Littafan Hausa Novels

First Ramadan with Habibi Hausa Novel Complete

Hotunan Yadda Ake Kwanciya Da Mace
Written by Hausa_Novels

First Ramadan with Habibi Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

FIRST RAMADAN WITH HABIBI.

Heart touching story.

 

 

 

 

 

 

FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA).

 

 

 

 

TSARABAR RAMADAN.

Manzon Allah (SAW)

Ya kasance yana yin buɗa baki da ɗanyen dabino kafin yayi Sallah, idan bai sami ɗanyen dabinon ba sai ya yi da busasshe, idan kuma bai sami busasshen ba sai ya ɗan kurɓi ruwa”.

[Tirmizi].

 

 

 

 

LAMBA NA BIYU.

A tunzure HABIBI ya mara ma sirikin shi  baya ya fice zuwa Masallaci domin gabatar da sallan Ishsha,ana idarwa aka kabbara sallan Asham jin yanda idon shi ke rufewa tsabar yunwa ya sa ya fice daga masallacin kai tsaye ya nufi wani madaidaicin gurin sai da abinci,

Tambarin Sarauta Complete Hausa Novel

Layi ya bi har aka kawo kan shi sai dai yana miƙa Debit card ɗin shi domin a zari kuɗin abincin ba network, ƙoƙarin yin transfer ya yi ta cikin bankin shi na Opay da ke wayar shi nan ya nuna ya shiga amma mai gurin sam bata ga alert ba dan haka ta hana shi tafiya,abu ya haɗu ma shi goma da ishirin ganin ana niyyar karɓar abincin daga hannun shi yasa ya fizge a tsiyace ya samu gurin zama ya fara kwankwaɗar kunun tsamiyar da ya siya,sai da ya yi rabi sannan ya fara cin masan a yunwa ce ,wani irin mugun kallo ya wurga ma waiter ɗin da ke jiran alert ya ce”Matsa anan ko in barar da ke wallahi”,

 

“Ba zan matsa ba,ka bani kuɗi dan ba mu ji alert ba.”

 

“Sisi bana magani dan kin fi kowa sanin wuyar da cash yake yi kuma Bank ɗin ku ne ke da matsala dan Ni ya tafi.”

 

Da wani bank ka yi Taransifar.”ce War mai gurin,

 

“Opay”ya furta a daƙile dan ji yake yi kamar ya shaƙe su dan takaici banda shirmen da Diya ta aikata mi shi me zai sa ma har su gan shi a waje,

 

Shikenan ba damuwa ka tafi idan bai zo ba gobe za mu haɗu.”ce War Hajiyar bayan ta ga receipt na transaction ɗin,

 

Wani dogon tsaki ya ja tare da ficewa sai dai me yana isa gida ya ƙara tadda wani kayan takaicin tun daga ƙofar falo in da ya hango throw pillows a zube a ƙofar shiga, tsallake su ya yi ya ƙarasa shiga falon in da ya tadda shi yanda ya bar shi sam Diyah bata kwashe kayan abincinta ba,tsaki ya yi ya shige cikin ɗakin shi domin ya watsa ruwa sam bai bi ta kan mashirmaciyan can ba a cewar shi.

Diyah kuwa tsabar takaicin abinda ta aikata yasa ta ji yunwar cikin nata ma kan shi ya ɗauke dan haka ta rarrafa ta shige cikin group na FRWM(First Ramadan with HABIBI)janyo wayarta ta yi ganin takwas har ta gota ta san akwai labari daɗaɗa,buɗe datar ta ke da wuya ta ga akasin haka saboda dukkanin waɗanda suka aikata kalar haukarta ko mafiyin nata ma ba su ƙarke da mazajensu lafiya ba ,matsalar da ya fi jan hankalinta shi ne na aminiyarta wacce aka saketa sanadin Ramadan time-table na social media wanda ta rubuta shi a group ɗin SIRRIN YA MACE dake Facebook in da ta ce”Ina son mijina amma ya sakeni sanadiyyar na ɗauki kuɗin shi na yi siyayyar kayan ƙwalam da maƙulashe wanda na kwafo daga shafin sada zumunta,na tambaye shi kuɗin da safe ya ce bai da shi,yana fita na ɗauki Debit card ɗin shi na je na yi siyayya dan Allah ku bani shawarar yanda zan koma hide my id sister yau aurenmu ke cika sati biyu cif da aure.”

 

Ai ban ƙara sa kai ƙarashen labarin ba na koma Facebook in da na shige SIRRIN YA MACE domin karanta comments kamar yanda na saba,

 

Cikin manyan baƙi na ga an rubuta”FIRST RAMADAN WITH HABIBI”sannan aka ɗauro post ɗin aminiyarta Laila wanda yawancin matan sirri Allah ya ƙara suke mata,sai masu kareta da sunan ƙaddara ne ai kuma mene amfanin bude gidan idan har ba za su ba ma juna shawara ba,dan haka sai ƴan abi yarima asha kiɗa suka fara bata shawara nan da nan na ji wani gamsuwa ya riskeni yayinda na haɗu da shawarwarin masu hankalin da suka ba da shawara dan haka nima na ce bari in gwada ko Allah zai sa HABIBI ya canza shawarar shi a kaina,

 

Ba tare da tunanin komai ba na yi post tare da tura ma mai girma admin domin ta yi hide ɗina,nan take kowa ta posta min dan na yi sara ne akan gaba tana online kuma ganin hukuncin da HABIBI ya ɗauka akaina  na cin tuwo ta san zai ja hankali dan haka ta yi min post aikuwa na sha zagi cin mutumci iri-iri kafin nagarin suka fara bani shawara,

 

Jin yanda idona ke min nauyi yasa na ajiye wayar a gefe sai dai ina rufe ido wani irin yunwa ya tasoni gaba dan haka dole na tashi a firgice tare da shigewa cikin kicin,

 

Haɗa shayi na yi tare da zabga Milo tunda madararmu ta ƙare,na sa sugar madaidaici tare da ɗaukan biredi da bota,sam yunwar ta rufe idona sam ban san da wanzuwar HABIBI a cikin madafar ba yana wanke kajin da na cika ma spices da yaji a gaban sink(Aikin Kwamared)

 

Har sai da naji ya ruƙo biredi da shayin cikin haɗe fuska ya ce”To be sencere ba zaki sha shayin nan ba almubazzara.”

 

Ganin yanda ya yi maganan yasa na san he is serious dan haka cikin kuka na ce”Ni yunwa zata kasheni wayyo Ammina,ka bani ko in ƙirata Billah.”

 

Wata muguwar harara ya doka min tare da komawa kan aikin shi na dirzan kaza da soson da yake yi duk kalar da na jibga mata ta fita,

 

Dariya ce ta so suɓuce min sai dai murɗawan da cikina ya yi yasa na fashe mi shi da kuka,cikin zafin nama ya damƙo hannuna tare da nuna min Iranian rice ɗin da na musu ya ce”Zo ki ci wannan in dai yunwa kike ji ko in maki bugun sakwara.”

 

Ɗebowa na yi na kai bakina jin yanda shinkafar ta yi zaƙo-zaƙo tare da kayan haɗin na cabbage karas,green beans,da su gurjin yasa na haɗiyeshi da ƙyar nan da nan wani tari ya turniƙeni HABIBI ya yi saurin miƙo min ruwa a cewar “Bai gama fanshe kuɗin da ya kashe ba na aurena dan haka in na mutu na cuce shi.”

 

Sai da tarin ya lafa sannan na ce”Ba zan iya cin wannan abincin ba mai kama dana ƴan fursin wallahi haba wannan wani irin gwale-gwale ne?.”

 

“Mu ɗin bayin gidanku ne da za ki bamu abincin nan ko fursunonin ki ne?”

 

“Eh fursunonina ne”na faɗi hakan a cikin zuciyata sai dai a fili ce wa na yi”A’a HABIBI ka yi haƙuri Ni fa da niyar kyautatawa na yi maku wallahi amma ka ga alhairi na shirin zamar min sharri.”

 

Harara ya banka mata ka fin ya ce”Wa ya koya miki wannan girkin mahaukatan?”Ya mata tambayar a harzuƙe dan ya san DIYAH ɗin sa ta iya girke-girken alfarma to mai yasa a wannan karon za ta kunyata shi.

 

A Tiktok na ga wata Chief ta ɗaura,sunan shi kawai ya ja hankalina na sauke shi a kan wayata kuma musamman na tanaje shi sai a farkon watan Ramadan dan in burgeka da shi HABIBINA.

 

 

Tiktok……..

 

 

 

 

More comments

More Typing..

 

 

 

 

Ummu-jidda.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment