Littafan Hausa Novels

Fatima Bintu Hausa Novel Complete

Sirrin Doguwar Mace
Written by Hausa_Novels

Fatima Bintu Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Fatima Bintu Hausa Novel Complete

Fatima BINTU

 

Page 14

 

 

Story and writing by

(Mom yasmin)

 

 

…..kafin ta dan na kiran yace “shi kenan jarabbebiya muje toilet din, five minutes ne ya daukesu wankan, sannan shima yafito ya Kara gyara kansa, sannan ya dau car key dinsa ya fice, baba mai gadi yana ganinsa yayi sauri ya bude gate din da sauri, bayan ya fita ya tsaya a bakin titi ya fara dialing din number fatima BINTU, bugu biyu ta dauka, daga can tace” assalamu alaikum “yace” wa,alaikum salam “dan shiru su kayi kafin salis yayi karfin halin cewa” kina lfy “amsa tabashi da eh, sannan tace, amma ban gane mai magana ba? cewa yayi” ok bikiyi saving din number ba kenan, to ki canka da kanki, “kit ya katse kiran ,tunani ta farayi to waye wannan, nasan dai ba Ahmad bane tunda nayi saving din tashi to kode, yaya salis ne, amma kuma kamar muryarsa kai shine ma zai rainan hankali” haka dai taita sambatu sannan ta ajiye wayar

 

minti talatin ne ya kawo shi gidansu fatima, yaro yasa yace yashiga yace ana sallama da fatima, koda ya shiga a tsakar gida ya sameta tana shara, hijjab ta dauka tafito,

Mr Bello Hausa Novel Complete

 

daram!daram!!kirjin ta yafara luguden bugu, kallan ta yayi sama da kasa, sannan yace “ko biki farin cikin gani nabane?” tace “nayi” yace “ai banga alama ba” fatima dai tayi shiru batace komaiba, sai daga can yace “inna tana nan” da mamaki ta dago ta kalleshi jin abinda yace wai inna ta na nan? Slowly ta bashi amsa “e..h”yace” ok”jeki kice zan shigo na gaisheta “tace” tom”

 

a bakin gado tasameta tana gyagyara dakin “tace” inna wai yaya salis zai gaisheki “tace” to maza kice ya shigo kin barshi a tsaye cikin rana “ita dai fatima mamaki ya isheta ganin wannan lamari, inna sai washe baki take

 

ajikin mota ta sameshi a tsaye tace” wai ka shigo ”

 

tabarma aka shunfida masa a tsakar gidan wanda yake da siminti anshareshi yayi fess dashi, zama yayi ya gaisheta cikin girmamawa, inna ce tace “fatima jeki gidan su hauwa, tunda itama tana zuwa, ki kaimata ziyara” to tace tatashi, amma tasan kawai korarta ake sanyi, tunda ita yanzu ba fita take ba

 

 

ajiyar zuciya inna ta,sauke sannan ta kalli salis tace “d’ana yanzu ya ake ciki ne” salis ya nunfasa sannan yace “aure na dai way’anda suka Sani iyaye nane da kanwata, amma ita kanta naimat din bata Sani ba gaskiya”, harma da mahaifita,da mahaifiyarta umma duk busu Sani ba

Inna tace” to kana ganin babu matsala “salis” eh babu mahaifina ya amince harma da mahaifiya ta”su wayancan ba matsala bane

acan Kaduna anan nayi binciken dan gin mahaifin nata, kuma k’aninsa malam dauda shi yazama wakili

 

 

TIR KASHI!!!!!!!

 

fatima BINTU matsayin kishiyar naimat maga yadda zamansu zai kasance, a Inuwa daya!!!!

 

ni taku a kullum mom yasmin

 

 

more comments more typing

 

 

 

 

Fatima BINTU

 

Story and writing by(mom yasmin)

 

 

Page 15

 

….inna tace “to masha Allah yanzu yaushe zata tare?” salis yace “nan da wata biyu insha Allah, sannan inaso muje gurin dangin mahaifinta,” inna tace “da nayi alkawarin yadda suka watsar damu bazamu k’ara kulasu ba, amma saboda halaccin da kayi mana bazan iya cewa a,a ba,Allah yakaimu lokacin idan ta tare sai kuje din,allah yayi maka albarka” salis ya sunkuyar da kansa kasa yace “amin,amin”

 

dubu dari ya ciro ya ajiye akan tabarma yace “gashi ayi wani abun,kafin nikuma dawowa” inna tace “ba,a gajiya” yace”bakomai inna

 

daga haka sukayi sallama, ya fice daga gidan,… ahanya suka had’u da ita, parking yayi, sannan yace “BINTU!mamaki ne yacikata domin ita bata taba zaton ma yasan sunanta ba, yadda yakirata kamar shi ya rada mata sunan

 

Yace” ina kikaje tace gidansu hauwa “yace” banasan yawo kinji mai nace “tace” eh,, “ina Ahmad yana zuwa?” Tace “da yana zuwa amma yanzu yadade baizoba, ko nakirashi ma baya dauka” aransa yace yaji warning dina kenan, amma a zahiri cewa yayi “wato harma kiransa kikeyi kenan”, maza kiwuce kibani guri” nan da nan mood dinsa yacanza, ita kuwa kasa tayi da idonta, aranta tace “daga cewa nakirashi sai yayi min tsawa lalle ma yy salis dinnan

 

 

Bayan sati daya>>>>>>>>>

 

 

Naimat ce da nadiya a baje a palour sunata hira suna shewa” kinsanme kawas idan kikayi using da maganin nan zakisha mamaki ,sai sanda kika ga dama zaki haihu, amma yanzu ai sai ki tsofe kizama inna rajab, “naimat tace” amma nadiya kina ganin babu matsala, gwara dai na fadawa umma tukunna “nadiya tayi sauri tace” haba besty ,sai kace biki yarda dani ba, aiba saikin fadamata ba, kinsan irin wahalar da nayi kafin nasamo maganin nan kuwa duk dan saboda dake”naimat tayi murmushi tace”ai nasan nadiya kina sona, kina support dina a komai, to yanzu yaushe zansha maganin?”nadiya tace “yanzu mana” naimat ta b’alle murfin kwalbar ta shanye yeshi duu,wani shegen kallo nadiya ta watsa mata sannan tace “yunwa nakeji ko abinci banciba na fito daga gida”

“Ok,bara na tashi na dora mana, ko jallof rice ce”

 

Kinsan me kuwa, “nadiya tace” a,a”

“Mutumin naki ko breakfast bai yiba yafita, Niko nace tafi nono fari” nadiya tace “yauwa haka zaki dinga yimasa”

 

 

 

More comments more typing

 

 

Fatima BINTU

 

Story and writing by

(Mom yasm)

 

 

Page 16

 

…”amma fa umma tace nadaina yimai haka “nadiya tace” idan kika daka ta ummanki rainaki zaiyi wllh”

 

…..

 

Salis ne zaune a palour, feenat tana []are masa []wai zai ci da shinkafa, bayan ta kammala ta ajiye masa agabansa, sannan ta koma ta zauna, ummi ce tafito daga bedroom dinta ta zauna akan kujera, salis yace “ummi ina kwana” ummi tace “lfy lau, ya naimat din” salis yace “tana lfy” ummi takuma gyara zama sannan tace “ina ganin son, a []aga tariyar nan, wata daya ai yayi sauri “salis yace “ai munyi magana da mahaifiyarta, na tsaida wata biyu” ummi tace “yauwa hakan yafi, saboda kaga baka dade da wani auran ba, allah yasa hakan shine mafi alkairi”” amin ummi ”

 

 

saida ya kammala breakfast dinsa tass sannan ya nufi bangaren dady, (mahaufinsa kenan)

 

feenat ce ta dawo kusa da kujerar ummi, kallanta tayi tace “ummi wllh anty naimat bata kula da yaya kwata ,kwata kalli fa yanzu fa, anan yake break fast, lunch kuma sai dai yayi take away,”

 

“Nasani feenat, dan uwanki yana cikin damuwa, shiyasa ma na amince da auran tun wuri, gwara ya zauna da mata biyu, ita kuma naimat sai yayi hakuri da ita gudun lalacewar zumunci”

 

Feenat tace “nima shiyasa na keta Allah,Allah, fatima ta tare”

 

 

GIDANSU FATIMA

 

inna ce zaune tana yiwa fatima nasiha akan auran da aka daura mata sati daya da suka wuce, domin daurin auran salis da naimat, harda fatima aciki, hawaye ne yake ta zarya akan kyakkyawar fuskarta ta fulani, ita tarasa wani mood take ciki sad or happy, tasani tanasan yaya salis so bana wasa ba, tun haduwar farko da yaje school dinsu dakko zaliha, amma tana tunani wani irin zama zasuyi da naimat, saboda tasan tun asali naimat ta tsaneta, ballantana yanzu da ta zama kishiyar ta

 

 

[]ago da kanta inna tayi tace “ya isa haka fatima, kar kanki yayi ciwo mana, tun da nafara maganar auranki kike kuka, ko bakya San salis dinne, idan bakya sanshi sai sauwa[]e miki, ba za aimiki auren dole ba”

 

fatima tace “a,a inna inasansa, amma shi yana sona,?” inna tayi dariya sannan tace “in banda abinki nafada miki duk wannan hidimar da kika gani shi yayi mana ita, to idan baya sanki zai miki hakane” sunkuyar da kanta []asa tayi alamun kunya, sannan tace “inna yau mai zamuci?” inna tace “mudafa []an wake kawai” fatima tace “yauwa inna ai kuwa ina San []an wake, bara na kwaba fulawar,” inna tace “yauwa yar albarka”

 

….

 

kwana cassa,in suke kallo a tashar arewa 24,gaba daya sunbada a tension, suna ta zura jellop rice a bakunansu, babu abinda kake ji sai karar TV, dana spoon, duk sun hargitsa palourn kamar bana amarya ba, tun shigowarsa yake ta kwa[]a sallama, amma inah sunkure volume, idan tane yakai kansa yana haurawa upstairs, da sauri ta zabura ta kalli nadiya tace “tayani kallo, kinga yaushe yadawo” nadiya tace “ina zansani hankalina yana kan tv” naimat tace “bara naje ina zuwa” nadiya tace “ok,sai kin dawo” sai da taga tajuya baya sannan ta bita da harara, harda su kwafa

 

 

akwance tasa meshi, akan gado yayi rigin gine, zama tayi kusa dashi, tace “habibi yaushe yadawo?” bazan yayi mata ,ko kallanta bai yiba ,cewa tayi naga duk ka gaji ko nayi maka tausa? wani kallan tsana ya watsa mata sannan yace “kullum, yarinyar nan sai ta zo gidan nan, to daga yau, wallahi kinji na rantse takara zuwar min gida sai dai kutafi tare da ita”

 

Zumbur tayi ta mike tare da zaro ido tace”bangane ba!!!!!!!

 

 

 

 

More comments more typing

 

 

 

Story and writing by

(Mom yasmin)

 

 

da sauri tafito daga bedroom din tanufi, inda nadiya take a zaune tana kallo, saurin dagowa tayi tare da kallanta tace”lfyarki naga kin wani sakko asukwane?”naimat tace “ba dole ki ganni haka ba, kinsan meyace,!” Nadiya tace “a,a” naimat tace “wai idan kika kuma zuwa gidan nan sai dai mutafi tare dake” aranta nadiya tace anzo dai dai gurin kenan,amma a zahiri sai tayi zumbur ta mike tare da fadin “nashiga uku na lalace, to meyake nufi kenan kawas?”.. To nidai gaskiya bara na tashi na tafi, haka kurum ina zaman zamana, daman na lura salis ya tsaneni, tafada tareda fashewa da kuka (niko nace kunji makira)..jikin naimat ne yayi sanyi ganin yadda nadiya take ta fama zubda hawaye, kallanta tayi tace” kinga nadiya, ai wallahi salis yayi ka[]an yace zai rabamu, kedai kawai yanzu ki tashi ki tafi gida, zamuyi waya “share hawayenta tayi tace” to nidai yanzu zubaman ragowar abincin a food flask intafi dashi gida, tunda waccan mutumun yakoreni, ai infadamiki naimat bai dace dake ba “saurin dakatar da ita naimat tayi tace” haba nadiya, kalleshi kikara kallansa ai wallahi salis ya hadu ga kyau, ga kudi ga class, duk inda namiji yahadu to salis yake “saurin canza chapter tayi ganin zata dago jirginta tace” yi sauri ki zubamin inyi gaba, dan na lura kema sokike intafi, ”

 

 

acan bedroom kuwa, yayinda su naimat suna kasa suna hira, shikuma ogan,yana nan yana waya da masoyiyarsa,, fatima, “kinyi shiru ko ba kyaso a kije kadunan” daga can tace inaso mana, ai ni bantaba ma zuwa ba, “yace” ko “tace” sosaima”yace, “llove you fatima bintu” shiru tayi bata bashi amsa ba, sai da suka dauki yan minute haka sannan ya nunfasa tare da cewa “kinyi shiru” daga can tace “,llove you too, my soulmate” wani irin farin cikine ya ziyarci zuciyarsa, sai yaji ma duk,damuwar daya ke cikima ta kau ,cewa yayi “kuma fadar sunan karshe inji” awani irin salo tafada Wanda ita kanta bata masan ta iyaba, saboda tsabar shaukin soyayya tace “soul…mateee” yace nikuma haka zandinga cemiki “heartbeat” daga can tace “thank you

 

 

Umma ce zaune akan kujera tana cin abinci,” oh ni yarinyar nan naimat ko ya ake ciki yanzu, oho, nace fa takirani ,kuma haryanzu shiru “abba ne dayaa fito daga wanka yace” maganar me kike hakane? “tace” nida yarka ne mana, nace takirani amma har yanzu shiru, bara dai ni nakirata, waya ta dauka, abba ya dakatar da ita da cewa “karki kirata ko kin manta amaryace yanzu, keda kikaci amarcinki,waya ta kuramiki” dariya tayi tace “kai alhaji,baka da dama” yace “ai gaskiya ne, bara naje []angaren waccar naga suna lfy” nan take ta hade rai tace “suna lfy mana alhaji ba gashi yanzu zaliha tazo ta wuce ba, ai da koshin lfy kaganta” nan jikin sa yafara rawa ganin ranta ya baci yace “ya hakuri my love tuba nake, yanzu dai bara na zauna ki ta kallo na kinajin dadi”

 

 

banko kofar gidan tayi tare da kunduma ashar “lallema naimat wllh bazan taba barinki ki zauna lfy a gidan auran kiba, ni ina gantali a unguwa ke kuma kina gidan miji, mijin ma irin Wanda nake da burin aure, kuma wllh sai na shiga gidanki a matsayin kishiyar ki, wannan alkawari nayi wa,kaina” larai mahaifiyartace,tace “ke da wa kuma nadiya?” Nadiya tace “daga gidan yar masu kudin can nake naimat wacce muka hadu a WhatsApp group,wai shine mijin ta yace nadaina zuwa gidan, kuma ta hanyar ne zan hanasu zaman lafiya!!!!

 

 

 

More comments more typing

 

 

 

Fatima BINTU

 

Story and writing by (mom yasmin)

 

 

 

Page 18

 

 

….cewa abba yayi “to ranki ya dade, angama kallan nawa ko haryanzu da saura?” tabe baki umma tayi kana tace, “alhaji kenan nayi maka uzuri tunda kafi wata bakaje gurinsu ba, amma karka dade” abba yace”to ranki yadade godiya nake “sannan yatashi yafita da sauri bai zame ko inaba sai part din momy

 

 

Momy ce zaune itada kanwarta suna hira, kallanta tayi wacce ake kira da saude tace” gaskiya mijinki baya kyautawa ace matanka biyu amma baka, sauke hakkin daya daga ciki, mata duk tabi ta asirceshi, ke kina zaune sai abinda tace “momy tace” karki ce haka saude ai gaskiyar mutum bata karewa sai dai ace karya takare, kuma duk abinda takeyi insha Allah zai fito fili kowa yagani “saude tace” aida shi salis din, mahaufinsa da zaliha yace a hadasu, amma matar nan sai da tayi kutun gwilar da yarta ta auri salis,gashi ai yakuma wani auran, ita bata saniba ba ,kuma kawar zaliha din “momy tace” kedai kawai Allah ya kyauta “sallamar abba ce takatse musu hirar tasu, guri ya samu ya zauna sannan yace” Hajiya saude Ashe kece tafe “saude tace” eh wllh nice ya gida “abba yace” lfy lau “kallan momy yayi ba yabo ba fallasa yace” ina zaliha? “Momy tace” tana dakinta “yace” ok,nazata ta tafi yawone domin sarauniya tace min yanzu tafiya yawo “tabe baki momy tayi, sannan tace Allah ya kyauta, tashi yayi tare da fadin” bara naje kar nayi lefi dan yanzuma da kyar aka barni na taho ”

 

 

Saude tace “amma kina ganin abin takaici, yanzu kina zaune ake miki haka, gaskiya kitashi tsayi abu kamar wasa har yana nema ya wuce iri”

 

 

 

WASHE GARI

 

 

salis ne zaune akan dining table yana breakfast,indomie ce yake ci, wacca naimat ta jagwal gwala ta dafa, kadan yaci yatashi dan ji yake zuciyarsa zata tashi, fitowa tayi sanye da kayan bacci ajikinta, tace “ashe har kashirya” tashi yayi yasa hannu a pocket dinsa ya dakko 1k,yace “gashi ko zaki bukaci wani abu” karba tayi tace “thanks” shikuma yafice

 

Waya ta dakko takira nadiya tace “kizo yafita, amma kafin yadawo sai ki tafi!

 

 

Kuyi hakuri da typing kadan inada uzuri ne

 

 

More comments more typing

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment