Littafan Hausa Novels

Fansa 2022 Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Fansa 2022 Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Fansa 2022

 

Bismillahir rahamanur rahim

 

Sadaukarwa ga Hassan ATK, Hussain 8k,Abubakar saleh Kurami, Sdeen, Abubakar Ak Saraki, Muhammad Kareem“`

 

 

*Free page 1*

 

 

 

Karfe sha biyu na dare AHUTA CLUB, club ne da ya amsa sunan shi, idan kana ciki bazaka gane cewa darene ba,saboda tsananin hasken fitilun wajen ko’ina tamkar rana,a wani waje da naga an rubuta VIP wajene wanda babu hayaniya.

 

Wani saurayi naga ya fisge wayar dake hannun wata budurwa,”Magana fa zamuyi ba chatting ba” tunda muka shigo wajen nan kiketa latse latsen waya.

Namijin Kishi Hausa Novel Complete

Ya fada hakan tare da ajiye wayar saman table din gabansu

 

murmushi budurwar tayi lokaci guda ta zuba mashi idanuwanta masu tsananin haske.

 

Ya jawo hannunta ya rungume a hankali yana fadin “Menene ya hana ki zuwa school Rahma tsawon one week?”

 

Takai hannu tadan bigi goshin tah tare da fadin kamar kasan abinda ya dami zuciyata kenan Dady ya sakaman takumkumi ya kunsheni cikin gida,tun kan case din nan na birthday din Ruky.

 

Usman ya sauke numfashi a hankali yana fadin “akan me? menene yashafi karatunki a ciki?Duk dai abinda zasuyi sai dai suyi hakuri tunda sun ruga sun haifomu,ni duk abinda suke magana banga wani abu me muni da muke aikatawa ba.

 

Ta daga kafada tana fadin abinda nagani kenan Usman ni kadai nasan takaicin da nikeji, abin kunya ne a gareni ,a ce kamar ni!!,da ajina,da wayewata,in rinka zama ‘Order’, zaman Controlling.” Rahma ke wannan maganar da alamun abin yana bata Mata rai.

 

“Ya kamata dai kiyi Kokarin dawowa school don lecture’s nata wuce ki Usman ya fada yana duba agogon hannunshi wanda ya nuna karfe daya da rabi na dare,ya mike yana fadin bari inje SAWABA hotel in kwana gida basu san na shigo garin a yau ba.

 

 

Rahma ta mike tana dariya Usman akwai ka da kumbiya kumbiya muje nima ka maidani gida kada Aunty ta lura bana nan,su Fauza ma sun shigo club amma inaga ba yanzu zasu tafi ba bazan tsaya jiransu ba.

 

 

Usman shima dariya yake ya gyada kai bazaki gane ba wallahi wasu abubuwan dole saida sakayawa muje in saukeki kema ai albarkacin maigadi kikeci da yake bude maki get,in ba haka ba kila ba ganinki zamu rinkayi ba.

 

Rahma ta turo baki tana fadin wllh Usman abin nan yana damuna kullum in zan fita na dunga sanda ina waige waige kenan kamar wata barauniya,

…………………………………….

Washe gari 10am

 

Babban falone da yasha kayan alatu daga can daning area baka jin karan komai sai na cokula, Dady ya ture filet din abincin dake gabanshi ya mika hannu ya dauko ’tissue’, yana goge baki tare da fadin”Allah yayi maki albarka Rahma” Mami da Aunty amarya suka amsa da Amin Dady.

 

Abdallah dake gefen dama ya gyara zama yana fadin “Dady babu albarka ga wanda ya auri duniya!” Ya ida maganar yana huci kamar wanda ya fito filin daga,dama tunda ya zauna yaketa cin magani.

 

Dady ya zaro idanu waje yana fadin “wacce irin magana kakeyi haka Abdallah waye kuma ya auri duniya?”

 

‘Rahma ce Dady’

 

Abdallah ya Fadi kai tsaye.

 

Dady ya kalli Rahma a zuciyar shi yana fadin ruwa baya tsami banza duba da yadda Rahman tasha jinin jikinta.

 

Mami ta katsesu da fadin Menene tayi har kake kira mata ta auri duniya,ka kuwa san wanda duniya ta aura?

 

“Mami har yanzu Rahma bata dena zuwa club ba”

 

What! su ka hada baki wajen fadi

 

ba suga mikewar Dady ba sai saukar maruka sukaji lokaci guda ya rufeta da duka yana fadin “kaico Allah yayi wadaran halinki wato fitar daren dana hanaki baki bari ba,ganin babu wanda zai ceceta cikinsu yasa ta tashi ta ruga da gudu,

 

wa je take neman fita hakan yasa Abdallah yayi saurin damkota janta yake keeee har ya dangane da dakin ta tunkudata yayi ta fadi kasa har saida kashin kafar ta ya lankwashe ta bude baki ta fasa wata kara kamar wacce aka yanka,shut up ya buga mata tsawa tsitt tayi kamar ruwa ya ci ta sai hawaye dake ambaliya a idanunta,ya bita da wani mugun kallo,ke baki isa kisawa mahaifinmu hawan jini ba,ni zanyi maganinki wawuya,kuma maigadin da kike hada baki dashi yau zai bar gidan nan shasha wacce batasan ciwon kantaba,yana gama fadin haka ya fice tare da bugo Mata kofar.

 

Gaba daya kukan nata nemanshi tayi ta rasa ita kuwa me zatayiwa Abdallah ta rama duk wani kunci dayake sakata,me yasa duk wani abu sai yace batayi daidai ba?

 

shine silar duk wani takumkumi da aka saka mata,duk wani motsi nata yana biye da ita,ta rasa wane irin sa idone wannan,tadan muskuta zata gyara zamanta lokaci guda ta fashe da kukan shagwaba tana yarfe hannu da alamun mugun nan yayiwa kafar ta illah.

 

Da dubara taja duwawu har zuwa kan gado anan ta baje tana maida numfashi tare da tunanin yadda zata kwatarwa kanta yanci da haka baccin wahala ya kwasheta .

 

 

A can falo tun barin Abdallah da rahma falon fadan Dady ya koma kan Mami fada yakeyi kamar itama zai rufeta da dukan,gani yakeyi duk wata lalacewar tarbiyyar Rahma Mami tanada hannu a ciki,shiru kawai Mami tayi amma wannan hali na Dady yana kona Mata rai babu halin Rahma tayi laifi idan ya tashi fada saiya hada da ita,Aunty keta bashi hakuri tana nuna mashi Mami na kokarin kulawa da tarbiyyar Rahma,Rahmar ce fitinan niyar yarinya,ganin dawowar Abdallah falon yasa duk sukayi shiru,duk da cewa wannan ba bakon al’amari bane a wajen shi Abdallah,a kullum Rahma zatayi laifi to fadan akan Mami zai kare wannan dalilin kesa yana kara tsanar yarinyar,gaba daya ta hana iyayen su zaman lafiya.

 

Dady zan je gida dagacan zan wuce asibiti akwai wadanda nayiwa aiki jiya inason ganin yanayin jikin nasu Abdallah ke fadin haka dai dai ya karaso wajen daning area, Dady yace “to idan ka dawo ka shigo akwai maganar da nikeson muyi”Abdallah yace ok insha Allah Aunty na tafi Mami saina dawo, dukkan su addu’a sukayi mashi tare da fatan dacewa ya fice daga falon.

…………………………………….

 

Tun bayan gama duba marasa lafiya da yayi ya koma office dinshi, ya kasa tsinana komài akwai aiyukan da yakeson shigarwa cikin wasu files, zuciyar shi gaba daya a cunkushe take tun ganin da yayi mata a jiya lokacin da maigadi ke bude mata get misalin karfe daya da rabi na sulusin dare, lokacin da yakamata ace kowanne bawa yana kan gadon shi yana bacci domin dare akace mahuta bawa,yayin da wasu ke saman abin sallah dan neman dacewa wajen ubangiji, amma ita lokacinne lokacin yawon ta kwararo kwararo,jin an dafashi yasa ya juyo dan ganin wanda ya shigo kasancewar ya juyawa kofar bayane, sannan tsananin duniyar tunanin daya tafi yasa kwata kwata beji karar bude kofar ba.

 

 

Doctor Ishak da ke kallon abokin nashi ya tabbatar ba lafiya ba saboda yanayin idanuwan Abdallah da suka canza launi zuwa jaa, Abdallah be iya magana ba sai nunawa Doctor Ishak kujera yayi da hannu, Doctor Ishak ya zauna yana kure Abdallah da kallon tuhuma tare da fadin “Menene matsalar ka Abdallah?” Tun shigowata naga alamun kana cikin damuwa wanda ya hanaka jin bude kofata da maganar da nayi maka kafin in dafaka.

 

“Rahma ce Ishak,”Abdallah ya fadi hakan a rikice idanuwan shi gaba daya sun rune sunyi jawur,yarinya daya tana neman gagara.

 

 

Cikin mamaki Doctor Ishak yace Rahma kuma Abdallah me kuma ta karayi inace kace hatta makaranta yanzu an hanata zuwa.

 

Abdallah yace club din da aka hanata zuwa ashe bata bari ba,jiya akan idanuna maigadi ya bude mata get ta shigo misalin karfe daya da rabi na dare ya ida maganar yana cije lebe.

 

‘Ishak yace amma baba maigadi anyi tsohon banza duk yadda muke kyautata mashi shine shi zai cutar damu,wllh wayewar nan ta Rahma bata tsinana mata komai ba sai tabewa,itafa duk wannan abun da suke gani suke wayewane.

 

Abdallah yace harda ma gata Ishak,Ina takaicin soyayyar da Dady da Mami suke nunawa Rahma a baya yanzu gashi yarinyar nan tsaye muke a kanta amma taki tankwaruwa nayi dukan nayi hargagin duk a banza,tanajin tsorona amma be hanata zuwa tayi wata fitinar da zata bata mana rai.

 

Ishak yace inaga harda kuruciya ma na damunsu, Allah dai ya kyauta,kaga lokacin sallah yayi muje masallaci idan mundawo ma kara tattaunawa.

 

 

*. *. *

 

Maganar da taji sama-sama yasa ta farka daga baccin wahala da ya kwasheta ta bude idonta ta na kallon rufin dakin, kafin ta yunkura da niyyar tashi,azaba tasa ta koma ta kwanta tana matsar kwalla,dai dai lokacin Mami da Lauratu suka shigo cikin dakin, Mami ta karasa bakin gadon ta zauna tare da fadin Menene kuma har yanzu kukan be kareba? Rahma ta kwantar da kaita a kafadar Mami tana kara narkewa “Mami kafata ya karyaman kafa” ta ida maganar tana yarfe hannu.

 

Meya samu kafar taki ne? Mami ta fada tana yaye blanket din da ta rufe kafar dashi.

 

Dukkan mu kallon babban yatsan muke ya kumbura har wani kyalli yake, hankali na ya tashi banason abinda zai tabaman jiki nan da Nan na kara volume din kukan da nikeyi.

 

“Yi shiru fadaman me yasamu yatsan har ya kumbura haka?”

 

“Mami Yaya Abdallah ne”

 

Dukan ki yayi ko ya akayi?

 

A hankali na zaiyane mata muguntar dayayi man dazun.

 

“Lauratu ajiye tiren hannun ki kije daki ki dauko man wayata tana nan saman mirrow”

 

 

“Lauratu tace to tare da ajiye tiren dake hannun ta ta fita,batafi minti biyu ba ta dawo ta mikawa Mami wayar, “zaki iya tafiya Lauratu Mami ta fadi hakan lokacin da take Kokarin latsa wayar.

 

Allah ya kara sauki Aunty Rahma Lauratu ta fada tare da ficewa daga dakin.

 

“Ka dawo ko kana asibiti? Mami ta fada da alamun Yaya Abdallah ta kira, “a a Mami gani akan hanya yanzu zan koma gida, idan nayi wanka nadan kimtsa zan shigo anjima”

 

“Ka wuto gida yanzu inason ganinka”

 

‘to gani nan shigowa insha Allah’

 

Ok Mami ta fada tana kashe wayar.

 

Da lallashi Mami ta samu ta taimakaman nayi wanka, sannan ta zubaman abinci wanda daker na samu na ci kaɗan ina yamutsa fuska,dama abinci ba wani damuwa nayi dashi ba,ga raki idan banida lafiya ciwo kaɗan sai ya wahalar da ni.

 

Wayar Mami tayi kara alamun shigowar kira ta ɗaga tana faɗin,”Ina dakin Rahma”

 

Befi ƴan sakanni ba Yaya Abdullah ya turo kofa a darare ya shigo yana kara tamke fuska dan beson shiga shirgin Rahma kwata-kwata.

 

“Harararshi Mami tayi tana faɗin “Shigo kaga illar da kayiwa yarinyar nan”

 

Abdullah ya hadiye miyau daker a zuciyarshi yana faɗin dama nasan maganar kenan yace “Me kuma nayi Mami?”

 

“Ubanka kayi, zaka matso ka duba mata kafar nan ko zaka tsaya tambaya ne!”

 

“Yi hakuri Mami Yaya Abdullah ya fada lokacin da ya duka saitin kafata”

 

 

Hannu ya kai yaɗan taɓa yatsan,na janye kafar ina matso kwallah.

 

“Ki tsaya induba ko in barki da abarki,inta rube kinga mun huta da fitinar ki,ya faɗa muryarshi babu alamun sassauci”

 

Ta Allah ba taka ba mugu insha Allah har tsufana da kafafuwa na,nayi maganar cikin gunaguni.

 

“Uban me kike cewa? Ya fada a harzuke”

 

Wanda bacin Mami da ke a wajen kila sai ya kai min mari.

 

Babu abinda yaya Abdullah ya tsana kamar tsaki da gunaguni.

 

“Mami ta ce Abdullah duba kafar zakayi ko biye mata?”

 

“Buguwace mami zan kawo magani ta shafa a wajen”

 

Ya fadi hakan ne saboda Mami ta kyaleshi,duk da yaga alamun targadene a yatsan,yafi son sai taci wahala ko zai gyara mata,yasan yau, wannan bajewar da take ta kwashi bacci sai rana ta fito tayi gatse-gatse ta tashi sallar asuba,yau kam bazai yiwu ba.

 

Jiya ta saka ya kwana beyi bacci ba itama yau baza tayi ba,ya ida tunanin yana murmushin mugun ta.

 

Mami ta katseshi da ce wa “ka rubutawa Lauratu sunan maganin taje khemis ta amso yanzu.”

 

Yace “to”be kara kallon inda nike ba ya fice daga dakin,

 

Mami ta maido hankalin ta kaina tana ce wa”sannu yanzu ki kwanta idan Lauratu ta kawo maganin sai in shafa maki.”

 

*. *. *. *

 

Kamar yadda Abdullah ya faɗa kuwa tsakar dare Rahma nason kwantawa kafa ta ce batasan wannan ba, kafin wani lokaci zazzaɓi ya rufe ta, gaba ɗaya ta rasa in da zata saka kanta taji daɗi.

 

A can ɗakin Abdullah ma,yayi nufin hanawa Rahma bacci,sai dai shima baccin ya kauracewa idanunshi.

 

Rahma ta na barazanar haukatashi da matsalolin ta,ya rasa wacce hanya zai bi dan ladabtar da ita.

 

Ƙarar da wayarshi tayi ne yasa shi saurin waigawa ya mika hannu ya daukota kasancewar tana saman bedside drowar,MY WIVE shi ke yawo a fuskar wayar,ya ɗan ja ajiyar zuciya tare da lumshe gajiyayyun idanunshi,”ashe fah yau,kiran da yake mata na dare kafin ya kwanta,be samu yinshi ba,fitinar Rahma ta mantar dashi.”

 

“WIVE me ya hanaki bacci har yanzu?”

 

A sanyaye yake maganar har ya tsorata Basma

 

Ta ce”Dear yau inata sauraran kiranka shiru baka kira ba, yanzu kuma na ji muryar ka ba yadda na saba ji ba,tabbas akwai abinda ke faruwa menene Dear?

 

“Na tashi daga bacci ne WIVE” Abdallah ya bata amsa tare da kwantar da kafadar shi a jikin fuskar gadon.

 

Basma ta sauke numfashi,My Dear niko na kasa bacci rashin jin muryar ka ya kangarar mun da ido.

 

“Sorry WIVE nima wayar ce babu chaji,sai na sakata a chaji da niyyar idan chajin yaɗan shiga in kiraki sai bacci ya kwasheni,” Kiran kine ya tasheni.

 

Abdallah ya yi mata ƙaryar hakan sanin cewa batason duk wata magana da ta shafi Rahma.

 

“Yakike,ina My boy yau beyi kukan dare ba?”

 

Basma ta kalli dan Babyn su dake kwance gaban ta,tana faɗin “Yanzun ba daɗewa na samu yayi bacci,ai kukan dare ƙa’idane kullum sai ya yi shi.”

 

“Zai bari nan gaba tunda an duba shi ba wata lallura dake damun shi,kuka ne kawai da wasu jariran kanyi.

 

Fira suka yi sosai,basu ajiye waya ba sai wajen karfe biyu da rabi na dare, tsananin kewa da kaunar matar shi da yaron shi, ta mamaye shi,gani ya ke yi kwanakin sunki gudu,shi kam wannan wankan gida ba akan son ranshi Basma ta jeshi ba.

 

Ganin tunani zai ƙara cin ƙarfin shi yasa ya yi amfani da wannan damar ya ɗauro alwallah ya ida raya daren da sallar Nafila.

 

 

*Wannan littafin na kudine idan kinason cigaba da karantawa zaki same shi akan farashin normal group 300 VIP 400 masu so ta private 1000 ki turo kudin ta wannan account number 1632036584 Sa’adatu Balarabe Access Bank ki turo evidence ta wannan number 07032895551 ko katin MTN ta wannan number 07032895551*

 

*Idan kuma littafin mu guda biyu kikeso TUSHEN MU DAYA da FANSAH 2022 Zaki turo normal group 500 VIP 800 ta private 1000*

 

 

 

ByKhilishi Ceh

 

Buhainat *FANSA 2022

 

 

 

SA’ADATU (KHILISHI CEH)*

 

 

 

“`Bismillahir rahamanur rahim“`

 

“`Sadaukarwa ga Hassan ATK, Hussain 8k,Abubakar saleh Kurami, Sdeen, Abubakar Ak Saraki, Muhammad Kareem“`

 

 

*Free page 2*

 

 

*Masu son a tallata masu hajarsu ko link din group din su zuyi magana ta wannan number 07032895551*

 

Rahma na zaune bakin gado gaba ɗaya ta fita haiyacinta,yau sallar asuba a kunnenta aka kira har zuwa lokacin da aka shiga sallah,Mami ta turo ƙofar dakin ta shigo.

 

“Kafar ce har yanzu Rahma”

 

Mami ta tambaya ganin yadda fuskar Rahma ta fita daga haiyacinta, rashin bacci da kuka yasa idanunta sun kunbura sosai.

 

Kai Rahma ta ɗaga mata kwalla nabin gefen idanunta.

 

“Ashsha bari Dady ya dawo daga masallaci in faɗi mishi mu tafi asibiti kawai” Dama dubawar da Abdullah yayi jiya be gamsheni ba.

 

Shida da rabi na safe a asibiti tayiwa su Rahma,ana dubawa aka tabbatar da targadene tayi a yatsan kafar,kuma dole sai an gyara shi, ko zata denajin wannan zugin.

 

Taci azaba wajen gyaran,kuka kuwa muryarta gaba ɗaya bata bita,ta dishe,tsamin da yayi shi ya haifar mata da wahalar da tasha, ana gama gyaran aka bata maganin bacci dana zazzaɓi.

 

A can gidan Abdullah tunda ya tashi tunanin ciwon Rahma ke damun shi,yasan ta da raki ba abinda ke ladabtar da Rahma kamar ciwo,ciwo kaɗan sai kaga ta fita a haiyacinta,don haka zuwa takwas saura ya shiga cikin gidan nasu,dama kuma tun bayan tafiyar Basma, a gidan nasu yake kalaci, sannan ya kan,shigo da dare kafin ya wuce gidanshi.

 

Falon tsit ba kowa sai kamshi turaren wuta dake tashi,kujera ya samu ya kishingiɗa,idanuwanshi ya lumshe wanda suke cike da bacci, zuciyar shi gaba ɗaya ta yi mashi nauyi, akwai abubuwan dake neman su gagari zuciyar.

 

Kowa ya ci bashin bacci sai ya biya,a haka bacci ya sace Abdullah.

 

Lauratu ce ta fara fitowa falon, kasancewar yau ita ke hada kalaci,gwanar shiga kitchen yau babu lafiya( Rahma )

 

Ganinshi tayi kwance saman three seiter, ba abin ta ta dashi ya gyara kwanciyar shi ba, yanayin kwanciyar da yayi idan ya dade wuyan shi dole zai sage, saboda a takure yake.

 

Aunty tabi Abdallah da kallo gaba daya tausayin shi takeji,tasan ciwon Rahma yasashi fitowa da sassafen nan,shi da Dady duk abinda Rahma zatayi bazasu iya fushi da ita ba sai dai suyi kurari dan ta gyara.

 

A hankali ta kira sunan shi tana bubbuga saman kujerar.

 

“Muryar Aunty yaji sama sama tana kiran sunan shi,hakan yasa shi bude ido daker.”

 

“Ka tashi ka tafi dakin ka, ka kwanta( kasancewar yanada daki har yanzu cikin gidan nasu ).

 

 

Ya yunkura ya tashi tare da fadin “Aunty ina kwana?”

 

“Lafiya qalau ya aiki ya wajen masu jego?”

 

“Lafiya qalau suke jiya munyi waya sun ce agaidaku”

 

“To Alhamdulillah,zakaje ka kwanta ne ko kaje ka fara breakfast tukunna”

 

“Bari in yi kalacin inason in leka asibiti,su Mami basu tashi bane naji gidan shiru” Yayi tambayar dake cin ranshi.

 

“Mami tun da sassafe suka fita asibiti,kasan su da rudewa in Rahma ba lafiya shima Dady yanzu ba daɗewa ya fita ko kalaci beyi ba wai zai je yaga yanayin jikin nata”kafar nan ta Rahma batayi bacci ba jiya,an nemi wayar ka a lokacin ba a samu ba.

 

“Gaban Abdallah ya fadi duk da yasan dama hakan zata iya faruwa”

 

“Ya dan ji ba dadi kasancewar yasan shine silar ciwon, ya sosa kanshi yana fadin bari in karya Aunty Allah ya bata lafiya”

 

Ya ida maganar ya na mikewa zuwa wajen daning area.

 

“Idan zaka tafi sai ka wuce masu da breakfast dinsu Aunty ta fada dai dai lokacin da suka isa, wajen daning table din.”

 

*****************

 

Yaya Abdallah be dade da zuwa ba aka bamu sallama muka dawo gida,sai da nayi kwana biyu sannan kafata ta dawo normal.

 

Abu daya yanzu ke damu na rashin fitar nan,duk da an barni na koma makaranta,amma Yaya Abdallah ke kaini idan muntashi Mami ko Aunty wata cikin su ta dauko ni,ba halin inyi ƙaryar lectures,Yaya Abdallah ya gama bin diddikin komai, gaba daya idon Yan gidan yanzu a kaina yake,Yaya Abdallah ma zan iya cewa kamar ya dawo gidan da zama ne kullum cikin zarya yake.

 

BAYAN WASU KWANAKI

 

Rahma ce da Abokanta su Usman Musty da Hud,sai Ruky,suna cikin cafeteria ne,Malamin da zai yi masu lecture be samu shigowa.

 

Hira suke yi sama sama.

 

Dukan table din da akayi ne yasa su waigawa gaba daya in ka dauke Rahma data lula duniyar tunani.

 

Matse hannun ta da Nameer ya yi ya maidota,ta yi “tsuwwa don zafi cikin shagwaba take fadin “kana son ka karyamun yatsu ne?”

 

Nameer ya yi murmushi yana karewa jikinta kallo tare da fadin “Kin yi fah wallahi baby kyawun nan naki yana kashewa gayu idanu.”

 

Ya akayi naga ba a kawo maku komai ba? Nameer ya fada yana kallon su Usman

 

Ruky tace no, mun fito shan iska ne kawai.

 

“Ok” ya fada lokacin daya ke zama kujerar da ke kusada Rahma,ya dan rankwafa ya na yi mata rada.

 

Cikin jan,aji take dan murmusawa.

 

” Sun cigaba da tattaunawa akan wani kwarya kwaryan party da Nameer ya hada masu ranar Saturday, zasu gabatar da partyn ( Kasancewar Nameer din Babanshi babban dan kasuwa ne, kudi dai a wajen Nameer ba a magana.)

 

Sama sama Rahma ke saka masu baki, hankalin ta na can ta na tsara yadda zata samu ta halarci partyn,wanda kusan za a ce zuwan ya zame mata dole idan aka duba yadda take da Nameer.

 

Nameer ya cancanci komai in aka duba yadda yake bala’in son ta,tun suna secondary suke tare, saboda ita yaki fita kasar waje karatu hatta course iri daya suka zaba.

 

*****************

 

” Hello!” Hajja kina ji na kuwa,Mami ce ke fadin haka,waya kange a kunnen ta.

 

Ta ci gaba da magana jin an amsa mata”Gani nike komai kaina yake dawowa,kina ganin ciwon da nayi kwanaki da aka auna ni ce wa aka yi jini na ya haw sosai.

 

“Hussein so yake yaga baya na duk wani a hali dazan shiga Hussain ne silah,sannan kuma kinga yanzu…….

 

“Dallah rufeman baki Saudatu!!”

 

Hajja ta katse Mami cikin tsawa

 

“Duk wannan bayanin da ki ke yi,me ki ke so kice man?”

 

“Ki na son kiceman har kin gaji zaki kyale Rahma da uwarta hadiza(Aunty) duk kuwa da abinda Alhaji Hussain ya yi maki?”

 

“Kin man ta Hussain shine silar ajalin Hassan”

 

“Kin manta duk wani kunci da Hussain ya saka ki”

 

“To bari kiji Saudat!. Aisha da yar ta Rahma sune garkuwar Alhaji Hussain don haka dole kici gaba da yaki dasu ta karkashin kasa.”

 

 

“Ban ce kibi malamai ko bokaye ba, amma dole ki cigaba da bin hanyar da muke kai”

 

“Hajja ta cigaba da fada tare da bawa Mami shawarwarin da take ganin sune mafita”

 

*******************

 

Yau kam zaman ɗaki nikeji kusan wunin yau a daki nayi shi,kasancewar banje school ba, yanzu ma wani Korea film nike kallo daya dauki hankali na na kosa inga ƙarshen Film ɗin.

 

Jin karar bude kofar yasa ni ɗago kai,ganin me shigowar yasa na jefar da laptop din saman gado na hantsulo cikin murna ina faɗin

 

“Yaya Sadik kai ne?”

 

“Of course gani kuwa kina gani”

 

“Na kai hannu na shafa fuskar shi dan tabbatar da shi ɗin ne”

 

“Na koma na zauna ina faɗin na ma yi fushi da kai shine jiya da muka yi waya bakace zaka zo ba.”

 

“Sorry Kanwa taso muje falo akwai labari”

 

Yasa hannu ya ɗago ni a hankali,nayi dariya ina kara mannuwa da jikinshi,Ina tsananin son Abubakar wanda muke kira da Yaya Sadik saboda sunan kakanmu da yaci,kila son da nike mashi ya samo asali da banida wani dan’uwa wanda yake shakiki na sai shi.

 

“Ya ya aka yi ne?” Yaya Sadik ya tambaya ganin na kura mashi ido ina murmushi”

 

“Gaba daya mu kayi dariya,dan ganewar da yayi ina tuniyar tunani ne,ban ma san ina kallon shi ba.”

 

Dai-dai lokacin kuma Yaya Abdallah ya shigo.

 

“Kamar wata mara gaskiya nayi saurin sakin Yaya Sadik,shi kuwa Yaya Sadik din kara rikeni yayi a gefen sa ya dubi wansa yana fadin “Bros ya gari? Na shigo kana asibiti.

 

“Me ka ke yi dakin ta?”

 

“Me na fada maka akan shigowa dakin Rahma?”

 

Yaya Abdallah ya tsare Yaya Sadik da Wadanan tambayoyin, idanunshi jawur da alamun bacin rai.

 

Daga Yaya Sadik din harni muna mamakin wannan hali na Yaya Abdallah,ko zai rabani da kowa be kamata ya shiga tsakani na da Yaya Sadik ba,Uban mu daya shi Kadai nike dashi makusanci na.

 

Gaba daya muka zuba mashi ido muna kallon shi cike da al’ajabi ba tare da ya yi magana ba,Yaya Sadik din ya wuce ya fita daga dakin. Nima fitar nayi na bar shi a tsaye ya na binmu da kallo.

 

Daga nan kitchen na wuce na shiga hadowa Yaya Sadik drinks.

 

Kai tsaye part dinshi na wuce dan nasan can zan same shi.

 

Na tadda shi zaune a falo yana latsa waya.

 

Na jawo wani dan table na ajiye tray din a kai,tare da fadin “Yaya Sadik kayi hakuri”

 

“No ba komai kar ki manta bani da kamar Yaya Abdallah ciki daya muka fito,dole in nayi wani abu wanda be dace ba ya tsawatar man”

 

Na zumbura baki “amma Yaya Sadik Menene abin gyara anan?” Hannunshi ya dora saman leben shi alamun inyi shi.

 

Na mike ina shirin barin mashi dakin gaba daya,wa za a nunawa yan’uwantaka dama shi baya son laifin Yaya Abdallah.

 

“Sorry yar kanwata zo ki bani drink din ya fadi lokacin daya kamo hannu na”

 

Na dawo amma fuskata a shagwabe.

 

“Albishirin ki, Yaya Sadik ya fadi ni nasan duk dan yaga na washene”

 

Nace goron ka zanyi maka hadadden girki kafin ka koma.

 

Yayi dariya yana fadin “Kin kusan zama momy Aisha ciki ne da ita,”

 

Wata kara dana buga sai ayi tunanin wani mugun abu ne ya sameni,na tashi Ina juyi saboda murna”

 

Yaya Sadik ya bini da kallo yana dariya dama yasan za ayi haka, Aisha matarshi ita da Rahma suna bala’in shiri,Kila dan halinsu yazo daya ne.

 

Ya mike dan shiga daki yana fadin ki jaman kofar zan kwanta in danyi bacci kafin la’asar.

 

*Wannan littafin na kudine idan kinason cigaba da karantawa zaki same shi akan farashin normal group 300 VIP 400 masu so ta private 1000 ki turo kudin ta wannan account number 1632036584 Sa’adatu Balarabe Access Bank ki turo evidence ta wannan number 07032895551 ko katin MTN ta wannan number 07032895551*

 

*Idan kuma littafin mu guda biyu kikeso TUSHEN MU DAYA da FANSAH 2022 Zaki turo normal group 500 VIP 800 ta private 1000*

 

#Khilishi ceh

 

Buhainat

 

*FANSA 2022

 

 

 

 

SA’ADATU (KHILISHI CEH)*

 

 

 

“`Bismillahir rahamanur rahim“`

 

“`Sadaukarwa ga Hassan ATK, Hussain 8k,Abubakar saleh Kurami, Sdeen, Abubakar Ak Saraki, Muhammad Kareem“`

 

 

 

*Free Page 3*

 

 

*Masu son a tallata masu hajarsu ko link na group nasu suyi magana ta wannan number 07032895551*

 

 

Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un kalmar da Baba Umaru keta maimaitawa kenan, yayin da ya gagara zama,sai kaiwa da kawowa yake yi.

 

“Sulaiman ka tabbatar da gaskiyar videon nan kafin ka kawo mani kuwa,ba irin hada hotuna da akeyi ba ne?”

 

“Baba wallahi sai da nayi bincike na tabbatar da gaskiyar videon nan sannan nazo na nuna ma ka.”

 

“Kira man Hussain din,ka ce ina son ganin shi gobe idan Allah ya kaimu,kuma ya taho tare da Rahma.”

 

Nan take Sulaiman ya kira number Dady Hussain bayan sun gaisa ne ya sanar dashi da sakon Baba Umaru.

 

“To insha Allah zan shigo din” Dady ya fada a sanyaye,don ya san dole akwai dalilin kiran,barin ma da ya ji an sako Rahma,” Addu’a yake a zuciyar shi Allah ya sa ba wani laifin Rahma ta yi ba.

 

“Bani wayar” Baba Umaru ya bukata”

 

Sulaiman ya tashi ya mika mashi,

 

videon ya tura a wayar shi ya yi deleting na wayar Sulaiman din.

 

Mika mashi wayar ya yi tare da faɗin “zaka iya tafiya”

 

Fita Sulaiman ya yi, a zuciyar shi ya na addu’ar Allah ya sa tarkon da ya haɗawa Rahma ta fada, Allah ya sa suce zasuyi mata aure,ba shi wani buri irin ya ga ya mallake ta a matsayin matar shi ta uku,tun tasowar Rahma ya ke bala’in son ta, amma Rahma duk idan sun hadu ko kallon arziki be isheta ba, saboda kawai ya na rayuwa cikin kauye, murmushi ya yi, Ya na hango kanshi a matsayin Mijin Rahma.

 

WASHE GARI

 

Misalin ƙarfe sha ɗaya, Dady da Rahma suna cikin kauyen kadanya,yara sai oyoyo su ke yi masu an baibaye motar su, takaici duk ya bi ya lullube Rahma irin hakane kesa ta na kara tsanar kauyen,a fusace ta bude kofar, har sai da ta kusa ture wasu yara da ke kusa da marfin mota.

 

Kai tsaye cikin gidan ta nufa tana dauke kai gami da shan kamshi,dan kuwa ba kowa ta ke gaisarwa ba,ta kan ce rashin aikin yi ne ke sakawa ayi ta wani gaishe gashe.

 

Matan Baba Umaru sun amshe ta hannu biyu,aka sauketa a dakin amaryar shi, kasancewar sun fi shiri da Rahmar kuma tafi ruwan wayewa ga tsafta ta na da ita.

 

Shi dama Dady falon Baba Umaru ya wuce daya ke akwai kofar da zaka shiga falon daga waje,draver kuma dama a nan kofar gida ya tsaya.

 

******************

 

A can falon Baba Umaru,Dady ne duke gaban Babban Yayan su wato Baba Umaru,wata irin zufa yaji tana diga cikin jikin shi,be taɓa shiga tashin hankali irin na yau ba,ya ɗago rinannun idanunshi da suka rikide da zallar tashin hankali, ya yi kokari sosai da ya hana kanshi fashewa da kuka.

 

Bakin shi na rawa ya ke faɗin “Yaya ku gafarceni bacin ran da na saka ku a baya,ashe haka iyaye ke ji?” amma wllh Yaya ban taba keta alfarmar diyar kowa ba” Anan gabar be iya rike hawaye shi ba, kawai sai ya fashe da kuka,lallai Rahma babbar Jarabawa ce Allah ya bashi.

 

“Ashsha bari yi mata kuka Hussain ai sai ta kara lalacewa” Baba Zakariya ke faɗin haka.

 

“Baba Ibrahim ya ce ya kamata a kira ta mu kara tabbatar da gaskiyar al’amarin nan”

 

Duk suka yi na’am da hakan,Baba Umaru ya daga waya ya kira amaryar shi ya ce ta turo masu Rahma falon shi.

 

Bayan kamar minti biyu Rahma ta shigo,ganin su su duka a falon yasa tasha jinin jikin ta.

 

Saman kafet ta zauna tare da gaishe su wasu sun amsa wasu kuwa ko kallon arziki bata samu ba.

 

“Matso nan” Baba Umaru ya fada da muryar bada umarni.

 

Dajan jiki ta matso kusa da shi da yake nuna mata, tsoron ta daya ka da su rufeta da duka,da alamun fuskokin su,babu sassauci…..

 

“Menene wannan?” Baba Umaru ya fada, lokacin da ya kunna mata videon ya na miko mata wayar.

 

Tun fara jin taken wakar,ta gane ko wanne video ne,rawa jikin ta ya dauka,me ya kawo videon partyn da Nameer ya shirya masu a wayar Baba Umaru? Wane irin cin amana Nameer ya yi mata? Nameer ya tabbatar mata da cewa daga cikin wayar shi babu wayar da videon zai shiga, wannan ne dalilin da yasa ba abar kowa shiga da waya wajen partyn ba.

 

“Zaki amshi wayar nan ko sai na tattaka ki a wajen nan? Baba Zakariya ya fada kamar zai rufe ta da duka.

 

Dama duk cikin su yafi zafin rai.

 

Ta amsa tana, dukar da kai,sama sama take kallon videon,dai dai lokacin da takalmin ta ya kusan fadar da ita, Nameer ya dauke ta cak,ya rumgume ta a kirjin shi a haka ya rinka hawa step din,be ajiye ta ba,har sai da ya dangana da wajen da zasu zauna, bayan ya aje ta, ya bi fuskar ta, ya na sumbata, lokacin ne kuma hole ɗin aka ɗauki sowa gami da tafa mashi,dai dai nan ta rintse ido,zufa na kara wanke jikin ta.

 

Ganin reaction din da ta nuna kaɗai ya isa ya tabbatar wa da su Baba Umaru gaskiyar videon.

 

“Tashi ki fita”

 

Baba Ibrahim ya fada wanda saboda tsananin bacin rai har fifita yake da babbar rigar da ke jikin shi.

 

Cikin sauri Rahma ta tashi kamar ta kifa,ta fice a falon.

 

“Wacce shawara ku ke da ita?” Baba Umaru ya tambaya yana kallon dukkan su ukun.

 

“Aure yakamata mu yi mata Yaya,” Baba Zakariya ya fada.

 

“Shawarar Zakariya ta yi” shima Baba Ibrahim ya fada.

 

“Baba Umaru ya maido hankalin shi wajen Dady Hussain da har yanzu be dawo dai dai ba” . Hussain kai menene shawarar ka?”

 

Cikin sanyin jiki Dady Hussain ya ce wannan shawarar ta yi Yaya.

 

“To Alhamdulillah ina fatan baku mance da wasiyyar dan’uwan mu Hassan ba?”

 

“Wannan ai ba wata matsala ba ce Yaya” Baba Zakariya da Baba Ibrahim suka hada baki wajen fadi.

 

“Idan mu ka yi amfani da wasiyyar marigayi Hassan muka hada Abdullah da Rahma aure mun cutar da shi Abdallah in mu ka yi duba,da Abdallah be da wata matsala da za’ayi kaico da shi, amma Rahma fah…..?” Dady ya fada cikin damuwa ya cigaba da fadin

 

“Sannan duka duka Abdallah har yanzu be cika shekara biyu da auren su da Basma ba,inaga nan ma akwai cutarwa, Abdallah beyi girman da zai rike mata biyu ba.

 

“Wadannan ba hujjoji bane Hussain ance mu kyautata zato,kuma Abdallah ai jinin daya suka fito da Rahma, dole duk yadda ta zama yayi hakuri da ita.”Baba Umaru ke wannan maganar.

 

” Baba Zakariya ya ce ni sai ingama auren ta da Abdallah zai taimaka wajen tarbiyyar ta,in muka duba yadda ta ke shakkar shi.

 

“Hakane Allah ya tabbatar mana da alkhairi”

 

Shidai Dady jinsu kawai ya ke amma Aure Abdallah da Rahma hadin nan beyi ba kwata kwata.

 

Karshe sun rufe maganar akan za a yi waya Abdallah ya zo gobe,dan Baba Umaru ya ce be son bikin ya dauki lokaci.

 

Dole kwana ya kama su Dady kenan

 

**********************

 

Misalin ƙarfe uku na washe gari duk wanda ake bukatar zaman dashi ya kammala a falon Baba Umaru,in ka dauke Rahma da ke cikin gida, amma ita ma an aika kiran ta.

 

Tun dosowar ta kofar falon gabanta ya yi masifar faduwa jin tashin kamshin turaren Yaya Abdallah, saboda bata san ya zo garin ba kwata kwata, kasancewar wuni ta ke cikin daki.

 

A darare ta shiga falon yanayin sanyin ta da natsuwar ta ya bawa kowa mamaki,ta nemi wuri can daga nesa ta zauna.

 

Baba Umaru ya yi gyaran murya ya fara magana kamar haka.

 

“Akwai wasiyyar da dan’uwanmu Hassan ya bari kafin ya rasu, wacce muka yanke shawarar fada maku ita ayau saboda lokacin fadin da ya yi,duk da lokacin ke Rahma ko cikin ki babu.”

 

“Marigayi Hassan ya bar wasiyya cewar idan har Allah ya bawa Hussain haihuwar diya mace,kuma ba Saudat ba ce ta haife ta to yana son a aurawa yaron shi Abdallah”

 

“A takaice dai mun kammala magana za mu cikawa Marigayi wasiyyar da ya bari zamu hada kai Abdallah da Rahma aure.”

 

Da sauri suka dako kai suna kallon Baba Umaru, maganar ta yi matukar bugun zuciyar su, Rahma kam harda suman zaune na a kallah mintuna biyu ta yi, nan da nan zufa ta shiga keto mata,ita kam tafi yadda mafarki ta ke yi.

 

 

Abdallah ma ya shiga rudani matuka wanda ban iya misaltawa,ya fada tunani wanda ya kasa gane bacci ya ke ko ido biyu ne?.

 

Baba Zakariya ya yi gyaran murya tare da fadin” Ku sauraremu dakyau Abdallah ku rike wannan a ranku mun zamu hada auren nan naku badan komai ba,sai dan cika wasiyyar Marigayi, saboda haka ku yi Kokarin hada kanku.

 

“Baba Ibrahim yace ku yi mana biyayya ka da muji kada mu gani.”kuna fahimta kuwa ?. Ya tambaya ganin kamar sun fice a haiyacinsu.

 

Kusan hakane kuwa dan Abdallah maganar da Baba Ibrahim din yayi da daga murya kusan firgitashi ta yi,ji yake kamar an jona mashi wutar lantar ki,kan shi ya shiga sarawa,nan da nan sanyi mai tsanani ya shiga ratsa jijiyoyin jikinshi,koma dai menene zai faru babu musu tsakanin su da iyayen su,sai dai in saɓon Allah ne wannan babu yadda za a yi su yi masu biyayya.

 

Lokacin guda kuma ya saukar da ajiyar zuciya tuna Rahma ce fah,yasan duk rintsi ba zata taɓa amincewa ba,don haka ya bita da kallo, babban burinshi ta bijirewa abin, amma babban abinda ya bashi mamaki shine ko ɗago kai batayi ba,sai dai zufa da take ta haɗawa.

 

Sun dade suna yi masu nasiha da jan kunne.

 

Dady kuwa ko tari beyi ba,addu’ar shi ɗaya kada yaran su ki amincewa,ya fi tunanin matsalar daga Rahma sai gashi batayi ko tari ba, amma akwai alamun firgici a tattare da ita.

 

Ikon Allah ne kawai ya kai Rahma cikin gida tana shiga dakin amarya ta fada kan gado wani irin numfashi ta rinka saukewa, ta kasa gane halin da ta tsinci kan ta.

 

Bata dade da kwanciya ba aka aiko cewa ta fito zasu tafi,abin haushi kuma da ta fito Baba Umaru ya ce ta shiga motar Abdallah su tafi tare,shi kuma Dady sun taho shida driver.

 

Takaicin hakan yasa tunda na shiga nike matsar kwallah,kwata kwata na rasa abin da ke min daɗi zuciya ta a cunkushe ta ke.

 

“Wai kukan kuma na uban menene ?” Uban wa ya hanaki magana dazun?”

 

Yaya Abdallah ya fada yana dukan sitiyari,ya gangara da motar ya tsaidata, idanunshi sun yi jawur,dama da alamun jira yake.

 

Tsoro ne ya kamata ganin su kaɗai ne,gudun kada tasha mari ta ja bakin ta tayi tsit.

 

Yaci gaba da bala’i na huci kamar ya rufeta da duka,

 

“Idan kin yi shiru ne danki kuntatani,kanki kika cuta.”

 

“Inada mata kamar Basma me zan yi da ke,baka mai bakin hali,ko da kinada hali mai kyau ban taɓa sha’awar baƙar mace ba.

 

“Don haka ya rage naki ko ki bude baki ki faɗa masu su fasa auren,in ya zama dole sai an maki auren kuma su samu can irinki su hadaku,ko kiyi shiru ki cuci kan ki,da ke da hoto duk ɗaya ku ke in kin shigo gida na,inada kishi yadda na tsare kaina bazan iya zama da mazinaciya ba,kodan yaran da zan haifa, kada su tsotso mugun hali.”

 

 

“Tun da ya fara magana Rahma ta kureshi da ido hawaye na kara ambaliya cikin su”

 

Ashe zargin da ya ke yi mata kenan shi yasa ya tsane ta,shi kenan daga an ganta jikin namiji ko ta rike hannunshi sai a kira ta mazinaciya?.”

 

 

Cikin sanyi ta ce ” Na sani Yaya Abdallah ba sai ka faɗi komai ba.”

 

“Sai dai shirun bani kaɗai na yi ba,me yasa kaima baka yi magana ba,duk da cewa nima bana son ka!, Kuma abu daya bakadashi cikin kalar namijin da nike burin aure, sannan……….

 

Marin da Abdallah ya kai mata yasa ta yin shiru,” Rufeman baki munafuka,ke har kinada wani quality da wani namiji zai soki.

 

Ya ja tsaki “Stupid shashashar yarinya ballagaza kawai”

 

Be kara kula ta ba har suka iso gida,suna iso ko gama parking be yi ba, ta balle murfin motar da gudu tayi cikin gidan,ya bita da kallon takaici.

 

Tana shiga ta afkawa mami wacce ta rafka uban tagumi jin abin da Dady ke faɗi masu”Abdallah da Rahma wai aure”.

 

Rahma ta faɗa jikin mami ta cukwikwiyeta tana sauke ajiyar zuciya.

 

Dady yace” Menene haka?”

 

“Maza ki tashi ki bamu waje”

 

“Tashi ta yi tana tura baki a haka tayi ɗakin ta.”

 

Aunty tace “Dady in akayi haka tabbas an cutar da Abdallah ka duba wannan al’amari da kyau.”

 

“Nima abinda na faɗa kenan amma ya zamuyi kamar yadda Yaya Umaru ya fada ne Rahma ba tada jigo kamar Abdallah,ba wanda zai rike ta da mutunci kamar shi duk kuwa a halin da ya risketa, Dady ya ida maganar yanajin ɗaci a zuciyar shi.”

 

“Mami da bata saka bakin ta a maganar ba,a zuciyar ta fadi take “Baƙin ciki yanzu ka fara ganin shi Hussain,insha Allah bakin cikin Rahma shi zai yi ajalin ka,kamar yadda ka silar mijina Hassan”

 

“Takai hannu dan ɗauke kwallar da ta ɗan fito daga cikin idanunta,har yanzu ta kasa mancewa na tsohon mikin dake zuciyar ta.

 

Dady da ke binta da kallon tuhuma,yace baki ce komai ba Saudat?”

 

“Allah yasa alkhairi”

 

ta faɗa tare da tashi ta bar masu wajen.

 

Gaba ɗaya da kallon mamaki suka bita dashi,duk da cewa wannan ba shi bane farko, wasu lokutan sukan rasa me ke damun mami.

 

Ranar kam Abdallah, Rahma,da Mami babu wanda ya runtsa,kowa da abinda yake ƙullawa.

 

A can bangaren Abdallah har wani zazzaɓi zazzaɓi ya ji ya na barazanar rufe shi,yana zaman lafiya da Basma za azo a juna mashi wahala.

 

ASALIN SU

 

#Khilishi ceh

 

*Wannan littafin na kudine idan kinason cigaba da karantawa zaki same shi akan farashin normal group 300 VIP 400 masu so ta private 1000 ki turo kudin ta wannan account number 1632036584 Sa’adatu Balarabe Access Bank ki turo evidence ta wannan number 07032895551 ko katin MTN ta wannan number 07032895551*

 

*Idan kuma littafin mu guda biyu kikeso TUSHEN MU DAYA da FANSAH 2022 Zaki turo normal group 500 VIP 800 ta private 1000*

 

Buhainat

 

*FANSA 2022

 

 

 

SA’ADATU (KHILISHI CEH)*

 

 

 

“`Bismillahir rahamanir rahim“`

 

“`Sadaukarwa ga Hassan ATK, Hussain 8k,Abubakar saleh Kurami, Sdeen, Abubakar Ak Saraki, Muhammad Kareem“`

 

 

 

*Free Page 4*

 

 

 

Malam Abubakar mai shanu,ɗan asalin ƙauyen kaɗanya ne,Matan shi biyu A’isha itace Uwargidanshi, wacce suke kira da Yakumbo, sai Fatima wacce suke kira da Inna,yaran Yakumbo su biyar ne akwai Umar,sai Ibrahim sai Zakariya da Hauwa’u,sai auta Ahmad.

 

Umar da Zakariya da Ibrahim dukkan su suna zauna cikin garin kaɗanya da iyalan su,Aunty Hauwa Kuma na aure a garin katsina,sai autah Ahmad da Allah ya yi wa rasuwa tun yana shekara sha uku sakamakon haɗarin mota.

 

Inna Binta kuwa yaran ta biyu,Hassan da Hussain,wanda a wajen haihuwar su Allah ya yi mata rasuwa,sanadiyyar jini da ya balle mata,an kaita asibiti ba daɗewa ta rasu.

 

Rasuwar da ta tadawa mutane hankali ciki kuwa har da abokiyar zaman ta, saboda Inna Binta mutuniyar kirki ceh😍

gadaishi iyayen ta masu arziki ne amma ba ta da girman kai ga alheri hannun ta a bude ya ke.

 

Rasuwar Innah Binta yasa iyayen ta suka nemi alfarmar a basu riƙon Hassan da Hussain sai mahaifiyar ta da ake kira innoh ta shayar da su, idan sun yi wayau sai a dawo da su gidan mahaifinsu,haka kuwa akayi,bayan anyi addu’ar bakwai yan’uwan Binta suka hada duk wani abu na Hassan da Hussain,suka tafi kaduna da su kasancewar Inna Binta yar asalin garin kaduna ce, sanadiyyar tana zuwa kaɗanya gurin wata yar’uwar babanta gwogwgwo kuluwa.

 

Allah ya kaddara suka hadu da Abubakar soyayya ta shiga tsakanin su,duk da a lokacin ta gama secondary shi kuwa malam Abubakar ko primary be yi ba,sai dai ya na da ilmin addini sosai,hakan ya jawo cece ku ce,da ta kawo shi a matsayin mijin da zata aura,da yawa Yan uwan ta suna ganin ci baya ne,ta rasa mutumin da zata aura sai dan kauye wanda be da ilmin boko, amma a ɓangaren iyayen ta sun bata goyan baya,to a haka dai akayi biki amarya ta tare ɗakin ta sukaci gaba da zama cikin aminci ita da Mijin ta da kishiyar ta.

 

Bayan wasu shekaru

 

Saboda sabo da shakuwar da ke tsakanin Innoh da Yan biyu yasa koda ta yaye su ta kasa bawa mahaifinsu su,duk kuwa irin yadda malam Abubakar yaso hakan amma dole ya yi hakuri ya bar masu rukon yaran a hannunsu,kuma wannan ne dalilin da yasa Hassan da Hussain suka ta so cikin garin kaduna kuma suka samu ilmin boko da na addini,sabanin Yan uwansu dake garin kaɗanya da suka yi karatun allo kadai.

 

**********************

 

Zaman Hassan da Hussain wajen kakanninsu zama ne da ake kira da rikon kaka,Zama ne da ba kwaɓa ba zangwama.

 

 

Hassan da Hussain irin tagwayen nan da ba kowa ke iya banbance su ba suna tsananin kama, amma a bangaren halayya babu halayyar su ta tazo ɗaya, Hassan ya kasance mutum marason hayaniya, akwai tausayi gashi da hakuri yana da son yan’uwansa barin ma ƙaninsa Hussain,a bangaren rayuwa baya da girman kai sannan kyale kyale be dameshi ba.

 

Saɓanin Hussain mutum ne mai hayaniya ga saurin sabo baya da hakuri idan har ka tabo shi, sannan be damu da yan’uwanshi ba,ya kan ce “Abin kunya ne ace waɗannan kauyawan ne yan’uwana,” Hussain mutum ne me kyale kyale shi irin matasan nan ne da basa son raini, wannan dama duk ya same ta ne tare da goyon bayan kakannin shi.

 

Duk wani abu da Hussain zai yi to fa zasu ce kuruciya ce, hakan ke kara bashi gudummawa sosai

 

 

lokacin da suna secondary malam Abubakar yakara yunkurin son ko Hussain ɗin ne su bashi ya dawo gaban shi, saboda wasu halaye da Hussain ɗin keyi na rashin tarbiyya

 

 

Tun suna secondary Hussain ke da ƴan’mata rututu,yau yana wajen wannan gobe yana wajen waccan,idan ka bari ya fara soyayya da diyar ka ko kanwar ka to bazaka gane kanta ba, irin samarin nan ne da suka iya kalallame ƴan’mata da dadin baki.

 

Hussain ya hurewa ƴan’mata da yawa kunne,ya haɗa ƴan’mata da yawa faɗa.

 

Hassan yanayiwa Hussain wani irin so ,da har zamu iya cewa yayi yawa,a kullum zaka ganshi tare da Hussain zakayi zaton ya bashi ratar shekaru ne saboda yadda yake kulawa da shi,idan zai samu abu na ci ko na amfani to fah,sai ya fara bawa Hussain ya yi amfani dashi sannan shima yayi.

 

Hatta makaranta tun daga nursary har zuwa secondary shi ke kokari ta fannin taimaka wa Hussain a wajen jarabawa da assignment,sai da suka shiga jami’a aka rinka samun matsala saboda shi Hassan yana karantar “Faculty of Engineering”,shi kuma Hussain “Politics” ya ke karanta. Yawan carry over da sukayi ta bawa Hussain, karshe da abun ya yi yawa hukumar makaranta ta kore shi,ba wai baya da fahimta ba ne, kawai karatun ne ba yada ra’ayi shiyasa baya maida hankali.

 

Hakan yasa,Kaka da,Innoh suka yanke shawarar fita dashi ƙasar waje,a cewar su karatun zai fi yi mashi sauƙi a can, wannan shine dalilin karatun Hussain a ƙasar malesia.

 

************************

 

MALESIA

 

Kallah! Kallah!wow matso dan’ubanka “Kaga yarinyar da nike fada maka”

 

“Kalli surarta sosai, cikin Ƴan matan da mukeyi ka taba ganin mai halittar da zata tsaya cak,ka ga fah siffar kwalabar lemon coke ne da ake fadi da ita”. Hussain ne ke fadin hakan yana nunawa Abokin shi Nasir Bujawa hoton wata hadaddiyar Baby daya cika screen din wayar shi.

 

Nasir Bujawa ya kalli yarinyar sosai ya gano gaskiyar abokin nashi,ya ja dogon numfashi,tare ta jan tsaki to wannan ai daga ganinta balarabiya ce ko ba indiya,kasan kuwa sun yi maka nisa.

 

“Inji uban wa?” To Dan ubanka yar Nigeria ce kuma har nayi fallowing dinta,sunan ta Fateemah yar asalin garin gombe ce.

 

Aini insha Allah nayi mata, Hussain ya ida maganar ya na murmushi,be taba jin ainihin soyayyar diya mace ba sai akan Teemah wani irin so yake yi Mata,yana jin in ya same ta burinshi ya gama cika aka duk wata diya mace, Teemah ba abin da za a nema a wajen wata mace ba a samu a wajen Teemah ba.

 

Hussain ya fara ganin Teemah a Instagram, yawan bibiyar ta dayake yi yasa tun tana share shi har ta fara kulashi,a ranar da ta fadi mashi cikakken sunan ta da sunan garin su ranar wuni ya yi cikin farin cikin kulashin da tayi.

 

A hankali ya rinƙa cusa kan shi a wajen ta har suka dan fara sabawa,Anan ne ya yi mata tayin soyayyar shi,. Sai dai kai tsaye Teemah ta ce mashi “Bazan yi cinikin biri a sama ba” Kamar yadda na ce maka bana bukatar hatta picture din ka,ka bari inganka a zahiri to haka ma duk wani abu daya shafi soyayya,ka bari sai ka dawo Nigeria,( kasancewar Hussain baya dora picture din shi a social media)

 

A lokacin yaji ba dadi sai dai kuma da yayi wani tunani sai ya hakura yasan duk ranar data ganshi a zahiri ba zata iya ture soyayyar shi ba.

 

Kwanaki na ƙara mirginawa soyayyar Teemah na kara rugurguza zuciyar Hussain,ita kuma tana kara janshi a kasa, saboda kwata kwata halayyar Hussain batayi mata ba,tafison Nakiji miskili,wanda magana ba ta dame shi ba, batason namiji mai surutu kwata kwata.

 

********************

 

Kwance yake akan tafkeken gadon shi,sanye yake cikin kayan sanyi, kasancewar garin yau akwai sanyi,ya lullube rabin jikin shi da bargo,da ka duba fuskar shi za kasan ya na cikin damuwa.

 

Cikin sanyin jiki ya janyo laptop din shi domin yin wani research.

 

Ba a wani dauki lokaci ba yaji duk aikin ya gundure shi,ba abin da ya ke bukata irin son jin muryar Teemah.

 

Wayar shi ya dauko ya kara neman layin ta a karo na babu adadi,yanzu ma, haka ta gama ringing ba tare da an dauka ba.

 

Ya dafe goshin shi yana furzar da numfashi me dumi,yau kaɗai da basu yi magana ba ji yake kamar ba shida lafiya, yarinyar nan tana bashi wahala,ya kasa zuciya ya kyale ta ko ya yi niyyar hakan zuciyar shi bata iya jurewa.

 

Ƙarshe dole haka ya hakura ya kwanta,dan yasan ko zai yi mata misscall dari ba ɗauka zatayi ba,dama takanyi hakan in ƴan wulakancin sun motsa.

 

Ya dade yana juyi daker ya samu bacci ya dauke shi cike da tunanin ta, hakan yasa ya kwana yana mafarkin ta.

 

………………………..

 

 

NIGERIA

 

Ƙwance ya ke a bayan ƙatuwar kirar Ferrari,baka sidik har sheki take yi, Driver ne ke tukashi cikin natsuwa da bin ƙa’idar tuki.

 

Matashi ne ɗan kimanin shekaru talatin,cokolate color ne irin kalar hutun nan,sumar kanshi tasha gyara, Idanunshi sanyi cikin farin gilashi, kyakkyawa ne na ƙarshe.

 

Hassan Abubakar Mai shanu kenan. Matashi wanda ke cikin ganiyar shi, bayan kammala digirin shi a fannin Foculty of ingenering ya samu aiki a wani babban kamfani.

 

Suna kan hanyar su ta dawowa daga kauyen kaɗanya ya kaiwa Mahaifinshi da ƴan’uwanshi ziyara.

 

“Malam Saminu kaɗan kara gudun motar nan kaga dare ya fara nisa”

 

To yallaɓa ina neman alfarmar in tsaya inyi bawalli,tun dazun nike rikeshi,naji yana neman gagara ta”

 

“Tsaki Hassan ya ja in banda abun ka Malam Saminu wake rike fitsari ai sai yayi maka wata illar”.

 

Jingina bayan shi yayi jiki kujera,ya rufe idon shi yana shakar iskar da ke ta kaɗawa cikin dajin.

 

“Ya yin da Malam Saminu ya fita dan gabatar da buƙatar shi”

 

“Ya duka ya fara fitsari kenan yaji alamun nishi a kusa dashi,wayar shi ya fiddo ya haska fitalar wayar,abin da ya gani yasa shi saurin mikewa,da alamun gudu ya bar wajen.

 

“Ƙarar rufe ƙofar da akayi cikin rashin natsuwa,ya maido hankalin Hassan,

 

“Lafiya kuwa malam Saminu?”

 

“Da sauƙi dai yallabai” malam Saminu ya bashi amsa yana maida numfashi,dai dai lokacin ne kuma yaja motar.

 

“Meya faru ne?” Hassan ya ƙara jefo mashi tambayar.

 

Malam Saminu yace “Mutum ne kwance cikin jini yallaɓai.

 

Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un shine kuma ka zo kaja mota?

 

Yi ribos mu koma wajen me yiwowa akwai taimakon da zamu iya mashi,idan mun bar shi a nan wazai san dashi.

 

Malam Saminu ba dan ya so ba ya yi ya tsaida motar dama basu wuce wajen sosai ba.

 

Hassan sauka ya yi ya nufi wajen ya yi amfani da wayarshi wajen haskawa.

 

Halin da ya riski mutumin yasa hankalin shi ya tashi.

 

Hannu yasa da niyyar ciccibar shi,sai dai jin bazai iya ba yasa dole ya nemi taimakon Malam Saminu.

 

A bayan mota suka sakashi lokaci zuwa lokaci Hassan yana lekawa ya haska mutumin gaba ɗaya hankalin shi a tashe yake, gani yake Malam Saminu ba ya gudu hakan yasa ya yi ta azalzalar shi.

 

 

A guje motar tasu ta shiga Eroson hospital,gudu gudu ya fita ya na kwala kiran.

 

“Nurse!!”

 

“Nurse!!”

 

“Pls help!”please help!”

 

Gaba daya hankalin mutanen dake emergency ya dawo kan shi,da sauri kuma nurses suka turo gadon dora marasa lafiya,su ka fice aka dora mutumin aka shigo da shi.

 

Sai dai kuma suna ganin yanayin raunikan da ke jikin shi,suka ce ba zasu taɓashi ba sai an kawo Police.

 

Hussain ya ji ba dadi,amma ya yi masu uzuri yasan suna kan aikin su ne,nan da take ya kira wani abokinshi video call, police ne mai muƙamin DPO ya basu shi suka yi magana sannan aka shiga da mutumin domin ceto rayuwar shi.

 

Malam Saminu ya matso gurin Hassan ya na faɗin, “yallaɓai ko zamu tafi gida sai mu dawo gobe muga yanayin jikin na shi?”.

 

“Eh amma mu jira fitowar likitan tukunna.”

 

Sun shafe kusan awa guda kafin su samu nasarar tsaida jinin dake zuba tare da cire bullet da ke jikin shi.

 

A lokacin ne kuma likitan ya samu fitowa,gaba ɗaya jikin shi ya haɗa gumi.

 

Ya karaso wajen su yana faɗin, “A binciken da mukayi mashi munyi nasarar cire harsashi guda, ɗaya a ƙirjinshi amma daga ɓangaren hannun damansa, akwai gwaje gwajen da zamu yi amma wasu result ɗin duk sai gobe.

 

Zaku iya tafiya zuwa goben sai ku dawo, akwai nurse’s da zasu kula dashi.

 

Dr.Mors ya ida maganar ya na mika masu takarda bill ɗin da zasu biya.

 

Nan take Hassan ya yi mashi transfer suka bar asibitin suna yiwa mara lafiyar fatan samu sauki.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment