Littafan Hausa Novels

Ga Irinta nan Love Story Hausa Novel

Written by Hausa_Novels

Ga Irinta nan Love Story Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

GA IRINTA NAN

_(LOVE STORY

*NA*

_BINTU UMAR ABBALE🍒_

*MANAZARTA WRITES ASSO🖊️📚*

 

PAID BOOK

Ga masu bukatar Complt na littafin 07084653262

 

 

*DANDANO🥰*

*1*

Cikin tsananin gajiya da ishirwa nake tafiya. burina kawai na isa gida na samu na watsa ruwa a jikina na kwanta na hutawa rayuwata. gabana ne ya fad’i! lokacin dana tuna d’an iskan yaron nan yana gari nasan da wuya ya bar ni na sha ruwa a gidan Khalid mugun fitinan nan yaro ne wallahi……..Daf da zan shiga layin namu motar Alhaji Nura take kokarin fitowa. d’auke kaina nayi na bashi hanya domin ya wuce! girgiza kaina nayi ganin yayi parking din motar ya tsaya cikin raina nace”Ai dama na san sai ya tsaya, gilashi ya sauke muka had’a ido fuskata na saki na ce”Alhaji barka da rana.” Cikin kulawa yace.”Barka dai Sa’ida ya aiki.”? Nace” Aiki Alhamdullihi.” kokarin wuce wa nake ya dakatar dani da fad’in “Sa’ida ina al’kawarinmu.”? Gefan hijab d’ina nasa na goge gumin fuskata nace” Alhaji al’kawari yana nan ina so na ware ranakun da zan fara gudanar da aikin naka.”

Auren Zobe Hausa Novel Complete

Yace.”Me zai hana ki ware ranaku biyu a cikin sati wato alhamis da juma’a tunda a ranakun yaran basa zuwa isilamiyya in yaso idan sun dawo daga boko misalin biyu ko uku sai ki dinga shiga kina musu lesson d’in.”

 

Shuru nai ina nazarin maganarsa nace”Shikkenan Alhaji zan duba maganarka insha Allahu.” Yace.”To godiya nake gimbiya duk shawarar da kika yanke sai ki kira waya ta ki sanar dani.”

 

 

Nace”To shikkenan babu damuwa.” Har nayi yunkurin barin gurin ya dakatar dani! cikin k’osawa na tsaya amma ban nuna masa ba, kudi ya miko min kusan dubu biyar…..murmushi nai nace”Kasan ba zan kar’ba ba Alhaji na gode.” da sauri na bar gurin ina mamakin yawan kyautar da yake min duk had’uwar da zamuyi sai ya dauki kudi ya bani bayan uwar hidimar da yake mana a gida……..Tun kafin na karasa na hango shi dogare a bakin kofar gidan namu yana sanye da k’ananun kaya 3qutar da singlet wacce ta matse shi gabad’aya suffarsa ta mazantaka ta bayyana Gabana ya yanke ya fad’i! duk sanda zan ganshi a haka hankalina yakan tashi ni kaina ina mamakin halin da nake shiga wannan dalilin yasa idan yana gida bana sakewa sosai mutukar zai dinga shige da fice a gidan babu sutturar arziki a jikinsa.

 

Fuska a murtuke na ‘karaso….”Malami Bani hanya na wuce.” babu wasa nayi maganar.

 

Hanyar ya sake tarewa yana kallona da ‘batacciyar fuska yace.”Aunty Sa’ida me ya tsayar dake a gurin wancan mutumin.”? wani irin kallo na watsa masa nace”Ina ruwanka da shiga sabgar da bata shafeka ba, dan Allah ni bani guri na wuce na gaji.”

 

Hanya ya matsa min naja tsaki had’e da kokarin ra’bashi na wuce kawai naji ya matseni a jikin kofar fuskokinmu suka hade numfashin mu na had’uwa.

 

 

Cikin fad’uwar gaba na tureshi! nayi saurin fad’awa soron ina addua akan Allah yasa wani bai ganmu ba! hannuna ya rike yana marairaice fuska yace.”Kina so zuciyata ta buga ko na hanaki kula wancan Alhaji kin raina magana ta ko.” Cikin takaici nake kallonsa a fusace! nace”Wallahi Khalid ranka zai ‘baci! mutukar baka fita harkata ba shin wai ni sa’arka ce da zaka dinga yi min iskanci.”

 

Zuba min idonsa yayi fuskarsa a had’e yace.”Ni ina sonki Aunty Sa’ida kuma kin san Allah baki da miji sai ni da kika raina zaki gane baki da wayo.”

Yana gama maganarsa ya fita, na dinga kallon bakin kofar ina mamakin maganarsa, bani da miji sai shi! Lallai Khalid baida hankali da tunani. tsaki naja na shiga gidan raina duk babu dadi.

 

“Ummatu sannu da aiki.” ciki-ciki ta amsa min ban damu da yanda ta amsa maganata ba kawai na shige ciki gidan, Gwaggo kakarmu na samu tana kad’in lagwani! hijab na cire na nemi guri na kwanta ina mayar da numfashi.

 

Kallona tayi tana cigaba da kad’in ta tace” Yau kin dad’e baki dawo ba Sa’ida anya baki fara yawace yawace ba ni wallahi wannan aikin naki ban yardar dashi ba.”

 

 

Cikin mamaki na kalleta, tace”Ai da gaskiyata wane irin aiki ne wannan da za’a fita tun karfe takwas ba za’a dawo ba sai karfe uku ko biyu haba jama’a.”

 

 

Murya na rawa Nace”Gwaggo mai kike nufi dani.”? ba tare da wata damuwa ba tace”Abinda nake nufi ai kin san shi.”

 

 

“Kina nufin ina yawon karuwanci kenan.”? da sauri tace.” Ooh! ni kada ki daura min jakar tsaba ba haka nake nufi ba.” hawaye na zuba nace”To meye na cewa baki yarda da aikina ba wato kema kin fara daukar magana aikaina ko.”

 

 

Shuru tayi tana cigaba da kad’in ta, komawa nayi na kwanta hawaye wani nabin wani! nace”Wato saboda ‘kasa ta rufe fuskar mahaifina shiyasa kike nema ki d’ora min kazafin na zina kamar bake kika haifi ubana ba.”

 

 

“Kinga Sa’ida kada kisa hawan jinina ya tashi da wannan magana taki ta isheni haka aiki kije kiyi tayi tunda ba zakiyi aure ba sharrin zina da bin maza dole jama’ar gari suyi miki.”

 

 

Da sauri na mike Nace”Gwaggo na gaji zan tattara kayana na koma gurin mahaifiyata tunda keda kika haifi ubana kin kasa yi min uziri a rayuwa ta ni ba ni zan dauki kaina nakai gidan aure ba sai ranar da Allah ya nufa to tunda kun kasa fahimta zan bar muku gidanku.” Saukowa nayi na fara hada kayana,

 

 

Kayan kad’in ta ajiye a gefe tace”Ke Sa’ida bana son shashanci da rashin tunani babu inda zakije kinji na fada miki maganar aure kuma ba zan fasa yi miki ba har sai kin tsayar da miji zanja bakina nai shuru to kaji.”

 

Jakar kayana na dauka na kama hanyar fita, sai ta fashe da kuka da fad’in” Au! takani zakiyi ki wuce to bari Babanku Iro ya shigo zan fada masa rashin mutuncin da kike min.” Saboda nasan banyi abinda take zargina dashi ba yasa ko sauraranta banyi ba na fita daga dakin da kayana a hannu, haba jamaa na gaji da masifar Gwaggo.

 

Turus! nayi ganin Baba Iro a tsaye suna magana da matarsa! ya kalleni yana kokarin yayi magana! Gwaggo ta fito daga daki tana kuka da fyatar majina da sauri ya karaso gurin yana fadin”Gwaggo lafiya kukan me kike.”? Ta ‘kara rurucewa da kuka da fadin”Gatanan saboda nai mata maganar aure shine ta hada kayanta wai gurin uwarta zata koma shine har tana sa kafarta tana taka ni ta wuce.”

Da sauri na kalleta ina mamakin sharrin ta gwaggo tsohuwa mai sharrin tsiya.

 

Baba Iro murmushi yayi inda sabo ya saba raba fad’a tsakanin mahaifiyar tasa da ‘Yar d’an uwansa Yace.”Haba Sa’ida in da sabo ai yaci ace kin saba da halin Gwaggo me yasa ba zakiyi hakuri ba yanzu da kika had’a kayanki ina kike nufin zuwa.” Gwaggo da sauri tace” Zataje can gurin Uwarta ne.” Cikin k’unci nace” Baba Iro wai kamar gwaggo itace take min k’azafi to meye amfanin zamana da ita.”

 

“Aa ni kada kiyi min sharri Sa’ida daka fada miki gaskiya sai kice nayi miki sharri.” Baba Iro yace.”Gwaggo maganar ta ‘kare haka.” Tace.”To kace mata kada ta tafi dan taurin kaine da ita.”

 

Baba Iro yasa hannu yana kokarin kar’bar jakar hannuna, nace”Baba dan Allah ka kyaleni na tafi wallahi na gaji da rashin hakurin gwaggo ka gafarce ni idan maganata ta ‘bata maka rai.”

 

Yana ‘kokarin magana ya shigo gidan hannunsa ri’ke da leda indomee yaje ya siyo, babu walwala a fuskarsa yace.”Me yake faruwa ne naga duk kunyi cirko-cirko a tsaye.”

 

Da sauri gwaggo tace”Yawwa d’a nagari ka ganta nan wai barin gida zatayi saboda nai mata maganar aure.” wani irin kallo yayi min kafin ya kalli jakar kayana dake hannun mahaifinsa, cikin yanayin takunsa ya karaso inda muke jakar kayan ya kar’ba hannun mahaifin nasa ba tare da yace wani abu ba ya shige dakin Gwaggo da jakar gwaggo bayansa tabi tana surutai!

 

Baba Iro ya kalleni a nutse yace.”Sa’ida kiyi hakuri kinji ko gwaggo tun kafin ta tsufa take da rikici ki fahimci halinta sai ki zauna lafiya kada wani sa’bani ya sake shiga tsakaninki da ita kice zaki bar gida nan shine tushenki, sannan kuma inaso ki bawa Alhaji Nura dama ya turo da maganar aure kamar yanda ya nuna alama.

 

Nace”Kawu babu wata maganar aure data ta’ba shiga tsakanina da Alhaji Nura kawai muna gaisawar mutunci dashi ne.” Cike da mamaki yace.”Sa’ida babu maganar aure data ta’ba shiga tsakanin ki da Alhaji Nura amma yake mana hidima a gida.” murmushin takaici nayi nace.”Wallahi Kawu babu maganar aure a tsakanina dashi.” girgiza kansa ya shigayi yana mamakin maganar, yace.”Shikkenan to tunda kince haka dukkaninmu zamu cigaba dayi miki addua akan Allah ya baki miji nagari.” a cikin zuciyata na amsa da ameen. gurin ya bari nima a sanyaye na d’aga labulan dakin Gwaggo na shiga, abinda naji suna tattaunawa yasa gabana fad’uwa….

*GA IRINTA NAN!!!

_(LOVE STORY🌺)_

*NA*

_BINTU UMAR ABBALE🍒_

*MANAZARTA WRITES ASSO🖊️📚*

 

 

PAID BOOK

Ga masu bukatar Complt na Littafin. 07084653262

 

 

 

*2*

“Haba ‘Da nagari ai idan da gaske kake wallahi ni zan baka goyon baya kaga sai ayi towo na maina dama hausawa na cewa gida bai koshi ba ai ba za’a kai wa dawa ba insha Allahu Sa’ida matarka c…..Shigowa ta dakin ya hana ta k’arasa maganar. gabad’aya ita dashi suka bini da kallo, ni kam jiri ne naji yana nema ya zubar dani a gurin dan tsaf na fahimci akan abinda suke tattaunawa Khalid yayi masifar raina ni da har yake iya bud’ar baki ya furta min kalmar so ina a matsayin yayarsa wacce ta girme masa nesa ba kusa ba na rasa wane irin tsaurin ido ne da yaron a matsayina da tsayin shekaruna sai nake ganin bai cancanta ya iya kallon tsabar idona yazo min da wata banzar maganarsa ba, Khalid da wayo na da shekaruna yayi girman jikin da yake tunk’aho dashi kuruciyarsa kaf a gaban idona yayi ta amma yau wai an wayi gari ni yake tare wa hanya yana cewa yana so.

 

Kwanciya nayi ba tare dana cire hijabin jikina ba kawai na dinga bin su da kallo ina jin tsantsar takaici a cikin zuciyata ni kam ko zan rasa miji a gidan duniya ban ga abin aure a jikin wannan mara mutuncin yaron ba.

 

Tun sanda na kwanta a gadon yake min wani d’an iskan kallo irin na manufarci a hasale! nace”Wallahi idan baka daina yi min wannan d’an iskan kallon ba sai ranka ya ‘baci shashashan yaro mara kunyar banza da wofi.”

 

‘Bata fuskarsa yayi dan har sai da fatar saman goshinsa ta tattare haka yake tun yana yaro idan ransa ya ‘baci sai goshinsa ya tattare ya watsa min kallon banza had’e da girgiza kansa…….Yana kokarin yin magana ta riga shi da fadin” Ke Sa’ida meye kuma na kiransa shashasha ina laifin wanda zai tallafe ki ni wallahi naji dadin maganar da yazo min da ita duk girmanki da shekarunki ba zaki gagareshi ba dan mace komai girmanta bata fin karfin namiji.”

 

Tsaki! naja ba tare da nace komai ba na juya musu baya….’Kawataccen sajan fuskarsa ya shafa idonsa ‘kur! a mazaunanta da yake bala’in ‘kwa-‘kwa! duk da da hijabi a jikinta hakan bai hanashi ganin tudunsu ba, ya dinga jin wata lafiyayyar sha’awa na taso masa, a sanyaye ya kalli Kakar tasu yace.”Gwaggo ga indomee na nan ki dafa min zanje na dawo.” da sauri tace”To d’a nagari bari na kunna risho ai ina da kalanzir a ciki.” Fita yayi daga dakin yana shafa sumar kansa.

 

Sama-sama nake jin surutan ta kafin bacci mai nauyi yayi gaba dani……Can cikin baccin naji maganarsa sama-sama! “Haba gwaggo kefe ba’a abin arziki dake yanzu dan Allah haka ake dafa Indomee duba kin zabga mata ruwa sai iyo take a ciki kawai kinsa nai asarar kudina.” Zaune na mike nai saurin cire hijabin jikina jin yanda ya jike da gumi! ina kallonsa yasa hannu yana sosa kansa idonsa kur! a kirjina. girgiza kaina kawai nayi na fara yunk’urin mikewa……Tace.”Sa’ida duba dan Allah wai duk wannan gwanintar da nayi masa ban birgeshi ba cewa yake banyi daidai ba.”

 

Tukunyar indomee din na kalla da sauri na dauke kaina jin dariya na nema ta sub’ce min indomee guda uku amma ta cika tukunya da ruwa indomeen tayi tsululu duk ta narke a ciki………Yace.” gwaggo bafa zanyi asarar kudina ba ki cinye wannan indomee ki bani dari ukuna ba.” da sauri tace .” Wallahi baka isa ba ba zanci kayan atini ba hakan nan zaka daure kaci idan kuma ba hakaba Sa’ida ta baka wata indomee tunda tana da ita in yaso sai ka kaiwa babarka ta dafa maka tunda ni ban iya ba.”

 

Ta’be bakinsa yayi yace.”Sai dai na kwana da yunwa akan na kar’bi abunta ni ba shashashan namiji bane kamar yanda take kira na nafi karfin ta ciyar dani sai dai ni na ciyar da ita.”

 

Gwaggo sakin baki tai tana kallonsa sai kuma tayi dariya da Fadin”Khalid jarumi a gida da wajan ya’ki ka burgeni kwarai da gaske yanzu dai kayi hakuri akan ‘barnar da nayi maka.” Girgiza kansa yayi yace.”Bafa zan hakura ba bari ma ki gani.” da sauri ya fara lalaben inda take ajiye Pose d’inta….

Da sauri ta ri’ke gefan rigarsa “Aa Khalid kada ka daukar min kudi wallahi zanyi maka rashin mutunci idan ka daukar kwabo a cikin jakata…..Fita nai daga dakin na barsu suna bugawa dama inda sabo sun saba idan ‘yan abin arzikin na kusa suyi ta mutunci idan kuma ‘yan tsiyar na kusa suyi ta bugawa, Gwaggo san kudin tsiya ne da ita duk neman da take ba zata ci a cikinta ba sai tai ta tara kudin tana ‘boyewa a cewarta sai auran Sa’ida ya tashi sai tayi mata kayan daki da kudin……Pose din ya bude yaga kudi dan’kam ‘yan dubu dubu duk sunfi yawa, yace.” Lallai tsohuwar nan kudi ne dake duba dan Allah Jakarki kamar ta matar alhaji.”

 

Tana kokarin fizge jakar tace”Khalid wannan kudin da kagani ba nawa bane kada ka dauki ko kwabo a ciki.” Murmushi yayi yace.”Haba gwaggo ina ganin kudi ki hanani kin san Allah sai na dauka.” dubu daya ya zara yasa a aljihunsa ya mika mata jakarta, aikuwa ta dinga yi masa mita tana surutai dariya yayi ya kama hanyar fita daga dakin da fadin”Ki cinye indomee da kika dafa ni kuma anjima zanje tevur din mai shayi.” Tace.”Kaji dai dashi saboda kai zan sanjawa jakata guri haka kawai ba zaka zo kana daukar min kudi ba.”

 

Ni dai Ina alwala ina dariya a cikin raina gwaggo san kudi Khalid son kudi koda yake dole Khalid yaso kudi tunda dan makaranta ne yanzu haka yana daf da kammala karatunsa a jami’ar Bayero dake jahar kano yana zuwa gida duk bayan wata guda yayi hutu na kwana biyu ya koma makarana..

 

‘Dakin na shiga na sameta tana ta surutai uffan bance mata ba dan har yanxu haushinta nake ji akan irin abubuwan da take min, na gyara dadduma a nutse na fara kokarin tayar da sallah, tace”Sa’ida dan Allah ungo wannan jakar tawa ki ‘boye min Khalid ya gane inda nake ajiyeta nasan kuma shikkenan kafin ya tafi sai ya tatike ni.”

 

Ba tare dana kalleta ba nace”Ki ajiyeta nan na idar da sallah.” tace”To ‘yar albarka, tukunyar indomeen da sauke daga kan risho tana fad’in “Waye zai ci wannan ai ko almajiri ba zan bawa ba zubar dashi zanyi dan ni banga abinso a wannan abincin ba…..har na idar da sallah gwaggo bata fasa surutai ba nace” Yau me aka girka a gidan.”

 

Ta’be bakinta tayi ‘kasa-‘kasa tace”Kin san halin matar gidan da jarabar son d’anwake shi tayi masifaffiyar mata kawai na haifi d’ana amma tafi ni iko dashi dama nasan Rabi tana bin malamai akan Ibrahim.”

 

Cikin mamaki na kalleta halin gwaggo sai ita surukar ta ma bata kyale ba kullum cikin zaginta take amma ba tayi a gaban idonta sai a bayan idonta dan itama Ummatu bata daukar raini mara mutuncin kanta ce nace”Gwaggo dan Allah ki daina wannan halin ki zauna lafiya da kowa yanzu meye amfanin zagin Ummatu har kina cewa tana asiri.”

 

Baki ta rike tana kallon hanya tace.”Ke! Sa’ida maganar ta isa haka kada ki d’aga murya taji amma ni tuntuni Uwale ta tabbatar min da cewa Ummatu ba’a zaune take ba tana yawace-yawacan malamai wai shin bakya ganin ko kara ta ajiye babanku baya iya tsallakawa gashi muma ta daure mana baki dik abinda tayi a gidan shine daidai sannan kice nai mata sharri.”

 

Nace”Gwaggo ki rabu da Uwale munafuka ce wallahi tana so ta had’a ki rigima da surukar ki ita kuma ta zauna lafiya da tata idan ba hakaba meye na cewa Ummatu na bin malam……bakina ta rufe tana zazzare ido irin na rashin gaskiya tace.”Haba Sa’ida nace dake ki daina kiran sunanta kada taji haba jama’a yarinya ba’a sirri da ita mtssw maganar a barta haka.”

 

Murmushi kawai nayi na mike tsaye ina ninke dadduma, ta mika min pose din nata da fad’in “Kar’bi ki adana min kada ya shigo ya sake daukar min kudi.” karba nayi na bude gurin da nake ajiye tufafina nasa key na kulle……….Da yake idan mun dauki albashi duk abinda nake bukata naci da sha dana d’aurawa ina siyan abina na ajiye duk ranar da akayi abinda bana ra’ayi sai nayi girkina naci na koshi, fita nayi tsakar gida na dauko doya a kicin na zauna tsakar gidan ina feraye wa.

 

Fitowa tayi daga dakin da buta a hannunta Gwaggo duk rintsi bata bari yara suyi mata wasa da butar alwalarta kullum butar ta cike take da ruwa Macace mai tsafta da kula da ibadah dama dan adam tara yake bai cika goma ba, ganin ina feraye doya yasa ta washe baki da fad’in “A lallai kice yau dadi zamu ci a gidan.” Murmushi nai ina kallonta gwaggo akwai kwadayi amma bata yarda ta fitar da kudinta ta siyi abinda take so ba.

 

Nace”Eh lallai doya da kwai zan soya nayi miyar alayyahu saboda haka ke zaki bayar da kudin ‘kwai dan banda kudi.” shuru tayi tana kallona dariya ta kusa ta su’bce min.

 

Tace.” Inji dai guda biyu zai isa.” Nace”Haba gwaggo a wannan uwar doyar za’a sa ‘kwai biyu guda biyar zaki siya.” tace”Haba Sa’ida ‘kwai biyar nawa kenan.”? kai tsaye nace”Dari uku da hamsin.” shuru tayi tana nazari kafin ta girgiza kanta tace”Bari dai nai sallah muyi maganar haba Jama’a yanda rayuwa nan tayi wahala kice ‘kwai biyar ina laifi biyu ko uku.”

 

Bin ta nayi da kallo ina k’unshe dariya gwaggo kenan mai kwad’ayin tsiya…….Hayaniyarsu naji yo daga waje kafin nayi wani yun’kuri sun shigo gidan su uku, babu walwala na daga kaina ina kallonsu su biyu suna sanye da kayan ‘kwallo (ball) mayar da kaina kasa nayi na cigaba da abinda nake naji yace.”Salim ku jira ni nasa kayana na fito.” Suka ce okey kayi sauri dan Allah.” cikin zuciyata nace “Aikin kenan.” ” Aunty Sa’ida barka da Yamma.” a nutse nace” Barka Salim ya kuke.” ya d’an sosa kansa yana mirmushi yace “Lafiya aunty muna fatan kina lafiya.” ” Lafiya Kalau nake.” shuru gurin yay na minti biyu na dago kaina kawai sai naga sun zuba min ido! cikin ‘bacin rai nace”Salim kaima ka fara zama mara kunya ko.”? da sauri yace.”Aunty mai ya faru.”? girgiza kaina nayi nace”Kuje waje gashinan fitowa daga yau kada ku sake shigowa gidan nan tunda duk kun zama baligai.”

 

Wannan magana da tayi a kunnasa ya karaso gurin yana mata kallon daya saba “Akan me zaki hanasu shigowa gida abokaina ne na ‘kuruciya kin sansu kin san iyayensu kuma iyakacinsu nan bakin ‘kofa ko wani yayi miki abinda bai kamata ba.”

 

Nace”Khalid na hanasu shigowa gidan nan saboda bai kamata ba su tsaya a waje ka fito ka samesu.” Girgiza kansa yayi yace.” Keda Gwaggo babu nauyin auran kowa a kanku meye dan abokaina sun shigo kike fita kina yawo a titi gardawa na kallonki a ofis d’inku na malaman makaranta akwai baligan da suka ci uwar abokaina a kuyanci kike mu’amula dasu baki damu ba sai dan kawai abokaina sun shigo gida kice su daina shigowa ba zai yiwu ba.”

 

“Khalid ni kakewa rashin kunya.”? ba tare daya kulani ba yace.” Salim ku muje dan Allah.” gaba yayi suka rufa masa baya, girgiza kaina nayi aikuwa zan samu Baba Iro da maganar dole ya tsawatar musu akan su daina shigowa mutane gida kai tsaye………….

[18/11/2022, 10:01 am] +234 810 433 5144: *GA IRINTA NAN!!!🙆🏼‍♀️*

_(LOVE STORY🌺)_

*NA*

_BINTU UMAR ABBALE🍒_

*MANAZARTA WRITES ASSO🖊️📚*

 

 

PAID BOOK

Ga masu bukatar Complt na littafin. 07084653262

 

 

 

*3*

Motsin fitowarta daga band’aki yasa nai saurin kallon gurin, asuwakin ta dake kan taga (window) ta dauka tana gyarawa tace”Surutun me nake ji ne ina bandaki naji kamar muryar Khalid kuna sa’insa.” shuru nayi mata saboda nasan ko na fada mata dalili bai zama lallai ta bani gaskiya ba, zama tayi kan kujera ‘yar tsuguno tana kokarin sanya asuwakin a bakinta tace.”Sa’ida in dai akace wannan namiji ne to komai ‘kan’kantarsa jagora ne, idan kina hantarar Khalid wani sa’in haushi kike bani dan duk ‘kan’kantarsa da kika raina watarana shine zai jagorance ki.” Kallonta nayi ina mamakin maganarta “A’ina Khalid din zai jagorance ni gwaggo dan Allah idan zaki fad’i magana ki dinga tsayawa kina tunani kafin ki fad’a yaro ‘kan’kani kina maganar zai jagorance ni Khalid mai ya sani a rayuwa.”?

 

Tana goge bakinta da asuwakin tace”Oho! ni dai na fad’a miki gaskiya ki daina raina Khalid da ‘kan’kantar shekarunsa komai girmanki ba gagararsa zakiyi ba.” Cike da bacin rai nake kallonta, ta d’auraye asuwakin ta ajiye shi a gefe cikin nutsuwa ta fara d’aura alwala.

 

Kaina na girgiza ina jin tamkar zuciyata ta tsage saboda ‘bacin rai gwaggo ta iya kuntukawa mutum abin haushi tayi kamar ba tayi ba, tabbas da wata ko wani ne yayi min wannan banzar magana wallahi sai nayi masa rashin mutumci amma da yake itace babu yanda na iya da ita dole nayi hakuri dan idan nace zanyi magana zata iya yanko wata maganar da zata tarwatsa min zuciya amma idan ba haka ba me zanyi da Khalid bayan manyan mazan dake sona a waje.

 

Sai da na daidaici cewa ta idar da sallahr na shiga dakin, tana zaune kan dadduma cikin hijabi da carbi a hannunta tana ja, ka’ida ne dama idan ta idar da sallar la’asar sai tayi zaman lazimi nace” Zan dauki kudin ‘kwan a Pose d’inki.”

 

Kanta kawai ta d’aga min na bude sif din na dauko pose din nata na zuge! gudar dari biyar na dauka na mayar da sif din na rufe…… fita nayi domin na samu yaron aike cikin ikon Allah na hango almajirin gidan Alhaji Nura ni’ki-ni’ki da kayan miya a hannunsa, da sauri nace”Sule dan Allah siyo min ‘kwai kantin Dauda.” da sauri yace.”To aunty Sa’ida.” kudin ya kar’ba ya tafi na juya da sauri na koma cikin gidan, Ummatu na samu ta fito daga gurinta tana d’auraye kwanuka. sannu nayi mata ta amsa ciki-ciki. wucewa nayi ciki ina girgiza kaina na rasa abinda na tsarewa Matar kwata-kwata bata kaunata duk abinda takeyi min a gidan na ganin ido ne.

 

Har yanzu Lazimin take sai kawai na shiga kwashe kayan wanke-wanken dake dakin na kaisu bakin rijiya na ajiye,

 

Wani irin kallo naga tana bina dashi kafin ta shiga bin kayan wanke-wanken da kallo tace”Sa’ida dan wulakanta abinci shine kika fito da abinci kika zuba masa ruwa idan bakwaci ai sai ku bawa almajirai shima wanda yake kawowa yana shan wahala kafin ya samo ya kawo amma na lura daka ke har Gwaggon bakwa tausaya masa.”

 

Jikina a sanyaye nace”Wallahi na manta ban duba ba na zuba ruwa akai kin san ni bana cin d’anwake shiyasa to ban san abinda ya hana Gwaggo cin nata ba.”

 

 

Da sauri tace”To yaya kuwa za’ayi taci bayan taga kina feraye doya ai ba zataci ba ni banta’ba ganin kwad’ayayyiyar tsohuwa irin wannan ba.”

 

Kallonta nayi ina mamakin maganarta tsaki taja ta cigaba da aikinta, Gwaggo ta bankad’a labulen d’akinta ta fito tana fad’in” Surutan me nakeji ne nifa bana san husuma a gida.” Ummatu aikinta ta cigaba dayi bata tanka mata ba nace.”Gwaggo babu wata husuma da zata faru ki koma d’aki.

 

Tace.”Ummatu naji kamar kina maganar d’anwake ko.”? Tace.”Eh hakane Gwaggo Sa’ida ta fito dashi naga ko d’aya baku ci ba shine nake mamakin hakan ai da kun san ba zakuci ba sai kuyi min magana na rage garin.”

 

 

Tace.”Au!! Sai na fada miki ? Rabi tuntuni fa kin san ni D’anwake bai dame ni ba me zai sanya ki dimanci yi mana shi a gida.” Da sauri tace.”To gwaggo shi aka bani akace na sarrafa shi Maigidan daya kawo shi zakiyi wa wannan maganar.” Gwaggo bakinta ta ri’ke tana jijjiga kanta

 

Ganin al’amarin na nema ya girmama yasa na shiga basu hakuri….Ummatu kwanukan ta ta dauka ta shige gurinta, Gwaggo ta zungura mata bakinta tanai mata yen-yen! da hannu. Dariya ce ta kusa ta su’bce min, ta ri’ke hannuna ‘kasa-‘kasa tace”Rabu da ita Sa’ida ‘bakin ciki takeyi ganin kin yanka doya zaki soya tunda ta fito da hassadarta a fili ko d’and’ane kada ki bata mu cinye kayanmu.” Tsabar dariyar dake cina ta hanani bude baki nai mata magana da sauri na tsuguna domin wanke kwanukan. ta cigaba da magana ‘kasa-‘kasa! nace “Dan girman Allah gwaggo ki tafi ki zauna a daki kada taji wata magana ranta ya ‘baci matar nan iya ‘kokari tanayi dake duk wata rashin kunya da takeyi miki kece kike janyowa kanki.”

 

Tsaki! taja tace”Kinga na bar maganar yanzu ina canji na na ‘kwai ina lazimi naga kin dauki dari biyar.”

 

Ina kokarin bata amsa Sule ya shigo! sai ta hau washe bakinta tana kallon ledojin hannunsa dan ta dauka Alhaji Nura ne yayo aiken daya saba…….Yace.”Aunty Sa’ida gashi.” Kar’ba nayi nace.”Nagode Sule.” ya juya ya fita daga gidan bayan ya gaisheta…ta kalleni da fadin” Ganin ledoji a hannunsa Wallahi na dauka aike ne Alhaji yayo mana.” shuru nai mata na cigaba da wanke-wanke na sai ta bar gurin tana surutai irin wanda ta saba.

 

 

Ina daf da kammala soya doyar ya shigo gidan jikinsa bud’u-bud’u! d’auke kaina nayi ciki-ciki na amsa sallamarsa, bece min komai ba ya nufi bakin rijiya ya cika bokiti da ruwa yana wanke jikinsa, kamar wacce akace d’ago kanki ki kalleshi naga jikinsa jagab! yana kokarin cire rigar jessi d’in jikinsa cikin gaggawa na kauda kaina daga kansa gabana ya dinga faduwa ganin yanda gajeran wandon jikinsa ya ji’ke jagab dik ya manne masa a jiki girmansa ya fito sosai…… zama yayi bakin rijiyar ya cigaba da wanke jikinsa sam babu wata damuwa a tare dashi.

 

Har ya gama abinda yake a gurin ban sake kallonsa ba ta gefan idona naga tashinsa daga gurin, ajiyar zuciya na sauke cikin zuciyata nace”Khalid Allah ya shiryar da kai hanya mai kyau.

 

Bayan na gama sai na d’ora ruwan wanka na d’auki fulas din doyar na nufi daki dashi ,karo muka buga da ita tace.”Yawwa gwanda da da kikayi kika gama magariba tayi nima yanzu alwala zan d’aura.”

Ajiyar zuciya kawai na sauke na bata hanya ta wuce na shiga dakin fulas din hannuna na ajiye na fito domin nima na daura alwalar.

 

Sai da nayi wanka tukkuna na samu sukunin zama naci soyayyar doyar. lokacin ita Gwaggo har taci ta koshi ta kishingida tana saurarar redio, zaune ta mike tana gyara daurin dankwalinta tace”Sa’ida badan hali Rabi ba kisa mata biyu a plate a miqa mata ta mayar da yawu.”

 

Nace.”Aiko baki fad’a ba dama sai an bata hakkinta.” komawa tayi ta kwanta tana sake gyara ma daidaicin fulas din dake gabanta.

 

Nace”Wannan fulas din na gabanki meye a ciki.”? Tace.”Doya ce na ajiyewa Khalid saboda nasan yana san doya da kwai shima.”

 

Karamin tsaki naja nace”A maimakon ki ajiyewa Kawu sai ki ajiyewa wani Khalid Baba Iro shi yafi cancanta ki ajiyewa doya ba wannan yaron ba.”

 

Tana gyara redion ta tace.”Khalid nayi niyyar ajiyewa doya saboda haka sai ki shafa min lafiya.” Ta’be bakina nayi a nutse na fara cin doyar dake gabana ina had’awa da lemo.

 

Labulan d’akin ya d’aga yana magana, tayi saurin mi’kewa zaune da fad’in “Yawwa yaro nagari shigo kaci doya da kwai da zafin ta.”

 

Baiyi niyyar shiga dakin ba amma ganin mutuniyarsa cikin ‘karamar shart irin ta shan iska yasa ya shiga dakin ya zauna suna fuskantar juna….fulas din ta tura gabanshi da fadin” Gashinan da zafin ta dan bata jima da gama soyawa ba.”

 

Girgiza kansa yayi yace.”Bana bukata.” da sauri na kalleshi ina mamaki! nasan halinsa da kwadayi dole shima zaiyi sha’awar doyar amma kai tsaye yace baya so.”

 

 

Gwaggo jikinta ne yayi sanyi tace”Saboda me ba zaka ci ba.” Babu walwala a tare dashi yace.”Gwaggo daga ranar dana cigaba da cin abincin Aunty Sa’ida zata cigaba da raina ni daga yanzu mutukar abu nata ne a gidan nan to kada ki ajiye min idan ina bukata zan siyo da kudina.”

 

 

Tace.”Aa wannan ai doyar ce kawai tata amma ‘kwai ni na siya da kudina dan Allah ka daure kaci.” Girgixa kansa yayi yana duba wayarsa. Yace.”Gwaggo bafa zanci ba wallahi koda zan kwana da yunwa kuwa.”

 

Ba tare dana kalleshi ba nace”Kanka ka cuta yaro.” Uffan bece min ba ya cigaba da dube-dube a wayarsa.

 

Nace”Gwaggo ai sai ki ajiyewa Kawu dama shi yafi cancanta da ki kyautatawa ganin irin dawainiyar da yake.” cikin jin haushi tace.”Ke! banyi niyyar bashi ba haba jama’a kin dameni da wani Kawu to bazan bashi ba ga wanda nayi niyyar bawa tunda yace baya bukata gobe da safe naci kayata.”

 

Shuru nai mata na cigaba da abinda nake, dakin yayi shuru na tsayin minti uku, kaina na d’ago kawai muka had’a ido dashi gabad’aya hankalinsa na kaina ya zuba min shegun idanunsa na fitina.

 

Nace.”Naci maka bashi ne da zaka sani a gaba kana kallona.” shuru yayi bai ce komai ba kuma bai daina kallona ba. Girgiza kaina nayi na mi’ke na fita daga dakin na barsu.

 

Kan tabarma na zauna ina duba waya ta ya fito daga dakin yana sanya takalmansa na kauda kaina…..”Aunty Sa’ida.” naji ya kira sunana cikin sanyi murya. a nutse na kalleshi, ya lumshe idonsa tare da shafa sumarsa yace.”Wallahi kin had’u auntyna duk inda ake neman cikakkiyar mace kin kai duk sanda nazo gida hutu da tsananin sha’awarki nake komawa skull.”

 

Gabad’aya ji nayi yawun bakina ya bushe! na dinga kallonsa ina mamakin tsagerancin sa Murmushi yayi ya had’e yatsun hannunsa yayi heart 💘 Ilov u auntyna muuuuhhhh!.” ya hura min iskar bakinsa. kafin nayi aune har ya fice daga gidan, kaina na sunkuyar ‘kasa gabana ya dinga bugawa sosai al’amarin ya firgitani anya kuwa yaron nan bai fara shaye-shaye ba! ? ni kam ina zan kai kaina da wannan abin kunyar dole sai na tasar masa a tsaye zai daina yi min wannan iskancin, jikina a mutukar mace na mike na shiga dakin na kwanta ina tunanin matakin da zan dauka a kansa..

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment