Littafan Hausa Novels

Gajerar Mace

Written by Hausa_Novels

Gajerar Mace

 

 

 

 

 

 

NIMA MACECE 1

by Benaxir Omar

NIMA MACECE
Cikin takun kasaita ta isa bakin motan wanda guard dinta har yabude tashiga gydan baya. Yabi yarufe. Motan tabar harabar kafteren gidan grand square suka nufa yayinda tafito mazan biyu wanda suke matsayin guards dinta suke biye da ita ta isa bakin kofan inda guards din gurin suka bude mata kofa tashige jakanta na hannun guard dinta wanda yake biye da ita cikin bakaken coats . Sanye take da jan dogon riga mai duwatsu a jiki dinkin fitet ne yafitar da shape din jikinta kaman wanda aka yi dokinta kana ganin rigan kasan dollars yaci uwashi agun!. Da takalminta high heel lafiyayye baki saita daura bakin gyale shima akwai desighns ajiki. Sanye take da goass a fuskanta wanda ta manna shi yayi balain mata kyau. Doguwa ce mai kirar kalangu zaki iya cewa coca cola shape.kalan fatanta yafi kama da black americans very fresh .tana da dogon hanci wanda yafado daidai karamin bakinta wanda fararen hakwaranta suna jere cas aciki.manyan ball eyes dinta farare tas wanda bakin glass din bazai hanaka ganin su ba. Taku take cikin kasaita wanda zakayi tsammani ko tayi makarantan koyon tafiya.
Dayan guard dinta shine yadauko basket yana binta dashi tana diba tana jefawa . Har suka kammala takarbi jakanta tabiya kudin suka fito.
Guard din yace Ma. Ina zamuje!. Ta juyo da fiskan agogonta taja tsaki sannan tace muje gyda kawai.hakan kuwa akayi suna isa gyda batako kula da kayan ba tahaura sama. Kafteren gyda ne wanda tsayawa yin bayani zai bata mana lokaci. Mai karatu saika kisfaya dakanka.
Kafteren dakinta tashiga hayewa kan katon gadonta tayi wanda akalla mutane 12 zasu iya kwana akai ba takuri. Batare da ta cire takalminta ba ta kwanta tana nishi kaman wacce tayi noman sati ba hutawa. Wayanta ne yayi kara tamika hannu taciro ajaka takara a kunnenta hy momy . Mamantan tace kixo daki kisameni. Tace tom. Batare da bata lokaci ba tafice tafiya tayi mai tsawo kafin ta iso wani falo yahadu iya haduwa tabude tana shiga taga wasu a zaune yayinda momyntan agefe itama . Tanemi gu tazauna batare da ta cewa bakin uffanba. Momy gani. Maman nata ta kalleta sannan tace ina kikaje. Tace shopping. Ohkay. To ga wadannan zaki kaisu office din dad dinki yace akwai aikin dazakiyi. Tajuya don taga suwaye. Maza ne biyu akalla bazasu wuce 30-32 ba. Tamike sannan tace kubiyoni.

 

 

 

NIMA MACECE 2
[12:18 AM, 26-Feb-14]
by Benaxir Omar
mota suka shiga tasasu a mota itama tashiga nata akaja suka nufi FAWU resources orientation
Basant iby Fawu . Ya ce kwaya daya tilo agun attajirin mai kudi wanda akasanshi da sanaan sayar da petur da gwalagwalai. Alhaji Ibrahim fawu. Dakuma mahaifiyarta hajiya aisha wacce ake kira Adda. Kasancewarta ita kadai yasa iyayen suka dauki son duniya suka daura mata . Anma hakan bai hanasu bata tarbiya na gariba. Tayi makarantan ta a turkish abuja. Yayinda ta tafi uk. Takarasa makarantann ta. Kasancewar tafara makaranta dawuri hakan yasa tagama dawiri tana da shekara 23 tana rike da qualifications na degree dinta na petroleum engineering!. Wanda tayi hakanne don ta dawo tasa hannunta a business din mahaifinta
*** bude kofan tayi tare da sallama tana mai cewa dad. Zaune taganshi da files agabanshi yadago yana murmushi my dota ya akayi?. Ta ce dad kalao munmy ce tace kana nemana sannan akwai wasu tace mutaho tare. Dasauri yace yes inasuke?. Tamike tafita jim saigasu sunshigo tare. Bayan sun zauna dad dinta yake sanar da ita yayan bappanshi zasu zo sufara aiki dasu . Tace ohk badamuwa. Office dinta tashiga tazauna minti kadan tamike tafito tace kuban key din motan zanje nadawo yanxu suka bata tafita da niyyan shakatawa. Tuki take hankalinta akwance daga ganinta kasan irin matan dabasu da damuwa ne. Wani hanya tagani wanda daga gani baa wucewa ta kusa kai batare da damuwan ina zata shiga ba . Tayi nisa a hanyan a tsammaninta bawani gubane anma saitaga hanyan yaki karshe. Birki ta ja dataga wasu mutane azaune agun daga gani yan dabane ko yan kwaya. Tajuya zata tafi anma tayi latti domin suntaho dasauri sunyi banke banke akan titin dazata wuce suna masu nunamata bindiga. Dayan yace gaskiya munsamu saa ayau . Dotan fawi guda gaskiya zamuci kudi. Bindiga suka dura akanta inkikayi motsi zamu harba miki. Cikin rawan jiki da tsananin kidima tare da kuma razana ta gyada kai alamun taji dadi. Motansu suka sakata. Wani towel dayan ta tusa mata ahanci wanda tayi bacci bashiri

 

 

 

NIMA MACECE 3
[12:19 AM, 26-Feb-14]
by Benaxir Omar
bude idonta keda wuya taganta awani daki. Wanda tunda uwarta ta haifeta bata taba ganiba. Dakin bakomai sai kyankasaye da beraye a razane tafara ihu. Wanda yajanyo hankalinsu ogansu bakikirin kato basamude fuskanshi a tamke ya kalleta ke bsmuson rakin tsiya munkiraki nanne don cimma burin mu agun mahaifinki bawai mu ajiye kaman hotoba. Ta kalleshi ta zuba mar harara.kai matsiyacin inane?. Yazaayi ka kawoni dakin bera ka ajiyeni da darajana da komi. Wani dariya yasake wanda saidata firgita yace ba hutu kikaxoba kimxo bautane. Gashinta yacafko yajawota ihu takeyi ganin zata cika musu kunne yasa yadauko seletape manyannan yatoshe mata baki.
Fusganta yake dakarfi kaman wanda yake fusgan buhun shinkafa. Look anmata dont mess up wit me inbahaka ba zanmiki tsiya. Tayi tsit don ta razana sosai da bayin Allahn. Ta kumshe jikinta kaman mage wani daki ya cusata. Sannan yadanna kira tare dasawa a handsfree. Acan aka dauka tare da sallama. Muryan mahaifinta taji cikin tsananin kidima zatayi magana yanausheta wanda yasa tabuga kanta da bango.yace alhaji batare da dogon bayani zamubaka sharudda kuma dole kabi don ceto rayiwar yarka. Miliyan 600 mukeso. Cikin rashin damuwa alhaji yace you are not serious aina zakuga yar tawa?. Mutumin wanda gaba daya basant ta tsorata dashi ganinshi take kaman malaikan mutuwa yabata wayan sannan yafinciko gashinta ihu tayi tare dacewa daddyy wayyo daddy zasu kasheni. Alhaji ibrahim cikin tashin hankali yace basant?. Kina ina?. Meya sameki?. Batasamu daman amsa mishiba alokacin basamuden ya kara a kunnensa sannan yace zaka yi magana da ita idan kashirya biyan kudin. Alhaji yace badamuwa aina zankawo muku?

 

Alhaji Da Yar Aiki

 

NIMA MACECE 4
[12:21 AM, 26-Feb-14]
by Benaxir Omar
4.mutumin yayi murmushi gaskiya harka da irinku da dadi. Kasan voice of nigeria.?. Yace ae!. A cikin gurin sighn board zaka mike har cikin jejin zakaga canopy agun ka ajiye kudin agun. Sannan idan kasanar da hukuma tamkar kace mu kashe maka yarka ne. So akiyaye doka a zauna lafiya .Alhaji iby yace anyi angama . Basamude sunanda basant tasamasa a zuciyanta ya kalleta sannan yace babanki nasonki yarinya!. Ki zauna anan har kudinmu yashigo hannu. Kuka mai tsima rai takeyi . Gani take bazata fita agunba. Alhaji iby cikin kidima yafita bai nufi ko inaba sai banki yacire kudin sannan yanufi inda akamasa kwatance ya ajiye kudin sannan yakira. Inda basamude yadauka alhaji iby yasanar masa dacewa ya ajiye kudin. Yace to kaje zakaga yarka a gyda. Atake ya aika aka dauko kudin shida abokan aikinshi sunzauna sunga kudin cif yacika. Ga basanta agabansu tace tunda anbaku kudin kutaimaka don Allah kumayar dani gun mahaifina. Basamuden ya kalleta sannan yace yarinya dazamu mayar dake anma munyi tunani mai kyau bazamu mayar dakeba kicire ranki da gyda sannan yanxu kinzama medium tsakaninmu da dad dinki kudi zamuyi yadda yakamata. Cikin kidima tace kuyi hakuri don Allah duk abinda kukeso zanbaku kubarni natafi . Dariya suka rinkayi wanda itakuwa kuka takeyi. Dayan yace oga tunda fauxa takimu mezai hana mu kama wannan? Basamuden yakalli basant sannan yace anma fa kayi tunani sosai. Yace kafin nan kugyra wancan dakin zamuji dadin harkan dakyau. Suka mike suka fice. Yayinda ya matso kusa da basant. Hannunsa yadaura akanta yana shafata ahankali. Bugeshi tayi dakarfi yayi dariya sannan yace kigama gwallinki u r now my new wife. Wani irim firgita tayi wanda zuciyanta saidaya buga nashiga uku don Allah kayi hakuri. Yace inafa!!! **alhaji iby yajira baiga basant ba donhaka yakira yaji dalili. Tunda nabaku kudinku kusake min ya. Firgita alhajin yayi alokacin da basamuden yake sanar dashi burinsa narike basant har abada. Sannan yace kar kayi garajen tinanin nemanta tazama namu har abada. Zufa da gumi ne yaketo ma alhaji duk da sanyin ac daya ratsa dakin adda ne tashigo tare dacewa nifa yau lafiya tunda basant tabika office shiru nakeji numbanta kuma nakira bata dauka. Alhaji cikin kuka wiwi yasanar da adda suma tayi tashin hankali atake suka nufi asibiti yashiga sanar da yanuwa da abokan arxiki. Nanfa hankalin jamaa yatashi. Labari yabaxa garin nigeria cewa ansace ya kwaya daya tilo agun alhaji fawu.

 

 

 

NIMA MACECE 5
[12:22 AM, 26-Feb-14]
by Benaxir Omar
5. Kwanan adda uku tafarka bayan adduoi da aka yitayi.alhaji iby yasa jamion tsaro nanfa aka hau bincike dafarko sunyi tracing layin akaga bata aiki. Anma gata last usage dinta ajeji anje gun baaga komaiba. Wayan basanta kuma kasancewar lokacin dasuka dauketa badubi ta motarba anan akaje aka samu motan dawayan aciki.adda tarame duk damuwa ta isheta har sumbatu takeyi ataimaka adawo mata da yarta. Alhaji kuwa gaba daya ya susuce yayi sanyi yadawo abin taysayi. Abin tashin hankali basu karajin duriyan su basamudeba balle asan nayi. Bincike kam saiyi akeyi agarin abuja karshema alhaji fawu yasa kyautan miliyan uku ga duk wanda yasamo masa yarsa. Hakan yasa yaro da babba kowa bincike yake. Titunan abuja duk jamian tsarone. *bangaren basant kuwa tun suna bata abinci bataci harta faraci. Tarame tayi baki. Ada idan kasan basant fawu ayanxu bazaka ganeta ba. Suka canja mata daki. Kullum basamude yakanzo yatauseta ya lallabeta so yake yasamu kanta kozai samu abunda yakeso donshikam sonta yake kamar ranshi. Baisamu yanda yakesoba domin kuwa dayaxo take shiga bandaki tazauna harsai yafice wani lokacin haka take wuni. Kuka kuwa yazama abincinta da ruwan shanta. Tafita hayyacinta. *alhajo fawu wayansa na gefensa da jamian tsaro wanda dazaran anji kira kowa zai hankalta a tsammaninsu ko basamude zaibugo donhaka koda yaushe suna kusa da kayan aiki. Hakan baifaruba. Abinci zai iyacewa yamanta lokacin dayaci . Gaba daya duniyan tafita masa arai. Adda kuwa baa magana dangi duk kowa ya susuce dan duk wanda yazauna da basant duk hassada saiya yaba da hankalinta hatta makiyanta basu isa suce tamusu wani abuba. Akullum tana kokarin kare hakkin dan adam. Matsalanta dai shine bata cika maganaba.hakan yasa mutane suke kallonta mai girman kai. Hatta masu aikin gydan sun nutsu kowa rashi yadameshi. Yayinda guards din ta kuwa alhaji fawu yabada umarnin a dauresu aganinsa meye amfaninsu tunda aikinsu kenan. *wasa wasa sai da basant tayi wata daya shiru ba labarinta bana basamude adda kuwa har hawan jini saidaya kamata. Alhaji fawu yasami malamai saukan alqurani suke Allah bayyanar dagaskiya. Inma tamutu Allah yanuna musu gawanta. Intanada rai Allah yakareta. *basant kwance akasan dakin. Indai kasan basant bazakataba cewa itace akwance ba gaba daya kammani yacanja. Basamude ne yashigo sannan yace yaukam yanda nakejin kaina kozaki mutune sai na kwanta dake!. Kuka mai tsanani takeyi. Tare da rokonsa kamin abinda zakamin anma kabarni kaji tsoron Allah. Ko kallonta baiyiba yashiga tube kaya tashi tayi zata gudu bandaki dasauri yafincikota abunka da marar karfi tuni ta fizgo ya wurgata kan gadon karfen!. Ganin zata kawo masa gardama yakira yaransa sannan suka shigo dayre masa ita akayi akan gado yabiya bukatansa cikin kwanciyan hankali. Sannan yamike basant kuwa tayi nadama nadama xuwanta duniya kuka takeyi sosai tare dajan Allah ya isa Oh Allah i caused you wit the blood of my virginity. Yajuyo yace mekikace? Ta maimata baisan lokacin dayahau kantaba dukanta yake sosai. Yadainga tsalle akanta tun tana kuka har tayi shiru

 

 

 

NIMA MACECE 6
[12:33 AM, 26-Feb-14]
by Benaxir Omar
6. Azaba wanda tasha shiyasata suma cikin tsorata kuma yadagota atake yadebo ruwa yayaffa mata duk hankalinsa yatashi. Bata farfadoba sai daddare duk yayi jigum akanta . Ganin ta numfasa yasa yskaraso gunta dasauri cikin tsorata ta matsa yace kece kike da taurin kai anma kiyi hakuri kinji?. Batace komaiba. **basamude ne agaban babban bokanshi. Yace boka nagode sosai daka taimaka nasamu kudinnan. Yanxu taimako daya yarage inason yarinyan wallah don Allah ka ban aminda zai mantar da ita gyda da duk wani danginta. Boka yayi dariya cikin jin dadin ganin aikinsa yana kyau. Yace abu mai saukine. Kuma da wahala. Yanxu kaje ka debo mana jininta na hailanta. Dashi zamuyi maganin. Dakuma gashin kan mahaifiyarta da mahaifinta a razane basamude yakalleshi boka!. Ta ina zan iya wannan danyan aikin. Ai asiri na yatonu. Boka yace kadai san yadda zakayi inbahaka ba aikinka zai lalace. A sanyaye yafito gyda yanufa duk tunani yake yazai nemo gashin kan adda da alhaji. Yafi kwana uku yana tunani kafin yasamu dabara. *alhaji naxaune wanda har yanxu yaki fitar daran zaasamu basant . Kuka yake sosai .haka adda baa magana duk tayi sanyi bakaman da ba. Hidiman gydan duk tasakewa senior maid din gydan. Sarah. Sarah tana duba aikin da masu flower sukayi akayi knocking gate mai guard yabude tare da tambayar mutanen aina suke. Rufe gate din yayi bayan yasaurari mesukace. Batare da bata lokaciba sarah tace yabude sushigo taji damuwansu kasancewarta mai tausayi. Mace ne danamiji. Tace lafiya?. Sukace ae! Madam aiki mukeso. Tace munada masu aiki kuyi hkr kunji?. Suka juya suka tafi. *basamude nazaune suka sameshi suna gayamasa haushi yaji. Sai wani yaronsa yace kaima oga kasan maaikatansu classified suke dauka wanda sukayi makaranta suka karanta fannin aikinsu. Anan yace hakane to yazamuyi?. Yace inada wata smart brat barin nemota awaya!. Wayansa ya danna cikin mintuna kadan aka dauka yace kina ina?. Tace office yace kixo muna bukatanki. **zuwanta keda wuya suka fara magana yayinda yake fada mata bukatarsa tace bakomai anyi angama!

 

 

 

NIMA MACECE 7
[12:25 AM, 26-Feb-14]
by Benaxir Omar
Tace anma tukunna nawa zakaban yace 500k yayi!. Tace wacce yarinya ce wannan?. Tana kallon basant. Yace baruwanki. Ta kalleshi sannan ta ce no prob. Your work will be done. But money first. Yace 50% discount. Anan yabata kudin Yamike yashige da basant byana murmushi dariya yake sosai yanacewa smart ass!! yayinda bata dago ta kalleshiba. Xuwa yayi zai tabata ita kuma tamike cikin gurnani. Karka kuskura katabani!!!! Allah ya isa tsakanina dakai. Kakiyayi ran mutuwanka. Kunnenta ya fizgo ki saurareni kiji banson taurin kai don zan iya laantaki. Duk randa kika fars jininku na mata kisanar dani.sannan yau zancanjamiki gyda. Shiru tayi batace komaiba. Har yafice wani sabon kuka ne ya kifce mata.
*adda nazaune tayi tagumi wanda yabi jininta yayinda sarah tashigo madam you have a visitor adda har zatace a a. Saitace let her in!!. Matar tashigo sanye da coat daga ganinta kaga wayayyiya adda tamike tamika mata hannu suka gaysa sannan tace madam sunana ruky naxo ne gameda cikiyar yarki. Inada details akai. Anma sai naga kudin da akayi alkawari tukun adda cikin razana tace karki damu da kudin baiwar Allah don Allah kigayamin aina take. Aina basant take. Ba abunda baxanmiki ba kitaimaka. Tace easy madam!. Kira maigidanki tukun. A tsorace adda takira alh. Tana sanar mishi cikin kuka da iina. Cikin hanzari yakaraso gydan gaba daya duk hankalinsu yatashi rokonta suke tanuna musu. Tace kushiga muje. Suka shiga mota tanufi gydan basamude
*cikin karfi ya fizgeta kimin sauri karkibatamin lokaci a mota yatusata ta booth suka bar gydan. Adaidai lokacin kuma su ruky da adda da alh. Sun yanko kwanan kenan. Basu lura dasuba. Gidan tanufa dasu. Inda alh. Yakira yan sanda da sojoji aka kewaye gydan caf. Kowa yayi tsit. Yayinda wani soja acikin speaker yace who ever is in the house. You are all under arrest come out. Shiru akeji akarshe suka banke kofan shiru akeji. Sama da kasa baaga komaiba. Har dakin basant suka shiga anan adda taga takalminta da dankunnenta takara kidimewa wayyo Allahna yata anan take rayuwa?. Jamaa kutaimaka kufitarmin yata. Ruky ce tarikota haj. Am sorry kiyi hkr kuyi trustn dina zannemo muku ita . Dakyar aka janye adda suka fice gyda!

 

 

 

NIMA MACECE 8
[12:30 AM, 26-Feb-14]
by Benaxir Omar
Bincike mai tsanani agydan akayi anma basu samu wani hujja dazai kaisu ga samun kokuma bin su basamude ba **yayinda su adda da alh yanxu sungama amincewa da ruky karshema alh cewa yayi tadawo gydansa da zama saboda tsaro kar wani abu yasameta. Hakan yasa tazama yargyda. Adda na kwance a falo ruky tace haj. Yakamata agyra miki gashinki damuwa yahanaki luradashi. Saidatayi magana sau uku sannan adda taji. Hankalinta yayi nisa. Hakan yasa tace badamuwa zanje agyramin. Ruky tace ina gydannan tayaya zanbari kifita ?. Barin zo ingyra miki . Nan tagyra mata akai anan ta yanka gashin adda kadan tacusa acikin purse dinta. Sannan data lura wanda yakewa alh aski. Tadage dazama agunsa. Tamayar aliyu abokinta. Watarana alh yace yamasa aski bayan yagama yamike yafice. Tace aliyu plx kadan karbomun ruwa nasha fitansa keda wuya takwashe gashin ta tusa a jakanta. Bayan yadawo tace barinje nadawo. Bata nufi ko inaba sai gydan da basamude suka koma. Tana shiga dagudu yarungumeta itakuwa cewa tace mission accompolished!!!. Yace i trust u. Nanfa suka sha soyayyansu sannan tace saurame?. Yace jininta!!!. Tace dolene saina haila?. Yace ae wlh. Haka suka zauna yana lura da take taken basant don bata fashin sallah. Hakan yabashi daman lura da ita. Watarana yags batayi sallahba hakan yasa yashigo sannan yace ungo wannan zanin jeki samin jininki. Ko kallonsa batayiba. Damkota yayi ya kwalawa ruky kira kixo nan taxo itada sauran yaran basamude. Suka danneta zai kwaye mata kaya ruky tace a a kaikuwa. Tsaya mana unguo tsumman kacusa kanka kacire dakanka. Yakarba suka ciro jinin . Basant kuwa kukanma yaki fita na xuci takeyi. Jira take ta hadiye rai ta mutu. Ahaka suka fice suka nufi gun boka nan yayita mamaki yace lallai nayadda kanada kwanya. Haka yamusu aiki. Yace kaje mun mantar da ita komai ko tagansu bazata gane suba!! Sukayi godiya suka fice

 

 

 

NIMA MACECE 9
[12:27 AM, 26-Feb-14]
by Benaxir Omar
Dawowa gydan keda wuya dama yadan siyo kajinshi yashiga gun basant ganinta yayi tana zaune yashigo my baby ykk?. Ta dago tana murmushi don wani sonshi taji ya mamayeta. Bata nunanin kowa sai shi shine ubanta shine uwarta. Yace sauko muci kaza da hanzari tasauko yana bata abaki tanaci hartaci takoshi. Lokacin daya fice itama ta mike kan gado. Ruky ne tashigo kinfara sallahne?. Takalleta tace meye sallah?. Ruky tayi shiru lalle malam ya iya aiki mai kyau tafdijam. Wato har ibadanta yamantar da ita. Saita tuna yace yin sallahnta zai hana aikin yiwuwa shiyasa aka mantar da ita. .
Alhaji nazaune a falo shida adda wayansa tadau kara yadauka . Sai yace a a. Ahmadu yaushe zaka dawo?. Allah dawo dakai lafiya ka kammala kenan ko?. To saikaxo. Yace ahmadu (dan yayanshi marigayi wanda ke zaune agydanshi tun yana yaro yafita uk. Karatun degree da masters dinshi daganan suka rikeshi yasamu aikin yi.). Juyowa yayi yacewa adda. Kinsan me?. Ahmadu nadawo tayi murmushi cikin murna tare dacewa Allah yadawo dashi lafiya.

 

 

 

NIMA MACECE 10
[04:02 AM, 28-Feb-14]
by Benaxir Omar
í ½í´ŸYanxu basant tasaba suci abinci da basamude tare susha. Hatta wanka shiyake mata.(Allah zai saka mana injini Benaxir).ganin yanxu ta sake shiyasa yabarta take shiga ko ina a gydan ruky kuma tazama munafukar tsakiya tana gydan alhjai tana gidan basamude.
*dawowan ahmed tamkar niima ce agun su adda domin kuwa ya kwantar musu da hankali ya gwada musu cewa insha Allah yamusu alkawari zai binciko basant kasancewar fannin daya karanta kenan. Dafarko yaje yakarbo wayan basant. Dakuma takalminta da gyalenta wanda su adda suka samu. Yakuma ziyarci gydan atakaice ansanar dashi komai har xuwan ruky dasauransu. Yace akira mishi ita.
Yana rubutu a office tashigo dagowa ya kalleta sama da kasa. Itakuma gaba daya tagama tsarguwa inka cire sonshi data faraji atake. Tana da kyau kam anma baiga amfanin kyan ba. Don yana ganin itace no.1. Contender na criminal case din. A gameda dan binciken dayayi saidai kuma yatuna its a game of intelligent criminals. Donhaka gwara shima yaxo da dabara. Yakalleta yace karaso madam. Ganin kallon daya mata yasa tashigo da dan takunta tazauna tana wani yauki dashan kamahi. Ya kalleta yace ruky ko. Tace yes sir. Yayi murmushi wanda yakara bayyana mata kyansa yace you can call me Ahmed Fawu. Ta gyda kai . Yace so back to business plx ya akayi kika ganta dasauransu. Tace nima ganinsu nayi a mota sainabisu danaga inda suka shiga sai nakoma. Tana magannanne yana kallon cikin idonta. Shi yanada wani abu hakan yasashi karanta law. dakuma socialogy Inya kalli tsabar idonka kana karya zaigane.(mutane ne basu ganewa anma shikanshi karya na kunyan kwayan ido duk rashin kunyan mai yinta inzaka kalleshi cikin ido tsantsa zaka gane injini kenan). Yayi murmushi yace insha Allah basant takusa dawowa. Itama murmushin tayi gaskiya kam nima nagaji naga kawaliyyata(kuji shishigi).
Wasa wasa ahmed ya rinjaye ruky takamu dasonsa sosai sannan yana lura da duk takunta. Itakuma yanxu jitake zata iya tona asirin basamude akan ahmed. Nuna mata yakeyi yana sonta sosai. Wata rana suna zaune da ahmed din. Suna tadi saiga wayan rukyn ankira tadauka tana yamutsa fuska ill call u later. Ahmed agogonsa yakalla tym sannan yacigaba da abinda yake sunje park dare dare yakarbi wayanta barin yi game . Anan yace log dinta yaga numban dayakira exact time din daya duba agogonsa. Sannan ya haddace no. Atake . Yana gamawa yace tashi mutafi tace bamu gamaba. Yace nagqji bacci nakeji. Dole ta tashi suka fice

 

 

 

NIMA MACECE 11
[04:03 AM, 28-Feb-14]
by Benaxir Omar
 11.Gyda yanufa da ita suna tadi tace baranje nayi wanka. Yace ban wayanki nayi game tace kaidai kaman yaro. Yace temple run bayaro ba babba. Tashiga kenan adda tafito takalleshi ahmadu ana kan aiki ko. Yayi murmushin jin dadi yace sosaima ai yanxu nasamu hanyan dazai kaini har gun basant ina bi a hankali ne. Tace to Allah nuna mana Allah saka da alheri.yadauki wayan yayi txt wa numban dayake zargi. Where are you?. Cikin mintuna kadan aka turo Guest house. Inkina tahowa kisayawa basant pizza . Yamayar da o.k. tananan kalao ko?. Akadawo da sosaima aikinmu nakyau ai. Wani irin dadi ahmed yaji yagoge txt din yabar inkina tahowa ki sayowa basant pizza. Saboda tagani kartace tamanta suyi zargi. Bayan fitowarta sundanyi tadi yace zaishiga daga ciki. Bataso hakaba don a yanda take jinsa ba abunda bazata iya masaba. Sukayi sallama
**basant na zaune asiri duk yacita hatta ibada tamanta ya akeyi. . Tace tasha shine aikin. Suci soyayyansu da basamude.

 

 

 

NIMA MACECE 12
[04:04 AM, 28-Feb-14]
by Benaxir Omar
Ahmed ne zaune a kujera saiga ruky tafito da dan sauri gud mrn dear. Yace ina zaki haka?. Cikin sauri tace zankai aikane wani gu. Yace safe journey. Fitanta keda wuya yamike bayan fitarta da motanta yadauki motan abokinsa wanda batasan da motarba. Yabi sawunta pizza taje tasiyo duk yana biye da ita kafin tawuce. Da dabara yakebinta. Harta isa inda yake zargin anan basanta take. . Shiganta keda wuya yaja motansa yakoma.
*tunani yake sosai yanda zai bullowa lamarin yafada wa yansanda kokuma yaje shikadai?. Gaskiya gwara yaje shikadai. Saidayayi sati yana monitoring din ruky da basamude. Yalura da lokutan da basamude yakefita da dawowa. Yalura cewa su uku ne agydan anma sauran yarane. Saikuma ruky. Saikuma wata mace wacce bai ganetaba(basant kenan). Yasissiyo kayan aikinsa. Randa yashirya musu tabargaza ranan yatashi da sassafe bakin kaya yaci. Kaman yanda yalura duk wanda suke gydan suke sawa. Batarda kamanni yayi yasaje dasu. Dafarko yanufi bakin gate din maigadin yaleko . Ganin kayan jikinsa yasa yabude tareda masa barka. Yace suna ciki?. Maigadin yace a a . Haj. Ce kawai.Tabaya yanufa window biyu yagani yaleka daya baiga kowa ba yaleka dayan yaga wata azaune. Sanin ba mutane agydan yashiga kallonta yake sosai. Yace ina basant bata tsorataba kodai dontaga shiganshine. Tace ni ce. Meyene. Yace zomuje basamude ne ya aikon. Tatashi tasaka hijabinta yariko hannunta sukafito yakalli maigadin yace bari muje mudawo. Tusata yayi a mota ya figi motan dakarfi

 

 

 

NIMA MACECE 13
[04:05 AM, 28-Feb-14]
by Benaxir Omar
Bai nufi ko inaba sai gydansu da ita. Adda da alh suna falo. Tashigo dafarko adda bata ganetaba anma data shigo sai ta ganeta sosai. Kuka ne murna ne?. Bakinta na rawa tace basant?. Kece.? Alhaji ma a tsorace yamike. Itakam kallonsu take batare datasan mesuke nufiba. Tacewa ahmed suwaye wannan?. Yakalleta saida gabansa yafadi adda ne ta rungume ta tana kuka. Basant tace nifa banganekiba. Adda a firgice ta dago tare daja baya. Baki ganeniba?. Ni mahaifiyarki?. Haba basant . Kallonsu take kawai. Adda tafadi a firgice suka jata sai asibiti . Kiri kiri dai sukaga haikam basant bata ganesuba hakan yasa alhj. Nemo malami aduba. Yana kallonta yace asiri akayi. Kuma mai karfi. Suka kalleshi sukace kaman yaya kenan. Yace donda gashin kan mahaifinta dakuma na mahaifiyarta akahada. A tsorace alhaji yace tayaya? Ahmed yayi murmishi yace ta ruky. Alhj yace banganeba. Anan ahmed ya ware musu komai. Jikinsu yayi sanyi lalle kabar dan adam ayanda yake. Inbadon ahmed baya karyaba da alhj. Zai iya karya tashi. Adda tasamu sauki . Anma basant kam wani firgici tafara da gurnani. A falle tabankadesu tafara gudu(aikin asirin. Don boka yace ko tatafi wani gu dole tadawo garesu).

 

 

 

NIMA MACECE 14
[09:50 PM, 07-Mar-14]
by Benaxir Omar
Binta yayi dagudu tana fizga tana wani gurnani. Wanda duk mai imani inyaganta dole ya tausaya mata. Malam yace zamu karya asirin donhaka dole a tsareta haka adda naji tana gani aka daure basant. Sannan gashi malam yace kar abari su ruky susan tana gunsu kar suje sukara wani sabon shiri. Dakyar ahmed ya lallabi adda karta nunawa rukayya a fuska Haka kuwa akayi. Dayamma sai ga ruky tashigo tana kadadi kamar yadda tasaba. Adda duk kokarinta data danne anma saidata canja fuska. Ruky tace adda lafiya?. Tace kalao. Ina tunanin basant dinane. Rukyn tace kikara hakuri hajiya zaa sameta insha Allah. Kuma jikina yana bani tana raye cikin kwanciyan hanksli. Kallonta kawai adda takeyi tana mamakin irin makirci da fuska biyu irinna ruky. Ahmed ma dayaxo bai nuna mata komai ba. Yana kam shirye shiryen yadda zaakamosu ne. Dare dare malam yakira alh. Yace akwai kwai dasuka ajiye a kwalba a boye. Sai anfasa kwalban asiri zai tonu. Alh. Ya dada rikicewa to shi ainama zai samu kwalban. Wayansa yacire yadannawa ahmed kira . Cikin minti kadan saiga ahmed din yaxo. Xuwansa keda wuya yagaya masa abinda ake bukata. Ahmed yace abu mai sauki. Dama daren yau zamuje kamosu.
*dare dare sunshirya tsaf jamian tsoro aka nufi gydan basamude . Saida suka kewaye gydan tsaf sannan suka shiga anan akaga basamude kam ya damko wata yar mutane. Aka kwada mishi sanda a firgice yadago ganin mutane akansa ya matse tare dacewa lafiya? Kunshigomin gyda kaman wanda nayi sata. Ahmed yace mekayi inba satan ba?. Ya kalleshi zaiyi magana ahmed ya kwadeshi anan yasa aka daureshi. Suka bincika gydan sama da kasa dakyar suka samo kwalban da malam yamusu kwatance aka tattaresu akayi office dasu

 

 

 

NIMA MACECE 15
[09:50 PM, 07-Mar-14]
by Benaxir Omar
15.Bayan ahmed yamika kwalban wa malam nan aka fasa malam yayi adduoinsa dasauransu. Sannan yamiko wani kwarya yace addua nayi ajiki tasha. Sannan taje tayi wanka anan tayi tana gama wanka tafito ta yanki jiki tafadi. Asibiti aka nufa da ita.
*basamude kuwa. Ahmed ya gana masa azaba duka kan shine abincinsa daruwan shansa. Gashi ahmed namasa horon yunwa. Ga barazana da yake masa kala kala. Yadawo wani abun tausayi(nidai bantausaya masa ba). Kulleshi akayi a prison.ruky kam bayan dukan datasha dakanta takashe kanta.shikuma basamude Dakanshi yafara wani ciwo wanda aka rasa gane meye. Sai doyi yakeyi hatta prisoners yanuwansa gudunsa sukeyi. Ko sumasa dukan tsiya. Agarin haka yakarye kafansa daya.ba mai taimakonsa ko kyan ganu babu. Anan yarinka nadaman ayyukan dayayi. Lalle yayarda da basant tace ”i caused u wit the blood of my virginity” gashi yana gani. Ga Allah ya isan mutane akanshi shikam rayiwanshi 0-0
*bayan farfadowan basant tayi sanyi sosai gani takeyi yagama da rayuwanta hatta aikin batason xuwa. Ahmed ne yaringa kokarin kwantar mata da hankali.
*tana zaune a garden tunani takeyi batare datasan meke faruwa agefentaba. Ahmed ne yaxo yafara sallama shiru bata amsaba. Ganin bata hayyacinta yasa ya tabataa firgice tadago ta kalleshi. Tare da cewa yaya ahmed. Yazauna sannan yace basant meke damunki. Tace babu fa. Shiru yayi tare dacewa shirya muje wani gu. Anan taje tashiryo sanye da dogon riga tayi kyau sosai. Duk tamayar da kammaninta anma raman nanan haryanxu. Suna mota yana janta da hira. Har suka isa shopping yamata sosai itakam sai kallonshi take bayan sungama yakaita gydan abokinsa wanda yake da mata aisha.anan suka kulla kawance. To sanadin dayasa basant tafara sakewa kenan
*bayan shekara biyu. Basant tadawo asalin rayuwanta gawani so da kauna da iyayenta suke nuna mata na mussaman. Damuwan adda shine basant tayi aure. To batama ga alaman basant nadawani ba. Mutum dayane suke zargi hala suna soyayya wato ahmed. Wanda shima yanmata suke boolloko akanshi sai gwalesu yakeyi. Ganin haka yasa adda tabawa alh shawaran a daura auren. Basant batace ae ba batace a a ba. Fuskanta ba yabo ba fallasa. Ahaka iyayen suka shiga shirye shiryen bikin. Wata rana basant taje gydan aisha suna tadi sai take gayamata ga auren da ake shirin mata . Aisha taringa murna tare dacewa kema kishigo kiji . Basant tafara xubda hawaye kinmanta konashiga banda abunda zanyi alfahari dashi?. Nima macece anma ankaumin datawa darajan. Aisha tace ki kwantar da hankalinki Allah yasanya alheri aishi maigidan yasani shiba bare bane. Sannan ko kintashi auren zamukaiki gun benaxir ta kimtsa mana ke. Kimayar da ahmed bita zoizoi. Keda kawai kishirya munufi bauchi Nan tayita kwantar mata da hankali.
Haka kuwa akayi aka taho gun hajja benaxir. Ta kimtsa ta na sati uku. Inkaga basant dole ka hadiyi yawu
Wasa wasa yau gashi andaura auren basant ibrahim fawu da ahmed muhd fawu. Anyi biki na manya donkuwa kowa yashaida . A gydanta na asokoro aka ajiyeta gyda lafi yayye wanda yaji kayan duniya . Anan ta tare. Maigidanta bayan sallama dakowa yashigo don bawanda yakaishi murna.basant kuwa firgici tashigayi. Gani take kaman basamude ne. . Tagagara nutsuwa. Haka yahakura duk nacinshi.
Ahaka saida sukayi wata suna kan haka. Dole ahmed yaje gun malam yamishi bayani. Malam yabashi adduoi. Dayaxo yarinka mata dakyar tasamu tasake dashi . Nima danake labe rufe labilen sukayi. Dole na hakura . Bissalam
Muhadu ana gaba wato
**SANADIN KIYAYYE**
**kadan daga sanadin kiyaye**
Marinta tayi tana mai cewa ahir dinki da bimin miji. Banza mai bin maza. Fauxiyan kuwa tace ke kuma waya kasa dake balle kidauka?. Ni kinmin kadan saidai mijinki. Sannan ke takalmi ce abanza zan takaki nawuce. Hafsat ta cukomota tare da hada kanta da garu******$$$$$
Naku bigboy

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment