Hausa Novels Littafan Hausa Novels

Falak Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Falak Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

FALAK🍒*

_Gajeren labari_

 

Zainab Habib (Mom Islam

 

E.O.W

 

_Bismillahir rahmanir rahim_

 

morning 11:30am Thursday 29/12/2022

 

 

Page 1-2

 

 

Iska ce ke kad’awa a hankali, garin yad’auki sanyi sosai, yawancin mutane suna sanye da rigar sanyi.

Tafiya take tana yarfe hannu kamar karamar yarinya,

“Falak”

Taji an kira sunanta cikin kausasashiyar murya, da sauri ta waiga ga mamakinta sai taga babu kowa, juyowar da zatayi taga wasu mutane guda uku ko wanne ya yane fuskarsa da bak’in k’yalle, a tsorace tace “suwaye ku mekukazo yi nan?”

‘Daya daga cikinsu ya d’agata cak yasata a mota suka shiga dukkansu suka yiwa motar key, sosai take ihu tana had’asu da Allah babu wanda ya saurareta, wanda aka kira da Oga ya mika saletif aka manne mata baki, tare da wani baƙin k’yalle shi kuma aka rufe mata ido.

 

•Da sauri  ta sauko daga kan gadon da take kwance tana share zufar dake sintiri a fuskarta, jiki a mace ta nufi k’ofar da zata sadata da d’akin sauran yan matan, tana buɗe k’ofar ta hangosu a kwance sunanta sharar bacci, cikin d’aga murya tace “Munira  Hibba Saudart ku tashi nayi wani mummunan mafarki”

Suna jinta sukayi mata banza, dole ta k’yalesu ta nemi guri a gefen gado ta zauna, sbda bacci ya kauracewa idanuwanta,

A hankali taji ana cewa “ga dakunansu nan ku shiga”

Falak ta waro ido kafin ta shiga tashinsu a hankali, abin mamaki suka jingina wata sanda a jikin Falak suka fice da ita kaf gidan babu wanda ya motsa, sai da aka fice da ita daga gidan.

Cikin tashin hankali Ummu ta bod’e k’ofar d’akinsu Munira, sbda jikinta na bata babu lafiya, kallon agogo tayi taga k’arfe 1:20pm tace “yakamata ku rage wannan barcin ranan da kuka sanarwar kanku, Hibba tayi juyi tana mutsuke ido kafin tace “Ummu ai Falak ma yazo tana ta damun mu bansan lokacin data fice ba”

Ummu tace “na d’auka ko tashiga wanka ne dan naga babu kowa a d’akinta”

Saudart ta diro da sauri ta bud’e k’ofar toilet, wayam tagani babu kowa, cikin tashin hankali dukkansu suka fito sunata Zagaye kowane sashe na gidan Ammae babu ita Babu alamar ta, Ummu tasa hijab taje gurin Mai gadi ta tambayeshi, yace “tun safe yake zaune anan baiga kowa ba…..

 

Inaso inga inda zaku amshi littafin, inhar naga anyi shar’i da comments read more da yawa zan dingayi duk da labarin bame tsayi bane 08141799224

*FALAK🍒*

 

 

Zainab Habib(Mom Islam

 

 

 

Free

 

E.O.W

 

 

Page 3-4

 

Cikin tashin hankalin Ummu tayi bedroom d’inta domin ta d’auki waya ta kira  Abba, kafin takai ga d’aukar wayar taji wayar na ringing, da sauri ta d’auki wayar tare da karawa a kunnenta,

“Sunana Oga zakiyi mamaki idan nace miki yarinyar da kukafiso kukafi k’auna tana gurina, nasani duk duniya keda mijinki kunfi sonta saboda ɓoyayyen sirrin dake tattare da ita”

Ummu ta fashe da matsanancin kuka kafin tace “dan Allah ku ƙyalemin yarinya na roƙeku dan girman Allah ko me kukeso zava baku”

Ta faɗa tana share hawaye dake kwaranyo mata.

“Karki damu ba wasu kuɗaɗe masu yawa muke buƙata ba, just 10 million nera zaku bamu sai mu sake muku tauraruwarku, nasani kun mallaki abinda yafi haka”

 

Oga ya fad’a ya tuntsire da dariya, ya cire sim card d’in dayayi kira dashi ya karyashi.

Juyowa yayi ya kalli Falak kafin yace “idan iyayenki suna sonki zasu bamu abinda muka buk’ata idan kuma basa sonki zamu zauna tare dake”

Idanunta da suka gaji da tsiyayar da hawaye ta d’ago kanta tana dubansa, duk inda kakai da gane kamannin mutum to shi wannan ya gama rufe fuskarsa, iya bakinsa da ido kawai ake iya gani, ya matso zai ta6a Falak, da sauri ya matsa tare da kallon idanunta da suka sauya daga kamanninta suka juye kamar na mage (cat),

 

“Ke wacece wane sirri ne a tattare dake, meyasa mahaifinki duk tafiyar da zeyi sai yaje dake k’asar waje, bayan ga y’an uwanku nan a gida harda yayarki”

Yaje a hankali ya cire mata salatip d’in dake manne a bakinta, kafin yace “ina jiran amsarki”

Magana take amma sam baya ma jinta, sbda tsananin kyawun hallitta da Allah yayi mata, farace tass gashin kanta Shiba jaba kuma Shiba bak’i ba, asalin k’wayar idonta baki ne gashin saman idonta Zara zara sai gashin girarta data kwanta tayi luf, bakinta ya kasance d’an karami Mai d’auke da pink color kamar ansa masa jambaki.

“Mugu”

Kalmar daya tsinkayo kenan, ashe harta gama tofe masa fuska da miyau yana zaune yana kallonta, ya shafe fuskarsa kafin yakai hannu zai mareta, hannunsa bai kai ga jikinta ba wani miciji yazo ya nannad’e masa jiki har hannunsa da k’afa, tafara magana da muryarta mai d’aukar hankali tace “meyasa kakeson cutar da rayuwata , meyasa kukeso sai kunga bayan Abbana mai yasa kuke bibiyarsa ko akwai abinda yayi muku ne?”

Oga dake d’aure snake ya cukuikuyeshi yace “please ki ce ya sakeni yanzu zaki koma gida”

Falak tayi murmishi kafin tace “bance maka inason komawa gida ba, ban kuma ce maka banason komawa gida ba, abinda nakeson ji shine me Abbana yayi muku?”

Bai sanar da ita abinda ta buk’ata ba, sai ma k’walawa abokan aikinsa Kira da yayi, da gudu suka shigo, a tsorace suka kalleshi kana sukace “oga meye naga kamar snake ne ya nannad’e ka?”

A hassale yace “ubanku ne ya nannad’e ni oya ku kunceni tun kafin inzo gareku”

‘Dayan mai suna man ya taho da k’arfinsa har wani huci yake, yaje da sauri zai tunkari Ogan nasu, macijin ya d’ago kansa yana kallonsu, suka arce da uban gudu,

“Dan Allah nasan duk wannan abun bai wuce keba please nakuma rokonki akan ki k’yaleni bazan sake bibiyar rayuwarki ba”

Falak ta lank’wasa hannunta yayi k’ara, abin mamaki sai micijinan ya 6ace, tace “fad’amin”

“Daman haka kawai ne, zanyi aure bani da kud’i shine nabi ta wannan hanyar Ina. ganin zan samu abinda nakeso”

Falak ta girgiza kai kafin tace “wannan ba hanya mai 6ullewa bace, kana tunanin da kud’in sata zakayi aure?”

“Kiyi hak’uri sai da nayi hakan na gano nayi kuskure”

Kallonsa take kallo na tsanaki kafin tace “sau tari akanyi kidnapping mutane akan dalilin da sam bashi da K’arfi wannan ba hujja bace, son zuciya ne, dani zakayi auran kenan for what?”

Ta fad’a tana kuka,

“Kunfi son ku dinga tayarwa da Abbana hankali, duk lokacin daya bar Nigeria sai an yi kidnapping d’in bansan me na tarewa mutane ba”

Oga yace “Dan Allah ki taimakeni karki sanar cewa nine na saceki wlhi kasheni za’ayi”

Ya fad’a yana kuka shima harda majina.

“Sau nawa kana kidnapping mutane?”

“Sau d’aya a kanki”

ya ciro wayarsa ya nuna mata save the date na auransu, tare da hotunan da sukayi da matar da zai aura, harda hoton da sukayi dukkansu harda mahaifiyarsa.

Yace “bari a kawo mota a kaiki gida”

Falak tace “no zan tafi da k’afata” ka bani account number d’inka, karka sake waiwayata ko godiya bana buk’atar ka Kira kayimin ka godewa Allah, inhar kayi tunanin sake cutar da wani zuwa gaba, to zaka iya rasa ranka”

Falak ta fad’a tana nunashi da yatsanta.

Bayan ya mik’a mata kati mai d’auke da number ta fice a hankali tana zuwa  bakin k’ofa ta k’ara  da gudu.

Tayi tafiya mai nisa kafin takai bakin titi, ganin shigar dake jikinta ne ya mugun kunyatata, gajeren wando ne na jeans iya guwaiwa sai riga mai siririn hannu ta rufe mata cibiyarta bata k’arasa har mararta ba, cikin sa’a wata mota tayi parking a gefen hanya,

Magidanci ne Wanda a k’allah zeyi shekaru 72yrs bakinsa yana sanye da hak’orin Makkah, ya rage tsayin gilashin motar kafin yace “tafiya ne Hajiya?”

Jikinta na kyarma tace “dan Allah ka ragemin hanya ko a y’an tifa ka ajiyeni zan k’arasa”

“Muje har gida zan kaiki”

Falak tace “a’a kaidai kawai ka ajiyeni a inda nace maka, sai ka bani aron waya”

Cikin son jin abinda ya faru da ita yace “shin meye matsalarki?”

Bata bashi amsa ba ta rufe k’ofar,

Ya mik’a mata wayar kana yace “a sim one zakiyi Kiran”

“Ok” tace masa ta fara jero number da zata Kira,

Cikin sa’a Kiran ya shiga akayi sallama daga can 6angaren tace “Hamma Aliyu kazo y’an tifa a gurin masu siyar da kayan miya ka d’aukeni”

Daga can Hamma Aliyu yace “Wai meke faruwa ne yanzu nake gani a T.v, batace masa komai ba tace “gani please kazo”

Tana gama waya ta goge number tare da share zufar data karyo mata.

Sunyi tafiya mai nisa kafin sukazo inda ze sauketa, tana sauka Hamma Aliyu na isowa, tayi wa Mai mota godiya ta shiga motar yayan nata suka wuce.

Hamma Aliyu ya kalleta kafin yace “k’anwata meke faruwa naga mood d’inki ya sauya ko ankuma ne?”

Falak tace “Hamma wlhi wannan mutumin ma ragemin hanya yayi idan dady ya sake dawowa sake dawowa zan bishi bazan sake zama ana neman hallakani ba gaira babu dalili ta fashe da kuka tare da tura y’an yatsunta cikin sumar kanta tana cigaba da cewa “bansan mena tarewa mutane ba bansan menake dashi wanda yasa suke neman rayuwata ba”

Hamma Aliyu yayi murmishi ya shafi kwantaccen sajen fuskarshi kafin yace “Falak kin kasance y’ar baiwa, duk da duniya tanada fad’in da babu wani mahaluk’in da zai iya lissafa adadin mutanen cikinta, kinada baiwar da kowanne namiji zai so had’a zuri’a dake, kinada kyau mai rikita maza harda mata, kinada kwarjini, sannan kinada wani sirri wanda babu wanda ya sanshi komu ma mundaiji ana cewa kinadashi amma har yanzu bamu gano komai ba”

Falak ta ta6o hannun Hamma tana share hawayen da suka zame mata jinin jiki koda wane lokaci tace “duk naji amman inaso in dinga rayuwa kamar ku, kamar inda kuke zuwa ko Ina a kuma lokacin da kukaga dama, shin nima zan zamo kamar ku?”

Hamma ya taka burki a lokacin da suke shiga anguwarsu Falak, Bauchi road, kafin yace “idan nace miki miki eh nayi k’arya babu tabbacin zaki iya rayuwa cikin dubban mutane ba tare da kin sami gagarumar matsala ba, so abinda nakeson ki sani shine ki kwantar da hankalinki ki rage damuwa har Abba ya dawo sai musan abinda zamuyi, ni daga nan zan wuce gida ne”

“Hamma bazaka shigar dani ciki ba”

Ta fad’a cikin marairaice murya,

“Am sorry idan na shiga Saudart zata rik’eni da surutu zuwa k’arshen sati zanzo ki gaida Ummu”

“To kawai tace masa ta bud’e get din gidansu ta shiga”

Ya d’au tsawon lokacin yana kallon k’ofar data shiga, ya girgiza kai tashi d’aya tausayin k’anwar tashi ya kamashi, yaja mota ya tafi.

Mai gadin gidan na ganinta ya durk’usa yace “Hajiyarmu uwar adalci barka da dawowa”

Ma’aikatan gidan sun saba da 6atanta saboda inhar ta dawo Nigeria sai an saceta duk da wannan na hud’u kenan, koda an saceta basayi mata komai ana basu kud’i shikenan ake saketa, ta shigo main parlonsu bakinta d’auke da sallama, Ummu Saudart da Munira Hibba dukkansu suka fito, suka rungumeta suna cewa “sister Falak babu abinda ya sameki ko?”

Falak tayi murmishi sbda Ummu dan tana ganin fuskarta a cikin damuwa kwana zatayi babu bacci, Falak ta rungume Ummu da har yanzu batace komai ba, Falak tace “Ummu Ina lafiya wlhi k’alau na dawo Ummu”

Sai a lokacin kukan da Ummu ke 6oyewa ta fito ta fashe da kuka tana cewa “Falak.. kowa bashi da damuwa sai Falak, mutane suna so su kashemin kene kokuma dukiyar mahaifinku ne ya damesu?”

Ummu tayi maganar tana zubewa a k’asa.

Saudart taje da sauri ta rungume Ummu kafin tace “Ummu kowane bawa da tasa k’addarar mu k’addara itakuma tata k’addarar kenan”

Ummu ta nuna Saudart da hannu tace “Saudart meyasa Falak bazatayi rayuwa kamar y’an uwanta ba?”

Dukkansu sukayi shiru saboda suma kansu abin yana d’aure musu kai.

Kiran sallahr Magrib ne yasa suka watse kowa yaje yayo alwalah, Falak kam sai da tayi Azhar sannan ta yi la’asar tayi magrib, tana idarwa ta d’auki alkur’ani wanda ya zamo mata farilla, sbda duk bayan kowacce sallah sai ta karanta koda aya goma ne kafin tabar kan sallahya.

Tana idarwa ta d’aga kyawawan hannayenta sama tana karanto sunayen Allah tare da rok’on buk’atunta a gurinsa, tana kammala adu’ar ta shafa tare da mik’ewa ta d’auki wayarta taga miss call har 50 bata duba ko waye mai Kiran ba ta cire zumbulelen hijabin datasa ta cire kayan jikinta, ta d’auki towel ta d’aura ta shiga bathroom, saidata tara ruwa Mai yawa, ta shiga ciki tayi lamo tare da lumshe ido, d’ago kanta tayi ta kalli mirror d’in dake manne a jikin bango ta janyo gashin kanta tana wasa dashi, abin mamaki kidnapping d’inta da akayi ta dawo babu alamun damuwa ko gajiya a tare da ita, sai data seke ruwan ya tafi kafin ta tar wani tayi wanka, bayan ta wanke gashinta da had’ad’un mai,  ta fito d’aure da towel fari ta d’aure Blu k’arami a kanta, ta zauna akan stool tare da kallon yawan gashinta, ta busar da gashin tana gamawa ta shafa mai da powder sai lipstick dasata mik’e tana cewa “Ummu..”

Maganar da K’arfi take kamar inda Ummu zata iya jiyota,

Ummu na kitchen itada Saudart tace “ku kammala had’a salad d’in auta na kirana”

Ummu na shigowa Falak ta kwanta a kan kafad’arta kafin tace….!

 

*FALAK🍒*

 

E.O.W

 

Zainab Habib (Mom Islam

 

Free

 

Marubuciyar

Ladidin  ƙauye

Lamarin ƙaddarar aurena

Mk mijin delu

Nancy ƴar ƙarya

Yarinya mai taɓargaza

Diyana

Guntun goro

Nida yarinya

Zaɓinshi ne

Hatsabibiyar yarinya

Macen sirri

Tsautsayin tauna

 

Page 5-6

Ummu ta k’araso bedroom d’in cike da kulawa tace “my auta gani”

“Ummu inason zuwa anguwa gidansu Amal ya zanyi?”

Ummu tayi shiru kamar wace ruwa ya cinyeta kafin ta kamo hannun Falak tace “yakamata ki dinga kiyaye abinda yake zuwa da dawowa, Falak kinsan rayuwarki na cikin hatsari ko?”

“Yes Ummu sanin hakanne yasa nake neman shawararki”

Ummu taja dogon numfashi kafin tace “just ki hak’ura kawai, fitarki zata iya zamowa barazana ga rayuwarki ko kinaso ki sake tayarmin da hankali ne?”

“Idanun Falak sun sauya launi tana shirin yin kuka tace “meyasa bazanyi rayuwar farinciki ba, meyasa kullum a killace nake way?”

Ummu ta dafa kafad’arta kafin tace “zakiyi Falak komai nada lokaci kinji”

Share hawayen da take k’ok’arin 6oyewa suka zubo tayi kafin ta koma ta kwanta Ummu ta fita.

Tayi juyi yafi abinda yafi, zaman gida ya isheta, kwatsam ta tuno mutumin d’azu, ta janyo wayarta tare da duba wandon data cire ta d’auko number mutumin tayi masa transfer na dubu d’ari biyu, ta koma ta kwanta.

Oga, wanda a zahirin sunansa Ammar, yana zaune tare da mahaifiyarsa yaga alert na kudi, a razane ya mik’e dama ya gama bawa mahaifiyarsa labarin lefin daya aikata, tana tsaka dayi masa nasiha yaga sak’o, ya nuna mata, sai da tayi hawayen farinciki tsabar jin dad’i, tace “shikenan gobe insha Allah biki zai kankama harna fara tunanin abinda za’aci.

Germany•• anguwa Munich

Akwai wani katafaren company wanda ya amsa sunansa, abin mamaki anan shine mamalakin company d’in dady Falak ne, yanada kamfanoni uku, kaf cikinsu wannan shine babba anan yake san’ar siyarda su zinarai gwala gwalai daduk wasu abubuwa da suka shafi hakan, sosai ya k’ware a aikin, amman Falak tafishi sanin makamar aikin sbda shi ta karanta sosai wanda har yanzu take karatu akansa.

Yana tsaye a jikin glass door yazo wucewa ta bud’e, a hankali yake tafiya har ya iso wata k’ofa, ita kanta k’ofar ta zinare ce, to abu nasu.

Yana zuwa yasa hannunsa a jikin wani abu kamar waya cikin d’akin ya bud’e tacan k’asa, yana isowa wata hanya nanma ya Kuma danna abun kamar na d’azu, cikin k’warewa ya sauka a gurin tare da ciro wata kwalba mai d’auke da jini ya d’an zubashi a jikin k’ofar k’arshe nan da nan saiga k’ofar ta bud’e, innalilahi d’akin badai kyau ba, ya had’u iya had’uwa, ciki kuwa harda kujerun zinare, wayar daya gani a gurinne ya d’auka kafin yace “meyasa na bar wayata a shago?”

Wata Number ya danna kafin yace “zaku sami kujera da gado Amma fa kaya sun tashi in kunso siya”

Daga can 6angaren akace “ok a ajiye mana inma duka room d’in za’a siyar mun shirya”

Gaban Dad ya fad’i yace “no meya kawo maganar siyar da Kaya duka?”

Kashe wayar da akayi  tare da fashewa da dariya, a fili dad ya furta “Malik ya zeyimin haka?”

Sai daya gama duba kayan da suka kasance akwai da wanda babu sannan ya fito kamar inda ya shigo, yana dawowa company ya shiga office d’insa kafin ya d’auki wayar da yake using da ita a shago ya danna number Falak.

Tana kwance idanunta na kallon silin taji ringing d’in wayarta, da sauri ta janyo wayar sbda ring din da tasa a number dad d’inta kenan, ta tattaro nutsuwa kafin tace “dad ya aikin?”

Daga can 6angaren yace “lafiya lau daughter meyasa baki zaki saka ranar dawowa ba, alhalin kinsan ina buk’atarki a tare dani?”

Cikin marairaice murya Falak tace “dad ina tsoro yanzu ma na shirya zani anguwa na fasa ina tsoro”

“Tsoron me kikeyi?”

Ta kalli wayar kafin tad’anyi shiru, a ranta tace “badan da dadynta take magana ba sai tace za’a Raina mata hankali, yasan komai akan kidnapping d’inta da akeyi Amma baya mayarda abin serious,

Dady yace “Falak ki dawo ranar Saturday kinga saura one week kenan”

“To” kawai tace masa kafin ta juyar da idonta gefe, ganin Saudart ta ajiye mata sinasir,

Kasancewar katse wayar da dad d’in yayi yasa ta ajiye wayarta ta fara cin abinci, tana gamawa ta janyo laptop d’inta, tana searching company na dad d’inta ta waro ido, da sauri ta mik’e tare da had’a kayanta tace “zance dad ya sakko da tafiyar nan”

Ta ruga d’akin Ummu da gudu tana cewa “Ummu in dady ya gama yimin booking komai zanyi gaba akwai matsala gaskiya, koda na sanarwa da dadyn ba lallai ya fahimta ba”

Gaban Ummu ya fad’i fad’uwar da yasa zuciyarta karaya, tace “gaskiya dad d’inki ya hak’ura da sana’arsa ta sirri wannan barazana gamu ne dama shi kansa”

Falak tace “nooo”

“Momy hanyar cin abincinmu da magance cututukan k’asa kike maganar ya dakata, yin hakan zai iya janyo masa hallaka tunda ya rigada ya saka kansa batun yauba”

Falak ta fad’a tana mai komawa d’akinta ta d’auko laptop ta nunawa Ummu,

“Kinga wancan gurin akwai bama bamai a k’alla sunkai uku a cikin company, kinga nan ta hanyar shigowa ta can kuma ta hanyar fita ta nan ta hanyar shiga d’akinmu na sirri, so abinda nakeso ki gane anan shine, Babu mahaluk’in daya San akwai d’akinnan d’aki ne wanda aka ginashi da zinare komai nasa na zinare ne, Ummu me kikeso a bari anan?”

“Sana’ar sirri, har yanzu Falak bata fahimci menene sana’ar sirri ba, tayi zama sosai tare da dad d’inta amma ta kasa gane menene aikinsa na sirri inba company d’insu da ake kawo musu hari ba, Ummu tai shiru kafin tace “jeki shirya idan ya kammala komai ko nanda kwana biyar saiki tafi.

Tana tsaye hanunta rik’e da system wayar Ummu tayi Ring, tana d’agawa dad yace “kowa lafiya ko?”

“Eh” Ummu tace kafin tace “ya yanayin aikin naku?”

Dad yace “aiki na tafiya dai-dai amma damuwata Falak akwai abinda nake ganin ban gane ba”

Falak ta kar6i wayar kafin tace “dad banason tayar maka da hankali amma barin bud’e system ka bud’e WhatsApp yanzu”

Dad yace “karki damu na bud’e”

Tace “dad kalli gefenka na hagu”

Yace “na kalla”

“Meka gani?”

Falak ta fad’a tana sanya farin glass a idonta,

Dady ya mik’e ya tafi inda Falak ta sanar Mai, yana zuwa yaga k’ullin bom a wani abu kamar bokiti, Falak tace “dad cire wayar data had’u da wannan blue d’in, dady ya cire jikinsa na rawa ya cire yana yarfe zufar data karyo masa,

Falak tace “dad sake duba can gefen da aka ajiye kafet”

Nanma ta sashi ya cire, ana ukunne d’akin ya d’auki hayak’i sosai, Falak da Ummu sun shiga damuwa sosai, Saudart ta shigo tana goge hannunta kasancewar tunda Ummu ta dawo gurin Falak sukuma suka koma kitchen, ganinsu a wannan yanayin yasa Saudart tsayawa tana kallon abinda Falak keyi, Ummu ta fashe da kuka tana cewa “ka fita karya tashi dakai”

Falak ta kuma yarfe zufar data karyo mata  kafin tace “dad ba damuwa zamu tsaya yiba dad kayi k’ok’arin cire igiyar data d’aure batir d’innan”

Hannun dad na rawa yasa hannu gurin hayak’innan yana bala’in jin zafi a hannunsa ya fincike har yana fad’uwa, daga cikin videon da su Falak suke kallonsa sukayi tafi, Dad yace “Falak d’azu naje na gama komai na tahowarki nanda kwana biyar ki shirya”

“Okay Dad”

Falak tace “dad Saudart nason biyoni” Dady yace “no karta sake tazo sbda baby abinda zatayi, kema aiki ne yasa nakeson ki dawo”.

 

Switzerland Maleek

Zaune suke su biyu, Maleek da Manaf wato k’aininsa haka suke kiransa, Maleek na sanye da wani farin abu ya yane kansa dashi, abun hangen nesa ne a hannunsa cike da masifa yace “Abdurraman ya mayar dani wawa jaki bansan me nakeyi ba, ya juyar da kansa gefe tare da cire abinda ya yane kansa dashi, bak’in sumar kansa ne ya baiyyana kasancewarasa fari bature, Manaf yace “Yaya nifa abinda ban gane ba shine, zai seyar mana da wannan d’akin sirrin ne kokuma a’a?”

Maleek ya bushe da dariya, ya ta6a kafad’ar Manaf kafin yace “ko ya siyar dashi ko kar ya siyar dashi babu buk’atar sake amincewarsa a komai, shegiyar yarinyar da yake gadara da ita ai bata wajensa ta koma Nigeria, inhar Abdurraman yayi kuskuren tunzuroni tabbas sai ya gwammace da baizo duniya ba, sosai nake d’aga masa k’afa, naso ace ya amince da auran Diyana da nace zan bashi, duk da yawan shekarunsa amma sai yayi burus kasan “y’an Nigeria da taurin kai kuwa?”

Manaf ya fad’a yana kallon Maleek,

Maleek yace “dole ze saukeshi jigonsa bata nan, duk ranar data dawo a hannuna zata kwana bayan haka insa a 6atar da kabarinmu mu tafi wata duniya, duniyarda shi kansa bazaiyi tunanin zamujeta ba”

Manaf yace “nikuma Yaya inda nine kai Babu ruwana da y’arsa shi zan kaiwa hari”

Maleek yayi tsaki mtsw, maganar hakan bata taso ba bakada hankali, wannan yarinyar tasan komai itace sirrinsa akwai abinda ita ta sani shi bai sani ba, yanzu kana zaune zata hango abinda ke cikin lungu da sak’o na gurinnan da muke, shiyas nakeso ta zamo babyna in biyata mu dinga aiki tare tunda naga yarinyar wayayyace”.

Suna cikin magana, wayar Maleek tayi ring, ya d’aga da sauri yana cewa “wow Kaya sun iso lafiya?, a wuce dasu kawai inanan shigowa zuwa anjima”

Ya katse kiran, Manaf yace “wato Kaya na tafiya indaya kamata, zomuje kawai saboda akwai abubuwan da zamu gudanar.

Kai tsaye suka shiga mota, Manaf na driving Maleek na bashi labarin inda zasu cigaba da gudanar da aiyukan safarar kayan nasu, suna isowa Maleek ya fara fitowa a hankali cikin takunsa na k’asaita, ya shiga d’akin da aka sauke kayan, Manaf na yabi bayansa, suna cikin tafiya sukaji kamar motsin mutum, har sun tsaya suna dubawa ganin basuga kowaba yasa sukaci gaba da tafiya.

Mutanensa su biyar suka samu a ciki, kowanne da aikin da yakeyi, masu d’urawa a wasu k’ananun leda nayi masu zubawa a buhu sunayi masu zubawa a y’ar roba suma sunayi, guri ya cika da aiki Maleek yace “gaskiya Alhmdulilh ansami riba a wannan karon ninkakkiya naji dadi, zamu sake gina wani gurin a wata k’asar ba wannan ba, amma maganar nan ta zamo sirri tsakanina daku”

Mutanen gurin sukace angama me gida, a hannunsa yasa kafin ya sheka yace “uhnnn ahhh, sabon d’auka sabon farashi sabon sari sabon aiki, hhhh” dukansu suka kwashe da dariya.

Falak na kwance tana kwatanto Switzerland da abubuwan dake faruwa, abin tana ganinsa kamar a mafarki ne Wanda takejin hakan har cikin ranta, me dangantakarta da lek’en sirrin wasu bayan ga babban aiki a company d’in dad d’inta?.

 

Duk meson karantashi ta group d’ina ba WhatsApp yayimin magana mata zallah please Banda Kira 08141799224

#Team Falak

#Team Maleek

#Team ohooo waye naku wai yan Facebook bana kun sani Happy banyi tunanin zakuzo littafin sosai ba, yan WhatsApp kuwa babu me godiya daga wannan page din inhar ba shar’i ko comments bye bye zanje Facebook incigaba.

 

Mom Islam

*FALAK🍒*

 

Zainab Habib/ Mom Islam

 

 

E.O.W

 

Page 7-8

A Zaman Duniya Hausa Novel Complete

Wayarta ta d’aga ta danna number Hamma Aliyu, kamar dama jiran Kiran nata yakeyi ya d’aga da sauri kafin yace “k’anwata”

Falak ta turo baki kafin tace “Hamma Aliyu har zan tafi bazakazo ba?”

Ya mayar mata da maganar kamar inda tayi masa yace “uhm Ina hanya ganinan”

Ta daka tsalle tana murna ta ajiye wayar, da gudu ta tafi d’akin Ummu, ta sameta a kwance tana bacci, cikin d’aga murya tace “Ummu Hamma na yana hanya”

“Kai Falak na gaji ne yasa na kwanta yanzu kuma ba lallai baccinnan ya d’aukeni ba”

Ta rungume Ummu tace “da izinin ubangiji zai d’aukeni harda mafarkin dad nayi miki wak’a kekuma kina rawa”

Ummu ta lumshe ido batace mata komai ba, d’akinsu Saudart da Munira da Hibba ta shiga wanada d’akinsu ya kasance a had’e nata kuma ita kad’ai, tana shiga ta samesu ko wacce hannunta rik’e da waya da alamu chart sukeyi, tace “hello” suka d’ago suka kalleta fuskokinsu d’auke da murmishi cikin had’in baki su biyu sukace auta lafiya kodai dad ya siya miki motar da kikeso ne?”

Falak ta zauna kafin tace “Hamma ne yake hanyar zuwa shine nazo gaya muku aunty Saudart naga kamar bakya farinciki”

Hibba tace “kyaleta itafa tace tana sonsa dan an matso da biki shine zaki wani dinga cin magani”

Saudart ta bige bakin Hibba suka fashe da dariya,

Ajiye wayar Saudart tayi ta sauko a hankali ta wuce kitchen,  abinda ta tabbatar yanaso tayi masa wato dankalin turawa da mai da yaji, idan zezo ta shiga kitchen dafa masa su Hibba suyita mata dariya, yauma kamar kullum kasancewar itace babbarsu suka shigo suka fara sana’ar tasu, bata kulasu ba taci gaba da aikinta, tana shirin saukewa wayarta tayi ring, a hankali ta d’aga kafin tace “my sweetheart kacemin kana hanya na jika shiru”

Hibba da Munira suka toshe baki suna dariya wai Saudart kamar ta shiga makarantar Love, tana ajiye waya ta juyo ta kallesu ta galla musu harar lokacin da ta juyo abincin a foodflaks, takai d’akin da suke saukar bak’i.

Falak ta k’walawa kira ta amsa kafin tace “inzo ne?”

Saudart tace “Baby ya iso yana kiranki”

Ta rufe abokiyar aikinta wato laptop ta fice waje, tsaye ta sameshi ya zura hannayensa cikin aljihu yana ganinta yace “Wai naji muryar antynki wani iri shin meke faruwa?”

Falak tace “Babu komai” yanzu bana nan za’ayi bikinku?”

Ta share siraran hawayen daya zubo mata,

Hamma Aliyu yace “ai kamar kina nan ne tunda zakiga komai kamar kina gurin.

Ta kawar da maganar da cewa “dad yace saura kwana biyar yau saura kwana hud’u in koma.

Ya rik’e hannunta suka shiga ciki.

Kai tsaye ta wuce d’akinta ta koma bakin aiki, shikuma ya fara rangad’a sallama kamar inda ya saba dayazo yake cika musu kunne,

Saudart ta taho da sauri tana sanye da riga da wando, sun kamata sosai kanta tasa hula wacce bata k’arasa rufe mata gashin kanta ba,

Ta kamo hannun Hamma Aliyu suka shiga d’akin da abincin yake tace “uhm mutane basa son surutu kaikam ka fara ko?”

‘Dabi’unsa da bata cika soba shine, dayazo sai dai ta zauna akan cinyarsa, hakan akayi dayaci dankalin ya dinga santi yana cewa “shifa a k’ara dafa masa, Saudart ta turo baki kafin tace “am dama inason sanar dakai jiya da mukaje kasuwa Kaya sun tashi” ya k’yalk’yale da dariya kafin yace “to Banda abinki ATM d’ina fa yana gurinki nace harda auta a siyawa duk abinda takeso”

Falak

Cikin tashin hankali ta tura hannayenta a cikin gashin kanta, a tsorace tace “ina dad ya shiga wayo Allah na!!”

Ummu ta shigo da sauri tana cewa “auta kukan me kikeyi?”

Falak tace “Ummu zokiga zokiga inda wannan mugun ya shigo shagon dad yake kwasar kaya wai duk cc tv babu wanda ya gansa abin ma dai abin mamaki”

Ummu ta zaro ido cike da damuwa kafin tace “to ki kirashi a waya mana”

“Bata shiga”

Falak ta fad’a tana kuka.

Germany••

Dad zaune a masallaci, yasan akwai masu kula masa da kayayyakinsa dan haka koda yaushe idan ya shigo masallaci baya fitowa da wuri, sai yayi adu’oi sosai wani sa’in ma yayi bacci, yana zaune yaji jikinsa bai bashi ba, kamar akwai abinda ke shirin faruwa, ya fito tare da sanya takalmi ya dawo shago, ga mamakinta yaga ma’aikatan gurin sunata kaiwa da komowa ana gudanar da kasuwanci dai-dai, ya zauna tare da hawa whtsapp, abinda yaga anyi screen shot an turo masa ne yasa hankalinsa tashi yace “Falak idan baki dawo ba zan iya samun matsala”

“Nasan nayi asarori masu yawa amma zanso ki zauna ayi bikin Saudart ana kammalawa sai ki dawo”

Dad ya ajiye mata a WhatsApp ya sauka.

Hankalinta yayi nisa sosai saboda wasu abubuwa da bincikenta ya bata tabbas akwai masu harin shigowa dad d’inta wannan d’akin na sirri d’akin da ya kasance shine gatan mahaifinta duk Wanda suke a waje ko an had’asu bazasu kai kwatan wannan d’in ba,

Kamar ance ta duba WhatsApp, tana dubawa taga sak’on dad, ta buga tsalle ta taje ta tashi Ummu tana gaya mata, itama Ummu tayi farinciki sosai dan koba komai zata shiga cikin y’an uwanta ayi biki da ita,

Gadan gadan aka fara shirye-shiryen biki komai akace anaso sai dai dad ya turo da kudi,

Sosai gidan Saudart yayi kyau gunin sha’awa gashi madai-daci sai uban kud’i da aka kashe masa,

Biki ya rage saura kwana uku, kaf gidan suka tafi wankin kai da lalle, Banda Ummu dake gida tana had’a wa Saudart turaruka, sbda sana’ar Ummu kenan siyarda turaruka da kayan gyaran jiki.

Duk cikinsu babu wacce ta kama kafar Falak a kyau, zanen bak’in lallen nan kamar dan ita aka yishi, ga gyaran gashi da akayi mata suka dawo gida a gajiye,

Kowacce tayi d’akinta, sallah kawai Falak tayi ta kwanta sakamakon gajiya da tayi sam ta rasa nutsuwarta haka kawai take jinta babu dad’i, Ummu ta shigo hannunta d’auke da yam balls ta ajiye akan table tace “auta naga kinaso”

Falak ta sauko a hankali ta rik’e hannun Ummu tace “Ummu kiyimin adu’a inajina cikin wani yanayi na rashin jin dad’i”

“Inasha Allah Babu komai auta ki kwantar da hankalinki”

Falak tace “to Allah ya kare mana dad”

Ummu ta amsa da “amin”

Switzerland

Kwashewa sukayi da dariya Maleek yace “mutumin nan da kuke ganinsa d’an Nigeria ne amma brain d’insa tafi tamu kawo light duk inda kuke tunaninsa ya wuce nan, a wannan karon mun samo zinarai na lak500 zuwa gaba wannan d’akin da yake tak’ama dashi zamu d’auko duka”.

Manaf dake gefensa yace “samun yaswirar gurin shine abu na farko daya kamata muyi inhar muka samu shine komai zezo da sauk’i.

Wayar Maleek tayi ring, ya d’aga cikin kausasashiyar muryarsa yace “sau nawa zan gaya miki idan ina cikin wannan yanayin karki sake ki kirani”

Ya ajiye wayar, Manaf ya mik’e cikin kulawa yace “kabarmin komai a hannuna ai acikin mutanen da suke jikinsa suke masa aiki a company akwai abokaina zanyi amfani da hakan ko nawa sukace sunaso zamu biya inhar d’akinnan zai zamo mallakinmu”

Maleek yasa dariya yace “k’anina shiyasa nake sonka bye”

Manaf na tafiya Maleek yayi wata muguwar dariya kafin yace “kaima kana gama min aiki kasheka zanyi bakada amfani Sam a cikin wannan rayuwar tawa”

Ya mik’e tare da gyara zaman rawanin daya d’aura a kansa, kai tsaye ya wuce gida.

Yana shiga ya samu yarinyarsa ta dawo gida kasancewar ta kammala karatu dawowarta suke jira, tana ganinsa ta taho da gudu ta rungumeshi, kafin tace “Papa Ina Arif?” Maleek ya basar da zancen ta hanyar cewa “kin huta kuwa? Ina mamanki tazo ta kawo mana shayi”

Cikin shagwa6a ta rungume Maleek ta Kuma mai-maita “papa Ina Arif”

“Beauty kinason ranki ya 6aci ko? to Arif yana Nigeria gurin abokinsa shikenan”.

Gabanta ya fad’i tasan har yanzu papa d’inta bazai k’yale dad d’in aminiyarta Falak ba, shin Anya tunda ta dawo makaranta ta gama bazata taya Falak farautar mahaifinta ba kuwa?”

Maleek yace “kinyi shiru muje mana”

Jiki a sanyaye beauty ta wuce ta barshi a guri , ta fad’a d’akinta tare da danna number yayanta Arif, sai da wayar tayi ringing sau uku sannan ya d’aga murya irinta mai maye yace “waye ban gane dake ba?”

“Yah Arif badai ka koma halin dana hanaka ba, da mukayi alk’awari akan cewa zaka fasa?”

“Arif ya Katse Kiran tare dajan tsaki mtsw”

Beauty ta fice da gudu ta hau steps zuwa gurin mom d’inta, tana zuwa ta ganta kwance akan kafar Maleek tana kuka tace “mom har yanzu Yah Arif bai dena shaye-shaye ba”

Maleek ya daka mata tsawa kafin yace “6acemin da gani ke wace irin yarinya ce kamar aljana anya ke jinina ce kuwa?”

Mom d’in beauty ta girgiza kai kafin tace “haba Papa me yasa kake irin wannan furucin bayan kasan beauty gaskiya take fad’a”

Maleek ya turo mom a hassale yana cewa “wannan yarinyar da kike gani batada hankali shiyasa bana sake mata fuska inhar nace zan sake mata zata iya fad’ar koma menene.

Beauty na komawa d’akinta taje gurin window ta bud’e labule tana ganin inda sararin samaniya ya had’a ga wani gagarumin hadari da yake had’uwa, da sauri ta zame k’asa ta furta “subanallah”

Daga nan ta jingina da bango tana hararo irin binciken da zatayiwa Arif shin kodai papa ya sashi wani aiki ne?, dan karsu gano yasa take 6oye musu”

Allah shine ya barwa kansa sani.

Nigeria

Kano

Yau Fulani day na Saudart, a inda Falak tayi shigar Fulani tayi kyau kai kace itace amaryar,

Gidan Ummu an cika sosai y’an uwa da abokan arziki kamar ranar ne biki,

Wata mata tazo tana washe baki tace” maman Saudart ashe kunada y’a baturiya ban sani ba? ina yiwa yarona kamu”

Murmishi kawai Ummu tayi kafin tace “Allah ya nuna mana”

Yawancin mutane basu san Falak ba, kasancewar ba a Nigeria aka haifeta ba, amman y’an uwan momy sun santa.

Washe gari ta kasance d’aurin aure, sunyi kyau yauma dukkansu hud’un kayan jikinsu iri d’aya, sunyi shigar weeding gwn ko Ina suka gifta photo ake yi musu, k’arfe hud’u 4:pm motocin d’aukar amarya suka iso, Saudart tayi kukan rabuwa da Ummu kamar me, itama Ummun tayi kuka sosai saboda d’a da uwa sai Allah, yayar Ummu ta kamo hannun Saudart zata shigar da ita mota, Saudart tace “Ina Falak?”

“Innalilahi wa inna ilaihir raji’un” Ummu ta ambata lokacin da taji ance ba’aga Falak ba, hankalin kowa ya tashi Munira ta fasa ihu cikin tashin hankali tace “shikenan ankuma d’auke y’ar uwarmu Falak me kikayi musu, keda ba fita kikeyi ba?”

“Ummu ta fad’i k’asa sumammiya”

Mutane sukayo kanta, hankalin su Saudart Munira da Hibba duk ya tashi, Saudart ta koma cikin gida da gudu tace “indai ba’aga Falak ba bazata jeba”

Babu wanda yayi yunk’urin takura mata, sai komawa da motoci sukayi jiki a sanyaye..

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment