Littafan Hausa Novels

Fuska Uku Complete Hausa Novel

Written by Hausa_Novels

Fuska Uku Complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

FUSKA UKU

 

 

 

*01*

 

 

 

*©Sameena Aleeyou…

 

 

 

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

 

 

 

_*Garin Misau Jihar Bauchi*_

 

 

 

Zaune take saman k’aramar kujera irin wanda mata ke amfani dashi a madafi… Yanda ta rafka uban tagumi ga buta ijiye gabanta zai tabbatar maka cewa cikin damuwa take, da alama alwala take shirin yi amma ko gizau da butan gabanta bata yi ba, tayi nisa matuk’a cikin duniyar tunani….

 

A haka ya fito daga makewayi ya kuwa hangeta yanda ya barta nan duk’ufe gaban buta… Girgiza kansa kurum yayi ba tareda ya furta koda kalma kafin ya k’arasa gaban k’aramar randar da kansa ya d’ibi ruwa ya tada nasa alwalan… Abin mamaki har yakai ga ida alwalansa wannan baiwar Allah sam batako motsa daga tagumin da tayi ba…

 

Cikin tsanaki ya warware hannun rigarsa kafin ya d’au karan goge bakinsa ya saka cikin bakinsa, lokaci guda ya k’araso yanda take a zaune….

 

“Bilkisu..!” Shiru bata amsa ba… D’an bud’e muryarsa ya kuma yi a karo na biyu

 

“Bilkisu..!”

 

Sai a sannan taji kiran nata da yake yi….

 

Saida ta sauk’e nannauyan ajiyan zuciya had’i da muskutawa kana tace “Malam wai har an sauk’o daga masallacin ne…?”

 

Yanda ta masa tambayar yaso basa dariya amma ya d’an gimste yace “Kiyi alwala kiyi sallah idan na dawo sai muyi maganar kinji koh… Amma wllhi wllhi kinji na rantse maki ban yarda ki tafi bariki neman d’anki ba, wannan shine rayuwar da ya zab’ar ma kansa tunda shi bamu da daraja bamuda mutunci a idanunsa, na tabbata akwai ranar da zai nememu da kansa basai kin tafi nemansa ba,…”

 

Baikai aya ba murya na rawa ta katse sa da fad’in “Malam wllhi ni nasan ba laifin d’ana bane tsinanniyar matar nan tasa ita ta shiga tsakaninmu dashi, wllhi nasan yana son zuwa gida amma bazai iya ba sabida ta jik’a ta basa yasha, kasan matan bariki sunfi maciji guba… Malam don Allah ka min izini na fita na nemo shi, yau fah kusan shekara kenan tim rabonmu dashi….”

 

Shiru Malam yayi tamkar mai nazari had’i da yin gajeren murmushi kafin ya girgiza kai yace “Mata kenan, akan ‘ya’yayenku zakuyi komai kuma zaku d’aura laifi kan ‘ya’yan wasu ku wanke naku ‘ya’yan… Shin kin tab’a sanin kalan matar tasa? Kinsan yaya akayi aka nema auren, kinsan wanda ya tura a matsayin wakili….? Duk baki sani ba, rana guda ya shigo tsakar gidan nan ya sanar damu yayi aure kuma bai buk’aci albarkan ko guda daga cikin mu ba… Sanin kanki ne tunda muka gama d’awainiyar karatunsa ya girma ya zama mutum ya tsallake k’afafu ya rabu damu,… Toh ina mai tabbatar maki kada ki kuskura ki d’aura laifi kan koma wacece ita matar nasa, wannan shine rayuwar da ya zab’ar ma kansa.. Laifina guda gata da na nuna masa da yawa, cikin sa’anninsa da suka taso tare a garin nan shi kad’ai ne ya tafi makarantar kwana na yaran hamshak’ai, kai tun daga alimantari d’insa karatu mai inganci na basa, idan baki mance ba har gona ta da shanayena na gado duk na sayar a dalilin na inganta rayuwar yaron nan amma ga sakayyan da yayi min, kar dai ki mance mahimmacin shanayen gado wajen bafillace…. Tabbas sai yanzu nake hango maganganun su Malam Dalha, shi yaro ba’a masa haka, yanda ka tarbiyartar dashi toh kuwa haka nan zai tashi maka, baisan babu ba tun tasowarsa shiyasa ya girma yana jin nauyin ya nunamu yace ga iyayen sa, na masa mai wuya tunda na turasa har k’asar waje yayi karatu ya sami abin yi…. Babu komai yajesa duniya ce tafi gabaruwa iya jima, bazan masa baki ba sannan bazan saka damuwarsa cikin zuciyata ya dameni ba, kuma kema ina shawartar ki da ki cire tunaninsa cikin zuciyarki domin hakan ne kurum zaifi maki sauk’i, mu zuba wa sarautar Allah idanu, rayuwarsa ce yayi yanda yaso da ita, duk yanda yaje yazo nan dai shine cibiyarsa kuma mahaifarsa…. Na wuce masallaci kinji liman har ya tada ik’ama, maza kema kar na dawo na sameki wajen nan….” Bai jira cewarta ba ya fice cikin sassarfa…

Darasi Hausa Novel Complete

 

Ta jima tana nan zaune a wajen tana sak’e sak’en hukuncin da zata yanke gameda al’amrin, har saida taji masallaci suna raka’a na uku kafin ta murmurs tana mai jin dad’in mafitan data samo, don bazata biye Malam ba ta zauna ta zuba idanu tanaji tana gani ta haifo tilon d’anta guda ma bariki ba…..

 

***

 

 

*Abuja*

 

 

 

Cikin sanyin muryarta taci gaba da buga k’ofar tana kuka take fad’in “NANA H please open the door, please listen to me sis…. Don’t shut me out again please…. Dan Allah ki saurareni…..”

 

Daga cikin d’akin kana iya jiyo sautin k’aran fashe-fashe… Cikin kukan itama take fad’in “Just go away NANA A I hate you, I don’t wanna see you ever again…. Ki fice min daga gida kuma kada ki sake zuwa yanda nake…. Burinki ya cika Ammah da Uncle SIRAJ suna fushi dani… Ki tafi bana son ganinki…”

 

 

Hannu tasa tana share hawayen da suka wanke mata fuska kafin tace “Sis I’m sorry…. I…. I didn’t mean to upset you, please let me explain.. Wllhi zanyi duk abinda kika umarceni kiyi hak’uri dan Allah….”

 

Jin kalamanta na k’arshe ya sanyata sakin wani shu’umin murmushi tana mai duban kanta jikin dressing mirror kana tace “I you sure zakiyi duk abinda na umarceki…”

 

Cikin sauri ta bakin k’ofar ta shiga jinjina kai tana fad’in “Wllhi zanyi kinji pls open the door…..”

 

Saida ta mik’e tsaye tayi rawa saman gadon tamkar mai tab’in hankali kafin ta dirk’o daga saman gadon ta nufo k’ofa….

 

Kallo d’aya tayi mata sanda ta bud’e k’ofar nan ta lura da yanda fuskar ‘yar uwartata ta kod’e sosai alamun taci kuka, lokaci guda tayi rau-rau tana fad’in “Oh Sis ki daina kuka pls… Kinji I’m sorry, bazan sake sakaki kuka ba kinji koh….”

 

Lokaci guda suka rungume juna kafin suka koma cikin d’akin hannayensu rik’e cikin na juna,…

 

Yanda suka jeru suka zauna bakin gado zaka gane tsan-tsan kamannin da suke, basai ance maka tagwaye bane sabida tsananin kamanni da suke, saidai d’aya ‘yar gayu ce ta k’arshe yayinda d’ayan gayun sam bai shalleta ba, hasalima bata iya ba….

 

“NANA ASMA’U….!” Cewar ‘yar gayun tana mai duban ‘yar uwar tata wacce itama ita take kallo….

 

“Kina jina, bawai bana son Uncle Siraj yayi aure bane, kinsan ‘yan matan yanzu wllhi idan yayi aure shikenan mun sallamawa matar da danginta shi, kuma sanin kanki ne bayan shida Ammah bamuda kowa, gwara ni ma nayi aure inada miji, but what about you, wa kike dashi? Waye zai tsaya maki a rayuwa namiji idan buk’atar hakan ta taso,… A kullum ina nusar dake hanya but baki ganewa, nifa idan ta ni ne Uncle Siraj zai iya zuwa yayi aurensa, but wllhi har ga Allah ke nake jiyewa Sis, kinga dai irin lalurar da kike fama dashi ta rashin k’afa guda, shin kina jin a haka zaki sami wanda zai k’aunaceki tsakani da Allah… Kema kinsan saidai ya aureki kawai don babban kaso na dukiya da mahaifinmu ya mutu ya bar mana, na sani kinada kyau Nana A amma duk yanda kyaunki yake baikai na lafiyayyayar mace ba maras nakasa a tattareda ita… Nana ki auna magana na ki gani, this world is something else now,…”

 

Tunda ta soma magana jikinta yayi sanyi dama hakan ne yake faruwa da ita duk sanda ‘yar uwar tata tazo mata da wani zance ko shawari….

 

A hankali ta shiga jinjina kai tana mai auna kalaman ‘yar uwar tata kana tace “Na fahimceki NANA HAFSAT, kuma duk abinda kika fad’a hakan take, amma wannan dalili sam baiki yasa mu hana k’anin mahaifinmu jin dad’in rayuwarsa ba, Nana H sam nakasata bata dameni ba, kuma nasan shi aure lokaci ne kuma abincin wani guban wani, nasan Allah zai kawo min wanda zai soni ya k’aunace dukda cewa yana sane da nakasan dake tattare dani, don haka ki daina saka ma ranki damuwa sabida lalurata… Sannan Uncle Siraj went through alot, yaga iftila’i daban-daban a rayuwa, kar ki manta a baya duk macen da ya nema toh fah mutuwa takeyi, sannan kar ki mance Aunty Zulfah a daren aurensu ‘yan fashi suka shigo har cikin gidan suka kasheta, daga wancan lokaci ya shafe shekaru kusan uku cikin tsananin tashin hankali da alhini, uwa uba sanin kanki ne babu abinda Ammah take so kaman taga autanta yayi aure…. Nana H nidai a gani na mu bar Uncle Siraj yayi aure idan har Allah ya tabbatar da hakan…..”

 

 

Tunda ta soma magana take binta da wulak’ancaccen kallo tana huci, lokaci guda ta mik’e tsaye tana nuna mata k’ofa take fad’in “Fita.. Fita nace idan ke baza’ayi shawarin arziki dake ba….”

 

Bata mik’e d’inba bata fice ba sai gyara zama data kuma yi…..

 

Lokaci guda tamkar ta tuna wani abin ta komo ta zauna a mazauninta kafin ta sauk’e ajiyan zuciya tace “Gaskiyanki ne Sis, Uncle Siraj deserve to be happy… Babu damuwa zanje har gidansu Nadiya na bata hak’uri, amma nasan yana fushi dani…” Lokaci guda idanunta sukayi rau-rau ta kuma damk’o hannun ‘yar uwar tata tana fad’in “Dan Allah Sis ki basa hak’uri kinji, make sure ya hak’ura pls kinji dan Allah….” Ta k’arashe kaman zata kurma ihu…

 

Lokaci guda tausayin ‘yar uwar tata ya shigeta….

 

***

 

 

Driver na ida parking ta hangi Ayiya tsaye farfajiyan gidan hannu hard’e da k’irji tana bin motar da kallo, ga dukkan alamu dawowarta take jira, ta kuwa sha mur….

 

Sosai tasha jinin jikinta don babu wanda yasan sanda ta fice a gidan, bayan tasan ya zamto tamkar doka duk yanda zataje tofah tareda Ayiya ne , Dattijuwa mai kimanin shekaru 66 a duniya…

 

Cikin takunta na d’ingishi ta nufo yanda take…

 

Sam bama ta kanta Ayiya take ba tukuna, Sule dreba kawai take kallo yanda yayi parking motar cikin tsoro don yasan zai iya kwasan nasa buhun bala’in tunda ta sa masa doka bataso ‘Yar Albarka tana fita ita kad’ai sabida lalurin dake tattareda ita….

 

“Ayiya barka da yammaci….”

 

Kallonta kawai tayi ba tareda ta amsa ba kafin ta k’arasa ta nufi yanda Sule ya ida parking….

 

Kafin ta soma magana Sule ya tari numfashinta da fad’in “Wllhi wllhi Ayiya ba laifina bane, kindaiga yanda Nana Hafsat ta fice a gidan nan cikin fushi da b’acin rai, ni kuma wllhi magiyan da Nana Asma’u tayita min shiyasa na kaita…”

 

 

Baikai aya ba ta katsesa da fad’in “Ka kaita a muzanta ta a wulak’anta ta a fad’a mata kalamai marassa dad’in ji koh… Kadai san Hafsatu ba mutunci bane da ita wulak’anci sam bai mata wahala, ni kuma ina numfashi k’aryan mutum ya muzanta ‘yar albarka ko ya wulak’anta ta… Kai billahillazi sai mu tafi har kotun Buhari da duk mahaluk’in da ya hana ‘yar Albarka rawan gaban hantsi….”

 

Sule dai dubanta yake cikeda mamaki yanda yaga bilhakk’i laifinsa kawai Ayiya take gani sam bataga laifin Asma’u ba…..

 

“Ayiya bafa ni na kar zomon ba rataya aka bani…..”

 

“Kai tafi can rufe min baki, da wani abin ya sameta yau da ka gane kurenka….”

 

Ta wuce fuuu tana ci gaba da sababi….

 

 

Nana A ta bita da kallon mamaki yanda sam fad’a bai mata wuya musamman idan akanta ne…. Ko tankata batayi ba ta janyo hannunta suka nufi cikin gidan..

 

Sum-sum Nana A ta take mata baya…

 

 

A parlor suka tarar da Ammah ta rapka uban tagumi, don duk ranar da Siraj da Nana H suka b’ata sam gidan haka zai zamto babu walwala domin gaba d’aya basu gane kan Siraj har sai ya shirya da niece d’in tasa wacce yake matuk’ar k’aunarta da kuma jida ita….

 

****

 

 

Bakin zaninta ta kamo tana kuma goge hawayen da suka mak’ale cikin idanunta take ci gaba da fad’n

 

 

“JUNAID ka tabbata zaku iya zama ku biyu rak, ka tabbata komawa wancan gari mai bak’in tarihi shine jin dad’inku….. Junaid I’m afraid… Ina tsoron kada su sake ganinka don na tabbata a iya tunaninsu ka mutu tuntuni….”

 

Matashi ne wanda a k’iyasce bazai gaza shekaru 32 ba zaune saman wheelchair aka kirada JUNAID, dukda cewa a ido k’afafunsa lafiya lau suke saidai a zahiri ko motsasu bai iya yi, yau kusan shekaru hud’u kenan da faruwan Al’amarin….

 

Cikin tsanaki ya soma tura tayan keken guragun nasa har ya iso gaban middle aged woman d’in da ke ci gaba da matsan k’walla…

 

Cikin muryarsa wanda yake tamkar ana hura sarewa ya soma magana…

 

“Umma Marie thank you for everything…. Thank you for taking care of us.. Nida Azeeza, na gode da jinyata da kikayi, na tabbata banida abinda zan biyaki dashi… Kuma na gode da b’oyeni da kikayi a lokacin da ake farautar rayuwata…. Umma Marie I don’t have a choice than to face those three….. Nayi alk’awarin d’aid’aita FUSKA UKUN nan ta ko wani irin yanayi, kiyi hak’uri Umma Marie dole ce tasa nayi hakan…”

 

Cikin rawar murya Umma Marie tace “Toh Junaid baka tsoron ka jefa rayuwar Azeeza cikin had’ari, meyasa bazaka tafi kai kad’ai ba ka barmin Azeeza, kar wani abin ya taso kai kuma ba k’afafu gareka ba…..”

 

Murmusawa yayi had’i da sunkuyar da kai ya k’urama k’afafunsa idanu kafin ya d’ago ya dubi Umma Marie yace “Kar ki damu Umma I can protect her and provide for her… Bazan tab’a bari wani abu ya sameta ba, ki kwantar da hankalinki kinji…..”

 

Jigum tayi tana dubansa kafin tace “Shikenan, Allah ya tsareku gaba d’aya, amma Junaid muddin naji wani mummunar labari gamedaku zan baro Yobe na taddaku a can Abujan….”

 

Murmusawa ya kumayi kana yace “Umman mu kar ki damu, na rigada na shirya, kawai taimako guda da zaki sake min shine ki shawo kan Azeeza ta yarda ta biyoni, and please kar ki sanar da ita komai gameda k’udirina…”

 

 

 

 

*SameenaAleeyou..

 

FUSKA UKU*

 

 

 

 

*02*

 

 

 

 

*©Sameena Aleeyou..

 

 

 

 

_*Tambuwal* _Sokoto_

 

 

 

 

Zaune suke baje-baje a tsakar gidan ko wacce hannunta rik’eda kananan beads irin wanda ake had’a sark’a na amare dasu….

 

Budurwa ta tsakiyar mai kimanin shekaru 24 itace ke fama zira na hannunta tana yi tana taunar chewing gum ga d’aurinta a gaban goshi irin wanda hausawa ke cema ture kaga bala’i, itako wacce ke zaune daga k’arshen tabarman sai faman ‘yan wak’e-wak’enta take tana had’a nata ‘yankunnen

 

Wata dattijiwar mace ce wacce bazata gaza shekaru 58 ba ta fito hannunta rik’e da langa tana duban ‘yanmatan wanda yanzu sun k’ware sosai a sana’ar tasu, har cikin ranta take jin dad’in yanda suka rik’i sana’arsu babu ruwansu da abin hannun saurayi, shiyasa take matuk’ar son k’awancen d’iyarta da Zaliha don ya fiye mata k’awance da yaran lungun nasu don duk bawai tayi na’am da tarbiyarsu bace….

 

Sai sannan ‘yan matan suka lura da ita, har suna had’e baki wajen cewa “Dadda barkada fitowa….”

 

Fuskarta d’aukeda murmushi tace “Sannunku da k’ok’ari ‘ya’yana Allah dai ya dafa maku….”

 

Gaba d’aya suka murmusa itako mai taunar chewing gum d’in harda wani yin k’araras dashi kana tace “Ameen Daddata abin alfaharita, da kud’in beads zan kaiki Makka na sai maki hak’orin gwal….”

 

Nan fah Dadda ta washe baki tace “Allahumma ameen d’iyata….”

 

Ana cikin haka wani almajiri yayi sallama ya soma gaida Dadda da tuni ta gimtse fuska don tasan yaron bazai wuce aike yazo ba…. Aiko kaman jira yaron yake nan ya soma fad’in “Wai ana sallama da MAIRO a waje….”

 

Ai bai ida maganar ba Dadda ta dasa butar ta a k’asa kana tace “Jekace bazatazo ba dan uwarka….”

 

Yaro kuwa jin haka ya fice a guje har yana cin karo da k’yaure…

 

Dadda taci gaba da sababi tana fad’in “Inyi ai kaji irinta, dagaji sune irin samari masu lalata yaran mutane, toh dan ubanka bazata zo ba, salon ya matseta a lungu koh… Ni d’iyata sai na darje mata miji kafin na aura mata ehe, babu shegen da zai wanko b’aragurbin k’afafunsa ya nemi auren d’iyata na basa…..”

 

Bata ida magana ba sai ganin saurayin sukayi har cikin gidan, don tsaf yana jiyo zage-zage da masifar da Dadda ke faman yi…

 

Saurayin nan yana shigowa ‘yan matan nan suka bar abinda suke suka mik’e tsaitsaye babu shiri suna kallon ikon Allah…

 

Dadda na ganinsa ta shiga gyara bakin zaninta tana fad’in “Toh jarabebbe d’an naci, ni dama nasan kaine fitinannen da bazaka d’auke idanu kan d’iyata ba… Toh duk maitanka haka zaka ganta ka barta dan uwarka, shege d’an bakin uwa….”

 

Batakai aya ba saurayin ya shek’e da dariya kana yace “Gwara ni ko uwata ta min baki inada uba, shegiyar ‘yar taki da kike b’oyeta uwa gwal ki sanar damu ubanta, aikin banza aikin wofi ashema yawon garuruwa da kuke ba haka kurum bane, idan ba tsoro ba ki sanar da d’iyar taki ubanta mana ko kuma ki sanar da ita ga garinta mahaifarta….” Yayi wata murmushi kafin yaci gaba da fad’in “Bakuda gari yawon duniya kawai kuke, ki jik’a ‘yar taki ki sha babu abinda zamuyi da shegiya maras asali, kuma kinji na rantse idan baku bar mana gari ba sai mun kwance maki zani a kasuwa…..”

 

Baikai aya ba yaji sauk’ar lafiyayyar mari a k’uncinsa…

 

Shaye da mamaki yake rik’e da fuskarsa yana duban wacce ta maresa gata a gabansa baifi yayi wurgi da ita ba…

 

“MAIRO ni kika mara….?”

 

“An mareka d’in maras mutunci wanda baisan darajan tsofaffinsa ba, kaji na rantse maka idan baka fice a gidan nan ba sai mu lallasa maka na jaki….”

 

Ta k’arashe tana kwance d’aurin kwalinta had’i da shan d’amara dashi…

 

A tamanin d’aya budurwar ta fad’a kitchen ta rarumo wuk’a ta shiga wasawa yayinda Mairo ta sunkuya ta wawuso k’afafunsa ji kake timmm ta kadasa k’asa babu ko gizau a tattareda ita.. Fad’i take “Zaliha yi maza ki kawo wuk’ar kafin ya tashi….”

 

Jin haka yasa Saurayin kukan kura zai tashi don bai zaci Mario nada k’arfi har haka ba, saidai kafin ya mik’e Dadda ta zaune akansa tana fad’in “Dan uwarka koma babu yanda zakaje…”

 

Ai tuni ya bud’e murya ya soma neman d’auki… Basu k’yalesa ba saida suka masa lilis, bai t’aba yarda da hausan da akace b’aro a hannun mata ba sai yau, shikam ya shaida dukda ba sata ya shiga ba…

 

Saurayin nan yana ficewa a guje Dadda tasha jinin jikinta don tasan yau an d’agowa Mairo gyambon dake zuciyarta, akasarin garuruwan da suka baro wannan dalili shikesa su baro, sannan wannan na d’aya daga cikin da yasa Mairo batada tak’amemmen manemi, da zaran sunji batada asali sai su gudu ko iyauensu suk’i yarda, idan ma baka gudu don rashin asalinta ba zaka gudu don bala’in uwarta Dadda….

 

Dadda zatayi magana Mairo ta d’ago mata hannu alamun dakatarwa, ta kuwa cika tayi fam sabida b’acin rai, cikin tsananin fushi ta wuce uwar d’aki ta kulle, don duk masifa irinta Dadda tana tsoron masifa da fushin Mairo…

 

****

 

 

*LAUSHI GROUP*

 

 

Tafe suke cikin tampatsetsen kamfanin wanda ya tsaru iyaka tsaruwa, yaji landscaping….

 

Matasa ne wanda a k’iyasce bazasu gaza shekaru 35 zuwa 36 ba, sannan da gani zasu iya kasancewa sa’anni ko kuma subawa juna ratan shekara d’aya zuwa biyu…

 

Wanda yake daga tsakiya shi ne yafisu haske gaba d’aya sannan sanye yake cikin business suit d’insa wanda ya amshi jikinsa sosai ya dad’a fito da kyaun halittarsa…

 

Shi kuwa d’ayan wanda yake daga b’arin dama sanye yake cikin kaki irinta Nigerian police force, shima kakin ta ‘yansanda ta amshesa sosai saidai shi baida haske kaman na mai sanye da suit d’in amma kallo guda zaka masa ka fahimci tsan-tsan bafillace ne ga sumarsa da suke a nannad’e irinta fulben usul…

 

Shi kuwa d’aya na b’angaren hagu sanye yake cikin wata lallausar yadi ruwan toka d’inkin half jampa, shi yafisu duhu gaba d’aya saidai Allah ya masa kyaun jiki da cikan zati, wanda hakan yasa yakeda gizo sosai a idanun jama’a…

 

A wata ‘yar k’aramar rumfa ta shak’atawa suka zauna suna ci gaba da tattaunawarsu lokaci guda wata mace sanye da farin uniform ta ajiye k’aramar tray a gabansu wanda ke d’auke da cups basai ance maka Champaign bane cikin cups d’in…..

 

 

Saida ya sipping Champaign d’in kafin ya kuma duban saurayin dake sanye cikin business suit yace “You’ve been an ass…. Ka sani ko?”

 

D’ago idanunsa guda d’aya yayi had’i da kanne d’ayan kana “Na sani…. Kuma bazan bata hak’uri akan abinda Nana H tayi mata ba, wannan ita ya shafa bani ba…. Kai nifa tunda na rasa Zeenatu bana tunanin akwai macen da zan kuma rasata ya dameni ba…. Banida lokacinta ma…”

 

Da gefen bakinsa yake murmusawa yana duban abokin nasa kafin ya d’ago cup d’insa alamun toast yana mik’awa d’aya abokin nasu yake fad’in “To Siraj Laushi’s pain in the ass behavior…. May he stay as forever bastard ….”

 

Kallonsa kawai Siraj yake had’i da girgiza kai kana yace “LAMID’O idan kana son Nadiya ce fah you can have her, wllhi I dont care…..”

 

Sai sannan mai sanye da kakin ya murmusa had’i da ajiye cup d’in hanninsa saman k’aramar table d’in kana yace “Wannan shi ake kira fad’an gauraye…. Ya kamata ku ajiye iyali tsufa kuke kun sani koh….”

 

“Fad’a masa Detective ya ajiye Iyali dai don shine mai manyan d’iyoyi ‘yanmata… Nikam I’m still young yanzu ma na soma cin tawa duniyar…..”

 

Siraj yayi k’wafa yana watsawa Lamid’o mugun kallo kafin ya dubi matashin dake sanye cikin kakin yace “AHIDJO tashi muje naga Hafsat, I’m worried about her….”

 

Kallonsa sukayi gaba d’aya yanda ya mik’e a birkice kafin Lamido yace “Wannan SHAK’UWA taku tayi yawa, a dai dinga ragewa ake tunawa Hafsat ta girma ba k’aramar baby bace infact tama fika samun experience na rayuwa tunda tayi aure kai kuwa bakayi ba….”

 

Banda watsa wa Lamido mugun kallo babu abinda Siraj keyi… Baida lokacin tsayawa amsa masa gajeren tsaki kawai yayi had’i da d’aukan car keys d’insa ya fice daga cikin rumfar…

 

A tare Ahidjo da Lamid’o suka mik’e suka take bayan abokin nasu…..

 

Suna tafe wayar Ahidjo ta soma vibrating daga wajen aikinsu ake kiransa dole ya wuce ofishin nasu yayinda Lamido da kuma Siraj suka nufi gidan Ahidjon domin duba Nana H, ‘yar gaban goshin Uncle Siraj wanda a kullum kafawa abokinsa Ahidjo sharad’ai yake akanta, ba’a b’ata ranta, donma shi kansa Ahidjon bawai lokacinta yake dashi ba yafi baiwa aikinsa mahimmanci, sam basuma faye zama tare ba sunan anyi auren ne kawai…

 

 

***

 

 

*Misau*

 

 

 

A guje yauma ta shigo gidan tagajan bagajan… Innah Balki tana lafiya meke faruwa… Ai kafin ta ida fitowa daga d’aki ta hangi mutum saman rijiya sai tsalle take tana kururwa…

 

Babu shiri zani a hannu ta fito burut daga d’akin tana sallalami…

 

Iya Gaje ce ta shigo cikin gidan itama a d’ari tana fad’in “‘Yar k’wal uba yau yankaki zanyi shegiya mai kamada mayu….”

 

Aiko Gaje tayi wajen rijiyan nan da d’aurin k’irji haka nan ta fito tun daga gidan nata…

 

Innah Balki banda salati bata komai sai rawa da jikinta keyi kaman an d’ana mata shokin ganin yanda Gaje ta biye k’aramar yarinyar da batafi sha hud’u ba suna kokawa jikin rijiya….

 

 

Innah Balki ta maza tayi ta rik’o yarinyar ta b’oyeta a bayanta yayinda Gaje taci gaba da sababi…

 

“Yau zaki bar min gida ehe, munafuka mai halin uwarta, tambad’add’iya kawai….”

 

A hasale Innah Balki ta soma fad’in “Ke Gaje ki sauk’ak’a harshenki kan ‘yar marainiyar nan, ke ko tausayi bakiji… Shin wai bakida imani ne….?”

 

Bata kai aya ba Gaje dake binta da kallon wulak’anci tace “Toh uwar shisshigi da iyayi, banida ita, nace banida imanin anyi rabonta ina bacci…. Yo dole ma kice d’a na kowa ne mana sabida naki d’an ya fantama bariki… Ayyiriri ni Gaje naga salo… Toh wllhi Balki ki fice a hidiman gidana idan ba haka ba billahillazi zan maidaki abin kwatance a garin nan…..”

 

Tunda ta soma magana Innah Bilki ke kallonta, girgiza kai kurum tayi tana mai bin Gaje da addu’o’i na shiriya….

 

Gaje ta gyara d’aurin k’irjinta ta dubi yarinyar tace “Dan ubanki zaki dawo gidan ki sameni ne….” Daga haka fuuu tayi ficewarta daga gidan….

 

Innah ta maido da dubnta ga yarinyar wacce har lokacin shan zuciya take kana ta dafa kanta tace “DEEJO mai kika mata yau kuma? Ba na hanaki rashinji ba..?”

 

Bakin d’amaranta ta kamo tana sharen hawayenta take fad’in “Innah waifa kawai don wannan Ladon mai kid’a a dandali yace na kai mai fura d’akinsa ya saya ban kaiba shine fah tayita dukata wai na mata asara…”

 

Innah ta shiga sallalami tana tafe hannaye cikeda mamakin bak’in zuciya irinta Gaje, Allah sarki tausayi Deejo ya kuma cika zuciyarta, Deejo k’aramar yarinya ce wacce kamata yayi ace tana makaranta bama tallaba, amma gaba d’aya Gaje ta tauye rayuwar wannan yarinya, sannan nema ma take ta d’aurata kan wata mummunar rayuwa, tabbas d’a na kowa ne idan ta taimaki Deejo watak’ila Allah yaji k’anta ya karkato mata da hankalin nata d’an zuwa gida……

 

 

***

 

 

Sosai Nadiya taji manikin ganin Nana H a gidansu, don irin d’iban albarkan da tayi mata a while ago kan Kawunta bata tsammaci zata kuma iya mata koda kallon mutunci bane, sai gashi kuma wai hak’uri tazo bata har tana neman su zamto k’awaye….

 

“I’m sorry for being bit emotional…. Aunty Nadynmu kiyi hak’uri da Nana H, kowa da kika gani a gidanmu wllhi hak’uri suke dani, kinsan ina son Uncle Siraj sosai kuma inaji dashi, so duk wata mace sai naga kaman rabamu dashi zatayi…..” Ta k’arashe tana sipping laccasera juice d’in da aka serving d’inta a cup, k’afafun nan kuwa d’aya bisa d’aya…. Ga wani tayani gantalin gyale wanda ake kira kafi rariya shi ta d’aura bisa kafad’anta, yatsunta kuwa kama daga na hannun zuwa na k’afa duk sunsha kwalliya da faratan roba, tamkar ba d’iyar musulmai ba balle kayi tunani wai har aure gareta….

 

Nadiya ta d’an murmusa kana tace “Babu komai Nana Hafsat na fahimceki kuma na hak’ura komai ya wuce insha Allah….”

 

Murmushi Nana H tayi had’i da matsowa kusan Nadiya tayi hugging d’inta tana mai bayyana murnanta…

 

Daga haka hira sosai ya b’arke tsakanin Nadiya da Nana H har saida taga kiran Uncle d’inta Siraj na shigo mata, nan ta nunawa Nadiya fuskar wayar taga mai kiran nata yanda aka rubuta _Uncle luv_

 

Da murnanta ta d’aga don ta sanar dashi gata gidansu Nadiya kuma ta fixing komai….

 

Siraj yaji dad’in hakan sosai, don yasan yanda baison b’acin ran Nana H haka itama bata k’aunar b’acin ransa…. Lamido da ya kanne idanu had’i da kafe Siraj dashi sai faman sak’awa da warwarewa yake…

 

Suna rabuwa da Siraj gidansa ya wuce yanda ya jera wasu pictures wanda akayi crossing d’insu da jan marker alamun an gama dasu…

 

Had’e kansa yayi waje guda yana wasa da zoben hannunsa saman hotunan…….

 

 

 

***

 

 

Ayiya da Nana A ne zaune a parlorn suna kallon tashan abin dariya cikin raha da jin dad’i…. Kaman daga sama sai ganin Hafsat da Siraj sukayi sun shigo cikin gidan mak’ale da juna…

 

Nan da nan Ayiya ta had’e fuskar nan tamau don itakam tak’i jinin wannan Shak’uwa mai k’arfi dake tsakanin Siraj da Nana Hafsat….

 

Ammah dake sauk’owa daga bene murmushi ta sakar masu sanda ta hangi Siraj da Nana H na shigowa cikin parlorn kana tace “Inyye kaga ‘yar gidan Kawu an shirya kenan….”

 

Nana H ta kuma shigewa cikin k’irjin Siraj tana wani murmushi take fad’in “Ammah kinsan bani son fushin Uncle luv yanzu ma daga gidansu Nadiya muke mun warware komai, tama riga ta zama k’awata…”

 

Ammah ta fad’ad’a murmushinta kana tace “Da kyau ‘yar gidan Uncle haka nake son ji maza ku k’araso nayi serving d’inku dinner….”

 

Ko takan Ayiya da Nana Asma’u basu bi ba suka nufi wargajejen dining area d’in…

 

Asma’u ta d’ago idanunta da suka d’anyi rau-rau tana duban Ayiya, domin har cikin ranta wani sa’in takanji zafin banbanci da Kakarta da kuma Kawunta da suke nuna mata k’arara tsakaninta da ‘yar uwarta…..

 

 

 

Cikin sauri Ayiya ta kamo hannunta tana girgiza mata kai alamun kada tayi kuka… A hankali Ayiya ta kamo hannunta tace “Tashi muje lokacin hutawarki tayi, a cire k’afar nan ki huta koh….”

 

Babu musu Asma’u ta shiga jinjina kai tana k’ok’arin dafa kujera domin mik’ewa….

 

Haka suka taho zasu wuce saman bene sai sannan Siraj ya kula dasu ya d’an bud’e murya yace “Nana A , sweetheart zo mana muci abinci….”

 

Daga yanda yayi maganan cikin nuna kulawa har cikin ranta Nana H bata so ba, amma gimtsewa kawai tayi tana ci gaba da cakalan fruits d’in dake gabanta…

 

Cikin sanyin muryarta had’i da murmushi saman fuskarta ta d’an kaikaito tana dubansu kana tace “A’a Uncle na riga naci abinci… You go ahead…”

 

“Come on sweetheart, zo ki zauna cikin ‘yan uwanki mana, kar ki koma d’aki ke kad’ai…”

 

Caraf kaman jira take ta tari zancen da fad’in “Uncle luv ka k’yaleta kasan ta saba da zaman d’aki, ko tazo nan ma bazata saki jikinta ba…..”

 

Ayiya data cika tayi fam kaman jira take nan ta soma sillesu tas…

 

“Toh bazata zaunan ba, data zauna yanda za’a muzanta ta a b’ata ranta gwara ta zauna ita kad’ai a d’aki… Ank’i ta zauna d’in…. Wuce mu tafi ‘yar Albarka….”

 

 

Ko amsarsu bata tsaya sauraro ba ta janyo hannun Nana A suka wuce..

 

Nana H ta rakasu da hara had’i da jan tsaki….

 

 

***

Sunfi minti talatin suna zaune a train station d’in babu alamun jirgi ga yunwa da sanyi dake azalzalanta

 

 

“Ya Junaid nifa yunwa nakeji…” Ta fad’i tana kuma kwantar da kanta saman luggage d’insu…

 

D’an dubanta yayi yanda take hamma babu ko k’akk’autawa cikeda tausayinta…

 

Hoodie d’in dake bisa kansa ya kuma janyowa ya rufe fuskarsa sosai kafin ya nufi kujeran da ya hangi dangin snacks ajiye saman kujerun…..

 

 

 

 

 

 

 

*SameenaAleeyou

FUSKA UKU

 

 

 

*03*

 

 

 

 

*©Sameena Aleeyou

 

 

 

 

 

 

 

 

Yaran sam basu kula dashi ba har ya isa yanda snacks d’in suke ajiye bisa dogon kujeran, sai faman tsalle-tsallen su suke a wajen…. Ya jima yana duban yaran kafin ya janyo hoodie d’insa ya kuma rufe fuskar shi da shi…. Cikin azama ya kwashi snacks d’in dake nannad’e cikin tissue paper ya zura cikin rigar sanyin nasa….

 

Har ya soma waina tayar kekensa cikin sauri don barin wajen, kaman wanda aka ce ya tsaya, cak yayi birki ya tsaya tamkar wanda ya tuna wani abin, cikin sauri ya kuma juyo kan keken ya nufi yanda ya d’au abincin, kaman yanda ya d’auka haka ya bud’e rigarsa ya maidasu ma’ajinsu…

 

Duk abinda Junaid keyi akan idon yarannan ne… Sosai Junaid ya basu tausayi musamman da sukaga halin da yake ciki a haka har mahaifinsu ya k’araso ya taddasu, nan suke nuna masa abinda suke kalla, d’an babban cikin yace “Daddy yunwa yakeji.”

 

Mutumin da ya ambata da Daddy shiru yayi tamkar mai nazari basu ankara ba sai gani sukayi babu Daddyn su a wajen, suka ci gaba da kallon Junaid yanda ya komawa Azeeza babu abinci sai faman kuka take masa yana lallashi….

 

Yaran har suna rige-rige wajen d’aukan sauran abincinsu suka kaiwa Azeeza, ta macen wacce bazatafi shekara biyar ba harda gogewa Azeeza hawaye tana fad’in “Aunty ki daina kuka you can eat our food kinji, tunda Momy ta tafi ta barmu Daddy ya hanamu kuka yace mai kuka tears d’insa zai k’are….”

 

Daga Azeeza har Junaid cikeda mamaki suke duban yarinyar, d’ago kai da zasuyi suka Kalli mutum tsaye akansu hannunsa rik’eda farin takarda wanda yake a nad’e basai ance maka snacks bane ciki… Jikin mutumin yayi sanyi sosai jin abinda ‘yar tasa take fad’i

 

Shiko namijin mai kimanin shekaru 6 kallon mahaifinsa yayi yaga yanda yayi sakare yana duban k’anwarsa sannan ya dubi su Junaid da Azeeza yaga yanda suma suke kallon mahaifinsa da k’anwarsa cikin wani irin yanayi…

 

Cikin sauri yaron ya k’arasa ya shiga janyo k’anwarsa daga jikin Azeeza yana fad’in “Taheera what do you think you’re doing, unhand her… Didn’t Dad warn us about strangers?..”

 

Cikeda damuwa yarinyar tace “But Hammad look she’s crying and hungry… I only want to help…”

 

Cikin sauri mahaifin nasu ya durk’usa had’i da dafa kan yaran kana yace “Hey kids go back to your seat now okay….”

 

Babu musu yaran suka jinjina kai , Taheera ganin abinci hannun mahaifinta harda d’anyin tsallen murna kana ta juyo da dubanta ga Azeeza tace “Aunty Daddy bought some…. Ki daina kuka kinji…..”

 

Azeeza da murmushi ya cika fuskarta don sosai yarinyar ta burgeta batasan sanda ta shiga jinjina mata kai ba tana share hawayenta…

 

Bayan su Taheera sun koma wajen zamansu sai kuma aka shiga kallon-kallo takanin mutumin dasu Junaid…..

 

Saurin saita kansa mutumin yayi kana ya mik’awa Junaid hannu donyin musabaha….

 

Junaid bai mik’a masa hannu ba sai kallon da ya bisa dashi…

 

K’ak’aro murmushi mutumin yayi yana d’an satan kallon gefen da Azeeza take kana yace “Am…. am…. Kuyi hak’uri da surutun Taheera, haka yarinyar take da son taimako,….” Ya maido da dubansa ga Azeeza wacce ta kafesa da idanu uwa ta sami TV… Gaba ya d’aya ya tsargu da kallon da take masa, cikin sauri ya ajiye abinda ke hannunsa a gefenta kana yace “If you don’t mind miss….”

 

“Bazataci ba…”

 

Kalaman da ya jiyo kenan tana fitowa daga bakin Junaid….

 

Mutumin ya bisa da kallo cikeda mamaki…

 

Azeeza da tuni har tasa hannu zata d’auka Junaid ya finciko takardan yayi wurgi da ita…

 

Cikeda mamaki mutumin ke kallon Junaid sai sannan ya tuna yayi shisshigi ta yuwu wannan yarinya matan gurgun nan ne dole abin ya zafesa idan yayi mata kyauta…

 

Saida ya daidaita tsayuwansa had’i da gyaran murya kafin yace “Kayi hak’uri bawan Allah taimako nayi niyyan yi kaman yanda naga yarana sun buk’aci hakan, sannan ni ba mugu bane bazan cutar daku ba kuma ni d’an uwanku musulmi ne…..”

 

“Malam naci bazataci ba… Bamu sanka ba bamusan daga ina kake ba kawai ka baiwa ‘yar uwata abinci.. A ina ka tab’ajin anyi haka…?”

 

Saida ya sauk’e nannauyan ajiyan zuciya jin Azeeza ba matar Junaid bace kafin ya d’an murmusa yace “Toh ni sunana Barrister Nasaar Gumau, kuma ni d’an asalin garin Gumau ne dake jihar Bauchi sannan mazauni garin Abuja…. wad’ancan yarana ne Hammad and Taheera, yanzu haka mun fito garin Maiduguri ne domin duba dangin mahaifiyarsu….. Kuyi hak’uri nayi abinda baku umarceni ba, a yanayin aikina kullum ina zama ne cikin shirin had’uwa da sabbin mutane….”

 

Tunda ya soma magana suke dubansa cikeda mamakin yanda ya zak’e sai basu labari yake uwa wanda suka tambaya….

 

A dai-dai lokacin jirgi ta iso ba tareda sun sami zarafin amsa masa maganganun tasa ba, iyakaci abinda suka fahimta shine gari d’aya suka nufa….

 

Junaid bai kuma cewa komai ba sai tura wheelchair d’insa da ya shigayi had’i da tura jakan kayansu…

 

Azeeza kuwa tuni ta d’au snacks d’inta ta soma ci tana alamu wa Barr Nasaar da hannu alamun godiya….

 

Kallonta ya dingayi yana murmushi har yaransa suka k’araso suka rik’e hannayensa, cikin sauri ya isa yanda luggage d’insu yake shima ya shiga janyowa suka nufi jirgin…..

 

***

 

*Misau*

 

 

A k’ofar makarantar allonsu ta hangi Lado ya kasa ya tsare hasken farin wata tal ya haske mata d’an duk’uninin fuskarsa…..

 

Jikinta ya d’auki kyarma don duk yanda taga Lado haka takeji, Lado ya zame mata kaman dodo a garin…

 

Sunkuyar da kanta tayi had’i da damk’e allonta sosai ta soma tafiya tamkar wacce zata auka k’asa….

 

Tana isowa yanda suke shida abokansa bugun k’irjinta ya k’aru ga uwar warin kayan maye da ya gauraye wajen, musamman suka maida wajen dabansu sabida hanyar wucewar Deejo ne….

 

Aiko kaman jira suke ta k’araso suka mik’e suka nufota, bata ankaraba duk saurin da take sai ganin Lado tayi tsaye k’ik’am a gabanta yana hura hayak’in sigari…

 

K’iris ya rage Deejo bata saki fitsari a wando ba sabida tsoro, ta yunk’ura zata sa gudu tayi d’aya hanyar sai ganin Tanimu tayi a wannan gefen, d’aya gefen ma Muntala ya tsare…..

 

Deejo ta soma kuka tana k’ok’arin duk’awa take fad’in “Dan Allah kuji k’aina kumin rai wllhi makarantar Allo na nufa….”

 

Bud’an bakin Muntala sai cewa yayi “Allah yasa tawada kika nufa gaba d’aya, banza kucaka ke kin tab’a ganin Lado ya kira budurwa d’akinsa a garin nan tak’i zuwa… Ke wacece??”

 

“Kaima ka tsaya kake tambayanta wllhi tunda nayi niyya ko babu kaji sai na d’ana shegiya ku nad’o min ita…..”

 

Lado ya fad’i cikeda umarni wa sauran abokan nasa…

 

 

Deejo ko dukda k’arancin shekarunta ta fahimci cutar da ita suke sonyi, tana ganin Muntala ya kai mata sura ta saita allonta ta sauk’e masa a gefen kunnensa saida yaji jinsa ya d’auke ya saki k’aran azaba…. Bata jira ba tasa gudu, zaninta sai filfilawa kake, ‘yan k’afafun kawai kake hangowa….

 

Lado da Tanimu suka bi bayanta a guje, abinka da wad’anda suke buge sai gani suke tana zille masu, idan wannan yakai mata wawusa sai ta zille ta k’asan k’afarsa har saida ta had’asu gware, ta dumbuzi k’asa ta watsa masu aiko nan suka soma ihu suna lalumen hanya….

 

Ai Deejo tunda ta samu hanya take gudu bata zarce ko ina ba sai gidan Innah Balki…

 

 

Innah da Malam na zaune tsakar gida suna sauraren radio abokin hiransu zab’en dare kawai sai ji sukayi an banko k’ofa an shigo… Ai a tamanin suka mik’e suna salati, k’afafuwan Deejo kawai suka hango ta d’age labulen Innah Bilki tana fad’in “Baffah a kule k’yauren zasu shigo….”

 

“Ke Deejo lafiyarki? Su waye zasu shigon…..” Innah ta tambaya cikeda tashin hankali, Baffah kuwa cikin sauri ya fice ya nufi wajen gidan ganin su waye suka biyo Deejo amma wayam baiga kowa ba….

 

***

 

Wajajen 12am suka iso Abuja, kowa sai watsewa ake amma su Junaid basu san yanda suka nufa ba, Allah yasa Barr da yaransa basu tafi ba don dama Azeeza da yaran sosai suka sha hiransu cikin jirgin, Taheera kam ma jikin Azeeza tayi bacci…

 

Barr baiji d’ar d’in tambayansu unguwar da suka nufa ba, ganin Junaid bai basa k’wakk’waran amsa ba yasa ya nemi alfarman da su wuce gidansa gaba d’aya, da farko Junaid k’in amimcewa yayi saida Azeeza tayita masa magiya don lokaci guda soyayyan Taheera ya shiga zuciyarta…

 

Ba don Junaid yaso ba suka d’unguma gaba d’aya suka nufi gidan Barrister Nasaar

 

****

 

 

Belt d’insa ya ida d’aurawa had’i da karkata hularsa ta ‘yansanda ya zauna cif akansa kafin ya feshe jikinsa da turaruka masu k’amshi…

 

Sai faman binsa da kallo take daga yanda take zaune saman gadon k’afafu d’aya bisa d’aya har lokacin cikin kayan baccinta take….

 

“Sweet kayi kyau…..”

 

Ta fad’i tana juya idanu….

 

Gajeren murmushi yayi kafin ya k’araso ya manna mata peck gefen kumatunta yace “I’m off to work…. Idan bak’uwar taki tazo ki gaisheta….”

 

Ta kuma murmusawa tanai masa wasu salo da yasan k’arshe sai yayi lattin fita, cikin dabara ya zame ya fice ko breakfast baiyi ba, idan da sabo fita babu breakfast yabi jikinsa….

 

Yana ficewa ta koma gado tayi kwanciyarta… Kwanciyarta da kaman minti ashirin taji doorbell na k’ara…..

 

Saurin mik’ewa tayi tana mamakin har Nadiya ta iso….

 

Abinka da jik’ekk’iyar ‘yar bariki d’an mayanin rigar baccin nata kawai ta yafa ta nufi k’ofan….

 

Da murmushinta ta hangame k’ofar tana fad’in “Thanks for accepting my invitation in such a short ti…..”

 

Had’iye maganar nata tayi ganin wanda ke tsaye gabanta…..

 

Tun daga sama har k’asa yake faman binta da kallo shu’umar murmushi kwance saman fuskar sa….

 

Tsaki tayi had’i da juyawa cikin gidan tana fad’in “So tell me, what the hell brought you here…. Bance maka ina expecting bak’uwa ba….”

 

“Come on darling, no even good morning kisses sai masifa…..”

 

Ya k’arashe yana rik’ota lokaci guda ta fad’o cikin jikinsa….

 

K’ok’arin turesa take duk yanda yake sumbatan ta tana fad’in “Lamid’o stop all this, and kindly get yourself outta here…. You can’t be seen here…. Dan Allah ka tafi kafin Nadiya tazo….”

 

“Oh really darling, korata kike… So tell me mai kike shiryawa akan Nadiya….?”

 

Ya k’arashe yana k’ek’ashe idanu….

 

Shu’umin murmushi tayi had’i da dafa bayan kujera kana ta soma fad’in “I’ll win her trust and then…. Move to the next step, besides no need to rush things….”

 

Murmushi Lamid’o yayi had’i da shafa sumarsa data sha low-cut kana yace “I trust you darling… So tell me, do you need my help….?”

 

Murmushi ta kumayi kana tace “Not really….. Ka gane kawai ka tafi we talk later….”

 

“Haka zan tafi babu komai….”

 

“Ka tafi before I hate you…..”

 

Ware hannayensa yayi alamun surrender kana yace “Alright fine, zan tafi…. If you need anything just call or text OK….”

 

Gira kawai ta d’aga masa had’i da binsa da kallo har ya isa k’ofa…. Saida yakai dai-dai k’ofa kafin ya juyo had’i da huro mata kiss saman hannunsa sannan ya fice…

 

Yana ficewa ta ruf’e k’ofar ta fad’a wanka…..

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment