Littafan Hausa Novels

Farar Haihuwa Complete Hausa Novels

Written by Hausa_Novels

Farar Haihuwa Complete Hausa Novels

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Farar Haihuwa Complete Hausa Novels

Mal yakubu ya fito ya gaishe da Alh Sulaiman

sannan ya gabatar da kansa. Alh Sulaiman yayi

masa bayanin wurin da filayen suke ya kuma

bukaci yazo kamfani ya same shi washegari.

Ihun da suka ji yasa su yin shiru Dijengala ta fito

da gudu tana kuka. Murya can sama tace Baba

kaga Mama ta hanani wanka yau ma wai zan

karar da ruwa. Kaji yadda nake tsami

kuwa…matsawa tayi gabansa tana daga masa

hannuwanta har gashin hammata Alh Sulaiman

yana gani. Kuma fa jinin wata na yazo tun jiya .

Subhanallahi Dije sauke hannun mana ya kama

hannunta zai koma cin gidan da ita. Tirjewa tayi

Baba dukana fa zata yi kuma kullum Yaya Hanan

tana yi da Zaliha. Duk kunya ta kamashi ya daga

murya don taji abinda yake fada…muje nace zan

mata magana. Burinsa kawai su koma cikin gida.

Sai lokacin taga mutane tsaye…lahh baba

modibbo sannu da zuwa. Sai ta rike baki au…duk

kunji abinda na fada ko? Wayyo kunya ta dafe kai

tare da komawa cikin gida. Alh Sulaiman kuwa

dariya ce ta kwace masa ganin yadda Dije take

baragada a gabansu. Sai dai fa akwai wari dan

kare.

 

FARAR HAIHUWA              17

Wani murmushin ya sake yi shi kadai Umma ta

jefe shi da pillow din kujera kai ni dariyar me

kake yi kamar kwancen hauka….wata dariyar ya

sake yi sannan ya bata labarin Dijengala kurma.

Itama dariyar tayi maimakon ka taimaka mata

shine kake dariya. Ni mubar wannan zancen dai

ya sunan yarinyar da kayi min zancenta ne? Ga

mamakinsa sai yaji yace Hanan.

Daren ranar tunaninta ya rinka yi. Tana da kyau

mai daukar hankali gashi da gani tana da tsafta

ba kamar Dijengala ba. Wani murmushin ya sake

yi da ya tuno yadda take magana. Daga nan har

yayi bacci tunaninsa yana kan Dije yana dariya.

Ranar litinin duk ya kagu modibbo ya iso. Yana

zuwa kuwa tambayarsa tayi ko anyiwa Hanan

miji. Modibbo yadan yi turus…Hanan dai yar

abokinsa ce amma ko kadan bata da hali. Ranka

ya dade ba ayi mata miji ba a iya sanina. To ka

sanar da mahaifinta idan ya amince zan nemi

aurenta. Modibbo ya nuna farincikinsa a fili

amma ba don yadda Dije ta tashi ba sai shirme

da shiririta ga lalurar kurumta da ita zai so

Alhajin ya nema.

 

Gidan Uncle Hausa Novel

*******************

Rana duk ta dami Hanan a kofar banki inda take

jiran kawarta. Wata mota take ta kallo, ba

karamin kyau tayi mata ba…duk mai motar nan

ko ba’a fada ba mai kudi ne kuma mai kyau. Tayi

dan tsaki ita kyau ma bai dameta ba indai akwai

kudi. Tana zaune a wurin wani matashi ya fito ya

bude motar. Gaba daya ya tafi da hankaliñta ta

bishi da ido. Kana ganinsa kaga kudi don yawan

shige shigenta tana gane mai kudi tana gane

yaron mai kudi. Wannan matashin kam shine da

kudin. Tashi tayi ta kade skirt dinta tayi saurin

zuwa gaban motar inda yake shirin rufe kofa

tace Alhaji kwana biyu. Ya dan dago kai a dakile

yace ya kin sanni ne? Tayi baya yi hakuri sai

naga kamar wani da na sani ne. Sai kashe murya

take tana magana ciki ciki. Ya bata rai bashi

bane to…matsa na rufe kofar. Kafin ta gama

matsawa ya bugeta da kofar ya figi motarsa.

Kafin ya bace ta gama haddace numbar

motarsa.

 

 

FARAR HAIHUWA              18

Kawarta Hajara ce ta fito jaka cike da kudi. Sorry

Hanan na barki jira ko? Gaskiya da mita zan miki

amma na fasa. Wani kamu nayi mai kauri. Hajara

tace haba a yana ina? Hanan ta fada mata yadda

suka yi. Amma zancen gaskiya kawata yayi min

akwai kudi. Ji nayi kamar kudin jikinsa yana

kirana. Shegiya uwar son kudi nasan wannan mai

cangala kafar zaki kaiwa. Allah sarki innata tafi

kowa kaunata. Ni ba wannan ba Hajara ki rakani

gidan Babba mana. Akan mutumin nan sai anyi

aiki.

 

 

Dayake halinsu yazo daya shiyasa kullum a

makaranta tare suke. Hajara da Hanan suka

wuce gidan Babba wani malamin tsibbu. Don

yanzu bin malamai harda yan mata. Allah Ya

kara shirya mu. Bayan dukkan bayani Babba yace

Hanan kin san sunansa? A’a amma ga numbar

motarsa, ka taba yi min aiki akan wannan wawan

malamin da numbar waya ai. Ba damuwa Hanan

ga wanan turaren ki saka kan garwashi sai ki

rubuta numbar motar a takaddu goma ki rinka

dorawa akan wutar har su cinye duka. Sai ki

lazumci zuwa wurin da kuka hadu na kwana

goma. Idan baki ganshi ba to motar ba tasa

bace. Godiya tayi sosai tace idan ciniki ya fada

zaka ganni.

 

Bayan kwana uku Modibbo ya sanar da Mal

Yakubu bukatar Alh Sulaiman. Murnarsa bazata

misaltu ba ya sanar da Uwale. Burinshi dama

tayi aure ya gaji da sintirin da samari ke yi masa

a kofar gida. Sabuwa ma tayi murna har ta sanar

da babarta Zulai. Cikin dare ta bawa mijinta

shawarar ya aurar da Dijengala. Banda abinki

Sabuwa ina Dije take da saurayi. Tayi wani

murmushin keta…wani kurma ne dan uwan

Zainab makociyarmu. Tace a kauyensu yake

Kura. Hade rai yayi dakata malama ni ‘yata bata

gama kurmancewa ba kinji ko. Ki rike abinki

rabonta na tafe. Kuma dama ina son yi miki

magana Allah ranar da kika sake hanata ruwan

wanka zaku yini a gidan nan ba ruwa. Yar hirar

tuni ta watse ya juya yayi kwanciyarsa.

 

Gari na wayewa cike da zumudi Uwale ta sanar

da Hanan zancen Sulaiman. Ta wani harareta

jiya tasha uban hayaki akan wani yau a kawo

mata zancen wani Alh Sulaiman. Kinga Inna ki

bar maganar nan ina da wani. Haba Hannan

mutumin nan fa kudi gareshi sosai. Mafarkina a

kanki ne zai tabbata. Hanan ta wuce zata shiga

wanka. Kinga Inna ki bar maganar nan ku bashi

Dijengala ko Zaliha. Auzubillah uwale ta fada

tana tofar da yawu. Dije ai ai musaki irinta.

Yarinya ga baki ga muni.

 

FARAR HAIHUWA              19

Hanan tayi sati daya tana zuwa bankin da suka je

da Hajara tun safe har sai sun tashi amma mai

motar bai dawo ba. Rai a bace ta koma gida duk

ta kusa gama kashe kudin hannunta a hawa

motar zuwa banki.

 

Dakinsu ta shiga zata cire kayanta tayi wanka

Dije ta shigo tana waka da karfi. Hakan ya kara

batawa Hanan rai ke rufa min baki banza kawai.

Ta fice tana tsaki. Babanta ta gani a kofar

kitchen yana magana da Sabuwa…yauwa zo

hanan dama zancenki muke yi. Ta turo baki

gaba ta karasa gabansa ta tsaya. Nasan an fada

miki maganar Alh Sulaiman ko. Wanda kuke aikin

gini dashi baba? Eh ya amsa mata. A zuci tace

tabdi magini zan aura? Allah Ya kiyaye, itama

Mama tsautsayi ya kawota gidan nan. Mal

yakubu yace dama tafiya ce ta kamashi amma ya

dawo zai zo yau da daddare inji modibbo. Uhmm

tace ta wuce bandaki. Wallahi bazai sameta a

gida ba ma. Me zatayi da talaka.

 

Haj Bintu tana ta kallon yadda Sulaiman ke shirin

fita daga dawowarsa ko abinci bai ci ba. Ina zaka

ne don nasan wannan shigar bata zaman gida

bace. Hular hannunsa ya gyara Umma gidansu

Hanan zani amma da Ammar zan tafi saboda zan

kaishi aski. Wato ka dawo zaka nuna min ban iya

kular maka da danka ba ko? Yana dariya ya bata

hakuri. To ina tsarabarta ko haka zaka tafi? Mata

fa sai da ihsani. Zan biya na siyo wani abun a

hanya. Hannun Ammar ya kama suka tafi yana ta

yi masa hira.

 

Hanan ta rasa yadda zata yi ta fice daga gidansu

tunda babanta yaki fita tun safe. In ba rashin

aikin yi ba kakkarfan mutum kamarsa ya zauna a

gida wuni guda….tayi tsaki. Zaliha tace lafiya.

Hararar ta tayi ban sani ba ta bata amsa tare da

fita daga dakin. Mal Yakubu na fita zuwa

masallaci sallar magriba ta fice ba tare da sanin

kowa ba.

 

Alh Sulaiman yana dosar gidan ya fara jin warin

kwatar kofar gidan. Shifa harkar warin nan baya

kaunarta. Ya rasa dan aike gashi bashi da

numbar wayar kowa a gidan.Ammar ya tura ciki

ya sanar da zuwansa. Yaro ya shiga kai tsaye

dakin da ya hango haske ya nufa. Uwale ce da

Sabuwa suke kallo yace salamu alaikum wai

daddy na yace ya zo. Sabuwa ta kalli dan

kyakkyawan yaron kai kuma daga ina wa ya turo

ka? Mal Yakubu ya shigo yace dan Alh Sulaiman

ne mai son Hanan. Kirata Sabuwa yana jirantaa

soro.

 

FARAR HAIHUWA              20

Sau uku ta kira taji shiru. A zaune ta tarar da

Dije tana gyangyadi kafin Zaliha ta dauko musu

tuwo. Shureta tayi da kafa ke kurma tashi…a

firgice ta tashi tace mama me ya faru? Ta

dungure mata kai tare da rage murya ubanki ne

ya faru. Dije ta bata fuska tana nuna kirjinta

ubana? Ubana?? Sai hawaye…ke yi min shiru

munafuka ana magana sai kiyi ta kallon bakin

mutane ina Hanan? Dije tace ta fita tun dazu.

Kai yarinyar nan zata ja min masifa ta koma daki

ta fadaw Mal yakubu.

 

Ransa yayi matukar baci gashi yar wayar tasa

ma ba kudi bare ya kirata. Uwale tace yarinyar

nan neman tona min asiri take ga wayata kirata.

A kashe suka ji wayar. Bari na fada masa kawai

,ita kuma yau tamu ce ni da ita.

 

Jin Zaliha bata dawo daga dauko musu tuwo ba

Dijengala ta duba kitchen bata ganta ba ga

yunwa yana cinta. Ita kuwa Zaliha cikinta ne ya

kada ta tafi bandaki. Wata tsohuwar naira ashirin

ta dauko a kasan akwatinta ta saci jiki zata je

siyan wainar fulawa a gidan Zainab makociyarsu.

Tana saka kafarta a soron aka dauke wuta,

saboda duhu hannunta take mikawa kamar

makauniya tana neman hanyar fita, wani

mulmulallen abu mai dan gashi gashi taji ta

shafa ta tabbatar ba kan daya daga tumakin

Sabuwa bane. Ammar data tabawa kai ihu ya

saka. Daddy kamani naji an taba min kai.

 

Sulaiman yace ina zuwa Ammar wayata nake

nema. Dije sake taba kan tayi don ta tabbatar da

abinda ta taba, gashi tana jin kamar maganganu

amma ta kasa gane me ake fada. Ihu tasa iya

karfinta wayyo Allah baba nayi gamo. Sulaiman

tuni ya gano muryar yar kazamar yarinyar nan

yace ke rufa mana baki yana neman hannun

Ammar su fita. Ta soma kuka Al’Quran naira

ashirin ce a hannuna waina fulawa zan siyo a

gidan Zainab yunwa nake ji. Gashi don Allah

kada ku mayar dani kaza ko doya. Ba shiri

sulaiman ya soma dariya…hannun dansa ya

kama. Yana jin yadda Dijengala take tsalle da

ihu. Mal Yakubu ne ya iso soron da yar fitila.

Shima bai kula da su Sulaiman ba don ya zata

sun tafi. Dije dena ihu nine…tana ganinsa tayi

saurin matsawa kusa dashi tana magana da karfi,

baba aljanu ne suke son bude min ido, dansu

suka turo min shegu. Kul kike zagi dije…shima

baba zuciyarsa ta kusa bugawa daya ji ance

daddy mu tafi. Sai a hankali ya gane Alh

Sulaiman ne da dansa.

 

FARAR HAIHUWA              21

Da kyar ya iya tsayar da dariyarsa yace Mal ‘yar

nan taka tana da abin dariya. Ai nima na tsorata

don nayi tunanin kun tafi. Ammar ya nuna

takalminsa ne ya kwance na tsaya daure masa

sai aka dauke wutar kuma ina tunanin wayata

tana mota. Sake sallama suka yi kafin Sulaiman

ya gama fita yaji mal yakubu yana tambayarta

ina zata.. wallahi baba yunwa ce kuma zaliha

bata kawo abincin ba, dama wainar fulawa zan

siyo ta ashirin. Dariya yayi haba Dije wainar

ashirin ai sai da kiyi kuskurar baki da ita. Me

kace baba? Banji ba. Muje na baki nawa abincin

kici a daki kada sabuwa ta gani. Daddy mu tafi

mana wari nan. Sai a lokacin sulaiman ya dawo

hankalinsa yaja hannun Ammar suka fita bakin

layin inda yayi parking motarsa.

 

 

****************

Ashir ya rasa abinda ke masa dadi. Tun

washegarin zuwansa banki zuciyarsa ke masa

radadi ya rasa dalili. Ji yake kamar ya koma

bankin ya nemi yarinyar da ta yi masa magana

amma shi ko fuskarta ma bazai iya tunawa ba

don bai kalleta da kyau ba. Wata biyu ya rage

bikinsa amma yan kwanakin nan baya son ko jin

sunan matar da zai aura. Dama dai auren baya

gabansa don shine na uku ma. ba ya dadewa da

mata suke rabuwa, hakan na damun yan uwansa

shiyasa wannan karon babansa ya yanke

shawarar hada shi da yar kaninsa da mijinta ya

rasu shekaru shida da suka wuce, wato sakina

mahaifiyar Ammar. Gidansu Ashir suna da rufin

asiri dai dai gwarwado. Lokacin da ya fara aikin

kwangila ga aikin office shine kudi suka zauna

masa sosai. Kasa nutsuwa yayi karshe ya yanke

shawarar zuwa bankin a daren bayan yayi

magriba a kofar gidansu.

 

Hanan na sauka daga adaidaita sahu suka hada

ido da mutumin da take ta nema. Gabansa ne ya

fadi yana ganinta. Banda kyawunta wani yanayi

ya shiga mai wutar fassara. Idan bai auri yarinyar

nan ba rayuwarsa tana cikin matsala. Har wani

gumi ke keto masa. Karasawa yayi inda take ba

tare da yayi mata magana ba ya mikawa dan

sahu dubu daya yace mata zo mu karasa bakin

motata. Ba musu ta bishi…lallai aikin Babba yayi

kyau.

 

FARAR HAIHUWA              22

Bude mata yayi ta zauna a seat din gaba. Shima

yana zama yace me ya fito dake a daren nan? Ta

rausayar da kai tana kare masa kallo, ga kyau ga

kudi.ready made kenan..kai ya kamata nayiwa

wannan tambayar. Hmm ina jin abinda ya fito

dani ne ya fito dake. Me kenan ta tambayeshi

ciki da jindadi. Yana kallonta yace tunaninki

mana. Duk kin hanani sakat…ina tunanin kema

hakan take a wurinki. Ni fa kudi nazo dauka ba

wurinka nazo ba. To fitar min daga mota indai

hakane. Tsoron kada garin jan aji ta rasa shi

yasa tayi saurin cewa wasa nake maka. Nima ka

hanani nutsuwa tun ranar da muka hadu. Yaji

dadin amsarta…ni sunana Ashir Sani. Ina aiki a

NNPC sannan ina harkar kwangila sosai. A

takaice dai i am a very busy man. Ina ruwanta

da yawan aikinsa indai akwai kudi. Ta fada masa

nata sunan daga nan hira suka rinka yi kamar

sun dade da juna. Ganin tara ta wuce yace muje

na kaiki gida.

 

Alh Sulaiman na fitowa daga layin gidansu Hanan

ya hangota cikin motar wani. Ina taje a daren

nan ya tambayi kansa. Motar na kara matsowa

yaga kamar yasan mai tukin amma ya kasa tuna

ko waye. Bai kawo komai a ransa ba ya tafi gida.

Cikin sati biyu soyayya ta kullu sosai tsakanin

Ashir da Hanan. Ta sanar da uwale da sabuwa

komai game dashi. Tuni ta sace zukatansu bare

da suka ga irin hidimar da yake mata. Mal

Yakubu dai ya nuna rashin amincewarsa. A

cewarsa bazasu mayar dashi karamin mutum ba.

Ya riga ya amsawa Alh Sulaiman har yace zai

turo iyayensa don baya son a dauki lokaci. Uwale

tace to dan nema mai toshe kofar arziki. Shi

Sulaimanun nawa ya taba bata tunda yazo. Inna

ki dena koyawa yarinyar nan son kudi, zuwansa

uku fa kullum ba ta gida. Yau idan ta dawo sai

naci mutumcinta. Shegen yawo kamar kaza.

Uwale ta sha kunu bana son irin haka fa, ka

manta tana karatu ne? Ni dai na gama magana

yarinya Ashiru zata aura. Jiya da ya shigo dubu

goma ya bani. Ni Uwale da dubu goma tawa ta

kaina. Ka sallami wannan abokin ginin naka don

bazan bashi jikata ba.

 

FARAR HAIHUWA              23

Abokin gini kuma Inna? Ni da na fada miki gini

zanyi masa yana da kamfani. Sabuwa da tun

farko bata yi magana ba tace haba Malam wai

kai a dole sai ka nuna baka son yarinyar nan ne?

Ya arziki na binmu kana sa kafa kana shurewa.

Babu wanda ya isa yayi mata dole. Wanda take

so zata aura. Idan kuma dole ne sai ks bashi

Dijengala ai itama mace ce. Inna Uwale ta

tuntsire da dariya…wa yaga barahaza. Ba yadda

ya iya dole ya kyalesu idan suka hade masa kai

don baya iya musu da Inna Uwale. A zuciyarsa

ya gama yanke shawarar sanar da Modibbo ya

bawa Alh Sulaiman hakuri. Dama can ba sa’an

auren yarsa bane shima don yaga kamar auren

zai hanata yawo ne.

 

Alh Sulaiman yana mamakin yadda duk lokacin

da yaje baya samun Hanan kullum sai ace masa

bata nan, gashi Umma duk ta kwallafa rai. Shi

kanshi yana son ya kara ganin kyakkyawar fuskar

Hanan din. Yarinyar akwai class. Yana dawowa

daga office ya shirya ya tafi gidansu da yamma.

kila don saboda zuwan dare yake shiyasa baya

samunta. Yau tararta zaiyi kafin ta fita. Yana tuki

Dijengala ta fado masa a rai. Shi kadai yayi

murmushi Allah Yasa itama na sameta…a ransa

har ya gama shawarar idan yau auri hanan zai ce

ta taho da kanwar tata.

 

Yau ma can baya ta ajiye motarsa. Sabuwar

benz ce da masu kudi ke yayi ya shigo lokon a

kafa. Farin yadi ne a jikinsa mai bula bula.

Wandon da shafi amma babu a rigar, ana ganin

farar vest din dake ciki. Takalminsa da hula duk

ruwan toka ne. Yayi kyau sai kamshi ke tashi duk

inda ya wuce. Bai ankara ba yazo daidai kwatar

kofar gidan Mal Yakubu yaji an kwala ihu sai

ruwan kwata ya gani ya fallatso masa ko ta ina a

jikin kayansa harda gefen fuskarsa. Ransa ya

gama baci sosai saboda shi mutum ne mai

matukar kyankyami. Dijengala ya gani kafarta

daya a cikin kwatar babu ko mayafi a jikinta tana

kuka. Ganinsa a tsaye yasa kukan ya karu ta

soma bashi hakuri da karfi. Don Allah kayi hakuri

ban sani ba. Inna ce ta biyoni da bulalar doki.

Kafin yayi magana wata dattijuwa ta fito daga

gidan da ke kusa dana su Dije. Daga murya tayi

yadda Digen zata ji…me ya faru Digengala? Ta

sake wani sabon kukan sannan ta fita daga

kwatar ta karasa wurin matar. Gwaggo, Inna ce

tace yau bazanci abinci ba sai na debo ruwa

bokiti goma. Kuma fa na debo shida amma

yunwa nake ji. Tace na sa baba yaki siyo ruwa

saboda sun hanani na wanka jiya daya fita.

Gwaggo taja hannunta kiyi hakuri kinji yar

albarka shigo kici abinci kiyi wankan. Ta kalli

Sulaiman wanda ya zuba musu ido. Alhaji shigo

kaima kuma kayi hakuri.

 

Ya kalli tsohuwar ba damuwa? Haba yaro ni da

‘ya’yana biyar ne a gidan nan babu mace ko daya

sai matar babban. Kazo ka dan gyara jikinka.

Suna shiga daga bakin kofa ya tsaya aka bashi

buta ya dauraye kafarsa yana ta dage hanci.

Kadan ya rage burinsa ya koma gida kawai. Yana

ta kallon yadda Dije ke cin abinci da sauri da

sauri. Yace don Allah ina da tambaya gwaggo.

Ina jinka ta amsa. Wai ita yarinyar nan wace ce

ita? Kamar jira take ta bashi labarin duk abinda

ta sani game da Dijengala da wahalar da Sabuwa

da uwale ke bata. Sosai ya tausaya mata bata da

wata damuwa sai ya cikinta. Yayi godiya zai fita

Gwaggo tana yiwa Dije waka. Dijengala ta

maigari, ba auren talaka ba. Yana bakin kofa

suka ji ance sai auren musaki ba, kurma irinta.

Inna Uwale ce ta hau kan wata katuwar bambu

ta ruwa da aka kifa daga gidanta. Sabuwa ta

riketa ta tsaya don kar ta fada ta leko ta

katangar da ta hada gidanta dana gwaggo.

Sulaiman har dan tsorata yayi sai kuma ya tsaya

yana jin tijara irinta Uwale. Dije tuni ta tashi daya

kan kwanon tuwon ta koma bayan gwaggo ta

buya. Zaki shigo gidan ki same ni ne ‘yar banzar

yarinya, waye bawanki da zai debo ruwan.

 

Gwaggo tace Ke dai Uwale kinji kunya

wallahi…idan zaki shekara kina nunawa yarinyar

nan tsana bazaki taba canjawa kanki suna a

matsayin kakarta ba. Kuma wallahi idan kika

sake min leqe da wannan shanyayyar kafar taki

sai na tsire miki idanu. Cikin fushi tace ni kike

fadawa haka…wallahi zan hadaki da hukuma su

shiga tsakaninmu. Makotaka ai ba hauka bane

duk kin samin ido inji uwale. Gwaggo tace anji

kunya dai ace danki ma hakuri yake da halinki,

duk kin bata masa gida da tashin hankali. Kin

rabashi da matarsa da yake so kin hada shi da

wannan makirar. Shewa uwale tayi kamar ba

tsohuwa ba. Ai na isa ne.

Sabuwa ce taji cizon cinnaka a kafa ta saki

Uwale ji kake timmm ta fado tana ihu. Gwaggo

tace Allah Ya kara kadan ma kika gani.

Shi dai Sulaiman tunda yaji maganganun wanda

basu san ma yana kofar soron ba sai tausayin

Dijengala mai cin tuwo ya kamashi

 

FARAR HAIHUWA              24

Yana isa gida Ammar ya tare shi a bakin

kofa…hmmm daddy wari. Umma dake zaune tana

yanke farce tace daga ina haka. Itama ta kama

hanci kai me ya sami kayanka. Ina zuwa umma

bari na gyara jikina.

Bayan yayi wanka doguwar riga yasa ya sauko

kasa. Yana zama ya fara yiwa Umma hirar

dijengala. Yadda yake bayanin cike da nishadi

kamar ba shi aka watsawa kwata ba. Umma tace

wai ni Sulaiman kanwar kake so ne ko yayar?

Murmushi yayi Umma yar nake so mana. Ita

wannan Dijen zanso ki ganta. To ai yadda kake

fada kamar babar hanan din ke takura mata. Ba

don yar ka fara nema ba ai da sai ince ka nemi

Dijen don naga tafi burgeka. Ahh haba umma

kurma ce fa. Ta rike baki to sai me Sulaiman?

Kurma ba mutum bace? Ni nafi son irin auren

nan da zai kasance taimako ga wani.

 

Tun da Umma tayi masa magana sai kawai

hankalinsa ya rabu biyu. Tabbas sau biyu yana

tarar da rigima da Dije akan ruwan wanka. Kana

ganinta kuma sam babu gyara. Yasan a kalla

zata kai shekaru ashirin. Da wannan tunanin ya

jira litinin tazo. A office ya sake yiwa modibbo

tambayoyi akan Hanan. Wannan karon gaskiya ya

gaya masa game da halayyarta. Kuma a yadda

babansu ya fada min jiya wai kakar ta zata

kaima aikin gini kake yi shiyasa suke son a bawa

wani. Mal Yakubu har kunyar ka yake ji saboda

yadda take ficewa daga gidan kafin kazo. Hmm

wato sun dauka talaka ne shi yake fada a ransa.

To idan ba damuwa modibbo ka sanar dashi

zanzo gidansa zuwa karshen sati akwai maganar

da zamuyi. Modibbo fata ya rinka yi Alh Sulaiman

ya nemi auren Dije.

 

Alh Sani ya kalli dansa Ashir..yanzu da gaske ka

fasa auren sakina? Ashir me kake son mayar dani

ne. Haj Lami tace kaga duk wancan auren kai

kake zaba masa kila shiyasa baya karko wannan

karon don Allah kada kayi masa dole. Ai dama da

saninki yake wannan wulakancin. Yanzu meye

aibun Sakina? Haj tace bazawara ce fa. Ga

budurwa ya samu son kowa. Har hotonta nagani.

Alh Sani yace shi ma ai bazawarin ne…bazan

tilasta masa aurenta ba kada ya bata mana

zumunci amma wallahi Ashir idan ka kara sakin

mace zan maka ba dadi. Shashasha wanda bai

san mutumcin kansa ba. Shi dai Ashir ko tak bai

ce ba ya tashi ya tafi gidansa. Me zaiyi da wata

Sakina ana zaune kalau. Yadda son Hanan ke ci

masa zuciya baya fatan a wuce wata daya bata

zama matarsa ba.

 

Yau Alh Sulaiman da abokinsa ya tafi gidan Mal

Yakubu bayan sun yanke shawara shi da

Ummansa. Umar yace yanzu Sulaiman har lokon

nan ka zo neman aure? Wannan yarinya ta ciri

tuta. Yayi dariya sai ma ka ganta mutumina. Ai

na iya zabe.

 

Goruba take ci a kofar gidan Gwaggo ita da

kawarta. Kawar ce ta fara hango su Sulaiman

tace ke Dijengala kinga wasu yan gayu can. Dije

na ganin Sulaiman ta gane shi. Al’Quran shine

mutumin dana watsawa kwata. Tashi mu gudu

dan sanda ya dauko min. Na shiga uku.

 

Da gudunta ta tafi zata shiga gida ta kira

babanta ya basu hakuri don taga kamar kayan

jikin abokinsa na yan sanda ne. Bakaken kaya ne

shirt da wando ne. A kokarin gudun ne dan

katakon daya raba kwatar gidansu ya rufta da ita

ta sake yi masa kwalliya da kwata. Rasa bakin

magana yayi don takaici yana tunanin fasa

abinda ya kawo shi. Ita kuwa Dijengala ta gama

tsurewa don tsoro ta bare baki tana kuka,

muryarta a sama.

 

FARAR HAIHUWA              25

Subhanallahi, Sulaiman kaga wata mahaukaciya.

Zo mu koma ka canja kaya sai mu dawo ko

anjima ne ko gobe. Kamar ba dashi Umar yake

magana ba, hankalinsa yana kan Dijengala da

take ta ihu. Dan matsowa yayi kusa da ita yi

shiru Khadija ba kama ki zanyi ba. Hannu tasa

tana share hawaye tace lah kaima kasan sunana

na makaranta ashe. Ita dai abokiyar cin goruba

tuni ta shige gidansu. Yace na sani yanzu dai fito

daga cikin kwatar nan. Ta kalli jikinta tabdi yau

na karar da nawa ruwan wankan sai da muje

gidan Gwaggo mu diba a rijiya. Ka tuna inda

muka je rannan???

 

Yayi murmushi cike da dauriya don wani amai ke

taso masa saboda yadda jikinsa ke wari.

Umar yace wai Sulaiman a nan zamu biyewa

wannan mahau….dakata fa Umar ya tsayar

dashi. Meet my wife to be. Dan murmushin

fuskar umar ya bace…are you serious? Cike da

nishadin da ke baibaye shi idan yaga Dijengala

kurma yace Allah da gaske nake. Dije dake tsaye

a gefe tace zo muje mana kafin kuda ya fara bin

mu. Suna tsallakowa tace wai kuwa kai ba dan

yankan kai bane? Umar har kusa faduwa yayi da

jin abinda ta fada. Sulaiman yace meyasa kika ce

haka? Ta dan tabe baki naga ka nace wa gidamu

ne…ance da haka kuke farawa sai kawai ku sace

mutane. Umar sai kallon ikon Allah yake yadda

take magana ko a jikin Sulaiman. Yace wurin

babanki nake zuwa bana satar mutane. Au to har

hankalina ya kwanta…ta jefar da kwallon gorubar

hannunta. Ai wallahi da niyata muna shiga gidan

gwaggo nayi maka ihu, kasan duk ‘ya’yanta maza

ne. Sai su kamaka a dora maka taya a cinna

maka wuta. Dariya sosai Sulaiman yake Umar na

kallonsa…anya kalau kake kuwa sulaiman? Tana

zancen sawa a konak kana dariya? Kuma kuna ta

daga murya kamar kurame. Sulaiman ya rage

murya kurmar ce ai. Isn’t she cute?

Suna shigowa soron gidan ta fella da gudu. Zasu

raina mata wayo sun zata bata gansu ba suna

wani magana a hankali. tana shiga tasa ihu

gwaggo ta fito da sauri…lafiya Dijengala? Har

haki take tace Gwaggo ashe mutum min nan mai

satar mutane ne? Yau ma ya dawo ina su Yaya

Tajo? Ayi gangamin kama su don yau harda wani

kato yazo.

 

Sulaiman da umar suna jin ta. Ya rinka dariya

Umar yace Allah tafiya zanyi kada a kona ni daga

rako ka zance.

 

FARAR HAIHUWA              26

Gwaggo ta dauko tabaryarta tayo hanyar soro.

Tana ganinsu tace au Alhaji kaine…kaji shirmen

Dijengala ko. Wallahi duk na zata da gaske take.

Kallon jikinsa tayi…ba dai yau ma kwatar kuka

fada ba? Murmushi yayi yace bata kula bane ta

fada ciki.

 

Daga ciki suka jiyo Dije tana cewa ba dai sun tafi

da Gwaggo ba. Na shiga uku me zan fadawa

‘ya’yanta. Shigowarsu ta gani ta saki baki na

tuba don Allah ku yi hakuri kaga ni bana ma ji

sosai kaina bazai yi kudi ba. Gwaggo tace rufa

min baki sarkin surutu.dauko musu ruwa a buta.

Kema ki je ki gyara jikinki.

Bayan sun kammala gwaggo tace kai kuma

kullum kuka hadu da Dije sai tayi maka wanka da

kwata. Ba komai Gwaggo dama mahaifinta nake

son gani. Bari naje nayi masa magana da kaina

to, kasan halin yarinyar nan ina iya turata taki

dawowa.

 

A wulakance su Uwale suka gaisa da gwaggo

tace wurin Mal nazo. Sabuwa tace bacci yake yi.

Mal yakubu ya fito suka gaisa. Tace dama kayi

bako ne shine babu dan aike nazo yi masa

sallama da kai. Uwale tace haka dai aka iya

gulma da sa ido. Gwaggo bata kula ba suka fito

waje…mal yakubu bakon yana gidana fa. Yace

sunansa Alh Sulaiman. Mal yace subhanallah

wallahi har kunyarsa nake ji. Ya sanar da ita

yadda suka akan maganar Hanan. Gwaggo tace

to Allah Ya kyauta muje sai kayi musu bayani.

Umar ne ya gabatarwa mal Yakubu bukatarsu

game da Dijengala. Sulaiman yace baba kada

kaga kamar ina maka yawo da hankali. Naga

kamar Hanan din tana da wani ne shiyasa.

Tamkar an mishi albishir da kujerar makka yace

da gaske kake Alhaji? Kai zaka auri Dijengala.

Sulaiman yace in har ka amince. Na fara sanar

da kai ne don neman izini kafin na turo maka

iyayena. Farincikinsa baya misaltuwa yayi godiya

sosai. Umar ya bashi dubu ashirin yace baba ga

wannan mungode.

 

Suna tafiya Mal ya dauki kudin ya bawa gwaggo

ajiya dama ya saba shawara da ita. Yace yanzu

zan sami nutsuwar amsawa wanda yazo neman

auren hanan. Dama saboda na riga na amsa tun

farko ne. Gwaggo tace ai gara tayi auren saboda

Uwale kara bata ta take yi. Haka suka yi ta yan

shawarwarinsu sanan ya kira Dije ta fito daga

daki suka koma gida.

 

Ashir ya dage sai shirye shirye yake. Anyiwa

gidansa sabon fenti an gyara ko ina. Dama ya

kusa gama hada lefen Sakina saboda haka

abinda ya rage ba yawa. Ya dai kashe kudi sosai

don duk abinda Hanan tace ta zauna. A dan

lokacin da suka hadu ya siya mata sabuwar waya

ga kudi daya ke kashe mata.

 

Mal Yakubu ya sanar da uwale zaije gida ya

sanar da kawunsa da nata yan uwan za’a zo

neman auren Hanan dana Dije. Uwale da Sabuwa

sam basu damu ba da jin Dije ta sami miji tunda

Mal Yakubu yace wannan abokin ginin nasa ne

zai aureta. Shima yana sane yaki fada don gudun

kada su toshewa yar tasa hanyar arziki. Ita

uwale harda cewa kyan da dama ya gaji ubansa,

tunda ita mace ce gara ta auri mai aiki irin na

ubanta.

 

Tunaninsa bai wuce ina ma Munari tana nan. Ina

ma zata ga auren yarsu. Babu ranar da baya tuna

su ita da Sadi. Amma gashi Inna uwale ta

gargade shi ko sau daya yabi hanyar gidan su

munari bata yafe masa ba.

Haka yaje kauyensu ya sanar da yan uwansa

zancen auren ya dawo a ranar.

 

FARAR HAIHUWA              28

Ranar asabar layin gidansu Dije ya cika sosai da

jama’a. Kamar anzo daurin aure. Cikin kudin da

take tatsa a jikin samari Hanan ta bayar aka

hada sha tara ta arziki na tarar baki. Uwale ma

tayo gayya sosai azo a ga yadda ake farar

haihuwa. Tabarmi aka shimfida a tsakar gidan

dama ta fadawa Mal yakubu masu kawo kudi da

lefen Dije suje gidan gwaggo don bata son a

hada su da yan uwan Ashir. Kasan harkar arziki

bata dadi data tsiya. Mal yakubu yace to. Ba

musu ya sanar da Gwaggo ita kuwa abin yayi

mata dadi.

 

Duka bayan laasar suka iso Zaliha tayi wa ‘yan

uwan sulaiman jagora gidan. Nan ta zauna dama

ita bata taba wulakanta yayarta. Abin mamaki

akwati takwas aka shigo dashi gidan gwaggo

matan unguwa da wasu dangin mal yakubu na

kauye suna ta mamaki. Sai ga wasu akwati uku

inji uwar ango. Murna da guda har waje. Cikin

dangin mal yakubu wata tace anya kayan

Dijengala ne kuwa? Uwale tace aikin gini yake.

Matan da suka kawo suka ce kayan Sulaiman

Hassan ne da aka kawowa Dije. Ga kudin aure

dubu dari sannan suna so ayi biki nan da sati

uku. Gwaggo duk ta rude da murna. Ajiyarta ta

dauko ta sami dubu ashirin da hudu. Haka ta

dunkule musu a matsayin tukwici. Haka suka yi

ta godiya aka tashi cikin farinciki. Kaya kuwa

gwaggo ta rinka saka ido ita da zaliha saboda

halin taro.

 

Can gidan Uwale kuwa akwati bakwai ne aka

kawo. Hudu seti daban da wasu uku manya suma

seti daban. Jikin Uwale sai bari yake taga kaya.

Sai ta cangala kafa tayi nan ta kuma cangala

kafa tayi can. Bakinta dana sabuwa sam yaki

rufuwa. Suma sun kawo kudi har dubu dari biyu

dukiyar aure sannan suna son ayi biki nan da

wani satin kamar yadda Hanan da Ashir suka

shirya. Uwale tace sun amince ya shiga daki ta

dauko dubu hamsin da Hanan ta bata ta basu

tukwici. A wulakance suka karba dama tun daga

waje suke yada maganganu.

 

Bayan sun tafi Uwale da Sabuwa suka tafi gidan

gwaggo kallon kaya. Sabuwa tace kada ace

muna bakin ciki gara muje muga abinda aka

kawo mata. Uwale tayi tsaki karshenta ma a

ghana mazi go aka zuba kayan. Ba karamin

kaduwa suka yi ba da suka ga akwatuna jibge a

wurin. Uwale tace ko dai anyi batan kai ne

wannan ne na hannan. Mata suka yi mata ca a

ka. Na Dijengala ne..yarinya ba auren talaka ba.

Sabuwa tace ai dijen ba daya bace a layin nan

kila dai nasu ne. Gwaggo tace sai kiyi kuma

Sabuwa. Kaya na yata ne Allah Ya bata. Bakin

ciki karara a fuskarsu suka fita daga gidan.

Sabuwa harda kuka wai mal ya haince su bai

fada musu gaskiya ba. Uwale tace barni da dan

banza ai wallahi Zaliha za a aura masa. Ni

Yakubu zai cuta…

 

Gwaggo dai ta haye kaya ko tsinke taki bari a

dauka kamar yadda suka yi da malam yakubu.

Uwale sai aike take mata karshe ta leqo ta

katanga tace zata hada ta da yan sanda. Tabarya

gwaggo ta dauko ko ki sauka ko na rotsa miki.

Tsohuwar banza.

 

Daren ranar kamar su sabuwa zasu cinye mal.

Gwaggo ta ce masa munafuki ai da suka dauka

mai gini me sai yayi musu bayani dalla dalla.

Yanzu ya kira yaron ya fada masa Zaliha zai aura

masa Dije tace bata so. Zaliha ta tashi cikin

tsiwa tace wallahi nafi karfin auren dole. Mal

Hafiz na islamiyarmu zan aura.

 

Uwale ta doke mata baki fakiri zaki dauko min

zaliha kamar ubanki? Ba ubana ba dai sai

dai….sabuwa tace karasa sai dai na wa? Mara

mutumci. Ranar dai anyi tashin hankali a gidan

har makota ana ji.

 

FARAR HAIHUWA              27

Tun daga ranar da Sulaiman yaje gidansu

Dijengala bai kara zuwa ba saboda yanayin aiki.

Wata rana ya dawo a gajiye wanka kawai yake

so yayi ya kwanta. Umma ta shigo dakinsa da

sallamarta. Ya amsa yace umma yau kamar anyi

min duka duk na gaji. Umma taca gashi kuma fita

nake son muyi bayan sallar magriba ba. Ba

damuwa indai kin yarda dreba ya tuka. Ya tafi

tun dazu naga kaima kuma kai kadai ka dawo.

Eh a hanyar gidansa nace ya sauka zan dawo da

kaina. Tace to don Allah kayi hakuri idan anyi

sallah mu je. Haba umma meye na rokona kawai

dai ki shirya yau Ammar ne zai tuka.

 

Umma na zaune a baya tana kallon danta

Sulaiman da yake kokarin yin ribas da mota sai

Ammar da yake gaba shima yana cewa daddy

nuna min birki sai na rinka danna maka. Dariya

yayi yana ta biyewa yaron. Zuciyar Haj Bintu fes

da jindadin yadda yake kula da marayan. Wani

dan hawaye ya fito tayi saurin sharewa Allah Ya

jikan Alhaji da Yusuf da sauran musulmi.

 

Kamar yadda ta fada masa gidansu Sakina suka

nufa. Ammar yana ta murna ganin anyi parking a

kofar gidansu mamanshi. Da gudu ya fita

Sulaiman yace umma baki fada min abinda yasa

zamu zo gidan nan a daren nan ba. Hmm wai

yaron da zai auri sakina ne yace ya fasa. Dazu

ta kirani tana kuka. Yaji tausayinta sosai suka

shiga gidan tare. Yasan dai sunan mutumin Ashir

dan wan babanta sun taba haduwa sau daya.

 

Umma ta jajantawa iyayen Sakina. Kishiyar

mamanta tace ai Hajiya in fada miki wata

shegiyar yarinya ya hadu da ita. Jiya da babansa

yazo yake fada tun yanzu ta fara juya shi.

shiyasa yace bai yadda ayi auren da sakina ba

kada su wulakanta ta. Umma tace hakane kam.

Yanzu ita zai aura kenan. Tace mata eh ranar

asabar ma za’a kai kudi. Umma tace Allah Ya

kyauta Ya kawo miki nagari. Shima Sulaiman

ranar asabar din za’a kai kudin aurensa. Sai ku

fadawa Alhaji don Allah.

 

Washegari Sulaiman yayi shiri officially zaije

zance. Umma tasa sha a gaba tana ta dariya.

Wato yau kananan kaya ka sa don kada ta sake

yi maka wanka da kwata. Ai ni umma yarinyar

nan sai addua…amma kazanta a jikinta ba kama

hannun yaro.

 

Motar rannan ya gani a bakin layin. Yana

karasowa ya ga Hanan zaune a gaba suna ta hira

da saurayinta. Sai a lokacin ya tuna inda ya san

shi. ASHIR! wanda zai auri sakina ne. Dama

Hanan zai aura…lokaci guda hankalinsa ya tashi.

Ita kuma irin halinta kenan yarinyar nan? Yayi

godiya ga Allah da yasa sonta bai yi zurfi a

zuciyarsa ba. Dama kyau ne ya rude shi wanda

kullum umma ke masa nasiha akan baya dorewa.

A soron gidan ya ganta zaune akan tabarma can

gefe kuma tumakin Sabuwa. Tuni ya dena jin

kamshin turarensa sai warin wurin kawai. Kanta

a rufe da wani hijab dakal dakal ya sunkuyar da

kai. Yayi sallama tare da kiran sunanta da dan

karfi…ta dago a firgice lah…dama kaine mijin da

zai aureni? Yace baki amsa min sallama ba. Yi

hakuri alekum salam. Tab sallamar ma bata iya

amsawa ba. Ta ce ai baba yace inyi maka ladabi

da biyayya kada ka fasa auren. Dije kenan ita ba

ruwanta komai fada take baki ba linzami. Yana

murmushi daga tsaye don bazai iya zama a wurin

ba. Miko masa ruwa a jug din roba har zai karba

tace a rijiyar gwaggo na debo ruwan dadi ne.

Hannunsa ya mayar aljihu barshi kawai nagode

kada nasha cholera. Ehhh me kace? Ba komai.

Ganin ya rasa hirar da zai mata yace dama size

din takalmi zaki bani da bra saboda hada lefe. Ta

fito da idanu…bra? Wai breziya rigar nono. Ya

gyada kai. Tabdi ashe ma kai dan iska ne. Ta

mike tsaye gwaggo ta fada mana idan dan iska

ya tare mu muyi masa waazi. Idan mugu ne muyi

ihu. To kaga Allah Yana da wuta gidan yan iska

da aljanna gidan mutanen kirki. Kuma zan hada

ka da mal na islamiyya ma yace bulala ake yi.

Dariya yake sosai idonsa harda hawaye lallai

zamansa da Dije sai ya shirya. Ganin yana dariya

ta fice daga gidan a guje. Shima tafiya yayi kafin

ta tara masa jama’a.

 

FARAR HAIHUWA              29

Itama Zulai da ta iso kanon washegari fafur tace

bata yadda Dije ta auri mai kudi ba sai dai a

bawa jikarta. Mal yakubu duk rashin son tashin

hankalinsa cewa yayi idan danki ne sai ki bashi

wadda kike so. Ta kuwa soma kukan gulma ita

anyi mata rashin kunya. Duk gidan ba dadi.

Hanan kanta sai da ta ciji yatsa sai dai bata

damu sosai ba saboda Ashir ma yana da kudin

sannan ta fara sonsa. Duk abinda suke don basu

ma san harda sarkokin gwal gudu biyu da

awarwaro bane wanda gwaggo ta dauke ana

soma bude akwati. Tsoro taji kada uwale tasa ido

a kai.

 

Duka kayan lefen ta nuna masa ya gani ya yaba

ciki tace wannan babban akwatin shine na iyaye.

Ya duba kaya ne masu kyau na maza da mata.

Rabawa yayi har abokinsa modibbo ya samu

shadda har biyu. Ya dauki manyan atampa har

uku, shadda daya da leshi ya bawa gwaggo.

Sannan cikin kudin wanda an fada masa ita ta

biya tukwici ya bata dubu arbain. Wayyo gwaggo

sai kukan dadi cewa take yakubu ayi haka? Duk

ni kadai? Yace ki dai yi shiru kawai gwaggo ya

sami yaro ya biyoshi gida da akwatin.

Uwale so tayi duk kayan a bata wai a raba

tsakanin ‘yan uwa. Mal yakubu yaki, akwatin daya

kai kuwa ko tsinki bata bashi ba ya dauke kai

abinsa. Duk wanda ta bawa sai tace na lefen

Hannan ne. Na Hanan din dakinsu ta ajiye harda

kudin ta hana kowa tabawa.

 

Ana ta shirye shiryen biki Hanan an tare gidan

gyaran jiki. Dama dai duk iskancinta bata yarda

maza su bata ta ba sai dai ayi abinda ba’a rasa.

Jikin nan nata ya kara kyau sosai duk inda ta

gifta sai kamshi. da kyar Mal Yakubu ya samu

aka daidaita ayi bikin nasu duka sati biyu bayan

an kawo lefen. Zulai ita ke kara haddasa fada a

gidan a cewarta nema ake a cuci jikokinta. Sam

bata zancen sauran ‘ya’yan sabuwa da suke

wajen babansu. Ita Sabuwan ce take musu aike

idan ta dan samu. Macen tayi aure namijin kuwa

ya zama dan daban kauye.

 

Ita dai Dijengala tamkar ba amarya ba. Aiki ake

tula sosai da dakon kaya idan anje kasuwa. Duka

mazajen dai sun yiwa mal yakubu adalci ance

kada yayi musu kayan daki. Gwaggo ce kadai ta

damu da rashin gyaran Dijengala. To ga rashin

wayewa shiyasa babu abinda take iya yi mata sai

dai sabulu da ta bata giv tace kullum tazo

gidanta tayi wanka sau biyu safe da dare. Ga mai

toni montana ta siyo mata. Dije idan tayi wankan

sai ta laftawa jikinta mai har sheki take yi.

 

FARAR HAIHUWA              30

Saura kwana hudu a fara biki mal Yakubu har

yasa anyiwa gidan fenti sai Ashir ya sa Hanan ta

fada musu ya saya musu gida a cikin unguwarsu

amma layi daban. Uwale duk ta kidime kafin kace

kwabo ta fara hada kaya. Jin haka zulai tace

bazata koma kauye ba tunda gidan albarkacin

jikarsu ne su biyu. Ba musu uwale ta aminci. Mal

yakubu yace babu inda zashi tunda ba’a daura

aure ba. Ya rage naka mai kashin tsiya shine

abinda uwale ta fada masa. Sannan tace tunda

Dije ma gidan masu kudi zata yi aure ita bata

yarda a tafi da ita ba. Gara ku gana da ita sosai

dama kafi sonta. Zaliha kuwa saboda irin cin

mutumcin da su Uwale suka yiwa saurayinta har

yace ya fasa auren itama kin binsu tayi.

 

A dan lokacin da ya rage kafin biki Sulaiman

yazo ganin Dije har sau uku. A irin hirar da take

masa ta shirme ya gane rabonta da mahaifiyarta

tun ranar da aka sake ta. A ransa yana mamakin

yadda mace saboda bacin rai zata iya yin fushi

harda yarta. Ya kudiri niyar idan sunyi aure dole a

nemi dangin mahaifiyarta.

 

Biki kam yayi biki amma tamkar na mutum daya

akeyi. Dijengala kullum tana gidan gwaggo haka

aka yi kamu da yini don Hanan bata yarda a hada

su ba kuma uwale ta amince da hakan. Yadda

take bin hanan sau da kafa yanzu ban jin tayiwa

babarta irin wannan biyayyar. Mal yakubu dai

yayi nasa kokarin da gwaggo. Burinsa kawai yaga

an dauke Dije zuwa gidan miji ko ta samu sauyin

rayuwa. Kamar yadda Umma ta bawa Sulaiman

shawara tace ya kauda kai a lamarin bikin idan

an kawo amarya sai yayi yadda yake so ttunda

bata karkashin ikonsa. Dole ya hakura zuwa

ranar daurin aure. Ita kuwa Hanan an kashe kudi

anyi party anyi dinner ta kasaita.

 

Ranar asabar aka daura musu aure. Dijengala

tasha kuka lokacin da aka zo daukarta zuwa

gidan miji. Cikin kayan lefenta aka dinka mata

wata atampa riga da zani. Rigar tayi mata

burmemiya. Ga lalle da tayi hannu da kafa na

salatif yasha gishirin kunshi yayi bakikkirin. Sai

bakin lalle da aka zana mata wasu munanan

filawoyi a hannu da kafa. Kana ganinta kaga

wadda bata waye ba. Mayafi ta yafa kato fuska

tasha jar hoda, an ja gira ta kara baki ga janbaki

yaji bajau. Matan da suka zo daukarta dai dama

an fada musu yar talakawa ce shiyasa basu

damu ba. Indai Sulaiman ne sai ta gyaru ko taki

ko taso. A bangaren Hanan kuwa kaya tasa na

gani na fada tana taku daidai uwale da Zulai

suka shige motar da zaa kaita a ciki.

 

FARAR HAIHUWA              31

Gidan Haj Bintu cike yake da mutane yan bikin

auta Sulaiman. Dama dakin umman a kasa yake

sama ne wurin Sulaiman shiyasa jeren da yasa

ayi mata dakin kusa da nashi aka yi. Gidan yasha

gyara sosai ga kayan more rayuwa kala kala.

Su Gwaggo ne ‘yan kawo amarya da wasu cikin

dangin mal Yakubu. Gwaggo tayiwa Dije da ke

kuka nasiha sosai akan zaman gidan miji. Wani

dan maganin mata ta samu a wurin kanwarta ta

bawa Dijen tuna gida ta fada mata ta rinka sha

da madara amma bayan taci abinci. Ko a jikinta

ta karba tare da godiya ta soke a gefen zaninta.

Dama sulaiman ya roki gwaggo kada a dinke

kayan lefenta idan an kawota zai bayar a dinka

da kansa.

 

Da Bismillah Dije ta shiga gidanta. Wurin Umma

aka wuce da ita tayi mata nasiha. Umma har

tafara magana a hankali gwaggo tace ai bazata ji

ki ba sai kin daga murya. Umma tayi yadda aka

umarceta tace ki kwantar da hankalinki ‘yata ni

babarki ce. Dije ta daga mayafin da dama a dole

ta rufe fuska kada gwaggo tayi fada tace da

gaske? Ta juya wurin Gwaggo kinji ashe a nan

din ma zan sami Mama. Umma tace har kin

samu ma. Ta share idanunta to na dena kuka

indai zaki rinka bari naje wurin babana da zaliha

da Gwaggo. Gwaggo dai kamar ta doke mata

baki. Umma da yan uwanta sai abin ya basu

dariya. Ita dai burinta ya cika sulaiman yayi aure.

Ya auri wadda da yardar Allah zata rike Ammar

da gaskiya.

 

Lokacin tafiyarsu Gwaggo da kyar aka rabasu da

Dije. Suka zama abin tausayi kowa cikinsu sai

kuka. Zaliha bata sami zuwa ba saboda tasha

zagi wurin sabuwa akan zama da tayi wurin Dije.

Jama’a na watsewa Umma ta shiga daki. Bayan

tayi wanka mai aikinta ta kawo mata tea wanda

ya zama kaidar ta duk dare ta dauki wayarta ta

buga. Taso kwarai ace matar ta halarci bikin

Sulaiman da sukayi a gidansu amma tana Saudia

taje Umra. Shekararsu biyar da haduwa a makkah

suka shaku duk da cewa Umma ta girmeta. Ba

kowa bace matar face shugabar Muslimah

Institute. Makaranta ce wadda take da bari

daban daban na kula da lamuran mata musulmai.

Ana koyar da ilimin addini,boko ga wadanda

basuyi ba, girki, gyaran jiki da gida da sauran

al’amuran zamantakewa na mata.

 

Bayan ringing biyu aka dauka da sanyin murya

aka yi sallama. Umma ta amsa tace anyi bikin

auta ba kya nan Malama. Kinsan cewa kinci

bashi ko. Daga daya barin aka yi dariya kiyi

hakuri Haj Bintu zan saka ango da amarya a

addua. Umma tace to nagode malama amma

akwai matsala wadda nake bukatar taimakonki

wurin shawo kanta. Nan ta zayyana mata irin

rashin gyara da Dije ta tashi dashi. Yarinyar tana

bukatar a gyarata sosai kinsan halin mazan

yanzu. Sannan harkar ilimi duk da tana da

matsalar kunne dole ta sami abinda zata samu a

ilimin addini. Malama ta ce hakane Haj ai kinyi

jihadi da kika bashi shawarar aurenta. Da ana

samun iyayen miji irinki da mata sunji dadi sosai.

Allah Ya biyaki da mafificin lada. Ki kaita

makarantar ko zuwa next week ne kafin na

dawo. Zan zauna seminar ne da za’ayi sati biyu

masu zuwa. Ke dai in kika je saudia dama sai

munyi cigiya kawai. Allah Ya dawo daku lafiya.

Amin malama ta amsa sannan ta ajiye wayar.

Shiru tayi tana ta tunani har taji an taba mata

kafada. Maama tunanin me kike yi ne haka…ta

kalli dan da ya rage mata a duniya tayi

murmushin bakinciki. Tunanin Khadija nake. Allah

kadai Ya sani ko tana raye. A gabanta ya

durkusa Maama kiyi hakuri da yardar Allah zamu

gano inda Baba ya tafi da ita. Ta gyara glass din

idanunta tare da mikewa tsaye. Allah Ya amsa

adduarka Sadi.

 

FARAR HAIHUWA              32

Wani katon gida aka kai Hanan a kundila. Tun

daga bakin gate Uwale ta saki baki tana kallo.

Suna shiga gidan ta kare masa kallo sai

kuka…wai ni Uwale ce a cikin irin wannan gidan

a matsayin gidan jikata. Ta kama hannun Zulai

kam suka hau bene tare. Komai na gidan yayi

kyau har da amaryar da aka kawo. Zulai tace

Uwale yau kinga         FARAR HAIHUWA        ko. Na gani Zulai

na gani. Allah Ya saka miki da alkhairi da kika

bani Sabuwa. Wallahi taci karenta babu babbaka

har abada bazan taba bari dan nan yayi mata

kishiya ba. Haka mata suka yi ta kallo ana son

barka.

 

Bayan sun tafi ya rage saura Hanan da

kawayenta uku. Hajara ta jawo ta gefe sauran

suna gyara inda aka bata to kinga dare ya fara yi

ki tashi ki sake yin wanka. Hanan ta tashi zata

shiga toilet…Hajara ta miko mata wani ruwa

baki a leda, Babba ne yace kiyi wanka dashi kada

ki goge jiki kawai ki bari ya bushe sai ki shafa

mai. Wata shewa Hanan tayi shegiya Hajara yar

gari ashe baki manta ba. Nagode yar uwa. Haba

ba komai, idan kika yi amfani dashi ko kaska

albarka don like miki zaiyi. Nima tun last week

nayi ai kuwa na kama Alhaji a hannu. Hanan tayi

dariya ranar aurenki zaki yi bayani idan miji yaji

fayau. Ni kinga hankalina a kwance yau. Baki san

akwai kayan mayarda mace budurwa ba? Au ke

kin yarda Hajara to wallahi duk bige ne, once aka

bude hanyar nan an bude kenan sai dai ‘yan

dabaru wanda basa hana mai hankali ganewa.

Ko da tayi wanka wata rigar bacci ta saka shara

shara mai santsi. Dogon gashinta yasha gyara ta

taje shi baya. Jikinta da kayanta sun sha turare

kala kala. Samun wuri tayi ta kashingida akan

gado sanyin AC na kada ta tana jin waka a

hankali a waya. Ashir shi kadai ya shigo da leda

a hannunsa ya rufe kofar dakin. Cikin sigar yanga

da daukar hankali ta tare shi. Kallonta yake cike

da shaawa har ta ajiye kayan da ya shigo dasu a

kan kafet. Hankalinsa duk ya tashi da kyar ya

iya hakuri suka ci kaza da dan juice. Ta sake

tashi cikin yanga tana karkada jikinta. Ashir

kamar wani mahaukaci ya fizgo ta ta fado

jikinsa. Yana taba ta shaawarta ta karu a ransa.

Kan gadon ya kwantar da ita tana

murmushi….abinda ya faru bayan nan shine ya

mugun daga mata hankali. Ashir baiyi wata wata

ba daga kwanciyarta ya juyata akan cikinta ya

danneta. Tun tana dariya ta dauka wasa yake

har ta soma kuka. Gashi saboda karfin maganin

data yi amfani dashi sau hudu ya nemeta a daren

ta bayanta. Duk yaji mata ciwo…yasha zagi da

Allah Ya isa tafi a kirga. Shi kuwa ko a

jikinsa…Ashir rikakken homosexual ne bata sani

ba. Da wannan dabiar yayi kudi lokaci guda.

 

Gabanin asuba bacci ya soma daukarta. Yana yin

juyi ta share hawaye da sauri zata gudu. A kofar

toilet ya tare ta ya sake danneta. Wannan karon

ihun ma ta kasa yi saboda muryarta har ta

dashe, sai nishi kawai take da kyar.

Dije tana ganin babu kowa a dakin ta bude

fuskarta ta karewa dakin kallo. Tashi tayi tsam

ta leka nan ta leka can. Komai yayi kyau tace

uhm kaga gidan ‘yan gayu. Sanyin AC ne ya fara

damunta gashi bata san daga ina yake fitowa ba

bare ta kashe. Ta karasa yaban wani karamin

fridge ta bude. Lemuka ne da ruwa a ciki duk

sunyi sanyi. Ta zauna bakin fridge din ta bude

daya tana sha har gaban rigarta na jikewa.

Sulaiman tunda ya shigo gidan wani nishadi yake

ji. Yayi murmushi yau kuma bai san shirmen da

Dije zata yi masa ba, a hankali ya bude kofar

dakin a tunaninsa tayi bacci don sha daya saura

na dare. Zaune ya ganta gaban fridge tana shan

juice. Ya kulle kofar ya karaso ciki. Inuwarsa

kawai ta gani a kanta ai kuwa sai ta zabura ta

tashi zata gudu. Hannunta ya kama ya janyo

ta…wani irin abu yaji ga dai kamshi tunda

Gwaggo ta sa mata humra ga wani wari wari da

bai gane masa ba. Ta kwalo ido shikenan ka

kamani amma wallahi ba sata nake ba. Umman

nan gidan ce ta ce min wai komai na dakin nan

nawa ne. Kuma dai babu wanda ya bani abinci

tunda nazo. Rabona da abinci fa tun dumamen

safe. Zaunar da ita yayi ya ajiye plate ya zuba

nama da yoghurt a gabanta ga abinci kici. Da

murnarta ta dauki cinyar kaza sai kuma tayi

saurin mayarwa….ta daga gira daya na gano

wayonka. Ai indo da tayi aure ta fada min wai

idan miji ya kawo kaza ba’a ci idan ba haka ba

ranar….ya girgiza kai ranar me? Ni ba ruwana

amma dai bazan ci ba. Yayi yayi amma taki ci sai

yoghurt din tasha. Tana zaune a gefe yaci ya

koshi ya tashi yin wanka. Kafin ya fito tayi bacci.

Kan gadon ya dora ta a hankali…wai yadda take

wannan tashin bazai iya kwanciya kusa da ita ba.

Filo yasa a kasa da bargo ya kwanta. Can cikin

dare wuraren karfe uku yunwa ta tasheta da

sanda ta duba taga yana bacci. Sauran naman ta

dauka tana ci da sauri tana kora ruwa idanunta

duk a kansa. Buruntun ta ya tashe shi amma

tunda yaga abinda take yi ya share don kada yayi

motsi ta kwana da yunwa. Ga dariya na cinsa

dole ya gimtse. Ita kuwa tana gamawa ta koma

gado ta kwanta sai bacci.

 

FARAR HAIHUWA              33

Washegari amaren kowacce ta tashi da sabuwar

rayuwa. Hanan bata sami yin bacci ba sai da gari

ya gama wayewa. Da kyar ta iya tashi Ashir ne

ya taimaka mata kamar babu abinda ya faru.

Ruwan da ta shiga kamar an saka barkono don

zafi amma haka ta daure saboda ta sami saukin

ciwon. A wani irin yanayi tayi sallah don zama

ya gagareta. Haka dai ta lallaba tayi sannan

bacci ya dauketa. Sai wuraren shadaya na safe

taji ana shafa mata fuska. A gigice ta tashi ta

soma kuka. Ashir ya jawota yana rarrashi…haba

amarya ai duk matar aure ranar da aka kaita sai

tayi hakuri. Ni ban taba samun nutsuwa da mace

kamar ki ba, nagode sosai. Ita dai a tsorace take

kallonsa. Ya dauko mukulli a hannunsa yana

murmushi..ga gift dinki for being a good wife.

Duk abinda kike so sai kiyi magana. Ita tsoronsa

ma take ji yanzu wace magana zatayi. Kamar ya

karanci abinda take sakawa a ranta yace kinga

sauran auren dana yi ban iya gabatar musu da

bukata ta ba saboda basu waye ba kamar ki.

Yanzu tunda jiya anyi yadda nake so yau kuma

irin naki za’ayi kinga an jefi tsuntsu biyu da

dutse daya kenan. Yana magana yana kashe

mata ido. Ai tuni jikinta ya fara bari sai hawaye.

Ashir kayi hakuri don Allah jikina ciwo yake min

sosai. Allah Sarki Hanan nima haka fa..na rasa

abinda yasa na kasa hakuri dake. Bari ayi

wannan sai inyi miki tausa ko. Bai kara saurarta

ba sai kukanta kawai ake ji. ko ta ina jini kawai

take zubarwa saboda karfi yake saka mata.

Tunda Sulaiman ya dawo daga masallaci yake

kallon Dije. Ita kadai akan gado amma duk

bedsheet ya tattare. Ta juya nan ta juya can.

Zama yayi akan gadon kusa da ita yana kallon

fuskarta. Zanen kalangun da uwale tasa ayi mata

ranar sunanta ya gani. Hannu ya kai ya taba ta

yi saurin tashi da ihu. Tana ganinsa a zaune tace

gizo gizo a fuskata. Ya girgiza kai, khadija da

sunan Allah ake tashi ba ihu ba. To amma ai ji

nayi ana bin fuskata. To yi hakuri zane na gani a

gefen fuskarki. Hannu tasa ta rufe, ai Inna ce

taso ta cuce ni wai sai anyi min kalangu irin

nata. Mama na kafin a saketa tace bata yarda da

shine aka fasa. Allah Ya saka mata da alkhairi da

ta hana. Kinsan zanen jiki babu kyau.

Yanzu ki tashi kiyi wanka kiyi sallah, zan ajiye

miki kaya. Anjima sai muje akai miki dinki ko. Ba

musu ta mike. Bata fi minti biyar da shiga ba ta

fito saman fuskarta duk kumfa. Ta sako katon

hijab. Lokacin karatu yake amma idanunsa na

kanta. Yana kaiwa aya yace koma Khadija

wannan wankan ai na tada dauda ne. Baki ta

turo masa ni a gida ma ban saba dadewa irin

haka ba. Ruwan ne naga yayi min yawa. Ajiye

Quran din yayi ya dan sha kunu wuce muje ki

sake wanka. Wai a gabanka kake nufi. Ya gyada

mata kai. To Al’Quran bazani ba. Tabdi kamar

wata yar….toshe mata baki yayi kafin ta karasa

zagin ya kinkime ta sai toilet. Wallahi wani karni

kike yi ya fada a hankali.

 

FARAR HAIHUWA              34

Allah Yasa akwai falo kafin dakin nasu amma duk

da haka yadda take ihu yasan kila umma ta ji

kukan. Duk da yadda take ihun ya bashi dariya

yau daurewa yayi yace ta cire zanin da hijab.

Kuka ta saka masa tana ta surutai. Bai kula ta

ba ya cire jallabiyarsa ya rufe kofar.

Ta riga shi fita daga toilet din sai harararsa take

kamar idonta zai fado. Shareta yayi ya dauko mai

me kamshi ya shafa mata. Dole Dije tayi karni ga

gashi bata askewa watarana ma wankan ba

sabulu ga baki baya samun gyara sosai. Komai

sai da ya gyara mata. Dama sunyi magana da

umma akan Muslimah Institute sai dai baya so

taje a muguwar kazanta shiyasa yake son ya dan

gyara mata jiki. Kayan da ya dauko mata

pakistan ne riga da wando da karamin mayafi, sai

da duk suka sha turare itama ya fesa mata na jiki

yace tayi sallah. Bayan ya gama da ita ya shiga

yin wanka. Duk sanda suka hada ido sai yaga

tana harararsa ko ta murguda baki. Kyayi kya

gama mai tsiwa kawai. Ga kurma da son zance

tace banji ba me kace? Cewa nayi muje a sake

wanka…dakin ta bari gabadaya harda bugu masa

kofa. Sai a lokacin yayi dariya…sannan yaji son

matarsa yana shigarsa.

 

Dakin umma ya tarar da ita tana bata labarin

yadda yayi mata wanka…wallahi umma duk ya

gurje min jiki da soso.Umma ta sunkuyar da kai

kasa ita ce mai jin kunyar. Ni ki barni na rinka

kwana dake kawai shi Sulaiman din nan…kul ki

dena kiransa Sulaiman mijinki ne kinji khadija.

Tace to Malam haka mama take kiran babanmu.

Shi dai saboda kunya fasa shiga dakin yayi.

Inna da Zulai tunda aka kai Hanan yau kwana

hudu basu da zance sai na gidanta. Ba don

Sabuwa ta dage kada suje gidan su zubarwa

‘yarta da mutumci ba da tuni washegari sun je.

Jira suke ta cika sati biyu kamar yadda Sabuwan

tace sannan suje.

 

Shi kuwa Ashir soyayya sabuwa yake nunawa

matarsa sosai. Kullum yana manne da ita. Kuka

tayi har ta gaji ga wani masifaffen tsoronsa da

take ji yanzu. Tun ranar da aka kaita ya karbe

wayarta a cewarsa honeymoon suke a gida

shiyasa ta kasa kiran Hajara ta tura ta gidan

Babba gara a warware asirin da irin wannan

rayuwa gara ta mutu ba aure. Itama Hajaran

tafiya ta kama ta shiyasa bata zo ba. Duk bakin

da akeyi a gabansu yake zama don yayi mata

warning idan ta kuskura ta tona masa asiri zata

ga abinda zai mata. Duk dare sai tayi kuka.

 

FARAR HAIHUWA              35

Sati daya da bikinsu Hanan sannan Zaliha taje

gidan. Mai aikin Hanan ita ta kaita har falo tace

bari na kira antin. Tun da Hanan ta bullo Zaliha

ke yi mata wani irin kallo. Wata irin tafiya take yi

a tattale kamar sabuwar yar kaciya. Duk ta fada

ma…zaliha taji tausayinta ta tashi da sauri ta

rikota. Yaya sannu baki da lafiya ne? Wani

hawaye ne yake kokarin saukowa Hanan wanda

Zaliha ta lura dashi. Muryar Ashir ita ta sa

Hanan saurin shanye kukanta. Daga wani falo

suka fito da abokinsa wani dan saurayi wanda

Ashir din ya girme shi. Babban Yaya ina wuni.

Cikin faraa ya amsa mata. Ya sami wuri ya

zauna kusa da Hanan. Tana son yin hira da ‘yar

uwarta yayi kane kane a wurin. Dole suka rinka

hira suna sawa dashi. Yace Hanan bazaki

nunawa Zaliha motarki ba? Yaya har mota gareki

bamu sani ba. Hanan tace ai zanzo da ita gida

ku gani. Amma sai tayi wata daya Ashir ya fada

tare da mikewa. Muje kiga motar sai na kaiki

gida. Kamar tayi kuka Hanan tace haba daga

zuwanta ko ruwa bata sha ba. Kallon da yayi

mata yasa tayi shiru, ita kanta Zalihan sai da

tasha jinin jikinta ko akwai matsala. Daga wurin

motar kuwa cewa yayi ta biyo shi gareji su tafi.

Dole suka yi sallama ta tafi. Suna fita waje tace

gidan daya yayar tawa zani a bompai fa. Da ka

ajiyeni ma kawai. Wani kida yake ji a hankali ya

kalleta. Maimakon ki nemi miji kiyi aure sai ki

zauna tsurku gidan yayyanki. Maganar ta kona

mata rai ta sha kunu. Sauke ni a nan…kamar bai

ji ba ya kara taka mota. Sai da ta tsorata. A

bajin junction kafin a bada hannu yace ta sauka

tare da mika mata naira dari ta shiga mota. Bata

iya masa godiya ba ma tayi saurin yin gaba.

 

A gidan Dije kuwa a falo ta gansu ita da Ammar

suna shan mangwaro duk sun bata jikinsu. Dije

na ganinta ta tashi da gudu suka rungume juna.

Zaliha tayi murnar ganin yadda yayar tata ta fara

yin fes. Tace Dijengala ta maigari. Ammar ya

tashi sai na fadawa Daddy na kin ce ma mommy

dijengala, yace sunanta mommy amma shi da

umma khadija suke kiranta. Zaliha tace tohh yi

hakuri kaji mommy nake nufi. Ya koma ya zauna

to zo ki sha mangwaro. Murmushi tayi ta zauna

suna hira da Dije. Muje ki gaisa da Umma tana

da kirki sosai tace ma zamu zo mu gaishe da su

Baba. Ta washe baki, in fada miki Daddy din

Ammar yace zai siya min waya mai touch me

touch you. Zaliha sai dariya suka je ta gaishe

da umma. Umma tayi murna sosai tace mata ya

mutan gida ina Gwaggo. Duk suna nan kalau.

Hira suka yi sosai da Dije inda zalihan ta bata

shawara akan ta rinka nutsuwa ta kuma rinka yin

tsafta.

 

Sai bayan magriba ta shirya tafiya bayan taci

abinci ta koshi. Umma ta hada mata kayayyakin

yan mata. Sulaiman ya hadu dasu a bakin gate

Dije taje rakata. Fita yayi daga motar yace

drebansa ya kaita gida. Shima dubu goma ya

bata tana ta godiya. Sai da Dije tayi kuka tana

cewa ki gaishe da Baba da Gwaggo, da su Inna

duka.

 

Har daki ta same shi duk da bata son zuwa

kullum sai yasa tayi wanka sau uku kwamar wata

kwaduwa. gashi na safen shi yake mata . Sai ta

yini tana murguda masa baki. Kamar yadda yake

koya mata da sallama ta shigo. Ya daga kai ya

kalli gaban rigarta. Khadija me ya sami kayanki

haka? Wallahi mangwaro ne amma kayi hakuri

zanyi wanka yanzu, tasan karshen magana yace

shi zai mata ne. Kin fiye tsoro ai babu abinda

zan miki. Ta durkusa a gabansa Daddy din

Ammar nagode sosai Allah Ya saka da alkhairi ya

kara budi. Cikin rashin fahimta yace me ya faru.

Kudi da yawa ka bawa zaliha shine nace nagode.

Khadija kanwarki ai kanwata ce kinji ko. Tace

to…amma dai ana son godiya. Kamar yanzu idan

nayi wanka sau ukun nan yakamata ka rinka

gode min. Hannunta ya janyo…nagane wato dai

kina son na rinka yaba miki ko. To jeki kiyi ki fito

kina kamshi kuma. Da sauri ta tashi ta shije

toilet din.

 

Fafur Uwale da Zulai suka ki yarda a gidan Dije

aka bawa zaliha kudi da kayan data zo dasu.

Zulai tace kina nufin naira dari kawai aka baki

tace eh mana. Ni mijin nata wallahi kamar bashi

da kirki. Ahir na sake jin haka inji uwale kema ai

kinyi garajen zuwa ne. Kuma ba gashi kince ya

siya mata mota ba. Ai kina ganin ashiru kinga

arziki. Shima mijin Dijengala nasan duk na neman

suna ne ko yanzu ya lura kin fita kyau yana son

yin canji. Zaliha tace da wa???Allah Ya kiyaye na

auri wanda ya saki yayata.

 

FARAR HAIHUWA              36

Cikin dare Uwale ta rinka juyi sam ta kasa bacci.

Duk da taki yarda da abinda Zaliha ta fada masu

lokacin da ta je gidan yayyenta, ta kasa samun

nutsuwa. Ya zama dole taje ta ganewa idanunta

tun auren baije koina ba. Yaushe zata yarda wani

namiji ya wulakanta Hannan da ranta da

lafiyarta. Yarinya fara ga kyau ga kyan diri. Dole

taje gidan gobe ta ganewa idonta don irin yadda

take son Hanan ko da iyayen Hanan din ne zasu

saba idan aka bata mata rai. Da wannan

shawarar bacci ya dauketa.

Gari na wayewa ko zulai bata sanarwa ba ta fice

daga gidan. Duk wanda mal Yakubu ya tambaya

ina Innarsa sai su ce suma basu tashi sun ganta

a gidan ba.

 

Bugu take ji a bakin gate kamar za’a balla shi. Da

kyar ta iya ture Ashir ta tashi. Jikinta yauma

ciwon yake ga wani zazzabi da take yawan yi da

ciwon kai saboda kukan da take kwana tana yi.

Karfe takwas ta gani da kwata, tsoronta daya

kada ya sake tashi don idan idonsa biyu bata da

hutu. Da sanda ta fita daga dakin ta sauka kasa.

Mai aikinta Nancy ta gani tana jera abinci akan

dinning table. Nancy jeki ta tambayi mai gadi

waye yake bugu da safen nan. Ba jimawa ta

dawo tace sunanta Inna Uwale, gurguwace. A

harzuke Hanan tace gurguwar uwarki. Kice ya

bude mata kakata ce. Duk duniya bata da masoyi

kamar uwale shiyasa duk neman kudinta a wurin

samari don ta kyautatawa kakar ne. Uwale na

shigowa ta tsaya turus, komai na gidan yayi ga

kamshi yana tashi sai dai Hanan ta fige kamar

kazar mayu. Auren sati daya duk idanunta sunyi

loko. Ba dole ba tana tare da fargaba. Hannan

me ya sameki? Tuni hawaye ya cika idonta sai

dai kafin tayi magana suka ji muryar Ashir yana

saukowa daga bakin benen. Sweety ke da baki

da lafiya me ya taso ki yanzu zo muje nayi miki

tausa. Zuciyar Hanan ta tsinke da jin muryarsa.

Ita kuwa uwale duk kunya ta kamata. Shima sai

yayi pretending kamar lokacin ya ganta harda

sunkuyar da kai…au Inna kece da safen nan?

Hanan ya kika barta a tsaye ku zauna mana.

Kusa da Hanan din ya zauna don kada ta sami

damar magana. Uwale ta durkusa har kasa ta

gaishe shi haba Inna ai sai kisa naji kunya ya

fada yana kallon Hanan. Kwana biyu zazzabi

take yi shiyasa kika ga duk ta fada. Rashin hutu

ke damunta saboda baki. Hanan tayi saurin

kallonsa…ji karya banda Zaliha ko yan gidansu

babu wanda yazo. Tafiya zanyi da ita America ta

huta na wata daya kafin su koma makaranta.

Uwale sai murna Allah Sarki Ashiru Allah Ya baku

zaman lafiya. kana ta dawainiya mungode sosai.

Haka suka yi ta hira Uwale har ta fara hadiyar

yawu saboda yunwa. Ga abinci kala kala tana

hangowa amma masu gidan basu yi mata tayi ba.

Ta dan kiftawa Hanan ido zo ki nuna min

bayangida zan dan zaga. Ashir yace bari Nancy

ta kaiki. Tana shiga toilet din tayi tsaki dama

niyarta tace mata bazata bata abinci bane. Data

fito a nan inda ta barsu ta samesu. Zata kuma

zama Ashir yace Inna muje insa dreba ya kaiki

gida ko. Hanan tashi kije kiyi wanka ina zuwa. A

tsorace ta mike tace Inna ki gaida su Baba. Sai

anjima. Mamaki karara a fuskar Uwale ta tashi a

sanyaye don yadda ya hade fuska bata ga damar

yin musu ba. Suna fita yace wa dreban ka ajiyeta

a bus stop ta sami mota. Inna ki gaida mutan

gida. Haka ta tafi ko na pure water bai bata ba.

A zuciyarta babu abinda bata saka ba.

 

 

Kaga ni nayi kyau? Green din material ne a jikinta

riga da skirt sai wani purple din hijab mai duhu

data saka. Murmushi yayi sosai ma Khadija ta ce

to daga yau zaka dena min wanka ko? Kullum sai

nayi istigfari dari fa saboda nasan ba kyau. Fin

karfina kawai kayi. A sati biyun da suka yi a

matsayin mata da miji kullum akwai shirmen da

Khadija zata yi masa. Don ma Umma tana

tayashi yi mata gyara. Yanzu waya fada miki

idan miji yayiwa mata wanka laifi ne? Oho ta

bashi amsa. Ya dan zare mata ido tayi saurin

cewa ina nufin ban sani ba. Haka na zata akwai

zunubi. Yace to babu kinji ko. Yau zamu je asibiti

a duba miki kunne sannan na kaiki makarantar

kawar umma. Wata dariya tayi har kasa Umma

tana ji tace ai asarar kudi zakayi idan ka kaini

makarantar Inna Uwale tace bani da kokari, kuma

fa gaskiya ne babu abinda na iya a makaranta

sai Arais okon pashon. Sulaiman yayi dariya

sosai yadda ta dage ta kai karshen national

anthem. Tace to meye na dariya ko ban iya

bane? Shi dai wannan da karfi akeyi a

makarantarmu shiyasa na iya. Ya riko hannunta

zasu fita daga dakin ….gaskiya kin iya sosai

Khadija. Tace don ma mura ta dan kamani ne fa

amma wata malamarmu tace ina da muryar

waka. Idan na fara sai kaji ana ta tafi. Yana

dariya yace don Allah kada kisa cikina ciwo.

Shige mu tafi.

 

Asibitin suka fara zuwa likitan ya bata

magunguna na sha da na digawa a kunne ya

badu sati biyu sannan su dawo sai asan abinda

za’ayi wa kunnen. Daga nan suka wuce

Muslimah Institute. Office din Director din suka

wuce wanda tun a bakin kofa aka rubuta

sunanta.

 

HAJ MAIMUNATU ADAM

FARAR HAIHUWA              37

Kwankwasa Sulaiman yayi tare da sallama. Daga

ciki aka amsa ya bude suka shiga. Khadija ta

kalli kan kujerar ta koma waje ta sake karanta

sunan dake jikin kofar. Kaine Haj Maimunatu

Adam din? Ta kalli Sulaiman, daddyn Ammar

sunan mace nagani fa kaga namiji kuma yayi

kwam akan kujerar. Salati Sulaiman yayi yace

zaki fara ko.? Don Allah kayi hakuri ya fadawa

matashin dake harhada wasu files dake gabansa.

Matashin da zai kai shekaru ashirin da biyar ya

tuntsire da dariya jin abinda Khadija ta fada.

Mama na ce Haj Maimunatu din. Sulaiman ya

mika mishi hannu suka gaisa. Kayi hakuri tana da

matsalar kunne ne. Hajiyan bata nan ne? Eh ta

fita Inno, sorry mamanta ce ta zame dazu shine

ta tafi asibiti wurinta. Kaine Alh Sulaiman Hassan

ko? Don ta fada min zaka zo da matarka.

Sulaiman yace eh. To ga wannan form din ka

cike. Maama tace zata shiga ajin karatun boko

da islamiyya wanda akeyi sunday zuwa

wednesday. Ranar alhamis da juma’a ba karatu.

Sai kuma special class na mata shi kuma bayan

an gama karatun safe ranar asabar da lahadi

akeyi. Sulaiman ya karbi form din yana

karantawa. Ajin matan ana koyar da girki da

yadda mace zata gyara jikinta. Sannan ana yin

gyaran jikin gaba daya har da gashi. Khadija sai

bin bakinsu take da kallo don bata jin abinda ake

fada sosai. Harda certificate ake bayarwa a

makarantar. Sulaiman ya zabi ajin da yake so ta

shiga sannan ya jaddada masa kurma ce amma

tana ji kadan kadan. Sun yanke shawarar

washegari zata fara karatu. Da zasu tafi

Sulaiman ya ce ya sunan malamin ne? Sadisu

Yakub. Amma ana kirana Sadi. Suka sake

musabaha sannan suka tafi gida bayan sun karbi

uniform din makarantar wanda dogon hijab ne

har kasa ruwan kasa.

 

Sati hudu da fara karatun Khadija ya fara ganin

changes. Kullum dare bata barinshi yayi bacci da

wuri sai ya sake koya mata karatun da aka yi.

Tace masa tana son yin ta daya idan anyi

jarabawa…wallahi duk karatun da nayi ta karshe

nake zuwa kamar na gaji dakikanci.

 

Ranar da ta fara ajin gyaran jiki relaxer aka saka

mata a kanta saboda yadda yayi karfi sanan aka

yi steaming. Ashe yana da dan tsaho ba laifi.

Tun daga ranar take yanga da gashi. Tana jin

dadin yadda kullum Sulaiman yake tabawa don

kuwa Mal Amina ta sanar dasu ba’a boyewa miji

jiki. Gyaran jikin da ake yi mata yasa fatarta ta yi

kyau sosai. Jikinta kullum kamshi. Yau da yake

an koya musu kwalliya irin ta zamani tana

dawowa bayan taje sunyi girki da mai aiki wanka

taje tayi ta zauna gaban mudubi gyaran fuska.

 

Ita kanta tasan ta canja sosai. Sai da ta tabbatar

tayi kyau sannan ta tashi ta hau shafa humra da

fesa turaren jiki. Riga da skirt ta saka yan kanti

ta saka ribbon a kanta. Tana gamawa ta dauki

hearing aid dinta wanda likita ya bata a asibiti ta

saka a kunnen hagu, kunnen daman bai tabu ba

sosai .ta dauko wani wata zuma cikin kayan da

mal Amina tace su rinka sha duk kwana uku kafin

miji ya dawo.

 

Yau tayi niyar fada masa ya dena kwana a kasa.

Tun safe take tunanin da yadda zata fada kada

yace tayi rashin kunya.

A falo ya ganta suna kallon wani cartoon ita da

Ammar. Da sallama ya shigo Ammar yaje ya taro

shi. Mommy bazaki zo yiwa Daddy na oyoyo ba.

Kai ta sunkuyar tace sannu da zuwa. Abin

mamaki Dije kurma ta koma khadija yar gayu.

Wai ita ce take jin kunyarsa yan kwanakin nan.

Ya sake kallonta…tayi kyau kamar ba ita ba yace

ina Umma ne. Yanzu ta shiga daki ta bashi

amsa. Dakin ya bita suka dan taba hira sannan

ya hau sama. Wani kamshi mai dadi ne ya ji a

dakin ga kayan bacci ta ajiye masa akan gado.

Dadi yaji sosai yana kara godewa Allah daya

bashi ikon karbar shawarar mahaifiyarsa gashi

yanzu ba karamin son khadija yake ba.

Dawowa kasa yayi yace a kashe film din haka sai

gobe. Ammar tashi ka tafi daki ka kwanta. Ni

daddy ba na jin bacci. Ka bari muyi hira da

mommy. Tabdi ai shima Sulaiman hirar yake son

yi da ita. Khadija kai min abincina daki bari na

kai wannan dan naki da kike shagwabawa wurin

kakarsa. Ba musu ta tashi…binta yayi da ido har

ta bace.

 

Ko yaya ya dago kai sai yaga tana kallonsa. Ya

ajiye cokalin hannunsa wai ni khadija so kike na

kware ne? Tayi murmushi tare da jin kunya a’a.

To zo ki bani a baki yau ina ciwon hannu. Harda

rufe fuska don kunya ta tashi zata gudu. Ya

janyota ta fada kansa. To karya ni ya fada yana

ture plate din abincin…tace yi hakuri. Nifa

gaskiya duk kin wani zama salihar karfi da yaji.

Ina kika kai min Dijengala ne. Nayi missing dinta

kinsan ita ta iya tarairayar miji. Murguda masa

baki tayi zata tashi wato ma tsokana ta kake yi

ko. Sai idanunta ya ciko da hawaye ta fara masa

kukan shagwaba…ya na share hawayen yace ba

tsokanarki nake yi ba Khadija, sonki nake yi.

Wata kunya taji zata sunkuyar da kai ya rike

habarta ina bakin tsiwar nan ya kamata ace mun

gaisa dashi….kissing dinta yayi sannan yace

tashi muyi sallah. Ai nayi ta fada kanta a kasa

yau kam kunyar sulaiman tayi mata yawa. Kada

kice malamarku bata fada miki ana yin sallah ba

tsakanin mata da miji don neman albarka

kafin….ita ma kafin ya karasa magana ta gudu..

*

Kwanansu Hanan uku da dawowa daga America.

Taci wahala sosai a hannun Ashir ga zulumi

shiyasa kullum take kara ramewa. Ya kaita gidan

iyayenshi sun gaisa. Hajiyarsa tayi ta mita sai

yau kaga damar kawo mana ta kitse don kada ta

narke?ko a jikinsa sai hanan ke aikin bada

hakuri. Gidan nata iyayen har ta gaji da magiya

yaki kaita. Wata rana da safe ta tashi tana ta

amai duk jikinta ba dadi. Rabonta da lafiya tun

ranar da aka kawota gidan gashi yanzu watanta

uku. Komai na jindadin rayuwa yana bata banda

kwanciyar hankali. Ta fito daga toilet ta canja

kaya sanan ta sauko kasa ta kira shi ya taimaka

ya kaita asibiti. tana bude falonsa ta ganshi tare

da wani yaro da baifi shekaru sha biyar ba.

Yanayin data gansu ne yasa ta sume.

 

FARAR HAIHUWA              38

Motsin da yaji a bakin kofar yasa shi saurin

juyuwa a firgice. Ya dubi yaron dama baka saka

key a kofar ba. Yaro ya ce to ba gidanka bane?

Ya harzuka kai rashin kunya zaka yi min mara

mutumci. Yaron ya kalle shi ido cikin ido aut

dama akwai wata kunya ko mutumci tsakaninmu.

Ya dauki kayansa ya saka sannan yayi hanyar

kofa ya tsallake Hanan dake kwance bata san

inda kanta yake ba. Ashir mamaki ya kamashi

lallai wannan yaron indai baayi da gaske ba sai

ya fi su shaidanci. Amma zai gamu dashi. Hanan

ya je ya daga ya nufi mota da ita. Shi yanayinta

bai dameshi ba kamar rashin kunyar yaron. Gashi

har ya fara sonsa! Subhanallah.

 

Bayan dogon bincike likita ya tabbarwa da Ashir

tana da ciki wata uku, sannan jininta ya hau

sosai. Ashir yafi kowa sanin dalilin lalurar

matarsa. Likitan yana fita yace to munafuka

dama labe kike yi min ko? To kinga uwar da ake

yi a dakin sai me. Tana hawaye tace don girman

Allah Ashir ka sake ni. Da irin rayuwar gidanka

gara na mutu na huta. Wa ya fada miki mutuwa

hutu ce ga kowa? Ai hutu ce ga mai rabo kawai

wanda bana jin kina cikinsu. Ko baki san duk irin

text din da kuke exchanging da kawarki hajara na

gani ba. Shiyasa na hanaki wayar. Kuma

bukatarki ta muyi auren har abada ya tabbata ba.

Ni dake Hanan mutu ka raba. Don yanzu na fara

sonki.Kudi da jindadin rayuwa kuwa yanzu kika

fara gani. Yana gama magana ya fice tare da

banko kofar har sai da gabanta ya fadi. Wani

kuka Hanan ta rinka yi mai sauti duk ta zama

abin tausayi. Tayi nadamar auren Ashir, da bin

malamai da ma irin rayuwarta ta son abin duniya.

Yau gata cikin kudi da daula amma bata da

kwanciyar ko kadan. Tashi tayi a hankali tana jan

karfen da aka saka robar ruwan da ake kara

mata ta bude kofa ta fice.

 

Atampa mai kyau ce a jikinta wadda ta rufe ta da

babban mayafi mai kauri. Kafarta takalmi ne

mara tudu sosai da safa ta rufen jan kunshin da

tayi. Fuskarta babu wani ado amma kana ganinta

kaga kyakkyawar mace. Farin glass din idonta ta

cire zata goge ta hango Hanan tana tafiya a

hankali tana bin bango. Da sauri ta karasa ta

tareta don saura kadan ta fadi. Sannu baiwar

Allah me ya fito dake haka babu wanda ya rike

ki. Wani irin numfashi Hanan take yi tace don

Allah ki taimakeni ki bani aron waya na kira

babana. Ka ji wahala tasa ta tuna babanta yau!!!

Nuna min dakinki tukunna kinga jikinki babu

kwari. Cikin kuka tace a’a ni dai ki kira min idan

yazo ya ganni hanawa zaiyi. Dankwalin kanta ta

cire ta shimfidawa Hanan ta zauna sannan ta

dauko waya a jaka ta bata. Duk wanda ta kira

bata samu cikin iyayenta. Gashi number dinsu

kadai ta haddace. Ita Sabuwa dama wayarta

kamar hoto bata fiye kula ta ba. Shi kuwa mal

Yakubu ya canja waya batare da saninta ba.

Sulaiman ya sama masa aiki a daya daga cikin

kamfanin sa. Ta kara fashewa da kuka na shiga

uku na lalace. Subhanallahi kina musulma me ya

hadaki da wannan kalma. Ki yi hakuri komai yayi

zafi maganinsa Allah. Ina kika bar azkar da

addua, ina tawakkali da imaninki. Hanan ta

rungume ta tana kuka na cuci kaina. A nan wurin

cikin kuka da dashewar murya ta fada mata

yadda ta auri Ashir da irin halayyarsa. Ya hanani

hulda da kowa a gidanmu. Wayata ma tana

hannunsa. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Kiyi

hakuri mu koma daki sai ki bani kwatancen

gidanku zani da kaina. Ai bai kamata mahaifinki

yayi fushi dake akan hakan ba. Sai dai kinyi

kuskure babba da kika rayuwarki da sabon Allah.

Bin bokaye da malaman tsibbu hanyar shirka ce

sai dai kuma Allah Yana duba zukatanmu a

lokacin da muke neman gafararSa. Ki kyautata

tubanki sai kiga Allah Ya kawo miki mafita.

Suna zuwa kofar dakin Ashir ya taho. Ganin

Hanan a waje yasa yayi saurin karasowa yana

muzurai. Sai yau ta tabbatar ashe mummuna

ne…ko kuma munin halayyarsa ce yasa take

ganinshi kamar wani kumurcin maciji. Ya wani

kwantar da murya Sweety daga ina ke da nace

miki ina zuwa. Me ya fitar dake. Ta kalli matar a

tsorace alamun neman agaji. Allurar hannunta ke

mata ciwo ta fito neman nurse. A hanya na

ganta shine na rakota daki zan kira nurse din. Ya

riko kafadarta no ba problem ki tafi kawai zan

nemo su. Tana tsaye saroro ya rufo kofar. Kafin

ta yafi taji yana yiwa Hanan fada. Gashi ko

address din gidan nasu bata karba na. Dole ta

koma dakin da Inno take kwance ta basu labarin

abinda ta gani. Kowa ya tausaya mata.

 

FARAR HAIHUWA              39

Saukar ruwan sanyi yaji a bayansa ya tashi da

sauri. Dariya take yi sosai ganin yadda ya

tsorata. Kanta ya yi tana gudu tana kiran Umma.

Gara ma ki tsaya na rama kawai. Ai kin fini sanin

sun tafi wurin Sakina ita da Ammar. Dama so

kika yi su tafi ki takura min ko. Shiyasa kika wani

langabe wai baki da lafiya. Ta tsaya tana haki

washh…don Allah kada ka rama wallahi a

magana jari na karanta labarin Yushau. Kuma ai

kaine kace na rinka karantawa. Dana saki karatu

ai ba cewa nayi ki gwada a kaina ba. Zama tayi

tana mayarda numfashi da kyar. Tana yamutsa

fuska. Gaskiya Daddyn Ammar na gaji daga sosai

daga yin dan gudun nan. Gefen cikina har ya

fara ciwo. sulaiman ya zauna kusa da ita. Zo mu

gani Dijengala ina ne yake ciwon. Abinda yake

mata yasa ta dariya… yace Khadija. Ta dan

nutsu naam. Ina son kara aure…hawaye ya gani

sharrrr yana saukowa ba kakkautawa. Meye na

kuka kuma. Ta sake bari baki me nayi maka?

Wankan nan yanzu sau uku nake yi a rana gashi

ina maka girki da tsafta. Don Allah kace ka fasa.

Yayi murmushi wai dama kina kishina? Sosai ta

bashi amsa tana share hawaye. Na zata wanda

ake so ake kishi. Ta zaro ido to ni an fada maka

bana sonka ne? Kada ma ka yarda nema ake a

hada mu kawai. Ta rike baki Ah…haka kawai ana

so a saka min ciwon zuciya.

 

Ni baki taba cewa

kina sona ba shiyasa ma zan yi

auren….rungumar sa tayi a cikin kunnensa tace I

love you Sulaiman. Wani farinciki yaji sosai ya

rike ta da kyau. To dama kishiyar taki mota ce

…ta dago kai da gaske? Sai murna take. Eh

amma sai nan da wata biyu idan kin gama ajin

mata naji ance kinfi kowa kokari. Daya ajin kuma

sai naga kinyi da daya. Khadija tace zanyi mana

ba dai kana min addua ba? Ina yi Khadija

mommyn Ammar.

Tunda suka yi aure Mal Yakubu bai taba jin

muryar Hanan ba. Kullum sai sunyi waya da Dije.

Da farko fushi yayi saboda yadda hanan din take

nuna bashi da mahimmanci a rayuwarta. Daga

baya kuma yaga gara ya hakura ya cigaba da

adduar shiriya gareta. Zaliha ya kira ya

tambayeta ko Hanan ta canza layi ne don baya

samunta a waya. Ta tabe baki Baba ai ta share

kowa. Nima idan na kira bana samunta. Ya dauko

dari biyar a aljihunsa. Gashi gobe kije gidan ki

binciko min lafiyarta. Har ta mike yace wai

yaushe rabon da kije gidan ma. Naje sau hudu

amma sau daya na shiga. Idan naje kullum

maigadi sai yace bata nan.

Jikin Hanan ya danyi sauki bayan tayi kwana

hudu a asibitin sannan aka sallamota. Ta kara

ramewa tayi baki sosai. Daren ranar data dawo

Ashir yazo ya sameta a kwance. Kanta yayi ya

danneta. Tana ta ihu Ashir kada ka danneni ka

manta ina da ciki? Ya kara matseta kada ki damu

bazan saka miki karfi ba nima ai ina son cikin.

Kamar wata dabba haka ya juyata tana kuka da

hawaye baiji tausayinta ba.

Washegari ta kasa tashi. Wani irin ruwa ne yake

fito mata ta baya. Tun karfe takwas Ashir ya fita.

Tana nan kwance mai aiki ta sanar da ita zuwan

zaliha. Bude murya tayi tana kiran Zaliha iyakar

karfinta.

 

Ko zama bata yi ba saboda wulakancin da Ashir

yayi mata wancan zuwan. Yanzu ma a gate karya

tayi tace ita yar uwar mai aikin gidan ce shiyasa

ya barta ta shiga. Kwala mata kira taji Hanan

tana yi. Da gudu ta hau saman ta ganta a

kwance duk ta yankwane. Ta soma kuka yaya

lafiya? Itama Hanan kukan take tace zaliha ki

kirawo su Mama da Inna suzo su fitar dani daga

gidan nan. Ashir zai kashe ni. Kiyi sauri kafin ya

dawo.Bata jira karshen zancen ba ta sauka cikin

sauri ko bas fada ba tasan Hanan tana neman

taimako. Dole tayi sauri taje gida ta sanar da

Baba. Kofar gidan taji a kulle gam. Ta juyu a

tsorace tana neman mai aikin ta bude mata.

Ashir ta gani da key a hannunsa ya hade rai

sosai. Shegiya munafuka kinzo an fesa miki

gulma ko.

 

FARAR HAIHUWA              40

Mal Yakubu tun yana daukar abin da wasa har

dare Zaliha bata dawo ba gashi baya samun

wayarta. Gaba daya ya rude ya kira Dije ko tazo

gidanta. Tace masa shekaranjiya tazo. Sabuwa

yazo ya tambaya ko sunyi da ita zata kwana.

Tace min ma bazata dade ba amma kasan halin

yaran nan. Kila ta matsa mata ne akan sai ta

kwanan. Zulai tace ni kana bani mamaki duk ka

wani gigice. Ka bari gari ya waye munyi magana

da Uwale zamuje gidan. Uwale dake sallah ta yi

wani gyaran murya ehem ehem harda gyada kai

wai ta gaskata abinda zulai tace. Inna kada dai

ki bata sallarki ya fada yana zama akan kujera.

Ku bari sabuwa zata je ai da girmanku bai

kamata….zata yi ruku’u tace Assalamma alekum

ta wani shafe goshi tare da mikewa, kaniyarka

dan nan. Meye zaka ce bazamu ba. To ni da

zulai zamu je idan sabuwan zata sai taje ni ban

hana ba. Ni ba haka nake nufi ba Inna. Sai ku

tafi gabadaya ba matsala. A wace unguwa gidan

yake? Sabuwa tace ai dayake ba gidan ‘yar so

bane Dije kurma dole ka bari sai yau ka tambayi

inda gidanta yake. Fuskarsa a hade ya dago kai

Dije nine uwarta nine ubanta dole na damu.

Kuma sau nawa tazo gidan nan, shima mijin yazo

amma ita hanan ko akuya na bashi ai ya

waiwayo ni. Uwale tace Hannan din ce akuya.

Yakubu ka kiyayeni fa.

 

Yaro ne yayi sallama suka shigo su biyu da kaya

niki niki. Buhun shinkafa ne, sukari, kwalin taliya

da makaroni ga jarkokin mai. Uwale ta cangolo

kafarta jikinta har rawa yake tace gasu nan ma

yan halak. Dan nan tashi ka bawa Ashiru wurin

zama. Mal yakubu ya kalli Inna duk ta kidime, ya

girgiza kai. Muryar dattijuwa suka ji Zulai ta tashi

kila uwar mijin ce Sabuwa samu ruwan sanyi.

Umma ce ta shigo tare da Ammar sai Dije da

Sulaiman a bayansu. Tsakin Uwale har waje don

takaici. Zulai ta koma ta zauna dabas dama gata

da kiba. Sabuwa ma dawowa tayi ta zauna.

Cikinsu banda zaliha babu wanda ya taba zuwa

gidan Khadijan Sulaiman. Da mal yakubu duk

suka gaisa Umma tana ta gaishe dasu Uwale

sukayi kamar basu ji ba. Dije ta durkusa har kasa

ta gaishesu nan ma sai kaji ance uhm kawai. Ta

kalli Sulaiman wanda ya gama hade rai kamar bai

taba dariya ba. Yayi mata alamar ta tashi su tafi.

Uwale tace kayan da aka shigo dasu bama

bukata fa. umma tace haba Inna kawo muku nayi

asa albarka. Uwale ta tashi tana cilla kafa aikin

banza neman suna. King munyi kama da

mayunwata ne? ta nuna Dije wannan bakar abar

ita zaku bawa abinci uwarta ce tayi gadon tsiya.

Mal Yakubu duk kunya ta kama shi don Allah

Hajiya kuyi hakuri. Inna meye haka ne don

girman Allah. Surukanki ne fa. Ahhh Allah Ya

kiyaye waya sani ko barawo ne? Tun farko ai

cewa akayi aikin gini dan naki yake yi sai daga

baya kuma aka canza labari. Zulai tayi tsaki ai

kece ma kike wani kulasu. Ayi dai mu gani…

Sulaiman ya gama harzuka ganin yadda matarsa

take kuka saboda yadda su uwale ke yi musu

rashin mutumci. Hannunta ya kama ya tayar da

ita tsaye. Tashi mu tafi khadija. Uwale tayi wata

shewa amma dai Allah Ya isa da ka kirata

Khadija, kalle ni da kyau sunana ne, ga fari ga

kyau . ainihin mai sunan ma balarabiya ce. Shine

zaka kira wannan jikar barebarin. Mal Yakubu

kamar yayi kuka yace Sulaiman dauki matarka ku

tafi. Umma kanta boye fushinta tayi amma tasa a

ranta akwai ranar da zata mayar musu da

martani. Ita Sabuwa tunanin ‘ya’yanta yasa basu

isheta kallo ba. A mota Umma da Sulaiman suka

yi ta bawa Khadija hakuri. Ace ranar da tazo

gidan da uwar mijinta ranar ne Inna zata yi mata

tijara irin wannan.

 

FARAR HAIHUWA              41

Wannan daren da kyar Sulaiman ya samu kan

Khadija. Tayi kuka sosai yayi ta bata hakuri. Can

cikin dare tana bacci tana ajiyar zuciya ya kalli

fuskarta da ta kumbura saboda kuka ya sake

rungumeta. Wata tsanar su Uwale yake kara ji

sannan ya yanke shawarar dole ya nemo mata

mahaifiyarta idan kuma bata da rai ya nemo ko

da mutum daya ne a danginta. Maganarsu da

sakina maman Ammar ce ta dawo masa. Yaje

gidansu bayan ya taso daga wurin aiki shine take

sanar dashi irin wulakancin da Ashir yaje yayiwa

Abubakar mutumin da yake neman aurenta

yanzo. A yadda ta fada masa da sassafe yaje

har gidansa yayi masa batacciya a cewarsa ai ba

fasa aurenta yayi ba. Idan Hanan ta kwana biyu

zai auro ta. Abin babu tsari sam…dawowarsa

daga nan ne ya zo ya hadu da zaliha a gidansa.

Dole ya samu lokaci yaje gidansa yayi masa

warning…sakina ta wuce ya zuba ido ayi mata

wulakanci irin wannan. Da wannan tunanin yayi

bacci.

 

Su Hanan da Zaliha kuwa ranar sunga tashin

hankali. Wayar zaliha ya karbe sanan yasa su a

gaba da fada. Da rana nancy mai aikin gidan tayi

abinci mai rai da lafiya aka kaiwa Hanan. Zaliha

kuma garin kwaki da gyada aka bata. Ashir yasa

su a gaba yace kowa sai yaci nasa kada su

mace masa a gida. Ke zaliha kiyi hakuri kinji

ko..dokar gidana ce babu wanda zaici dadi ya

tada kai dashi sai iyalina. Suna kuka suna cin

abincin. Hanan tana gamawa sai amai ya dubi

zaliha to uwar gulma tashi ki guara wurin ai ‘yar

uwarki ce ta yi.

 

Alamun da ya gani cewa hanan na bacci shi ya

bashi damar yin waya taji yana cewa an samu

kanwarta ranka ya dade. Ba dai cewa kayi a sami

wani daga cikin yan uwanta da take so ba wadda

bata da miji. Ina ganin jinin wannan yarinyar ma

zai yi, gobe sai azo a dauke ta. Ya dan yi shiru

ba damuwa ai babu wanda zai zarge mu. kawai

zamu ce bata zo gidan ba.Gaban Hanan yayi

mummunan faduwa. Wai shin waye ma Ashir

kuma meye sanaarsa? Wannan tambayar ita ta

rinka mata yawo a kanta. Tana tsoron tashi ya

sake danneta don zuwa yanzu tasan bayanta ya

gama lalacewa.

 

Kamar masu zuwa sallar idi zulai da Sabuwa duk

sababbin kaya suka saka. Dayake akwai kwadayi

sam uwale ta manta abinda Ashir yayi mata. Sun

riga Sabuwa ma shiryawa. Uwale ko abinci ta

kasa ci. Yau dai duk tsiya sai taci abincin gidan

Ashir. A daidata sahu suka dauka har gidan.

Maigadi da yake bakinsu daya da ubangidan nasa

yaso hanasu shiga. Zulai tace haba dan cin arziki

ya zaka hanani ganin jikata. Ni fa na haifi uwarta

ka ganta ta nuna sabuwa. Uwale ta cangalo yar

kafarta ni kuma na haifi ubanta ba. Jin hayaniya

tayi yawa yasa Ashir fitowa da kansa. Wani

mugun murmushi yayi da ya gansu. Idan yayi

cinikinsu ba karamin kudi zai samu ba. Yayi dan

murmushi inna sannunku da zuwa. Ku shigo

mana. Uwale da zulai har da neman ture juna.

Suna shiga falon sai kalle kalle. Sabuwa dadi ya

kara kamata yarta tayi dacen mijin kwarai. Hanan

da Zaliha ya kira daga sama. Dukkansu a tsorace

suka fito. Suna ganin iyayensu zaliha ta karasa

saukowa da gudu. Ita kuwa Hanan ta gama

tsinkewa da lamarin Ashir tunda taji maganarsa

ta waya jiya. Daga bakin benen ya rikota ya

hanata sauka. Sabuwa ta saki baki me zan gani

ni Sabuwa, Hanan kin ganki kuwa. Duk kin kare

kamar kudin guzuri. Kai yaro sako min ita mana.

Garin yaya zaliha ta kwana baku sanar da kowa

ba. Uwale tace ke kuwa ki bari su sauko mana.

Duk kin tsare su da tambaya. Gashi ko karyawa

bamuyi ba. Hannan sauko ki bamu abinci kinji

yar jikalle.Ashir ya daka musu tsawa ke don

Allah ku dakata duk kun isheni da zance. Ke

Hanan ki zabi wanda kika fi so cikinsu nayi miki

alqawarin babu abinda zai cutar dashi. Sauran

kuwa na gama cinikinsu. Zulai tace kai kana da

hankali kuwa. Wane irin zance ne wannan?

Nancy mai aiki ta fito yallabai sunyi waya fa,

idan ta zabi wanda baza a kashe ba zan shiga da

ita a dora mata maganin. Zata zama kurma kuma

bebeya don haka bazata taba tona maka asiri ba.

Sabuwa tace wai Hanan me yake faruwa ne. Ya

kalleta yi musu bayani sweety. Ai kamar an

kunna rediyo ta sanar dasu komai. Kowa sai

kuka da salati. Uwale tace kina nufin Ashiru dan

luwadi ne? Tace eh inna da kuma yin kudi da

jinin mutane. Meyasa kuka zo? Sabuwa tana

kuka tace yanzu wata biyar dinnan a haka kika yi

su? Mun shiga uku. Hanan itama kukan take

yi…ni kam naga illar son abin duniya. Uwale ta

cangala ta rungumo ta. Ba laifin kudi bane

Hanan ina jin hannu Dijengala ta sa miki. Wasu

garadan maza ne suka shigo gidan su uku. Oga

yace ka nuna wadanda zaa dauka. Ai tuni suka

saka kuka ana rokonsu. Yace idan bata zabi daya

ba shikenan. Gaba dayansu zai kashe. Zulai tace

ni na yarda na zama kurmar don Allah ki zabeni

Hanan. Uwale tace ni dai idan har kayi alqawarin

zaka saketa kuma ka barta tayi rayuwa mai kyau

shikenan. Tana kuka tace ni na dorata akan

wannan hanyar. Zulai tace kinji ko Hanan ki

zabeni. Kema sabuwa zan kular miki da sauram

yaranki. Yanzu gwaggo akan kudi kin zabi na

mutu. Hanan ta kalle shi Ashir na zabi inna

uwale. Sai ta fashe da kuka. Zulai tace sannu

inuwar giginya wato ni na mutu ko? To kinyi

kadan billahillazi baki isa ba. Nice nan kadai

kakarki don babar ubanki ta dade da mutuwa.

Sabuwa tayi saurin rufe mata baki yi shiru

gwaggo. Barni na fadi son raina kinji ko. Ke

uwale Hanan wallahi ba jininki bace. Da cikinta

Inuwa ya saki sabuwa. Zaliha ce kawai yar

Yakubu to kinji. Haka kawai zaki zabi bare ki bar

na gida. Jiri ne ya debi Uwale ta yanke jiki ta

fadi.

 

FARAR HAIHUWA              42

Hanan duk ta gigice yadda taga Uwale tana

shure shure. Ta kalli zaliha ki debo ruwa a shafa

mata mana. Zaliha tayi saurin shiga kitchen ta

taho da ruwan. Da kyar uwale ta farfado ai kuwa

kan Zulai tayi. Yanzu har abin ya kai kiyi irin

wannan sharrin. Jinina ki raba ni da shi. Zulai

tana kokarin kwace kanta tace Sabuwa ki fadi

gaskiya mana. Ya zaki yi shiru kina kallon

gurguwar nan zata yi min rauni. Sabuwa wadda

ta zauna a kasa tana kuka tace Gwaggo ko

Ashiru bai kashemu ba kin riga kin daba mana

wuka. Uwale ta kara cakumar Zulai…Allah Ya isa

tsakanina dake bazan taba yafe miki ba. Tana

kakari saboda taji matsa tace dana yi miki

alfarma ko. Yanzu dai kin yarda bakar fata a

jininku take tunda gashi yar Yakubu da Sabuwa

itama bakar ce. Zaliha da Hanan sai kuka suke yi

sosai. Ashir ya dubi kartin dake tsaye…wai me

kuke jira ne? Duk a sa min su a mota. Fatana

shima uban nasu yazo a kara da nashi kan.

Hajara aminiyar Hanan ta gaji da shirun da take

ji daga wurin kawarta. Aure wata biyar amma

rabon da su hadu tun ranar da aka kaita. Tana

yawan buga wayarta ma bata samu gashi idan

tazo gidan sai mai gadi ya tambayi sunanta.

Tana cewa Hajara zai ce matar gidan bata nan.

Yanzu har ya ganeta. Ita Hajara ta matsu su

hadu saboda mutuwar wulakanci da Babba

malamin tsibbunsu yayi. A kwata aka tsinci

gawarsa. Lamuranta duk sun sukurkuce. Saurayin

da take wa asiri sai da akayi da gaske harda

hukuma kafin ya kyaleta. Tamkar wani bunsuru

ya zame mata. Malamin daya karya asirin yayi

mata nasiha sosai shiyasa take son yadda shiriya

tazo mata itama Hanan ta samu rabo. Yau da

wuri tazo kada tayi rashi saa Hanan ta fita. tana

zuwa maigadin ya sakar mata fuska. Hajiyan

tana ciki dama ta fada min zaki zo yau…sai wani

murmushi yake. Hajara tasan basuyi waya da

Hanan ba shiyasa ta dan ja baya. Maigadi na

ganin haka baiyi wata wata ba ya fizgota ciki

tana ihu. Shima cinikinta zaiyi ya sami rabonsa.

Bata dade da soma ihun ba tayi shiru.

 

Khadija tashi kada ki makara sallah fa. Tayi mika

idanunta har yanzu a kumbure ta bude su da

kyar. Ta dafe kai, Daddyn Ammar kaina ciwo

yake kamar ana sara min guduma. Anya ba

fashewa zaiyi ba? Dafa kan yayi tabbas yayi zafi

sosai…kinga illar kukan da kika yi min jiya ko?

Yar hirar soyayyar ma ta gagara duk irin

rarrashinki dana yi. Ta kara kwanciya a jikansa

to ai baka iya rarrashin bane. Ya rike baki lallai

kinci ganye yarinya. To ni dai ki tashi kiyi sallah

zuwa bakwai ki koma baccinki. Zanje wani wuri

ne anjima kadan. Ina zaka kuma bayan bani da

lafiya ta langabe masa. Hancinta ya ja…ba nisa

zanyi ba sai na dawo zan miki bayani.

 

karfe tara da kwata a layin gidan Ashir tayi wa

Sulaiman. Wayar abokinsa tasa yayi parking a

gefe yana amsawa. Yana cikin wayar yaga

adaidaita ya sauke wata budurwa. Tana cikin

magana da maigadi yaga an fizgo ta cikin gidan

tana ihu. Abin ya daurewa Sulaiman kai sosai.

Yana ta tunani sai ga mota baka mai tint a glass

din ta shiga gidan. Amma kafin ta wuce wasu

maza ya hango a ciki. Zuciyarsa babu abinda

bata kitsa masa. Ya sake kiran Sakina a waya ta

tabbatar masa gidan da yake hange shine na

Ashir. Har yazo kofar gate din ya tuna da Azkar

din safe da baiyi ba..yayi adduarsa sai kawai yaji

zuciyarsa bata aminta da ya shiga ba. Office din

‘yan sanda mafi kusa yaje ya nemi a taimaka

masa kanwarsa ce wani ya sace. Yadda yayi

niyya a ransa idan har ba cutar wannan yarinyar

zaayi ba sai kawai ya wayance yace kama tayi

da kanwarsa.

 

Dukkansu aka jere a bakin motar an daure musu

idanu, baki da hannuwa. Ruwan hawaye kawai

suke yi. Hanan ta durkusa gaban Ashir tana ta

magiya ko a jikinsa. Karshe ma cewa yayi idan

an sami kudin fa ni dake zamu ci da dan jaririna.

Mamaki ne ya kara kamata lokacin da taga

maigadi yana jan Hajara kamar tunkiya a kasa.

Yace yallabai nima ga nawa kamun ayi mata

kudi. Hanan ta tashi da gudu zata je ta riketa

tana kiran sunanta Ashir yasa kafa ya tadeta ta

fadi kasa. Wani ihu ta fasa don akan cikinta

wanda ya fara fitowa ta fadi.

 

Sulaiman yace da yan sandan kunji abinda nake

fada muku ko. Daya daga cikin mazan yace Ashir

kana son matarka ta tara mana jamaa ne? Idan

bata yi shiru ba zan hada da ita. Bugu suka ji a

bakin gate…maigadi yayi dariya yallabai ga wani

naman ya iso. An fara loda su Uwale a mota

kamar kayan wanki maigadin ya bude karamar

kofar gate. Bindiga ya gani a saitin goshinsa yayi

saurin yin baya. Yan sanda sunfi goma suka

shigo gidan tare da Sulaiman. Sai gudu mazan

zasu tsere, shima Ashir hanyar shiga gidansa

yayi da gudu. Yan sanda suka bude wuta sai da

suka harbi mutum biyu daya a kafa daya a

kafada. Sauran duk suka nutsu. Ashir ya rasa

inda zaiyi…yana kokarin shiga gida wani dan

sanda yana cewa stop! Stop!! Ganin bai tsaya ba

ya harbe masa cinya. Sannan aka hada su akayi

waje dasu.

 

Sulaiman da taimakon wani dan sanda suka

kwance su Uwale. Saboda idonta ya dade a rufe

bata gani sosai tace har mun zo lahira ne?

Wayyo ni ko kalmar shahadar ma ban sami yi ba.

Kasa ta durkusa da yar kafarta tace Allah, Allah ,

Allah na tuba Ya Allah. Ina tsoron wuta dama na

zata zan sami lokacin tuba ne. Sulaiman yace

Inna bude idonki da kyau nine sulaiman. Ta kara

sa kuka ayya ashe kaima Ashirun ya kashe ka.

Allah Sarki Dije da Munari ban sami damar

rokonsu gafara ba. Zulai tace ke banza bamu

mutu ba fa. Ai ni na debo da yawa. Uwale na jin

muryar zulai tace shikenan nima wutar za a

sani…na shiga uku ai tunda muka sake haduwa a

lahira zulai nasan tawa ta kare. Wani wawan

mari taji wanda yasa ta dena sumbatu…zulai ce

da wannan aikin. Uwale na bude idonta da kyau

taga Sulaiman. Rungumarsa tayi kamar uwa taga

jaririnta daya bata ta dan albarka nagode..

 

FARAR HAIHUWA              43

Ashir da dukkan jamaar gidansa aka kwashe su a

mota. Zaliha tayi karfin cewa yallabai akwai

mace a ciki. Nancy a cikin toilet ta buya tunda

taji harbi…amma bata tsira ba don kuwa sai da

suka binciko ta.

 

Zaliha ta kamawa Sulaiman suka saka Hanan a

mota. Dukkansu asibiti suka nufa aka ajiye wasu

yan sandan da wadanda aka harba. Sauran kuma

aka wuce dasu police station. Sulaiman ya kira

Mal Yakubu, ummansa da mahaifin sakina tunda

kanin baban Ashir ne. Cikin kankanin lokaci

asibitin ya cika da mutanen da abin ya shafa.

Dakin theatre aka shigar da Hanan saboda yadda

take zubar da jini. Duk suna zaune jugum jugum

har aka fito da ita. Sabuwa tayi ta addua a ranta

Allah Yasa cikin ya zube, me zasu yi da jinin

Ashir. Sai bayan awa daya da yan mintuna aka

fito da Hanan. Ana turata daki likita ya bukaci

ganin iyayenta. Dakin suka shiga Uwale har da

cewa Umma kema ai babarta ce ki shigo. Ina

Sulaiman dan albarka. Yace inna gani tace ku

taho mana. Ai wannan abin ya shafi kowa. Kema

mahaifiyar Ashiru kinfi kowa cancanta da jin

komai. Likita ya dube su yadda suka cika dakin

yace lallai Hanan Yaqub kina da dangi, kin zama

yar gata tayi wani murmushin bakin ciki..sannan

ya cigaba da bayani yana kallon Mal Yakubu. Na

riga na sanar da ita komai, amma kana ganin

dukkan mutanen nan ya kamata su ji komai? Mal

Yakubu yace kayi bayaninka kawai likita ba

damuwa. Ya numfasa to a gaskiya Hanan tana

da hawan jini domin har ya taba zuciyarta. Zulai

ta katse shi ni ba wannan ba ya batun cikin?

Uwale ta wani harareta. Likita ya shareta ya

cigaba da magana. tana bukatar hutu da

nutsuwar zuciya sosai, cikin jikinta bai tabu ba

sai dai dole zamu bata bed rest wato hutu har ta

haihu. Abu na gaba shine bazamu bari ta haihu

da kanta ba saboda taji ciwo sosai a bayanta.

Aiki zamu yi mata. Mal Yakubu cikin rashin

fahimta yace me ya sami bayan? Likita ya

sunkuyar da kansa. Mijin Hanan yana nemanta ta

baya ne don a halin yanzu ya kamu da infection

a wurin sai munyi maganinsa har ruwa yake yi.

To ina ganin haihuwar zata zo kafin ta warke

tunda cikin yayi wata biyar. Inna lillahi wa inna

ilaihi rajiun. Kowa ya na ta salati su Dije harda

kuka. Haj Lami maman Ashir tace cikin kuka

sharri zakuyi masa don kunga baya nan? Likita

yace yana nan mana ana cire masa bullet daga

cinyarsa ne. Ta zaro idanu ta kalli baban Sakina.

Mun shiga uku Alhaji kaga zasu kashe min da.

Zulai tace dole ki fadi haka mana tunda kin

haifawa duniya masifa. Nan dai suka hadu har da

yan sandan dake gadin su Ashir aka sanar da

kowa abinda ke faruwa. Tamkar anyi rashi haka

suka rinka kuka. Musamman da Hanan ta fadi

irin zaman data yi. Mal Yakubu yana zubar da

hawaye ya matsa zai zauna bakin gadon ya

rarrasheta Uwale ta daka masa tsawa. Sabuwa

na jin haka tasha jinin jikinta. Uwale tace dawo

nan munafuka. Dan nan ko kasan Hanan ba

yarka bace? Ashe bayan an saketa da kwana

biyar aka daura muku aure ba iddah ga ciki wata

biyu. Subhanallah!!! Kawunan su duk sun daure

saboda kaduwa da jin zancen. Mal yakubu ya

kalli Sabuwa, Allah zai mana sakayya ni da ke da

mahaifiyarki. Ya kalli Zaliha ita wannan tawa ce

ko kuwa? Tana rawar jiki tace wallahi mal yarka

ce. To ni dai ban ma san hukuncin aurenmu na

amma na sakeki saki uku. Uwale ta rangada guda

Allah Yayi maka albarka. Ta kalli Zulai sai ku

kwashe kayanku a kara gaba. Mak Yakubu yace

dukkanmu zamu tashi ai gidan wannan dan iskan

ne. Hanan tayi kuka sosai. Khadija da Zaliha

suna ta rarrashinta. Mal Yakubu yace bazan taba

kyamarki ba domin ke yar aure ce kamar kowa.

Itama zaliha yar aure ce tunda an sake sabuwa

amma hakkin mijinta ne tayi masa idda kafin

wani ya aureta. Ki koma ki nemi gafarar tsohon

mijinki da Allah SWT. Hanan tace to Baba ni

meye makomata? Yadda tayi maganar abi tausayi

yace da kaina zan kaiki wurin mahaifinki domin

yasan gaskiya amma zan roke shi alfarma ya bar

min ke. Tana zubar da hawaye tace nagode baba

Allah Ya saka maka da alkhairi. Sannan tayi

musu bayanin asirin da tayiwa Ashir. Ku tayani

adduar neman gafarar Allah ko da mutuwa zata

riskeni.

 

Mahaifiyar Ashir ko dakin d yake taki shiga tunda

taji irin sabon da yake aikatawa. Cewa tayi ko a

lahira bata fata sake ganinsa. Ta dubi Baban

sakina ,kaga da yake bata da hakki Allah Ya

kiyayeta har ta sami wani mijin. Tana gama

magana ta fice.

 

A wannan ranar su Mal Yakubu suka tashi suka

koma tsohon layinsu. Gidan Gwaggo suka nemi

alfarma su zauna kafin ya gama gyaran gidansa.

Ba yadda Sulaiman baiyi ba su tafi tare Mal

Yakubu yaki. Haka Zaliha da khadija suka rinka

jinyar Hanan. Itama Uwale da ta leqa lahira ta

dawo ta saduda. Ta amsa laifinta na kara batawa

Hanan tarbiya shiyasa bata guje ta ba tunda abin

ya faru. Mal Inuwa da sauran ‘ya’yansu har

asibitin sun zo. Shima dai yace bazai yafewa su

Zulai ba kuma yana fata Hanan zata rinka zuwa

wurinsa a kauye tunda yasan har abada ita yar

Mal Yakubu ce.

 

FARAR HAIHUWA              44

Bayan Hanan tayi sati biyu jikinta ya danyi sauki

‘yan sanda suka bukaci ta zo domin tayi cikakken

bayani akansa. Tare da iyayenta maza biyu suka

je da Uwale. Nasa iyayen duk sun zame

hannunsu akansa. Da kyar yake tafiya saboda

tadda cinyarsa wurin da aka cire bullet yaki

hadewa. Kafar ta kumbura suntum tana wari.

Suna tsaye mal Inuwa yace cakumi wuyansa

yana cewa ya sakar masa ‘ya. Ashir yayi wani

murmushi ai ni da ita mutu ka raba. Sai dai tayi

min takaba. Mal Inuwa yace kai ni fa wallahi

dan tasha ne in fada maka. Sai na karasa ka

idan yaso a kulleni. Mal yakubu yace kayi hakuri

a gaban hukuma muke fa. yan sanda suka shiga

tsakani sai ga wani dan dattijo ya shigo da wani

yaro kyakkyawa. Suna tsoho rai a bace yace

,kara ya kawo makocinsu ya bata masa jiķa.

Yaron nan maraya ne ga kokari a makaranta.

Lokaci guda ya zama fitsararre mara kunya.shine

na tsananta bincike ya fada min har makaranta

mutumin yake binsa. Wani dan sanda yace Baba

dan dakata ka huta sai kayi bayani cikin

nutsuwa. Wace nutsuwa kuma dan sanda? Kaga

fa duburarsa ta kusa burmawa ga wani ruwa mai

doyi. Wallahi kakarsa har suma tayi jiya. Hanan

ta karewa yaron kallo ai shine wanda ta kama

Ashir da shi. Yaron idanun sa ko gezau ya ga

Ashir yace ai ga saurayin nawa. Kakansa ya

kunduma masa zagi yallabai kun gani ko? Ko

rissina baiyi ba. Dan sanda yace kai kam Ashir

ka gama yawo laifinka yayi yawa. Zamu shiga

kotu ranar litinin idan baka saki matar taka a nan

ba alkali zai raba. Mal Yakubu yace da kakan

yaron kaga ka kai shi asibiti a nema masa

magani sai ka nemi makarantar yara marasa ji a

saka shi domin a gyara tarbiyarsa.

 

Umma tasa Sulaiman ya nemarwa Mal Yakubu

wani gidan amma sam yace bazai shiga ba. Aikin

da aka bashi ya ishe shi. Da kansa da taimakon

abokansa yake gyaran tsohon gidansu. Gwaggo

ba karamin taimako take masa ba da iyalinsa.

Watanni biyu da faruwar wannan al’amari Khadija

ta gama ajin mata a Muslimah Institute. Ta koyi

gyaran jiki, hada humra da turaren wuta, gyaran

gida da girke girke kala kala. Duk juma’a

Sulaiman yana kaita gidansu ta yini idan ya taso

aiki yazo daukarta. Uwale tamkar ta lashe

Khadija da mijinta. Bata gajiya da rokonta tayi

hakuri. Sulaiman yace idan anyi musu walima da

bada certificate daga makaranta zai kaisu

garinsu a nemi Munari.

 

Wani hadadden lace Khadija ta saka. Jikinta duk

ya ciko da kara kyau. Tana saka sarka Sulaiman

yayi hugging dinta ta baya yana shakar kamshin

jikinta. Khadija duk kin canja ko dai…ya dan

shafa cikinta. Tayi dariya ko dai me? Ina ganin

kamar akwai dan saurayi ko budurwa a cikin nan.

Ta sunkuyar da kai tana murmushi…ya rike baki

yanzu shine baki fada min ba, Wata nawa ne?

Bata bashi amsa ba ta fice daga dakin tana

dariya. Ita kanta bata san ko wata nawa bane

kila dai yakai uku. Umma ce ta fara ganewa tace

mata ta dena hawa sama da gudu saboda jikinta.

Tace Umma ai ance motsa jiki yana da kyau…ita

bata gane abinda surukar tata take nufi ba.

Umma tace ai ko dai idan yayi yawa irin wanda

kike yi yana sa mace tayi bari. Ta zaro ido bari

kuma umma? Ai Daddyn Ammar yafa cin abinci a

kasa ma. Kuma fa wallahi sai na rike tray sosai

nake hawa dashi. Zan dai fada masa a hakura da

cin abincin a sama. Haka kawai naje na fadi naji

ciwo. Umma duk yadda taso daurewa sai da tayi

dariya. Tace khadija baki yi gwajin ciki bane?

Nan tasa Khadija jin kunya.

 

Hijab dinta da takalmi ya biyota dasu falon .

Umma sa Ammar duk sun shirya zasu walimar

makarantarsu Khadija. Iyalin gidan Mal Yakubu

da Gwaggo suma daga hotoro Sulaiman yayi

musu kwatancen makarantar.

 

FARAR HAIHUWA              45

Harabar makarantar cike take da motocin

alfarma. Duk bayan wata shida ake yin walimar

dalibai daga ajujuwa daban daban. Masu karatun

boko da islamiya ne kadai suke yin shekara uku.

A wannan bangaren Khadija da sauran karatu.

Iya zamanta Allah baisa sun taba haduwa da mai

makarantar ba. So take tayi mata godiya bisa

wannan taimako da take yiwa ‘ya’ya mata. Su

Inna ta hango ana cangala kafa tasha leshi.

Hanan ciki ya soma nauyi da kyar take takawa

amma ta nace sai tazo. Zaliha kuwa da gudu

tazo ta rungume Khadija. Sulaiman yace kinga

kiyi mata a hankali bana son ganganci. A hankali

kuma Yaya Sulaiman? Ta dan dag gira ko dai

abin yazo? Dundu khadija tayi mata don tasan

Uwale tana jinsu. Ai kuwa uwalen tace yara zaku

sha ruwan zafi indai ba samari kuka haifa ba.

An nunawa baki wurin zamansu. Dalibai masu

fita kowacce suna bangarensu. Yan ajin dinki

sunsa farin hijab har kasa, su Khadija maroon sai

masu saka brown. Yawancinsu duk masu aure

ne. Manyan baki suna daga gefe daya. Bangaren

maza daban na mata daban. An bude taro da

addua , Sadisu Yaqub shine a matsayin mai

gabatarwa.

 

Manyan bakin yawanci manyan yan kasuwa ne

dama aikatan gwamnati. Bayan jawabi daga

babban bako na musamman sai aka kira

shugaban AmJu Airlines wato Rayyan mijin Amal

da Juwairiyya (Ju) wanda yayi alqawarin kujerun

makka ga dukkan dalibai da suka yi ukun farko a

kowanne bangare. Nan da nan wurin ya kaure da

kabbara. Daga nan aka kira Alh Salihu Ado wanda

yayi fice a harkar siyasa da kasuwanci. Yana

fara magana gaban Mal Yakubu da Uwale dake

can gefen mata ya fadi. Tabbas Yaya Salihu ne

yayan matarsa. Hanan tayi yunkurin tashi Zaliha

tace ina zaki? Tace matar nan data taimaka min

a asibiti wadda nake baku labari ita na hango.

Uwale bata ma ji abinda hanan ta fada na don

hankalinta sam baya tare da ita. Shima Alh

Salihu yace ya bada dubu hamsin ga dukkan

wadanda suka yi na ukun farko. Su Khadija sai

murna.

 

Hanan ta sameta suka gaisa. Da farko ma bata

ganeta ba saboda ciki ya sa ta kara kiba. Tace

‘yata ya jikinki ya maigidan? Hanan tace mata

Haj idan an gama taron nan zan miki bayani.

zata sake magana aka fara kiran sunayen ukun

farko a kowanne aji. Hanan tace bari na koma

Allah Yasa a kira kanwata. Ai kuwa tana zama

aka kira ta biyu daga ajin gyaran jiki da girki….

Khadija Yakubu murna a wurin Dijengala baa

magana. Ta mike da sauri ta kallo wurin da su

Inna suke. Suma daga mata hannu sukayi. Ta

kallo Sulaiman yayi motsi da bakinsa wanda ta

gane I love you yace.shi kuwa mal Yakubu

burinsa ayi a gama taron ya sami ganin Yaya

Salihu. Ammar ya baro wurinsu da gudu yana

ihun Mommy.

 

Bayan an gama ne aka bukaci uwar taro tazo ta

rufe wurin da addua da godiya. Sadisu yace mai

masaukin baki muna bukatar ki fito kiyi godiya ga

dukkan wadanda suka sami halartar taron

nan…Haj Maimunatu Ado.

 

FARAR HAIHUWA              46

Cikin nutsuwa ta tashi ta nufi wurin da Sadi yake

tsaye yana mata murmushi. Matan dake wurin

suka rinka cewa Maama suna murnar ganinta.

Sunanta kenan har a makarantar. Tana karbar

mic din tace Assalam Alaikum….sai ji suka yi

cikin daga murya ance La ila ha illallahu

MUNARI????

Gabanta ne ya fadi sosai…kamar muryar Inna

Uwale. Mal Yakubu ya kusa isa inda take tsaye.

Inna Uwale ma ta kusa faduwa daga kujerar da

take zaune saboda saurin da take yi ta tashi. Su

ukun duka kuka suke yi. Tani da sauran yan

uwanta duk sun gane su. Munari muryarta har

rawa take yi amma bata ajiye loudspeaker din

ba. Tace Inna? Malam?

Mal Yakubu wurin da khadija take zaune yaje ya

janyo hannunta. Haka ta bishi suka karasa

Munari tana kallonsu tana kuka jamaa kowa yana

tunanin me yake faruwa. Suna tsayawa gabanta

Mal Yakubu ya kama hannun Khadija yace

Alhamdulillah Dije ga mahaifiyarki.

 

Sulaiman saurin tasowa yayi ya karasa wurin

domin kowa yaji abinda ya fada. Salati da

kabbara kawai ake yi. Munari ta daga hannu ta

shafa fuskar Khadija wadda ta gama jikewa da

hawaye. Rungume juna suka yi sosai suna kuka.

Muryar Munari tana ta kuwwa tana cewa Allahu

Akbar. Sadi ya sauko shima ya tsaya gefen su.

Munari bata saki Khadija ba tace masa ga

mahaifinka Sadi, ga kanwarka. Allah Ya amsa

adduarmu.

 

Uwale ta samu ta durkusa gaban Munari tana

rokon gafara. Tayi saurin dagata suka rike juna

haba Inna don Allah ki bar wannan maganar.

Haduwar mu a nan ya ishemu godiya ga Allah.

Kuzo mu shiga ciki. Uwale tace bani abin

maganar nan don girman Allah. Ba musu ta mika

mata.

 

Jama’a assalamma alekun. Nasan kowa yana

mamakin abinda yake faruwa a wurin nan. Ta

nuna munari, shekaru goma sha takwas kenan

dana sa dana ya saketa babu gaira babu dalili.

Na takura mata, na cutar da ita. Nayi sanadin

mutuwar yarta ma amma bata taba daga min

murya ba. Ta cigaba da kyautata min. Ni kuma

na dora mata karan tsana…Uwale haka ta rinka

bayanin rayuwarsu da irin yadda ta rike Dije. A

karshe tace hakika

 

FARAR HAIHUWA

 

ba a haihuwar

da fari mai kyau bace. Kowanne da da arzikinsa

yake zuwa. Duk abinda Allah Ya bamu don Allah

mu karba da godiya da farin ciki. Arziki da

talauci duk na Allah ne. Ku tayani rokon yaran

nan su yafe min. Na zamewa dana alaqaqai

saboda bakin hali. Gashi yau arzikin bakaken

muke ci gaba dayanmu. Kyau da muni ba sune

mutum ba. Zuciya da albarka daga Allah SWT

shine abin nema daga Allah. Nagode

Mata har da wasu mazan sai kuka sukeyi.

Rayuwar su Uwale ta zame musu wata ishara a

rayuwa. A gaggauce aka rufe taro suka tafi gidan

Haj Maimunatu. Bakin Uwale a bude tace yanzu

munari nan gidanki ne? Kina da miji ne?

Murmushi kawai tayi suka shiga gidan

Gida kam babba ne kuma mai kyau. Sun hadu da

Inno da Inna Ladi.Suka zauna aka gabatar musu

da su Umma da Gwaggo. Maama wato munari

tace ai Haj Bintu kawata ce Allah baisa na taba

ganin surukarta bane. Ta kalli Sulaiman tace

Allah Yayi maka albarka. Hanan tace ai ita ce

matar da nake fada muku Baba. Munari ta taya

su bakin cikin abinda ya faru dasu sosai. Hira dai

har dare ranar. Khadija duk inda mahaifitarta

rasa kafa tana biye da ita. Sadi ya bada labarin

lokacin da suka fara haduwa. Matar Alh Salihu

tace dama ita ce kurmar da ka bamu labari.

Kowa sai dariya da suka rinka jin shirmen da

take yi da. Munari ta basu labarin auren data yi

da kuma rasuwar mijin. Inda tayi amfani da

gadonta wurin fara makarantar da taimakon

yayanta. Dare nayi suka fara tafiya…Umma tace

wa Sulaiman zaka bar Khadija anan ta kwana

biyu ko? Yace ai dole ne Umma. Maama tace

idan ma yaki sai na basu daki.

 

Haka suka kasance cikin farinciki. Bayan sati

biyu aka yiwa Hanan aiki aka ciro mata danta. Dr

Auwal shine likitan da yake dubata tun farko

kuma shi yayi mata aikin. Bayan an ciro dan ya

rike shi yana kallon Hanan yace kinga munyi

kama dashi. Ina fata zaki yarda ya kirani Baba.

Hawaye ne ya zubo mata data tuna waye ainihin

babansa. Dama an raba aurensu bayan kotu ta

yanke masa daurin rai. Yan uwan Hanan na

bangaren babanta duk sun zo. Zulai da Sabuwa

ma sunzo dubata. Da kyar aka samu ta yafe

musu. Iyayen Ashir kuwa sunyi mata sha tara ta

arziki. Domin sunce suna son jikansu. Hatta

Sakina da mijinta sunzo.

 

Yaqub ta zaba a matsayin sunan danta. Suna

kiranshi Abba. Dr Auwal kuwa da gaske yake

yana son ta amince ya aureta. Zaliha ma an

soma daidaitawa da Ali babban dan Alh Salihu.

A ranar sunan ne Munari ta samu yin magana da

Mal Yakubu. Baya taba bari su kebe. A soro ta

hadu dashi zata fita suka gaisa yana sauri zai

wuce. Tace Mal Yakubu zance fa nazo

wurinka….har tuntube yayi saboda mamakin

abinda ta fada. Zan..zan me? Tace zance mana.

Wane iri ya fada cikin rashin fahimta. Tace na

neman aure mana. Ya kalleta har yanzu yana

matukar sonta amma wutsiyar rakumi tayi nesa

da kasa. Haj Maimuna ba Munarinsa ta qauye

bace. Itama tasan meyasa yake gudunta shiyasa

ta zabi yin magana. Maimunatu ina zan kaiki?

Inda ka kaini da Malam. Kinga gidan da nake ciki

fa? Nawa gidan da duk arzikin dana yi namu ne

mal. Ban taba dena sonka ba.

 

Satin daya zagayo aka daura musu aure. Uwale

tana ta kukan farinciki. Ga shi sun koma gida mai

kyau. Gwaggo ta zama yar gida itama. Su

Khadija suna kyautata mata sosai.

 

Rayuwarsu abin shaawa ga kowa kuma darasi ga

mai fahimta. Bayan wata shida Khadija ta haifi

‘ya mace. Sulaiman kamar wani ango don murna.

Umma da kanta take yiwa jaririya wanka. Ranar

sunanta ga mamakin kowa yarinya taci suna

Ramlah. Munari sai da tayi kuka don murna.

Tana ta sa musu albarka. Sadi yace to maama

tunda kika ga wannan yar ni kuma kin sani a

gefe. Dundu yaji mai zafi daga wurin Khadija.

Yace kai kai kai sai na rama. Haba Sadi haihuwa

fa tayi Maama ta fada tana saurim tarewa.

Umma tace eh lallai maganarka ta fito dana.

Sulaiman ya kalli Ammar da ya rungume baby

yace indai tsokana ce to Dijengala ta zarce

kowa. Filo ta jefa masa tana tura baki. Umma

kin ganshi ko. Uwale tace kyale su zan rama

miki.

 

HAMDAN KATHIRAN DAYYIBAN MUBARAKAN

FIH.

About the author

Hausa_Novels

Add Comment

Leave a Comment