Littafan Hausa Novels

Haduwar Facebook Hausa Novels Complete

Written by Hausa_Novels

Haduwar Facebook Hausa Novels Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

HADUWAR FACEBOOK {part 3} By Adam so

 

Idan baku manta ba na tsaya a wajen da Nayiwa Fatima Wakar birthday party har ta turo mini kudi Wanda har Saida na mike tsaye Ina daga zaune saboda ganin yawan kudin.

Prince Salman Hausa Novel Complete

take na kamu da wani sabon farinciki tare da furta kalmar Alhamdulillahi. Amma ta dayan bangaren Kuma yawan tinani Sai ya Karu a zuciyata domin nasan kudin da Fatima ta bani ya zarce na Wakar da tasani nayi Mata. haka na tsaya Ina jira nasan fatimah zata Kira ni ko Dan tayimin fatan Alkhairi Kamar yadda ta saba yimin. Jim kadan Fatima Bata Kira ba Sai na yanke shawarar na Kira ta nayi Mata godiya bisa Abun Alkhairin da tayimin

 

ai kuwa Ina Kira ta daga tare da fadin fatan Alkhairi nake yiwa jarumi Mai hali na kirki. Nace Mata na gode da Abin Alkhairi ranki ya dade naga sakonki na gode da hidima. tace Babu komai Adam Muna tare na Amsa da cewar insha Allahu. Haka ta fara bani labari akan Yan gidan su tun daga kan mahaifan ta har kannen ta kuma tace saura sati daya1 zata dawo gida kano nace to Allah ya kawo ta lfy ta Amsa da Ameen.

 

Fatima ta cigaba da cemin idan Babu damuwa ina bukatar zuwanka wajen Birthday Dina domin Zan so ka hau Wakar da kayi a gaban yan gidan mu domin Ina so na nuna ka a wajen yan uwana. nace Babu matsala insha Allahu. Haka dai ta cigaba da bani lbr cikin wata irin murya Mai dadin sauraro.

 

Bayan mun Gama wayar ne naji wani irin sabon yanayi a tare Dani Nayiwa Allah godiya tabbas fatimah Alkhairi ce a gareni tun da ta shigo rayuwta na samu sabuwar rayuwa tin daga Nan fatimah kullum Sai ta turomin da sakon barka da safiya. ga Kuma Kati a waya tana turo mini har Bata gajiya

 

Bayan wasu Yan kwanaki fatimah ta Kira ni a waya ta shaida mini gobe zata dawo daga Abuja zata shigo kano tace idan ta shigo zata neme ni domin zuwa wajen Birthday dinta domin na hau Wakar da nayi Mata

 

MU HADU A KASHI NA HUDU 4 ZAKUJI YADDA MUKAYI DA ITA

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment