Littafan Hausa Novels

Gidado Ba Shege Ba Hausa Novels Complete

Written by Hausa_Novels

Gidado Ba Shege Ba Hausa Novels Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

GIDADO BA SHEGE BANE

 

 

Zahra Muhammad Mahmud.

 

 

wannan littafin kirkurars nayi,banyishi dan wani ko wataba,so in wani abu yayi kama da rayuwarka arashine,a kiyaye juyamin shi ta kowacce siga

 

 

na sadaukar da wannan littafi ga kawata kuma aminiyata Amina Maman Gid’ad’o,Allah yabarmu tare cikin aminci

 

 

Dedicated to Amina Maman Gidado

 

 

1-2

 

 

Ɗakin tarone me kyan gaske,wanda ke dauke da kujeru na alfarma.zagaye da wani tebur.

 

Mutanene kimanin mutum hamsin zaune akan kujerun kowa rai abace,yayinda wasu yanmata su uku ke tsugune agaban mutanen,daya cikinsu dauke da wani jariri se kuka yake tsalawa.

Karanta Littafin Auren Lagos

“Fatima Abubakar Radda,Hauwa’u Abubakar Imam,Amina,acikinku wlh idan baku fada mana dan waye wannan jaririnba,se na koreku dukanku a makarantar nan,taya zaa haifi yaro acikinku amman akasa gane wacce ta haifeshin”cewar chancellor na makarantar nasarawa state university wacce akafi sani da suna Nsuk.

 

Gaba ɗaya hankalin yanmatan inyayi dubu ya tashi,sabida dukansu suna level four hundred ne kuma final exam suke zanawa.

Muwaddat Hausa Novel Complete

“Sir wlh ni ba dana bane,wlh banida wata alaka dashi,Fatima ce ta tsintoshi ta kawo mana shi dakinmu jiya da daddare,bayan haka ni wlh bansan komai ba game da yaron”cewar hauwau Abubakar imam tana share hawaye.

 

 

Amina ce ta tsananta kukanta,harda majina,inda tafara mgn.

 

“Taya mu da muke yanmata zaace wai mune kuma muka haifi yaro,nima wlh ba dana bane,sam banida alaka dashi,sede atuhumi ita fatiman data kawo yaron,danni wlh a idona ma gani nake tana kama da yaron”ta karasa maganar cikin kuka.

 

 

Allah sarki fatima baiwar Allah ware ido kawai takeyi,sabida ita tun farkonta bata iya magana me tsayiba hasalima wuya take bata,shiyasa su hauwau suka fita baki,

 

Tsawa vice chancellor ya yimata gami da cewa.

 

“zaki mana bayanin inda kika samo yaron ko bazakiyi ba?”

 

A daburce tace.

 

 

“Sir wlh ba ɗana bane,wlh banida alaka dashi,kwatakwata nima tsintarshi nayi jiya na fito fitsari zan koma daki naganshi cikin kwali ruwa na dukanshi yana kuka,shine na ɗaukeshi nakaishi ɗakinmu,amman wlh ba ɗana bane”ta karasa maganar tana kuka gamida jijjiga yaron dake ta faman kuka.

 

 

Shuru gurin yayi,kowa na nazari,inda su Amina da hauwau suka tubure sufa ba ɗansu bane,inda amina kai tsaye ma ta alakanta yaron da fatima.

 

 

Fatima se kuka takeyi,Tana rantsuwa akan tsintar yaron tayi amman sam anki amincewa da ita,sabida shaidar da aminanta suka bada kamar haka.

 

” sir watanni shida dasuka wuce fatima Abubakar Radda ta taba cemin watanninta uku rabonta da ganin aladarta,wanda har na bata shawarar taje taga likita,bayan haka bata cemin tasamu saukiba ko akasin hakan”cewar hauwau tana kallon fatiman.

 

“ke fatima anyi haka ko ba ayi ba?”cewar chancellor .

 

“eh anyi haka,sede na bari ne akayi hutu sannan naje asibiti dana koma gida aka bani magani kuma nasamu daidaituwar abun”cewar fatima tana kuka.

 

“Nima ta fadamin hakan,bayan haka kuma tazo tana fama da yawan ciwon mara,wanda lokacin,har cewa takeyi tanajin motsi acikinta,sannan lokacin tana yawan yin bacci dan so tari ko aji bata iya zuwa”cewar Amina tana kallon fatiman.

 

“Fatima anyi haka ko baayi ba?”inji chancellor.

 

Cikin matsanancin kuka tace.

 

“Duka anyi,sede motsi da nakeji a cikina danaje asibiti cewa akayi infection ne ke haddasa hakan,yawan bacci kuma lokacin banida lfy ne,ciwon mara ma danakeyi yanada alaka da infection din,ku yard dani wlh ni ba dana bane”ta rushe da kuka.

 

Bayan angama muhawarane,aka maida hankali,dan sauraron hukuncin da shugaban ze yanke.

 

“Fatima Abubakar Radda bincike da shaidu na kusa dake damuka samu,mu mun gamsu wannan yaron nakine,kuna sanda kika shigo makarantar,sunanki ajerin yanmata akasa,bakice kinada aureba,so bazamu ci gaba barin barna na yawa acikin makarantar muba,dan haka abisa dokar da aka tanadarwa budurwar da tayi ciki,hukumar makarantarnan ta koreki,daga makarantar”cewar shugaban.sannan yayi signing a wata takarda,yamike yafice,kowa ma ficewar yayi.

 

Ya rage daga fatima se kawayenta,da jaririn,fatima kuka takeyi kamar ranta ze fita,tama rasa abinda zatayi,suko se rarrashinta sukeyi,

 

Miƙewa tayi dauke da yaron da ko zaa kasheta batasan daga inda yakeba,amman se gashi,an maidashi danta,kuka take,sosai,a hankali take ɗaga kafarta har ta fito daga gurin,dalibai tasamu birjik a waje suna mata tofin Ala tsine

 

Su hauwau ne sukazo suka tareta har ta fice daga inda ɗaliban suke,

 

Hauwau da Amina ne suka cemata.

 

“Fatima kiji tsoron Allah ki kula da yaron nan,kodan ladan hakan se kiga Allah ya yafemiki zinar da kika aykata,kiyi hakuri da kaddarar data faɗa miki kinji”simuka faɗi suna kuka.

 

Bata ko waiwayesuba tasa kai ta wuce hostel,ta debo kayanta,tazo ta fice,tabarsu se kuka sukeyi na rabuwa da ita.

 

Goye da yaron tafito,tanemi abun hawa zuwa tasha,tana zuwa motar garinsu katsina ta nema,tahau tana kuka,

 

 

hmmmmmm.

 

Tofa,wannan lamari akwai daure kai,aciki,anya kuwa yaron ba dan fatiman bane?,inba hakaba taya zata anshi dan da ba nata ba?

 

mudeje zuwa.

 

 

 

Surbajo for life

 

 

GID’AD’O BA SHEGE

BANE

 

 

 

Zahra Muhammad Mahmud

 

 

Don Allah kudena tambayar nanah aseeyah,wlh har rasa amsar baku nake,pls din girman Allah kudena tambaya,duk randa Allah yasa zaa ci gaba zaku ganshi,so don Allah kudena tambayata don girman Allah

 

 

Dedicated to Amina maman Gidado

 

 

3-4

 

 

Haka mota ta cika suka kama hanyar katsina,fatima se kuka takeyi,

 

Zuwacan yaron yafara kuka,kowa na motar akamata ca akan ta bashi nono,dan da gani yunwa yake ji.

 

Zuciyarta kamar zata tsinke,haka tasa yaron cikin hijab dinta tasa masa nonon a baki,carab ya kama,ita kuma ta runtse ido,sabida azabar da takeji,

 

Yaron ganin ba ruwa a nonon ne yasa yaci gaba da tsala kukan shi,haka gankalin fatima yabi ya tashi ta rasa yadda zatayi dashi,wata matace,ta amsheshi ta shiga jijjigashi har ya hakura yayi bacci,sannan fatima ta ansheshi.

 

Da laasar suka isa katsina,mota ta hau da zata kaita unguwarsu,tana sauka tabi layin daze sadata da gidan su.

 

Da sallamarta,ta shiga gidan,ummantace zaune tana gyaran alaiyahu,fatima na ganinta ta rushe da kuka,ta nufeta,a rude ummanta ta rukota tana tambayarta.

 

“lafiya kuwa fatima kike kuka?”

 

“umma an koreni a makaranta akan laifin da ban aykata ba”ta faɗi sanda take sakko yaron daga bayanta.

 

A firgice umman taja baya tana binta da kallon tuhuma.

 

“Umma wannan bawan Allah tsintarshi nayi a kofar dakinmu na makaranta,an yar dashi,ruwan sama na dukanshi,sanadin taimakon da na mishine ni kuma aka koreni”daganan ta kwashe duk abinda ya faru ta sanar da umman nata.

 

Fatima yace ta gari me tsananin biyayya ga mahaifiyarta,wacce kuma kullum bakinta cikin furta gaskiya yake,shiyasa mahaifiyarta natsuwa da kalamin bakin fatiman.

 

Matsowa tayi kusa da ita,ta amshi yaron,hawaye na zuba afuskarta,tace.

 

“kowa da irin tashi kaddarar,kai taka a haka tazoma,Allah ya rayaka rayuwa me amfani duniya da lahira,ke kuma fatima kiyi hakuri,bamu da karfin fahimtar da hukumar makarantar bakowane ke yarda dame gaskiya a lokaci guda ba,ni musulmace fatima na yarda da kaddarar Allah,wannan abu daya sameki ki rikeshi amatsayin kaddara kuma ki yarda da ita kamar yadda nima nayi,da yardar ubangiji,wannan yaron zeyi rayuwa me amfani,sekinyi alfahari dashi agaba,Allah ya shiryi mahaifiyarsa”ta karasa maganar hawaye na bin fuskarta.

 

Se a lokacin hankalin fatima ya kwanta,dan ita bata makomar karatunta takeyiba,ta makomar rayuwar yaron takeyi idan mahaifiyarta bata amince da zaman yaron a tare dasu ba,yayanta umar kawai takeji,tunda ko ummanta ta amince tasan shima zata shawo kanshi ya fahimta,dan umar mutumne me tsatstsauran raayi,baya juyuwa ta daɗi.

 

 

Umman mikewa tayi,ta ɗauko zamzam da dabino ta tauna dabinon ta zuba acikin zamzam din tafara ba yaron ayko carab ya amsa yana sha yana turo harshe waje gamida bude idanunshi tar,seda ya koshi ya fara turoshi waje in an bashi.

 

 

Wanka umman tai masa,da ruwa me zafi ta gasheshi da kyau,ayko tun acikin ruwan yafara bacci.

 

Haka ta gama ta masa kwalliya sannan ta nadeshi a zani ta kwantar dashi,bayan ta kwantar dashine tacewa fatima.

 

“kije ki samu kiyi wanka kema,bari naje na anso masa kayan sawa gurin dije dillaliya ko kala biyu ne,kamin Allah ya hore a siya masa da yawa”

 

Murmushi fatima tayi sannan tace.

 

“umma na kenan,me kyan zuciya,wlh ina godewa Allah daya bani ke a matsayin uwa,Allah ya kara nisan kwana ummana”ta fadi tana dariya.

 

Murmushi umman tayi,sannan ta juya ta nufi hanyar fita daga gidan,har takai bakin kofa ta waigo tacewa fatiman.

 

“Ki kula da yaron nan,duk wuya duk runtsi ki jure,wata rana se labari,jikina na bani wannan yaron shi zeji kanki,ki rikeshi amana”ta fadi jiki a sanyaye.

 

Dariya Fatima tayi sannan tace.

 

“ummana kenan keda zaki ki dawo meye nabada sakon a hanyar kofar gida”tayi maganar cikin nishadi.

 

Murmushi umman tayi tasa kai ta fice daga gidan,tanufi gidan dije dillaliya.

 

Ayko taje a saa dan ankawowa dijen kayan yara masu saukin kuɗi hakanne yasa ta zaɓo masa kala hudu,gamida wanduna,da bulumboti,ta biya kudin ta amso kayan ta nufo gada.

 

Tana zuwa zata tsallaka titin da dagashi se gidansu kasancewar gidan abakin titi yake,kawai sega wata mota aguje ta bigeta tabi ta kanta

 

jamaane akayo ca akanta,sede ina gaduk wanda yasan mutuwa yana kallon umnan fatima yasan ta mutu,

 

me motar dama burkine ya tsinke masa yana bugetane yasamu motar ta tsaya,a gigice ya nufo ta shima se salati yakeyi.

 

 

kan kace kwabo tuni gurin ya dinke da mutane,ganye aka samu aka rufa mata,kamin akawo makara daga masallaci.

 

Fatima dake gidan bayan fitar ummanta ji take gabanta na faduwa,hakanne yasa ta kasa wankan,duk ta rasa natsuwa.

 

 

Hayaniyar da ta jiyo a kofar gidanne yasa ta leka dan ganin abinda ke faruwa.

 

innalillahiwainnailaihirrajuun,ita kawai take maimaitawa sanda tai karo da gawar ummanta kwance kan titi,da gudu tayi kanta tana kuka tana jijjigata,

 

wanda ya buge ummanne ya matso gurinta,matashine me cikar kamala da mutunci yace.

 

“don Allah ku gafartamin wlh bada sanina na buge ta ba,”

 

A hargitse fatima ta juyo ta kafeshi ta mari,sannan ta rufeshi da duka tana fadin.

 

“ka cuceni ka cuci rayuwata,ka kashemin uwata me tausayawa rayuwata,wlh bazan gafarta makaba,mugu azzalumi”

 

Da kyar aka kwacr mutumin a hannunta,wanda zuwa lokacin gaba daya hawaye ya gama wanke masa fuska,

 

 

haka aka shigar da gawar umnan cikin gidan,wanda hakan tayi daidai da dawowar,yayan fatiman umar daga gurin ayki.

 

Tashin hankalin daya shiga baa mgn sabida umar ji yake ummansa itace rayuwarsa,yanasonta yana kaunarta,yau gashi ta tafi ta barshi.

 

Haka aka hada umman aka sallaceta,aka kaita gidanta na gaskiya,kowa se yabon kyawawan halayenta,yakeyi.

 

kayan data siyone,wani matashi yashigo gidan yamikawa fatima,ayko tana budewa taci gaba da kukan se alokacin ta tuno da yaron dakecan dakinta yana bacci,mikewa tayi taje ta dubashi,har lokacin baccinshi yakeyi.

 

Ranar fatima da yayanta ba wanda ya runtsa,duniyar ta musu zafi,dama gashi shekarar mahaifinsu uku da rasuwa,mahaifiyarsu ce ke ci gaba da dawainita dasu to gashi yau itama ta tafi ta barsu.

 

Haka aka cigaba da zaman makoki har zuwa ranar bakwai,umr yan ganin jariri a hannun fatima amnan azatonshi dan daya daga cikin yan uwansune,shiyasa be taba kawo komaiba aransa,suma jamaa kowa yaganta dashi dauka yake na watane acikinsua haka har kowa y watse ranar sadakar bakwai da daddarw.

 

Umar ya shigo cikin gida ya leka dakin fatiman yasamu tana yiwa yaron wanka yana kukansa.

 

cike da tsananin mamako yace mata.

 

“wai yaron nan na waye?,ina uwarsa?”ya tambaya a bukace.

 

gaban fatimane yafara dukan uku uku,baki na rawa tace.

 

“Nima bansn wacece uwarshiba,tsinto shi nayi nima a makarantarmu,sanadin hakan aka korenima a makarantar shine nazo na fadawa umma komai a ranar d zata rasu”ta karasa maganar tana kuka.

 

 

tsigar jikin umar tuni ta jima da tashi,bacin rai na aynihine ya bayyana akan fuskarsa,afusace yace.

 

“what!!!!!!”

 

 

 

muje zuwa

 

 

surbajo for life

 

 

 

GID’AD’O BA SHEGE

BANE

 

Zahra Muhammad Mahmud

 

 

Dedicated to Amina maman gidado

 

 

5-6

 

 

“Ni zaki rainawa hankali?,su makarantar mahaukatane da zasu koreki hakannan batare dasun tabbatar da nkin bane,?”cewar umar cikin matsnancin fushi.

 

“wlh yaya ba karya nake maka ba,ko umma ma ta fahimta dana mata bayani,don Allah kaima ka fahimceni wlh. Ba dana bane”tayi mgnr cikin kuka.

 

“Se yanzu na gano musabbabin mutuwar mahaifiyata,ashe bakincikin kine yasa tafice agidan batare data luraba ta fada mota ta taketa,to wlh bari kiji in faɗa miki,wlh kin gana zama tare dani,kamin nima bakin cikin naki ya kar ni”

 

“yaya wlh ba haka bane gidan dije dillaliya taje siyowa yaron kaya,shine a hanyarta ta dawowa tsutsayin ya rutsa da ita,don Allah yaya karka tozartani,banida kowa sekai”ta tsuguna agabanshi tana kuka.

 

Ko ajikin umar,ranshi yagama baci ya yarda hundred percent ita tayi sanadin mutuwar ummansa,dan haka bayajin ze iya gafarta mata.

 

Fincikota yayi ita da yaron,yana jansu hanyar kofar gida,kuka take tana rokonshi amman ko ajikinshi haka ya cillasu kofar gidan,sannan yadawo yadauki jakar kayanta da ledar kayan yaran daya gani a kai yazo ya cillo mata,sannan yafara mgn.

 

“koda wasa kika sake yunkurin kallon gidan nan a matsayin gidanku wlh sena halakaki,kamar yadda kika halaka mahaifiyarmu,tur dake fatima,ki rasa sakamakon da zaki ba umma se kikawo mata shege gida”

 

Tuni jamaa sun zagayesu sunajin abinda ke faruwa,ayko nan kowa yashiga tofin ala tsine.

 

 

mikewa tayi jikinta na bari,ta hoya yaron,sannan ta kwashi kayansu,tabar harabar gurin,dan tafi kowa sanin waye umar,ze iya yimata abinda yafi haka ma,

 

Tafe take tana kuka tana tausayin rayuwarta data yaron bayanta,sam umar be musu adalciba,

 

Haka take ta tafiya da kafarta wanda ita kanta ko zaa kasheta batasan inda take sa kafarta ba,kawaide tafiyar take.

 

 

Har dare yayi mata,gefen wata bishiya taje ta rakube rungume da yaron  ,data rufe da hijabi,a haka bacci yayi awaon gaba da ita.

 

Bata farkaba,seda garin Allah ya waye,shima kukan yaronne ya farkar da ita,a rude ta tashi,tashiga jijjigashi.

 

Tafiya taci gaba dayi har tazo gurin wasu masu saida abinci,anan tanemi taimakonsu akan tanaso ta dunga yi musu wanke wanke,dakyar suka amince nanfa ta duka tashiga yimusu wanke wanke,harta gama suka biyata kuɗinta,

 

Shagon saida madarar yara taje,ta siyowa yaron,wanda sabida yunwa ko kuka bayayi,gurin saida abincin ta koma tasamu ruwan dumi ta dama masa tasa a bulumboti,ta sa masa abaki,

 

Yadda yaron kejan madarar kadai abun tausayine,dan har kwarewa yakeyi sabida hanzari,tas yashanye wanda ta hada masa,se gumi yakeyi,alamun yaji daidai.

 

Matar dake saida abincin ce,tacewa fatima.

 

“keko in banda abunki me ze hana kinemi maganin dake kawo ruwan nono,kidunga shayar da danki,inaga hakan se yafi cacar kudin madara,”

 

Shuru fatima tayi tana sauraronta,tabbas da zata samu maganin zatayi amfani dashi Kodan inganta lfyr yaronta.

 

dubanta takai gurin me abincin tace.

 

“hajiya kitaimakamin inkinsan masu saida maganin wlh banuda kudi amman innayi wanke wanke se adunga cirewa a kudina,don Allah ki taimakamin”tayi zancen hawaye nabin fuskarta.

 

“karki damu kawata ce ke siyarwa,insha Allahu zan amsar miki,inyaso kya biya daga baya”

 

 

godiya sosai fatima ta dunga yiwa matar harda kukanta.

 

Dayake matar ita da maaikatanta agurin suke kwana shiyasa fatima ta shiga cikinsu itama hankali kwance,da dare tayi matar ta kawomat maganin,ta nuna mata yadda ake amfani dashi,

 

Wanka tayiwa yaronta sannan t sauya masa kaya,ta wanke wanda ta cire masa,sannan taimasa shinfida ta kwantar dashi taimasa rufar da sauro baze cijeshiba.

 

 

Haka rayuwar fatima ta kasance agidan abinci ita da yaronta,koda wasa bata sake waiwayar gidansuba,hankalinta ya kwanta da inda take.

 

 

Suna nan suna sanaar abinci,madara take ci gaba da bashi sabida ruwan nonon yaki zuwa,ayko ba laifi yaron gwanin shaawa yayi kubarsa abunsa,dan wata hudu kamar yakai shida,sabida wayo.

 

 

Hajiya me abinci ce ta buɗe sabon gidan abincinta a garin Abuja,dan haka ta tara maaikatanta ta sanar dasu,ayko kowa cikinsu yayi murna,sabida hajiya uwace tana kare musu hakkinsu da mutuncinsu kamar kowacce uwa,ba kamar sauran yan tuwo tuwon ba.

 

Nanfa ta kawo motoci guda biyu suka kwashesu ita da maaikatanta zuwa garin Abuja,fatima cike da kewar mahaifarta wato katsina.

 

 

Wacece fatima?

 

 

Fatima Abubakar Radda shine cikakken sunanta,

 

Anhaifeta agarin katsina,tana da yaya namiji guda daya,me suna umar,su biyu kawai Allah yaba iyayensu.

 

Tayi makaranta tun daga primary zuwa secondry da islamiyya duk ajihar katsina,inda dakyar mahaifinta yayi fafutukar samomata makarantar nsuk dake garin keffin  ya musa,ta jihar nasarawa.

 

Kasancewarsu masu karamin karfi,shiyasa ya wahala kan agama registration,nan aka shiryata ta tafi karatun.

 

bata jimaba ta hadu da Amina da hauwau,wanda suka kulla kawance,Amina yace ga shugaban nnpc ta jihar kaduna,yayinda hauwau ma mahaifinta hamshakin me kudine,fatimance kawai ba yar kowaba.

 

Ta saki jiki dasu aminane sabida taga basu da wani hali mara kyau duk da suna yayan masu kudi,amman basa nuna mata hakan.

 

Tunda ta hadu dasu suka dauki nauyin karatunta,musamman Amina ta taka muhimmiyar rawa a rayuwarta dan Amina macece me matukar tausayin na kasa da ita.

 

So tari in anyi hutu,har kayan abinci take siyawa fatima takai gidansu,itama hauwau haka akwai tausayi tana iya kokarinta wajen ganin sun inganta rayuwar fatima.

 

 

Tana tsaka da karatun Allah yayiwa mahaifinsu rasuwa,wansa hakan sosai yadaga hankalinsu dana mahaifiyarsu,haka dole suka fauwalawa Allah lamuransu suka rungumi kaddara.

 

 

kowa a gidansi yasan labarin kawayenta duk da basu taba zuwa gidan su fatimanba amman alkhairinsu yasha zuwa.

 

 

Haka rayuwarsu taci gaba da tafiya cikin aminci har zuwa ranar da wannan tsautsayin ya rutsa da ita,

 

 

cigaban labarin

 

 

 

muje zuwa

 

 

Surbajo for life.

 

 

 

GID’AD’O BA SHEGE

BANE

 

 

Zahra Muhammad Mahmud

 

Dedicated to Amina Maman Gidado

 

9-10

 

Tun daga lokacin Fadil ya maida gidan abincin su fatima gurin cin abincinshi,sabida shi mutum ne meson abu me dadi.

 

Tare suke ci da danuwansa Gidado idan ya siyo,shiyasa shima gidadon yanzu inba abincin gurinba baya cin na ko ina.

 

.Yauma kamar kullum zaune suke fadil da gidado suna cin abincin sunyi kaca kaca da gurin,mahaifiyarsu ce tafito.

 

Macece kyakkyawa,ga aji sanye takecikin wani hadadden leshi,wanda yadace da jikinta yayin da idonta ke sanye cikin farin glass siriri shima mekyau.

 

Koda ta shigo falon sam basu lura da ita ba abincinsu kawai sukeci.

 

Guri tasamu ta zauna tana musu kallon so da kauna,ba abinda hajiya maryam takeso sama da yaran nan nata guda biyu,bata da wani buri daya wuce taga sunyi aure,amman kowa taiwa batun auran,se yace be shiryaba.

 

“Ande ji kunya wlh,daga yayan har kanin anji bitir,yanzu fisabilillahi abunda kukeyi daidai kenan,?ku kenan kullum fita siyan abinci waje,to wlh na dakatar da wannan iskancin,duk wanda ya sake fita siyan abinci cikinku sena saba masa kunji na fada muku”cewar hajiya cikin hada rai.

 

Fadil ne ya turo baki gaba irin na shagwababbun yaran nan yace.

 

”haba mummy don Allah,kefa yan aykinki duk basu iya girkiba,yanzu kuma mun samo inda aka iya kince mudena zuwa yanzu don Allah adalci kenan yaya?”ya karasa maganar yana kallon gidado.

 

“ah sam baa mana adalciba,ina bayanka”cewar gidado yana dariya.

 

“nide na hana kuma dole ku hanu kunji na fada muku”cewar mummy.

 

“To inde hakane yaya muma muje gurin masu abincin su bamu me girka musu abincin amatsayin me aykin girka mana agida tunda abun hakane”cewar fadil.

 

Dariya mummy takeyi dan tasan wawtar fadil tafi gaban haka ma.

 

“Wannan shawara taka tayi sosai haka kawai zamuyi,kuma komun kawo me girkin mu kadai zaa dunga dafawa”cewar gidado.

 

“kude kuka sani,nide asiyo a waje ne akawomin gida ban aminceba”

 

Daga haka hira suka shigayi da mummyn tasu gwanin ban shaawa,

 

Da yamma suka shirya fadil da gidado,suka nufi gidan abincin,gidado kejan motar,suna parking,fadil ya fita yashiga cikin gurin.

 

Fatima na ganinshi ta mike zumbur,dan be taba fitowa daga motar ba,hajiya ma da sauri tazo inda yake.

 

“yalabai ay da base ka shigoba,inka tsaya acanma ay zaa kawomaka”cewar hajiya.

 

Murmushi atakaice fadil yayi,shima dan girmamawa yayi mata sannan yace.

 

“ba abinci nazo siyaba yau,alfarma nazo nema”

 

Ido hajiya ta ware tana kallinshi baki na rawa tace.

 

“alfarma kuma dannan?”

 

“Eh so nake ki taimaka kibani me girka abincin danake siya,zan kaita gidanmu tadunga girka mana acan,”

 

Shuru hajiya tayi tana nazari,zuwacan tace.

 

“yaran dake ayki atare dani amanane a hannuna,taya zan baka daya cikinsu alhalin ban sanka ba?”

 

“Fadil bukar Adam maliya,shine sunana,nasan ay may be kinsan mahaifina?”

 

itade hajiya bata yarda ba,ganin hakane yasa yaciro complementry card dinshi yabata,ta karanta,sannan yaciro id card dinshi shima yabata ta duba.

 

Se a lokacin hajiya ta amince dashi dan tasan bukar Adam maliya bawan Allah ne me tsoron Allah dagashi har matarshi.

 

“Fatima,shirya kizo”cewar hajiya tana kwalawa fatima kira.

 

jiki a sanyaye fatima tazo gurin,

 

“Gidansu zaki koma dayin ayki,insha Allahu na tabbatar da babu wata matsala,koda akwai matsalar ki dawo nan kanki tsaye kinji”

 

Itade fatima ranta besoba hasalima gabanta bugawa yakeyi.

 

Haka ta dauko jakar kayansu ita da gidado,tazo tabi bayan fadil zuwa motar bayan sunyi sallama da hajiya da sauran maaikatan.

 

Gidan baya ta bude ta shiga,shikuma yashiga gaban motar.

 

Wani sassanyan kamshine yabugi hancin fatima take ta lumshe ido sabida jin dadin kamshin.

 

“me ya zaunar dakai ne haka fadil?”inji gidado yana driving.

 

“wlh tambayoyine nasha kaga dole in tsaya in amsa kan abani”

 

“mtsssuu dan kawai zaka dauko yar ayki ake maka tambayoyin?”cewar gidado.

 

“eh wlh”inji fadil.

 

Itako hamshakiya mandiya fatima bata ma san sunayiba,dan har ga Allah kamshin da take shaka,yasanyata cikin wani farinciki mara misaltuwa,hakanne yasa ta saki gidado dake ta faman kiriniyarsa bata saniba.

 

Rarrafawa yayi yasauka akan kujerar,dan gidado rigimamme ne na ajin farko,ga kiriniya,shiyasa tafi goyashi dan kar yayi barna.

 

Gidado da fadil se hirarsu sukeyi,sannu a hankali,gidado karami yayi nasarar dafa kujerar direba yamike tsaye,hannunshi yake dagawa irin yadda yara keyi in suna jon nishadi.

 

Daga hannunshi keda wuya,se jikake fuf ya saukeshi da karfi abakin gidado babba da ke mgn da fadil,

 

Akan idon fatima hakan ta faru,a gigice tace.

 

“Gidado me yasa bakajin maganane?”tafadi gamida fincikoshi.

 

Da sauri gidado babba ya waigo bayan motar rai a bace jin da ya yi an ambaci sunanshi,

 

muje zuwa

 

surbajo for life.

 

 

GID’AD’O BA SHEGE

BANE

 

 

 

Zahra Muhammad Mahmud

 

 

 

Dedicated to Amina Maman Gidado.

 

 

13-14

 

 

Haka fatima taci gaba da zama agidan amatsayin me aykin dafa abinci.

 

Sosai take jin dadin zaman gidan,sede matsalarta dayace,itace ta rashin jin gidado,

 

Ya iya barna kamar dan bera,tanayin iya bakin kokarinta wajen ganin ta tsawatar masa amman a banza,kullum kamar sake ingizashi takeyi.

 

Halin gidado na rashin jine yasa,gidado babba ya tsaneshi,haka itama husna,ko kadan basa kaunarshi,shiko kamar ance ya nace musu,duk wani guri da suke zama yaron ya gama haddace gurin,

 

 

Yauma kamar kullum,gidado babba ne kwance cikin garden din gidan yana karanta jarida,yayin da gefe daya kuma juice ne yazuba a cup time to time yana dan kurba,sosai yake enjoying,din yanayin.

 

Goga na umma sarkin barna ne ya karaso gurin cikin tafiyar shi ta yaran dake koyon tafiya.

 

Ko kadan gidado babba beji zuwan gidado karami ba,shi ko karasawa yayi gurin da ya ajiye cup din juice din,be bata lokaci ba,ya dauka ya fara sha,yana cikin sha abunka da yaro se ya mayar dana bakinshi ciki,

 

Gaba daya na cikin cup din se yayi wani iri,shiko gidado babba,hannu ya mika kawai ya dauki cup din yakai bakinshi yafara sha ya kusa shanyewane  yafahimci dandanon lemun ya sauya,yanzu har  wani yauki yakeyi.

 

Yana kai dubansa cikin kofin yaga abun mamaki,burtsatsin miyau ne gashinan birjik cikin lemun sanz din da yake sha.

 

A gigice yafara waige waige,carab idonshi ya sauka kan gidado karami dake zaune yana masa dariya.

 

a fusace yayi kan yaron,ba kunya ba tsoron Allah ya wankeshi da marin da se da yaron ya tintsira,.

 

Ayko ya tsanyare da kuka,hakan yay daidai da zuwan fatima gurin,wacce ta jima tana neman gidadon.

 

Da gudu tayi kanshi,ta daukeshi,zuciyarta ta gama hassala,dan a rayuwarta ta amince ay mata komai,amman kar ayiwa dan amanarta,

 

“kai wanne irin jaki ne dabba mara tausayi?”cewar fatima cike da fushi me tsanani.

 

A duniya ran gidado be taba baci irin na yauba,

 

Yana waigowa kawai se ya rufeta da duka,yana fadin.

 

“ubankine jakin da ya barki kina yawon gantali har kika samo wannan shegen dan naki”

 

.”wlh GIDADO BA SHEGE BANE sede in ubankane shegen”cewar fatima dake kasa bakinta na zubar da jini.

 

wayyo zuciyar yan maza ta motsa,haka gidado yasaki kwanji yana bugun fatima,itama ko tasaki baki se ihu takeyi,iya karfinta.

 

Gaba daya ahalin gidanne sukayo garden din dan ganin abinda ke faruwa,harda mahaifin su  wanda be jima da shigowa gidanba.

 

Da kyar fadil da daddynsu da masu gadi suka kwaci fatima a hannun gidado.

 

 

Rai a ɓace daddynsu yace.

 

“Gidado kanada hankali kuwa?,taya zaka kama yar mutane kaita duka kamae kasamu jaka,ko baiwar kace ita?,me tayi maka?”

 

 

A kaida in ran gidado ya baci ko magana beson yi,dan haka koda daddynsa ke tambayarsa be iya bashi amsa ba.

 

Maida tambayar daddyn yayi gurin fatima dake durkushe tana ta faman gunjin kuka.

 

“ke yarinya me kika masa?”

 

A ranta tace.

 

“wlh be daki banza ba sena koya masa hankali,ta yadda ko sunana aka kira agabanshi seya firgita”

 

Amman a fili sake rushewa da kuka tayi inda cikin kukan ta fara cewa.

 

“Ni yar katsinace,nida gidado mun hadune a airport a Abuja,inda tundaga ranar muka kulla soyayya me karfi,sannu a hankali gidado ya fara yaudarata,harde yayi nasarar kawar min da mutuncina,wanda tun daga ranar ya maidani tamkar matarsa, koda nai korafi alkawarin aurena yayimin,ana hakane Allah ya bani ciki,inda iyayena suka koreni sanadin hakan har a makaranta ma seda aka koreni,koda  nazo gurinshi shima guduna yayi,cikin ikon Allah na haihu lafiya inda na haifi wannan yaron,nasa masa suna gidado ne sabida sunan mahaifinsane,kwatsam sega fadil yazo gurin abincinmu siyan abinci,tunda naganshi nasan naga gidado,dan sometimes lokacin muna tare da gidadon yana nunamin hotonshi,a hakade har sukaje da kansu suka daukoni zuwa gidannan,shine nazo yau ina masa tuni,gameda makomar danmu,shine ya rufeni da duka”ta  Karasa maganar cikin matsanancin kuka.

 

 

Gurin gaba daya ya kaure da salati,mummy rushewa tayi da kuka,yayinda dady ya kife gidado da mari,

 

Shiko ko ajikinsa murmushi yayi sannan yace.

 

“Tunda nakejin abarin shaiɗan ban taba sanin yanada mata ba se yau,ke kinyi kadan ki hadani da iyayena,niba mazinaci bane,ke kozanyi zina bazanyi da rikakkiyar karuwa irinkiba,tunda kince wannan shegen danane,to muje asibiti a aunamu a tabbatat”

 

Ido fatima tashiga warewa,dan tasan inde akaje asibitin karyarta ta kare.

 

Kowa ya gamsu da aje din inda mahaifinshi yace masa.

 

“Gidado,wlh tlh blh,mukaje aka tabbatar da cewa dankane wlh seka auri yarinyarnan,dan baka isa ka cuci yar mutane a banza ba”

 

Murmushi Gidado yayi yace,

 

 

“Wlh daddy inde ya tabbata danane,daga asibitin a zarce masallaci a daura mana auran”

 

 

Fatima cikinta har kartawa yake sabida tsananin tsoron da take ciki.

 

Mahaifin su gidadonne yakai dubansa gareta yace.

 

“ke kuma in mukaje aka tabbatar da karya kike masa wlh sekin mutu a prison,kin amince?”

 

 

Wayyo fatima,gaba  daya ta daburce,amman bata da zabin daya wuce ta amince din.

 

“Eh na amince”cewar fatima.

 

Daga haka gaba daya suka dunguma zuwa asibiti domin gwada gudado da gidado,

 

 

tofa,

 

 

 

muje zuwa

 

 

Surbajo for life.

 

 

 

GIDADO BA SHEGE

BANE

 

 

Zahra Muhammad Mahmud

 

Dedicated to Amina maman Gidado

 

15-16

 

Tunda suka tafi inbanda addua ba abinda fatima takeyi,tabbas tasan yau kwananta ya kare tunda tasan dole a gano karya takeyi.

 

Suna isa Asibitin,suka samu likitan daze aywatar da aykin

 

“likita,inaso kadubi girman Allah yayin wannan aykin kasanar damu iya gaskiyarka,banason ka boyemin komai”cewar daddy.

 

“insha Allahu zanyi tsakanina da Allah,”cewar likitan sanda ya mika hannu ya amshi gidado a hannun fatima.

 

Koda likita ya bukaci fatima ta taso ayi gwajin da ita carab gidado yace.

 

“Ay ita kowa yasan danta ne,nine tayiwa kazafi dan haka ni kawai zaka auna da kuma dan dan a tabbatar”

 

Murmushi likita yayi sannan yayi gaba gidado yabishi abaya.

 

Duk wani gwaji daya kamata ayi dan tabbar da danshine ko banashi ba anyi.

 

Fitowa sukayi zaman jiran results,

 

Fatima cikinta kartawa yake bada wasa ba,in kana kusa da ita har kararshi zaka dunga ji.

 

Likitan yadan jima sosai sannan ya fito hannunshi rike da sakamakon.

 

Hankalin fatima ne yakara tashi,

 

Bayan likitan ya zaunane,yafara bayani,yayinda dukansu suka maida hankalinsu gurinshi.

 

“Mun gudanar da gwaji na kwayoyin halitta wato DNA tsakanin gidado da kuma wannan yaro,inda sakamakonmu ya nuna mana tabbas gidado dan gidado ne,ba ko tantama”

 

A firgice gidado yamike yana duban likitan,fatima ma a firgice take dubansu duka.

 

“Lalle kai jakine bakasan aykinka ba,taya zaka dubi wannan shegen yaron ka alakantashi dani,?wlh karya kakeyi”cewar gidado kamar ze kaiwa mutumin duka.

 

Mummy itade kuka kawai takeyi,yayinda fadil da daddy suka kasa mgn.

 

Shide likita ko ajikinshi gaskiyarshi ya fadi.

 

“wlh ban yarda da wannan likitanba sede muje wani gurin”cewar gidado kamar zeyi kuka.

 

Daddyn beki ta gidadon ba,haka ya biye mishi sukai ta zagaya asibitoci,duk inda sukaje amsa daya ce,dan shine.

 

Ganin wahalar banza kawai sukeyine yasa suka koma gida.

 

wayyo duniya,gidado lokaci guda har ya rame,hawayene kawai kebin fuskarshi tashin hankaline karara akan fuskarshi,taya zaace danshine alhalin tunda yake ko a mafarki be taba kusantar wata mace ba,taya zaa ce danshine,

 

A falon gidan gaba daya suka taru,inda daddy yasoma da cewa.

 

“Gaskiya dayace gashi kuma tayi halinta,gidado kabani kunya wlh,duk tarbiyyar da muka baka amman ka iya saka mana da haka?ba komao kanka kayiwa ba muba,sede kasani,yanzu base anjima ba zan daura auranka da fatima,ko bayan raina ka saketa ban yafe maka ba,shasha kawai”

 

“Wayƴo Allah na daddy kamin rai,wlh ka aura min ita zan iya mutuwa,wlh niba dana bane ka yarda dani”cewar gidado cikin kuka me tsanani.

 

Har ga Allah yaba fatima tausayi,to amman bazata karyata kanta taje peison ba,abu daya ke daure mata kai taya akayi yazama dansa,in danshine to wacece uwarshi?.

 

“ni dama tunda naga yaron nan nasan nakane gidado,sabida hatta baccin yaron irin nakane,kai ko kamaninsa ma nakane,taya zaka  karyata zamantowarshi dannaka?kade ji kunya wlh”cewar mummyn cikin kuka.

 

“wlh ba da na bane”cewarshi yana kuka.

 

Waya daddy yaciro yakira wasu numbobi ba jimawa sega mutane sun shigo falon,maza

 

mummy barin gurin tayi ita da husna,yayinda fatima ta ɗauki danta itama ta shige daki,

 

Umartar mutanen daddy yayi dasu daura auran gidado da fatima.

 

Rokonsu gidado yakeyi amman ko takanshi basu biba haka aka daura masa aure da fatima,yayi kuka kamar ze mutu.

 

mikewa yayi yabar gurin zuwa dakinshi,kanshi yashiga bugawa da karfi,fadil ne yashiga yasameshi a haka,da sauri ya rikeshi,ayko rungume fadil din yayi yana kuka me tsuma ziciya.

 

itama fatima haka kukan takeyi kamar ranta ze fita,tabbas tasan ta cutar da gidado,shiyasa tausayinshi ya kamata,dan tasan tabbas sakamakon karyane,babu ta yadda zaayi gidado yazama dan gidado.

 

A can dakin mummy ma husna ce ke kuka kamar magaukaciya fadi take.

 

“wayyo Allah na mummy yanzu shikenan wata ta rigani mallakar yaya gidado as mijinta,bayan tsawon shekarun dana kwashe ina zaman jiransawayyo Allah na”tasake rushewa da kuka.

 

Hakuri mummy take ta bata gamida rarrashi.

 

muje zuwa

 

Surbajo for life.

 

 

 

GIDADO BA SHEGE

BANE

 

 

Zahra Muhammad Mahmud

 

Ina barar adduarku Allah yayiwa school mummyna  Fatima ismail yako rasuwa,a sanadin haihuwa,don Allah kusamin ita a addua Allah yajikanta yasa ta huta,yasa aljanna makoma,halinta nagari ya bita domin alfarmar Annabi S,A,W

 

Dedicated to Amina maman Gidado

 

17-18

 

Da kyar fadil ya rarrashi Gidado yadena kuka,amman zuwa lokacin tuni zazzafan zazzabi ya rufeshi da ciwon kai,ko ido be iya budewa.

 

Kwantar dashi fadil yayi sannan yakira number family doctor su,ba jimawa yazo yadubashi yabashi magunguna inda yayi musu karin bayani kamar haka.

 

“yana tattare da matsananciyar damuwa wacce ke barazanar hifar masa da hawan jini,so sekun lura dashi da kyau dan gudun faruwa hakan”

 

Sosai batun ya tsoratar da fadil,a zuciyarshi tadunga fadin.

 

“Anya yaronnan na bross ne kuwa?wannan damuwar daya shiga tayi yawa,inda nashinne baze damuba kamar haka,Allah ka bayyana mana gaskiyar wannan lamari”

 

Hakade yayiwa likitan godiya ya tafi,shi kuma ya mike ya shiga cikin gida dan yayi musu bayani.

 

Mummy ta tausayawa dan nata amman seta kira fatima tace mata.

 

“kije ki kula da mijinki bashida lafiya,”

 

kasa tashi fatima tayi,agurin karshema seta rushe da kuka,tausayin gidado babu wata jijiya ta jikinta wacce be ratsa ba,tayi danasanin abinda tai masa,da zata iya warware komai ba tare data samu matsala ba data warware.

 

“kije ki kula dashi nace ba kuka nace kiyiba”cewar mummy tana murmushi.

 

Mikewa fatima tayi,ta nufi dakin gidadon yayinda goga kiriniya yarigata yin gaba kai kace shi aka ayka

 

Fatima na fita fadil ya matso kusa da mummyn tasa yace.

 

“mummy kiduba lamarinnan fa ki gani,ni wlh gani nake yaron bana bross bane gaba daya ya daga hankalinshi fa”ya fadi cikin damuwa.

 

Murmushi mummy tayi ta dafo kafadar shi tace.

 

“Fadil kenan,yau da ace gidado zekai kara kotu wlh sena tsaya gaban kotu nabada shaidar cewa danshi ne,idan kamannin da yake da yaron kama ce,ay dabiun koyanr se an samu banbanci,amman gidado dashi da wannan yaron wlh kaji na rantse maka,babu wani hali guda daya da gidado yakeyi tana yaro wanda wannan yaron baya yinshi ni na haifi gidado dan haka nafi kowa sanin waye shi,kawaide muita addua Allah yabayya gaskiya har mugano tayadda akayi suka hadu har yay mata ciki”

 

Shuru fadil yayi yana tunani,gaba daya batun mummy ya dama masa lissafi.

 

Ita ko fatima a tsorace ta tura kofar tashiga,ta maida kofar ta rufe,ta jingina da kofar tana hawaye.

 

Shiko oga kiriniya,da gudunshi yaje ya haye kan gadon da gidadon yake kwance.

 

dukanshi yafarayi yana tsillo ajikinshi yana fadin.

 

“dada”nufinshi baba,amaganarsu ta yara.

 

tunda suka shigo dakin akan idon gidadon har sanda gidado karami yazo ya haye jikinshi duk yana ji,yade yi shurune.

 

Fatima ganin gidado karami se tsalle tsalle yake akanshi ne yasa tayi saurin karasawa gurin,ta mika hannu zata daukeshi.

 

ta daukeshi kenan taji an rike mata hannu,da sauri takai dubanta gurinshi gani tayi yana kallonta hawaye nabin fuskarshi.

 

janta yayi ta zauna shi kuma ya yunkura da kyar ya mike zaune,

 

Har zuwa lokacin hawaye bedena bin idonshi ba,itama kukan takeyi.

 

“Fatima meyasa kikamin haka?,na dauka nidake tun wancan lokacin dana miki cikin mun gam magana akan zaki zubar da cikin?,meyas baki zubarba fatima?,ko kin barshine dan kici muruncina?”cewar Gidado yana kallonta ido cikin ido.

 

Gaba daya fatima ta rude ta firgice,ido kawai take zarewa bakinta har rawa yake gurin fadin.

 

“wlh karya kakemin,ni ko me kama dakai ban taba gani ba se zuwana gidanku,wlh badani kayi wannan maganar ba,ni ba wanda yamin ciki barema na haihu,wlh karya kakemin”ta karas maganar tana kuka.

 

Shuru gidado yayi dan ya fahimci dawa zatai nama,cugaba da cewa yayi.

 

“karki maidani yaro mana,taya nidake mu hadu mu samar da yaronnan kizo kina wasu maganganu na dabam?”

 

Sake rushewa fatima tayi da kuka ta fara rantse rantse tana fadin.

 

“wlh karya kakemin,kamar yadda gidado yake ba danka ba haka nima wlh ba dana bane,dan haka kadena cewa kamin ciki wlh ni ba yar iska bace”takarasa cikin kuka harda share majina.

 

“to kinsan haka meyasa kikace dana ne?”

 

“na maka sharri ne sabida tsanar da kake nunawa yaron,amman wlh koni sharri akamin akace danane”

 

Dariya taga gidado nayi wacce tasa ta dunga binshi da ido,wayarshi taga yaciro daga cikin bargon,ya kunna.

 

Sega recording din hirar da sukayi da ita yanzu ta bayyana,tsorone matsananci yakamata,.

 

shiko mikewa tsaye yayi,yana dariya yace.

 

“karamar yar bariki,to gashi nadauki muryarki zanje na kunnawa Abbana ya ji wanda na tabbatar daga dakinnan se prison zaki zarce”ya karasa maganar yana  dariya.

 

Fatima ta kasa magana,tuni hawaye ya wanke fuskarta,

 

Shiko ko ajikinshi juyawa yayi ze fice daga dakin.

 

muje. Zuwa

 

Surbajo for life.

 

 

 

GIDADO BA SHEGE

BANE

 

 

 

Zahra Muhammad Mahmud

 

 

Ina barar adduarku Allah yayiwa school mummyna  Fatima ismail yako rasuwa,a sanadin haihuwa,don Allah kusamin ita a addua Allah yajikanta yasa ta huta,yasa aljanna makoma,halinta nagari ya bita domin alfarmar Annabi S,A,W

 

 

Dedicated to Amina maman Gidado

 

 

19-20

 

 

Da kyar fadil ya rarrashi Gidado yadena kuka,amman zuwa lokacin tuni zazzafan zazzabi ya rufeshi da ciwon kai,ko ido be iya budewa.

 

Kwantar dashi fadil yayi sannan yakira number family doctor su,ba jimawa yazo yadubashi yabashi magunguna inda yayi musu karin bayani kamar haka.

 

“yana tattare da matsananciyar damuwa wacce ke barazanar hifar masa da hawan jini,so sekun lura dashi da kyau dan gudun faruwa hakan”

 

 

Sosai batun ya tsoratar da fadil,a zuciyarshi tadunga fadin.

 

“Anya yaronnan na bross ne kuwa?wannan damuwar daya shiga tayi yawa,inda nashinne baze damuba kamar haka,Allah ka bayyana mana gaskiyar wannan lamari”

 

 

Hakade yayiwa likitan godiya ya tafi,shi kuma ya mike ya shiga cikin gida dan yayi musu bayani.

 

Mummy ta tausayawa dan nata amman seta kira fatima tace mata.

 

“kije ki kula da mijinki bashida lafiya,”

 

kasa tashi fatima tayi,agurin karshema seta rushe da kuka,tausayin gidado babu wata jijiya ta jikinta wacce be ratsa ba,tayi danasanin abinda tai masa,da zata iya warware komai ba tare data samu matsala ba data warware.

 

“kije ki kula dashi nace ba kuka nace kiyiba”cewar mummy tana murmushi.

 

Mikewa fatima tayi,ta nufi dakin gidadon yayinda goga kiriniya yarigata yin gaba kai kace shi aka ayka

 

Fatima na fita fadil ya matso kusa da mummyn tasa yace.

 

“mummy kiduba lamarinnan fa ki gani,ni wlh gani nake yaron bana bross bane gaba daya ya daga hankalinshi fa”ya fadi cikin damuwa.

 

Murmushi mummy tayi ta dafo kafadar shi tace.

 

“Fadil kenan,yau da ace gidado zekai kara kotu wlh sena tsaya gaban kotu nabada shaidar cewa danshi ne,idan kamannin da yake da yaron kama ce,ay dabiun koyanr se an samu banbanci,amman gidado dashi da wannan yaron wlh kaji na rantse maka,babu wani hali guda daya da gidado yakeyi tana yaro wanda wannan yaron baya yinshi ni na haifi gidado dan haka nafi kowa sanin waye shi,kawaide muita addua Allah yabayya gaskiya har mugano tayadda akayi suka hadu har yay mata ciki”

 

Shuru fadil yayi yana tunani,gaba daya batun mummy ya dama masa lissafi.

 

Ita ko fatima a tsorace ta tura kofar tashiga,ta maida kofar ta rufe,ta jingina da kofar tana hawaye.

 

Shiko oga kiriniya,da gudunshi yaje ya haye kan gadon da gidadon yake kwance.

 

dukanshi yafarayi yana tsillo ajikinshi yana fadin.

 

 

“dada”nufinshi baba,amaganarsu ta yara.

 

tunda suka shigo dakin akan idon gidadon har sanda gidado karami yazo ya haye jikinshi duk yana ji,yade yi shurune.

 

Fatima ganin gidado karami se tsalle tsalle yake akanshi ne yasa tayi saurin karasawa gurin,ta mika hannu zata daukeshi.

 

ta daukeshi kenan taji an rike mata hannu,da sauri takai dubanta gurinshi gani tayi yana kallonta hawaye nabin fuskarshi.

 

janta yayi ta zauna shi kuma ya yunkura da kyar ya mike zaune,

 

 

Har zuwa lokacin hawaye bedena bin idonshi ba,itama kukan takeyi.

 

“Fatima meyasa kikamin haka?,na dauka nidake tun wancan lokacin dana miki cikin mun gam magana akan zaki zubar da cikin?,meyas baki zubarba fatima?,ko kin barshine dan kici muruncina?”cewar Gidado yana kallonta ido cikin ido.

 

Gaba daya fatima ta rude ta firgice,ido kawai take zarewa bakinta har rawa yake gurin fadin.

 

“wlh karya kakemin,ni ko me kama dakai ban taba gani ba se zuwana gidanku,wlh badani kayi wannan maganar ba,ni ba wanda yamin ciki barema na haihu,wlh karya kakemin”ta karas maganar tana kuka.

 

Shuru gidado yayi dan ya fahimci dawa zatai nama,cugaba da cewa yayi.

 

“karki maidani yaro mana,taya nidake mu hadu mu samar da yaronnan kizo kina wasu maganganu na dabam?”

 

Sake rushewa fatima tayi da kuka ta fara rantse rantse tana fadin.

 

“wlh karya kakemin,kamar yadda gidado yake ba danka ba haka nima wlh ba dana bane,dan haka kadena cewa kamin ciki wlh ni ba yar iska bace”takarasa cikin kuka harda share majina.

 

“to kinsan haka meyasa kikace dana ne?”

 

“na maka sharri ne sabida tsanar da kake nunawa yaron,amman wlh koni sharri akamin akace danane”

 

 

Dariya taga gidado nayi wacce tasa ta dunga binshi da ido,wayarshi taga yaciro daga cikin bargon,ya kunna.

 

Sega recording din hirar da sukayi da ita yanzu ta bayyana,tsorone matsananci yakamata,.

 

 

shiko mikewa tsaye yayi,yana dariya yace.

 

“karamar yar bariki,to gashi nadauki muryarki zanje na kunnawa Abbana ya ji wanda na tabbatar daga dakinnan se prison zaki zarce”ya karasa maganar yana  dariya.

 

Fatima ta kasa magana,tuni hawaye ya wanke fuskarta,

 

 

Shiko ko ajikinshi juyawa yayi ze fice daga dakin.

 

 

muje. Zuwa

 

 

 

Surbajo for life.

 

 

GIDADO BA SHEGE

BANE

 

 

 

Zahra Muhammad Mahmud

 

 

Naji korafinku na rashin typing da nakeyi kamar da,kumin uzuri,ina typing ne idan banida wani abu muhimmi da nakeyi,so yanzu gaskiya inada uzuri,in na samu sarari zan dunga yi da yawan ina fatan kun fahimceni,

 

meenat kabeer pls am looking for you urgently

 

 

Dedicated to Amina Maman Gidado

 

nayi mistake na number a last page dina zansa 17-18 sena sa 19-20 duk dade na gyara amman yana da kyau na sanar daku so yanzu 19-20 zamu tashi

 

19-20

 

 

Da wani mahaukacin gudu fatima taje ta rungumeshi,kallo daya yay mata ya gane gab take sa ficewa daga hayyacinta.

 

Itako kuka take me tsuma zuciya,tana kankame dashi,daga karshe zubewa tayi akan guiwowinta ta rike kafarshi tafara cewa.

 

“Don Allah karka jefa rayuta acikin wani hali a karo na biyu,ka rufamin asiri,wlh nakusa hakura da dawainiya da yaron da ni kaina bansan iyayenshi ba,matsalar dana shiga asanadin tausayin yaron nan tana da yawa aciki harda rasa mahaifiyata”daganan ta kwashe duk abinda ya faru ta sanar dashi tundaga ranar da ta tsinci gidadon.

 

Sosai tausayinta ya ziyarci zuciyarshi,sede be gama gasgatata ba,hannu yasa ya dagota daga durkuson da tayi,se kuka takeyi,bin ta kawai yake da shanyayyun idanuwansa,a ransa yace.

 

“a haka de kamar gaskiya take faɗi amman tunda ta iya yimin sharri zeyi wuya ba wani tarkon takeson hadaminba”

 

Amman a fili cewa yayi.

 

“Naji labarinki amman ban gasgataki ba”

 

Kukan tane ya yawaita tana fadin.

 

“wlh da gaske nakeyi,ba karya nakeyiba”

 

Murmushi yayi ta gefen baki,sannan yasa hannunsa a aljihu ya dauko wayar da ya yi recording din ya kamo hannunta yasa a ciki ya furta a hankali.

 

“kisamin ita a charge,sannan ki gyaramin dakina kan nadawo kinji ko,kuma ban yarje miki kibar dakinba har se na dawo”yana kaiwa nan ya saki hannunta yasa kai yafice daga dakin.

 

Fatima shuru tayi tana tunani,Allah de yasa ba wata makarkashiyar ze shirya mata ba.

 

Kamar yadda ya bukata haka tasa wayar a charge,so uku tana yunkurin goge recording din tana fasawa,haka ta barshi bata goge ba,

 

Gyaran dakin tai masa me kyau,sannan ta nemi guri ta rakube,shiko dama gidado karami tuni yayi bacci a gurin.

 

 

Gidado babba da ya fita,motarshi Bugatty yaja yabar harabar gidan,tafe yake yana tunani,tabbas duk wata damuwa ta yaye daga zuciyarshi,shiyasa yasamu kwarin guiwar fita ma.

 

tunaninshi shine,taya ze tabbatar da cewa ba fatima ce ta haifi gidado ba?taya ze gane duk abinda ta fada masa gaskiyane.

 

a haka har ya isa gidan saida abincin da fatima tai ayki a da.

 

hajiya yasamu inda yay mata tambayoyi gameda fatiman,itako bata boye komaiba ta sanar dashi,harda yadda fatima tai fama da rashin ruwan nono wanda daga karshede da madara ta shayar da yaron.

 

Bayan yagama jin komai daga bakinta,motarshi ya koma ya nufi gida,sosai yayi mamakin yadda bakin fatima dana hajiya yazo daya.

 

Da wannan tunanin ya isa gida,yana parking,wayarshi ta fara ringing,da sauri ya dauka ganin daddyn shine ke kira.

 

Nemansa yake yi,dan haka kashe wayar yayi ya fito daga motar yanufi falon daddyn nasa.

 

Duka family din yasamu a falon,wato mummy,daddy,fadil,husna.

 

Guri yasamu ya zauna bayan ya gaida iyayen nashi.

 

Daddy ne yafara magana.

 

“Gidado banji dadin abinda ka aykataba,amman kaddararka ce wacce ni ban isa na hanata fadow kanka ba,tunda ni musulmine yazamarmin wajibi na yarda da kaddara,me kyau ko mara kyau,Allah ya kyauta gaba ya yafemaka kuskuren ka”

 

“Amin”cewar gidado.

 

murmushi mummy tayi sannan tace.

 

“ko dan nan gaba ku kiyaye yaudarar yayan mutane,dan bakusan inda sakamakon ze faɗo ba”

 

Fadil cikin mamaki yace.

 

“Bross nufinka yanzu ka yarda yaron nakane?”

 

Murmushi gidado yayi gamida dafa kafadar fadil din yace.

 

“ko ba nawa bane yanzu na amsheshi amatsayin nawa,tunda ya kasance dan matata ay nima yazama nawa”

 

Baki sake kowa ke kallon gidadon shiko ko ajikinshi,.

 

“to ina ka baro fatiman? tun dazu na ayketa gurinka amman bata dawo ba”cewar mummy.

 

Murmushi gidado yayi sannan yace.

 

“kai mummy nifa gaskiya alamu sun gwada samin ido zaku dunga yi nida matata,dan haka a shirya komai abani abata natafi gurin aykina da ita”

 

 

Duka mummy ta kaimishi gami da cewa.

 

“ina take nace?,mara kunya kawai”

 

“Tana dakina nasata tayi bacci”

 

Gaba daya falon dariya akeyi,amman banda husna da fadil,da gudu husna tabar gurin tana kuka,shiko fadil ba komai ya hanashi dariyaba illa.

 

 

Yafi kowa sanin wanene gidado,tabbas yasan baya fushi ya sauka one time batare daya dau matakiba,sannan gidado baya taba karbar abunda tun farko yaki karbarsa,komenene shi,

 

 

 

Haka de sukai ta raha,i junansu,inda daddy ya tsaida lokacin da zaayi hidimar bikinsu.

 

 

Daga gurin daddyn kai tsaye dakin shi ya nufa,inda yana shiga yagansu kwance a falo akasa ita da gidado karami,suna bacci,se rawar sanyi sukeyi kasancewar garin akwai hadari,iska ta fara kadawa,ga kuma sanyin ac.

 

Dukawa yayi ya ɗauki gidado ya shigar dashi Bedroom dinshi ya kwantar da shi akan gado,sannan ya dawo itama ya dauketa,yaje ya kwantar da ita akan gadon.

 

Se mamakin rashin nauyinta yakeyi,wacce a ido gata nan yar duma duma,

 

bargo yaja ya rufesu,sannan yaje ta rage gudun Ac,bin dakin yayi da kallo yaga ta gyarashi sosai,wayarshi ya dauka da yagani jone jikin chager,recording din ya duba yaga yana nan kamar yadda ya barshi,sosai yayi mamakin abinda ya hanata gogewa,wanda dama gwadata yayi yaga zata goge ko bazata gogeba.

 

Yana nan zaune ruwan sama ya fara sauka dan haka shima kwanciyarshi yayi ya shiga bargon,dan ko kadan gidado bayason sanyi irin na damuna dn daga masa hankali yake yaji yana bukatar mace a kusa dashi.

 

 

muje zuwa

 

 

Surbajo for life.

 

 

GIDADO BA SHEGE

BANE

 

 

Zahra Muhammad Mahmud

 

Hafsat marubuciyar mijin mum dinmu,ina matukar godiya da jin dadi na sadaukarmin da littafin, da kikayi Allah yabar kauna,ngd sosai

 

marubuciyar ni da zahra yakamata ki bayyanawa surbajo kanki gaskiya ay zumunci,kullum nemanki nakeyi,kinsa mutane sunki yarda bani nake rubutawa ba,pls inason ganinki aradu,wlh ina sonki sosai,dan duk wanda ke sonka kaima ka soshi,love you dear,i need to see you pls

 

Zahrammahmoud11@gmail.com

 

Dedicated to Amina Maman Gidado

 

21-22

 

Gidado wannan ne karo na farko daya fara hada gurin bacci da mace,dan haka jinshi yayi duk ya takura ya gaza sakewa.

 

Fatima baccinta take hankali kwance,sede hannunta na yawo tana shafawa tajiyo gidado karami,hakanne yasa hannunta ya sauka akan marar Gidado babba ba tare data saniba.

 

Numfashin Gidadone yafara sarkewa. Jin hannun fatima akan babbar harka,ido kawai yake warewa dan ko miyau ya kasa hadiyewa.

 

Itako batama san tayiba tunda taji hannunta kan abu kawai ci gaba tayi da baccinta a zatonta danta ta dafa.

 

Hmmmmm gidado farashi yafara tashi,dan dama ga sanyi ana yi,sosai ga kuma fatima tazo da sabuwar rawa,wacce tasa ya kame kam

 

Kasa jurewa yayi,dan koya fatima ta motsa hannunta ji yake kamar wasa take mishi,dadin da yake ji ne yasa ya kasa cire hannun nata.

 

Sannu a hankali ya matsa jikinta sosai,fuskarta ya kurawa ido,yana kallon kyan fuskar,ba abinda yafi burgeshi kamar dan karamin bakinta,ji yayi yana shaawar shan bakin.

 

Sannu a hankali ya dora bakinshi akan nata,yafara kissing,cikin bacci fatima ta fara jin bakon abu na ratsa ta,bude idonta tayi dan ganin ko menene.

 

Ganin gidado ne ke mata haka sosai ta firgita,kokarin kwace kanta takeyi amman be bata damar yin hakanba,ci gaba yayi da ayka mata sako,sanda hannunshi ya sauka kan kirjinta,daga shi har ita seda numfashinsu ya dan dauke,

 

Tunda ya fara wasa da kirjinta fatima jikinta ya mutu,sosai take jin daɗin hakan,dan haka batayi yunkurin hanashiba.

 

Sannu a hankali abubuwan ke kankama,harta kai cikinsu babu wanda wata sutura tai saura ajikinshi.

 

Da kyar gidado ya iya adduar saduwa da iyali,sannan ya fara kokarin cinma burinshi.

 

jin da yayi a rufene yasa yayi gaggawar dagowa yana kallon fatima wacce ta runtse ido tana addua dan ta fara jin azabar da duk wata kamilalliyar mace take ji.

 

Tsananin mamaki ne akan fuskar shi,fasa kusantarta yayi,ya murgina gefe,jawota yayi yaci gaba da wasa da ita har zuwa ya samu ya fitar da abinda ke damunshi.

 

Ya jima rungume da ita kana daga bisani ya nufi toilet yayi wanka ya fito daure da towel,fatima na ganinshi da sauri ta rufe idonta,dan fatima ko gari banza ita macece me matsananciyar kunya.

 

Murmushi gidado yayi,ya karaso bakin gadon ya yaye bargon data rufa dashi,dama kuma ba kaya ajikinta,dukunkunewa tayi tana rokonshi ya rufeta,amsa ya bata da cewa.

 

“wlh bazan rufe ki ba sekin saki jikinki,”

 

“wlh bazan iya ba don Allah kayi hakuri,”cewar fatima kamar me shirin yin kuka.

 

Sakin bargon yayi akasa sannan ya dauketa dukanta yayi toilet da ita,

 

Da kanshi yay mata wanka,Fatima kuka take bilhakki da gaskiya na takaicin wankan da yake mata,shiko ko ajikinshi,seda yatabbatar ya sulleta ya fice ya barta tayi na tsarki.

 

Yana fitowa ya samu sarkin kiriniya ya farka,da sauri ya isa gareshi ya daukeshi,ayko kamar jira ya shiga tsalle tsalle ajikin gidado babba.

 

Tausayin yaronne yafara ratsa zuciyar gidado gamida sonshi,yayinda gefe daya kuma son matarshi da tausayinta yagama zagaye ciki da wajen zuciyarshi.

 

Ya amince da fatima yanzu fiye da kanshi,tabbas ya yarda duk abinda ta fada masa gaskiya ne,

 

“Da yardar Allah fatima haduwata dake babu danasani tsakaninmu,zan maidake sarauniya acikin mata wacce babu irinta,ke mace ma kika iya jure duk daci sabida yaron nan bare ni danake namiji,zan zamewa gidado uban da babu irinshi,duk da yanzu na fara ji ajikina jinina ne amman bansan taya na samar dashi ba,”furucin gidado kenan a zuciyarshi.

 

Maida hankali yayi gurin wasa da danshi,har fatima ta fito wanka,daure da towel,ganinshi yasa duk ta daburce ta kasa kwakkwaran motsi,se sosa kai takeyi,

 

Ajiye gidado yayi ya karaso gurinta,ja da baya ta dunga yi yana binta har suka kai jikin bango,hannu yasa ya zagayeta a jikin bangon ya matseta sosai da jikinshi.

 

Runtse ido tayi ta kauda kanta gefe ganin yanufo bakinta,murmushi yayi yace.

 

“princess ni dinne kuma ba kyason gani,wato tunda na gama yimiki abun dadi dazu shine yanzu bazaki kalleniba,wato ko godiya ma bazakimin ba ko?”ya fadi sanda yayi nasarar hade bakinsu guri guda ya shiga sumbata,

 

yayinda ya rike kanta da hannu daya dayan hannun kuma yana kan mazaunanta.

 

Fatima tarasa dalilin dayasa takasa kwatar kanta,sam zuciyarta bata mata biyayya intayi yunkuri kwace kan nata,sabida dadin da takeji.

 

Kukan gidadone yadawo dasu duniyar da suka shiga,da sauri ya saketa yazo ya dauki gidadon.

 

itako da gudu tasa doguwar rigarta ta fice daga dakin,ta nufi nata.

 

Dubansa yakai kan pant da bra dinta data mance akan gadonshi,a hankali ya furta.

 

“princess kenan,wlh sena cire miki duk wata kunya tawa da kikeji,”

 

Shiryawa yayi,yayi kyau sosai,daukar danshi yayi suka nufi bangaren mummy,lokacin ana kiran sallar magrib.

 

muje zuwa

 

surbajo for life

 

 

 

GIDADO BA SHEGE

BANE

 

 

Zahra Muhammad Mahmud

 

kowanne dan adam yana da uzuri,so pls surbajo ma uzurinne yasha kanta don Allah kuyi hakuri,wlh uzurinne yamin yawa,ko hidimar yusuf jinta nake kamar ta yara biyar bare sauran ayyukaso pls in Komai yazama normal nima zan koma normal

 

Dedicated to Amina Maman gidado

 

23-24

 

Yana shiga falon mummy husna ya samu zaune tana kallo,baki sake take binshi da kallo ganinsa dauke da gidado a kafada,

 

Ajiye gidadon yayi sannan yace mata.

 

“ke bazakije kiyi sallah bane,kike zaune kina kallo?”

 

Yatsina fuska tayi sannan tace.

 

“period nakeyi”

 

Mamakin husna gidado yakeyi,sam bata da kunya irin ta mata komai fada masa takeyi kanta tsaye.

 

Juyawa yayi ya wuce masallaci,ita kuma ci gaba tayi da kallonta,gidado karami,kiriniyarsa yaci gaba dayi.

 

Zuwa can mummy ta sakko falon,da sauri gidado ya nufeta,dukawa tayi ya daukeshi tana masa wasa.

 

Takaicine ya cika husna,dan aganinta shege be dace ana masa hakaba.

 

Zaman mummy ba jimawa gidado da fadil suka shigo sun dawo daga masallaci,

 

Zama sukayi ana ta hira har zuwa sanda fatima ta gama abinci,

 

da yake su ɓasason cin abinci a dinning ne yasa ta zo ta dunga jere musu abincin a falon bayan ta shimfida ledar cin abincin.

 

Ganin yadda gidado ya kafeta da ido ne yasa duk ta daburce,wata kunya duk tabi ta kamata,da kyar ta iya gama jera abincin,tana gamawa husna tace cikin isa.

 

“amman de kinsan ni akan dinning nake cin abin,dan haka sekije ki jera min nawa nima”.

 

Mikewa fatima tayi da nufin aykata hakan,carab gidado ya ruko hannunta,sannan ya dubi husna rai abace yace.

 

“yaushe raini ya shiga tsakanina dake?har kece zaki ayki matata kece wa?bari kiji matukar zakisata ayki,to nima zaki iya sani,dan haka ki kiyayi kanki,bazata jera mikin ba”ya karasa sanda yaja fatima ta zauna.

 

Baki husna ta turo gaba,gamida mikewa tabar gurin tana kuka.

 

mummy shuru tayi bata kulasuba,dan inda sabo husna da gidado sun saba yin faɗa.

 

Fatima haka take zaune gurin kamar kasa ta tsage ta shige,duk yadda gidado yaso ta saki jikinta ta kasa yin hakan,daga karshema da gudunta ta bar gurin,ta nufi dakinta.

 

kwanciya tayi kan gadonta tana haki.

 

Mummy mikewa tayi,dauke da gidado karami ta nufi dakinta,ganin hakane yasa gidado ya mike yabi bayan fatima zuwa dakinta,

 

yana shiga,yamida kofar ta kulle,yanufi kan gadon da take kwance ta lumshe ido tana murmushi,sam bataji shigowarshi ba,

 

kwanciya yayi akan gadon ya rungumota jikinshi,yace.

 

“gani kusa dake ki dena tunani na” ya fadi yana lalubo bakinta.

 

Fatima rufe ido tayi ta lafe a kirjinshi,dan har ga Llah tunanin shi take yi,tana marmarin jin dumin jikinshi.

 

Haka yafara tsotsan bakinta,cikin salon daya dace.

 

Sannu a hankali fatima ta fara maidar masa da martani.

 

sun jima a haka suna kissing din juna,daga karshe,rabata yayi da rigar jikinta dan yaji dadon gabatar da wasanninsa.

 

Ganin abun na neman wuce gona da iri ne yasa fatima ta mirgine kasan gadon ta barshi akan gadon.

 

Da kyar gidado ya mike zaune,dan zuwa lokacin bayan shi ya fara rikewa.

 

“pls princess,kizo gareni,don Allah,wlh ji nake kamar zan mutu.”cewar gidado cikin dasasshiyar murya.

 

Sake dukunkunewa fatima tayi a inda take bata da niyyar zuwa gurin nashi.

 

Sakkowa yayi yazo gareta,jikinshi se bari yake kamar wani mazari,haka yay ta yi mata magiya,dan se a lokacin yake ganin shirmenshi na kyaleta dazu da yayi.

 

Duk yadda gidado yaso ta Amince dashi fafur taki yarda,haka Ya mike cikin fushi ya fice daga dakin yana jan kafa.

 

Yana fita yayi karo da mummy da tazo kawo gidado wanda yay bacci,

 

Be kulata ba haka ya fice,binshi tayi da kallo sannan ta shiga dakin,ganin fatima zaune ba rigane yasa kunya ta kama daga fatiman har mummyn kowa ya daburce.

 

Kwantar da gidado tayi a kan gado ta juya da sauri tabar dakin.

 

fatima kamar tai hauka dan kunya.

 

Tun daga lokacin gidado yadauki fushi da fatima,amman a zuciyarshi azabtuwa yake da hakan.

 

Itama anata bangaren ta damu.

 

kuyi hakuri da wannan,uzuri gareni.

 

Muje zuwa

 

Surbajo for life.

 

GID’AD’O BA SHEGE

BANE

 

 

 

Zahra Muhammad Mahmud

 

ku dunga yimin uzuri pls,wlh har tsoron hawa online nake,sabida pc chat,gwanda group ina clear shikenan,😜yau gani gareku kyauta,inde me duka ya lamunce

 

 

Dedicated to Amina Maman Gidado

 

 

25-26

 

 

Yau kamar kullum Fatima ta tashi tayi abinci kamar yadda ta saba,

 

Bayan ta kammala ta nufi toilet tayi wanka ta fito ta shirya,dan gidado karami tuni anmasa wanka a part din mummy,

 

Fitowa tayi,tanufi parta din mummyn domin shaida mata ta gama girkin,

 

Ta fara hawa step kenan,shi kuma gidado babba na sakkowa da dan gudun shi.

 

Ay fatima na ganinshi,a rude ta juya zata koma kasa tsautsayi yasa ta fadi ta fara gungurowa,da gudu yake binta ya rukota amman ina seda ta isa kasa,jikake tim.

 

Da kyar ta yunkura ta mike,jamin ya karaso ta gudu dakinta,tana kokarin kulle dakin ya tura kofar da karfi,ya shiga dakin.

 

Yana shiga ya fincikota ya mannata da kirjinshi,ya fara mgn cikin fushi.

 

“ke nifa iskancinki yafara isata,ko bomb ne ni iya gudun da zakiyi kenan domin tseremin,ko dan kinga na zuba miki ido,bafa tsoronki nake jiba”

 

Ita de ta runtse ido jikinta se bari yake,tama kasa bashi hakuri.

 

Kureta yayi da ido,se a lokacin yaga ciwon da taji  gishinta,har ya dn kumbura.

 

Janta yayi bakin gadon,ya zauna sannan ya dorat kan cinyarshi,a tsorace ta zauna,mulmula mata gurin yayi se kuka take masa na shagwab wanda ya haddasa masa kasala a jikinshi.

 

Kwantar da kanta tayi a kafadar shi taci gaba da rera masa kukan,tun yana daurewa harde ya gaza,dan arayuwarshi baya son kuka ko kadan,bare na princess din shi,

 

Dago kanta yayo yana dubanta,itama shi take kallo a karo na farko,sun dan jima a haka sannan yace mata cikin muryar rada,

 

“Baby menene kuma?”

 

Wasu hawayenne suka sake biyo fuskarta,sharr,murmushi gidado yayi dan ya fahimci ita kuka be mata wuya,

 

Sake shigewa jikinshi tayi,sannan tace cikin kuka.

 

“Ba kaine kake fishi da ni ba”

 

Shinshina wuyanta yayi sannan yace yana murmushi.

 

“Ba kya so ina fushin da ke ne?”

 

“eh”

 

“To baby ay kece ba kyajin magana shiyasa”

 

“kayi hakuri don Allah zan dunga ji”

 

Dariya yayi,waccr take kara masa kyau yashiga yimata cakulkuli,ayko ta shiga tuntsira dariya itama ,tana tsillewa.

 

Tunda ya fahimci bata so ya kusance ta ne yasa yasha alwashin baze sake neman taba sede in ita ta nuna tana bukata

 

Hannunta ya kamo suka fito falon inda suka samu kowa ya hallara,kunyace ta kama fatima ta shiga kicikicin kwace hannunta,ganin hakane yasa gidado rungumota gaba daya zuwa jikinshi,yajata da karfi zuwa cikin falon.

 

Kowa se dariya yake musu,dan dramer tasu abar dariya ce.

 

mummy cikin dariya tace.

 

“gidado zakaci megarinku fa,taya zakasamin diya agabane haka?”

 

Dariya yayi yace.

 

“mummy nifa ban mata komai ba kunyar da takeji ne na cire mata”

 

Sosai batun nashi yabasu dariya.

 

itade fatima tunda ta durkushe agurin bata cewa kowa kala ba a haka har aka gama cin abincin.

 

 

WAIWAYE

 

Amina da hauwau cikin saa suka kammala karatunsu,batare da sun sami wata matsalaba.

 

Bayan sun gama karatu,Hauwau tayi aure a keffi,da mijinta me suna Adam wanda ya kasance dan kasuwa,kuma matashi me jini ajika.

 

Adam na son hauwau ba karamin so ba,wanda har mutanen gari ke ikrarin ta mallakeshine,har mahaifiyar Adam ansha zuwa akai mata gulma,amman da yake Allah yasanya son hauwaun a zuciyarta sam bata yarda.

 

Auransu da shekara guda hauwau ta haifi danta na fari,sede Allah beyi rayayye bane tana haifarshi ya koma.

 

Yan Asibiti sunsha kallo dan Adam kuka hauwau kuka,dan sun gama sa ransu akan dan,dakyar aka rabasu da gawar yaron.

 

Haka suka zauna cikin jimami na rashin dan nasu,

 

Cikin hukuncin Allah shekara na zagayowa ta sake haifar yarinya ta mace son kowa kin wanda ya rasa.

 

 

Fadin irin murnar da sukayi da samun yarinyar abun baze faduba.

 

Ranar suna aka sawa yarinyar sunan kakarta suna kiranta d Afnan.

 

Rayuwar hutu dajin dadi sukeyi da yarsu.

 

Wacce sukeso kamar rai,ko kadsn basa son damuwarta.

 

 

Anata bangaren Amina itama tayi aure da wani hamshakin me kudi a jihar kaduna,mijinta ibrahim  nasonta itama tana sonshi basa son bacin ran junansu.

 

Sede matsalarta daya tunda tayi aure ko batan wata bata taba yiba,

 

Wannan shi ya fara haifar mata da matsala,dan dangin mijinne suka taso ta agaba,game da rashin haihuwarta.

 

Har kasar india sunje akan matsalar,sede binciken likitoci ya nuna lafiyarsu lau lokacine kawai beyiba.

 

Haka suka dawo kullum cikin bakin ciki take da damuwa,duk yadda ibrahim yaso kwantar mata da hankali,taki ta kwantar,

 

Sosai Amina take daga hankalinta,wanda ya janyo mata yawan yin kuka,

 

Se abun yayi kamar ya barta se ta sake dawo dashi cikin ranta.

 

 

Kullum adduarta Allsh ya bata haihuwa itams,ko zata hucewa gorin haihuwa.

 

Cigaban labari

 

Tun daga lokacin gidado da fatima suka shirya,ko yawaita wasa da ita yadaina,befi yamata kiss ba kawai ya kyaleta.

 

hakanne yasa fatima ta saki jiki dashi,wanda kullum setaje ta gyara mishi dakinshi sunyi hira,wani lokacinma acan take kwana,dan gidado karami yanzu mummy ta janyeshi daga gurinsu.

 

Kullum gidado takura kwakwalwarsa yake gurin son tuno masa tayadda akayi gidado yazama dansa.

 

kullum cikin wannan tunanin yake,daga karshe de fara sadaka yayi da adduoi akan Allah ya bayyana masa gaskiyar abinda ke boye.

 

 

Yau kwance yake yana bacci da Rana,a baccin nasa yafara mafarki,me tsansnin tsoratarwa,Fuskarta yake gani tana kuka,me tsuma zuciya,yayinda bayanta,wasu irin halittune ke kokarin kaita kasa har zuwa lokacin bata dena kallonshi tana kuka ba.

 

 

Zuwacan Abubuwan suka fara janta,a firgice ta kwallah kara tana kiran sunan shi.

 

“GIDADO!!!!!!!!!”

 

 

Arazane ya farka daga baccin,gumi ya gama jika mishi jikinshi,da gudu ya bude kofa yayi part din daddyn su wanda jiya ya dawo.

 

 

muje zuwa

 

 

Surbajo for life.

 

GID’AD’O BA SHEGE

BANE

 

 

Zahra Muhammad Mahmud

 

Dedicated to Amina maman gidado

 

27-28

 

Da gudu ya fada falon daddyn,jikinshi har bari yake ya nufi jikin daddy dake zaune shida mummy da fadil yana kuka.

 

A rude kowa ke tambayarshi abinda ya sameshi,amman ina yagaza magana se haki yake yi.

 

Ruwa me sanyi fadil ya kawo mummy ta bashi yasha bayan ya sha dinne yasamu kwanciyar hankali,

 

“gidado me ya faru dakai ka hargitse haka?”cewar daddy yana taba kafadar gidadon.

 

“Daddy mafarki nayi wata yarinya na kiran sunana cikin yanayi na firgitarwa,shine na razana”

 

Murmushi daddy yayi sannan yace

 

“kai de anyi rago wlh,daga mafarki se firgita,wa ya ce maka mafarki gaskiyane?”

 

Shide gidaɗo shuru yayi yana jin shi,amman yana da tabbacin ko shine yayi mafarkin hakan zeyi.

 

 

“Haba bros be a man mana,yazaka dunga yin abinda mata sukeyi,?”cewar fadil dake gefe yana dariya.

 

Duka Gidado ya kai masa yace.

 

“Ba gwanda ni ba,mage bata taba kaini ga kwanciya asibiti a uk ba”ya karasa maganar yana tuntsira dariya sosai harda kwanciya.

 

Dariya mummy tayi tace

 

“Bamu gane ba,yaushe mage ta kwantar da autana a asibiti ban sani ba?”

 

Dariya daga gidadon har fadil sukeyi,kowa na nuna kowa,harda kwanciya a kasa dan dariya.

 

Da kyar Gidado ya daure yadena dariyar,shiko fadil ko yayi shuru da zaran ya tuno zeci gaba da dariya.

 

WAYE GID’AD’O?

 

Alhaji Bukar Adam,shine sunan mahaifinsa,Hajiya Maryam Usman shine sunan mahaifiyarsa.

 

Asalinsu yan Asalin jahar Borno State ne,a cikin garin maiduguri.

 

Alhaji Bukar,ya kasance kanuri ne,yayinda Hajiya maryam ta kasance Bafulatana wacce zamane yakai iyayenta maidugurin aman su yan asalin jihar taraba ne.

 

Haduwarsu ta samo asaline sanda mahaifin Bukar ya rasu,inda maryam da iyayenta suka zo gaisuwa kasancewarsu makwabta ne.

 

Tun daga lokacin shakuwa ta shiga tsakaninsu me karfi,har takai kowa na danginsu yasan da alakarsu.

 

Ko kadan mahaifiyar bukar batasonshi da maryam tafi so ya auri kanuri kamar shi,

 

Suko iyayen maryam sunyi naam da bukar din sabida mutum ne shi nagartacce da kowanne mutum zeyifatan ya zama sirikinsa.

 

Duk yadda bukar yaso ya janyo raayin mahaifiyarsa ta barshi ya auri maryam amman ina fafur taki amincewa.

 

Kin amincewartane ya jefa Bukar cikin yanayi na damuwa da tashin hankali,wanda haksn seda ya janyo mas kamuwa da ciwon hawan jini.

 

Ganin tana gab da rasa tilon dan nata ne yasa ta amince da auransa da maryam amman bawai dan har zuciyarta tana son abun ba.

 

Anyi auran maryam da bukar cikin kwanciyar hankali,

 

Bukar bashida matsala mutumne me dadin zama haka itama maryam din,soyayya suke nunawa junnsu bata wasa ba.

 

Tsawon shekara biyu da auransu amman ko batan wata maryam bata taba yiba,wanda hakan ya janyo mahaifiyar bukar tafara fada akan sese ya kara aure,ita bazata amince da zama ba haihuwa ba.

 

Hankalin maryam yatashi da jin matakin da hajiya ke son dauka na mijinta yay mata kishiya.

 

Tun daga lokacin suka fara zaryar asibiti,ita da bukar inda likitoci suka basu tabbacin lafiyarsu ƙalau lokacine kawai beyiba.

 

Bukar da kanshi yaje yayiwa mahaifiyarshi bayani amman fafur taki amincewa.

 

A haka suka ci gaba da neman magani,mahaifiyarshi na masifa akan se ya kara aure har suka sake kwashe wasu shekaru biyun yazama shekara hudu kenan da auransu ba haihuwa.

 

Cikin hukuncin Allah a lokacin se Allah yaba maryam ciki,murna da farincikin da sukayi baya misaltuwa.

 

Mahaifiyar bukar tafi kowa murna da samun cikin dan arayuwarta tanaso taga jikokinta,kasancewar bukar din shi kadaine danta.

 

kulawa sosai marƴam take samu daga kowanne bangare,inda har cikinta yakai wata tara,duk wani tanaji na haihuwa,ba wanda baa tanada ba,sede kullum shuru kakeji,ba alamun nakudar ma.

 

Hankalin kowa yatashi ganin har maryam ta shiga wata na sha daya amman haihuwa shuru kakeji,

 

Asibitoci ba inda ba a kai maryam ba sede suce musu lokacin haihuwarne beyiba.

 

A takaice seda cikin Maryam ya shekara guda cib a jikinta sannan ta haifi sanralelen danta me kama da mahaifinsa.

 

Tunda ta haihu da yan uwan mamanta suka zo barka kowa in ya dauki yaron se yace masa.

 

“Hannu Gid’ad’o”

 

kasancewa an jima baa samu cikin shi ba,kuma da aka samu cikin seda ya shekara sannan aka haifeshi,shine dalilin da yasa suke kiranshi gudado.

 

Ranar suna yaro ya amsa sunan kakansa na gurin uba wato Adam,amman se aka ci gaba da jiransa gidado.

 

Duk wani gatan duniya gidado ya sameshi agurin mahaifiyar babansa.

 

Tunda aka haifi gidado kamar an haifi taki ga mahaifinsa daga lokacin dukiyarsa ta fara bunkasa kullum se karuwa takeyi.

 

Shekaru uku tsakani maryam ta sake haihuwa inda ta haifi namiji,

 

Aka s masa suna fadil,kakar yaran tafo kowa murna da samuwarsu.

 

Sannu a hankali arzikin bukar yaci gaba da bunkasa,yaranshi na girma arziki na bunkasa

 

Tun tasowar gidado da fadil akwai siyayya da shakuwa me tsabta a tsakaninsu,shiyasa ko makaranta guda daya sukeyi sede gidado yafi fadil aji kasancewar ya rigashi fara karatun.

 

Tun tasowar gidado mutum ne shi me tausayi,sede ko kadan beson raini,rashin son rainin nashine ma yajanyo ko laifi yayi baya bada hakuri dan kar arainashi,mutum ne shi me tsare gida,ko kadan beson raini.

 

in kaga dariyarsa da walwala to yana cikin family dinsa ne da zaran ya fita ze rikide,yakoma gidadonsa na aynihi.

 

Sabanin fadil,da kowa nashine,ko kadan be dauko halin gidado ba,sede shi akwai jan ajine.

 

Haka rayuwar gidado da fadil ta taso cikin kulawa ta musamman daga iyayensu,wanda a lokacin sun jima da baro maiduguri zuwa abuja

 

Bayan gidado ya kammala karatunshi na secondry school ne mahaifinshi ya kaishi UK domin yaci gaba da karatun shi acan.

 

A UK gidado ya fara karantar fannin tuka jirgin sama,wato filot.

 

Yana da shekara uku a Uk aka turo Fadil shima yayi karatu a makarantar su gidadon,inda shi kuma yake karanta,fannin mechanical engineering,

 

Zaman su kasar da ba tasu ba besa sun gurbata tarbiyyarsu ba,suna rike da addininsu riki bana wasa ba.

 

Husna yace ga kanwar mummy,wacce mahaifiyarta ta rasu  bayan ra haifeta,tun tana jaririya mummy ta dauketa taci gaba da kulawa da ita,har zuwa girmanta.

 

Se bayan ta girmane ta fahimci mummy ba mahaifiyarta bace.

 

Tun tasowar husna take kaunar gidado kamar rai,yayin da shi ko bemasan tanayiba,dan shi kokadan beba soyayta dama va vare tasamu gurbi a zucuyarshi.

 

Husna nason fada masa abinda ke ranta,amman tsoronshi ya hanata tayi hakan.

 

muje zuwa.

 

Surbajo for life.

 

GID’AD’O BA SHEGE

BANE

 

 

 

Zahra Muhammad Mahmud

 

 

Dedicated to Amina maman Gidado

 

 

29-30

 

 

Haka husna tai ta yunkurin sanar da gidado damuwarta amman tana kasawa.

 

ta kuduri aniyar sanar dashi sede duk abinda ze faru ya faru,amman ita ta gaji.

 

 

Kullum adduarta Allah yasa yazo hutu dan tafison suyi gaba da gaba ba wai ta waya ba,

 

Cikin ikon Allah kuwa yazo hutu,daga uk,husna tafi kowa murnar ganinshi.

 

Seda ya kwana biyu da zuwa hutun sannan ta nufeshi da maganar.

 

 

A garden din gidan ta sameshi yana shan iska.

 

“salam bross,”ta fadi cikin wata murya me jan hankali.

 

Ko kallo bata isheshiba bare ya bata amsa,dan ko sallamar a ciki ya amsa.

 

Jiki a sanyaye Ta nemi guri ta zauna,ta sake cewa.

 

“bross iska kake sha ne?”

 

 

“wuta nake sha”ya bata amsa batare daya dubeta ba.

 

Gabanta ne ya shiga dukan uku uku,dan ta lura yau tanbotsan a kusa suke.

 

Komawa tayi kalar tausayi sosai sannan tacd.

 

 

“Bross tunda na fara hankali,zuciyata ta kamu da sonka,nayi iya bakin kokarina wajen ganin na cireka a raina amman abun yaci tura,don Allah kataimakamin”ta karasa maganar cikin kuka.

 

mamaki ne sosai ya bayyana akan fuskar gidado,cikin zakuwa yakai dubansa gareta yace.

 

“yanzu husna har ke kinsan so?”

 

Da sauri ta gyada mishI kai a zatonta ze amsa mata ne.

 

Murmushi yayi sannan ya kara da cewa.

 

“kuma ke a zatonki kin isa aure?”

 

Da sauri ta sake gyada masa kai.

 

 

Kwantar da kanshi yayi akan kujerar da yake kai ya furta a hankali.

 

“ni kuma husna kinga bansan so ba,uwa uba ma ni ko auran ban isaba,to ya zamuyi kenan?tunda ke kinsan so,kuma kin isa aure?”

 

Sosai batun nashi ya bata mamaki,musamman cewa da yayi be isa aureba,mutumin dake da shekaru talatin,shine be isa aure ba.

 

“bross inde rashin iya so ne ni zan koya maka,batun baka isa aureba kuma zan jiraka,nide don Allah ka amsa kana sona”cewar husna data durkusa agabansa.

 

“da kaina zan koyawa zuciyata son abunda takeso,bana bukatar malami awannan fannin,batun ki jirani kuma nide ban saki ba,bance ki jirani ba,dan kar gaba kizo kice na yaudareki,so kuma ina miki irin na yan uwantaka,after all bawani bayan shi”

 

mikewa yayi yabarta agurin,

 

Sosai take jin dacin kalamansa a zuciyarta,amman ta kuduri aniyar zaman jiran nasa dan ita shi kadaine namijin dake burgeta a duniya kuma takeso da kauna.

 

 

Tun daga lokacin husna ta shiga damuwa wacce ta janyo har mummy ta fahimta.

 

Sa ta a gaba mummy tayi akan ta sanar da ita damuwarta,ayko bata boye mata ba ta sanar da ita.

 

hakuri mummy ta bata sannan ta shaida mata zata masa mgn.

 

koda mummy ta tuntubeshi abinda ya fadawa hisnan shi ya maimaitawa mummy dan shi baya boye abinda ke ranshi.

 

jin hakane yasa mummy tayi yunkurin fahimtar da husna amnan fafur taki fahimta,kuma taki sauka akan aniyarta ta jiran giɗaɗo.

 

Sati biyu tsakani gidado ya koma uk sabida wayar da fadil yake damunshi da ita.

 

koda ya isa airport fadil din yasami yazo tarbarsa,da murna suka rungume juna daganan suka dunguma zuwa gida.

 

Bayan gidado yayi wanka ya shirya,yaci abinci,fadiƙ yasa musu wani sabon film dayasa aka kawo masa,suna kallo.

 

cike da nishadi suke kallon,da yake gidado a gajiye yake kuma gashi dare yayine yasa ya kwanta akan kujerar da yake kai,tuni bacci yay gaba dashi ,shiko fadil ci gaba yayi da kallonsa,inda seda film yayi nisa,sannan aka nuno wata,jibgegiyar mage,baka me jajayen idanu tana cin naman wani jariri,

 

a tsorace fadil ya kashe tv,ya mike ya nufi dakinsa domin yayi wanka,ya shiga toilet din ya cire kayanshi.

 

ya fara sabawa jikinshi kumfa,kawai se ya ji kukan mage,ta window din toilet din,a tsorace ya Leka window din,ayko mage yagani kan katanga tana kokarin  dirowa cikin gidansu.

 

Da sauri ya daura towel ya fito daga toilet din,dan in akwai wani abu da fadil ya tsana kuma yake tsoro to mage ce.

 

cikin sanda ya shiga bedroom dinshi,yana waigewaige.

 

Shiko gidado bayan tafiyar fadil ya farka,koda ya farka,wutar falon ya kashe sannan ya Kunna tv da nufin zeci gaba da kallon sede ina tuni ya sake komawa baccin.

 

Sannu a hankali fadil ke sakƙowa zuwa falon,sede yana zuwa falon ya samu ba haske bakikkirin,ze koma kenan,kawai se fuskae magen ta bayyana akan fuskar tv,tana tauna naman mutum jini nabin bakin nata.

 

Jikin fadil rawa ya farayi,yayinda yaci gaba da jin kukan magen dake kan katanga.

 

A zabure ya nufi komawa dakinshi sede yana juyawa,yaƴ taho mu gama da magen, da wani mahaukacin gudu ya juya zuwa gurin gidado dake falo,kanshi ya fada yana ihu.

 

Itako magen,ta kofarsu ta baya ta shigo gidan bayan ta sauka akan katangae.

 

idon magen ne ya sauka kan magen tv tans gurnani dinnan irin na maguna,ayko itama take ta fara yi dan a tunaninta ta tv da ita take.

 

wayyo fadil,numfashinshi har ya fara rikewa,a rude gidado ya farka,idonshi ya sauka kan ta tv da kuma ta zahirin yaso yadan firgita,sede ya lura ba ta tv bace a fili b.

 

ita ko magen tana yin wata sufa a zuwan zata fada kan takwararta ta tv ay se ta fada kan fadil.

 

Wani dogon numfashi yaja ya zube kasa sumamme agurin.

 

A gigice gidado yayi kansa,kiran sunanshi yake amman ina yayi nisan zango.

 

 

Dan haka kwasarshi yayi zuwa asibiti a 360.hankali a tashw.

 

wasa wasa seda fadil yayi sati biyu cur a asibitin,sanadin mage.

 

Gidado dama in an samu keta an iya dariya dan haka,in ya tasa fadil a gaba yana dariya be denawa se ya gaji dan kanshi.

 

 

muje zuwa.

 

 

Surbajo for life.

 

GID’AD’O BA SHEGE

BANE

 

 

 

Zahra Muhammad Mahmud.

 

 

masoya kune silar yin murmushina,ako ina kuke nima ina kaunarku,ina muku fatan alkhairi,zan canja number dana ke whatsapp,nan da 24hours,so duk me abun fadi yayi gaggawar fadi kamin na sauya din,kar kice na saki a group,dan simcard dina ya cika,09068360016,itace number real surbajo,dayawa mutane na chat dani but sunki su yarda nice yanzu de ga number nanan zata bar ayki nan da 24hours nagode

 

Dedicated to Amina Maman Gidado

 

 

31-32

 

 

Duk wani motsi na fadil gidado se yayi dariya,

 

Tun fadil na daurewa har yazo ya gaza in gidadon na masa dariya shima se ya tayashi.

 

A haka har gidado ya kammala karatun shi,inda yasamu ayki a Kamfanin jiragen sama na Etihad ,shi kuma fadil na ci gaba da karatun shi.

 

Duk sanda ya samu hutu yake zuwa,nigeria,to hakan ce ta faru wannan karon ma,fadil ya kammala karatu,shi kuma gidaɗo  ya samu hutu,hakanne yasa suka taho nigeria tare,

 

CIGABAN LABARI

 

 

Tun daga ranar da gidado yay mafarkinnan shikenan mafarkin ya zamar masa farilla kullum se yayi.

 

Gaba daya hankalinshi ba a kwance yake ba hakanne yasa ya shiga yin sadaka da rokon Allah akan ya bayyana masa maanar mafarkin.

 

Fatima ta damu sosai da halon da ya shiga,itama tana taya shi adduar akan Allah ya kawo sauki cikin lamarin.

 

Da misalin karfe goma na dare,gidado ne kwance akan makaken gadon shi na alfarma yana bacci.

 

cikin baccin nasa kamar yadda ya saba,yauma mafarkinta yake,sede da banbanci ba kamar wadda ya saba yi bane,

 

Na yau zaune yake cikin jirgi a bangaren first class,yarinyar ta shigo ita ma,cikin shigar alfarma ta zauna a kusa dashi tana ta masa murmushi.

 

Dai dai nan ya farka daga baccin,wani gumi ne ya shiga karyo masa,jikinshi na rawa,tabbas Allah maji roƙon bawa ne,duk abinda ya faru a baya ya dawo cikin kwakwalwar gidado,wanda dama shi ya roki Allah ya mantar dashi kuma Allah ya amsa rokon nasa yanzu kuma ya rokeshi ya tuna masa kuma ya amsa masa.

 

Ranar gidado be iya yin barci ba,har garin Allah ya waye,kwana yayi yana sallah,

 

Washe gari da wuri ya nufi,cikin gidansu,inda ya bukaci kowa na gidan ya hallara ze basu labarin jarabtar data fada masa shekarun baya da suka wuce.

 

 

Kowa ya hallara har fatima da husna suma suna gurin.

 

Daddy ne yace.

 

“To muna sauraronka”

 

Hawayen da suka zubo masa ne ya share sannan ya fara basu labarin kamar haka.

 

 

Kamar yadda kuka sani ina aykine da kamfanin jiragen sama na Etihad a matsayin captain.

 

Wata rana Nida abokan aykina Umar hassan,da kabir hamza,mun dauki fasinjoji daga uk zuwa dubai,bayan mun sauka a airport,se kuma  aka sake bamu fasinja daga dubai zuwa uk.

 

mun tashi kenan se kaina ya fara yimin ciwo me tsanani,wanda hakan yasa  na nemi excuse a gurin abokan aykina.

 

Da yake,first class ba bu fasinja aciki sosai,shiyasa na je can kawai na kwanta,

 

Ina kwanciya ba jimawa,sega wata yarinya budurwa ta shigo fuskarta dauke da murmushi ta nemi guri ta zauna.

 

Zamanta ba jimawa,muka fara jiyo hayaniya acan cikin jirgin,da sauri nayi karfin halin mikewa na leka,

 

Abunda na gani sosai ya firgitani,wasu mutanene,sunkai su takwas,rike da bindigogi sun rutsa fasinjojin cikin jirgin,atakaice de yan fashi ne,sanye cikin bakaken kaya sun rufe fuskokinsu,tayadda bame ganesu.

 

Guri guri suke bi suna kwace kudin hannun fasinjojin,suna tarawa acikin wata jaka.

 

Na firgita matuka da ganinsu,dan ban taba tsammanin,zaa samu me shigowa da makami cikin jirgi me matakan tsaro kamar na etihad airways ba.

 

A rude na juya zan koma se ji nayi an dora bindiga akaina,ahaka aja ingizoni zuwa inda yarinyar nan take.

 

Wani cikin yan fashinne yace cikin harshen turanci.

 

“Kai in banda munafunci kana captain uban me ya fito dakai nan?”

Nide ban ce musu komai ba,

 

Can daya ya hango wannan kyakkyawar yarinya dake,tsugunne jikinta se rawa yakeyi.

 

Da sauri ya isa gurinta,ya cafko ta.

 

cikin tsoro take ta yunkurin kwatar kanta,sede yaki sakinta,hakanne yasa ta dokeshi a gabanshi wanda da sauri ya saketa,ya rike gurin.

 

ita kuma da gudu tayo gurina,ta rungumeni tana kuka.

 

Mikewa mutumin yayi yazo ya fincikota yana fadin.

 

“Tunda kika daki sandar girma dole kema sandar girma ta dake ki”yana kaiw nan yafara rabata da suturar jikinta,itako se ihu take tana fadin,

 

 

“ni ku kyaleni don Allah kar ku ci mutuncina,bawan Allah ka hanasu don Allah”ta karasa maganar tana kallona tana kuka.

 

Ta maza nayi na kwace yarinyar na boyeta bayana,

 

Ayko hakanne ya fusata su,se gani nayi sun saka rigar saukar lema,sannan sukace.

 

“Tunda mu ka hanamu mu kwashi gara,to kai yazama wajibi ka kwasa,in ba haka ba,zamu kashe suran direbobin da kai da kuma ita,mu kuma mu sauka,kaga daga jirgin har mutanen ciki sunansu konannu”

 

Kabir hamza ne ya shigo first class din,dan duba lafiyata,dan tuni sun buga waya,sun sanar da cewa cikin jirgi akwai matsala.

 

Yana shigowa aka rutsa dashi,jikinshi se bari yake,

 

Gaba daya fasinjan dake cikin first class din mutum biyar ne.se ni da kuma kabeer da tsautsayi ya shigo dashi.

 

Duk wata magiya babu wacce ba muyi musu ba amman sunki yarda,sunce dole sena kwanta da wannan yarinya.

 

Ganin bazasu yarda bane yasa nace.

 

“zanyi abunda kuka bukata amman don Allah kubari a daura mana aure nida ita in yaso se inyi abinda kuka bukata”

 

Da har sunki amincewa,sekuma daya daga cikinsu yace,

 

 

“mun amince,dan burinmu kawai,ashigi babynnan tunda bata da kunya”

 

cikin first class din akwai mutane biyu maza musulmai,da kabir na uku,jikina na bari na ciro kudi a aljihuna wanda bansan ko nawa bane,na mikawa yarinyar amamsa tayi tana kuka,jikinta se rawa yake.

 

Take kabir yay min wakilci,daya acikin musulman guda biyu na cikin gurin yayiwa yarinyar waliyyi,dayan kuma ya daura auran,acikin abunda be wuce mintuna goma ba.

 

Haka suka sa na afkawa yarinyar mutane,wanda kuma nine mutum na farko daya fara tarawa da ita,nayi kuka nayi bakin ciki,har Alƙah wadai nayi da kasancewata acikin jirgin.

 

Akan idonsu komai ya wakana sun rutsamu da bindigogi,se dariya sukeyi,itako yarinyar,tuni ta sume.

 

A tsorace na ɗagata,sede sam bata numfashi.

 

Suko ficewa sukayi suka barmu,hatta kabir shi kanshi kuka yakeyi.

 

suna fira,suka bi duk wata camera ta cikin jirgin suka kashe,sannan suka kashe fitilun cikin jirgin duhu ya bayyana ciki sabida tafiyar dare ne.

 

Cikin hikima suka cire marsk din da sukasa a buskarsu da safar hannun suka kuma zubar da bindigogin akasa,suka nemi guri suka zauna.

 

 

Cikin yardr ubangiji umar ya saukar da jirgin lafiya,a airport a uk.

 

Sede tuni jamian tsaro sun yiwa jirgin kawanya.

 

haka akai ta checking,na fasinjojin,wanda cikin yardar Ubangiji aka kama mutanen,ta hanyar camerar da ta daukesu sanda suke saka marsk a fuskarsu a toilet na cikin jirgin.

 

 

Nide ban bi takansu ba dan sun riga da sun gama cutata,haka yan jarida sukazo kanmu nida yarinyar da aka gunguro agadon daukar marasa lafiya,take na tsaya rai abace nace musu.

 

“Bana bukatar ku yada abunda ya faru dani a media,in kuma daya daga cikinku yayi yunkurin aykata hakan wlh kotu ce zata rabamu”

 

 

ina kaiwa nan nabar gurin,da yake kasace datasan hakkin dan adam,take suka gige rohoto akaina da matata ta cikin jirgi.

 

Asibiti aka kaita,duk wani taimako daya dace su bata shi suka bata.

 

Ta farfado inda na taimaka mata tayi wanka,se kuka takeyi,tana share hawaye.

 

Wasa wasa seda mukayi kwana uku a sibitin ni nake kulawa da ita, a rana ta ukunne ta warke sosai.

 

inda na bukaci ta sanar dani sunanta da kasar data fito.

 

Murmushi kawai tayi tace min.

 

“Kai ya sunanka daga wacce kasa ka fito?”

 

“Gidado sunana daga nigeria”

 

“Gidado”ta maimaita sunan,se kuma tayi shuru.

 

 

Duk yadda naso nasan wacece ita fafur taki yarda,daga karshe kuka tasamin dole na kyaleta.

 

 

Washe gari likita ya sallameta,dakaina na daukota a mota,inda nakaita gidanmu nida fadil,na gabatar wa fadil ita amatsayin sabuwar maaikaciyarmu ce a kamfanin etihad,zata kwanane gobe zata wuce masaukinta.

 

 

Sosai fadil ya karramata,har zuwa washegari dana ɗauketa zan kaita masaukinta,sede fafur taki amincewa wai sede na ajiyeta a bus stop ta hau bus.

 

Bayan na kaita bus stop dinne harta bude murfin motar seta juyo gareni tana murmushi ta kama hannuna tasamin wani zobe tace.

 

“na bakane dan wata rana ka tuno kataba yin aure na tsawon kwanaki hudu a rayuwarka,”

 

Shuru nayi kawai ina kallonta,sam na kasa mgn.

 

wayarta ta ciro ta dora kanta akan kafadata ta daukemu hoto kala kala.

 

sannan tace.

 

 

“To gidado muna shirin rabuwa amman baka sake niba ko so kake naita yawo da auranka?”

 

 

Haka kawai naji banson rabuwa da ita,amman tunda ta matsa haka na saketa saki daya,na bata kudi masu yawa,sannan mukai sallama nida uta muka rabu wanda har yanzu ban sake ganin ta ba.

 

To se yanzu na lura da kyau da kamannin gidado karami wlh murmushinshi irin natane haka ma kukansa,duk irin natane.

 

Tunda haka ta faru nakasa samun natsuwa a zuciyata hakanne yasa nadunga sadaka da rokon Allah akan ya mantar dani duk abin da ya faru domin na zauna lafiya,

 

Allah ya amshi addua ta inda koda wasa ban taba tuno abun ba,

Bayyanar gida

do a matsayin danane yasa naci gaba da rokon Allah ya bayyana min gaskiya,to shine jiya nayi mafarkin yarinya wanda hakanne yasa na tuno komai da ya faru.

 

 

ya karasa basu labarin cikin kuka.

 

 

Kowa na ɗalon kukan yakeyi,dan tsananin tausayin su.

 

Sede kuma kowa yashiga mamaki gami da rudu,tun da gidado yace gidado karami na kama da matarsa ta jirgi to ita kuma fatima ya take da yaron?

 

 

muje zuwa.

 

Surbajo for life.

 

GIDADO BA SHEGE

BANE

 

 

Zahra muhammad mahmud

 

i really sorry masoyana don Allah kuyi hakuri da barinku da nayi jiya idonane ya fara ciwo shiyasa

 

Dedicated to Amina Maman Gidado

 

33-34

 

Falon ne yayi tsit sabida kowa ya tafi tunani,se zuwa can daddy yace.

 

“munji bayaninka kuma mun gamsu,dashi,Allah ya bayyana wannan yarinya dan musan abinda ya shige mana duhu”

 

Kowa haka ya dunga jajantawa gidado.

 

“muna so fatima tai mana bayanin inda tasamu wannan yaro”cewar mummy.

 

Ayko ba musu,cikin kuka fatima ta kwashe komai da ya faru ta shaida musu.

 

Sosai suka tausaya mata,gamida yimata jajen rasuwar mahaifiyarta.

 

“Ya kamata Ka shirya ka koma gurin aykinka da iyalinka,hutun ya isa haka”cewar daddy yana kallon gidado.

 

Kukan husnane ya maida hankalinsu kanta,inda cikin kukan taje ta kama kafar daddy tana fadin.

 

“Daddy son bross ze kasheni,don Allah kasa gidado ya aureni,wlh ina sonshi,kuma na fada masa yaki amincewa dani,don Allah kataimakamin wlh zan kashe kaina in be aureni ba”ta karasa maganar cikin matsanancin kuka.

 

Kowa mamakin maganar yakeyi,su fatima ko iyayen kishi,tuni maganar ta kawo mata wuyanta,

 

gidado ranshi ne ya baci da abinda husnar tai mishi agaban mahaifansa.

 

murmushi daddy yayi,sannan yasa hannu  ya dago husnar yana dariya yace.

 

“yanzu ke akan yayan naki kike kuka?to share hawayenki,tunda kin tabbatar da kina sonshi,zan aura miki shi”

 

A razane gidado ya ɗago yana  duban daddy,bakinshi har rawa yake yace.

 

“daddy..”dakatar dashi daddyn yayi sannan yaci gaba da cewa.

 

“Sati me zuwa zaa daura auranku,in yaso sati na sama se ku tafi uk din duka na gama magana”

 

“Alhaji bafa a yiwa namiji auran dole,taya zaka aura masa abinda baya so,don Allah kabar maganar nan,don Allah”cewar mummy cikin damuwa.

 

“na gama magana nace”cewar daddy,daya mike yabar gurin,dauke da jikansa.

 

Hannu gidado ya dora akai kamar zeyi kuka,dan bakin ciki,itako husna harda rawarta ta mike tabar gurin.

 

Fatima tafi kowa shiga damuwa cikin lamarin,da kyar ta iya mikewa ta nufi dakinta.

 

Tana shiga ta fada kan gadonta tana kuka.

 

“Wanne iein son kai ne wannan,aure ko tarewa ban yiba acw anmin kishiya,na shiga uku ni fati,wlh bazan iya zama da kishiyaba,musamman husna da bata kaunata”

 

Sune zantikan dake fitowa daga bakin fatima tana kuka.

 

A falo ko mummy da fadil ne suka sa gidado a gaba suna bashi hakuri,dan zuwa lokacin tuni ya fara kuka,dan yasan mahaifinsa kaifi dayane,baya sauya magana.

 

Dakyar suka samu yayi shuru,mikewa yayi yabi bayan fatima,yana shiga dakin ya jingina da kofar yana kallon yadda take kuka,abun na taba zuciyarshi,dan yasan tabbas baa mata adalci ba.

 

Takawa yayi a hankali ya isa inda take,kamota yayi ya rungume,a jikinshi,cike da masifa fatima ta shiga kwace jikinta,tana fadin.

 

“sake ni mayaudari kawai,ay dama na jima da sanin baka sona,jikina kakeso,dama can husna kakeso shiyasa ka kasa yiwa daddy bayani akan baka sonta”taci gaba da yin kukanta.

 

Dafe kai gidado yayi,zuciyarshi na mishi kuna,se yanzu ya yarda tabbas mata nada kishi,dan maganganun fatima sun sosa ranshi.

 

“princess don Allah ki saurareni,wlh babu soyayya tsakanina da husna,ko kadan bana sonta pls karkimin haka don Allah,”

 

“baka da abun fadamin na yarda,dama tashi kayi ka ficemin daga daki,tun kamin arubuta sunanka ajerin makaryata,dan komai ze fito daga bakinka karya ce”cewar fatima tana kuka.

 

Ganin bazata saurareshi bane yasa ya mike ya fice daga ɗakin.

 

kifewa tayi taci gaba da kukanta,dan fatima macece me kishi me zafi,har addua take akan Allah ya yaye mata.

 

Gidado ya rasa inda zesa rayuwarsa ga auran dole gashi fatima na fushi dashi,

 

a haka har lokacin da majaufinsa ya diba yayi aka daura auransa da husna,auran daya samu hallarta mutane da dama.

 

inda shagali sosai akayi,na auran,fatima a ɗaki ta rufe kanta dan gani take wani abunma da biyu ake mata shi.

 

Bayan angama taro kowa ya watse, ne ta bude kofar,zuwa lokacin kowa ya ganta ze dauka ta shekara ne tana ciwo sabida fita hayyacinta da tayi.

 

Mummy sosai take tausayawa fatima,sede duk son da take mata bekai wanda takewa husna ba,dan husna jininta ce.

 

gidado ko ba baka se kunne,duk yabi ya susuce sekace ba ango ba,damuwarshi kawai fatima da taki yarda su hadu.

 

Husna farincikin da take ciki abun be misaltuwa,dan ta cika burinta,na mallakae gidado,saura ta rabashi da fatima.

 

Daddy ne ya tarasu yay musu waazi dukansu akan su zauna lafiya,

 

inda yaja kunnen gidado akan yayi adalci a tsakanin matanshi.

 

A haka akayimusu visa dukansu,harda gidado karami,inda mummy ta basu daya daga cikin masu aykinta,dan ta dunga kula da gidado karami,me suna Ligido

 

Ligido sanda taji da ita amasu tafiya uk,har kusan suma tayi,dan farin ciki,

 

Kamin su tafi daddy yasa angyara daya daga cikin sauran gidajensa na uk,an zubawa kowacce kayan daki na gani na fada,abun se wanda ya gani.

 

Ranar tafiya,haka suka rankaya,zuwa airport,jirginsu ya daga se uk.

 

Kuyi hakuri da wannan pls.

 

muje zuwa

 

Surbajo for life.

 

GIDADO BA SHEGE

BANE

 

 

 

Zahra muhammad mahmud

 

 

Dedicated to Amina Maman Gidado

 

 

35-36

 

 

UK

 

 

Sun isa da safe,kowa cikinsu ya gaji,gidado karami,tuni yayi bacci.

 

Husna se wani langabewa take acikin gidado,ita ga me miji.

 

A haka suka nufi motar da tazo daukarsu,da sauri fatima ta bude gaba ta shiga.

 

Husna da ligido da gidado suka shiga baya,sam gidado beji daɗin abinda tai masa ba,amman ya cinye be nuna mata ba.

 

Koda suka isa gidama haka,inda yace fatima ta zabi bangarenta,ta tsaya bakin kishinta wai se ta ja aji ta zaba.

 

Ganin haka ne yasa husna cewa.

 

 

“Bross nide fitsari nakeji,dan haka ni nazabi cancan dan bazan iya jiraba”tana kaiwa nan ta nufi wanda yafi kusa dana gidadon,wanda a zuciyar fatima shi take da burin zaba,amman bakin kishi yasa tai nauyin baki.

 

Gidado be hana husna ba,sabida ta fisu gaskiya,bakin ciki ne yasa fatima ta samu guri a falon ta zauna,rai a bace.

 

Ligido ma tuni ta nemi dakin ta ta shige,rike da gidado karami.

 

Gidado bin fatima yayi da kallo,wacce bata ma san yana yiba,ta cika ta tumbatsa,kawai.

 

Wucewa yayi shima dakinshi,dan ya lura fushi take sosai.

 

Tsawon awanni kowa yayi a dakinsa yana hutawa,amman banda fatima da kishi ya dabaibayeta,ya hanata motsawa.

 

Tana nan zaune a falon har yamma tayi bata tashi ba,gidado ne ya fito,da nufin zuwa ya dubota.

 

turus yayi yana binta da ido sanda ya sameta zaune a falon kamar yadda ya barta.

 

Karasawa yayi gurinta ya tsuguna,ya dora hannayensa akan cinyarta,ya langabar dakai,kamar me shirin yin kuka yace a tausashe.

 

“princess nine fa,meyasa kike azabtar dani da fushinki,akan laifin da ba nawa ba?don Allah kiyi hakuri,ki taso muje daki,pls”yayi maganar kamar zeyi kuka.

 

Harara fatima ta watsa masa,sannan ta ture hannunsa akan cinyarta,tace rai abace

 

“a kanka nake zaune da zaka zo ka sani a gaba akan se na tashi,?to babu inda zani”ta karasa maganar cikin murguda masa baki.

 

Murmushi yayi ya mike,ya tattare hannun rigarshi.tuni tsoro ya bayyana akan fuskar fatima ta fara ja da baya,tana fadin.

 

“To me nayi maka kuma da zaka dakeni?”ɗmdan ita duk zatonta dukanta zeyi.

 

Dariya yayi mara sauti sannan ya karasa inda ta rakube,yasa hannu ya dauketa cak,ya nufi dakin ta da ita.

 

Suna shiga ya sauketa ya janyota jikinshi yace.

 

“Kina abu se kace yarinya,bakisan kina da kishiya bane a gidan,mata fa basaso kishiyarsu tasan tsakaninsu da mijinsu,amman ke kin zauna a falo se zuba kikeyi”ya fadi yana jan hancinta.

 

Kuka tasa mishi,gamida doke hannun shi daya ja mata hancin,tace cikin kukan.

 

“Ay dole kacemin hakan,tunda yanzu kayi amarya,kuma yar uwarka,ba dole kaita rawar kafa ba,nide wlh bazan zauna adakin nan ba,ko de ka bani naka ko kuma ka maidani nigeria,inci gaba da sanaata ta saida abinci”

 

Dariya ce ta kubcewa gidado,ayko yashiga kyalkyalata harda kwanciya a kasa.

 

Fatima tsayawa tayi tana duban jikinta dan taga abinda yakewa dariyar amman bata gani ba,nufarshi tayi tana duka tana fadin.

 

“wato ga mahaukaciya ko,wlh da gaske nake yi,sena koma seda abinci abakin titi wlh”

 

Janta yayi ta fada jikinshi,zatayi magana ya hade bakinsu guri guda ya shiga ayka mata sako,tuni ta mance da bacin ranta,seda taji ze zarce ne ta kwace kanta tana haki.

 

Bin ta da ido gidado yayi,dan amatse yake,sosai amman alkawari ya dauka baze kusanceta ba se lokacin da taso dan kanta.

 

“wlh bazan zauna a dakin nan ba”muryar fatima ta doki kunnenshi.

 

Mikewa yayi da kyar,yace mata.

 

“duk yadda kikeso hakan zaayi gimbiyata,muje na rakaki dakin nawa”ya fadi gamida ruko hannunta,ba musu ta bishi zuwa dakin nashi.

 

Dakin har yagaji da haduwa,dan yafi nasu kyau nesa ba kusa ba,duk wani abun more rayuwa yana ciki.

 

Tunda suka shiga dakin fatima take dariya,dan tasan ta cutawa husna,kuma tana da tabbacin ranta se ya baci in taga gidado ya bar mata dakinshi.

 

Gidado ganin fatima na dariya ne yasa yaji sanyi a ranshi,dan ya lura tayi farinciki da bata dakin da yayi.

 

Ficewa yayi,da jakar kayanshi,zuwa wancan dayan dakin,sannan ita kuma yakai mata nata dakinta.

 

Wanka ta shiga,wanda ta jima tana kyalkyale jikinta,bayan ta fitone,ta zauna gaban mirror ta fara tsara kwalliyar da tunda take bata taba yin irinra ba.

 

“Masha Allah”,ta furta a hankali,sanda ta kalli kanta a mudubi taga yadda tayi kyau.

 

 

Gurin zabar kayan da zata sakane,ta tsaya ruwan ido,harde idonta ya sauka akan wasu riga da wando pink da fari,wandon three Quater,yayinda rigar ko cibiyarta bata gama rufewa ba,gashin kanta,raba shi tayi gida biyu,ta kama da farin ribon,se ta koma kamar wata yar baby,

 

bin jikinta tayi da kallo.

 

Fatima farace amman ta sirka da ja,hakan yabata damar yin kyau dan gaske,ita ba doguwa bace sannan ba gajera bace,wato medium size,tana da shafaffen ciki kuma tsukakke,yayinda kugunta kuma yake da fadi wato tana da hips masu kyan tsari,wanda koya ta motsa suma sesun motsa,kirjinta cike yake da na shanu,fuskarta cycle ce me dauke da dogon ganci me kyan tsari,tana da dan karamin baki,da labba masu dan tudu,ga sexy eyes da Allah ya bata,koya ta motsa bakinta dimple dinta se ya bayyana,ga yar siririyar hushiryar dake tsakanin kyawawan hakoranta,tana da bakin gashi,me santsi da sheki,gashi me tsayi har gadon bayanta. Kai abunde se wanda ya gani.nana fatima Abubakar Radda kenan jinin katsinawa yarinya me jini acika bafulatanar usuli.

 

tsaya tayi gaban mirror tana ci gaba da kallon kanta tana godewa Allah.

 

Anata bangaren husna ma  nacan tana kure adaka,ansha wankan riga da siket matsatstsu,masu kyan gaske,baki da fari,ba laifi husna ma akwai kyau,sede koda wasa bazaa hadata da fatima ba,da diri da komai fatima ta fita.

 

feshe jikinta tayi da turaruka kalakala,sannan tasa takalmi,ta fito zuwa,dakin gidado,wanda batasan yanzu ya koma na princess dinsa ba.

 

 

 

muje zuwa

 

 

Surbajo for life.

 

GID’AD’O BA SHEGE

BANE

 

 

 

Zahra Muhammad Mahmud

 

Dedicated to Amina maman gidado

 

 

37-38

 

 

Cikin takun daukar hankali,husna ta isa bakin kofar dakin,

 

Nucking tayi,wanda yasa fatima dake ciki,takowa,cikin izza da isa,tazo bude kofar dakin.

 

Kallon kallo suke yiwa juna,kuma kowaccen su ranta ya baci da ganin yar uwarta.

 

Tun kan fatima tai magana,husna ta rabe ta jikinta ta shige cikin dakin tana tsaki,fatima harde hannu tayi a kirji tabi bayanta da kallo.

 

Ko ina a falon babu inda husna bata leka neman gidado ba,amman bata ganshi ba,dan haka hanyar bedroom ta nufa.

 

Da sauri fatima tasha gabanta ta hanata shigar mata daki gami da cewa.

 

“Rainin wayon naki naso ya wuce hankali,taya zaki shifomin daki ba tare da izinina ba,kuma kita wani zagayawa ciki sekace wata yarsanda,ubanme kika bani ajiya,da kika zo karba?”

 

Murmushi husna tayi sannan tace.

 

“Dakinki ko dakin mijina?sanin kanki baki da wata kima ko darajar da ni husna zan baki ajiya,kuma har ki tunanin zanzo da kaina in amsa ba ki kaimin da kanki ba,gurin mijina nazo kuma yazamar miki wajibi,ki bani hanya na wuce”

 

“Da kinmin bayani tun farko da ban varki kin shigo kinsha wuyar nemansa ba akuya,dan haka yanzu se ki ficemin daga daki,dan yajima da mallakamin shi,so se kikai fiin cigiya da sanarwa a nemomiki shi”

 

“ji banza,kehar kin isa,ki rainamin wayo?to wlh baki isa ba se na shiga”

 

Kaucewa fatima tayi tabata hanya,har takai bakin kofar shigan fatima tace.

 

“na barki ki shiga,amman wlh,dayan biyu zaayi daya,ko a fito dake amace,ko kuma a sume a kakkarye,inde kika sake kika shigarmin daki wlh se na miki dukan mutuwa”

 

Cak taja ta tsaya,ta waigo ta kalli fatiman taga yadda tayi shirin yi mata barin makauniya,wanda tayi imani in ta kamata dakuwa zatayine yasa ta juya ta fice daga dakin,tana kunkunin ta ta nufo falin gidan,inda ta sami gidado zaune yana kallon kwallo a tv.

 

Jikinta har bari yake ta isa jikinshi ta rushe da kuka,da sauri,ya dagota,yana tambayarta lafiya.

 

Cikin kukan munafunci,da son samun fada tace

 

“Fatimace,daga naje dakinka nemanka,shine ta wankeni da mari”

 

Tureta yayi ajikinshi,ya fara mgn a fusace.

 

“me kika yiwa princess dina daya bata mata rai haka?munafuka ki fadamin me kika yimata nace?”

 

 

ido husna take warewa na mamaki,wato ma shi ta fatima yake bata ita ba.

 

Karar takun takalmar fatima ne yasa yakai dubansa gurinta.

 

Yadda kugunta ke kadawa,yafi komai kawata tafiyar tata,take gidado yayi suman tsaye,baki sake yake bin ta  da ido,har ta karaso gurin shi.

 

 

Tana zuwa,jikinshi ta nufa,ta ɗora hannayenta akan kafadarshi,shiko jiki na bari ya dora hannunsa akan mazaunanta.

 

A hankali,ya matso da ita sosai jikinshi,yace.

 

“Baby kinyi kyau,sosai,”

 

 

murmushi fatima tayi gamida,dora kanta kan kirjinshi tace.

 

“ngd hubby na”

 

wani sanyi,giɗaɗo yaji aransa da zuciyarshi.

 

Sake tausasa murya yayi sannan yace.

 

“princess me kanwar taki tai mikine kika mareta?”

 

 

Dagowa tayi takai dubanta gurin husna dake yashe kamar almajira a kasa,wani murmushi tai mata,sannan taba gidado amsa da cewa.

 

“Hubby kenan,Niko Me zanwa husna,rashin kunya taimin shine nai mata hukuncin da ko kai na kawowa kara irinshi zakai mata”ta fadi gamida manna kirjinta a jikinshi.

 

Wata ajiyar zuciya ya saki dan gaba ɗaya fatima ta gama burkita masa lissafi,da kyar yacewa husna.

 

“Ay dama nasan hakakawai bazata mareki ba seda kwakkwaran dalili,dan haka ki shiga taitayinki”

 

Jan hannun fatima yayi,suka nufi dakinshi,se shagwaba take zuba masa.

 

Kifewa husna tayi a gurin tana kuka me tsuma zuciya.

 

Hakan yay daidai da fitowar ligido,daga kitchen dauke da kulolin abinci,da sauri ta jere kulolin kan dinning table,ta karaso gurin husna dake ta faman rusa kuka.

 

Da sauri ta kamata ta mikar da ita taja hannunta zuwa,cikin dakinta ta zaunar da ita kan kujera,sannan ta fara da cewa.

 

“Haba uwar dakina,wannan ay se ki tona mana asiri,wayacemiki ko duka mijinki yay miki kina nunawa kishiya kinji zafinsa?taya zaki zauna kina kuka,gaban kishiya,ki kwantar da hankalinki,nai miki alkawarin kwato miki yencin ki agidan nan matukar duk abinda nace kiyi zakiyi”

 

“wlh zanyi ko menene shi,matukar shi ze kawo karshen zaman fatima da giɗado wlhzanyi shi”cewar husna dake share hawaye.

 

 

Ligido abun nema ya samu,dama bazawarace,tsabar gulma da munafuncine yasa mijinta sakinta,to gata yanzu tsakanin husna da fatima abun se Allah kuma.

 

 

muje zuwa

 

 

Surbajo for life.

 

GID’AD’O BA SHEGE

BANE

 

Zahra muhammad Mahmud.

 

 

Dedicated to Amina maman gidado

 

 

39-40

 

 

Haka ligido tasa husna agaba,taita kota mata makirci iri iri,

 

Shiko gidado da fatima nacan dakin shi,sunata wasanninsu,duk yabi ya birkice mata,se yimasa abunda ze kawo masa sauki takeyi.

 

Janyota yayi ya dora bakinshi akan kirjinta,yaci gaba da ayka mata sako,tuni ta fara yi masa yan koke koke,tana wani juyi ajikinshi sekace wata tarwada.

 

Kunnenta ya lalubo ya raɗa mata.

 

“yaushe zaki barni,na shigekine baby na?wlh a matse nake dake,don Allah kibani dama”yayi maganar cikin dusashewar murya.

 

Mirginewa tayi zata bar jikin nashi,da sauri ya kamota,kuka tasa mishi na shagwaba tana fadin.

 

“nide banason,wannan abun Allah kuwa,wannan ma da mukeyi,ay yafi wancan dadi,dan haka ni banga amfanin wancan dinba,kawai kabari muci gaba da jiyar da junanmu dadi ta haka kawai”

 

Murmushi gidado yayi,sannan yace.

 

“princess,duk sanda idona ko hannuna ya dira akan kirjinki,bana jin dado inde ba can din naje ba,don Allah ki tausayamin”

 

Kai ta juya masa,gamida turo baki gaba tace.

 

“to ay se kayi kuma,inbanda son dorawa kai,ga wasanninan kalakala,muyi su mana,nide wlh,banason,kace zaka kusanceni,dan wlh babu wani dadi nasani sede azaba,dan haka nide aganina muyi masu dadin mubar mara dadin kawai”

 

sake rungumeta yayi ajikinshi,yace.

 

“To shikenan gimbiyata,yadda kikeso hakan zaayi,sede daga yanzu,ko wasan zamuyi,ban amince ko ɗan kwali ki bari ajikinki ba,kome sekin cire,kin amince?”

 

shuru tayi tana tunani,zuwacan tace,

 

“Na amince,amman banda yanzu danni yanzu ma yunwa nakeji”

 

“ba damuwa ay akwai anjima,muje kici abincin”

 

Haka suka maida rigunansu,suka nufo falon,inda suka samu husna,goye da gidado karami,tana jijjigashi,

 

Da sauri fatima ta nufeta,tana fadin.

 

“wayyo my boy i miss you so much,zo mu gaisa”tayi maganar gamida yunkurin kwance gidadon abayan husna da se dariya yakeyi yaga mammansa.

 

Da sauri husna taja baya dashi abayanta tace.

 

“meye haka,kuma yaro na bayana kina wani kokarin kwanceshi,naga de dan mijinmune,vaki fini iko akanshi ba,kijira ki haifi naki seki shimfida iko akansa amman banda wannan”

 

Jikin fatima ne yay sanyi,itako husna wucewa tayi goye da gidadon a bayanta,dan hakan ma da tayi shirin ligido ne.

 

Gidado babba ne ya karaso gurin fatima yana dariya yace.

 

“wlh dariya kike bani,ki dena nunawa husna jin haushinki akan abun da taimiki,inba haka ba raina min ke zatayi wlh,dan wani abunma da biyu zata miki dan ki nuna kinji haushi”

 

Murmushi tayi ta fada jikinshi,ya rungumeta,suka karasa dinning area,suka cika tumbinsu tab,sannan suka dawo falo,suna kallo.

 

Sun dan jima a falon sannan suka mike ya rakata dakinta shima yatafi nashi,domin gabatar da Sallah,dan lokacin ta yayi

 

Husna na shiga daki ta kwance gidado ta mikawa ligido tana dariya tace.

 

“ligido kina da basira,kinga yadda tayi dana fada mata maganar kuwa?wlh sosai ranta ya baci”

 

Shewa sukayi su dukansu,sannan ligido tace.

 

“Ay dama na fada miki,cikin ruwan sanyi zaki koreta tabar miki mijinki”

 

Daga haka ligido taci gaba da dora mata karatun makirci.

 

 

Da daddare da misalin karfe tara na dare gidado ya tarasu,domin yaja kunnesu akan su zauna lafiya inda kuma ya raba musu girki.

 

“Tunda fatima bata tareba,dan haka ita zan fara yiwa kwanaki bakwai,sannan ke husna”

 

“Duk tarewar da kuka dunga yi a gida,ba tarewa bace se anan ne zaku taren?”cewar husna.

 

Ran fatima ne ya baci tace.

 

“Au kice kome mukeyi nida mijina idon ki nakai?”

 

Shuru husna tayi bata bata amsa ba,sabida ligido tace,ta dena bari gidado na ganin tana fada da fatima a gabanshi.

 

Gidado ne yaba husna amsa da cewa.

 

“eh ba tarewa bace,anan ne zamu taren,sabida nanne gidanmi na aure”

 

Murmushi husna tayi sannan tace cikin kashe murya.

 

“Ayya bross,wlh se yanzu na fahimta,to ba komai mukwana lfy,ay kwana bakwai kamar yaune,da yardar Allah”

 

Mikewa tayi takai dubanta gurin Fatima tace.

 

“Auty seda safe” ta juya tayi wucewarta dakinta.

 

Fatima ta kasa mgn dan mamaki,tabbas tasan akwai abinda husna take kutsawa dan ruwa baya tsami banza.

 

Daukarta  gidado yayi cak,se ɗakinshi,alwala sukayi suka gabatar da nafila ta godiya ga Allah,kana daga bisani bayan sun idar,ya rabata da kayan jikinta,shima haka suka shiga,wanka,sun jima a toilet din,sannan suka fito,ya goge musu ruwan dake jikinsu da towel sannan ya wurgar da towel din,ya kwasheta se kan gado,yaja musu bargo,ya kashe wuta,.

 

Agigice fatima tace.

 

“haba hubby wanne irin abune wannan,wanne irin bacci ne zamu kwanta ba kaya ajikinmu?”

 

“irin wanda mata da miji sukeyi,dan haka,banason musu”yana kaiwa nan yajata cikin bargon.

 

Ayka ayka yadunga aykata mata a …….,da bakinshi da hannunshi wanda hakan ya kusa haukata fatima,tashiga yin kukan dadi,takai kololuwa gurin bukatarshi,seda ya tabbatar data kamu ya zare jikinshi yaje yayi wanka ya fito,ya zira gajeren wando yaje ya kwanta.

 

Fatima,ko hannu takasa dagawa,sabida tana cikin wani yanayi,daga karshema da taga yayo wanka,ji tayi kamar ta rufeshi da duka,dan a ganinta be mata adalci ba

 

 

Hakade ta kwana ta gaza yin bacci,wanda shima din beyiba,amman yayi kamar yayi,sede aboye yanata mata dariya,danshi da kanshi yasan ya mata mugunta.

 

 

 

muje zuwa.

 

 

Surbajo for life.

 

GID’AD’O BA SHEGE

BANE

 

 

 

Zahra Muhammad Mahmud

 

 

Dedicated to Amina maman Gidado

 

 

41-42

 

 

Koda garin Allah ya waye,haka fatima ta tashi sam bata jin kwari ajikinta,se fushi takeyi,wanda ita kadai tasan daliƙin yin fushin.

 

Shiko gidado,da zaran ya kalleta yaga dan karamin bakin nan nata ta cuno shi gaba,wata dariya ce take kokarin kamashi,dan yasan fushin nashi ne akeyi.

 

Da misalin karfe goma na safiya,duka suka hallara kan dinning domin cin abincin safe,husna an caba ado se wani tattalin gidado karami takeyi,wanda hakan ya janye hankalin gidado babba zuwa gurinsu.

 

Shuru fatima tayi tana nazarin ta yadda zata kwato danta daga hannun husna adaidai wannan lokacin ba tare da ta nuna fushi ko bacin rai yayin kwatowar ba.

 

Tsam ta mike ta isa kusa da husna,ta dafata tana dariya,tace.

 

“kai husna wlh baki da dama,tun dazu se nuni nake miki da ki mikon dana mu gaisa amman kin wani basar,bacin kinsan ko uwarshi ta aynihi bazata nunamin sonshi ba,rasa uwa makaranta,dangi,da mahaifa gaba daya at the same time asaboda shi,ayko inaga ko shi hubbyna sede ya biyoni a baya inde akan nunawa dana so ne,”ta karasa maganar tana kashewa husna ido.

 

Shiko gidado karami yana ganinta ɗarab ya mike ya mika mata hannu,yana murnar ganinta.

 

Wata ƴar shewa tayi gamida ɗaukar yaron tana fadin.

 

“My boy kenan,ay nasan dama zaayi haka,uwar datayi dawainita dakai tsawon shekara biyu,akwai distance me nisa tsakaninta,da uwar kwana guda”tana kaiwa nan ta juya dauke dashi a kafaɗarta se zullo yakeyi,najin dadin zuwa gurinta.

 

komawa tayi gurin zamanta dashi,abinci tacu gaba da bashi kamar yadda ta saba.

 

shide ogan da akeyi dominshi binsu yake da ido,se yanzu ya kara gasgata zancen fatima,na cewa uwa ta shekara biyu nada banbanci da uwa ta kwana guda,domin ko yadda yaron take walwala a gurinta bayayi agurin husna,yadda take bashi abincinma da banbanci dana husna,murmushi yayi,yana jin son fatima na sake shiga zuciyarshi.

 

Husna ko rasa amsar da zata ba fatima tayi,dan ta rufe mata bakin maganar.

 

Haka sukaci gaba da cin abincin,sosai fatima keba gidado dariya,dan har yanzu dan bakin nata nanan a cune,dan ya tsokanetane ya kai hannu yadan buge bakin yace.

 

“princess,me ya sami bakinki?,ko faduwa kikayi ne? naga tun da safe yadan turo gaba”

 

Wata uwar harara ta watsa mishi,sannan ta bashi amsa da cewa.

 

 

“ba faduwa nayi ba,karo nayi da jirgin kasa,shine bakin yadan tasa”wohoho yar katsinawa,wani ma yay rawa bare dan makadi

 

 

Dariyace ta sose ta kubcewa gidado yashiga kyalkyalata harda sauka akan kujera,husna da ke gefe ma sosai  amsar ta fatima ta bata dariyar dan haka itama ba a barta a baya ba,ta shiga kwasar dariyar.

 

 

Rai a bace Fatima ta mike ta dauki gidado ta wuce dakinta,husna da gidado kuwa dariyarsu taki tsayawa,dan harga Allah koni ta bani dariyar.

 

Tana shiga ɗakinta itama ta fara kyalkyala dariya,dan se yanzu aɓun ke bata dariya musamman data tuno,hakikanin abinda takewa fushin.

 

 

Ci gaba tayi da yiwa gidado karami,duk abinda yakeso,shima ko se dariya yakeyi,yana jin dadin kasancewa tare da ita.

 

Gidado ne ya turo kofar ya shigo,da sallamarshi.

 

amsawa tayi, gamida mikewa ta nufeshi,tana zuwa dukan shagwaba tashiga yi masa a kirji tana fadin.

 

“Dariyar da kukamin acanne bata ishekaba kabiyoni daki kamin sabuwa?” tayi maganar cikin shagwaba.

 

murmushi yayi dan shagwaɓa nadaga cikin abunda yake burgeshi da ita

 

“pricess ni na isa naita miki dariya,wlh ko dazunma,kece kika bani dariya,but am sorry kinji gimbiyata”.

 

Rungumeta yayi akirjinshi yana aykin rarrashinta,dan zuwa lokacin tuni tasa mishi kuka.

 

Kan kujera yajata,ya zaunar da ita kan cinyarshi,yana ci gaba da rarrashinta,

 

Da kyar yasamu tai shuru,suka ci gaba da hirarsu ta masoya gamuda yan kananun wasanni.

 

Anata bangaren husna ranta ne ya baci ganin gidado ya nufi dakin fatima,a fusace ta mike ta nufi,gurin ligido,

 

Tana shiga dakin ta rushe d kuka,ta kwashe duk abinda ya faru ta snar da ita.

 

murmushi ligido tayi,sannan tace.

 

“barni dasu uwar dakina,bame tabamin ke cikinsu na barshi ya zauna kalau,dan haka zan koyar dake sabbin dabaru”

 

 

Daga haka taci gaba da kitsama husna munanan dabiu ita kuma tana haddacewa.

 

 

muje zuwa.

 

 

Surbajo for life.

 

GIDADO BA SHEGE

BANE

 

 

Zahra Muhammad Mahmud

 

Dedicated to Amina Maman gidado

 

43-44

 

Haka gidado da fatima suka kasance har tsawon sati guda na kwanakin girkinta.

 

Babu wani abu daya taba shiga tsakaninsu,sede duk dare se gidado ya ɓirkita mata lissafi da salon soyayyarshi.

 

Fatima nason kasancewa dashi,sede kunya ta hanata nuna masa hakan.

 

Yau husna an amshi girki se wani rawar kafa takeyi,yayinda fatima kuma kishinta ya motsa ji takeyi kamar ta rufe husna da duka.

 

Ganin in ta cigaba da zama a inda zataga gilmawar husnar ze iya sawa tayi abinda ba shikenanba ne yas tabar gurin zuwa dakinta.

 

Gidado dama tuni ya koma bakin aykinshi,se dare yake dawowa,

 

Koda ya dawo,husna yasamu a falo,anci uwar kwalliya ana jiranshi,tabe baki yayi,dan ko kadan bata burgeshi ba,shi haushi ma ta bashi,dan aganinsa rawar kanta tayi yawa.

 

A matsayinta na sabuwar amarya ay jira zatayi yazo gareta ba tazo da kanta ba.

 

Da sauri ta mike ta nufoshi,tana kada jiki,tazo gurinshi ta rungumeshi,gamida yi masa sannu da zuwa.

 

Sanin hakkinta akanshine yasa,yadan rungumeta ta shima ya karata  gefenshi,yace.

 

“maam ya gida?”

 

baki ta turo gaba gamida cewa.

 

“lafiya lau,mman ni ba sunana madan ba,naga fatima princess kake ce mata”ta karasa maganar cikin shagwaba.

 

murmushi yayi,daya bayyana hakoranshi sannan yace.

 

“To naji,”

 

Yana kaiwa nan,ya wuce dakinshi,domin yayi wanka.

 

Binshi tayi a baya,har zuwa cikin dakin,yana cire botir din rigarshi,tayi saurin karasawa,tana tayashi cirewa.

 

Shide bin ta kawai yake da ido har ta gama taimaka masan.

 

toilet ta shiga ta hada masa ruwan wanka,sannan ta fito shi kuma yashiga wankan.

 

ya jima yana wankan,sannan ya dauro towel ya fito.

 

Kamar yadda ligido ta koyar da ita,mikewa tayi ta nufeshi,tana tayashi goge ruwan jikinshi.

 

Husna de ita ta taimaka masa ya shirya,sannan ta kawo mishi abinci,yaci ya koshi,yayi brush.

 

Sannan ya fito ya nufi dakin fatima,wacce tunda ya shigo gidan har tarbar da husna tai masa akan idonta.

 

kifewa tayi akan gado tana kuka kamar ranta ze fita Zuciyarta na zafi kwarai matuka.

 

tura kofar ɗakin yayi,ya shiga,sautin kukanta ne yasa yayi saurin karasawa gareta.

 

Ɗagota yayi yana tambayarta abinda yasameta akidime yake maganar.

 

“princess me ya sameki,pls kimin mgn”

 

A fusace ta kwace jikinta,daga jikinshi,tafara magana cikin fushi.

 

“me zaka fadamin kuma bayan wanda idona ya gani,wlh kai mayaudarine,dan haka kaficemin daga daki,katafi gurin matarka kawai”.

 

shuru yayi yana kallonta,tabbas batun yauba ya fahimci fatima nada matsanancin kishi,wanda halittartane yasani,dan haka dole yay mata uzuri.

 

Abu daya kawai yasani,yanasonta,yayinda ko kadan bayason husna,amman dole ya gyara lahirarshi,dan haka baze tauyewa husna hakkinta ba tunda itama auranta yakeyi.

 

Duk yadda yaso ya kwantarwa da fatima hankali,amman fafur taki yarda,hakan yasa dole yafice daga dakin nata.

 

Rai a bace ya nufi dakinshi,tura kofar yayi afusace yashiga.

 

Sede take fushin ya kauce sanda yay arba da husna sanye cikin wata farar rigar bacci,wacce ta kasance net ce,kuma daidai cinyarta ta tsaya.

 

halittun jikint duk sun bayyana afili,zaune take kan kujera ta dora kafa daya kan,daya tana tsotsar lollipop,sweet.

 

Mikewa tayi cikin takun daukar hankali,ta nufeshi.

 

Tunkan ta iso,ya bude mata hnnayenshi,tana zuwa kirjinshi ta shige ya.maida hannu ya rungumeta.

 

Haka tashiga birkita masa lissafi,wanda hakan yay nasarar daga mishi hankali.

 

Janta yayi suka fada kan gado.

 

muje zuwa

 

Surbajo for life.

GID’AD’O BA SHEGE

BANE

 

Zahra Muhammad Mahmud

 

Mata! Mata!! Mata!!!

 

Abun yanzu bazamuce kishi bane,tsabar haukane da jahilci,mata mun dauki kishi kamar wani ado dazesa mazajenmu su somu,wanda ko kadan ba haka bane,wlh kishi na janyo mana tsana agurin mazajenmu,kishi na hanamu cin ribar soyayyar da miji yake mana,ni a ganina,tunda ba ke kika haifi mijinki ba,to ko baki isa ki bashi umarni yabi ba,sede shawara,idan har kinsan baki isa kisashi yayi dole ba,to ke yar wacece da bazaa miki kishiyaba?wlh manzon Allah yayi gaskiya,a wuta mata semun fi yawa,ba kuma komai ze kaimu ga hakan ba illa son zuciya,kishi,da kwadayi,baki da gashin wance taya zakice zakiyi kitson wance,wlh ku farka mata kishi ya maida da yawanmu mahaukata masu raba abun kunya,da ka cuta gwanda a cuceka,ina amfanin badi ba rai don girman Allah

 

wlh,maza ku tuna akwai ranar da bakin da ya saba karya baze mgn ba agaban Allah,gabobin da suka aykata su zasu fadi a bainar mutane,kun ajiyemu a gida kuna cutar da mu,sabida kunga mune a kasan ku,Allah ya baku dama,kuna amfani da ita gurin samu aykata,mummunar barna

 

daga karshe Kirana ga mata shine muji tsoron Allah,maza ingiza me kantu ruwa suke mana,su cucemu mu rama a lahira adannamu wuta,wa gari ya waya?KE!!!!

 

Dedicated to Amina maman Gidado

 

45-46

 

Gaba daya sun fice daga hayyacinsu,ba kamar gidado ma,da yafi husna kaguwa.

 

wasannin da zasu rikitata,yashiga yimata,wanda hakan yasata,sakar masa ragamar rayuwarta.

 

Sun jima suna abu guda,husna ba karamar wuya tasha a hannunshi ba kuka cizo yakushi babu wanda bata yi masa ba,amman be saurara mata ba,seda yagama biyan bukatarsa.

 

Gefe ya koma yana sauraron kukanta,da yake dakar masa dodon kunne,ko kadan beda kwari ajikinshi,

 

da kyar ya iya janyo ta,jikinsh yana shafa bayanta,alamun rarrashi,su husna abun nema ya samu,se sake narkewa takeyi.

 

Yajima yana rarrashinta kana daga bisani,ya kwasheta zuwa toilet,yayo musu wanka dukansu.

 

Se albarka yake saka mata,sabida ta shayar dashi zumarta.

 

kan gado suka koma bayan ya sauya bedsheet,ya kwantar da ita a kan kirjinshi suka shiga yin baccin me dadi.

 

Fatima ko ko runtsawa batayiba,zuciyarta na hango mata gidado nacan na yiwa husna,abinda yake mata,batasan yamata ma abinda ita be taba yimata ba.

 

 

idanunta sun kumbura,sun kankance sabida kuka,zuciyarta na mata zafi,a haka har garin Allah ya waye.

 

 

Koda gari ya waye,gidado se lallaba husna yakeyi,da kanshi yay mata wanka,sannan shima yayi ya shirya.

 

Dakinta ya nuɗa,ya dauko mata kayan da zata saka,yazo ya shiryata,da kanshi se sannu,yake mata,itako sabida tsabar kirsa har zuwa lokacin hawaye bedena zuba a idonta ba.

 

Da misalin karfe tara,na safe,fatima ta tashi tayi wanka,tayiwa gidado,ta shirya,shima ta shiryashi,sannan,suka nufo dinning domin cin abinci,da ligido ta shirya musu.

 

Bata ga kowa a dinning dinba hakan seda ya sake,sosa ranta.hakade ta zauna uta da ɗanta ta hada musu abincin,suka zauna suna ci.

 

A dakin gidado kuwa,bayan ya shirya ya shirya,babyn shi kamar yadda ya radawa husna,kamota,yayi tana dingishi,gamida dan warw kafa,ita adole taji maza suka nufo dinning din domin cin abinci.

 

Ko kadan gidado bemasan da Fatima a gurinba,hankalinshi nakan yar kanwarsa daya dagargaza,se sannu yake mata.

 

Ay husna na ganin fatima agurin se ta sake narkewa,kai kace nakuda takeyi,a haka suka karasa kan kujera.

 

seda ya zaunar da ita tukuna,shima tana zama ta wani zabura ta mike tana fadin.

 

“wayyo bross,wlh da zafi har yanzu,nide in mun gama cin abincin muje kasake,gasamin da ruwan zafin,”tayi mgnr harda hawayenta.

 

jiki na bari gidado yadan rungumota,jikinshi yace.

 

“wayyo baby na nine ko,am sorrybazan sake ba,ki daure ki zauna kici abincin se muje na sake zaunar dake acikin ruwan za……”maganar ta katse snda idonshi ya sauka akan na fatima,wanda ya hango tsabar masifa acikin su.

 

shi kanshi,besn sanda ya saki husna ya zauna ba,sede kawai jinshi yayi a zaune sabida tsabar firgita da ganin fatima agurin da yayi.

 

Bacin rai na karshw ɗatima ta shiga cikinshi,zuciyarta takwas takwas take bugawa.

 

Murmushi ra kirkiro gamida cewa.

 

“wayyo husna,wlh,ina daki ina tausayinki,dan nasan dole dama ki sha wuya,dan jiya hubby cewa yayi baze kusancekiba,ni nadunga takura masa akan ya daure ya miki kamar yadda nima yamin,dan kin bani tausayine da wlh nima se na miki daritar da kikamin washegari dana fito ina tura baki,kuka hadu kunamin daeiya”maida dubanta tayi gurin gidado da ya saki baki yana mamaki,

 

Duka takai masa na wasa,tana dariya tace.

 

“oh su hubby ko kunya,kaje ka kama yar mutane zaka cinye duka,bayan dakayar nasha kanka,kai ka dage akan baka sonta baka kaunarta,kai va abinda zakayima da ita”kara tsananta dariyar ra tayi sannan taci gaba da cewa.

 

“kasan Allah hubby danaga da gaske kakeyi akan bazaka kusancetaba tunda baka sonta,wannan juice din dana baka kasha,fakar idonka nayi nasa maka kwayae dake tayae da shaawa dan de itama tasamu kai mata”

 

Dubanta takai gurin husna,wacce zuwa lokacin hawayen bakin ciki  da takaici sun fara sintiri a fuskaeta tace mata tana dariya.

 

 

“am sorry sis na janyo ya.miki mugunta wlh taurin kai ne dashi,fafur fa yaki amincewa ya kusanceki shi yasa nai masa haka”

 

Tana kaiwa nan ta dauki gidado karami ta wuce dakinta tana dariya,sede tana shiga dakin ta rushe da kukan bakin ciki wanda tunda take bata taba yin makamancinsa ba.

 

Gidado a falo gaba ɗaya kanshi yashiga charge yana tunanin maganganun fatima,yama rasa abun cewa.

 

itako husna kuka ta rushe dashi ɓna takaci,wato ashema rokonshi kishiyarta tayi akan ya kusanceta,harma yanaki,shine tasa mishi kwayar tada shaawa,no wonder taga ya shigo dakin rai abace a daren jiya,ashe ba ason ranshi ya kusancetaba,haba shiyasa yadunga yimata kamar wani machine

 

Mikewa tayi da gudu ta nufi dakinta tana kukan takaici.

Shiko gidado

ji yayi kamar andaureshi da sarka a inda yake,motsin kirki ya kasa ti,fatima taimasa salalan tsiya.

 

 

muje zuwa.

 

 

surbajo for life

 

 

GID’AD’O BA SHEGE

BANE

 

 

 

Zahra Muhammad mahmud

 

 

Dedicated to Amina maman Gidado

 

 

47-48

 

 

 

Husna dakinta ta shiga da gudu tana rusa kuka,tayi danasanin mallakawa gidado kanta a daren jiya,ashe bama a hayyacinshi yake ba,shiyasa .

 

Kuka take kamar zata kashe kanta,ligido ce ta shigo dakin jikinta na bari irin na munafukannan.

 

Da sauri taje gurin husna tana tambayarta abinda ya faru,amman fafur taki fada mata.

 

Duk yadda ligido tayi da husna akan ta sanar da ita damuwarta amman fafur taki fada mata.

 

Haka ta hakura ta kyaleta ta fice daga dakin,ita kuma taci gaba da kukanta.

 

Anashi bangaren gidado mikewa yayi dakyar daga kan dinning din tsayawa yayi atsakiyar dakunan,yana tunanin gurinwa ze fara zuwa,dan gaba daya a birkice yake.

 

Tabbas yasan yaje gurin fatima a yanzu shi bashi ma da kwarin guiwar hada ido da ita,dan wlh kunyar da yakeji tata,ji yake kamar kamashi tayi yana zina.

 

Salalo salalo ya nufi dakin husna,yana tura kofar,ta mike,cikin bacin rai tace.

 

“Bakin munafuki me ya kawoka gurina,bayan kun hadu kai da matarka kun cutar dani,wlh bazan kyaleku ba sena ɗauki fansa”tayi mgnr cikin matsanancin kuka.

 

Tabbas yasan anmata abinda yafi haka ma dan haka jiki a sanyaye ya nufeta,da nufin kamata,ayko,batayi kasa aguiwaba tasa kafa ta tokareshi a gabanshi

 

Durkushewa yayi agurin rike da gurin yana murkususu,ita ko ko ajikinta,dan se lokacin ne ma takejin dan sanyi a zuciyarta,gameda abinda fatima tai mata

 

 

Ya jima a gurin sannan yasamu gurin yadan dawo normal ya mike rai abace yace.

 

“Husna akan laifin da ba nawaba,kike son halakani,me nai miki ni?”

 

harararshi tayi gamida murguda baki tace.

 

“har akwai wani, me laifin da ya kaika,tsohon munafuki kawai,kuma wlh ka taka a sannu wataranma,cire maka ita zanyi gaba daya ka huta”

 

Be kulata ba ya juya ya fice daga dakin,ya nufi dakin fatima,ya zazzage mata kwandon masifa,tunda itace silar komai.

 

Fatima wacce,zuwa lokacin ta dena kukan da takeyi sabida karatun qurani da tayi ya sanyaya mata zuciya.

 

ko sallama beyiba ya fada dakin rai abace,mikewa tayi tana masa kallon uku saura kwata.

 

Duk zafin da yatafi dashi,seji yayi yama kasa hada ido da ita,bacin zuwa yayi yaja mata kunne

 

“Ango kasha kamshi,zuwa kayine nima kadan sammin kanshin,?”cewar fatima da tayi mgn ba tare da alamun wasa a fuskarta ba.

 

 

Shuru gidado yayi,ya sunkuyar da kanshi kasa,yana danasanin zuwa dakin nata,dan yasan yau me kwatarsa sede Allah.

 

Takowa tayi ta matso gabanshi taci gaba da cewa.

 

“har ka gama gasa babyn taka ne?”

 

nanma shuru yayi ya gaza amsawa.

 

“Gidado kenan”

 

A zabure ya dago kai yana kallonta dan tunda yake da ita yaune karo na farko data ambaci sunanshi.

 

“ni kace bazaka kusanceni ba,se randa na budi baki nace maka inaso,ita husna zuwa tayi tace maka tana son ka kusancetan?”

 

Wayƴo duniya,gidado duk da ac dake dakin zuwa lpkacin ya fara zufa.

 

Kukane yafara kubcewa fatima tace cikin kuka.

 

“ko wacce amarya,darenta na farko,tilasta mata mijinta yakeyi wajen kusantarta koda kuwa tsine mishi takeyi,karewar rashin so,a haka ze kusanceta,ni bakamin hakan ba,sabida dama banice burinka ba,wlh ka cutar dani,cutarwa mafi muni,ka aureni baka hada shimfida daniba,seda amaryarka da kake so,dan ita yar uwarkace,to kaji matukar ka cuceni wlh ban yafe maka ba,kuma yanzu base anjima ba,ka rubutamin takardata ka bani,nima inje in auri sabin jini,dan bazan zauna dakaiba bayan nasan kaidin sauran watane”ta kife a gurin tana kuka.

 

jikin gidado rawa yakeyi,da kyar ya daga kafa ya isa gareta,ya fara rarrashinta,dan yasan tabbas,shi be takura mata kamar yadda ya takura Husna ba duk da cewa itama husnan ta nuna bataso.

 

janta tayi jikinshi yana rarrashinta amman fafur taki yin shuru,se kukanta takeyi,yayinda duk abinda yazo hannunta buga mishi takeyi,zuciyarta na tafasa.

 

“wlh seka sakeni gidado,yadda bazan sameka saboba,nima wlh bazaka sameni sabuwa ba,kishina ya wuce tunaninka,bayan ko tarewa banyiba a gudanka akamin kishiya sabida zalincu kuma ka riga saninta kamin ni,to wlh,bazaka budeni a leda ba”takarasa mgnr tana kuka gwanin ban tausayi.

 

hankalin gidado in yayi dubu ya tashi,haka ya mike ya fice daga dakin ko gabanshi,baya gani,ya shiga dakinshi.

 

kan gado yaje ya kwanta,tunani yakeson yi amman kwakwalwar tashi gaba daya ta toshe,ya kasa yin tunanin.

 

taya ze saki fatima bayan yana ji ajikinshi itace rayuwarshi,wannan itace tambayar d yake yiwa kanshi.

 

 

muje zuwa.

 

 

surbajo for life.

 

 

 

GIDADO BA SHEGE

BANE

 

 

 

Zahra Muhammad mahmud

 

 

Dedicated to Amina Maman Gidado

 

 

49-50

 

 

Fatima fadamasa maganganun da tayine,yasa zuciyarta tayi sanyi,har tasamu kwarin guiwar mikewa daga inda take taje ta dauki gidado tana mishi wasa.

 

Husna ko ko kadan zuciyarta ba alamar sassauci,dan fushin dan gaske takeyi ba wasa ba.

 

Giɗaɗo nacan dakinshi,kwance kan tiles,ko motsi baya iya yi,sabida takurawa zuciyarshi da yayi gurin son yasan hanyar da ze bi yasamu zaman lfy da iyalinshi,musammam ma fatima.

 

Haka gidan ya kasance,har zuwa lokacin cin abincin rana,fatima da husnane kawai sukazo dinning din,banda gidado.

 

Fatima bata ji dadin rashin ganinshi ba,dan tasan itace silar rashin zuwan nashi,hakade suka gama ci kowa na ballawa dan uwansa harara.

 

Da daddare ma bata sauya zaniba,su kadai sukazo cin abincin banda shi,fatima kasa jurewa tayi ta mike,rike da hannun gidado ta nufi dakin babannashi.

 

Bin bayanta husna tayi da wata uwar harara,gamida yin tsaki.

 

Suna zuwa kofar dakin fatima tai sallama amman baa amsa ba,tayi nurcking shima ba amsa,

 

Hakanne yasa ta tura kofar ta shiga,kwance yake kan tiles ya zubawa kofar ido,suna shiga gidado karami ya tafi da gudu,ya haye jikinshi yana ta tsalle tsallen ganin shi.

 

Hannu yasa ya rungume shi yana sumbatarshi,bayan yadan taba wasa dashine,daga kwancen da yake,yasakeshi,shikuma ya ruga da gudu zuwa cikin dakin baban nashi.

 

Fatima dake jingine jikin kofa,ido kawai ta tsura mishi,gaba daya tausayinshi yagama cikata.

 

Shima idon ya bita dashi,yana jira yaji ta fara masifar,dan beyi tunanin,shi tazo dubawa ba.

 

Sunfi minti biyar suna kallon kallo,a idonta gidado ya gano,abinda yakawota na aynihi,kuma ko yanzu da take tsaye so take tazo gurinshi amman tsoron yin hakan takeyi,dan yaga duk ta daburce.

 

Hannu ya mika mata,alamun tazo gareshi,ayko harda dan gudunta tazo ta fada jikinshi,tana kuka,rungumeta yayi yana dan bubbuga bayanta.

 

Itako kuka takeyi sosai,se cusa kanta cikin kirjinshi takeyi,dago da fuskarta yayi,yana kallonta,yace.

 

“dan ni banyi kukan bane princess yasa kikazo ke kinayi?”

 

kai ta girgiza masa ta runtse ido tana kuka.

 

Mikewa zaune yayi,rungume da iran ya sake cewa.

 

“to meyasa kika,zo kina kuka,bayan kinsan kukanki na dagamin hankali?”

 

Cikin kuka tace.

 

“Don Allah kayi hakuri da abinda nayi maka dazu,wlh idonane ya rufe,raina kuma ya baci da abinda kayimin,shiyasa amman don Allah ka yafemin”tayi mgnr cikin matsanancin kuka.

Wani sanyi ne ya ratsa zuciyarsa,sosai ranshi tayi masa sanyi,dan dama gaba daya a burkice yake.

 

Dago kanta yayi ya hada goshinsu,sannan yace.

 

“princess kiyi hakuri don Allah,tabbas nasan banyi mii adalciba,amman inaso kisani,rigen zuwa fada bashi ke nufin ka zama sarki ba,dan haka ki kwantar da hankalinki,wlh har gobe da jibi baki da ta biyu a zuciyata,inasonki ina kaunarki,badan komai ba sedan gaskiyarki”ya karasa maganar yana murmushi.

 

Zuwacan kamar an tsunguneshi yace.

 

“Af na manta,yanzu kin koyo karya,babba ma kuwa,tundazu gashi kinyimin ita,wacce sabida tsananin mamakinta ko motsi na kasa”ya karasa mgnr yana jan hancinta.

 

Doke hannu tayi tana dariya ta kara shigewa jikinshi tace.

 

“Ay inde irin wainnan karerayinne to wlh yanzu ka fara jinsu,matukar naga zaain rawar kai,toko zan kawo karshen rawar kan”.

 

Bakinshi ya haɗe da nata ya shiga ayka mata sako,yayin da hannunshi keci gaba da yawo a jikinta,.

 

Da kyar ta kwaci kanta tana haki,murmushi yayi yace.

 

“nifa matsalata dake ragwanta”

 

Harara ta falla mishi tace.

 

“eh din nayi din,shikenan sena barka ka tausheni kenan?”

 

 

Dariyace ta kamashi sosai,itama tana tayashi.

 

mikewa sukayi,yasata ta hada mishi ruwan wanka,duk yadda taso karta bishi toilet din,amman ina kwasarta gaba daya yayi,zuwa ciki,gaba dayanta ya tsunumata cikin ruwan wankan.

 

 

Ayko de sunsha dramer kan a gama wankan,dan seda yamata sabon wanka,se kuka take masa.

 

 

Bayan sun fito ne daure da towel,fatima ta fice daga dakin ta nufi nata domin shiryawa,ga kanta daya jika mata se digar da ruwa yake.

 

A zahirin gaskiya fatima dama ta fitane a haka sabida husna tayi zaton gidado ya kwanta da itane ranar girkinta.

 

Ayko ilai,tana fitowa sukayi kacibus,da husna,kallonta husna takeyi baki a sake,itako wani killer smile ta saki gamida shafo gefen fuskar husna tace.

 

 

“kinga zahiri ko,cewa yayi na taimaka,nazo na kore masa kishin ruwanshi,sabida,shide jiya be gane da mace ya kwana ba”

 

 

Murmushi ta sake yi,ta kure husna da ido tace mats.

 

“sis anya kuwa kina shan tsuminmu na mata?”cewar fatima tana dariya.

 

“na maza nake sha”husna ta bata amsa a zafafe.

 

 

dariya tayi tace

 

 

“no wonder ashe ya kasa gane da macen yake tare,to yanada kyau ki nemo na mata”tana kaiwanan,ta wuce ta barta zuciya na mata zafi.

 

 

Gaba daya husna tama rasa abunyi.

 

Kitchen ta auka da gudu,ta dauko wuka,ta nufi dakin gidado,dake tube sintir,yana shafa mai.

 

Allah yasa,da wandon karfe kusa

 

 

 

Muje zuwa.

 

 

 

surbajo for life

 

 

GID’AD’O BA SHEGE

BANE

 

 

 

 

Zahra muhammad mahmud

 

Mata mu kiyaye,mu adana saurin fushinmu a gidan mazajenmu,mudunga bin komai a sannu,inba haka ba muna tattare da dana sani,zafin kishi ba namu bane,kirsa ita ke kwatarki gurin kishiya,akwai kirsa ta girki,ta kan gado,ta mgn,ta tafiya,ta kwalliya,wannan tsakaninki da mijinki kenan,ita kuma kishiya,ba ruwanki da kaita gurin boka ko malam,ko kije ki hada mata munafunci gurin miji,sam hakan ba daidai bane.akwai kirsa wacce ake kira mirsisi tusar gaban siriki,itace wacce fatima keyi,wasu sunce fatima bata kyautaba,but na musu uzuri,amman ina kara jan hakalin mata,da adena bin malamai akan kishiya ta dameki,babu kyau,wlh babu kyau,akwai azaba me girma a tattare da hakan,ki kama kirsa yan mata kisha mamaki

 

 

Don Allah masu yimin mgn ta pc kuyi hakuri zakuga bana kulaku,idona ke ciwo,so bazan iya baku amsa ba,dan da zaran nayi posting nake sauka online,so don Allah kuyi hakuri yanzu de bana chatting pc,har se na gamsu da samun lafiyar idona,dan haka kuyi hakuri don Allah

 

 

Dedicated to Amina Maman Gidado

 

 

51-52

 

 

Da gudu husna ta banka kofar dakin ta shiga,wanda hakan yasa gidado ya juyo adan firgice dan ganin meke faruw.

 

Ita ko husna ganinshi da tayi ba kayane yabata tabbaci gamr da abunda fatima ta fada,wani kukan bakin ciki ne ya kubce mata.

 

Tace cikin kunar rai tana daga wukar hannunta.

 

“zaka iya min duk wani wulakanci na jure,amman wlh baka isa kaci amanata ba aranar girkina,dan haka wlh sena koyama darasin da mata ke koyawa mazaje maciya amana”tana kaiwa nan ta nufeshi.

 

Ja da baya ya fara yi,baki na rawa yace.

 

“wacce amana taki naci,kuma da kike biyoni da wuka me kike shirin aykata min?”

 

“Second roud kaciya,zan maka,tunda ta farkon da aka ma bata gamsar da kaiba”cewar husna.

 

Wayyo Allah gidado,ay ji yayi kamar ya zama tsuntsu ya tashi sama,dakyar yace.

 

“ke mahaukaciyar inace,husna,?ubanwa yace miki ana sake yiwa namiji kaciya,cewa zakiyi kawai kasheni zakiyi,”

 

 

Bata bashi amsaba,sabida har cikin zuciyarta burinta ta kaddamar masa,da abinda tai niyya.

 

 

Shikuma yana ja da bayane sabida koshi mahaukacine baze iya tinkararta da wukar dake hannunta ba,dan komai ze iya faruwa.

 

Tuntube yayi vatare daya ankaraba ya fadi akasa,kan ya tashi tuni ta karaso kanshi.

 

 

Hakan yayi daidai da shigowar fatima dakin,bayan ta shirya,dai dai lokacin husna ta daga wukar kenan Fatima tai kukan kura,ta nufeta tana ihun.

 

“kin aureshine dama dan ki kashemin shi,wlh baki isa ba”

 

Tana zuwa tai ciki ciki da husnan,nanfa suka shiga kokawa iya karfinsu.

 

 

Da sauri gidado ya mike yasa kayanshi,sannan ya nufesu,dama fatima ce akan husna,tana duka,da sauri ya kama fatiman ya dagata,husna na dagowa batare da sun luraba,ta cakawa fatima wukar a gefen cikinta,ta zaro ta sake dagawa zata caka mata a kirjintane gidado ya rike kaifin wukar iya karfinshi wanda take husna ta zuge masa hannu,se jini ke zuba,fatima ko tuni ta fadi rike da cikin nata.

 

Wani kukan kura gidado yayi har tsalle yayi sannan yayiwa husna fashin kwakwa akai,zubewa tayi akasa agurin.

 

Ko ta kanta beyi ba,a gigice ya kwashi fatin sa se asibiti,dayake sucan ba irin nan bane,sun san mutuncin rai,basu maida kasarsa makabarta ba,dan haka basu ce se anzo da yan sanda ba,kai tsaye suka amsheta,suka nufi emmergency da ita.

 

Gidado rushewa yayi da wani matsanancin kuka,ji yake,Zalincin yayi yawa,fatima bata cancanci haka gurinshi ba.

 

Kukanshi yake kashirban gamida adduar Allah yasa kada fatiman shi ta mutu.

 

Maaikatan gurinne keta faman bashi hakuri amman ko sauraronsu baya yi.

 

An kwashe sama da awanni biyu akan fatima sannan likitocin suka samu nasarar,gyara duk wata barna da wukar tayi,

 

Dakin kwantarwa aka kai fatima,gidado na bin su da gudu.

 

har zuwa lokacin bacci takeyi,shi kuma sata agaba yayi yana kuka,ko raunin hannunsa be dameshi ba.

 

likitocinne suka lura daciwon sannan sukabukaci daya taso ya biyosu,dan dole se an masa dinki dan yankan ya shiga sosai.

 

 

Binsu yayi badan yasoba,haka shima aka masa duk abinda ya dace,kan agama masa ma har yan sanda sun iso gurin,abisa kiran da hukumar asibitin tai musu.

 

 

Sa gidado,sukayi agaba da tanbayoyi,shide binsu kawai yake da ido,

 

Wayar likitan ya ara ya kira number mahaifinsa,yay masa bayanin komai,sosai hannkalin daddyn ya tashi,dan yasan dole kasar seta hukunta husna,ba irin nigeria bace,bare abada cin hanci asaketa.

 

Da kyar de gidado yayiwa yan sandan bayanin komai,ayko address din da ya basu suka bi zuwa gidanshi,

 

itako husna bayan fitar su gidado,da kyar ta iya mikewa a gurin,tana ganin jiri,hakade ta daure ta fito dags dakin zuwa dakin ligido.

 

Ganin jini ajikin husnane ya dagawa ligido hankali,tashiga tambayar,ta me ya faru.

 

murmushi tayi sannan tace.

 

“Na kashe,fatima”

 

 

“me!!!!!?”cewar ligido da idonta ya zazzago kamar goruba.

 

jikin ligido ne yashiga rawa tana fadin.

 

“kin mutu husna,kin taro match da messi,wlh jamian tsaron kasar nan va irin na Nigeria bane,me yakaiki aykata haka,husna me yasa bazaki fadamin abinda tai miki ba,me yasa,wayyo Allah na husna kin jamin komawa nigeria”cewar ligido cikin zubar da hawaye.

 

Suna tsaka da muhawarar yadda zasu bullowa lamarin,karar jiniyar yan sanda ta cika kofar gidan nasu,kan suyi wani yunkuri,tuni har sun shigo cikin gidan dan haka tasa keyarsu sukayi dukansu,zuwa cikin motarsu,tuni ligido ta fara tsinewa husna,a haka aka wuce dasu,

 

 

muje zuwa.

 

 

 

 

Surbajo for life

 

GIDADO BA SHEGE

BANE

 

 

 

 

Zahra Muhammad mahmud

 

 

 

A makarantar jahilci ajinmu daya da tsohuwa,Kuma kaf class dinmu ba wanda yakaita kokari,musamman in akazo yimana subject din makirci,da yawan yan class din ita muke tambaya ta fahimtar damu abinda ake nufi,shiyasa kaf taronmu na jahilan makarantar kowa ke girmamata,dan tafimu,kuma kowa ya yarda tafimun,Koda muka gama makarantar ba wani sakamako me kyau da muka samu,hakanne yasa muka yanke shawarar komawa islamiyya nida itabisa jagorancin Shawarwarin da yan uwa da abokan arziki suka bamu

 

KIRSA TASA MANZON ALLAH S,A,W YA SAKI AMARYARSA ADAREN DAYA AUROTA

 

MANZON ALLAH S,A,W, YAYI AMARYA,ADAREN DA AMARYA TA TARE,KAMIN ANGO YA SHIGA DAKINTA,SE MATANSA SUKAI AYARI SUKAJE GARETA,BAYAN SUNGAISA,SE SUKA CE MATA.” YANZU MUNZAMA DAYA DAKE TUNDA MIJINMU YA RIGA YA AUROKI,TO ZAMU FADA MIKI ABINDA MIJINMU YAFI SO MATARSA TA DUNGA FADA MASA,”

 

“MIJINMU A HAR KULLUM BA ABINDA YAKESO KAMAR KICE MASA AUZUBILLAHI MINKA”

 

SOSAI AMARYA TAI MUSU GODIYA GAMIDA NUNA JIN DADINTA,BAYAN FITARSU,SE MANZON ALLAH S,A,W YA SHIGO DAKINTA,YANA SHIGA DA SALLAMARSA,BUDAR BAKIN AMARYAR SE TACE “AUZUBILLAHI MINKA”SOSAI ABUN YA BASHI MAMAKI,SE YACE MATA,”KIN NEMI TSARI DAGA ABUNDA YAFI KOMAI ZAMANTOWA ALKHAIRI AGAREKI”TAKE A GURIN MANZON ALLAH SAW, YA SAKETA

 

SABIDA HAKA ME HANKALI SHI YAKE GANE KARATUN KURMA

 

 

Dedicated to Amina Maman Gidado

 

 

53-54

 

 

Bayan antafi dasu ligidone,gidado ƙarami,dake bacci a dakin gidado ya farka,ya fara kuka,da kyar ya gano hanyar fita falo,

 

koda ya fito falon kukanshi yaci gaba da yi tana kiran mummyn shi,har ya nufi ƙofar fita daga falon.

 

tsakar gidan ya nufa,yana kuka,megadin gidanne ya hangeshi,da sauri yaje ya daukeshi yana rarrashinshi,da kyar yayi shuru.

 

Acan asibiti ko,fatima ta farka da wani matsanancin ciwon ciki,se kuka take gidado na tayata,seda likirocin suka mata wata allurane cuwon ya lafa.

 

hannunta gidado ya rike yana kuka,murmushin karfin hali tai masa gamida girgiza masa,alamun yadena.

 

“taya zan iya yin shuru fatima?bayan da kina rayuwa cikin jindadi da annashuwa,cikin danginki,amman tundaga shigowar gudan jinina rayuwarki kika rasa komai na jin dadin rayuwa,haduwata dakene yadace yazama karshen shigarki cikin damuwa,amman kamar karo miki akeyi,yanzu princess da kin mutu me zancewa Allah,bayan kin sadaukar da farincikinki domin ni da dana”ya karasa maganar yana zubar da hawaye sosai.

 

Itama hawayen takeyi,da kyar bakinta ya bude,sede muryar bata fita sosai,shima karfin hali kawai tayi,dan tanajin zafi acikinta,a haka tace masa.

 

 

“komai kagani yasamu bawa daga Allah ne,nayiwa husna hakane sabida ina sonka,itama kuma tamin hakanne sabida tana sonka,da babu so daga ni har ita babu wacce zata yiwa yar uwarta daya daga cikin abunda mukayiwa juna,kuskuren husna,shine kasa fahimtar abinda ake nufi da kirsa,da ace tasan kirsa to ko makawa babu zata gano duk abinda nace mata karyane kawai,kuma abinda nayi,nayi imani,acikin mata dubu,se anyi saa asamu mutum goma da zasu iya yin hukunci me saukin wanda nayi,ki auri miji baki tare ba amiki kishiya,be fara kusantarkiba,ya kusanceta,sannan afito gaban ki ana miki wani kwarkwasa,wlh hubby na akwai matar da se ta kusa kashe ku daga kai har husnan,amman banyi hakanba,nai amfani da hikimata,nima na rama bakin cikin data turamin,ko kadan ni ban riketa arainaba,kuma banaso ka,saketa,kabarta muci gaba da,zama tare ayi zube ban kwaryata,amman tabbas,kirsa bazan dena yinta ba,dan banida kudin kaiwa malami,”

 

 

“bazan iya ba princess husna bata da hankali,nan gaba bansan me zatayi ba,kuma yanzu bazaa kyaleta ba,sabida su nan basa wasa da hukunci”

 

Murmushi tayi sannan tace.

 

 

“kada ka damu,nasan duk inda take yanzu tana cikin dana sani,nan gaba bazata sak aykata hakanba,dan haka kabata dama ta biyu”

 

 

Shide shuru yayi kawai yana kallonta,yana jinjina hakuri irin nata,kamin yayi mgn ma tuni bacci yayi gaba da ita sabida allurar da sukaimata dazi mesa bacci ce.

 

Se a lokacin ya tuno da danshi,dan haka agigice ya mike ya nufi motar shi,ya fice daga asibitin zuwa gida,

 

 

Yana parking ya hangi gidadon suna buga bsll da megadin,wanda megadin yanayine dan ya rarrasheshi yadena kuka.

 

yana fitowa daga motar gidado ya nufeshi yana murnar ganinsa,daukarshi yayi,yana masa wasa.

 

 

megadi ne ya karaso,gurin, yamasa bayani,akan kama husna da ligido da akayi.

 

murmushi kawai gidado yayi ya wuce cikin gidan,dauke da yaronshi,

 

 

dinning ya nufa inda kulolin abinci ke jere a gurin,wanda su fatima sukaci suka rage,budewa yayi yagani sannan yazuba yafara ba gidado yanaci,bayan ya koshine shima yaci,sannan yashiga dakinshi yayi wanka,ya shirya,sannan ya dauki gidado shima yamasa yasauya masa kaya,ya ɗaukeshi suka fice daga gidan zuwa asibiti.

 

 

 

Koda suka isa asibitin har lokacin bacci take,

 

 

Su husna ko nacan gurin yan sanda se kuka take tana danasanin abinda ta aykata,tayi Allah wadai,da hakan.

 

Gashi ance bazaa kaisu kotuba se fatima tasamu sauki tayiwa hukuma bayanin komai.

 

 

Haka rayuwa taita tafiya har tsawon sati biyu sannan fatima ta warke srai sedan abinda baa rasa ba.

 

koda yan sanda ke mata tambaya,cewa rayi husna bada saninta ba ta caka mata wukar,

 

 

yansandan sukace,to ay mijinsu yabada bayanin tana sane ta caka mata wukar.

 

 

Haka fatima ta dage kai da fata akan itade Husna batasaniba,dole tasa suka yarda sabida duk wata shaida da zasuyi amfani da ita bayan ta fatiman da aka cakawanne.

 

 

Haka aka sako husna da ligido,se kuka sukeyi,

 

daga gurin yansanda kai tsaye airport Gidado ya wuce da ligido,karkashin umarnin da fatima ta bashi.

 

 

ligido ko kadan bataso barin uk ba haka aka taso keyarta zuwa nigeria se kuka takeyi,gashi babu damar ta koma gidan iyayensa,tunda husna ta gama tona mata asiri agurin gidadon inda tace itace ke zigata.

 

bayan tafiyar ligido sosai husna tanemi yafiyar gidado amman duk yadda yayi da ita akan ta nemi yafiyar fatima fafur taki,yin hakan,dan aganinta ajintane ze zube.

 

Gidado daukar zafi yayi da husnan dakyar fatima ta bashi hakuri ya hakura ya yaleta.

 

Zaman doya da manjane yaci gaba da wanzuwa agidan,kowa inkaga dariyarta to tare da mijinta takeyi,ba ruwan wani da wani,duk yadda gidado yaso yaga sun hada kansu abun yaci tura,kuma laifin daga husnane,dan duk kwanan duniya se fatima ta gaisheta amman taki amsawa.

 

 

Iyayen gidado sosai sukai murna da godiya ga fatima abisa ceton husna da tayi daga faɗawa zaman gidan yari da tayi.

 

 

A haka har husna ta gama kwanakinta shiɗda da suka rage,

 

Bayan ta fita girkine fatima ta karbi girki,wanda kuma tasha alwashin sallamawa mijinta kanta koda kuwa be nemetaba,dole zata kwato fadarta da husna ta rigata shiga.

 

 

 

muje zuwa.

 

 

Surbajo for life.

 

GIDADO BA SHEGE

BANE

 

 

 

 

Zahra Muhammad Mahmud

 

 

Kuyi hakuri fans,for now bana chatting pc,both facebook/whatsapp,sabida inganta lafiyata,kuyi hakuri don Allah,dan kar kuga kunmin mgn ban baku amsa ba,ngd sosai da yadda kuka tsaya kai da fata gurin ganin kun sharemin kukana akan abinda akamin ngd sosai Allah yabar zumunci,ina sonku sosai ko a ina kuke

 

 

Dedicated to Amina maman Gidado

 

 

 

55-56

 

 

 

Ko girki da fatima tayi na gani na fada ne,dan komai na musamman ne,kan wani lokaci tuni gidan ya bade da kamshi.

 

Tana gama girki,dakinshi ta nufa ta fara gyarawa,shima gyaran dakin na musamman ne,tuni dakin yafara fitar da kamshi me sanyaya zuciya.

 

Daga dakinshi nata ta nufa,komai cikin sauri takeyinshi sabida,gidado ya kusa dawowa.

 

Gidado karami tayiwa wanka,sannan ta shiryashi shima se kamshi yakeyi,kamanninshi da mahaifinsa suka kara fitowa.

 

 

Tana gama shirya shi,ita ma ta fada toilet,tayi wanka gamida dauro alwala,shi kanshi wankan da tayi na musamman ne.

 

Sallah ta fara yi tukuna,sannan taje gaban mirror tafara tsantsara kwalliyar da bata taba yin irinta ba.

 

Kyanta ne ya fito na musamman,wata doguwar riga tasa yar kanti marroon colour,wacce ta kasance me hannun ves,daga saman rigar tana da faffadan wuya,yayinda kirjin rigar ya kasance lase ne,hakan ya janyo ana ita ganin albarkar dake kirjinta kasancewar bra mara hannu tasaka,yayinda rigar ke dauke da wani tsaga tun daga kasa har saman cinyarta,ta gefen kafarta ta hagu,yayinda rigar taba hips dinta damar watayawa acikin rigar kasancewar rigar rober ce,gashin kanta bata sa masa ribom ba sakinshi tayi zuwa gadon bayanta,takalmi me igiya ne kuma me tudune sosai akafarta,shima maroon,

 

Hmmmm me karatu ka hangomin fati na abunka da farar mace acikin maroon din kaya,abun baa cewa komai.

 

iya kyau fatima tayishi,na daukar hankali, gashi koya ta motsa mazaunanta suma sesun motsa.

 

barin turare tayiwa jikinta,tana ajiye turaren taji karar tsayuwar motar mr right dinta.

 

Da sauri ta ajiye komai a mazauninsa,sannan ta juya ta fice daga dakin ta nufi gurin tarbo mijinta,cikin takunta me daukar hankalin me kallonta walau namiji walau mace.

 

Lokacin data fito,husna na zaune a falon tana kallon wani film da tashar joy prime ke haskawa,me suna,jorda akhbar,gidado karami kuma nakan kekenshi na yara yana wasanshi.

 

 

Takun fatima ne ya waigo da husna gurinta,ba karamar firgita husna tayiba da ganinta,gaba ɗaya daburcewa tayi,itako se murmushi take sakar mata wanda ke karawa fuskar tata kyau.

 

Gidado ne ya turo kofar falon ya shigo,da sallamarsa gami da fadin.

 

“My Hus-Gi-Fat”ya fadi cikin murmushi.

 

idonshi ne ya sauka kan fatima dake taka rawar odonko wata wakace da ake yin tallan wani magani a tashar joyprime din,kai da ganin yadda take rawar,kasan dama danshi takeyi,

 

 

jakar hannunshi ce ta subuce ta fadi,batare da yasaniba,baki sake yake kallon fatin tasa.

 

haka ta taka zuwa gurinshi tana cigaba da rawar tana juyawa har ta iso gurinshi.

 

tana zuwa bata ce masa komaiba dukawa tayi daidai setin marar shi,ta kaiwa…,kiss,gamida furta.

 

 

“Your fat is always with you and your hus and gi are also fine,you’re highly welcome back my soul mate”ta fadi gamida mannan fuskarta cikin marar tashi.

 

A birkice yasa hannu ya dagota ya mannata da kirjinshi,dan ji yake zuciyarshi kamar zata fado in be hadata da kirjinshi ba.

 

kara narkewa tayi ajikinshi,tana masa shagwabar tayi missing dinshi,

 

Shiko yama rasa inda zesa ta yaji dadi,dan tunda yake be taba fadawa yanayin da yake ciki yanzuba.

 

wayyo husna ta,idonta yamata mugun gani,tayi danasanin sanin tashar joyprime bare wani jorda akhbar,tayi danasanin kin zama tayi kallon a dakinta,zuciyarta wata irin suya take mata wacce takeji kamar taje ta shake fatiman,

 

 

Shiko gidado har ga Allah besan husna na gurinba tun farkon shigowarshi,bare yanzu da network dinshi ya kauce.

 

Dukawa fatima tayi ta dauki jakarshi,shi kuma ya dauketa cak suka nufi dakinshi,

 

GIDADO BA SHEGE

BANE

 

 

 

 

Zahra Muhammad Mahmud

 

 

Kuyi hakuri fans,for now bana chatting pc,both facebook/whatsapp,sabida inganta lafiyata,kuyi hakuri don Allah,dan kar kuga kunmin mgn ban baku amsa ba,ngd sosai da yadda kuka tsaya kai da fata gurin ganin kun sharemin kukana akan abinda akamin ngd sosai Allah yabar zumunci,ina sonku sosai ko a ina kuke

 

 

Dedicated to Amina maman Gidado

 

 

 

55-56

 

 

 

Ko girki da fatima tayi na gani na fada ne,dan komai na musamman ne,kan wani lokaci tuni gidan ya bade da kamshi.

 

Tana gama girki,dakinshi ta nufa ta fara gyarawa,shima gyaran dakin na musamman ne,tuni dakin yafara fitar da kamshi me sanyaya zuciya.

 

Daga dakinshi nata ta nufa,komai cikin sauri takeyinshi sabida,gidado ya kusa dawowa.

 

Gidado karami tayiwa wanka,sannan ta shiryashi shima se kamshi yakeyi,kamanninshi da mahaifinsa suka kara fitowa.

 

 

Tana gama shirya shi,ita ma ta fada toilet,tayi wanka gamida dauro alwala,shi kanshi wankan da tayi na musamman ne.

 

Sallah ta fara yi tukuna,sannan taje gaban mirror tafara tsantsara kwalliyar da bata taba yin irinta ba.

 

Kyanta ne ya fito na musamman,wata doguwar riga tasa yar kanti marroon colour,wacce ta kasance me hannun ves,daga saman rigar tana da faffadan wuya,yayinda kirjin rigar ya kasance lase ne,hakan ya janyo ana ita ganin albarkar dake kirjinta kasancewar bra mara hannu tasaka,yayinda rigar ke dauke da wani tsaga tun daga kasa har saman cinyarta,ta gefen kafarta ta hagu,yayinda rigar taba hips dinta damar watayawa acikin rigar kasancewar rigar rober ce,gashin kanta bata sa masa ribom ba sakinshi tayi zuwa gadon bayanta,takalmi me igiya ne kuma me tudune sosai akafarta,shima maroon,

 

Hmmmm me karatu ka hangomin fati na abunka da farar mace acikin maroon din kaya,abun baa cewa komai.

 

iya kyau fatima tayishi,na daukar hankali, gashi koya ta motsa mazaunanta suma sesun motsa.

 

barin turare tayiwa jikinta,tana ajiye turaren taji karar tsayuwar motar mr right dinta.

 

Da sauri ta ajiye komai a mazauninsa,sannan ta juya ta fice daga dakin ta nufi gurin tarbo mijinta,cikin takunta me daukar hankalin me kallonta walau namiji walau mace.

 

Lokacin data fito,husna na zaune a falon tana kallon wani film da tashar joy prime ke haskawa,me suna,jorda akhbar,gidado karami kuma nakan kekenshi na yara yana wasanshi.

 

 

Takun fatima ne ya waigo da husna gurinta,ba karamar firgita husna tayiba da ganinta,gaba ɗaya daburcewa tayi,itako se murmushi take sakar mata wanda ke karawa fuskar tata kyau.

 

Gidado ne ya turo kofar falon ya shigo,da sallamarsa gami da fadin.

 

“My Hus-Gi-Fat”ya fadi cikin murmushi.

 

idonshi ne ya sauka kan fatima dake taka rawar odonko wata wakace da ake yin tallan wani magani a tashar joyprime din,kai da ganin yadda take rawar,kasan dama danshi takeyi,

 

 

jakar hannunshi ce ta subuce ta fadi,batare da yasaniba,baki sake yake kallon fatin tasa.

 

haka ta taka zuwa gurinshi tana cigaba da rawar tana juyawa har ta iso gurinshi.

 

tana zuwa bata ce masa komaiba dukawa tayi daidai setin marar shi,ta kaiwa…,kiss,gamida furta.

 

 

“hus-gi-fat we are all fine,you’re highly welcome back my soul mate”ta fadi gamida mannan fuskarta cikin marar tashi.

 

A birkice yasa hannu ya dagota ya mannata da kirjinshi,dan ji yake zuciyarshi kamar zata fado in be hadata da kirjinshi ba.

 

kara narkewa tayi ajikinshi,tana masa shagwabar tayi missing dinshi,

 

Shiko yama rasa inda zesa ta yaji dadi,dan tunda yake be taba fadawa yanayin da yake ciki yanzuba.

 

wayyo husna ta,idonta yamata mugun gani,tayi danasanin sanin tashar joyprime bare wani jorda akhbar,tayi danasanin kin zama tayi kallon a dakinta,zuciyarta wata irin suya take mata wacce takeji kamar taje ta shake fatiman,

 

 

Shiko gidado har ga Allah besan husna na gurinba tun farkon shigowarshi,bare yanzu da network dinshi ya kauce.

 

Dukawa fatima tayi ta dauki jakarshi,shi kuma ya dauketa cak suka nufi dakinshi,

 

 

Tofa.

 

 

kuyi hakuri banda lfy ne wlh.

 

 

muje zuwa

 

 

 

 

surbajo for life.

 

Tofa.

 

 

kuyi hakuri banda lfy ne wlh.

 

 

muje zuwa

 

 

 

 

surbajo for life.

 

GIDADO BA SHEGE

BANE

 

 

Zahra muhammad mahmud

 

Dedicated to Amina Maman Gidado

 

57-58

 

Suna shiga dakin shi,ta fara tsille tsille har seda ya sauketa,yana ajiyeta da gudu taja baya tana kallonshi ta fito da idanu waje,kai da gani kasan atsorace take.

 

Abun nata dariya ma yaba gidado dan haka zama yayi gefen kujera yana dariyar.

 

Dagowa yayi yana dubanta tayi wiki wiki kamar anjika zakara,wata sabuwar dariyarce ta kubce masa,mikewa yayi yafara takawa inda take,

 

Ja da baya ta fara yi,yana binta har seda suka isa jikin bango,matseta yayi ajikin bangon,ita ko tabe baki tayi tana shirin sa masa kuka.

 

Hannu yasa ya shafo hips dinta zuwa mazaunanta,ya dire kan kirjinta,itade runtse ido tayi,dariya yayi,yace.

 

“Don Allah ji mace har mace,amman tana tsoron mijinta,ji baya don Allah,wlh princess kunya kike bani,ki ganki fa,fulawa har fulawa amman ba ban ruwa,wlh bushewa zakizo kiyi”

 

Cike da shagwaba tace.

 

“Eh din naji,nide kabani guri in wuce”

 

Murmushi yayi Gamida dukan mazaunanta yace.

 

“ke kin iya kirsa ko?to yau nima zan koya miki irin kirsarmu ta maza,dan wlh yau bazan kyaleki ba”

 

ture hannunshi tayi daga jikinta,dan sosai ta tsorata da batunsa,shiko dariya yake,yace.

 

“jeki hadamin ruwan wanka,”

 

jiki a sanyaye ta nufi toilet din,bin bayanta yayi da kallo yan kisma yadda ze huce gajiyarshi yau da daddare.

 

bata jimaba ta fito ta shaida mishi ta hada.

 

“muje kimin”yafadi cikin tsokana.

 

make kafada tayi alamun bazata ba.

 

Shigewa yayi toilet din,kamin ya fito ta fito mai da kayan sawa.

 

har ya fito ya shirya,sannan suka fito zuwa dinning area domin yaci abinci.

 

Husna bayan shigarsu daki,dakyar ta iya barin gurin ta nufi dakinta,duk yadda taso ta daure kartayi kuka amman ina seda tasha kukanta kamar wacce akawa mutuwa.

 

Gidado karami ko ko ajikinshi wasanshi yashiga yi afalon.

 

Bayan sunci abincine Gidado se santi yake mata,dan abincin sosai yamasa dadi.

 

Yana gama cin abincin mikewa yayi ya nufi dakin husna,inda ita kuma fatima ta gyara gurin,sannan taja danta suka nufi dakinta tai masa wanka itama tayi,ta sa wata arniyar rigar bacci,hmm abun baa cewa komai.

 

Shiko gidado,yana shiga dakin husna samunta yayi tayi rashe rashe tana kuka,da sauri ya karasa kusa da ita,yana tambayarta me ya faru.

 

“Baby na me ya sameki?”

 

sake rushewa tayi da kuka,da sauri ya janyota jikinshi,ya dorata kan cinyarshi bayan ya zauna,yaci gaba da cewa.

 

“fadamin me yafaru kinji babyna”

 

Cusa kanta tayi a kirjinshi,tana kukanta,da kyar ya samu tayi shuru,tace.

 

“ba ku bane ku kayi abinda ya batamin rai a falo bayan kuma kunsan ina gurin”ta karasa maganar tana kuka.

 

Murmushi yayi yana dan dukan bayanta,se yanzu ya tuno abinda yasa fatima ta birkitashi tun daga falo,ashe dan tasan husna na gurinne,wanda shi bemasan tana gurinba.

 

Dago fuskarta yayi ya hada goshinsu guri guda,yace mata.

 

“Baby na ki kwantar da hankalinki kinji,karki sake yin kuka gameda hakan,kema duk ranar girkinki kudunga yimin kema kinji ko,kuma koda anyimin agabanki kar ki nuna kinji haushi kinji ko yar kanwata”

 

murmushi tayi gamida gyada masa kai,dan shinshina wuyanta,yayi sannan yace cikin wasa.

 

“hmmm kanwata batayi wanka ba,shiyasa nakejin tsami tsami”

 

dukan wasa takai masa na wasa tana kukan shagwaba.

 

mikewa yayi yaje toilet da kansa ya hada mata ruwan wanka,sannan yazo ya dauketa da kanshi yamata wankan,

 

husna jinta take kamar wata sarauniya,ganin yadda gidado yau ya rarrasheta.

 

da kanshi ya shiryata,sannan ya jata suka fito falo.dan taci abinci.

 

Inda suka sami Fatima zaune sanye da after dress tana kallo,amman a zahirin gaskiya ba kallon takeba,zuciyarta na gurin gidado,wanda ya dauki tsawon awa guda a dakin husna

 

da ido tabisu yayinda husna ta fara wani iyayi ita ala dole me miji.

 

Guri suka samu suka zauna,inda husna tace.

 

“amman bross nafa ji dadin wankannan da kamin kaji yadda iska ke ratsani kuwa,gaskiya ka samu lada”

 

Ran fatima in yayi dubu ya baci jin abinda huana tace,amman a fili murmushi tayi sannan tace.

 

“Ay dama shuru nayi naji yamikin ko be miki ba,ashe yayi,gaskiya bross dinki na ji dake,tunda muka shiga daki in banda zancanki ba abinda yakemin,ki godewa Allah kinji husna”

 

Wani kallon banza husna ta watsa mata,sannan tace.

 

“ay ko baki fadi ba nasan yana ji dani”ta fadi gamida kwantar da kanta a kafadarshi.

 

Murmushi fatima tayi sannan tace.

 

“Tunda abun naki hakane,to bari na fasa kwan kowa yaji warin,to shi kanshi shiga dakin naki ni nace masa yaje,kuma na bashi umarnin yamiki wanka dan ɓa shaida mishi tun safe bakiyi wanka ba”ta karasa maganar tana dariya,

 

Da sauri husna takai dubanta gurin gidado wanda tunda suka fara yake dariya,tace.

 

“Wai hakanw bross?”

 

Dariya ta hanashi bata amsa,da sauri fatima tace tana dariya.

 

“hakane mana,meye na tambayarshi”.

 

Ganin ran husna ya fara bacine,yasa gidado y rungumosu dukansu jikinshi yace.

 

“Dukanku kun fadi gaskiya,ba wacce tayi karya”

 

Turo baki gaba husna rayi gami da cewa.

 

“utance kenan tasaka kamin wankan?”

 

“Baby rigima,kawaide naga bakiyi bane yasa nai miki,auntynki tsokanarki takeyi,batamasan zan shigo gurinki ba”

 

Da sauei husna ta dubi fuskar fatima,

 

murmushi fatima tai mata tace.

 

“bross gaskiya ya fadi,shalelen bross,”

 

wani dadine ya ratsa zuciyarta,hannu  tasa ta rungumeshi.

 

Ranar de sun jima suna hira,wani fatima ta tsokani husna tai fushi wani kuma su sata dariya,dan sun fahimci tsabar yarinta ce ke damunta.

 

se karfe goma na dare hirar ta watse,inda gidado ya raka husna har daki,ita kuma fatima taje ta dauko gidado karami ta kawowa,husna,ba musu ta amsheshi taje ta kwantar dashi,sannan sukai mata sallama.

 

Suna zuwa falo,gudado ta suri fatima se dakinshi.

 

tunda ya cire after dress din jikinta ya fara fita hayyacinshi,

 

da kyar suka dangana da kan gado,yafara dirje guminshi,

 

Abunfa ya wuce tunaninsu duka,fatima kuka take tana rokonshi,shi kuma kuka yake sabida dadin duniyar da yakw ciki,

 

banvancin a bayyane yake tsakaninta da sauran matan.

 

Fatima tasha wuya sosai a hannunshi,wanda tun tana kuka har tadena,shiko kukansa sisai yasha,kai kace dukanshi akeyi.

 

be saurara mata ba,se gefin asuba,tunda ya mirgine gefe,shi kanshi ko motsin bayayi.

 

muje zuwa

 

Surbajo for life .

 

GID’AD’O BA SHEGE

BANE

 

 

Zahra Muhammad Mahmud

 

Dedicated to Amina Maman Gidado

 

59-60

 

Suna kwance kowa baya iya motsawa,fatima hawayene kawai ke zuba a fuskarta,anashi bangaren shima hawayen yakeyi,dan baze iya misalta iein natsuwar da ya samu da ita ba.

 

Kusan 20minutes suna kwance,zuwa lokacin tuni zazzabi ya rufe fatima,rawar sanyin da takene yasa gidado mikewa dakyar,ya nufi toilet.

 

Ruwan wanka,ya hada mata,me zafi,sannan yazo ya dauketa zuwa toilet din,se tangadi yake kamar abuge yake.

 

Da kyar de yasamu yanata wankan shima yayi,ya nadota a towel zuwa daki.

 

Kwantar da ita yayi sannan yanufi locker dake gefengadon yana neman magani daze bata,firfito da kayan cikin yayi yanata ajiyewa agefen gadon da take kwance.

 

Kwatsam idonta ya sauka kan wani abu da yake mallakinta ne,kuma tasan rabonta da wannan abu tun tana lavel two hundred a makaranta,

 

Jikinta har rawa yake gurin mika hannu ta dauki abun tana kallo,tabbas shine,to Amman me ya kawoshi gurin gidado.

 

Tana rike da abun har yadauko maganin ya juyo gareta,ganinta rike dashine yasa yayi murmushi,yace.

 

“my princess kina so ne?”

 

Rufe idonta tayi,sabida wata kunyarshi ce ta ziyarceta.

 

Bata maganin yayi tasha,sannan yajata jikinshi,suka koma bacci,se albarka yake samata,gamid nuna mata jin dadin shi game da yadd ya sameta.

 

Ita de ta kasa bacci tunaninta taya yasamu wannan abu?bacci barawo ne ya saceta.

 

Koda safiya tayi,dakyar tayi sallah sabida jikinta duk ciwo yake,shima da taimakon gidado tasamu tayi din.

 

Bacci suka koma,har zuwa karfe goma na safe,

 

Ita ko husna tunda ta tashi bata koma ba sabida sarkin barna daya tashi,yana ta bidiri.

 

Karfe tara suke breakfast amman taga har goma shuru,hakanne yasa ta fito ta nufi kitchen da kanta, ta hada abincin ita da gidado karami.

 

Acan dakin kuwa gidado ne ya shiga wanka,bayan ya fito ya shirya,cikin shigar alfarma,itako fatima har lokacin bacci take hankali kwance.

 

Ficewa yayi zuwa falon inda yasamu husna na zaunar da gidado kan kujera domin suci abincin.

 

Karasawa yayi gurinsu ya rungumesu duka,sannan yace.

 

“rigimammuna yakuke,?”

 

murmushi husna tayi sannan tace.

 

“lafiyar lau,kawai yau an mana horon yunwa”ta karasa maganar cikin sigar zolaya.

 

Dariya yayi yaka kumatunta,sannan yaja kujera ya zauna yace.

 

“Auntyn takine ba lafiya shiyasa”

 

A haukan husna ta dauka laulayi take dan ita zatonta fatima anjima dajin mazadan haka se tace.

 

“Ayya Allah ya bata lfy,ya raba lfy kuma”

 

Dariya kawai yay mata yasa hannu akaci abincin dashi.

 

Bayan sun gamane,ya roki husna ta dafawa fatima nata abincin,

 

ba laifi batai musuba taje ta dafadin.

 

shi kuma zuwa yayi ya lallabi  fatima ta tashi yay mata wanka yaje ya dauko mata kayanta tasaka,sannan ya janyo hannunta zuwa falon,tana jin zafin hade cinyoyinta amman haka take daurewa tana hadawa,dan kar husna ta fahimci komai.

 

Husna gaisheta tayi gamida mata fatan samun lfy.

 

Abincin taci,sannan tasake shan magani.

 

Dayake gidado beda ayki ranar zama cikinsu yayi,ana ta hira,itade fatima zuciyarta taki yimata dadi,gameda abunda ta gani jiya.

 

Mikewa tayi ta nufi dakin nashi,da sauri yabi bayanta,suna shiga,tace masa.

 

“hubby don Allah zoben jiya a ina kasameshi?”

 

Murmushi yayi yajata,jikinshi suka zauna akan kujera,sannan yace.

 

“na maman gidado ne,ranar da zamu rabu da ita ta bani shi”

 

A firgice tabishi da ido,tace bakinta na rawa,

 

“Kana nufin ita ta baka shi da kanta?”

 

“yes”ya bata amsa.

 

Gabadaya firgice masa tayi tana kuka,tana fadin,

 

“inde hakane wlh ta cutar dani,ta azabtar dani bazan yafe mata ba”

 

Jijjigata yake yanaso ta dawo haytacinta dan gani yake ta fita hankalintane.

 

“princess pls tell me,kin santa ne?”

 

“na santa wlh na santa”

 

Sosai batun nata ya rudashi da sauri yace

 

“wacece to kuma a ina take?”

 

“Amina ce,hubby wlh Amina ce”tayi maganar tana kuka.

 

Rungumeta yayi sosai ajikinshi,yace.

 

“meye alakarki da ita?”

 

“kawatace a makaranta,zoben nan nawane,tun muna lave two hundred,ta nemi dana bata shi inason zoben haka na daure nabata sabida amintarmu”tasake rushewa da kuka.

 

Shuru yayi yana nazari,zuwacan yace.

 

“to yanzu a ina zamu ganta?”

 

“nima bansaniba,sede mu gwada nemanta a facebook dan nasan sunan da take amfani dashi ada amman ban saniba ko ta sauya”

 

Da sauri ya dauko wayarshi ya shiga facebook,yasa sunan da ta fada masa,ay bayyanar hotonta akan dp dinta seda hanjin cikinshi ya karta,dan da dauka yake duk zafin first night dinne yasa fatima sambatu.

 

Ci gaba yayi da duba profile din nata,inda yaga wani gurin ta rubuta sunan shi,da manyan harruffa,inda tace.

 

“Looking for you Gidado”

 

Wani gurin kuma tasa.

 

“forgive me fatima”

 

wani gurin kuma tasa.

 

“i miss my son”

 

Daga gidadon har fatiman kuka sukeyi da suka fahimci itama tana nemansu.

 

Suna zaune sega gidado karami ya shigo,da sauri gidado ya daukeshi,janyo fatima jikinshi yasa wayar shi ya daukesu hoto,

 

Sosai sukayi kyau a hoton,yana gama dauka,se yaje inda tace tana nemansa gurin comments,se ya tura hotunan,gamida cewa.

 

“Muma neman naki mukeyi tuntuni,”gamida number wayarshi.

 

Bayan ya tura ne ya maida hankalinsa kan fatima dake ta faman kuka,tambayarta yayi,abinda yasata kukan.

 

“ina mamakin abinda yasa amina zata yadda danta,kuma sannan tafi kowa zakewa gurin cewa nawa ne,wannan abu yafi komai cimin rai”ta karasa batun cikin kuka.

 

Rungumeta yayi yanata rarrashinta.

 

 

 

Anata bangaren kuwa Tabbas Amina itace mahaifiyar gidado.

 

Tana cikin halin bakin ciki gami da tsangwamar dangin mijinta gameda rashin haihuwarta,tayi kuka har ta godewa Allah,

 

Yanzu haka tana dauke da hawan jini sabida damuwa,ta nemi address din su fatima taje sede yayan fatiman cemata yayi shima nemanta yake ya nemi gafarar ta.

 

Sanda taji abunda yasami fatima sanadinta ranar a asibiti ta kwana,neman fatima take ruwa a jallo ta nemi gafararta,

 

muje zuwa.

 

Surbajo for life.

 

GID’AD’O BA SHEGE

BANE

 

 

Zahra muhammad mahmud

 

Rukayya Hassan Usman,naga book nagode sosai Allah yabar zumunci,Allah ya kara daukaka da basira,naji dadi sosai,

 

Zuwairat ummu Maryam,surbajo takice,kina bamu feelings sosai Allah yakara basira,daukaka kinsamu sede muyi fatan ki dade ki karko♥

 

Aisha Yar’aduwa,nakasa magana,domin dukan girma kikamin litattafai wajen uku,duka nawa ni kadai surbajo,gaskiya kinyi matukar sani farinciki,Allah ya kara miki basira da daukaka ina sonki sosai acikin raina

 

Hafsat bello,mijin mum dinmu nakai mana karo fa,nagode sosai hafsat Allah yabar zumunci yakara daukaka da basira ngd

 

munira,me Amatullah,kema ina godiya Allah yabar zumunci yakara basira,ke masoyiyace ta hakika nasan hakan Allah yabarmu tare

 

Halilose madubin surbajo,Allah yabarminke kijima ki karko,nidake mutu ka raba takalmin kaza

 

Dedicated to Amina Maman Gidado

 

61-62

 

Kwance take,akan cinyar mijinta tana latsa wayarta,kallo daya zaka mata kasan tana cikin damuwa.

 

“my dear ni bansan damuwarki ba,kwana biyu ko bacci bakya yi,in batun su hajiya ke damunki naga ay yanzu ta kwana biyu bata zo ba,pls ki fadamin damuwarki,dan na gaji da ganinki haka”cewar mijinta ibrahim dake shafa kanta.

 

Wasu hawayene suka biyo fuskar Amina,masu zafi,da kyar tace.

 

“my love,bakina zeyi wuyar sanar dakai damuwata,sabida sanar dakai na nufin kawo karshen zamana dakai ne,sabida zaka tsaneni,shiyasa bazan iya sanar dakai ba”ta karasa maganar cikin matsanancin kuka.

 

Hankalinshi ne ya tashi,ganin tana kukan,janta jikin shi yayi ya rungumeta,yana rarrashinta,gamida furta.

 

“Ba abinda ze rabani dake matata komai muninsa,ni zan zauna dake,kidena tunanin rabuwarmu pls”

 

murmushin takaici tayi,sannan tace.

 

“koda kuwa laifin da nayi maka yakai girman ace,ba budurwa ka aureni ba?”

 

A zabure ya tureta daga jikinshi,yana furta

 

“what!!!!look Amina ya isa haka,banason wasa irin haka,pls,kinsanni da zafin kishi karkisa na aykata abinda baze mana dadi ba nida ke”yafadi rai abace.

 

Murmushi tayi sannan tace.

 

“lalle ka tanaji takarda da biro kusa,dan igiyar auranka,lilo take,sabida na lura bazaka rungumi kaddarar data fadawa matarka ba,zan sanar dakai komai amman se ranar dana samu cikakken bayani daga garesu jinin jikina”

 

Tana kaiwa nan ta kwanta abinta akan kujerar,tana danna wayarta.

 

Ibrahim tsayawa yayi kamar gunki yana kallonta,dan gaba daya tasashi a rudani.

 

Kamar wasa Amina ta kunna data,ta shiga facebook,

 

“Gidado Adam maliya commented on your post”

 

Shine abu na farko da Amina taci karo dashi a Notification dinta.

 

jikinta bari yake,haka hannunta,gurin shiga taga me yace.

 

Wayyo Allah na,hotonshi dana dansu da fatima ta gani,gashi kuma yace,”muma nemanki muke”

 

Wata kara ta kwallah,kawai ta yanke jiki ta fadi sumammiya,

 

da gudu ibrahim yayi kanta,yana kiran sunanta,amman ko alamun numfashi babu a tattare da ita.

 

da gudu ya dauketa zuwa mota,se asibiti,nanfa likitoci suka rufu akanta,duk wani abu da ya dace shi sukai mata,cikin hukuncin Allah ta farka,

 

In banda kuka babu abinda takeyi,rungumeta ibrahim yayi yana rarrashinta,amman fafur taki tayi shuru,daga karshema,fige cannular da ake samata drip tayi tace su koma gida.

 

Duk yadda akaso a hanata tafiya amman fafur taki amincewa.

 

dole tasa ibrahim yabita suka tafi gidan,suna zuwa wayarta ta dauka  dake kasan carpet.

 

Hotunan,ta dibo tana kuka ta mika masa,ya karba yana kallo,cikin rashin fahimta yace.

 

“naga mata da miji da dansu,me ya faru dasu?”

 

“macen kawatace,namijin tsohon mijinane,yaron kuma danane nida shi”

 

wani zazzafan mari daya sauka akan fuskarta shi ya katse mata duk abinda tayi niyyar fadi.

 

ibrahim ne ya mareta sannan yasa kafa ya kwasheta ta fadi kasa yabita yasa hannu ya shake mata wuya yana fadin.

 

“ni saanki ne da zaki dunga fadamin wainnan mugayen maganganun,a gidan ubanwa ya zama mijinki?”

 

Dakyar Amina tasamu ta kwace daga shakar da ya mata,ta angajeshi,da gudu ta dauki wayarta ta fice daga gidan,

 

Kasancewar motar da suka dawo aciki,be cire key ba sabida zaa wanketa,batayi kasa a guiwaba,ta fada motar,tana tada ita ibrahim ya karaso gurin kamar wani tsohon zaki,ayko da gudu ta fice daga gidan,dan megadi tana ganin ta shiga mota ya bude get.

 

Se bayan ta fice ne ya tsinkayo muryar ibrahim yana fadin.

 

“karka barta ta fita”

 

ta baya ta rago,tuni amina ta jima da hawa titi domin zuwa gidan iyayenta.

 

Muje zuwa.

 

Surbajo for life.

 

 

GIDADO BA SHEGE

BANE

 

 

 

 

Zahra muhammad mahmud

 

 

My Eshat Mustapha,my Hafsat Dahir,Allah ya saukeku lafiya,ya kawo mana babys dinmu cikin sauki,Amin don alfarmar Annabi

 

Salma b bata da mashinshini,bare insa ran baby kwanannandama banda kishi ay da kin shigo na karaki

Salman jb,ba mashinshini shamadarallilo

 

 

Dedicated to Amina Maman Gidado

 

 

63-64

 

 

Da gudu ta fada falon gidansu,bayan ta yi parking din motar.

 

Kuka take,ga haki da takeyi kai kace akafarta tazo,da rarrafe ta karasa cikin falon.

 

Mamanta ce,ta fito da sauri daga dakinta dan taji karar bude kofa,shiyasa ta fito ganin ko waye.

 

Ganin Amina a halin da take ciki shi ya daga mata hankali,da sauri ta nufo aminan tana tambayarta.

 

“Amina lafiyanki kuwa?me ya sameki?ina ibrahim din?”ta karasa maganar sanda ta rungumota jikinta.

 

Rushewa tayi da wani matsanancin kuka,sannan tace cikin kukan.

 

“Mama na shiga uku,ina cikin matsala,dama na fada miki mama ba lalle ne asirinmu ya rufu ba,yau gashi ranar tonon asirin tazo,wayyo na shiga uku,mama ibrahim yau kasheni yayi niyya Allah ne kawai ya taimakeni”

 

“Banganeba kimin bayani,wanne asirine namu ze tonu yau,ki sanar dani?”

 

“mama batun kwantarmin da cikin da kikasa likita yayi,shi nake nufi”

 

Azabure maman ta mike tana salati,tana fadin.

 

“Na shiga uku yau ni ina zansa rayuwata,amina kina nufin yanzu cikin ya tashi kenan?”

 

“Mama ciki ya tashi tun shekaru uku da suka wuce,har ma na haifi abinda ke cikina,sede,na yarda dan gudun tonuwar asirina”ta karasa maganar cikin matsanan cin kuka.

 

tsananin mamaki ya hana mamanta magana,illa mikewa da tayi ta jata suka shige dakinta,gudun kar wani ya jiyo su.

 

Kuka Amina takeyi haka itama uwar kukan takeyi wanda cikin kukan tace.

 

“Haba Amina,meyasa kikayi shuru baki sanar dani damuwarki ba,meyasa,kika zabi yarda yaron,akan kikawominshi na eaineshi amatsayin tsintoshi mukayi?meyasa kika aykata wannan rashin imanin?”

 

“Mama banaso auranki ya mutu ne,banaso wata matsala ta shiga tsakaninki da mahaifina,shiyasa na zabi hakan”tayi maganar cikin kuka.

 

“yanzu a ina kika yarda yaron?”

 

“ki kwantar da hankalinki mama,yanzu haka yaron yana tare da mahaifinsa,tare da kawata,sede bansan yadda akayi har yaron yasami mahaifinsa ba”

 

Daga haka ta nuno hotunan da gidado ya turo mata ta nunawa maman,se alokacin ta lura da number wayar daya turo.

 

jikinta bari yake kamar mazari,ta dauki wayar mamanta,tasa number ta kira.

 

Adaidai lokacin,gidado da fatima da gidado karami sun tafi shopping,sabida gobe ne birthday din husna,sun barota a gida ana mata gyaran jiki,dan yanzu babu wani kishi me zafi tsakaninsu.

 

Wayarshi ce ta fara ringing,da ya share kamar baze dauka ba,cande ya sauka gefen titi sannan ya dauki wayar.

 

“hello wa ke mgn?”ya tambaya.

 

jin muryarshi da amina tayi kawai seta rushe mishi da kuka,

 

Gaban gidado ne yay mugun faduwa,dan wannan sautin kukan ko amafarki aka tasheshi ze faɗi wanda yake kukan,dan irinshi takeyi asanda aka tilasta mishi kusantarta.

 

Runtse idanu yayi yana sauraron kukan nata,wanda ke taba masa zuciya,ira taki denawa,shi kuma yagaza mgn.

 

Da kyar ya iya bude baki yace.

 

“ya isa haka,pls banason kukan,in kuma ba so kike nima nayi ba”

 

shuru tayi ammande ta kasa mgn,

 

Shima shurun yayi,ga fatima dakw gefe ta kureshi da idanunta,tanason sanin da wa yake mgn.

 

cigaba yayi da mgn da cewa.

 

“Kina ina yanzu?”

 

 

cikin kuka tace.

 

 

“ina Abuja”

 

“Bana nigeria ni yanzu haka,but zanyi kokarin zuwa next week”

 

 

Jin alamun ze kashe wayar ne yasa tayi saurin cewa.

 

“Don Allah kana tare da fatima da danane?”

 

murmushi yayi sannan yace.

 

“Danki ko dan fatima,ki gyara hausar taki,ina tarw dasu yanzu haka zamuje anguwa,ne”

 

Shuru tayi ta kasa mgn,dan tabbas abinda ya fadi beyi karya ba,jira yake yaji tayi mgn,kawai sejiyayi ta rushe da kuka,tana fadin.

 

“Dan fatima ne,amman wlh nima danane”tayi mgnr cikin shagwaba,wacce taba gidado dariya sosai hakan ya tuno masa da zamanshi da ita a asibiti.

 

“To naji danki ne,kibari muzo nigeria din se yaron ya nuna mana mamansa kinji ko”

 

 

Yana kaiwa nan yakashe wayarshi,haka kawai ya tsinci kanshi cikin nishadi.

 

Fatima ko dake gefe tuni ta cika tayi himdan ta gano da wacce yake maganar.

 

juyowa yayi yana kallonta,uwar hararar datake wurga masa ce tasa ya rungumota gaba daya jikinshi,yana dariya,yakai hannunshi kan marar ta yana fadin.

 

“wannan dan baban ya maidamin mummynsa mafadaciya,irin wannan kallo in na jefamu a kasan gada fa?”

 

kokarin kwacewa takeyi,shiko yaki sakinta,tana bude baki zatayi kuka ya jefa bakinshi cikin nata,ayko ji kuke luf tayi shuru

 

 

Seda ya tabbatar da ko ya saketa bazata sake yin maganaba sannan ya kyaleta,ayko kwantar da kanta tayi jikin sit,shi kuma yaja suka tafi,dama gidado karami yana baccinshi abayan motar.

 

 

muje zuwa

 

 

Surbajo for life.

 

 

GID’AD’O BA SHEGE

BANE

 

 

 

Zahra Muhammad Mahmud

 

 

Dedicated to Amina Maman Gidado

 

 

65-66

 

 

Haka sukaje gurin siyayyar fatima batace masa komaiba har suka dawo gida.

 

Husna cikin murna ta tarbesu aka fara bude kayayyakin,se godiya takeyi dan fatima ta zabo mata masu kyau sosai.

 

Gidado dakinshi ya wuce,ya watsa ruwa sannan ya fito bayan ya shirya ya nemi guri yana tunani.

 

Ya rasa ta ina ze fara tunanin,dan tabbas yanaso yayi tunanin game da abunda yasa amina ta yar masa da da alhalin tasan danshi ba shege bane.

 

Yana tsaka da tunanin fatima ta shigo dakin,kallo daya yay mata yasan acike take tab,dan haka kirkiro murmushi yayi kanta karaso.

 

Koda ta karaso guri tasamu nesa dashi ta zauna.

 

“uwar biyu na ya akayi ne naga an tamke fuskar ko murmushin dake sanyayamin zuciyar yau babu?”

 

Wata uwar harara ta wurga masa,sannan ta fara magana,kai da ganin yadda take maganar kasan da gaske takeyi.

 

“Anyi na farko anyi na biyu duka na kauda kai,to karka kuskura kayi ganganci na biyu,dan wlh in wancan na bari wannan zan iya yin komai,ina nufin komai”ta maimaita masa,tana kaiwa nan,ta mike zata bar dakin,da sauri ya kamota.

 

Duk yadda yaso ta zauna amman taki zama,be takurata seta zaunanba sabida cikin dake jikinta wanda yake matukar so.

 

“Princess tun dazu kin daga hankalina,kin sauya gaba daya don Allah kimin bayanin damuwarki dan in kiyaye pls”

 

“Aminace silar gurbacewar komai nawa,karatuna mutuncina a idon duniya,gata na,uwa uba mahaifiyata,gamida yencina da asalina,duka wainnan abubuwan tayi nasarar rabani dasu a rana daya,to wlh bata is yanzu kuma ta dandani mijina ba,matukar kabari son Amina ya rabi zuciyarka,wlh nida kai har abada,”tayi mgnr cikin bacin rai.

 

Shuru Gidado yayi yana binta da ido dan zancan nata sosai ya firgitashi,

 

Ganin ya kasa mgn ne yasa takwace daga rukon da yay mata ta fice daga dakin.

 

 

Shiko guri yasamu ya zauna,yana tunani, dan shi lamarin gaba daya ya kulle masa kai,in banda abun Fatima ita bataji yace ze auri amina ba meye na daukar zafi har haka?.

 

Ranar fatima ce da girki,dan haka girke girken data saba yi ranar bata yiba,sabida ko kadan bata cikin walwala,dan gani take gidado ze auri amina ne,shiyasa tayi taliya kawai tayi shigrwarta daki.

 

koda gidado yafito cin abincin sosai abun ya bashi dariya,dan rabon da ta dafa taliya,har ya manta,yau ko tunda ana fushi mara dalili ta dafa.

 

Haka suka ci abincin shida husna da gidado ba tare da tazo ba,suna gamawa dakinshi ya koma yayi wanka yasa kayan baccinshi ya nufi dakinta,dan yasan yau yan mulkin bazasu barta tazo ba.

 

A gaban mirror yasameta tana shafa mai ajikinta,tunda ta dago kai ta kalleshi ta murror bata sake kallonshiba taci gaba da harkokinta,

 

Karasawa yayi inda take,daukarta yayi cak,ya nufi kan gado da ita,se zillewa takeyi,amman yaki ajiyeta seda yakaita kan gadon.

 

Yana ajiteta kuka tasa mishi,me tsuma zuciya,shuru yayi yana sauraronta,kasa jurewa yayi ya lalubi bakinta ya hada da nashi,ya shiga kissing dinta.

 

Seda yaga ta natsu sannan ya fara mgn.

 

“princess wlh matukar ina tare dake,na haramtawa kaina Amina,bazan auri amina ba princess,dade nayi alkawarin duk sanda naganta zan aureta,amman kasancewarki atare dani princess yasa na kwance wannan alkawari,pls kidena hukuntani da laifin daban aykata ba,ni nakine ke kadai har abada”

 

wani sassanyan sanyine ya ratsa zuciyar Fatima batasan sanda ta rungumeahi ba itama tana dariya

 

nanko ya shiga tsokanarta da “iya me taliyar kishi”dariya sunyita kamar cikin su zeyi ciwo.

 

Acikin satin duk abinda ya kamata gidado ya tanadeshi gameda tahowarsu Nigeria shida iyalinshi.

 

Tunda sukai waya da amina so dayannan basu karayiba dan duk abunda ze bata ran fatima gudunshi yakeyi,shiyasa ko ta kurashi be dauka.

 

Yau jirginsu ya daga,daga uk zuwa nigeria,domin warware zare da abawa.

 

muje zuwa

 

 

Surbajo for life.

 

GID’AD’O BA SHEGE

BANE

 

 

 

 

Zahra Muhammad Mahmud

 

 

A kullum a koina ina tare daku masoyana,Allah yabar mu tare cikin aminci,surbajon ku ce har abada

 

 

Dedicated to Amina Maman Gidado

 

 

67-68

 

 

 

Tarba ta musamman suka samu daga iyayen gidado,

 

Bama kamar fatima,da koya ta motsa daga mummy har daddy tambayarta suke,sabida cikin dake jikinta,ita abun har kunya ma yadunga bata.

 

Shima fadil baa barshi abaya ba,sosai yadunga tsokanar fatima da maman biyu,itade sede tayi murmushi,

 

Suna zazzaune bayan yan ayki sungama jere kayan abunci,kowa ya zauna zasu ci abincin,se fadil ya dubi husna kamar yadda ya saba da yace cikin daka tsawa.

 

“ke husna jeki kitchen ki daukomin wani cup din”

 

 

Wani kallon uku saura kwata ta watsa mushi gamida makalewa jikin gidado cikin sigar sin girma tace.

 

“da kenan dan kaninmu,amman yanzu ay sede na aykeka wlh”

 

Gaba daya gurin suka sawa fadil dariya,shima dariyar yake,dan se yanzu ya tuno katobarar da yayi,amman duk da haka seda ya mika hannu,yakai mata duka.

 

Gidado da sauri ya janyeta jikinshi yace.

 

“ikon Allah zamani ya kawomu da fadil yacire hannu ya dokeni”

 

Da sauri fadil yace.

 

“haba bross taya zan dokeka,?”

 

“tunda ka daki matata ay ka dakeni”

 

Gaba daya gurin sake kaurewa yayi da dariya,husna ko se tsokanar fadil din takeyi,zuwacan de ta tashi taje ta dauko masa cup din.

 

Bayan sun gama cin abincine gidado yayiwa iyayensa bayanin abinda ke tafe dasu,sosai sukai farinciki da bayyanar aminan,saura suji dalilinta na yar musu da jika bayan tasan ba shege bane.

 

Anata bangaren Amina kuwa,gaba daya tayi baki ta rame,burinta tasa gidaɗo da fatima a idonta,da danta dan ta nemi gafarar su,

 

Mijinta ibrahim ko,koda yazo gidansu mamanta bata boye mishi komaiba,gameda yadda lamarin ya faru,ayko dan tsabar kishi da takaici a sume aka kwasheshi zuwa asibiti.

 

Ba komai ya haddasa masa hakanba,sedan munafuntarshi da aminan tayi ya aureta as budurwa ba bazawaraba.

 

Koda aka sallamoshi daga asibiti,kai tsaye ya rubuta mata takardar saki ya tura gidansu,Lamarin ya firgitata amman daman tasan dole hakan zata kasance dama dan zalin fatima data ci tayi imani bata ma fara ganin sakayya ba.

 

Duniyar gaba daya ta hadu taimata baki,ko abinci bata jin dadinshi a bakinta,cinshi take kamar magani.

 

 

Yau gidado ya shirya sanar da amina dawowarshi nigeria,dan haka text ya tura mata gamida address ,inda ya shaida mata yana bukatar ganinta,a lokacin.

 

Sanda sakon ya isa gareta yi tayi kamar mahaukaciya  dan farinciki da gudu ta shaidawa mamanta,suna tsaka da shiryawa su tafine mahaifinta ya dawo daga tafiyar da yayi wacce basu tsammaci dawowarshi a lokacinba.

 

Daga Amina har ummanta sun firgita da ganinshi,se kame kame sukeyi,dan shi beda masaniya akan.komai.

 

Dakyar mahaifiyarta,ta tarbeshi,a tsatstsaye,dayaga de a firgice suke dukansu ne yasa ya mike,yace.

 

“Tunda naga alamun unguwa zaku muje na rage muku hanya”

 

Arude suka hada baki gurin fadin.

 

“aa kabarshi mungode yanzu zamuje mu dawo”

 

murmushi yay musu gamida gyada kai,alamun ya amince,ayko da gudunsu suka fice daga gidan,sede suna fita,shima yabisu abaya,batare da sun saniba,

 

Yayi mamaki matuka dayaga sun tsaya a kofar gidan amininsa,

 

Suko suna zuwa da yake ansan da zuwansu aka bude musu get,da hanzari,baban amina ya matsa sosai kusa da tasu motar,dan haka masu gadi sunyi zaton tafiyarsu daya,so atare sukashiga gidan dashi.

 

Sanda suka fito sukai arba dashi,gaba daya sun firgita,kan suyi wani yunkuri,su gidado sun karaso gurin domun tarbarsu.

 

 

Jikinsu rawa yake sosai dan sun tsorata matuka,shiko mahaifin gidado da sauri yazo gurin mahaifin Amina yana me murnar ganinshi.

 

Kam baban Amina yayi matukar kullewa,haka de yabi bayansu zuwa gurin da aka tanada domin ayi maganar.

 

Sanda fatima tayi arba da Amina,ji tayi komai daya faru abaya ya dawo sabo,dan haka kukane ya kubce mata,da sauri gidado ya isa gareta,ya rungumeta yana rarrashinta.

 

Bayan kowa ya natsa ne,mahaufin gidado yafara bayani.

 

“ba komai ya taramu anan ba se dan sin sanin meye dalilin dayasa Amina ta yarda jaririn da tasan ba shege bane,da badan yaron ya fada hannu na gari ba da yanxu watakila ma bashi raye”

 

 

 

Da sauri mahaifin Amina ya katse shi da cewa.

 

“nifa yata Amina bata taba haihuwaba,to taya kuma zakayi zancan ta haihu harda da?”

 

 

Batun nashi yaba dangin gidado mamaki,dan haka cikin kwantar dakai gidado yay masa bayanin duk abinda ya faru.

 

A gigice yake kallon Amina da mahaifiyarta,baki na rawa cikin bacin rai yace.

 

“ni kuka munafunta,ƴar tawa ta haihu har ta yarda dan ni banida labari garin ya hakan ta faru,”yayi maganar kamar ze kaiwa maman aminan duka,wacce tun dazu se kuka take.

 

Cikin kuka ta fara mgn.

 

“Sanda Amina ta dawo daga tafiyar da tayi,har abun ya faru,sosai naga canji gameda ita,koda na tambayeta nunamin tayi ba komai,kawai inda taje dinne be karbeta ba,haka na zuba mata ido,har ta tafi makaranta,da kusan kowanne weekend daga keffi seta dawo gida tayi shi but tunda ta dawo senaga batamason zuwa gidan koda kuwa hutu akayi,sede taje gidan kanwata,bayan watanni uku se kanwata take shaidamin Amina fa cikine da ita,ban yarda ba seda mukaje asibiti da ita likita ya tabbatar da hakan,ranar jinayi kamar na mutu,koda muka titseta,da tambayar wanda yay mata,se tace itama batasanshiba,amman cikin ba shege bane,zancan nata ya batamin rai,dan har rufeta nayi da duka,to a lokacin mahaifinta bayanan,dan haka yana dawowa daga tafiya,naje na sameshi,akan maganar,inda nace masa”

 

“Alhaji lamarin Amina yanzu dekam sede addua,dan gata nan cikine da ita”

 

“Sanda na shaida masa seda ya kifeni da mari har seda na fadi,sannan yacemin, ”

 

“wlh bade agidanaba,cikin shege,dan haka wannan tatsuniyar taki ki nemi gurin yinta danni ba saan wasanki bane,ke bari kiji,wlh matukae ya tabbata cikin gareta,wlh sena sakeki,ita kuma sena tsine mata albarka,dan bazaku janyomin zagi agari ba”

 

“Jin kalaman dake fita abakinsa ne ya dagamin hankali,dan haka kasancewar muna cikin watan april sena cemasa”

 

“Dama april full nake maka fa,haba yazaayi amina tayi ciki?wasa nake maka”

 

“jin nace hakane yasa yasaki ransa,yana faraa ya bani hakuri gameda marin da yamin,tundaga lokacin yasaki jiki akan aprilfull nayi masa,ban boyewa amina yadda mukayi dashiba wanda hakan sosai ya daga mata hankali”

 

“Hakanne yasa na dauketa zuwa asibiti domin acire cikin,inda likitan yamana dabara da cewa yanzu baa cire ciki sede a kwantar dashi,haka yay mana yan dabaru azuwan ya kwantar da cikin muka dawo gida,to nima sena kwantar da hankalina funds an kwantar da cikin,iya abinda nasani kenan gameda faruwar cikin amman bansan sanda amina ta haihu harta yarda danba”ta karada maganar cikin matsanancin kuka.

 

Dubansu suka mayar zuwaga Aminan domin ta dora musu daha inda ummanta ta tsaya,sede kukan da takeyi ya hanata magana.

 

 

muje zuwa.

 

 

Surbajo for life.

 

GIDADO BA SHEGE

BANE

Zahra Muhammad Mahmud

 

 

wannan shafin nakune writers masoyana,wainda kuka sadaukarmin da books dinku,badan nafiku komaiba sedan nuna kaunarku gareni,You guys are making my day great with full of happiness,banida bakin gode muku sede inmuku fatan alkhairi,nagode nagode nagode,ina tare daku har abada,#one love,together for ever even in Paradise

 

 

Dedecated to Amina Maman Gidado

 

 

69-70

 

 

 

Da kyar aka samu tai shuru tafara yimusu bayani.

 

“Tun bayan da mukaje likita yace ya kwantar da cikin,hankalina be kwanta ba,sabida duk alamun da nakeji da ina ci gaba da jinsu,haka de na koma makaranta,”

 

“Hankalina ya fara tashine sanda na fara jin motsi acikina,gashi kuma cikin se girma yake karawa,hakan yasa na tsiri saka katon hijabi,gudun kar aga cikin,kasancewata doguwane yaba cikin damar bin jikina,batare da ya bayyana ba,wani asibiti naje a boye suka gwadani suka kuma tabbatarmin da cewa cikina ya shiga wata na shida,Ranar ko bacci na kasa yi,ba abinda ke daga hankalina se furucin mahaifina,dayace ze tsinemin kuma ya saki ummana,shine dalilin dayasa nadena zuwa gida hutu ko anyi,nazama malamar karfi da yaji gurin yawo da hijab .”

 

“ina cikin wannan damuwarne nafara karantar halayen kawayena,wainda muke tare dasu wato fatima da hauwau,tunani na ya tsaya kan fatima ne dimin na yarda da tarbiyarta,kuma ina ganin gidansu babu tsanani kamar gidan su hauwau,tundaga lokacin nafara shirya yadda zanyi na rabu da abinda zan haifa ya koma hannun fatima batare da saninta ba,A haka cikin ya isa haihuwa,koda wasa ba wanda yataba tunanin ciki gareni,sabida boyeshin da nakeyi,kwatsam cikin wani dare nakuda ta kamani,da misalin karfe bakwai na dare,lokacin su fatima na masallaci,ni kuma nai musu karyar bana sallah,dayake mu uku ne a dakin,kuma dama in muka tafi masallaci bama dawowa hostel da wuri,muna zamane a compound mudanyi hira,ko muyi nazarin takardun mu,yo bare lokacin exam akeyi,ina kallo su fatima suka debi books dinsu wanda hakan yasa nasan ba yanzu zasu dawoba,suna fita,na kulle kofar naci gaba da murkususu,zuwacan naji fitsari,ayko da gudu na shige toilet,ina dukawa naji wani abu ya fashe,nasha wuya sosai cikin hukuncin Allah na haihu lafiya,yaron se kuka yake da yake na kulle window ba wanda yajiyo,na jima akwance sannan nadan smu kwarin jiki na mike zaune,dayake muna ajiye raza sababbi a toilet dya daga ciki na dauka na yanke masa cibiya bayan na daure da gefen dankwalina,goge mishi jiki nayi,se kuka yake nima inayi,dan ina sonshi amman bazanso auran uwata yamutu sabida shiba gefe na maida shi,na dunga kwarawa gurin ruwa har jinin yawuce zuwa sokawe,bame cewa anyi haihuwa agurin,haka na daure,nayi wanka,da ruwan zafin dana jona tun farkon jin nakudar,shima yaron na masa,snnan na nadeshi  a znin da bawanda yasanni dashi,muka fito daga toilet din,shiryawa nayi,duk da inajin jiri haka na daure nasauya kaya,wanda na haihu dasu kuwa,mahaifar na nade aciki,na dauki yaron cikin hijab na fito daga dakin,wani kwalin indomie na gani na dauka,nabi hanyar toilet din da nasan fatima tafi zuwa,na saka yaron ciki wanda a lokacin baccinshi yake,ni kuma nayi sauri naje na binne kayan da mahaifar abayan hostel dinmu,duk wand ze wuce bazeyi zaton dane acikin kwalinba,sede ayi zaton kwaline kawai,ina gama birnewa nayi sauri na nufi,gurin da na ajiye yaron,ina gadi gudun kar wani ya dauka,ina nan na hango su fatimasun taho,ita da hauwau,ga hadari ya hadu sosi wanda nasan shi ya korosu a lokacin,da suri na shige dakinmu na kwanta nayi kamar ina bacci,ina jinsu suka shigo,hauwau ce ta shiga toilet din ba jimawa ta fito tana mita cikin raha take fadin.”

 

“Dadina da in amina na period karnine zeyi kamar ze kashemu in muka shiga toilet,”

 

Dariya sukayi su duka,ni kuma se na farka,adan tsorace,nace musu.

 

“Se yanzu kukadawo?”

 

amsawa sukayi da eh

 

sake cewa nayi sanda naji ruwa ya fara sauka.

 

“Fatima kije kiyi,kashinki na sabo tun yanzu dan wlh bazan rakaki ba in dare yayi”dayake toilet din dakinmu na wanka ne kawai.

 

Ayko tana dariya ta ajiye hijab dinta ta fice daga dakin,fitarta yayi daidai da saukar ruwan kamar da bakin kwarya,runtse ido nayi ina addua akan Allah ya nunawa fatima yaron nan,

 

Ayko tafita ba jimawa segata ta dawo rude,dauke da kwalin danasa yaron aciki se kuka yake sabida ruwan ya fara jikshi.

 

D suri na mike,na mats ina tambyarta in tasmo da,tkasa mgn sabida a rude take,da sauri na amshi kwalin,na ciroshi aciki,na cire masa zanin jikinshi,n janyo brgona n rufa masa na dorashi akan kirjina ina rarrashinshi sisi tausayin dana ya kamani.

 

Hauwau itama zuwa tayi tana tayani rarrashin yaron,fatima guri tasmu ta zauna tana binmu da kallo.

 

Hauwau ce ta takura mata da tambaya sannan ta sanar da mu inda tasamo yaron.

 

Shuru mukayi alamun bamu yarda ba,haka na rike yaron agurina zuwan tausayinshi nakeji,ko gurin bacci ma ban ba fatima shiba,sashi nayi cikin bargona,bayan naci abinci,na koshi,gefenshi naje na kwanta,na rufemu da bargo kwanciyata ba jimwa yafararigim wacce nasan nono yake nema,ayko da yake bargon arufe yake ajikinmu haka na ciro nono na bashi,carab ya kama yadunga sha inajin zafi amman haka na daure,

 

 

haka na kwana ina shayar da yarona,cikin so da kauna batare da kowa ya saniba,da gari ya waye ne fatima ta amsheshi taimsa wanka sannan ta nufi hukumr makaranta dashi akan cewa tsinta tayi,koda aka nememu shine nafi kowa kafa hujja akan cewa dan fatima,ba komai yasa nayi hakaba,sedan iyayena sunki yarda akan crwa ta hanyar aure na sameshi,sannan ina gudun tsinuwar mahaifina kuma banso yasaki mahaifiyata,nazabi fatima ne domin nagartarta,amman don Allah ki gafartamin,ta karasa maganar tana kuka me tsuma zuciya.

 

Fatima ma kukan takeyi domin duk abinda amina ta fada duka anyi,

 

kowa afalon jikinshi yayi sanyi ba wanda be tausaya mata ba,laifinta daya yarda yaron da tayi.

 

Amina gaban fatima taje ta duka tana kuka kamar zata mutu akan ta gafarta mata,cikin kuka fatima ta rungumeta tana shaida mata ta yafe mata,komai ya faru da ita daga Allah ne.

 

Hakade kowa yadunga nrman yafiyar kowa,gidado karami fafur yaki zuwa gurin amina,hakan ko seda yasata kuka sosai,seda fatima tajashi ta kaishi sannan yaje,ayko rungumeshi tayi tana kuka,

 

 

Mahaifinta sosai ya koka dan shine ummul abaisin komai,da beyi furucinba da bazata yarda yaron ba.

 

 

Ranar wuni su amina sukayi ahidan se dare suka tafi,kowa na kewar kowa.

 

Waya amina tasa ta kira yaya umar wanda yagama cire rai da ganin yar uwarsa fatima duk yayi baki ya lalace sabida rashinta,yarasa inda ze je nremanta,kullum ikin kuka yake ko abinci baya iya ci,da yake yayi aure matarsa hafsat kullum cikin rarrasjinshi take.

 

kwatsam srga wayar AmiNa tana shaida mishi anga ɗfatia,A ranar ya dauki matarshi suka kama hanyar Abuja,da yake yayi mita,cikin dare sosai suka iso Abuja,dan gab da Asuba suka iso.

 

Amina tayi mamakin gaminsu,ayko gari na gama wayewa tamusu jagora zuwa gidan su fatima.

 

 

Sanda fatima taga umar sumane kawai batayiba,haka suka rungume juna suna kuka yana neman gafararta,

 

 

komai yazama normal,rayuwa natafiyawa fatima cikin jin dadi ga mijinta ga yayanta ga iyayen mijinta,ga danta gidado kowa na kaunarta,bata da damuwar komai seta fatan Allah yasauketa lfy kamar yadda suma burinsu kenan.

 

Bayan watanni biyar,fatima ce kwance akan gadon asibiti yayinda dangi gabadaya ke kanta kowa fuskarsa dauke da fara,a babu kamar gidado da umar,badan komaiba sedan haihuwar tagwayen da fatiman tayi duka maza masu kama da ubansu.

 

murnar da suke bata muialtuwa,ga husna itama dauke da nata tsojhon cikin,

 

Amina tayi aure da wani dan aminin babanta me suna muhammad,daidai gwargwado suna zaune lafiya cikin so da aminci.

 

Itama baa barta abayaba tazo duba fatima.

 

Ranr suna haka yaran suka amsa sunan baban fatima dana gidado,ana kiransu,Amir da khalifa.soyayyace mekyau da tsabta hgiddo ke nunawa matarsa fatima,ga yaransu masu shiga rai,yanzu hankalin fatima akwance sabida yanzu ta koma makaranta,ba abinda ta nema ta rasa.

 

 

Mijinta na sonta haka yan uwanshi,ga danuwanta dake ji da ita shima,

 

Alhamdulillahi rabbil alamin

 

Anan na kawo karshen wannan littafi,kuskuren dake ciki Allah ka yafemin,abinda na rubuta daidai kuma Allah kabani ladan,nagide nice taku har kullum zahra Surbajo.

 

kuzama cikin aminci,semun hadu cikin sabon bok dina me suna  Zahra Autar mama

 

 

 

Surbajo for life.

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment