Littafan Hausa Novels

Gindi Dadi Hausa Novel Wattpad

Maganin Karfin Maza
Written by Hausa_Novels

Gindi Dadi Hausa Novel Wattpad

 

 

 

 

 

 

 

Gindi Dadi Hausa Novel Wattpad

 

BY

 

~AYSHA NALADO~

 

 

FREE BOOK

 

 

{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}

 

 

 

 

 

 

Page 106

 

 

 

 

Haka suka ƙare wannan yinin cike da damuwa a zuciyar kowannen su, a bangaren Asmah Abu biyu ke damunta, maganganun da sukayi da ummi ɗazu, sai kuma, tunani da kewar Aslam daya addabi zuciya da ruhinta, gaba ɗaya jinta take kamar wata Mara lafiya, a haka har lokacin kwanciya barci yayi, koda ta kwanta kasa bacci tayi sai juyi kawai takeyi a makeken bed dinta, karshe ta janyo pillow ta rungume a kirjinta kamar yadda ta saba amma a banza, ji takeyi kamar ta tashi ta fita ta ganshi koda a boye ne,ba tare daya ganta ba,ba karamin dauriya tayi ba da ta hana kanta aikata hakan, daga karshe ta kwabi kanta da cewa, ya kamata ta kama ajinta koba komai ai shiya mata laifi shi ya kamata ya fara nemanta ba ita ya kamata ta fara neman shi ba.

Gindi dadi

Gindi Dadi Hausa Novel Wattpad

A bangaren Aslam kam ya ma fita shiga damuwa, har karfe goman dare ya kai a falo yana zaman jiran tsamanin fitowarta, amma shiru gashi shi kuma ya kasa zuwa ya tunkareta, ganin goma da kwata yasa ya mike jiki ba kwari ya nufi dakin shi, wanka yayi tare da shirin bacci, kashe wuta yayi ya haye bed dinshi ya kwanta, saidai koda gigin wasa babu alamar bacci a idanun shi, gani yayi ma gadon ya mishi wani irin mugun fadi da girma, kai gaba daya ɗakin ma, ga wani irin sanyi da yakeji yana shigar shi duk da kuwa ƙudundunewa da yayi da katon bargo.

 

 

Idanun shi a bude kerr agogo ya buga 12am dai dai, kasa daurewa yayi ya mike ya kunna wutan dakin tare da zura slipas dinshi ya fice daga ɗakinshi ya doshi nata gaban shi Na faduwa, gara yaje ya tunkareta ayi wacce za’ayi komai ta fanjama fanjam, don ya tabbatar idan bai sanyata a idanunshi yau ba lallai bazai iya rintsawa ba.

 

Kuruciyar Minal Hausa Novel Complete

Saida yayi tsayuwar kusan minti goma a bakin kofar yana tunanin anya kofar ma a bude take ko a kulle, a hankali yakai hannunshi kan handle din kofar ya murda tare da tura kofar a hankali, wani wawan ajiyar zuciya ya sauke jin kofar a bude.

 

 

Ware idanunta tayi daga lumshesun da tayi jin motsin ƙarar taba ƙofar dakinta, kafin tayi tunanin wani Abu ta ga ya tura kofar ya shigo dauke da munafukar sallama a bakin shi, ita ba a boye ba kuma baza’a kirata a fili ba ,wani irin mugun dadi ne ya ziyarceta, take ta sauke wani boyayyan ajiyar zuciya, a halin da zuciyarta ke ciki kiriss ya rage ta tashi ta bishi a cikin tsakiyar daren nan, saidai gashi Allah ya kawo mata shi, lamo tayi tana kare mai kallo ta cikin hasken kofar daya bari a buɗe.

 

 

Shikam Aslam bai ganta ba kasancewar dakin dimdim yake da duhu, kuma daga haske ya fito,idanunshi baya iya ganin komai sai duhu, jin bata amsa sallaman shi ba, hakan ya Tabbatar masa tayi bacci, wayar shi ya kunnu ya haska dakin ganin haka yasa tayi saurin rintse idanunta ba tare da ya ganta ba, lallabawa yayi a hankali ya kwanta a bayanta, duk abinda yakeyi tana jinsa, shiru sukayi daga ita har shi Na kusan 20 minutes, shi yana tunanin tayi bacci, ita kuma mamakin karfin halin shi na neman kashe ta, tayi shiru tana jiran taga mai yake shirin aikatawa.

 

 

A hankali ya dinga matsawa kaɗan kaɗan jikinta, har ya manna kirjin shi da bayanta, jin shiru bata motsaba yasa ya mike hannu a hankali ya rungumota jikin shi sosai, yana sauke ajiyar zuciya.

 

 

Kamar daga sama yaji tayi gyaran murya tare da cewa “welldone” ba shiri ya saketa tare da mikewa zaune, itama mikewan tayi tare da lalabur makunnin wutar dakin mai haske ta kunna.

 

 

Kallon cikin idanun juna suka shiga yi, kowannensu idanunshi cike da kewa da begen Dan uwanshi, zuciyoyinsu kamar yayi tsalle ta fado kasa tsabar a zalzalan da take musu, yadda ya ganta haka sanye cikin kayan barcinta masu dan kauri riga da dogon wando ga kuma gashin kanta daya barbazu kasancewar bata dauresu ba, sai tashin kamshi take ba karamin hargitsa shi tayi ba ji yake kamar ta wuff ya rungumota amma babu hali.

 

 

Marairaice fuska yayi, cikin wata irin marainiyar murya yace,”my husnah dama kema bakiyi bacci ba? ” shiru tayi bata amsa ba saima dauke kanta da tayi daga kallon shi, ganin haka yasa ya matsa gabanta ya mika hannunshi ka kamo nata ya rike cikin nashi, a hankali cikin marainiyar muryarshi ya fara cewa”kiyi hakuri Mrs Asmah na San na miki laifi mai girman gaske, amma ina mai baki hakuri kisani wlh ni ba makaryaci bane, hasalima na tsani duk makaryaci, soyayyarki ce ta maidani haka kaunar kice ta rikiɗar dani na koma haka, ina sonki Asmah nasani kema zaki shaida haka, Dan Allah ina rokon ki da kiji ƙaina ki tausaya min ki bani dama na mallaki wani sashe a zuciyarki komin kankantarsa,zuciya ta na daf da kaiwa matakin da baza ta iya juriya akanki ba, hakurina ya kusa karewa a kanki, na miki alkawari husnah zan maki duk wani abin da kike tsammanin samu daga wurin mijinki fiye da yadda kike hasashe, zan nuna miki zallar madarar soyayya mara sirki, fiyye da yadda kike tunani, zan kula dake fiyye da yadda zan kula da kaina da tarin dukiyoyina, zan biya dukkan bukatarki,wanda na sani da Wanda ban sani ba fiyye da tunaninki, zan kare duk wani hakkin ki daya rataya a kaina iya karfina na, zan biya miki bukatar rai da gangar jikin ki yadda baki taba tsammani ba, Dan Allah Mrs Asmah ki bani dama komin kankarta ta, ki yarda dani da abinda nake fada miki wlh baza ki tabayin nadama ba,ina sonki my husnah ina mahaukacin kaunarki, ki tausayamin ki dubeni Dan fiyayyen halitta annabin rahama,sallahu alaihi wasallam”

 

 

A zuciyarta tama annabi salati itama, tare da dagowa ta sauke mishi dara daran idanunta a kanshi, shima dama idanun shi nakan fuskarta, kallon idanun juna sukeyi, kowanne da abinda yake karanta a cikin idanunn ɗan uwanshi, ta hangi tsantsar matsanancin soyayyarta a cikin kwayar idanunshi tare da tsantsar gaskiya akan abinda ya fada mata yanzu, yayinda shi kuma ya hangi tausayi, da burbushin soyayya da kaunar shi a idanunta.

 

 

Itace ta fara katse kallon ta hanyar zare hannunta cikin nashi, tare da juyawa mai baya ta kwanta, gaban shi ne ya yanke ya fadi me hakan me nufi, yes take nufine kokuma A’a.

 

 

Sun kwashe kusan 20 minutes a haka babu Wanda ya sake cewa komai, kundunbale yayi ya, mika hannu a hankali ya daura akan damtsen hannunta, wani irin shock taji a jikinta, lumshe idanunta tayi tare da budesu a hankali.

 

 

Ganin tayi shiru bata hanashi hakan ba, yasa a hankali ya shiga shafa hannun yana matsawa a hankali, daga karshe kuma ya koma ya kwanta, tare da janyota jikinshi ya rungume, a tare suka sauke ajiyar zuciya.

 

 

A hankali ya shiga cusa kanshi cikin sumar kanta dake nan a kwance Dan Sam bata iya parking din gashinta idan zata kwanta, yana shakar daddar kamshin dake tashi a cikin gashin, yayinda ya mika hannushi, ya dage Dan rigarta na barci ya daura tafukan hannayenshi akan shafaffen cikinta yana shafawa.

 

 

Sun kusan kwashe 30 minutes a haka, ko wannensu cike da begen Dan uwansa, a hankali ya farayin sama da hannayenshi yana kokarin kaisu inda zuciyar shi ke muradi,inda tun daga ranar daya gansu har yau hoton su bai taba bace mai a idanun shi ba, jin haka yasa tayi tsam tana zazzare idanu.

 

 

Kamar Wanda aka dannawa tsop, haka ya tsaya ƙem da hannayenshi, zuciyarshi ce ta kwabe shi da cewa, kul Aslam me kake shirin aikatawa ne haka, ka cika zalama wlh, kabi komai a hankali ka samu kaɗan raba ta ƙyaleka kuma kana neman ka wuce gona da iri, ka kiyaye ka maida zalamarka ka Adana, ka lallabata ka koya mata yadda zata saki jiki da kai ta yadda wata rana ita da kanta sanda zata mika maka kanta bata da labari, amma yanzu idan kayi haka saita dauka ba soyayyar gaskiya kake mata ba wani Abu kake bukata a jikinta, da wannan shawaran ya dingayin kasa da hannun shi harya maida shi inda yake da.

 

 

Ajiyar zuciya ta sauke jin bai karasa can ɗinba, shiru sukayi suna sauraren bugun zuciyar juna kowannen su zuciyar shi cike da anashuwa, kusan awa daya a haka kafin a hankali wani irin daddadan barci da ta daɗe ba tayi irin shi ba ya kwasheta.

 

 

Saukar nunfashinta da yaji ya tabbatar mai da barci ya kwashe ta, murmushi ya saki tare da kissing tsakiyar kanta, shima a hankali ya lumshe idanu ba bata lokaci barci ya kwashe fuskar shi dauke da kayataccen murmushi.

 

 

 

Wani irin barci mai dadi sukayi ranar wanda suka daɗe basuyi irin shi,bacci suke hankali kwance kowannesu furkarshi dauke da murmushi mai kayatarwa, gaba daya ya kanannadeta a jikinshi ta yadda ko kwakkwaran motsi tayi saiya a farka.

 

 

Basu suka farka ba kuwa saida hasken rana ya ratso cikin dakin,ita ta fara farkawa,gani tayi haske gaba daya ya cika dakin alamar har rana ya bullo, bin jikinta tayi da kallo ganin yadda ya kanannadeta gaba daya, ya saka ta ajikin shi bata da damar motsawa kallon fuskarshi tayi, fayau da shi yana dauke da murmushi sai sharar barcin shi take hankali kwance, kura mishi idanu tayi ta kalle shi son ranta,gaskiya yaya Aslam kyakkyawa ne ajin karshe, ta ayyana hakan a ranta, murmushi ta saki, bata San sanda takai ɗan bakinta tamai kiss a wuya ba, ahankali kuma ta shiga zare jikinta daga nashi, harta gama ta yunkura a hankali zata mike karaf taji ya cafkota ya maidata ya kanannade har fiyye da da, cikin murya mai ciki da barci ya shiga ce mata a kunne “ina zakije? Dan Allah karki gusa kibar mahaukacin masoyinki shi kadai” cikin in,ina tace”gari ya waye fah” ba shiri ya waye idanunshi tare da sakinta ya mike zaune yana furta”subhanallah astagfirullah” mikewa yayi ya shiga toilet din dakin da sauri yayi brush tare da dauro alwala ya fito, a bakin bed ya sameta zaune ta ziro kafafunta kasa, jin motsinsa yasata dagowa ta kalle shi murmushi ya sakar mata tare da mika mata hannu alamar ta miƙo nata, ba musu ta mika mishi, Dan ta daukarwa ummi alkawain cewa duk abinda ya umarceta zatayi matukar bai sabawa Allah ba.

 

Ita kuma ummi tayi amfani da wani hikima ne ta manya ta daurawa Asmah wannan nauyin tasan hakan zai bada gagaruman gudunmawa wajen daidaita tsakanin su.

 

 

Har cikin toilet din ya kaita, tare da kokarin yi mata alwala, tana da uzirin kama ruwa, ganin baida niyyar fita, yasa ta naimi alfarman ya bata waje zata kama ruwa, ba musu kuwa ya fice daga dakin ma baki daya, kama ruwan tayi tare da yin brush a karshe ta dauro alwala, koda ta fito baya dakin, direct gaban wawakeken wardrobe dinta ta nufa, wani dogon Riga Mara nauyi ta fitar tare da hijjab din da take sallah dashi ta ajiye a bakin bed, cire kayan jikinta na barci tayi, har pant din kuwa bata bari ba dan bata yarda da tsarkinsa ba, dama babu maganar saka bra, wani sabon wankakken pant ta dauka ta saka sannan ta dauki dogon rigarta, ta daga zata zira kenan ya shigo dakin dauke da sallama, kallo daya ya mata yayi saurin dauke kai kamar baiganta , yayinda ita kuma tayi saurin karkare zira rigarta, sannan ta saka hajab dinta.

 

 

Sanye yake da jallabiya na maza ruwan hanta mai guntu hannu, direct inda take ajiye pray mat ya karasa dauka yayi ya shimfida duka biyun, nashi a gaba nata a bayan nashi daga gefen dama, ganin haka bata tsaya bata lokaci ba, ta daidaita sahu, jam’i ya jasu kara’i saboda makaran da sukayi, bayan sun idar kuwa, sunyi tasbihi, ya shiga kwararo musu addu’o’i manya manya, batayi wani mamaki ba kasancewar ta riga tasan shiɗin yana da ilimin addini sosai tunba yau ba.

 

 

 

Bayan idar da dukkan addu’o’in juyowa yayi da murmushi a fauskar shi yana kallonta, cikin sa’a kuwa itama ta dago kai tana kallon shi, wani irin kyau kwarjin da haiba taga ya kara mata ba shiri tayi kasa da kanta tare da cewa “ina kwana ya Aslam” shiru yayi bai amsata ba, bai kuma daina kallonta ba, jin shiru yasa tayi tsammanin ko baiji bane, hakan, yasa ta sake maimaita gaisuwarta, da Dan karfi wannan karon, still ba amsa, hakan yasa ta dago kanta ta kalle shi, tare da sake cewa”ina kwana Mr Aslam” maimaikon ya amsa mata sai gani tayi yakai Dan yatsan shi manuniya kan labbanshi, yace mata “shiiiiiiii” da mamaki take kallon wannan irin ikon Allah, murmushi ya saki tare da cewa, “daga yau na haramta irin wannan gaisuwar a tsakanin mu indai a ba agaban mutane muke ba” kamar sokuwa haka take binshi da kallo ganin haka yasa yace kinsan wani irin nake so, girgiza mai kai tayi alamar A’a, yace kina son ki sani, sake girgiza mai kai tayi alamar Eh.

 

 

Aiko kafin tayi wani tanani taji ya janyota jikinshi ya hade bakinsu ya lalubi harshenta ya cafke ya shiga bata wani irin slow kiss mai saurin kashe gaɓɓai.

 

 

Wani irin zaro idanu Asmah tayi, take firgici mamaki da tsoro suka diran mata a lokaci guda, tunda take a rayuwarta wannan ne karo na farko da wani mahaluki ya sumbaceta……………

 

 

 

 

 

 

 

Comment dinku shine zai tabbatar min da cewa kunyi farin cikin dawowana online

Daga yau posting zai ci gaba insha allahu har sai mun ɗire

 

 

 

Ɗinbin godiya a gareku masoyana masuson farin ciki da da cigaba na, wadanda sukayi contributing din kudi domin su bani kasancewar sun samu labarin wayata ta samu Matsala, na gode muku Allah ya saka muku da alkhairi Allah yabiyaku da Gidan aljannah madaukakiya, inayinku over

 

Wadanda sukayi niyar bayarwa Allah bai basu iko ba kuma na gode Allah yaga niyyarku, wadandama basu niyya ba duk na gode Allah yabar kauna😬

 

 

 

 

 

 

 

Oum Ummeetarh

07041130088

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Share

And

Comment

Fisabilillah

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment