Littafan Hausa Novels

Fansar Fatalwa Hausa Novels Complete

Written by Hausa_Novels

Fansar Fatalwa Hausa Novels Complete

 

 

 

 

 

 

 

FANSAR FATALWA

( _Horror Story_ 💀☠️).

 

_Tsarawa / Rubutawa_

 

© *SHAMSIYYA MANGA*

 

*MANAZARTA WRITER’S* *ASSOCIATION*

 

*SADAUKARWA* _Wannan book ɗin gaba ɗayan shi Sadaukarwa ne gareku Anty Hadiza D_ _Auta_Anty Binta Umar Abale, _sis Amira Adam_ _Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda kuke ina son ku fisabillillahi._

 

*NOTE*

Wannan labarin haƙƙin mallakata ne ban yadda a juyamun labari ta kowace fuska ba yin hakan babban kuskure ne.Sannan Labarinnan ƙirƙirarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wani ko wata ba kamanceceniyar labari akasine.

 

*Free book*

 

————————————-

*Bissimillahir rahmani rahim*

 

*001*

_________________________

 

*ƘAWAYE* ! Hmmm idan naji wannan kalmar a kullum sai naji zuciyata kamar zata tarwatse saboda yadda na tsani jin an ambaci kalma mai kama da Ƙawance,tabbas Ƙawaye sun min babbar illa a rayuwata,tabbas Ƙawaye sun zama wani sashe daga cikin sashin tarwatsewar farin cikina,tabbas Ƙawaye sun illata rayuwa ta illa mafi muni. A wasu lokutan Ƙawaye su kan zama alkhairi ga rayuwarmu while a wasu lokutan kuma su kan zama babban sharrin da yake tarwatsa duk wani farin ciki na daga cikin rayuwar tamu kamar yadda ya faru a kaina. A zamanin baya Ƙawaye tabbas su kan zama alkhairi a rayuwar mu amma banda wannan zamanin da muke ciki in da kaso tamanin daga cikin kaso ɗari na Ƙawaye suke ba abun yadda ba,da yawa daga cikin ƙawaye suna zaune da juna ne ba da zuciya ɗaya ba sakamakon hassada da ta yiwa zukatan su katutu.Na tsani Ƙawance! na tsani duk wata kalma mai alaƙa da Ƙawance,na kasance mai wata iriyar zuciya wadda nake saurin yadda da mutane musamman Ƙawaye ina matuƙar basu muhimmanci kafin su min Illah,idan zan zauna da mutum to ina bashi duk wata yarda da ta dangance ni sannan akan Ƙawa na gwammaci a cimun mutunci akan a ciwa Ƙawata,duk bayanin da zan muku ba zaku taɓa gane irin yadda na yadda da Ƙawance ba,sai dai ashe bansan cewa hakan babban kuskure bane nake aikatawa Sai da suka mun Illa kafin na farga. Ƙawaye sun illata rayuwa ta illa mafi muni inda suka yi nasarar tarwatsa duk wani jin daɗi da farin cikin da na mallaka ba kuma komai ne ya janyo hakan ba sai tsantsar hassada da kuma son zuciya.

 

****

Gudu take tsalawa a kan titin wanda zamu iya ƙiran shi da gudun ceton rai duba da yadda take gudun ko kallon inda take jefa ƙafarta ba tayi, dare ne sosai ƙarfe biyu da rabi, bakajin motsin komai face kukan ƙwaruna da baza’a rasa ba,Tsananin duhun daren ya sanya ko tafin hannun ka baka iya gani,ga wata irin tsawa da ake yi mai firgitar wa wadda hakan yake nuni da cewar akwai hadiri sosai a garin wanda a kowane lokaci ruwa zai iya ɓarkewa. Juyawa tayi ta kalli bayanta don ganin shin ko ta tsaracewa abun da take gudu ɗin,sai dai kash! Da ta san abun da zata yi tozali da shi da bata juya ba domin kuwa tana juyawa tayi arba da abun da take gujewa ɗin daf da ita,wani irin ihu ta sake tana fatan ko Allah zai sa wani ya jita domin a kawo mata ɗauki duk kuwa da cewa ba lalle ko an jita ɗin a fito ba,sai dai abun da bata sani ba shine duk ihun da take ɗin babu mai jin ta. Bata ankara ba sai ji tayi taci karo da wani ƙaton dutse da yake gefen titin sai gata warwass a ƙasa take ta fara gangarawa zuwa gefen titin inda yake wani wawakeken rami ne a wajen,daf da ta kusa faɗawa cikin ramin taji an ruƙota buɗe idanunta ta fara yi a hankali tana jin zuciyarta tana mata wani irin bugu, Tarwal ta buɗe idon nata take tayi arba da abun da take gujewa ɗin wanda hakan ya sanya ta ɗaukewar jin ta da ganin ta sakamakon tsoratar da tayi ɗin. Zazzafan ruwan da taji ya sauƙa a jikin ta ne ya bata damar farfaɗo wa daga sumar da tayi ɗin,wani marayan kuka ta sake inda ta fara magana cikin wahaltacciyar murya.

 

“AMRAH dan Allah ki yi haƙuri ki taimake ni kar ki kasheni, wallahi nayi dana sanin duk abun da muka aikata miki dan Allah ki duba girman Allah ki yi haƙuri”.

 

Wata dariya AMRAH ta sake wadda ni kaina sai da kunnuwana suka ɗauke ji na wani lokaci,take kuma ta fashe da wani irin kuka mai ban tsoro a lokaci guda kukan suka shiga fitowa tare da dariya, haɗe fuska tayi kamar ba ita tayi dariyar ba sannan ta fara magana cikin muryar ta mai tsoratar wa.

 

“Ashe kinsan girman Allah!?, Afrah nace ashe kinsan Allah!?,Hmmm wai shin ko kin manta irin tozarta mun rayuwa da ku kayi?,shin kin manta jefamun rayuwa da ku ka yi a cikin tashin hankali da masifa?,ki sani idan maye yaci ya manta to uwar ɗa ba zata taɓa mantawa ba.Sannan ki sani wallahi nayi alƙawarin yadda kuka rabani da farin ciki a rayuwata to tabbas kuma sai kun ɗanɗani baƙin cikin dana ɗanɗana,ai matuƙar ban dawo ƊAUKAR FANSA ba to bazan taɓa yafewa kaina ba, domin kuwa rama cuta ga macuci ibada ne,dan haka ki shirya girbar abun da kika shuka”.

Shedaniyar Suruka Hausa Novel Complete

AMRAH tana kaiwa nan a zancen ta ta saki wata mahaukaciyar dariya wadda ta sanya wa tsuntsaye saurin tashi daga kan bishiyoyin da su ke tsabar tsorata,ita kuwa Afrah take wannan dariyar ta sanya mata ɗaukewar jin ta da ganin ta na wani lokaci, AMRAH ce ta sanya dogon hannunta mai cike da dogayen farata ta cakawa Afrah a tsakiyar ƙwayar idonta,wani gigittaccen ihu Afrah ta sake sannan ta tafi luuuu zata faɗa cikin wannan ramin,harshenta AMRAH ta sanya wanda ya kusa kaiwa tsayin wani mutum ɗin sannan ta nannaɗe Afrah dashi ta jata ta nufi wani Daji da yake gefen titin da ita.

 

*****

Yau gidansu Afrah tun ƙarfe shida da suka farka basu koma ba sakamakon shirin auren Afrah ɗin da suke ta yi wanda za’a ɗaura nan da kwana uku in sh Allah shiri sosai akeyi a gidan kowa ka kalla fuskar shi cike take da farin ciki.

 

Wata farar mata ce doguwa ta fito daga cikin wani ɗaki ta sha ƙunshi na jan lalle abun ka da farar fata sai ya mata kyau sosai,kallo ɗaya zaka mata ka fahimci cewa mahaifiyar Afrah duba da yadda suke mugun kamanni, kallon ƴanmata da suke zaune a kan kujerar falon tayi suna shirya kaya a cikin wani akwati,wanda sun kai su goma sannan tace.

 

“Fadila wai nikam ina Afrah take ne har yanzu bata fito ba gashi har mai mata lalle ta ƙaraso?”.Ta faɗa tana mai kai duban ta ga ɗaya daga cikin ƴanmatan.

 

“Hmmm Mom kinsan halin ƴar gidan naki bata son kwana a cikin mutane wallahi tana ɗakin baƙi jiya a can ta kwana ita ɗaya” ɗaya daga cikin ƴan matan ta faɗa tana mai cigaba da sanya kayan a cikin akwatin.

 

“Ke Husnah je ki taso ta dan Allah ta haƙura da wannan baccin asarar da take ɗin ita da bacci baya isar ta” cewar Mom ɗin tana juyawa dan komawa cikin ɗakinta.

 

Tashi Husnah tayi ta nufi hanyar ɗakin baƙin domin dubowa Afrah ɗin,turus! taja ta tsaya lokacin da ta shiga cikin ɗakin ganin ba kowa a cikin ɗakin,bakin toilet ta ƙarasa tana ƙiran sunan Afrah amma shiru ba alamar za’a amsa mata.

 

Da sauri ta kama handle ɗin jikin ƙofar toilet ɗin sannan ta tura ƙofar to her surprise sai gashi ƙofar ta buɗe shiga tayi cikin toilet ɗin inda ta fara ƙarewa kowace kusurwa da take cikin toilet ɗin kallo sai dai babu Afrah babu alamar ta, juyawa tayi ta fito daga cikin toilet ɗin cikin sauri ta nufi hanyar komawa cikin falon dan sanarwa da Mom abun da yake faruwa ɗin,tun daga bakin ƙofar ɗakin baƙin ta shiga ƙwalawa Mom ƙira cikin ruɗewa.

 

“Kai Husnah wai lafiyarki kuwa kike mun wannan ƙiran haka kamar zaki tashi sama,ina Afrah ɗin?” Mom ta faɗa wadda take fitowa daga cikin ɗakin nata.

 

“Mom ina kuwa lafiya Afrah fa bata cikin ɗakin baƙin”.Husnah ta faɗa tana mayar da numfashi kamar wadda tayi gudu.

 

“Bangane ba wace irin magana kike haka wai Afrah bata ɗakinta?” Mom ta faɗa tana nufar hanyar ɗakin baƙin.

 

Juyawa itama Husnah tayi tabi bayan Mom ɗin inda suma su Farida suka miƙe gabaɗaya tare da rufawa Mom ɗin baya.

 

Duk wani bincike da su Mom zasu yi a cikin ɗakin sun yi shi amma babu Afrah babu alamarta,tun abun bai fara ɗaga musu hankali ba har takai sun fara tsorata da lamarin domin kuwa tun suna bincike iya cikin ɗakin har takai sun fito sauran sashin cikin gidan amma ko mai kama da Afrah basu gani ba,sosai hankalin su ya tashi inda suka koma cikin gidan Mom ta ɗauki wayarta ta ƙira Dad ɗin Afrah domin shaida mishi halin da ake ciki kasancewar tun da yayi sallar asubah bai shigo cikin gidan ba suna massallacin ƙofar gidan tare da mutane.

 

Yana ɗaga wayar Mom ta fashe da kuka tana sanar mishi ganin Afrah ɗin da ba’a yi ba,shima sosai hankalin shi ya tashi inda ya nufo gidan cikin sauri tare da yayun Afrah ɗin.A tsaye suka tarar da mutanen gidan cirko-cirko a harabar gidan tashin hankali ya bayyana ƙarara akan fuskokin su,da sauri mahaifin Afrah ya ƙarasa wajen su

 

“Hajiya mai ya ke faruwa ?” Cewar mahaifin Afrah hankalin sa a matuƙar tashe

 

” Alhaji ina kuwa lafiya mun nemi Afrah sama ko kasa a cikin gidan nan mun rasa” ta faɗa cikin fashewa da kuka.

 

“Innalillahi wa’innailaihi rajiun” mahaifin Afrah ya faɗa cikin tsananin tashin hankali sannan ya cigaba da magana

 

“A garin yaya hakan ta faru? Ya za’a yi a ce a cikin gidannan an nemi mutum an rasa gaskiya abun da mamaki!”.

 

“To Alhaji ni ya za’a yi na sani, wallahi nima abun ya matuƙar bani mamaki kuma duk inda ya kamata mu duba mun duba a cikin gidannan amma bamu ga Afrah ba,wannan wace kalar masifa ce ace ana saura kwana uku biki an nemi amarya an rasa” Mom ta ƙarashe maganar cikin karyewar murya.

 

Shiru mahaifin Afrah yayi na wani lokaci kafin daga baya kuma yace.

 

“Shikennan yanzu bara naje wajen ƴan sanda na sanar da su”.

 

“Amma Alhaji ya kamata mu ƙira Anwar mu sanar da shi halin da ake ciki shima ya sani a matsayin shi na wanda zai auri Afrah ɗin”.

 

Saurin dakatar da ita Mahaifin Afrah ɗin yayi sannan yace

 

“A’a ba za’a yi haka ba, yanzu ki bari muje wajen ƴan sandan muji abun da zasu ce tukunna”ya faɗa yana juyawa tare da nufar wajen motar shi, da sauri wani yayan Afrah wanda ake ƙira da Aliyu ya bi bayan shi.

 

Gudun da Aliyu ɗin yake a titin shi ya sanya basu wani ɗauki tsawon lokaci ba suka isa police station ɗin.

 

Kai tsaye office ɗin DPO suka nufa inda basu wani tsaya ɓata lokaci ba suka zayyane mishi abun da yake faruwa.

 

Shima DPO ɗin sosai ɓatan Afrah ɗin ya tsaya mishi a rai domin kuwa wannan abu da ɗaure kai yake,a hankali ya ɗago kan shi yana juya biron da yake hannun shi sannan ya kalli su Aliyu ɗin yace.

 

“Amma ranka ya daɗe wannan auren da zaku yiwa ƴarku da son ranta ne ko kuwa zaɓin kune?”.

 

Wani murmushin takaici mahaifin Afrah ɗin yayi sannan yace.

 

“DPO meyasa kamun wannan tambayar?”

 

“Ka fara bani amsar tambaya ta tukunna kafin ka jefa mun wata tambayar” Cewar DPO ɗin yana kafe mahaifin su Afrah ɗin da ido.

 

“Tabbas da son ranta za’a yi wannan auren asali ma zaɓin ta ne ba zaɓin wani ba”.

 

Shiru DPO ɗin ya sake yi kamar mai nazarin wani abu sannan ya dube su yace.

 

“Shikennan Alhaji za ku iya tafiya mu kuma inshAllah zamu yi duk mai yiwuwa dan ganin mun nemo inda Afrah take,ina buƙatar photon yarinyar taka idan kuna dashi ko a waya ne ku tura mun,sannan gidan ka ma ku kasance a cikin shiri domin kuwa a kowane lokaci binciken mu zai iya biyowa ta cikin gidan naku. Abu na ƙarshe shine ina son ka bani address da kuma wasu information akan wanda Afrah zata aura shima zamu yi bincike a kanshi domin kuwa a halin yanzu ko kuma baku fice daga cikin suspect ba”.

 

Sosai mahaifin Afrah suka cika da mamakin maganar DPO ɗin har ya buɗi baki zai ce wani abu Aliyu ya dakatar dashi inda ya sanarwa da DPO ɗin duk abun da ya buƙata game da Anwar ɗin.

 

Ranar gidan su Afrah kwanan zaune suka yi domin kuwa waɗanda suka iya yin Bacci a cikin gidan ƴan ƙalilan ne,kowa ka gani hankalin shi tashe yake.

 

Washegari kuwa ƙarfe takwas dai-dai ƙiran wayar DPO ya shigo wayar mahaifin Afrah ɗin a lokacin gaba ɗaya ƴan gidan suna hallare a cikin falon gidan sun yi tsumu-tsumu kamar an jiƙa ɓera a buta.

 

Cikin sauri mahaifin Afrah ɗin ya ɗaga wayar gabanshi yana dukan uku -uku sannan yayi sallama.

 

“DPO ya ake ciki fatan dai akwai wani sabon labari?”.

 

“Alhaji gamu a ƙofar gidan ka zamu iya shigowa”.Fita Mahaifin Afrah ɗin yayi sannan ya musu iso tun da ya isa inda suke faɗuwar gaban shi ta tsanan ta sakamakon arba da wani abu da yayi an lulluɓe shi da wani farin yadi a ajiye a ƙasa.

 

“DPO ya ake ciki?” Mahaifin Afrah ɗin ya jefawa DPO wannan tambayar cikin tsananin tashin hankali da rawar murya.

 

“Alhaji mu shiga ciki tukunna domin kuwa maganar ba zata yiwu a nan wajen ba”

 

Gaba mahaifin Afrah ɗin yayi inda DPO ya umarci wasu ƴan sanda guda uku da su ɗakko wannan abun da yake lulluɓe ɗin sannan suka bi bayan shi suka shiga cikin gidan,a falon gidan suka yada zango inda suka ajiye wannan abun da ba wanda ya san meye a ciki.

 

“Bisimillah DPO ga wajen zama” Mahaifin Afrah ɗin ya faɗa yana nuna musu kujera.

 

“Alhaji ai zama bai kama mu ba tukunna, inspector jamil buɗe musu wannan gawar su gani ko an dace”

 

Daram gaban duk jama’ar cikin falon ya buga jin abun da DPO ɗin ya faɗa,ai basu ƙara tsinkewa da lamarin ba sai da suka yi arba da abun da yake cikin wannan zanin a lulluɓe,take wasu daga cikin mutanen falon suka dinga zubewa suna sumewa masu ƙarfin halin cikin sune kawai suka tsaya a ihu kawai.

 

*MANGA* ✍️

_Comment_

_Share_

_Fisabillillahi_.

[22/01, 6:07 pm] +234 706 094 3991: *FANSAR FATALWA*

( _Horror Story_ 💀☠️)

 

_Tsarawa/Rubutawa_

 

© *SHAMSIYYA MANGA*

 

*MANAZARTA WRITER’S* *ASSOCIATION*

 

*SADAUKARWA* : _Wannan book ɗin gaba_ _ɗayan shi Sadaukarwa_ _ne gareku Anty Hadiza D_ _Auta, Sis Adam Amira_ _Alkhairin Allah ya_ _kai muku a duk inda_ _ku ke ina son ku_ _fisabillillahi_ .

 

*Free book*

 

—————————————-

*Bissimillahir rahmani* *rahim*

 

*002*

__________________________

 

Ba komai mutanen suka yi arba da shi ba wanda ya firgita su face arba da suka yi da gawar Afrah wadda idanunta duka biyu suke a ƙwaƙule, idan ban da shi babu wani abu da zaka kalla a jikin ta kace gawa ce domin kuwa babu ta inda aka bar alama ko shedar irin kisan da aka mata ɗin.

 

Ihu ne ya cigaba da tashi a cikin falon nan da nan kafin kace mai masu raunin zuciyar cikin su har sun fara yanakar jiki suna zubewa a ƙasa suna sumewa, ciki kuwa har da mahaifiyar Afrah, masu dauriya da ƙarfin halin su ne waɗanda suka tsaya a kuka kawai, gaba ɗaya falon ya hautsine baka jin komai sai iface-ifacen mutane. Duk yadda wannan Dpo ɗin ya su ya sa mutanen falon su yi shiru abun ya gagara,da ƙyar dai wasu suka ɗan tsagaita inda Dpo ɗin ya dubi mahaifin Afrah mai suna Alhaji Shareef yace.

 

“Alhaji kuyi haƙuri da abun da ya faru ku ɗauki hakan a matsayin ƙaddarar ku,domin kuwa ita ƙaddara bama iya hanata aukuwa,duk yadda muka so mu kauce mata hakan ba zai taɓa yiwuwa ba,sai dai mu rungume ta hannu bibbiyu ko da kuwa bata zo mana da daɗi ba” Dpo ɗin ya ƙarashe maganar cikin son ya kwantarwa da mahaifin Afrah hankali duk da kuwa ya san abu ne da kamar wuya.

 

Ɗago kai mahaifin Afrah yayi wanda idon shi suka kaɗa suka yi jawur sannan cikin shesheƙar kuka ya fara magana.

 

“Yanzu Dpo da gaske ƴata ce Afrah a kwance a gabana?, innalillahi wa’innailaihi rajiun,wannan wace kalar BAƘAR ƘADDARA ce haka?, fisabillillahi mai Afrah ta aikata wanda ta cancanci wannan hukuncin?, Wallahi duk wanda ya aikata mana wannan mummunan aikin ba zamu taɓa yafe mishi ba”. Ya ƙarashe maganar yana fashewa da kuka kamar wani ƙaramin yaro.

 

“Ahhh Alhaji Shareef abun da nake so da kai shine dan Allah kuyi haƙuri a halin yanzu Afrah addu’ar ku kawai tafi buƙata, shi kuma duk wanda yake da hannu a cikin wannan aika-aikar inshAllah zamu yi iya bakin ƙoƙarin dan ganin mun gano ko waye kuma mun bi mata haƙƙin ta”.

 

“Wallahi duk wanda ya aikatawa ƴar uwar mu wannan aikin zaluncin ba zamu taɓa yafe masa ba, sannan ko waya sai mun yi Shari’a da shi matuƙar aka gano shi” Cewar Aliyu yayan Afrah.

 

A dai-dai wannan lokacin ne kuma Anwar saurayin Afrah da zata aura ya faɗo cikin falon kamar an jaho shi,kallo ɗaya zaka yiwa fuskar shi ka hango tsantsar tashin hankalin da yake kwance a kanta. Da gudu ya ƙarasa kan gawar Afrah ɗin da take shimfiɗe a tsakar falon inda ya zuba duka gwaiwowin shi a saitin ta,kamar wani zauttace haka ya fara magana.

 

“Afrah wana marar imani da tausayin ne ya aikata miki wannan ɗanyen aikin?, Afrah meyasa za’a raba mu?, Afrah meyasa zaki tafi ki barni?, Kai! Ƙarya ne Afrah ki tashi nasan kina jina kuma nasan baki mutu ba, Afrah dan Allah ki tashi ki gayamana wanda ya aikata miki wannan aika-aikar” Anwar ya ƙarashe maganar cikin sakin wani kuka mai ratsa zuciya ga fuskar shi duk ta ɓaci da hawaye da majina.

 

DPO ɗin ne ya ƙarasa inda Anwar yake tsugune sannan ya dube shi cikin tausayawa ya fara magana.

 

“Haba mana aboki na be a man mana,ya zaka zauna kana kuka kamar wata mace, common share hawayen ka dan Allah,ka sani kamar yadda na muku alƙawari inshAllah zamu yi iya bakin ƙoƙarin mu dan gano wanda yake da hannu a cikin wannan kisan”. DPO ɗin ya ƙarashe maganar cikin ƙarfafa gwaiwa.

 

Hannu Anwar ya sanya ya share hawayen da suka ɓata mishi fuska sannan ya dubi DPO ɗin yace.

 

“DPO dole nayi kuka domin kuwa an cuce ni matuƙar cutarwa, DPO wannan wana irin zalunci ne ace sai ana saura kwana uku aure na a kashe mun mata,ai kuwa kaga kuka ya zama dole, Allah ya ji ƙanki Afrah, Allah ya tona asirin duk wanda ya miki wannan aika-aikar”.

 

A dai-dai wannan lokacin ne kuma mahaifiyar Afrah ta farka daga suman da tayi ɗin,inda ta farka da wani razannannen ihu ta koma kamar wata taɓɓaɓiya ta dinga wani irin fisge-fisge tana wasu irin surutai marrassa kan gado.

 

“Ku ƙyale ni in je wajen ƴata wallahi ƙarya kuke mun ƴata bata mutu ba bacci take”, Haka ta dinga faɗa inda daga baya sai ta koma daga ta yi kuka sai kuma tazo ta kwashe da wata irin dariya irin dai ta mahaukata sabon kamu,da ƙyar aka shiga riƙe ta tana fisgewa duk wanda yake cikin falon sai da ta bashi tausayi, da yawa sai suka daina kukan mutuwar Afrah suka koma kukan tausayawa mahaifiyar ta.

 

Waya DPO ya ɗaga inda ya ƙira ma’aikatan asibiti akan su zo su wuce da gawar Afrah mutuary har sai an kammalla bincike, lokacin da ma’aikatan lafiyar suka ƙaraso sai da likita ya ƙara duba Afrah inda ya ƙara tabbatar mu su da cewar Afrah fa ta riga mu gidan gaskiya. Ita kuwa mahaifiyar Afrah sai da aka mata allurar bacci wai dan ta yi bacci amma kamar wanda aka ƙara kunnata haka wannan allurar ta maidata.wani tashin hankali ma sai da aka zo fita da gawar Afrah a nan ne fa aka kafa sabuwar sumewa daga wajen ƙanne da yayun Afrah ɗin ita kuwa mahaifiyar ta daman tunin ta sume ya kai sau ba adadi.

 

Haka dai suna ji suna gani aka fice da gawar Afrah ɗin aka kaita asibiti aka ajiye ta a mutuary har zuwa sanda ƴan sanda zasu gama binciken su.

 

*****

 

Yau Sati guda Kennan da mutuwar Afrah amma gidan su afrah kamar yau aka yi mutuwar domin kuwa su kullum mutuwar sabuwa take zamowa a wajen su.

 

A ɓangaren Anwar ma kullum a gidan su Afrah yake yini har zuwa dare kafin daga bisani ya tafi gidan su. Yau ma kamar kullum ƙarfe goma ya tashi tafiya gida kamar yadda ya saba, lokacin da ya isa gidan bai tarar da ƴan gidan su a falo ba kowa ya shige ɗaki ya kwanta, shima ɗakin nashi ya nufa,inda ya tura ƙofar ɗakin ya shiga,kasancewar wutar ɗin ɗakin a kashe yake ya sanya ya nufi wajen makunnar wutar ya kunna, tabbas da Anwar ya san abun da zai yi tozali da shi idan ya kunna wutar da bai fara kunnawa ba, lokacin da haske ya gama gauraye illahirin ɗakin ne ya juya da niyyar nufar wajen gadon shi. Turus! Ya ja ya tsaya sakamakon arba da mace da yayi a zaune a tsakiyar gadon shi ta juya mishi baya kanta ba ɗankwale gaba ɗaya gashin ta ya barbazu a kan gadon, wani mugun tsoro ne ya mamaye zuciyar Anwar ɗin har sai da ya haɗiyi wani yawu ji kake Muƙuttt wucewar yawun zuwa maƙoshin shi, a hankali ya fara takawa ya nufi wajen gadon duk da irin bugun da zuciyar shi ta ke mishi hakan ba sai ya dakata da isa wajen gadon ba,hannu ya miƙa da niyyar juyo da fuskar ta ta sai dai tun kafin hannun nashi ya sauƙa a jikin ta ta juyo da kanta suka yi arba da juna fuskarta shaɓe-shaɓe da hawaye sai dai kuma a maimakon ya ga ruwan hawaye sai ya ga jini ne yake kwaranyowa daga cikin idanun nata, suman tsaye Anwar yayi cikin rawar murya ya fara nuna ta da hannun shi yana ƙoƙarin furta sunan ta Amr….. Amma ina! Tun kafin ya ƙarasa yaji kamar an saka igiya an ɗaure mishi wuya take ya yanki jiki ya faɗi a wajen.

 

Anwar bai tashi tsintar kan shi a ko ina ba sai a gadon asibiti ana mishi ƙarin ruwa, ƙoƙarin miƙewa zaune yake amma ya kasa a hankali ya fara ƙoƙarin tuno abun da ya faru dashi amma abun mamaki hakan ya gagara duk wani ƙoƙarin sa na ganin ya tuno abun da ya faru ɗin ya kasa inda take ya ji kan shi ya ɗauki wani matsanancin ciwo,dafe kan nashi yayi tare da runtse idanun shi, mahaifiyar shi ce ta fara mishi sannu.

 

“Sannu Anwar ka tashi ya jikin dai?”. Ta jefa mishi wannan tambayar da sauri yayi saurin buɗe idanun shi da suke a runtse dan ganin wanda yake mishi sannun domin kuwa a maimakon ya ji muryar mahaifiyar shi sai ya ji wata murya daban wadda ko shekara ɗari yayi wannan muryar bazata taɓa zama sabuwa ko baƙuwa a gare shi ba,ga mamakin shi yana buɗe idon nashi sai yaga mahaifiyar tashi ce take mishi sannu, Innalillahi wa’innailaihi rajiun ya shiga maimaitawa a cikin ran shi tare da jefawa kan shi tambayar to mai hakan yake nufi?, Mai yasa muryar ta take mishi gizo?. A hankali ya fara jin alamar kuka a kusa dashi saurin juyawa yayi dan ganin waye aikuwa a take yayi arba da ita a zaune a kusa dashi fuskar ta sharkaf da hawaye, wani ras ya ji gaban shi ya faɗi,da sauri ya juya ya dubi inda mahaifiyar shi take zaune ko ita ma taga abun da ya gani ɗin,sai dai daga yanayin fuskarta ya fuskanci cewa bata ga abun da ya gani ɗin ba,sake juyawa yayi inda take zaune ɗin still tana zaune sai dai a wannan karon murmushi take mishi, addu’a ya fara yi duk addu’ar da tazo bakin shi, aikuwa ba’a ɗauki lokaci ba ya nemeta ya rasa, kallon mahaifiyar shi yayi sannan ya buɗi baki da niyyar sannar da ita abun da ya faru ɗin sai dai kamar mai cutar mantau haka yaji komai ya kuma shafewa a ƙwaƙwalwar shi.

 

*****

 

*AHMADU BELLO* *UNIVERSITY ZARIA*

 

Babbar jami’a ce da ta amsa sunan ta jami’a domin kuwa tana ɗaya daga cikin manyan jami’o’in da muke da su a Nigeria,ko ina ka waiga a cikin jami’ar ɗalibai ne ta ko ina kowa yana harkar gaban shi. Wata matashiyar budurwa na hango wadda a ƙalla bazata haura shekaru ashirin da biyu zuwa da uku haka,tafe take a cikin makarantar ta fito daga wajen Admin Block inda ta nufi hanyar hostel ɗin mata, fuskarta kaɗai zaka kalla ka fuskanci tsananin farin cikin da take ciki,wayar ta ce ta fara kuka alamar tana neman agaji,ɗaukan wayar tayi murmushi shimfiɗe a kan fuskar ta sannan ta kara wayar a kunne tare da furta.

 

“Dad barka da rana”

 

Daga ɗayan ɓangaren wani dattijon mutum ne zaune a wani ƙayattaccen falo wanda ya gaji da haɗuwa amsawa yayi tare da furta.

 

“Daughter ya result domin kuwa idan ban manta ba yau kika ce zasu manna muku?”.

 

Murmushi tayi kafin daga bisani tace.

 

“Dad as usual Kai ma kasan ai bazan taɓa baka kunya ba,Dad result ɗina yafi na kowa kyau na kasance wadda tafi kowa highest mark a Depertment ɗin namu”.

 

“Masha Allah Daughter congratulations Ubangiji ya cigaba da dafa miki,ya sanyawa karatun ki Albarka”.

 

Da Ameen ta amsa sannan suka yi sallama ta kashe wayar, a dai-dai sannan kuma ta ƙaraso bakin ɗakin su,inda ta sanya mukuli ta buɗe ƙofar,Chaɓal taji ta jefa ƙafarta a cikin wani abu mai yauƙi, cikin sauri ta kai duban ta kan ƙafarta da take ƙoƙarin zarewa daga cikin abun, Daramm gaban ta ya faɗi sakamakon arba da jini da tayi male-male a tsakiyar ɗakin nasu kamar an yanka rago,jikin ta ne ya fara wani irin karkarwa take wata irin zuffa ta fara keto mata, ai bata gama shiga ruɗani ba taga wannan jinin ya fara dunƙulewa waje guda a hankali har ya gama curewa waje ɗaya sai gashi ya fara komawa siffar mutum, wata irin mummunar hallita ce ta bayyana a gabanta idon hallitar guda ɗaya ne kuma a tsakiyar ka,sai wasu ƙafo masu matuƙar tsini guda biyu da suke gefen idon, tsayin hallitar kuwa ba zai faɗu ba domin kuwa tsayin ta har ya tokare silik ɗin ɗakin, lokaci guda kuma fuskar wannan hallitar ta juye zuwa fuskar Amrah. Ido ta zaro waje take kuma ta buɗe baki da niyyar yin ihu sai dai kafin ta kai ga sakin ihun taji wata irin guguwa ta kwashe ta inda ta jita a sama tana gudu kamar wani jirgi,da ƙoƙarin da take na ganin ta buɗi baki tayi ihu ko zata samu mai kawo mata agaji hakan ya faskara inda aka shiga gwara mata kai a kowane kusurwa na cikin ɗakin,take aka haɗa mata jini da majina,sai da ta suma ta farfaɗo saboda azaba kafin daga bisani aka yi jifa da ita ta bugu da jikin ƙofar toilet ɗin ɗakin,sannan aka shiga ƙiran sunan ta da wasu irin muryoyi mabanbanta.

 

“Azraaaaaaàa!,Azraaaaaa!, Azraaaaaa! yau zaki girbi abun da kika shuka,yau zan ɗauki Fansar abun da kuka aikata mun, FANSA! FANSA!FANSA! Na dawo ɗauka”. Ana kaiwa nan a maganar aka bushe da wata irin dariya mai haɗe da kuka wadda tayi sanadiyar Sumewar Azraa.

 

*MANGA*✍️

_Comment_

_Share_

_Fisabillillahi_

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment