kwance ta tarar da Iman tana danna wayar ta da ba kasafai ta cika wani amfani da ita ba, yanzun ma wani labari ne yaja hankalin ta a Facebook take karantawa.

 

” Kina da babban bako a waje da galleliyar ranar nan.”

 

” Waye?”

 

” Idan kika je idon ki zai gane miki shi.”

 

” Owk.”

 

Tace tana tashi zaune, har yanzu bata gama dawowa daidai ba amma haka ta karfafa jikinta tayi ayyukan ta. Hijab ta saka madaidaici akan doguwar rigar jikinta ta fito. Daga chan hanyar gate ta hange shi a tsaye ya rataye hannayen sa a bayan sa, kansa a kasa yana wasa da kafar sa.

Dogo ne na ajin farko, jikin sa ko ina a murje babu alamun rama ko kad’an, yanayin shigar sa bata dace da tsarin zubin halittar sa ba, kafin ta karasa ta gama ayyana shi a ranta. Da sallama ta isa, ya dago da sauri a lokaci daya kwayar idon sa ta sauka a cikin ta ta, gabanta ne yayi masifar faduwa, tayi saurin janye idon ta, ta russuna kad’an tace

 

“Ina wuni?” Lumshe idon sa yayi ya bud’e, fuskar sa dake cike da kasumba ta dan yi fadi alamun farin ciki, ya tattaro dukkan nutsuwa da jaruntar sa yayi gyaran murya yace

 

“Kina lafiya?”

 

“Alhamdulillah.” Tace a gajarce ta matsa wajen wasu kujerun roba guda biyu ta dauko daya ta kawo masa.

 

“Bismillah zauna kana ta tsaiwa.”

 

Hannun sa ya dora a saman kujerar ta kalli hannun yayi saurin janye shi ya zauna sannan yace

 

“Kefa?”

 

Wani dan tudu a wajen ta nuna masa da hannu, ta zauna akai tana jin duk ta takura ganin yadda yake bin ta da kallo da wasu irin idanun sa da suka sake shiga ciki sosai.

 

“Na same ki lafiya? Ya gida yasu Mama da yan uwa?”

 

“Lafiya lou Alhamdulillah.”

 

“Ban gane waye ba amma?”

 

“Me sonki ne, me kaunar ki da son duk wani farin cikin ki, yan kwanakin nan da na dauka banga wucewar ki ba, sun zame min kwanaki mafiya muni a rayuwa ta. Na kan zauna a duk yini ina dakon wucewarki, ban taba yunkurin yi miki magana ba, sai dai zuciya ta, ta gaza dauka har sai dana biyo bayanki, ina fatan ban takura miki ba?”

 

Girgiza kai tayi tana jin wani bawai, wai ita ake karantawa wannan kalaman, idan har taji daidai wato ya dade yana bibiyar ta, bata ma sani ba.

 

” Kinyi shiru!” Yace yana gyara zaman sa

 

Shirun ta sake yi dan bata san me zata ce masa ba.

 

” Nasan dama karambani ne irin nawa, ban kai ajin ko da me wanke miki takalmi bane, kiyi hakuri idan nayi miki shishigi a rayuwar ki.”

 

” A ah wallahi, ba haka bane ba, a kalla mutumin da yace yana son ka ai yafi makiyinka, nagode sosai da soyayyar ka gareni.”  Tace da sauri sannan tayi murmushi, ji yayi kamar zuciyar sa zata fito daga kirjin sa, ya danne sosai ya maida mata murnushin

 

“Nagode Nuryyy… Nagode sosai.”

 

Shiru ya biyo baya, ta dinga wasa da gefen Hijab dinta shi kuma yana satar kallon ta. Nutsuwarta tafi komai tafiya dashi.

 

“Bari na wuce.”

 

Da sauri ta mike kamar me jiran kad’an,

 

“Ka gaida gida.” Tace tana saurin yin gaba

 

“Ko zan samu number waya dan Allah?”

 

Tsayawa tayi ta mika masa hannu, ya shafa aljihun sa dukka

 

“Kinga garin sauri na manta wayar a daki, amma zan rik’e fad’a min.”

 

“Ok .” Tace ta karanto masa,

 

” Nagode sunana Muhammad.”

 

” Fatima, ka gaida gida.”

 

Ta juya ta barshi a tsaye a wajen. Sake maimaita sunan Fatiman yayi, ya saki murmushi a hankali sannan ya juya ya fice daga gidan.

 

 

***A zaune a falo ta tarar da Mama na waya, zata wuce ta tsaida ta da hannu ta cigaba da wayar ta

 

” Ba za dai ka bar maganar nan ba ko Khalil? Toh shikenan sai kazo din dai ma sake tattaunata, idan yaso ko a dangi ne sai ka duba sosai ba za’a rasa ba ai.”

 

Amsa ya bata daga bangaren sa, ta ja tsaki tace

 

” Matsalata da kai kafiya wallahi toh sai anjima, sai kazo din.”

 

Ta kashe wayar ta dangwarar da ita a gefen ta

 

” Na rasa shegen taurin kai irin na Khalil wallahi, sam baya kaunar ya ganni cikin farin ciki, mtsw.”

 

Ta sake jan tsaki a karo na ba adadi.

 

” Daga ina kike?”ta jeho mata tambayar bayan ta riga ta san inda take.

 

” Wani ne yazo dama.”

 

” Waye shi?”

 

” Bansan shi ba nima, wai a bayan layi yake.”

 

” Toh kina jina? Idan zaki yiwa kanki kiyamullaili ki rik’e shi hannu bibiyu toh, idan kuma kika yi wasarairai da shi shima ya gudu kamar sauran, sai ki zauna muyi ta jerawa a gidan nan,tunda dai bakin hali ya hana samarin zama kowa yazo sai ya tafi.”

 

Bata dago ba, bata kuma ce kala ba, tana jin Maman tana kuma ajiye kowacce magana a mazaunin da ya dace, sai da ta gama yi mata cin fuskar sanann tace

 

” Khalil zai zo gobe, babu ruwanki dashi da shiga harkar sa, ko falo bana so naga kina kaiwa da komowa har ya tafi, zan fi so ki tattara ki koma wajen Gaji da zama aikin ma na yafe miki, idan ya gama kwanakin ya tafi shikenan, bana son daukar magana dan shi ba kunya magana yake ji ba, kinji dai na gaya miki.”

 

” In sha Allah.”

 

” Jeki.”

 

Tashi tayi ta bita da kallo ranta na tafasa, da gaske take kishi da ita dukda bata zauna da mahaifiyar ta ba, amma duk sanda ta kalle ta sai ta tuno abinda ya faru.

 

 

****A guje suka taso ganin ya fito, ya nufi wajen da jerin motocin ke fake suna jiran sa, ransa a bace yake da kiran amma bashi da ikon kin amsawa, dole ya ajiye shirin sa a gefe ya kirawo su domin ba zai taba yarda da shigar masa shirin sa ba. Shiyasa su kansu basu da yakini ko masaniyar komai, dan ya tabbatar da zasu taimaka wajen lalata masa shirin sa. Dan su din basu da ikon kansu sai abinda aka gindaya musu.

 

Bud’e masa bayan motar daya daga ciki yayi, ya russuna kad’an sannan yace

 

 

“We are very sorry sir!”

 

Be tanka masa ba, ya shige cikin motar ya jingina bayan sa da kujerar ya lumshe idon sa.

 

“Oga Main house zamu?” Yayi tambayar yana tada motar

 

 

“Lamido Crescent!” Yace yana sake rufe idon sa.

 

Chan suka wuce direct, suna isa ya fito ya shige ciki, tun daga falo ya fara wurgi da kayan jikin sa, ya rage daga shi sai boxer da farar singlet, kallon kansa yayi a jikin tangamemen mudubin dake tsaye kikam a falon, ya juya ya sake juyawa sannan ya wuce zuwa cikin bedroom din sa.

Wanka ya fara yi a gurguje sannan ya fito ya shirya cikin shigar babbar riga da jamfa da wando farare kal, sau cikin sa ya jawo ya ajiye a gefe ya fara saka farar socks a ciki sannan ya saka ya fito rik’e da babbar rigar a hannu.

Zama yayi sannan ya danna remote din kofar, da sauri suka shigo su biyu, ya mik’a wa daya babbar rigar, karba yayi ya taimaka masa ya saka sannan ya dauki abubuwan da yasan zai bukata ya fita dasu.

 

“Ka zauna anan zan kiraka da zarar na sauka.”

 

Yace da dayan sannan ya tashi ya fice cikin takun da yafi kama dana jinin sarauta.

Motoci biyu ne suka fita daga gidan, shi yana cikin daya su kuma suna bin sa a daya har zuwa airport.

Muhammad Ahmad Santuraki

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment