Littafan Hausa Novels

Gurguwar Tafiya Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Gurguwar Tafiya Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

๐—š๐—จ๐—ฅ๐—š๐—จ๐—ช๐—”๐—ฅ ๐—ง๐—”๐—™๐—œ๐—ฌ๐—”

 

 

๐—Ÿ๐—”๐—•๐—”๐—ฅ๐—œ/๐—ฅ๐—จ๐—•๐—จ๐—ง๐—”๐—ช๐—”

 

๐—•๐—”๐——๐—”๐—ช๐—˜๐—˜๐—ฌ๐—˜๐—ฅ๐—› ๐—”๐—›๐— ๐—”๐—— ๐— ๐—จ๐—”’๐—ญ๐—จ

(๐—ฅ๐—จ๐—•๐—•๐—ฌ)

 

 

 

 

** *ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*

 

*_____________________________________*

 

*๐ŸŒˆ๐Ÿ‡ฐAINUWA ๐Ÿ‡ผRITER’Sโœ๐Ÿผ*

*๐Ÿ‡ฆSSOCIATION๐Ÿค๐Ÿป*

”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’

 

 

**

 

 

 

 

 

๐™ถ๐™ฐ๐™ฑ๐™ฐ๐šƒ๐™ฐ๐š๐š†๐™ฐ

๐™ณ๐šŠ ๐šœ๐šž๐š—๐šŠ๐š— ๐™ฐ๐š•๐š•๐šŠ๐š‘ ๐š–๐šŠ๐š’ ๐š›๐šŠ๐š‘๐šŠ๐š–๐šŠ, ๐š–๐šŠ๐š’ ๐š“๐š’๐š— ฦ™๐šŠ๐š’.

๐™ณ๐šž๐š”๐š”๐šŠ๐š— ๐šข๐šŠ๐š‹๐š˜ ๐š๐šŠ ๐š”๐š’๐š›๐šŠ๐š›๐š’ ๐š๐šŠ๐š–๐š’ ๐š๐šŠ ๐š๐š˜๐š๐š’๐šข๐šŠ ๐šœ๐šž๐š— ๐š๐šŠ๐š‹๐š‹๐šŠ๐š๐šŠ ๐š๐šŠ ๐™ฐ๐š•๐š•๐šŠ๐š‘ ๐š–๐šŠ๐š๐šŠ๐šž๐š”๐šŠ๐š”๐š’๐š— ๐šœ๐šŠ๐š›๐š”๐š’ ๐š–๐šŠ๐š’ ๐š”๐š˜๐š ๐šŠ ๐š–๐šŠ๐š’ ๐š”๐š˜๐š–๐šŠ๐š’, ๐š๐šœ๐š’๐š›๐šŠ ๐š๐šŠ ๐šŠ๐š–๐š’๐š—๐šŒ๐š’ ๐™ฐ๐š•๐š•๐šŠ๐š‘ ๐šœ๐šž ฦ™๐šŠ๐š›๐šŠ ๐š๐šŠ๐š‹๐š‹๐šŠ๐š๐šŠ ๐š๐šŠ ๐™ฐ๐š—๐š—๐šŠ๐š‹๐š’ ๐™ผ๐šž๐š‘๐šŠ๐š–๐š–๐šŠ๐š (๐š‚.๐™ฐ.๐š†), ๐š๐šŠ ๐š’๐šข๐šŠ๐š•๐šŠ๐š— ๐šœ๐šŠ, ๐š๐šŠ ๐šœ๐šŠ๐š‘๐šŠ๐š‹๐š‹๐šŠ๐š— ๐šœ๐šŠ, ๐š๐šŠ ๐š ๐šŠ๐š๐šŠ๐š—๐š๐šŠ ๐šœ๐šž๐š”๐šŠ ๐š๐šŠ๐š‹๐šŠ ๐šŒ๐šŽ ๐š–๐šž, ๐™ฐ๐š•๐š•๐šŠ๐š‘ ๐š”๐šŠ ฦ™๐šŠ๐š›๐šŠ ๐š–๐šŠ๐š—๐šŠ ๐š”๐šž๐šœ๐šŠ๐š—๐šŒ๐š’ ๐š๐šŠ ๐šœ๐š˜๐šข๐šŠ๐šข๐šข๐šŠ๐š› ๐™ผ๐šŠ๐š—๐šฃ๐š˜๐š— ๐™ฐ๐š•๐š•๐šŠ๐š‘ ๐š‚๐šŠ๐š•๐š•๐šŠ๐š•๐š•๐šŠ๐š‘๐šž ๐™ฐ๐š•๐šŠ๐š’๐š‘๐š’ ๐š†๐šŠ๐šœ๐šŠ๐š•๐š•๐šŠ๐š–.

 

 

 

Yankan Baya Hausa Novel Complete

๐™น๐š’๐š—-๐š“๐š’๐š—๐šŠ

๐™น๐š’๐š—-๐š“๐š’๐š—๐šŠ ๐š๐šŠ ๐š–๐šž๐šœ๐šŠ๐š–๐š–๐šŠ๐š— ๐š๐šŠ ๐š’๐šข๐šŠ๐šข๐šŽ ๐š—๐šŠ, ๐™ฐ๐š•๐š•๐šŠ๐š‘ ๐šข๐šŠ ๐šœ๐šŠ๐š”๐šŠ ๐š–๐šž๐š”๐šž ๐š๐šŠ ๐šŠ๐š•๐š”๐š‘๐šŠ๐š’๐š›๐š’, ๐™ฐ๐š•๐š•๐šŠ๐š‘ ๐šข๐šŠ ๐š–๐šž๐š”๐šž ๐šœ๐šŠ๐š”๐šŠ๐š–๐šŠ๐š”๐š˜ ๐š๐šŠ ๐š๐š’๐š๐šŠ๐š— ๐šŠ๐š•๐š“๐šŠ๐š—๐š—๐šŠ๐š‘ ๐š›๐šŠ๐š—๐šŠ๐š› ๐š๐šŠ ๐š‹๐šŠ๐š‹๐šž ๐š–๐šŠ๐š’ ๐šœ๐šŠ๐š”๐šŠ๐š–๐šŠ๐š”๐š˜ ๐šœ๐šŠ๐š’ ๐šœ๐š‘๐š’.

๐™ฑ๐šŠ ๐šฃ๐šŠ๐š— ๐š๐šŠษ“๐šŠ ๐š ๐šž๐šŒ๐šŽ๐š ๐šŠ ๐š‹๐šŠ ๐š๐šŠ๐š›๐šŽ ๐š๐šŠ n๐šŠ ๐š–๐š’ฦ™๐šŠ ๐š“๐š’๐š—-๐š“๐š’๐š—๐šŠ ๐š๐šŠ ๐š–๐šž๐šœ๐šŠ๐š–๐š–๐šŠ๐š— ๐š๐šŠ ๐šข๐šŠ๐š—’๐šž๐š ๐šŠ๐š—๐šŠ n๐šŠ, ๐™ฐ๐š•๐š•๐šŠ๐š‘ ๐šข๐šŠ ฦ™๐šŠ๐š›๐šŠ ๐š–๐šŠ๐š—๐šŠ ๐šฃ๐šž๐š–๐šž๐š—๐šŒ๐š’ ๐šƒ๐šŠ๐š›๐šŽ ๐™ณ๐šŠ ๐š”๐š ๐šŠ๐š—๐šŒ๐š’๐šข๐šŠ๐š› ๐š‘๐šŠ๐š—๐š”๐šŠ๐š•๐š’ ๐šŠ ๐š”๐š˜ ๐šข๐šŠ๐šž๐šœ๐š‘๐šŽ .

 

 

๐™น๐šŠ๐š— ๐š‘๐šŠ๐š—๐š”๐šŠ๐š•๐š’

๐š†๐šŠ๐š—๐š—๐šŠ๐š— ๐š•๐š’๐š๐š๐šŠ๐š๐š’๐š— ฦ™๐š’๐š›ฦ™๐š’๐š›๐šŠ๐š›๐šŽ๐š— ๐š•๐šŠ๐š‹๐šŠ๐š›๐š’ ๐š—๐šŽ, ๐š‹๐šŠ๐š— ๐šข๐š’ ๐šœ๐š‘๐š’ ษ—๐šŠ๐š— ๐šŒ๐š’๐š— ๐šฃ๐šŠ๐š›๐šŠ๐š๐š’๐š— ๐š ๐šŠ๐š—๐š’ ๐š”๐š˜ ๐š ๐šŠ๐š๐šŠ ๐š‹๐šŠ, ๐š’๐š๐šŠ๐š— ๐šข๐šŠ ๐šข๐š’ ๐š๐šŠ๐š’๐š๐šŠ๐š’ ๐š๐šŠ ๐š‘๐šŠ๐š•๐š’๐š— ๐š”๐š’/๐š”๐šŠ ๐š๐š˜ ๐šŠ๐š”๐šŠ๐šœ๐š’ ๐šŠ๐š”๐šŠ ๐šœ๐šŠ๐š–๐šž, ๐š”๐š˜๐š–๐šŠ๐š’ ๐š—๐šŠ ๐šŒ๐š’๐š”๐š’๐š— ๐š•๐šŠ๐š‹๐šŠ๐š›๐š’๐š— ฦ™๐š’๐š›ฦ™๐š’๐š›๐šŠ ๐š๐šŠ ๐šŒ๐šŽ, ๐šœ๐šŠ๐š’ ๐šŠ๐šข๐š’ ฦ™๐š˜ฦ™๐šŠ๐š›๐š’๐š— ๐š๐šข๐šŠ๐š›๐šŠ๐š ๐šŠ, ๐™ฐ๐š•๐š•๐šŠ๐š‘ ๐šข๐šŠ ๐š๐šŠ๐š๐šŠ๐š› ๐š๐šŠ ๐š–๐šž ๐š”๐šž๐š–๐šŠ ๐šข๐šŠ ๐šœ๐š‘๐š’๐š›๐šข๐šŠ๐š› ๐š๐šŠ ๐š–๐šž ๐š‘๐šŠ๐š—๐šข๐šŠ ๐š–๐šŠ๐š๐šŠ๐š’๐š๐šŠ๐š’๐šŒ๐š’๐šข๐šŠ.

 

๐™ฑ๐šŠ๐š— ๐šข๐šŠ๐š๐š๐šŠ ๐š ๐šŠ๐š—๐š’ ๐š”๐š˜ ๐š ๐šŠ๐š๐šŠ ๐šข๐šŠ ๐š“๐šž๐šข๐šŠ ๐š–๐š’๐š— ๐š ๐šŠ๐š—๐š—๐šŠ๐š— ๐š•๐šŠ๐š‹๐šŠ๐š›๐š’๐š— ๐š‹๐šŠ , ๐š”๐š˜ ๐šข๐š’๐š— ๐šŠ๐š–๐š๐šŠ๐š—๐š’ ๐š๐šŠ ๐šœ๐š‘๐š’ ๐š๐šŠ ๐š”๐š˜ ๐š ๐šŠ๐šŒ๐šŒ๐šŽ ๐š’๐š›๐š’๐š— ๐š‘๐šŠ๐š—๐šข๐šŠ, ๐š‹๐šŠ ๐š๐šŠ๐š›๐šŽ ๐š๐šŠ ๐š’๐šฃ๐š’๐š—๐š’ ๐š—๐šŠ ๐š‹๐šŠ, ๐šŠ ๐š”๐š’๐šข๐šŠ๐šข๐šŽ.

 

 

 

 

๐—ž๐˜‚ ๐—บ๐—ฎ๐˜๐˜€๐—ผ ๐—ธ๐˜‚ ๐—ท๐—ถ ๐Ÿค—

 

๐—ช๐—ฎ๐—ป๐—ป๐—ฎ๐—ป ๐—น๐—ถ๐˜๐˜๐—ฎ๐—ณ๐—ถ๐—ป ๐˜†๐—ฎ๐—ป๐—ฎ ษ—๐—ฎ๐˜‚๐—ธ๐—ฒ ๐—ฑ๐—ฎ ๐˜€๐—ฎ๐—น๐—ผ ๐—ป๐—ฎ ๐—ฏ๐—ฎ๐—ป ๐—บ๐—ฎ๐—บ๐—ฎ๐—ธ๐—ถ, ๐˜€๐—ฎ๐—น๐—ผ๐—ป ๐˜€๐—ฎ ๐—ฑ๐—ฎ ๐˜๐˜€๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ๐—ป ๐˜€๐—ฎ ๐˜†๐—ฎ ๐—ฏ๐—ฎ๐—ป๐—ฏ๐—ฎ๐—ป๐˜๐—ฎ, ๐—ฐ๐—ถ๐—ธ๐—ฒ ๐˜†๐—ฎ๐—ธ๐—ฒ ๐—ฑ๐—ฎ ๐˜๐—ฎ๐˜‚๐˜€๐—ฎ๐˜†๐—ถ, ๐˜‡๐—ฎ๐˜‡๐—ฎ๐—ณ๐—ฎ๐—ฟ ๐˜€๐—ผ๐˜†๐—ฎ๐˜†๐˜†๐—ฎ, ฦ™๐—ถ๐˜†๐—ฎ๐˜†๐—ฎ,๐—ฟ๐—ฎ๐˜†๐˜‚๐˜„๐—ฎ๐—ฟ ๐—ฎ๐—ฟ๐˜‡๐—ถ๐—ธ๐—ถ ๐—ฑ๐—ฎ ๐˜๐—ฎ๐—น๐—ฎ๐˜‚๐—ฐ๐—ถ, ๐—ด๐—ฎ ๐˜€๐—ฎ๐—ฟ๐—ธ๐—ฎ๐—ธ๐—ถ๐˜†๐—ฎ ๐—ธ๐˜‚๐—บ๐—ฎ ๐—บ๐—ฎ๐—ถ ๐˜„๐˜‚๐˜†๐—ฎ๐—ป ๐˜„๐—ฎ๐—ฟ๐˜„๐—ฎ๐—ฟ๐—ฒ๐˜„๐—ฎ, ๐—ž๐—ฎ๐—ฑ๐—ฎ ๐—ฑ๐—ฎ๐—ถ k๐˜‚ ๐—ฏ๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ ๐—ฎ ๐—ฏ๐—ฎ๐—ธ๐˜‚ ๐—น๐—ฎ๐—ฏ๐—ฎ๐—ฟ๐—ถ, ๐—ธ๐˜‚ ๐—ฏ๐—ถ๐—ป๐—ถ ๐˜€๐—ฎ๐—ป๐—ป๐˜‚ ๐—ฎ ๐—ต๐—ฎ๐—ป๐—ธ๐—ฎ๐—น๐—ถ ๐—ฑ๐—ฎ๐—ป ๐˜„๐—ฎ๐—ฟ๐˜„๐—ฎ๐—ฟ๐—ฒ ๐—บ๐˜‚๐—ธ๐˜‚ ๐—ฑ๐—ฎ๐—ธ๐—ถ -๐—ฑ๐—ฎ๐—ธ๐—ถ .

 

 

๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฅ

 

๐Ÿ…ฟ๐Ÿ…ฐ๐Ÿ…ถ๐Ÿ…ด 1 & 2

 

Tafi minti talatin a durkushe a wajan da suke wanke -wanke,wasa ta ke yi da kumfar da ta kaษ—a da wani ษ—an ฦ™aramin kofi da ke hannun ta, haka ta ke ษ—aga kumfar kamar wacce ta samu shayi mai kauri, yayin da zuciyarta bata tattare da ita,wasa kawai ta ke da kumfar amma hankalin ta da tunanin ta sun yi nisa yayin da zuciyarta ta cunkushe da tunane-tunane marasa amfani ษ“alle makama.

Saukar ludayi taji a gadon bayanta wanda ya sa ta miฦ™ewa a kiษ—ime ba tare da ta shirya wa hakan ba abinka da shgwaษ“aษ“ษ“iya tuni har kwalla ta cika idanun ta, Mahaifiyar ta ce ta kalle ta cike da faษ—a tana faษ—in

“Ke wai Umaimah wacce irin yarinya ce da ba kya jin magana? Kullum akan wanke -wanke anyi ta fama da ke kamar wata yarinyar yar shekara goma? To wallahi na baki minti goma ki kammala inba haka ba… ” Kwafa tayi ba tare da ta karasa maganar da za ta yi ba ta wuce, Umaimah bata iya cewa komai ba ta tsugunna ta fara wanke -wanken kamar zata fashe da kuka dan ita a rayuwar ta babu abinda ta tsana sama da aiki to gwara ma tayi shara sau dubu da tayi wanke -wanke, tana zumษ“ura baฦ™i dai har ta samu ta kammala domin tafi kowa sanin halin Mahaifiyar ta, duk da tsananin son da ta ke mata hakan baya hana ta hukunta ta indai ta aikata laifi ko kuma tayi ma ta faษ—a, hakan ya sa ta ke shakkar Mahaifiyar ta sossai.

Cikin sauri ta share wajan da ta yi aikin tare da tattara kwanukan cikin kwando ta kai cikin ษ—an madaidaicin kicin ษ—in su, zuba kwanukan ta ke yi cikin kwandon tana mita ฦ™asa -ฦ™asa

“Dubi yadda kwandon nan ya fashe dan Allah, kaiii wlh talauci bai yi ba, Allah ma yaga zuciyata a bisa dole nake iya rayuwa a gidan nan dan babu yadda zan yi ne kawai,amma komai baya min kyau, mtseww” ta karashe zancen da jan doguwar tsuka ta fice a kitchen din domin kullum sai ranta ya ษ“aci, a nata ganin tafi ฦ™arfin wannan rayuwar,kamata ya yi ace kamar ita tana daga zaune tana bama masu aiki umarni,tafi so ace komai yi ma ta ake yi tana daga zaune, irin rayuwar masu kuษ—i take buri,bata son talauci ko kaษ—an, ko da ta fice a kitchen ษ—in wani daฦ™i ta nufa tare da kwanciyar a wata yar yololuwar katifa tana faษ—in

 

“Wash Allah!! Na gaji wlh, Allah ka raba ni da yin wanke -wanken nan, na san duk randa nayi sati ban yi aiki ba sai an kalle ni an sake kallo saboda kyan da zan ฦ™ara yi” a bayyane ta ke maganar ta cikin nuna gajiyawa da aikin da ta ke yi a gidan nasu kullum, wayar ta kirar goinee P32 ta dauko ta fara dannawa,gaba daya wayar ta fice a hayyacin ta, har ga Allah tana jin kunyar shiga mutane da wannan wayar musamman ganin kusan ko wacce yarinya iPhone 13 pro max ne a hannun ta idan ta leฦ™a shafin sada zumunta, harta kawayen ta tampatsa-tampatsan wayoyi ne da su…

 

“Umaimaaah” Mama ta kwalla kiran ta da karfi wanda hakan ya sa ta jefar da wayar da ta ke dannawa a gefen katifa ta fito waje tana bata rai kamar za ta kurma ihu, a taskar gida ta tarar da Mama tana kokarin daka yajin barkono, cikin tsawa Mama ta ce :

 

“Uban waye zai dora miki abincin rana naga kin koma ษ—aki kin kwanta, baki da aiki sai kwanciya? Ke dai ki kwanta dai kamar manja, to Allah ya shirya “, Ba tare da Umaimah tace komai ba ta juya ta tafi wajan kitchen, taliya yar murji taci karo da shi a wata yar roba a ฦ™ofar shiga kitchen ษ—in hakan yasa ta ja wani dogon tsaki “mtseww” ba tare da ta shirya ba, kunkuni ta shiga yi tana tura baki gaba tana faษ—in “Ni ni wallahi na gaji da cin taliyar hausa, haba ayi ta cin fulawa kamar me, salon mutum ya yi ta narka ฦ™iba ta ba gaira ba dalili, ni dai gaskiya na gaji” cike da ฦ™osawa da gajiyawa ta ฦ™arashe fadin haka tare da figar robar tayi cikin kitchen ษ—in ta fara kokuwar haษ—a icen da zata dafa abincin da shi.

Tana gama dafa taliyar ta ษ—ora ruwan zafi a kan gaushin da ya rage, fitowa ta yi ฦ™ofar kitchen ษ—in ta ja kujera yar tsugunno ta zauna gami da share zufa, gaba ษ—aya idanun ta sun chanza launi saboda hayaฦ™in da ta shaฦ™a, sai murza idanu ta ke yi tana cewa a fili

 

” Ni wallahi ficewa ma zan yi a gidan nan, sabuwar Atamphar nan da na dinka zan dauka na kira Musa ya kaini ta anguwar G.R.A ya min hotuna na samu na status kwana biyu”

Tana gama fadin haka ta saki murmushi mai sauti wanda ya bayyana annurin dake fuskar ta karara, miฦ™ewa ta yi ta koma cikin daki da yake mallakin ta, tana ci-gaba da saฦ™a irin hotunan da Musa zai mata na kece raini da ษ—aukar hankalin masu bibiyar ta a shafukan sada zumunta.

 

 

Suhail ne ke bacci hankali kwance, daga shi sai singlet da shorts, ga sanyin AC yana ratsa shi ta ko ina, daga yadda numfashin shi ya ke sauka zaka fahimci lallai ba ฦ™aramin jin ษ—adin baccin ya ke yi ba, cikin magagin bacci yaji karar wayar shi, ba shiri ya miko hannu ya ษ—auka gami da kashe ta gaba ษ—aya,domin baya son abinda zai takura mai ko ya katse mai jin daษ—in baccin shi.

Sai da ya shafe sama da awa uku yana bacci sannan ya buษ—e ido a hankali gami da lalubo wayar yana kunnawa, ko da ya kunna wayar bai kuma duba wanda ya kira shi yana bacci ba ya mike zuwa cikin toilet ya watsa ruwa, bayan ya fito ya zauna yana goge jikin shi da towel, yana cikin shafa mai kenan yaji wayar tana sake ฦ™ara, dauka ya yi ba tare da yace komai ba, sai da ya gama jin me ake fada daga ษ—ayan bangaren bai ce uffan ba ya kashe wayar gami da jan wata doguwar tsaki tare da jefar da wayar a gefe, ya ci-gaba da shiri cikin wasu baฦ™aฦ™en kaya, shirt da wando, dake lokacin yamma tayi sossai, duk saurin da yake yi kokari kawai yake yaga ya bar gida, so yake ya je ya tarar da abinda aka fada a waya domin hakan ne kaษ—ai samun kwanciyar hankalin shi domin yanzu kawai daurewa ya ke yi yana controling kan shi har ya gama shiryawa, key’n motar shi ya ษ—auka ya fice ta kofar baya dan baya son kowa ya gan shi ballantana ya tsayar da shi har a bata mai lokaci.

 

 

 

๐—ง๐—ฎ๐—ธ๐˜‚ ๐—ฎ ๐—ธ๐—ผ๐—ฑ๐—ฎ ๐˜†๐—ฎ๐˜‚๐˜€๐—ต๐—ฒ

๐—•๐—ฎ๐—ฑ๐—ฎ๐˜„๐—ฒ๐—ฒ๐˜†๐—ฒ๐—ฟ๐—ต

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment